Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
dauki lacasera Ta dauka wa ya shamsu fanta dantasan abinda kowa yakeso Umma ta ce yau fa shagwaban yatashi Abba yace a din tayi baruwanki ai sunfi kusa yakarasa maganar yana dariya Husnah tace yauwa Abba fada mata dai Ya shamsu yayi murmushi Dan yanason yadda suke rayuwarsu cikin son juna acikin gidansu Suna gamawa Husnah ta tashi tadauko Dan karamin kula tasaka naman da komai yadda sukasha sai wannan lemu sunkai uku Tasaka a Leda tace ya shamsu wannan na anty kubra ne idan kaje kace mata inji sweet kanwarta Umma tace kai wannan soyayya da Husnah takewa kubra Inba auren nan akayi ba hankalin Husnah bazai kwanta ba ba Abba yace ai soyayyar Dan uwantane yashafi khadijan Husnah tace gaskiya Abba kana da ganewa wallahi yadda anty kubra takeson ya shamsu yasa na ke ganin girmanta Shidai shamsu inbanda murmushi ba abinda yakeyi Nan yawa mahaifinsa da ummansa bayanin yadda sukayi da maigidansa Abba yace Allah yasa hakan shine mafi alkairi Kaga girman alkawariko To haka akeson mutum aduk inda yake ya rike gaskiya Ya shamsu yace hanekam Nan yabawa mahaifin nasa kudin gabadaya yace ya ajiye agunsa Ya tashi yashiga wanka Wanda Husnah ce takai mai yana fitowa yayi alwala zuwa sallar magriba Bayan ya dawo daga isha ne yadauki kayan da Husnah tabashi yakaiwa kubra Ya fesa turarensa mai Dan arha duk da talaucin su ya shamsu baya rabuwa da turare danshi mutum ne mai tsafta sosai Dan gado sukayi a wajen iyayensu Saikuma Husnah tace matsa kaban guri akan tsafta kokadan Husnah bata son datti Yana isa gidansu kubra ta fito da hijabinta dogo Duk yadda takai taboye abinda aka mata agida kubra takasa sai da yagane Yace Lafiya naga fuskarki haka kubra Kubra tayi yake tace bakomai wallahi abune yafada min a idona amma nacire Kafin ya shamsu yayi magana wata kanwarta wadda suke uba daya tazo tace wai kizo inji mama kicigaba mata da abinda tasaki Kubra tace kice inzuwa yarinyar tajuya takoma zuwa cikin gidan Tausayin kubra Yakama shamsu sosai yace kiyi hakuri kinji watarana sai labari nasan duk akaina kikaganin wulakanci Dan kin ki bada hadin kai amma namiki alkaqarin komai yazo karshe insha Allah Yace karbi wannan inji kanwarki tace nakawo miki Kubra tace Allah sarki Husnah Dan Allah kace mata nagode sosai Yaciro dubu uku a aljihunsa yace karbi wannan kirike a hanunki Kubra ta kalleshi ta kalli kudin tace haba sahibina ya daga samun aiki zaka fara barna da kudi kawai kabarshi Yace ai duk abinda zansamu kina da kaso aciki kikarba kawai kubra idan baki karba ba zaki bata min rai Cikin sanyin jiki kubra ta karbi kudin Tace nagode Allah yakara budi yace amin Maza koma gida kikarasa abinda aka saki karkiyi laifi ko Tace to sai anjima ko kuma saigobe ba inji ya shamsu Washa gari dasafe ya shamsu yagama shirin zuwa aiki bayan sun karya Yafito yace wa Husnah muje ko Husnah tace to yaya suka wa umma sallama Suna futa kuwa suka yi sa ar keke napep yaya shamsu yatare musu sukashiga Suna tafiya suna hira yace inga jakanki tabashi bata kawo komai a ranta ba Ya shamsu kuwa yafaketa yasaka mata 1000 a ciki dubu daya kenan Suna zuwa dai dai gate din su Husnah ya shamsu yace wa driver tsaya ta sauka nikuma kayi dani BUK Husnah tasauka tana daga wa ya shamsu hanu Yayi dai dai dannowar motar copper bash Yaji lokacin datace ya shamsu kanan ya shamsu ne acikin keke napep din nan Inkuwa shine zanbisa namishi bayanin komai aikuwa copper bash yayi ta bin yaya shamsu abaya har yasauka a gate din BUK Bayan ya shamsu yabiya kudin yayi gaba abinsa Copper bash yayi parking yafito Yabi bayan ya shamsu Har yaje yayi signing yazo kafin yaje can kujerashi kofar PROFESSOR HAKEEM yazauna Copper bash yamishi sallama ya shamsu ya amsa yace kozan iya taimakonka Copper bash yace a daman taimakon nazo nema amma a gurinka ya shamsu Yadda copper bash yakirashi ya shamsu yasan duk yadda akayi yasanshi ne Ya shamsu yanuna mishi kujera Nan copperbash yafada wa yaya shamsu irin son da yake wa kanwar shi amma taki bashi dama hakan Ya shamsu yace bazata ta taba amince maka har sai nabata izini Umarni nabata nima kuma bazan taba amincewaba har sai nayi bincike akanka kafin nan kuma na tabbatar tana sonka na uku kuma zakamin alkawarin barin ta tayi karatu bayan kinyi aure amma wannan zaizone bayan nayi bincike nagar tarka Copper bash yace wallahi ya shamsu indai akan asali ne bana shakku aje ayi bincike fata na kawai idan kabincika bani da matsala ka amince min nakawo sadakina gidanku shikadai ne zaisa hankalina yakwanta Ya shamsu yayi murmushi yace karka damu Allah yashige mana gaba Nan yawa ya shamsu sallama yatafi ******* HUSNAH zaune kan kujerar class dinsu teacher din dazata shiga musu ta haihu shiyasa suka samu Free time Meenat tace gaskiya Husnah baki da kirki yanzu kakan dad dina da mummy na ya mutu amma kikasa Neman gidan mu kije kiwa kakata ta aziyya Husnah tace afuwan aminyi insha Allah ranar asabar zanzo gidanku nawa kakanmu ta aziyya Meenat tace kai amma danaji wallahi har na matsu asabar tayi Hajiya ta taganki labarinki kawai takeji agurina Husnah tace aikuwa zanzo nagaisheta Tace amin Allah yasa daddy ma yazo sai kigaisheshi Kinsan tun yadawo kano aiki duk Saturday yake zuwa yaganni Husnah tace to Allah yakaimu ranar Suna haka wata junior tashigo tace anty husnah wai kizo inji uncle bash Husnah tace OK kice ganinan zuwa Meenat ta kebe baki tace wai meke tsakaninku da copper bash ne Husnah tace sirrine amma zakiji nan gaba tashi muje kirakani kawai Meenat ta tashi jiki a sanyaye tabi Husnah zuwa office din uncle bash Suna shiga suka gaishe da bash ya amsa idonsa akan Husnah Takaici Yakama meenat Dan ita ba namijin datakeso irin copper bash Tayi shishigin amma bata samu karbuwa ba Ya kalleta yace zaki iya jiranta a kofa magana zamuyi Meenat cike da bakin ciki ta fito Copper bash ya kalli Husnah yace munhadu da ya shamsu Cikin sauri husnah ta dago kanta da sauri tace meyace maka shikenan nasan yaya zaiyi fishi dani Copper bash yace karkidamu ba abinda zai miki shima naga alama yana da fahimta Nan yafada mata yadda sukayi da ya shamsu Cike da jin dadi Husnah ta tashi tayi hangar waje Yana kiranta amma taki juyowa saboda kunya Tana shiga sukacikaro da meenat Kuka shabe shabe a fuskar meenat Husnah cikin tashin hankali tace lafiya kuwa meenat cikin rashin sanin mezatace tafara in inna Tace wallahi bansan menayi wa copper bash ba ya tsani yaganni aguri sai yakoreni Husnah tace kiyi hakuri zanmishi magana kuma I sha Allah zaiyi dai dai Meenat ta share hawayenta tace Husnah na tambayeki meketsakaninku da shi baki fada min ba Husnah tayi murmushi tabata labarin komai Meenat tace yanzu kinaso kice min kun Dade kuna soyayya da shi Husnah tayi murmushi tace a Amma ni banbashi daman zuwa gidan mu ba Shine yanzu yake cemin ya wa yayana magana Meenat tarike kai alamun jiri nason yarda ita Husnah ta taimaka mata tazauna tace Amina Hakeem anya lafiyarki kalau kuwa Gaskiya kitashi mu dispensary Abaki magani Meenat tace gida ma zantafi tai maka min da phone dina acikin bag Husnah tabude jakar meenat taga wasu hadaddun wayoyi masu tsadar gaske kuda biyu aciki Ta kwaso duka tace gasu meenat ta karbi daya takira driver din ta Taba wa Husnah wayar ta mayar mata dashi jaka ****** Bayan kwana hudu ankai sadakin yaya shamsu gidansu kubra Sannan kuma Abba yasai block da yashi ma aikata sukafara aikin gyaran inda ya shamsu zai zauna acikin gidan ne amma ciki da fall da bayan gida acikinshi Har Dan karamin kitchen dinta basai ta fito tsakar gida ba Komai nasu aciki yake Umma da Husnah sukaje kasuwa suka nemo akwatunansu masu kyau guda uku Aciki akafara zuba kayan lefe Wanda yanzu kusan duk asabar sai sunfita kasuwa Dai dai gwargwado dai aka hada lefen ya shamsu Aka kai gidansu kubra Nan da sati biyu za adaura auren Dubu ashirin ya shamsu yaba wa kubra tayi hidiman biki dashi ***** Hakeem zaune kan kujerar yana hada wani muhimman file Sai Ahmad yashigo yace wai baka gama ba har yanzu kasan time kuwa Hakeem yace nagani ai nan da Kaduna dai insha Allah komai dare Ahmad yace Allah yasa nidai kai nake jira kawai nagama shirina Hakeem yayi dariya yace bantaba ganin ango merawankai irinka ba Ahmad Ahmad yayi dariya yace ai gwamma ni kai inkatashi karawa ai bansan dokin dazakayi ba Hakeem yayi murmushi dayake kara fito da zallan kyanshi Yace tabbas kuwa lokaci yakusa zuwa inji ajikina nakusa samun choice dina sai dai bansan a inabane Ahmad yace kai amma fa akwai rigima Dan madam Laila zatayi rikici bakadanba Hakeem yayi murmushi yace zatawa kanta danzan iya komai akan matata da zan aura Dan itace zabina Kaga kuwa ta taka a sannu Ahmad yace wallahi man I like your style gaskiya zanso Gina gidana kaman yadda kake handling naka Hakeem yayi murmushi yace banbaka shawarar hakanba Dan na tabbatar Aisha ba halinsu daya da Laila ba Kagakuwa ba za amusu hukunci iri dayaba ko Ahamad yace gaskiya Dan hankalin Aishat nagani yasa har nayi shaawar aurenta Ya shamsu yashigo ya musu sallama suka amsa suka mika mishi hanu suka gaisa Ya shamsu yace wa Hakeem gani yallabai Hakeem yace dama zanfada maka ne zamu tafi Kaduna Sai nan da sati daya zamu dawo Hakeem yadauko invitation card na auren Ahmad Yabawa ya shamsu yace muna gayya tarka daurin aure Ya shamsu yayi murmushi yace masha Allah Allah yabasu zaman Lafiya Sai dai ranar yazo dai dai danawa auren Hakeem yakalleshi yace har ansa rana baka fada minba malam shamsu Dama bakayi niyyar gayya tarmu bakenan kokana ganin inka fada ma bazamu bane Ya shamsu yayi murmushi kawai yace aikuna kokari ma da aiki Kuma har ga Allah bani tunanin inna Baku invitation zakuzoba Saboda matsayinmu badayaba Hakeem da Ahmad suka kalli juna Ahmad yace haba malam shamsu karkace haka saikasa muga kaman mu ba mutane bane Ya shamsu yace to afuwan Nayi kuskure Hakeem yace to yanzu dai bazamu samu zuwaba amma muna maka fatan alkairi Tace ban account number din ka inbada nawa gudumawar asiyawa amarya kaji Ya shamsu yace wannan yana daga cikin dalilin dayasa naji fada muku zamanin yanzu kowa yana fama da kanshi Dan Allah kabarshi karka damu kanka Hakeem yace karka damu ni nayi niyya kuma kasan bakyau maida hanun kyauta baya Ya shamsu yace hakane yakaranto wa Hakeem number account din Shima Ahmad yanaji kuma ya kwashe number. Hakeem yace zakaji alert Allah yabada zaman Lafiya Ya shamsu yace ameen nagode Sukayi sallama har wajen mota ***** Da daddare suna zaune tsakar gida ya shamsu yace Abba da ina son ba wa manemin auran Husnah dama yaturo iyayensa Kaga tana gama makaranta sai aiyi aurenko Baban yace ai nalura yaron nan bashir kaman da gaske yakeyi Umma ta ce sau biyu yana kawo mahaifiyarsa muna gaisawa Shamsu yace alhamdulillahi gaskiya konina yaba da bashir Kara shigowar sako yaji a wayarsa yaduba yaga alert ne na dubu Dari biyardaga professor Ahmad Kafin yayi magana wani alert din yasake fadowa daga boss dinshi a office Wato professor Hakeem Shima dai dubu Dari biyar dinne yaturo Sun hada mishi 1 million NIRA cas su biyu suka bashi Nan shamsu yakalli mahifinsa yafada musu Abba yace kai amma wannan uban gida naka Allah yasaka mishi da alkairi Umma tace ameen wallahi ko a mafarki bamutaba tunanin samun dubu Dari nan kusaba Ballantana har million daya Allah yasaka musu da alkairi Kai kuma saika kazauna dasu da zuciya daya Nan dai ya shamsu yakira Hakeem a waya yace ga Abba na zai muku godiya Hakeem yace haba shamsu yanzu saboda kyautar da baitaka kara ya karya ba zaka wahalar da Abba wajen gode mana To gaskiya indai Dan inbari Abba yagode min ne zankashe wayata Insha Allah idan nadawo zanzo nagaisheshi da ka ina amma banda godiya tsakanin malam shamsu Ka gaida umma da kanwarmu Sai da safe Dif Hakeem yakashe wayarsa Dama wayar ya shamsu a handsfree take duk su Abba sunji komai Abba yace gaskiya duk inda akeneman shugaba nagari wannan yaro ya kai Allah yarabashi da sharrin duniya Lafiya Ameen Ameen gaskiya dai bantabajin mekudi hakaba da Jan talakawa ajikinsa kamar wannan uban gidan naka Nan dai suka ta tatattaunawa akan yadda za ayi da kudin Abba da umma dai suka barmai zabi Ya shamsu yace shikenan Allah yakaimu gobe aga yadda za ayi Itakuwa Husnah Allah Allah take safiya tayi taje school taba wa aminiyarta labari Za a ba copper bash daman turowa gidansu Washagari Husnah da meenat suna zaune a inda suka saba zama Husnah tabata labarin za a ba copper bash daman turowa gidansu aikuwa gaban Meenat yatsinke ras Wani tashin hankali ya ziyarceta Tarasa meyake mata dadi aikuwa har aka tashi daga school meenat batadawo dai dai ba Tana kallo copper bash ya budewa Husnah gaban motarshi zai kaita gida Dan tunda aka sanshi yaroki alfarmar zai dinga dawo da Husnah gida idan antashi Da kyar aka yarda mashi Dan saida yahada da mom dinshi Husnah tana daga wa meenat hanu Ina AMIN ABDUL HAKEEM kam batasan tanayiba Ta Lula dunitar tunani ** MEENAT tana zuwa gida tafada cinyar hajiya rukayya kakanta Tafashe da kuka maitsanani Hankalin hajiya rukayya yatashi Dan ta dauki soyayyar duniya ta daura akan 'yar jikan nata bakaramin so takewa Amina ba Nan dai dakyar tasamu meenat tayi magana Tace hajiya nashiga uku nakusan mutuwa Wallahi idan ban auri copper bash hajiya zaku iya rasani dan mutuwa zanyi Nan hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki kimin bayanin komai Nan meenat ta kwashe komai tafada mata Ba abinda yafi burge Hajiya rukayya a labarin sai jin cewan Bash Dan hamshakin mai kudine a kano Tace kwantar da hankalinki kaman yazama naki ma anfama Aure shida Husnah kuma yazama tarihi Zanje Kaduna aiko Zan baki mamaki bash da bakinshi zaice yanasonki Next page Your comments is needed fans Kamar yadda nayi typing metsayi haka nakeson Comments dinki da tsayi Wallahi comments mai tsayi yana burgeni Sosai Ina yinku masoya AKWAI LOKACI=??=??=??=??=??=?? =???=???=???=???=??? [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN

Chapter 5 of 10