Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya bata mata rai a skull sai ta sauke akaina, maman Suhaila tayi dariya tace kice iffatun dai har yanxu hukumace kenan suka dara gabaki dayansu... ***** Ranar iffaat tana zaune gindin bishiya a makaranta tana shan malt da snack sai taji wasu yan mata suna tadi akan soyayya ta kuwa kashe kunne, dayar take bada labarin cewa tanason yaron qanin baban ta amma batasan yanda zata bullowa abinba tana bayanin duk abinda takeji a ranta game dashi dayar ma tana fadar nata keni Zumar abinda yafi bani haushi baimasan inayi, Zibraheeem tace kar kuwa kisake ya sani Dan raini ne zai shiga tsakaninku. Iffat sai taji d same da abin da takeji suma shi sukeji, ta juyo ta kallesu sun girmeta duka ta musu sallama, please tambaya ce dani, naji kuna wata magana, yanxu kuna nufin duk maijin wayannan abubawan da kuka fada shine me,?? dayar tace its mean ya fada tarkon soyayya!! ta kallesu, kuna nufin nima na fadane? Toni wa nakeso?? Suka kalli juna suka kwashe da dariya, mu muka San Wanda kikeso, dayar tace Wanda kikejin haka akanshi shi kikeso!! Ta zare Ido kuna nufin YAYA FARHAAAH NAKESO?? suka kalleta sukayi tsaki ke baquwace yarinya dayar tayi dariya tace kinji suna mai dadi daji gayen zai hadu, daji akwai zafi a gunsa har naji inasonsa !! Iffaat ta juyo a fusace keeee ta wanketa da mari..... [11:28PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??47 Na Hauwa M. Jabo Yan matan gaba daya suka miqe tsaye, dayar ta gefe ta kwasheta da mari itama dayar taci kwalarta suka mata lilis,duk sun buge mata fuska, suna tsaka da dukanta saiga baba sajeen yana kora kamin yazo sun gudu bai tsaya duba halinda iffaat take cikiba kawai yaganta kamar tsugune yahau zuba mata bulala tun tana kuka har tayi shiru. Ke wace irin mai taurin kaice? Maza ki tashi ki wuce class bai tsaya kulataba ya hango wasu yara biyu ya bisu a guje suka tsere, iffaat dai an mata lilis baki sai jini yake yaji duka gun yan mata gashi baba sajeen ya qara mata wani, tana nan gurin taji ana cewa still tanananfa, kixo mu dubata, nidai baxanjeba ke kije , habadai sabida kefa na daketa kuma kice bazakijeba, please kixo muje, sukazo gurin iffaat sai kuka ganta tana xubar da jinin baki da hanci duk hijabinta ya lalace, nidai jabo abin har mamaki ya bani wai iffaat ce take daukar xilla yau!! Rayuwa juyi juyi....!!! Suka dagota suka tallabota hannu biyu dayar ta ruga ta siyo pure water Leda daya sukaxo iffaat bata iya koda magana, suka wanke mata jikinta suka qaro ruwa suka wanke mata hijabinta da duk gun da jini ya bata, dayar take gulma a hankali tace kalli gashinta! Dayar tace ummm nagani, suka kalli iffaat wacce ta bige mata bakince ta fara bata haquri, sai dayar ma tac ci gaba da bata haquri batace dasu komai ba, hasali ita batajin zafin dukanda aka mata illa xafin Cewar da akayi Yy farhaaan takeso.! Sunata bata haquri ita kuwa tanata tunaninta.! Wai yaza'ayi taso saurayin yayaryta? Yaza'ayi taso Wanda nake kallo a matsayin yayantaa? Lokaci daya ta tuna da rashin kamun kansa shegen Neman mata, ta tuna duk wani iskanci nata yasanshi, shine yafi kowa sanin WACE CE ITA, har abada baxai karbi soyayyar taba, idan ma zai karba yazatayi da yayarta Suhaila, anya ma gaskiya suka gaya mata da sukace sonshi takeyi,??? [11:32PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 48 Na Hauwa M. Jabo Tayi ajiyar xuciya Ta juyo ta kallesu sunyi cirko cirko dasu, da kunburarren bakinta take musu magana, kiyi haquri Dan Allah wallahi bansan lokacinda na daki qawarkiba, sukace ba komai kema kiyi haquri, nan dai suka yafi juna suka qulla qawance da ita da alqawarin zasu taimakamata da duk abinda sukasan zasu iya. Haka suka zauna Kowa shiru har aka tashi makaranta.. *** iffaat na zuwa gida mama ta fara tambayar ta lafiya kike kunbura haka kamar jabo tayi kuka?? Wallahi mama anyo korane, zasu shiga class tayi karo da wata frnd dinta sai kuma ta fadi qasa shine bakinta ya kunbura, Subhanallahi. Kinga yanda kika kunbura kuwa? Allah ya tsare gaba ta amsa da amin ta wuce dakinta. Bayan ta shiga daki ta cire uniform, ta zauna ta fara tunanin abinda yan matannan suka fada tabbas kuwa idan har abinda suka fada shine kaji kanason mutum to wallahi tanason Yaya farhaaan, aiki jaa wanda zai zama mijin yayarta takeso?? Dole ta dauki mataki wa zuciyarta.! Tayi murmushi Kai amma so shegene shine ya hanata sukuni shekara da shekaru! Amma so ya wanketa! Waima miyasa bata ganeba? Tayi tsaki ni ko zan mutu zan auri Yy farhaan ne gashi da shegen son mata! Duk maganar da takeyi aranta takeyinta amma Sam zuciyarta bata aminta da ko kalma daya tataba, kawai tana fadane amma tasan yanda takeji da gudu idan yace yana so zata amince,... Hmmmm dole zuciya taso Yy farhaan ta saba dashi, yy farhaan duk inda namiji mai lfy zai shiga yana shiga haka tayita karanto siffarsa da maganar sa da tafiyarsa da murmushinsa tana murmushi, lallai ta yarda tanasonsa but miye mafita??? Dole ne ta ijiye sonsa taci gaba da danneshi har Allah ya bata mijinta tayi aure?? Anya zata iya kuwa?? Zaki iya mana dayar zuciyarta ta bata amsa aiki ja gabanta.. Suhaila ce ta shigo tana waya ta gane da farhaan take wayar kuma taji yanayinda ta saba ji amma ta basar..... [11:37PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 49 Na Hauwa M. Jabo Ta juyo suka hada ido Subhanallahi sister miya sameki? Tambayawa kawai tayi batayi tunanin samun amsa ba, Dan tasan halin mutuniyarta, cox jiyama da dare ma kamin su kwanta bacci sun sayar da hali.. Ta miqe zaune Ki bari kawai Yy Suhaila..... ta bata labarin abinda yanda ta baiwa mama labari, Eyyah kinji yy farhaan yaba miki sannu Allah ya kiyaye gaba, sai kuma taji sanyi aranta, nagode bani mu gaisa, ta karba tana karba ya fara mata tsiya anya faduwa kikayi ba tsokana kikayiba aka miki duka? Tasa dariya. Laaa wallahi aah faduwa nayi, koda naga yanzu kin natsu kamar bakeba,amma kinfi kyau da qiriniyafa, tayi dariya sai mu samo miki miji mu aurar dake kowa ya huta, kar kuma mu samo ki kashe Dan mutane da rigima, da yake Suhaila tanajinta itama tayi dariya, Yy Suhaila karbi wayar ki kinji tsiyar da yy farhaan yake min ko !? Ta bata waya chike da nishadi, Ta shiga bayi ta kalli kanta a madubi taga yanda ta kunbura kamar rukayyah qawarta ta qauye Dan haka fuskanta take kamar fulawa ta kwana ta tashi, tayi wanka ta fito, tanata Jan Suhaila da hira itadai Suhaila abin mamaki yake bata, cox tun dawowarta ba ranar da basa saida hali har ta saba, idan basuyi da safeba tasan kamin a kwanta sai anyi, dama ita bamai kulawa bace, haka bata baiwa Abu muhimmanci...! ********* Tun daga wannan ranar iffaat ta daina fada da Suhaila idan taga tana wayarta sai ta tashi ta fice gun mama ko ta danna eir ps dinta tana sauraro waqoqinta. Ataqaice dai sun daina fada da juna, bata kula da ita idan tana abinda tasan zai bata mata rai, Iffaat itada qawayenta. skull mate dinta zainb Ibrahim da zainb Umar da ita iffaat Habeeb, da yake sunan baban farhaan take amfani dashi tun lokacinda ya sakata makaranta har yanxu. Zan iya ce muku ZZ sun ninka su dijee iskanci da rashin kunya kowa yasansu a makarantar kuma anqi korarsu sai suka hadu da iffaat Habawa sai abin ya qaru dama iffaat ba bayaba soyayya ce ta dangwasheta amma yanxu kam ta gano bakin zaren so bonewa takeyi bata baiwa abin muhimmanci Sam duk da tana jin zafi cikin ranta... [11:43PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 50 Na Hauwa M. Jabo Suna zaune gindin bishiya sun fito break aka fara kora ko ajikinsu tadinsu suke yi suna baiwa iffaat shawara kada ta yarda ta nuna tanason farhaan harma yanda suke gida daya da wacce zai aura, daga sama suka ji bulala akansu Malam tunde ne zibraheem ta tashi ta riqe bulalarshi, haba sir miyasa kullum sai ka riqa dukanmu Dan muna kunyar Kane kawai muka sharewa but gaskiya ya isa haka.! Ta fuske, ki sakarmin bulala Mara kunya, sai nayi maganinku a skull dinnan, duk da English suke zancen nan. Da hausa zumar tace saidai muyi maganin juna bayajin hausa so baiji mi sukace ba, yadai qyalesu ya wuce gaba abinsa, iffaat tace malamin nan Dan rainin wayo ne, suka kama hanya ko wacce ta kama hanyar clss dinsu da yake duk yara sun shiga clss sai su gagararru. Koda iffaat taje clss malami ya shiga kuma Malam jocob ne baya wasa ko kadan,economic master, ta fuske yace from ware? Tace daga gidanku da hausa ta fada duk clss suka saka dariya, Habawa yaji haushi ya gane zagin sa tayi ya fara zuba mata bulala taji zafi tuni tayi cikin sa tana duka ta kamashi da kokowa clss ya dau ihu ana buga table, saida sukaci uban juna kawai ta saki jiki ta fadi wai ita mai aljannu so aljanun sun tashi, dama su ZZ sun gaya mata cewa tayi iskancinta idan ta qare ta fadi kawai ita batasan tayiba, Kaji iskanci... Haka dai akasha oga jocob a banxa gashi ta wawwaskamai mari ta karyamai glass.. Tofa iffaat hatsabibanci ya dawo. Akaje gun principal tace ita sam batasan tayiba sharri ake mata, haka a ka rufe case akasha oga jecon a banxa. Wata rana suna zaune suna tadinsu kowa ya tafi class saisu kawai saiga principal ta biyo hanyar duk yara suna clss amma su suna nan zaune kamin ta qaraso iffatu tuni ta haye bishiya, principal taga hawanta amma bata San kowayeba, iffaat kuwa tayi tsanda a hankali ta hau rufin classes din kamar mage taje qarshen rufin ta diro qasa, koda taje class ta tarar malimi ya shiga yana note ta lallaba ta shiga ba tare da ya gantaba tayi sauri ta dauko note book ta fara rubutu. Tana fara rubutu saiga principal tare da ZZ akaxo nemanta, malamin mu yace lallai koda ya shigo ina clss din, students dinda suka ganni sukace yanxu Na shigo malamin yaji haushi kuna nufin kunfini ganine ko qarya nakeyi? ya za'ayi mutum ya shigo clss banganshiba..... [11:50PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??51 Na Hauwa M.Jabo Duk sukayi tseet principal taja su ZZ aka Basu punishment mai tsanani dama ansha kawo qararsu gaskiya sunji jiki ba kadan ba ga duka ga uban aikinda aka sakasu, duk sun kamawa iffaat mutunci sunqi mata magana, aka tashi suka kama hanyarsu itama tayi banxa dasu. Gobe sukazo nan ma gaba sukeyi sun shirya mata sharri da zataci duka amma bata saniba tazo ta musu magana sukayi banza da ita har ta juya sai Zumar tace ke banza ce wallahi, jiya shine kika gudu kika barmu, mufa duk wani hanyar dojewa mun koya miki amma ke baki koya mana komaiba kalli Dan Allah jiya yanda aka lallasamu, ta nuna mata hannunta dayasha bulaloli. iffaat tayi dariya son ranta sannan ta Basu haquri suka fara tambayar ta ya akayi daga saman bishiya ta wuce clss? Harda baba sajeen aka saka yahau bishiya amma baki ba labarin ki tayi dariya sosai lallai bakusan iffaatu Yar mamaba nan ta Basu details yanda tayi sunata mamaki lallai wannan yarinyar mayyace, kuma hartashiga class malamin bai gantaba...... Sun shirya mata sharri ZZ kenan sun hada mata gadar zare sukace sujee baya, sunje baya kuma an hana xuwa wajen da yake iffat bata taba zuwa gurin ba, kuma batasan an hana zuwa gurinba suka turata sukace suna zuwa, har ta shiga sai kawai ta hango bishiyar mangoro ya nuna tayi murmushi haba Ashe dadi suka turota tasha tuni ta haye bishiya ta fara tsinko mango tana saman bishiya kawai sai taji maganar su da wani malami wallahi tananan kullum nan take zuwa mun gaya mata an hana zuwa tace ba ruwanta. yanxu ma mungaya mata zamu fada muku tace sai dai a kasheta, kaji mugayen qawaye.... Iffaat tanajin haka tayi tsanda daga saman bishiyar tahau garu ta dira a toilet, ta barsu a gurin, taje da gudu ta kira principal tace tana bayi taji maganar mata da maxa a bayan skull principal taje da sajeen koda akaje aka gansu duk sun cire hijabi suna Neman ta wai ko ta hau bishiya coz ta gaya musu ta iya hawa bishiya ko wace irikuwa. jikinsu ya fara rawa ganin principal tana zuwa ta fara yiwa Malaminda yake tare dasu fada mi yaxo yi da yayan mutane anan bayan an hana zuwa anan tasa aka tafi da su ZZ office.. iffaat tayi wata dariya ta musu gwalo aranta tace wallahi saidai Ku wahala duk case dn dana shiga a duniya zan iya fitardakaina yanxu ya rage naku ta kakkabe hunnu ta qara gaba..... Muje zuwa. [11:13AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 52 Na Hauwa M.Jabo Anje dasu office ana tuhumarsu da aikata lalata, Dan yan iska kawai suke zuwa gurin kuma duk Wanda aka kama gurin qa'idace korarsa za'ayi da sukaga lallai korarsu za'ayi suka fara kuka suka fadi gaskiya principal abin ya bata dariya tace a kira iffaat aka kirata akace ta fadi gaskiya ko a hadasu a koresu ta fuske tace gaskiyar kenan yanda ZZ suke kuka sai suka bata tausayi, sai kuma ta tuna da ita aka kama korarta za'ayi imani dai ya shigeta ta fadi gaskiya... abin ya ba kowa dariya wato ko junansu basu bariba sharri suka mata tafisu zama yar duniya ta rama, nan dai aka shirya su aka musu fada akace suje class tun a hanya iffaat take musu dariya tana maimaita abinda ya faru tun suna daurewa har suka fara dariya lallai iffaat taci jinjina duk abinda takeyi Allah yana taimakonta...... Akwai lokacin da iffaat tayi zazabi aka bata maganin mura da maganin bacci to maganin yana Jakarta ne, sai kawai ranar tayi lettin shiga clss to malamin akwai shegen gayu da jiji da kai kawai ta karbi permission tace xataje bayi da gyar ya barta ta fita taje ta siyo drink ta bude ta saka maganin baccin har guda shida a ciki ta girgiza ta kulle ta baiwa wata students tace ta kaiwa malaminsu tace inji anti funke. Aka kawo masa yana mamakin funke zata kawo mai drink yace bari yayi sauri ya shanye kar azo ace ba nashi bane, ya zuge banxa ko minti biyu ba'ayi ya buge da bacci iffaat sukayi iskanci a clss sir na bacci sannan ta daukeshi hoto a wayarta ta bayan kowa ya qare aka tayar dashi bacci ya fara na yan giya tamai video, yanata sunbatu yana fadin ya akayine baby??wallahi saida aka kwasheshi ranar cox ya kasa ko bude idonsa.. Goben ranar aka saka bincike amma ba Wanda ya gano anti iffaat... Kai iffaat manyan duniya. Kuma haka tayita tura video da hoton nasa gashi malamin Dan gayu da jiji dakai tuni ta zubar mai da clss a gurin yan matansa da sauran students, yanxu sunansa ya koma ya akayine?? Cox lokacin da aka tayar dashi bacci sai ya fara fadar ya akayine baby yana layi.... Wasa wasa iffaat Iffaat an kai Ss2 su ZZ kuwa ana final year sun yi hatsabibanci bana wasa ba har andaina kulasa kuma iffaat ce leader dinsu....... [11:21AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 53 Na Hauwa M. Jabo ******* An saka ranar auren Yy farhaan da Yy Suhaila 20/5 daidai da ranar brdy din Hauwa jabo. Tunda aka saka ranar auren iffaat sukuni ya qara kubce mata saidai ta fuske takeyi tayi harka amma tana azabtuwa matuqa, ta fadawa ZZ suka bata shawara taci gaba da haquri kawai.. Lokaci sai matsowa yakeyi ita dai mama ta rasa gane sirrin zuciyar iffaat farko ta gano cewa tanason farhaan ne musamman lokacin da ta suma, nan zatoñta ya zama gaskiya, sai kuma yanxu komai ya tsaya mata yanda iffaat ta chanxa gaba daya duk wani Abu da take da wa suhaila batayinsa yanxu, hakan yana basu mamaki sai kawai suce ta qara girmane.... An fara shirye shiryen biki su iffaat da farahnax sune qirjin biki dama farahnax ta hada auren, shi farhaan irin ya nuna yanason suhaila irin soyayyar shan minti sai kawai farahnax taje ta fadawa su umma, kuma Suhaila ce keson farhaan sosai shi ba wani sonta yakeba, amma ganin iyayensa sunshige gaba yasa ya sallama ko banxa Suhaila kyakyawace kuma tana daga cikin matan da yake so dalilin da yasa ya amince da ita kenan. amma bai taba sontaba daidai da rana daya.. hasalima mafi yawar da sukeyi ita take kiran shi kuma ita Suhailar tasan ba wani sonta yakeyiba haka take son kayanta. Allah sarki Suhaila tana bala'en burgeni cox ba ruwanta abinda na fahimta farhaan ya sace zuciyar Suhaila da iffaat ne amma iffaat ta barwa Allah tasan ba yanda za'ayi ya aureta bayan ma ya rainta gata qanwar matarshi... haka dai akayi komai cikin jin dadi auren ya qayatar anyi komai cikin jin dadi da arxiki naira taci ubanta... An kai amarya dakin mijinta, Hmmm Daren dai iffaat ba'ayi bacci ba gaskiya na jinjinawa iffaat matuqa cox tayi jarrumta ba kadan ba nidai jabo idan nice wallahi sai nayi ciwo, Ashe Banida labari hadda iffaat anyi zazzabin daurewa kawai takeyi, ta bani tausayi matuqa kowa sai yace gajiya ce da kuma kewar Yar uwarta har mama Dan yanxu mama ta gane ba komai zatonta ba gaskiya bane,..... [11:27AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..??54 Na Hauwa M. Jabo Suhaila anachan ana barsar amarci da angonta... Iffaat kuwa ananan ana fama da axaba gwanin ban tausayi.... ko wata Biyu ba'ayi farhaan ya fara chanza wa ya gama da ita kenan, ya koma Neman matanshi duk qoqarin Suhaila na kyautata mishi ta ko wace hanya duk abinda tasan zaiji dadi tana masashi iya qarfinta kuma qaryane yace bata gamsar dashi cox a dare daya sai yayi round biyu haka take haqura duk da tana jin jikii burinta ta faranta masa, amma abanza takeyi su farhaan kam ba hali.. dama mai hali baya barin halinsa abin dai ba dadin ji sau tari takan qyanqyasawa iffaat amma tace kada ta fadawa mama..... Ranar Suhaila ta kama farhaan yana waya da wata akan zasu hadu wani guri, ranta ya baci ta mai magana kuma tace sai ya fada mata ina zaije sannan ta barshi ya fita... Habawa kamar jiranta yake ya wani taso mata kamar ya cinyeta hadda su gori wai albarkar qanwarsa takeci ita tasa ya aureta, ba itace choice dinsaba inda yake shiga banan yake fitaba, maganganun farhaan sun qona Suhaila matuqa ta shige daki tana kuka...! Allah sarki Suhaila.!! Kamar daga sama saiga iffaat yan mata dama iffaat bata cika xuwa Gidan ba cox abinda take gani ranta yana quna, idan dai kaga tazo Gidan to aikota akayi, yanxuma wani tsimine aka kawo mata daga sokoto shine akace ta kawo mata aka aiko iffaat... tin tsakar gida take kiran yy Suhaila har tashigo palo bata nan, tashiga daki taganta tana kuka hankalinta ya tashi tayi ta tambaya amma taqi fada mata dagyar ta fada mata Ashe yana bakin qofa yana jinta tana qare fada ya shigo a fusace.. Kin gayawa uwata sai ta kasheni ko ta hanani yin abunda naga dama wawuya kawai.! Ashe bazaki iya rufawa mijinki asiriba..?? yayi tsaki ya koma Palo tofa masu sayen fada da kudin su bare an sami dalili,ta miqe tsaye ta tsallake Suhaila ta fito Palo... Taxo gaban sa ta riqe kunkumi amma wallahi Yaya farhaan ka bani mamaki, ashe har yanxu kana wannan mugun halin naka?? Koda ba abin mamaki bane hali zanen dutse. Ta nunashi da hannu abin kunya namiji kamilalle a fuska amma xuciya ta shedan tirr da hali irin naka, koda ba komai bane wayewace!!! Amma Allah wadaran wayewa irin taka wacce akeyinta da Neman mata ni wall...... Kamin ta qare farhaan ya miqe ya kwashe ta da mari kuuut..... [11:32AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 55 Na Hauwa M. Jabo kaiiii..! Ya na sauke hannu itama ta wanke shi da nata Marin, kamar daga sama saiga Suhaila taga an mari mijinta tuni ta wanke iffaat da mari tofa iffaat ansha mari ta daga kai ta kalli yayarta taga yanda tayi wani iri haushi ya qara kamata, dama ita iffaat duk bala'en da takewa farhann da biyune ga kishin abin da ya aikata ga baqin cikin rashin samunsa. Yayar ta fara mata masifa, bata cewa yayar komaiba taci gaba da yimai masifa da fitsara yayar tanata cewa ta bari tana rufe mata baki Amma inaaa saida takai aya ta zazzagemasa kwandon rashin mutunci Suhaila abin ya qara kwabe mata baqin ciki kamar ta hade rai ta mutu, ta qare tamai tsaki ta murguda baki ta juyo gun yayar ke kuma ki zauna yana qunsa miki baqin ciki kina shiga daki kina kuka kamar wata doluwa.! ta kama hanyar fita Suhaila ta bita tanason tace kada ta fadawa mama farhaan ya daka mata tsawa akan ta dawo, ta rasa yanda zatayi, taxo gabansa ta tsuguna tana bashi haquri abin mamaki yace ba komai ya wuce laifin sane shima dama baiji dadin abinda ya fada mataba nan dai suka shirya hmmm mata da miji sai Allah hardai suka aikata aikin lada nan take, farhaaan yasan bala'en iffaat yafi nashi nesa ba kusaba cox shi yasan WACE CE ITA baisan miyasa yake shakkartaba.!! Ta isa gida a fusace amma kuma saita tsinci kanta da kasa fadar abinda ya faru, ta rufa masa asiri chaiiii soyayya bala'ece nan ma qarya ta xubawa mama tace wasu samarine suka bata haushi. mama tace nidai zanso naga mijinki kullum cikin korar samari waike yarinya, tayi murmushi ta wuce dakinta,. Tana shiga ta kulle qofa ta fara kuka tayi nadamar dukan farhaan koba komai ya girmeta kuma gashi mijin yayarta haka kuma masoyinta ta tsinewa kanta yafi sau dubu amma ita kanta batasan lokacinda ta aikata hakan ba.!! Farhaan kuwa duk ya damu yayi nadamar abinda ya aikata qarshe yasa Suhaila ta kira iffaat tana bata haquri itama ta bata haquri tana ce mata ga yy farhaan zaiyi magana da ita ta kashe wayar farhaan yace ta kyaleta amma ya damu matuqa... [11:38AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 56 Na Hauwa M. Jabo Su ZZ an qare skull an bar su Iffaat yan mata anata gwagwatawa Da students, dama ko ita kadai tana abinda taga dama.... Cikin ikon Allah iffaat ana shirye shirye kammala secndry skull any qara hankali amma fa har yanxu tana jinyar soyayyar farhaan a zuciyarta, ba Wanda yasani sai qawayenta ZZ.... ****** Wata Ranar Suhaila taje sokoto bikin dangin mamarta kusan sati biyu tayi bata gari, ana gobe zata dawo tace wa iffaat taje ta gyara mata gidanta tasan yayi qura ba kowa aciki tunda tasan farhaan aikin banxa ne ba abinda yake iya tabukawa kuma idan ta dawo ma ba wani abin kirki zata iyaba gata da tsohon ciki kwata 7 , dagyar iffaat ta aminta shima saida aka hada da mama sannan ta aminta. mama batasan sirrin ba iffaat tun lokacin da abin nan ya faru bata qara zuwa Gidan Suhaila ba sai wani zuwa da sukayi duba Suhaila itada mama, sai kuma yau... Waike Dan Allah idan bakiyimata wa zaki yiwa?? yarinyar tana qaunarki ta damu dake amma ke kina Neman ki yanke zumunci mama dai haka tayi fadanta dole tasa iffaat ta tafi Gidan.. Hmmmm Su farhaan ba'asan da zuwan iffaat gidanba, kuma yasan sai gobe matar shi zata dawo hankalinsa kwance shida karuwarsa... iffaat tazo ta gyara ko ina na Gidan har ta kammala Basu saniba suna chan ciki. haka kawai taji tanason shiga dakin farhaan ta gyara kuma batasan yana gidanba. Takama hanyar dakinsa Ta buda qofar tajita abude sai ta tsaya ta qara budewa Sanyin Ac da qamshin turarensa ya daki hancinta ta lumshe Ido ta dauke numfashi hadi da wani ajiyar zuciya ta tura kai dakin tana bude ido sai taga mace kwance tana sharar bacci daga ita sai wasu tsinannun kayan bacci, numfashin tane ya tsaya chak..!! tama rasa mi zata mata ta gane ta tsab hafsa ce tsohuwar budurwar farhaan, ta tsaya waige waige ta hango Yar yawo gefen fridge ta Ciro ta zo zata fara zabga mata sai ta tuna duka ana bacci bashida xafi sosai, ta bude fridge ta samo ruwa ta juyesu a jug taje ta yaye bargon da ta rufa ciki da qarfi, hafsa ta juya cikin shagwaba tace dear kabarni zuwa anjima mana.!! tace kinci ubanki keda dear. ta watsa mata ruwan da qarfi a fuska, hafsa ta wani zabura da qarfi tana miqewa zaune iffaat ta kwashe banxa da mari saida ta koma kwance tuni hafsa ta gigice, iffat kuwa batayi qasa a guiwa ba tafara zuba mata bulala hafsa tana ihu, ta mata lilis chan farhaan ya fito bayi da gudu yayi turus da ganin madam iffaat..... [11:41AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 57 Na Hauwa M. Jabo Bata tsaya ba taci gaba da chin uban hafsa farhaan ya kasa aikata komai kunya ta isheshe dagyar hafsa ta samu ta miqe tayi bayan farhaan da gudu tana kuka, tabbas hafsa ta gane iffaat Dan kuwa itace ta qona mata qafa shekara wajen Shida da suka wuce, iffaat ji take kamar ta hada da farhaan din ta musu lilis amma bazata iya dukan farhaan ba, tsanar sa ta rufe mata ido ta tausayawa yayarta da take tareda fasiqi irin sa tagodewa Allah da bata aureshiba, da saidai suyi kashin kai a gidan Dan bazata dauki wannan iskancinba ta dakawa hafsa tsawa tabar gidannan hafsa ta kasa fitowa bayan farhaan ta qara mata tsawa wallahi idan naxo sai na kakkaryaki, inbanda hafsa batada gaskiya ai ko qanwar hafsa iffaat bazata iya fada da itaba bare hafsa mai Shekara wajen 30, zata kakkarya iffaat. amma tunda batada gaskiya dole ta boye farhaan kuwa ya rungume hannuwa yana kallon ikon Allah kunya ta isheshi da nadamar abinda ya aikata, tayi cikin hafsa da qarfi hafsa ta riqe farhaan da qarfi wani baqin cikine ya qara tasomata yanda taga tana rungume farhaan ta baya uhum su kishi manya tayi cikinta da qarfi ta janyo gashin da tayi qara da qarfi ta wurgata a kan fridge farhaan ya dakawa iffaat tsawa akan miye haka ta juyo tamai kallo keep quiet ina zuwa gunka kaima..!!! tama hafsa gargadi kamin ta lissafa biyar tabar gidannan hafsa dagyar ta miqe ta kwashi kayanta a hannu taji jiki tana gudu tana tunanin wai wannan WACE CE ITA?? House girl ce haka kyakyawa kuma ta mata haka gaban farhaan. Anya kuwa?? Bayan ta kori hafsa ta juyo ta kalli farhaan ido cikin ido tana tunanin balbala masa masifa ji take kamar zuciyarta ta fito Dan baqin ciki aranta tace wai ita kenan inaga matarsa da sukasan juna idan taga haka sai hade rai ta mutu.! Ya dago ido ya mata wani kallo ta mayataccun sexy eyes dinsa tuni ta manta abinda takeson ta masa sai ya bata tausayi tayi tsaki..... Har zata fita dakin sai kuma ta daure ta dawo ta gyara ko ina ta tattara sauran kayan hafsa data bari ta miqa masa tace ga kanan tsohuwar karuwarka nan idan ka bita ka kai mata.. ta juyo kenan ya janyo mata gashi da qarfin bala'ee saida tayi wata qara.... [12:12PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 58 Na Hauwa M.Jabo Ta sa hannu tana qoqarin kwacewa amma ta kasa ya qara janyota da qarfi saigata saman qirjinsa, ta daga kai tuni idonta sun cika da kwalla Dan tsabar azabar da takeji, da qarfin hali, tace, so bansan kacika wayayyeba sai ka aikata abinda kake da niyyar aikata wa aikana.!! yanxu ya gane manufarta tuni ya saketa yayi tsaki ya fada bayi ya kulle kansa cike da baqin ciki da nadama, a duniya ba wacce ya

Chapter 6 of 10