Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels WACE CE ITA MARUBUCIYA HAUWA M.JABO By Hauwa jabo 15:44 3 comments [3:43AM, 4/25/2015] .: WAC CE ITA..?? 1 1⃣ Na Hauwa M. Jabo Kiyi sauri ki sauko maigadi ya kusa zuwafa, Daga saman icen wata siriyiyar yarinya kamar bulala da qarfi tace mangoro nawa na tsinko? Daga gefen wata yar lukutar yarinya tace guda 8 ne Amma uku basu nunaba. Yarinyar da take saman ice tace yauwa.. haka naga ta diro kaman biri daga saman iccen ni jabo da naje gano muke WACE CE ITA? saida na firgita mace haka ba tsoro na kalli bishiyar naga tsawonta abinda yafi bani mamaki ya akayi ta hau bishiyar ba tsani.? Kamin in waigo sai kawai na hangota saman dayan bishiyar har ta Dane bishiyar, ta fara tsunko gwaiba tana wurgowa qasa qawayenta suna cabewa, da gani wayannan yaran taqdiraine waima ya take hawan bishiyar ba tsani?? Yau sai na kakkaryaku Dan ubanninku! Matsiyata..!! Muryar wani dan tsoho naji da alama shine mai gadin wurin Iffatu sauko baba shehu.!! baba Shehu!! Haka suke fada suna ihu, Timmm naji Abu siririyar yarinyar ta fado na tsorata Dan na dauka ta karye Amma inaaaa tana fadowa qasa ta dauki dayar gwaibar ta basu daukaba ta filfila har ta wucesu koda ta iso bakin qofar gonar taga baba Shehu ya kulle qofa tashin hankali..... Kunsan baba Shehu ya kulle qofa dole zamu tsallaka ne kamin yazo, tana fada jikinsu na rawa, ke dijee kulllum ke kike bamu matsala wallahi bazaki qara biyomuba gashi ke baki iya gudu sabida shegun duwawun nan naki. Mtswwww... Kuzo mubi ta chan ginin yafi gajarta. Suka kwasa a guje suka samu suka tsallakar da dije da yake ita rukayya irin ippatu CE ba auki da kanta ta tsallaka duk da haka sai da iffatu ta taimakamata. Juyowan da ippatu zatayo ta hango baba shehu da gudunsa ya kusa kawowa gurinta, ya wurgo mata sandarshi amma bai sametaba, da yake gurgune sai ta yanka a guje kamar fanka fil fil da ita, gurin ginin yafi tsawo dama, na yanda ta iya baba Shehu zai iya kamata, tana nisa dashi,taja baya sosai tazo a guje sai kawai ta dane ginin saida ta hau ta waigo tayiwa baba shehu gwalooo sannan ta dira a qasa...... WACE CE ITA..?? 22⃣ Na Hauwa M. Jabo Tana dirowq dijee rukayya kozo nan ta basu umurni. Sukazo ina mangurona da gwaibata ? Taki ko tamu inji dijee, ta wani harereta itama dijee ta harereta ta jajayen idonta gasu qanana itadai rukayya batace dasu komaiba tayi tsaye dama sune hatsabiban dije da ippatu. Ippatu ta rufe ido cikin tsiwa, abani kayana kamin in lissafa uku. Ta fara lissafi daya biyu uku itadai rukayya ta miqaa mata kayanta dijee ko ta sakasu a Dan kwali ta gulle taci damara da Dan kwalin. Bude idon ippatu ta kwashe dije da mari dama sun saba. Suka fara danbe aka tima dije a qasa dama batada qarfi sai rashin kunya, dagyar rukayya ta rabasu Amma duk manguron da gwaibar sun turmuje a qasa sai guda biyu da gwaiba hudu suka rage. Ko wannen su na fitarda numfashi daddaya. Amma fa dije anji ji jiki kusan kullum sai sunyi dambe da dijee Dan dukansu basuda kunya kuma basuda haqurin juna gashi basu iya rabuwa da juna.! Gamon jini da hali ita rukayya batada fada biye take dasu kamar raqumi da akala duk yanda akayi da ita chan takeyi. Ippatu ta baiwa rukayya mangoro daya gwaiba daya ta riqe mangoro daya gwaiba uku kaji adalci irin na ippatu dije kuwa tahau tsini Dan bata bata komaiba. Ta daure fuska muninta ya qara fitowa, Sunkama hanya ana gaba da juna kowacce tabi hanyarta ippatu na tafe tana shan magoro da gwaibarta, Bala'eeeee wallahi ga bello mai kifi chan, inji rukayya, Habawa baima hangosuba Amma tuni sun yanki ticket suka fara gudu ba tsayawa basu tsayaba saida suka daina hangoshi suka fara dariya. Kamar basune sukayi danbeba har sun shirya. Ippatu tana dariya tace dijee kin tuna faduwar da bello mai kifi yayi suka qara kwashewa da dariya suka tafa ai ranar saida ya bani tausayi habadai, wallahi baibani tausayiba kifinsa bala'en tsada sai shegen dadi inji dijee, Dan yaga ana saye yake yiwa mutane yanga. Shegiyarda sukamai saida ya qare suyar kifi ya jera akan tire zaije talla kawai sukayo tsokana aka biyosu suka zo a guje suka barar mai da kifi kuma sukabi takai suka wuce ko waigowa basuyiba shiko bello mai kifi dan jaraba maimakon ya tsaya kwashe Dan kifinsa sai kawai ya biyosu a guje, garin binsu ya fadi a qasa ya huge bakinsa, sukam tuni suka bace mai ko mai lafiya baya iya kamasu idan suna gudu bare bello mai kifi daya tsufa. Dan ko dijee bai mangalar duwawu idan ta saki qafa ba dama bare rukayya mai kamar bulala, Nidai Jabo bantaba ganin gyauyawa kuma Yan iskan yara, marasa kunya ga tsokana da rashin tsoro irin wayannan yaranba dije da ippatu ba, Dan ita rukayya yar kallo ce sai zugasu da takeyi idan sun samo su sammata ko ta musu gadi suyi abinda zasuyi. Suna dariya suna tafawa abinsu har suka iso gida sai lokacin ippatu ta tuna da aikenta akayi sayen daddawa da manja, ko shakka babu ta xubar da kudin, ta kwance Dan kwalinta data daure kudin amma ina tuni sun fadi, zakuwa tashi qaniyarta idan ta koma ba daddawar nan da manja ga uban shiririritan da tayi.. Maimakon ta shiga gida sai kawai ta kama hanya tana tafe tana tunanin yanda zatayi da saqon googo, kicibis taci karo da wasu yara suna fada ta tsaya kallo suma aikensu akayi sai taga sun yarda kidi naira ashirin da biyar ta dauke ta qulle a habar zaninta. Yau wace rana ippatu taga fada bata tsaya sayen fadanba da walakin. Taje ta siyo manjanta na goma daddawan biyar ta siyo kan kifi na biyar tana tafe tanaci har taje ta dawo suna fada fadan yanzu kuma na an sace kudin dayane ta kyalkyale da dariya iron ta mugunta ta wuce abinta..... WACE CE ITA..?? 3 3⃣ Na Hauwa M. Jabo. Ta wuce abinta koda taje gida ta rasa yanda zatayi ta shiga Gidan ta fara labe labe. Ubanme kikeyi anan ??muryar babanta taji ya mata tsawa saida hanjin cikinta suka juya duk duniya babanta kawai take tsoro ta fara kame kame, bakomai baba sannu da zuwa. To wuce gida munafukar banza ya tasa qeyarta suka shiga. Malam ina ka tsintomin ippatu? wallahi tun qarfe biyu na aiketa Dan nasan halinta batadawoba sai yanxu, kaga har na qare tuwo! Dan ubanki ina kikaje? Ta fashe da kuka wallahi baba sai bayan la'asar ta aikeni ko minti uku banyiba na dawo. LA ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi... Ihhatu "haka take kiranta Dan bata iya sunan ba" kina nufin qarya zan miki? Kinma saba bani kayana ta qwace manjanta da daddawarta, baba ya juyo ya kalleta ina kika samu kifi sai qarnin kifi kikeyi. Ta fuske kamar gaske gidan su kulu mai daddawa suka sammini.! Na dauka kin qara tsokano bello mai kifine. Aah wallahi baba.!! Idan ta tashi zama ta Allah sai ki rantse da Allah ba ita bace take taqdiranci a hanyaba kamar wata waliyiya har ma dai gaban babanta..... ********************* Ippatu yarinyace yar kimanin shekara 11 duk yanda zan muku bayanin ta idan dai ba ta muku taqdiranci nata kungani da idonkuba ba zaku gane WACE CE ITA ba, Sabida batada kunya, batada tsoro ba tada ladabi ba tada mantuwa ba yafiya haka take wata hargitsatsiyar yarinya da ita. Gata qazama taqin qarawa, batasan tsabtaba ko kadan haka batasan wankaba bare wanki farace Amma yanxu tafi zainb khalifa baqi, haqoranta Dan rashin wankewa har sunyi tsatsa daga sama, daga qasa kuwa kamar an kwaba laka an shafa mata idonta kuwa gasu Manya Manya Amma sunyi jaa kamar na sister khade qafar nan kuwa duk tayi wani iri Allah ne ya tsareta qafar bata Faso da tuni ta farfashe Dan su dijee tuni qafafunsu sun yayyage da Faso, bata yawo da takalmi, a cewarta takalmi basa barinta gudu. Mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tanada shekara 6 tanada yayye guda biyu maza duk mamansu daya, suna gurin mamansu, itama babansu yaje gun mamar ne akan dai ta bashi yayanshi, ta hana, dazai dawo ippatu ta maqalemasa ya dauketa ba da son ran mamarba, tana zaune gun kishiyar mamanta gwagwo rabi, gwagwo batason ippatu ko kadan ita kuwa ippatu ba abinda ya dameta harkar gabanta take bata damu da asotaba kuma gwagwo rabi duk abinda zata mata saita rama cox bata mantuwa bata yafiya.! Shiyasa hankalinta kwance bata tsoron kowa duk qauyensu sai babanta kuma bata ragawa kowa duk qauyen nan. An sakata makarantar boko har uku ana korota sabida uban yara da takeci, a makarantar allo ma Dan yana maqocinsune da tini ya korota ippatu kenan.... WACE CE ITA..?? 4 4⃣ Na Hauwa M. Jabo ************ Ta dauki allo na tafi makaranta, gwaggo ko kallonta batayiba Dan tasan ba makaranta zatajeba wacce batason makaranta zata fita tun qarfe biyu, za'a gurin jarabadai, allonta har rubutun ya goge dan tsabar rashin zuwa makaranta da takeyi tana fita taje bayan qyaure ta boye allon ta sa mai bata tsayaba sai gidan su dijee da yake dijee da rukayya gida daya suke dagyar suka samu suka sulalo suka fito. Suna tafe suna tadi duk yaran garin har Manya tsoronsu suke dan basu bar kowaba, idan babbane ya daki daya taron dangi sukemai ko suyita jifarsa da duwatsu, basu tsaya ko inaba sai rafi suna zuwa suka tube dagasu sai qajeren wando rukayya dai ta fara girgar dangi dija ma ya kunmo kai Amma basu kunyar kowa suka fada ruwa sukayi iyo sosai kaman kifaye sun iya ruwa kaman me suna ruwa suka hango baba shehu mai gadi shima ya hangosu sunsan kamin su fito ya iso sai dijee tace kar mu gudu idan yashigo kamamu mu bashi ruwa mu danneshi a ruwa.! Sun haqamai gadan zare, Baba shehu dayazo sai yaqi shiga kaman yasan abinda suka fada, ya kame guri daya kamar bai gansuba, sukayi jira har suka gaji Amma yaqi tafiya sai kawai suka yi shawara akan su nutse su tafi chan nesa dashi su fito. Suka nutse a ruwa, baka ganin tafiyarsu, saida sukayi tafiya mai nisa sannan suka fito suka lallabo suka zagayo suka saka tufafin su suka nufi gona satar mangoro shiko baba shehu yanachan yana jiran fitowarsu daga nutsewar da sukayi yaji shiru sai abin ya bashi tsoro kardai ya kashe yayan mutane!!! Tuni ya fada ruwan ya shiga lalube Amma basu ba labarin su chan ya hangosu suna gudu sun ciko zaninsu da mangoro da gwaiba yau hadda lemu da basu cika diva ba sun debo. Tsoro ya kama baba maigadi daganan baba shehu mai gadi ya sallama cewa ba mutane bane aljanun dajine ko Yan ruwa suke addabarshi, dole ya nemo tsari karsu hallakashi. Da sauri ya fito ruwan saida sukaxo Dan kusa dashi suka kwashe da dariya sannan suka mai gwalo suka gudu. Kaji hatsabibai.... ***** Tun daga ranar baba maigadi bai qara binsuba, hasali ko kallonsu baiyayi idan suna abinsu, da suka gane ya saka musu Idone sai suka maida abin Sana'a kullum zasuje su debo sai suje su wanke suje talla da sukaga basa ciniki sabida baqin halinsu sai suka riqa daurawa rukayya tallar rukayya kuwa akwai farin jinin talla, talla ta karbeta nan danan suke saidawa gurin rabon kudi suyita bala'e da danbe. Ba ranar da basa fada kuma aranar suke shiryawa,..... [4:50PM, 4/26/2015] .: CHI GABA.... WACE CE ITA..?? 5 Na Hauwa M. Jabo ******************** Yauma kamar kullum yan matan uku dije ippatu da rukayya suna tafe suna labari suna shewa da dariya da gani dai kasan basu da kamun kai bare uwa uba tarbiya, laaaaaaaa dije kalli malan garba da ya dakemu ranar.! suka waiga gaba dayansu suka kalleshi, ippatu tayi tsaki share shi mugun banza, dijee ta kalli ippatu bazamu share shi ba,yakamata mu rama, mi zamu masa mu rama kalli fa har yanxu tabon bulalanshi, ta nuna hannunta, kawai mu ramako ? Eh mu rama, Suka fara shawara sharrin da zasuyiwa Dan saurayin malamin makarantar allonsu, yayo wankansa na juma'a zashi masallaci sallar juma'a baima kula dasuba. har sun hada sharrin da zasuyi tunda nanne hanyar sa kamin ya dawo daga masallaci, sun nemi toka ta murhu sukaje Gidan da ake daka taba gari irin wannan da tsofafi suke sakawa a qasan lebonsu, suka siyo ta ashirin suka siyo garin barkono na goma suka hada guri daya suka ijiye suka samo bokoti daya suka debo ruwan kwata mai shegen wari suka je suka samo kashin shahu sabo suka kwaba da kwatar nan suka labe gefen hanya, ippatu ta dane bishiya kamar biranya, da bokitin kwatar ta da suka dama da ruwan kashi, malam garba na bullowa shida dije ta watso mai garin tokar daidai fuskarshi, da suka yiwa hadi ita, ita kuma ippatu ta watsomai ruwan kwatar daga saman bishiya, daga kansa har qasa ta diro gasa suka waske, idon malami sun cika da yaji ya sai ihu yake yana Neman dauki,yana murxawa ga ruwan wari a saman kanshi kamin mutane suji ihunsa tuni sun gudu gidajensu. Kuma ba Wanda ya gansu Amma sabida hatsabibancinsu duk Wanda ya sami labari sai yace hatman aikinsu ne sun koma gida duk ranar ba Wanda ya fita cikinsu, wayanda tun safe idan sun fita gantali basa dawowa sai guraren yamma shima Dan sunsan idan sunyi dare akwai samarin da zasu hallakasune shiyasa duk la'anarsu da dibar albarkarsu basa fita gida da dare. Ina ippatu? tana daki, Malam lafiya kashigo a hargitse?? Inafa lafiya yarinya tana son tasa xaman qauye nan ya gagareni.. Ke ippatu.!! Na'am baba, zonan mara kunya yarinya, ku ne kuka jiqe Malam garba da ruwan kwata kuma kuka zuba masa barkono a Ido ko?? LA ilaha illallahu Muhammad rasullullahi wallahi tana taba hannu tana salati kaman gaske, wallahi baba ka tambayi gwagwo yau duk ban fita koda zaureba, Dan banida lafiya, ko goggo,?? to ubanwa zai masa wannan ta'addancin idan bakuba gashichan ido sai Allah, kuma yace bazai barwa Allah ba. Salamu alaikum. Daga waje sukaji sallama koda baba ya fito saiga yan sanda biyu an kamo dije da rukayya akazo a tafi dani, ina kuka ina kiran baba, amma saida yan sanda suka tafi damu police station.. ************ Kun Dade kuna addabar mutane a garinnan, ba makhluqin da bai kawo qararkuba a qauyennan, kun zama annoba jaraba a gari to zamu kulleku har sai likita ya tabbatar mana da samun idon malam garba, DPO yake wannan bayani wasu ippatu, iyayensu sunyi sunyi abasu belin su amma sunqi badasu aka kullesu suna kuka suna basu bane! DPO yasa an musu Dan karen duka tunda ba wata sheida da take tabbatar da cewa su suka aikata wannan laifin, kawai sanin hali yasa aka tsaresu, sunji wuya matuqa, amma dukda haka sunqi fada gaskiyane, rukayya ta gaji ta tona asiri tace sune dije da ippatu duk wahalar da suka sha sun qi aminta hasalima sun qaryata rukayya ne, Dpo dayaga ba nasara kuma likita yace malam garba ya samu sauqin idon sai aka sakesu, aka musu kashedi mai tsanani, sunyi wujiga wujiga dasu, tun suna police station suka fara shirya sharrin da zasu yiwa dpo insun fito kaji hatsabibai dpo ne next target dinsu....... WACE CE ITA..??6 Na Hauwa M. Jabo ********* Bayan sun fito da sati biyu sundan yi lafiya dan iyayensu sun manna musu mari a qafafu basa zuwa ko ina hatta makarantar allo, gari ya samu lafiya two days, bayan sati biyu kamar sun shiryu sun zama na kirki, aka kwance musu marinda aka saka musu, ranar da suka hadu da juna suka fara dariya suna bada labarin yanda iyayensu suka musu, bayan sun qare labari suka fara shirrin yanda zasu yiwa Dpo su dau fansar dukanda yasa aka musu da marinda ya riqa tsinka musu lokacin, bayan iyayen su ba Wanda ya taba marinsu saishi.!! Sun shirya zuwa har gidanshi su fasa mai glss din akwalar motarsa. Amma basusan yanda zasuyiba, sun gargadi rukayya akan idan ta kuskura ta qara tona musu asiri basu ba ita ta amince, matsalar su daya kada a ganesu, sun yanke shawarar fita da dare Amma suna tsoron samarin garin. Yauwaaaaaa ina yan matannan da muke tsokana masu saka baqiin Abu da hijabi su kulle fuskarsu?? Eh nagane inji dijee naji ana ce musu wani Abu namanta sunan, yauwa mu samo irin wannan abin da suke sakawa mu rufe fuskar mu sai a dauka sune zasu makaranta sai muje mu fashe mu dawo, kaji hatsabibai marasa tsoro.!! Suka saka dariya sun sami wani tuggu da zasu qulla, Matsalar su daya basu da niqab din nan dijee akwai gyallen tatan gasara na Maman su zata dauko sai su yagashi suyi niqab tunda gyallen baqine haka kuwa akayi, suka tare yar makaranta ita ta dauka dukanta zasuyi, sai taga kawai sun karbi niqab dinta suna kalloyanda yake, suka sa allura suka hada irinsa, kaji shegun yara... da dare suka fita sai unguwar su dpo suka shiga har chikin gidansa batareda shakkun komaiba, da qarafunansu da suka samo gun kanikawa, suka ma glss din motar tamas tamas, da yake dpo yana gurin aiki, matarshi tana islamiyya yarane kawai suke Gidan wataqil suna bacci sukayi operation din ranar har suka gudu ba Wanda ya gansu,har suka iso gida!! Labari ya chika qari, ya yadu a kowa yace da dai da rana ne da sai muce su ihhatu da dijee ne, Amma yanzu duk qauyen an yarda basu bane barayine kawai suka masa wannan karen aikin... uku bala'e kenan!! suna nasara aduk aikinda sukasa gaba koda zasusha wahalane.. ******************* Yauda gobe ba wuya a gurin Allah abubuwa da yawa sun faru a dan qaramin qauyen nan ciki kuwa harda rasuwar mahaifin ippatu sanadiyar hatsarin mota, yajee birni siyo kayan shagonsa anan babbar mota ta bi saman motar su Allah yayi mai cikawa.! Su ippatu an Dan natsu kadan an rasa mahaifi, mahaifiya kuma dama batasan duniyar da takeba coz ba rabuwar allah sukayi da babantaba duk sharrin goggone, tunda tayi wayo bayan babanta ya kwatota a hannun mahaifiyarta bata qara saka mahaifiyarta a idoba haka ma yayyenta.. Tun farko farko zaman haquri goggo takeyi da ippatu, bare yanxu da ba mahaifin ippatu, sabida haka ta yanke shawarar miqata birni wanke wanke ko ta moreta.... [4:50PM, 4/26/2015] .: WACE CE ITA..?? 7 Na Hauwa M. Jabo Tashin hankali ni kaina Jabo na tausaya wayanda zasu dauki ippatu aiki gidansu kamin su korota nasan zataci ubansu.! Goggo kullum gori take mata har ta fara girgar dangi a gida, amma ba mashinshini bare a aurar da ita. Wazai kwasar ma kanshi jaraba. ippatu da yar birni ce da sai anyi haddadiyar mace dan komai Allah ya bata sak mamanta ta dauko fulani gaba da baya sai ta hada da da duhun babanta sai tayi Dan duhu farinta mai haske ne da duhu gata qirar kalangu ga gashinan kamar yakasheta amma ba gyara idan akayi kitson sallah qarama sai babbar sallah ake tsefeshi, tayi baqi Dan na tabbatar da tafi zainb khalifa baqi sabida tsabar rashin wanka, qafafu duk sun jeme haqora sunyi tsatsa da wata laka laka a ciki idonnan sunyi ja duk jikinta tabone sabida fadowa saman bishiya da akeyi a jijji ciwo, ko saman Garu da ake dirowa ko a na gudu a fadi a ji ciwo haka dai take masha Allah..... ********* Goggo tayi magana da altine akan tanason a kai ippatu birni aiki amma inaaaaaa altine taqi aminta Dan tasan halin ippatu sama da qasa, gaba da baya, altine taqi yarda har goggo ta gaji da zuwa gidanta neman alfarma ta haqura, ranar goggo taje suna maqotansu taga wata mata daga birni tana maganar a nemo mata yar aiki yarinya qarama mai qoqari da kuzari goggo batace komaiba, Dan tasan idan ma tayi magana anan mutane zasu fadi mugun halin ippatu. Saida aka watse matar na fita goggo ta faki ido ta bi bayanta, tajata gida tace tanada ya amma batason kowa yasan zata kaita aikine zatace takaita gun yar uwartane goggo tace yarinyar marainiyace, tanason ta dan riqa samun abinda zasu chi su rufawa kansu asiri, Amma batason kowa ya sani, hakadai goggo yayita tsara matar, ana haka saiga ippatu an dawo daga kogi tun safe dataje sai yanxu tayi shudi daya, Koda matar taga ippatu taga uban bokitin data dauko saman kanta chike da ruwa ta tabbatar da cewa ippatu Nada kuzari, kamar gaske ippatu ta gaida matar ta wuce abinta matar kuwa ta amince da ganin ippatu kuma tace baxata fadawa kowaba. Matar da yake gidan biki tayi sanarwar anata kawo mata yara yan mata amma Duk wacce aka aiko sai tace musu ai ta samu bata fadawa kowa cewa ippatu CE ta samuba har ta koma birni,.!! Bayan kusa sati uku da magana matar tazo ta tafi da ippatu birni ta mata dinki kala biyu Dan kar taje Gidan daga shigarta a koresu , aka hada da yan kayan sallarta. Ippatu tayi kukan rabuwa da qauyensu Dan batason zuwa aikin da za'akaita sun rabu da dijee da rukayya sunata kuka sai birni...... WACE CE ITA..?? 8 Na Hauwa M. Jabo ******************* Bayan sun isa birni matar da nikaina Jabo bansan sunantaba takaita gidanta, tasa tayi wanka ta saka kayan da ta dinka mata, suka kwashi hanya takaita gidan da zatayi aiki, ippatu tunda ta shigo birnin sokoto take qauyanci ganin sabuwar duniya ya hanata kula da fadan da matar take mata bare ta mata rashin kunya, data shigo gidan Alhaji Habib nan kallo ya koma sama, gidane da idan na tsaya muku bayaninsa zan bata lokacine, duk unguwar ba gidan da yakaishi girma, ga lambu a gidan shuke shuke manyan itatuwa swimming pool ne, gurin ijiye motoci ga abubuwa nan kala kala, ataqaice dai Gidan dai ya hadu, ippatu tana shiga palon santsin tayis ya kwasheta ta xube qasa tiiiiim..!! Wata Yar budurwa da matar gidan suka saka dariya, taji haushin dariyar da aka mata ta daure fuska abinta, badan yau tazoba da sai ta tsula musu rashin mutunci su har sun isa su mata dariya.!!? Matar data kawota ta riqa hannunta suka qarasa palon suka zauna, sanyin ac tuni ya fara shigarta ta fara rawar dari sai qarar haqoranta kikeji kakaf. kakaf, alhaji yace a kashe ac din baquwarsu tanajin sanyi.! haba Abba wallahi zafi akeyifa wani Dan saurayi ya fada yana yatsina fuska alamar zafi! Alhajin dakanshi yatashi ya kashe ac ya dawo ya xauna. Wacce ta kawoni ta fara musu bayanina kamar yanda goggo ta mata bayani, taji qaryarda goggo ta zuba tayi yawa ta kasa haquri Dan ita ba'aqarya gabanta, tayi charb ta chabke ta fara zuba, goggo ba itace mahaifiyataba mahaifiyata sun rabu da mahaifina tun ina qarama mahaifina ya rasu shekara kusan biyu da suka wuce kum..... Keeee, keep quiet mana ya fada yana mata kallon wulaqanci, chikin tsawa ya fadi maganar ta gane keep quiet dan lokacinda tana boko kamin a korota Malaminsu yana yawan fadar haka idan ana surutu kuma daya fada sai kowa yayi shiru, shima malaminsu da qarfi yake fada kamar yanda wannan ya fada, ta dallamai harara hadi da yimai kallon banxa ta zubar. Kaiiiii abba u see? Kaga yanda take kallona kuwa,? Farhaan yakamata ka riqa haquri mana, da zuwan baquwa zaka tsaneta haka, kada ka manta da ita zaka zauna.. farhaan ya juyar da kai gefe gaskiya dady bana tunanin xan iya zama da wannan, kalletafa!! wata kyakyawar dattijuwa ta kalleshi wallahi kayi kadan wannan itace ta qarshe ba chanji. Duk maganar. da suke da englsh suke yinta, Ya bata fuska ya tashi yabar musu guri yar qanwarshima ta bi bayanshi suna gunagunai da turanci, Matar data kawoni ta basu haquri tace kuma kada in qara magana, ganin maganata kamar itace ta haifarda rigima sai nayi shiru bawai dan raina yasoba, taci gaba da musu bayani inajin tana qarya amma ba halin magana...... Mujeee zuwa muji yanda iffat za'azauna a gidan aiki, da wannan hali nata......M jabo ....... [4:00PM, 4/27/2015] .: WAYE ITA..?? 9 Na Hauwa M. Jabo Wacce ta kawoni Ta qare bayananta na qarya dana gaskiya da goggo ta kitsa mata.... Kyakyawar matar tace Allah ya bamu ikon riqeta yar marainiya da ita, dama yaron mune muka nemowa mai aiki, duk wacce aka kawo sai su sami sabani dashi kusan mai aiki 13 ana kawowa suna samun sabani, shine yanxu yace asamo mai qaramar yarinya tunda aikin nashi bashida yawa yace bayason Yar cikin qari sabida sauran daga qazamai sai barayi sai yan iska sai marasa kunya da sauransu, shi kuma baya iya zama dasu

Chapter 1 of 10