Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
gaskiya nima anan naba da goyan bayan tafitar da miji kafin nan da tagama secondary school Hajiya rukayya tace wannan ba abin muwabane Abamu nan wani lokaci saurayinta zaizo dakanshi yagaisheku aitana dashi Alhaji abubakar yace to alhamdullila Dan Allah komai ya wuce Ke Laila ba wa mijinki hakuri aikuwa hajiya rukayya tace ya za ace tabashi hakuri bayan shiyakamata yabata hakuri daya dauki hanu ya tsinka mata mari acikin mutane Ganin abinda hajiya rukayya takeyi yasa Hakeem barin falon yayi sashinsa Yana fita suka hadu da Ahmad Hakeem yace ango Ahmad yace komaidai yakoma dai dai ko Hakeem yace barin shiga nashirya nazo muwuce Muje musallami friends dinmu na nesa Ahmad yace karka damu nagama komai Hakeem yace yanzu har ka rakasu airport Ahmad yace kwarai Hakeem yace amayar fa Ahmad yayi murmushi yace ai andade da tafiya da amarya Dan dazu nakirata harsun huta ma Yan uwanta ma sun kamo hanyar dawowa Hakeem yace to ai sai musamu mushirya muwuce muma ko karnayi laifi dayawa agurin Madam Aisha Ahmad yayi murmushi yace a haba aitasan komai Idan taga bamuzo ba tasan abinda yatsare mu Hakeem yace yau zaka shiga dakin amaryar ka Barima kagani Hakeem yashige sashinsa Yafada bathroom yayi wanka Yana gama shiri cikin shadda marun colour ya balain masa kyau kamar danshi akayi shaddar Yana fesa turare Laila tashigo Tace daddyn meenat naga kaman tafiya zakayi baka sallamemuba Hakeem ya watsa mata wani kallo Yace mekuke bukata tace kayan abinci da na amfanin gida yace kizauna kirubuta duk abinda bukata zansa driver yakawo muku Daga yau nabar baki daman da kikesamu harkike ganin kaman kinfi karfina sai yadda kikayi dani ko cikin tashin Hankali Laila tace Dan Allah karkamin wannan horon kasan nasaba sayan abinda nake bukata da kaina Hakeem yayi murmushi mugunta yace nawa nakebaki dama Laila tace dubu Dari uku duk wata Hakeem yace hakane ko ta ce a hakane Yace kedawa nabari agidan nan tace nikadai Yace good yanzu duk wata zanturo miki dubu hamsin Kekadai dai nasan zasu isheki Yana gama fadan haka yayi waje da brief case dinshi Haukane Kane kawai Laila batayi ba Amma hankalinsa yatashi sosai nan tadauki gyalanta tayi gurin mahaifiyarta hajiya rukayya **** Bayan wata shida professor Hakeem zaune kan kujerar office din shi Yadauki wayarshi yakira yaya shamsu Ya shamsu yashigo yace Barka dai yallabai sannu da aiki Hakeem yayi murmushi yace yauwa malam shamsu Yace ga wannan ya shamsu yakarba yace ina zankai yallabai Hakeem yayi murmushi yace nakane malam shamsu zaka kaiya dubawa kagani Ya shamsu yabude Aikuwa ya shamsu ya dago ido yakalli PROF Hakeem Yace admission fa nake gani yallabai Hakeem yace yes nasan kana da burin karatu a rayuwarka Iyakacin zamana da kai na lura kai mutum ne mai son karatu So yanzu ga dama nan malam shamsu zaka iya farawa nagama komai har registration da komai sai dai ka kai credentials dinka asa maka a file Kuma daga Level two zakafara nariga nayi komai A department of business administration Ya shamsu baisan lokacin da tashiba yace yallabai gaskiya ba abinda zance da sai dai Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira Allah ya jikan mahaifanka ya ramaka zuria Hakeem yace ameen malam shamsu na gode kwarai da adduarka a gareni Sai dai ni har yanzu baka taba tambayata wani Abu da yashafi rayuwata ba malam shamsu koba bukatar sanin daga ina nafito ne Ya shamsu yayi murmushi yace zanso sanin tarihinka dakuma tarihin nagartarka a rayuwar alumma Nan professor Hakeem yayi murmushi Yabashi labarin rayuwarshi kaf bai boye mai komai ba Ya shamsu yaja numfashi yace yanzu tun kana 20years kayi aure kenan Hakeem yace kwaraikuwa ina da 17 year old girl yanzu haka Da mamaki ya shamsu ya kalleshi yace masha Allah Gaskiya kai kam duk abinda ake nema a rayuwa Allah yabaka Hakeem yace zakasan daughter nawa ma ai duk sati tana zuwa ranar alhamis Ya shamsu ko wacce kake cewa amina Hakeem yace yes ita nake nufi Ya shamsu yayi shiru yace am sorry sir wallahi duk azatona madam dinkace Hakeem yayi murmushi yace 'yata ne nacikina Ya shamsu yace masha Allah wallahi gaskiya labarinka ya burgeni Bude kofar office akayi Prof Ahmad ne yashigo yace Kace kuna tare da malam shamsu ne Hakeem yace ai tundazu muke hira anan Ahmad yabawa ya shamsu hanu sukayi gaisa Ahmad yace wa Hakeem madam fa tagama abincin rana yakamata muje muyi lunch Hakeem yace gaskiya dai nima yaka mata nasan abinyi Kaga madam Aisha sai tadinga hutawa ko Ahmad yace Aisha ce zagaji wai caf yanzu kasan Allah da zankoma inje cin abinci nikadai sai tambayi ina kake baka biyoni ba Duk randa kake azumi haka nake fama da ita Hakeem yace Allah sarki madam tana tausaya wa marayan Allah Ahmad yayi murmushi yace maraya a kano ba Ahmad ya kalli ya shamsu yace malam shamsu gaskiya yau Na kamaka sai munje kaci abincin amarya Hakeem yace aifa dai kam tunda shi yana mana rowan abincin amaryarsa da kuma ladan da zamu samu wajen gaida su umma da Abba Ya shamsu yayi murmushi yace bahaka bane banyi tunanin inna gayyaceku zakujeba shiyasa Hakeem yayi murmushi yace saboda gamu aljanu bama cikin jinsin mutane ko Ahmad yayi dariya yace zamu baka mamaki sai dai kaganmu agidanka Ya shamsu yace ina zuba ido ,nan dai kyar ya shamsu ya yarda suka je dashi cin lunch Suna kan dining din Ahmad suna cin abinci itakuma Aisha tana kan two sitter Tace wa Ahmad honey yaushe zaka kaini yawo kasan fa bansan kowaba a kano kuma inason inga gari Ahmad yace zan hadaki da kawance da madam din malam shamsu kinga saikije mata itama tazo miki amma sai malam shamsu ya amince Ya shamsu yayi dariya yace ina zata iya erea mu ai sai mu Hakeem yace kaidai kawai malam shamsu kace bazaka bar madam dinka suyi zumunciba Ya shamsu yayi murmushi yace shikenan Allah yashige mana gaba Sukace amin Dazasu tafi ne Aisha tace wa ya shamsu Dan Allah agaisar mata da kawarta kafin suhadu Ya shamsu yace zataji insha Allah **** Bayan wata biyu da fara zuwa makarantar shi Ankawo sadakin Husnah Harda kayan lefe akwati gomashabiyu cas Sadaki kuma naira dubu Dari biyu Yanzu haka ana jiran suyi waec da neco ne kawai asha biki Shakuwa ce maitsanani da kaunar juna tsakanin copper bash da Husnah *** Meenat zaune kan carpet dinsu hajiya rukayya tadawo daga tafiyan datayine wajen boka Dan karbowa meenat maganin MALLAKA da zata mallake copper bash yazama nata Hajiya rukayya tace a abinci zaki zuba mishi idan yaci zai kamu da soyayyarki Wanda ko uwarsa bazai mata Sannan kuma zaiji ya tsani Husnah aduniya Cikin farincki amina tace kai Allah yabar minke kakus dina Laila dake gefe tana kallonsu Dan itama jiya tazo Laila tace hajiya Nifa ba abinda kika karbo min Akan daddyn meenat Hajiya rukayya tace ai wannan yaro fa asiri bazai kamashi ba sai dai kawai musa a kawar mana dashi Har lahira kinga masamu dukiya muyi yadda mukeso da shi Meenat caf daddyn nawa za a kashe wallahi bazaiyi yiwuba Haka kawai ita mummyn bata San yadda zata karbi kudi a ahanunshi ba sai ankasheshi Hajiya rukayya tace to ai murasa yadda zamuyi da wannan uban naki ne jikalle Meenat tace natabbata baza arasa wani hanyar ba kudaiyi tunanin Husnah zaune a dakin amarya kubra tana asigment dinta Kubra tace kedai Husnah kinji dadi wallahi wannan irin gashi aikoda shi zaki yaki mijinki balantana ga uwa uba kyau da diri duk Allah yabaki Husnah tadago manyan idonta ta kalli kubra tayi murmushi Tace anty kubra kenan sai kace ke Kubra tayi murmushi tace zakicimin fuska ko ai idan dai kina guri muai saidai muyi shiru Husnah tace banda zuga fa matar yaya Husnah ta fashe da dariya ita kadai Sai kubra tace meyabaki dariya Husnah tace kawai danku nakeson gani keda yaya wannan irin kyau da kyau ai sai dai kuhaifo mana aljani Dan kyau fa Kafin Husnah takarasa maganarta kubra ta dauki pilon kujerarta zata kwadawa Husnah Husnah ta tashi ta gudu dai dai shigowar ya shamsu Yace lafiya kekuma Husnah tace Lafiya qlw ya shamsu anty kubra ce ta biyoni Umma dake kan sallaya a faranda tace o keda kubra dai zanga ranar rabuwanku akwai drama Ya shamsu yayi murmushi yace sai tabita ai Umma tayi murmushi tace andawo Dan albarka ya makarantar Ya shamsu yace alhamdulillah umma bara nayi wanka sai nazo muyi hira umma tace To banana Ya shamsu yashiga dakinsa yasami kubra zaune ta tashi tana mishi sannu da da wowa Yayi murmushi Dan kullum son matanshi karuwa yakeyi saboda yadda take matukar mutunta 'yan uwanshi hakan nasa yana Dada jinta cikin ranshi Murmushi yasakar mata yace kamu hanunta yace meya hadaki da kanwartaki Kubra ta yi murmushi tace tsokanata tayi shiyasa tagudu Wai karmu haifi aljanu Dan kyau fa Ya shamsu yayi dariya yace ai haka tace Shiyasa na tambayeta tamin shiru Washagari da safe bayan anfito break sai copper bash yakira Husnah office din sa Dan ta serving din abinci Dan baya break shima sai goma Shiyasa daga gida akekawo mishi Ba kullum yake kiran Husnah ba Dan idan yakirata bata zuwa Dan kare mutuncin kanta Ba kullum ana ganinta a office din shi ba Suna zaune itada meenat wayarta yayi kara ta dauka tace aslammu ailaikum Yace wa alaikumussalam my love Husnah tayi murmushi tace inajinka ranka yadade Yace alfarma nake nema kizo Dan Allah ki serving dina break fast Husnah takalli meenat tace kice to Dan Allah Husnah tace shikenan ganin nan zuwa Husnah takashe wayar ta kalli meenat tace meyasa kikasa na amsa mishi Meenat tace tace haba kekuwa Dan ya roki alfarmar yau dai ai sai kiyi mishi Husnah tace bazaki gane bane amma tashi muje kiraka ni dama abinda meenat kesonji Suna isa office din copper bash Yace wa amina taje cikin motarahi zataga basket din abinci ta dauko mishi Aikuwa amina cike da farinciki ta wuce class dinsu ta dauko maganin ta da zata sawa bash Sai da ta bude flask din ta zuzzuba dama soyayyan doya da kwai ne Sai ruwan tea Aikuwa ta zuba ta dauka takai mai Husnah tayi serving dinshi Yayi dai dai lokacin komarwar su class Husnah tace zata wuce class yace ita bazataciba Tace ai yau alhamis suna tana azumi Yace yayi kyau kikula min da kanki kinji ko Tayi murmushi dimple dinta suka lutsa yace I like your smile Husnah tace thanks Ta wuce zuwa class Wanda tuni meenat tarigata Yagama break dinshi tsaf Washagari jumma a Dama bashir yasaba zuwa duk Jumma a Husnah zaune tagama shirinta tsaf bashir kawai take jira Kubra tace gaskiya dai tunda yasaba kiranki kuma yasaba zuwa yakamata kikarashi kiji kolafiya Husnah ta yarda da shawarar anty kubra Takira bashir yakai sau goma amma yaki dauka sai a kiran karshe Yadauka yace dalla malama me na damuna haka Kebari nafada miki karkisake kirana daga yau banza Mara mutunci Na tsaneki Husnah bana son jin sunanki kifita a rayuwata Sadakina da kayan aurena duk za azo karba kafin yafadi wata magana Husnah ta yanke jiki ta fadi Ya yi dai dai da shigowar kubra Aikuwa kubra tayi ihu umma da abba da ya shamsu suka zo Next page Your comments is needed fans Ina dadin comment din Ku fan's=??=??=??=?? Ina alfahari da Ku =?M?=?M?=?M? =???=???=???=???=???=???=??? [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN

Chapter 6 of 10