abunda kika aikata mana".Kuka kaka ta fashe da shi,jin shewar Aunty yasa tayi wuki-wuki da idi tana kallon Aunty dake kururuwa tuni ta cire Dan kwalinta ta baje guntun gashinta ya gama mikewa tsai-tsaye kartar jikinta takeyi da akaifan dake hannunta,ihu take tana fadin duk wani abu data aikata.Da sauri Zafar yaso ya janye Irfan da Nihla wanda aunty ke niyar kaiwa hari.Saurin ja da baya tayi tana rufe ido dan wani irin tsoro da kwarjinin Zafar ya kuma dirar mata a guje tayi hanyar waje tana sambatu da jiwa kanta ciwo.
A tsawace Miemie tace"kaima kabar gidan nan bana bukatar ko a lahira na kuma ganin wannan mumunar fuskar taka Kamal,na tsaneka na tsaneka".
"baxan iya rayuwa babu ke ba Miemie,idan kika rabu da ni hakan shine karshen rayuwata,amma ina so ki sani ina matukar sonki"kamal ya kare maganar yana yin hanyar waje da sauri.Fadaww jikin Ammi Miemie tayi tana kuka kamar ranta zai fita.
Daddy ne ya dauko tsadaddiyar zoben azurfa da kuma zoben zinari ya saka su a yatsun hannun Nihla tare da cewa"wannan shi ne sadakinki da ni a matsayina na wakilinki na karba a hannun Abban Zafar da kuma shi,ina fatan ba zaki bamu kunya ba ,duk da labarin ya sauya kala Nihla kiyi hakuri ki karbi Zafar a matsayin zabin da Allah ya yi maki".
Hawaye kasa tsayawa sukayi a fuskar Nihla,kai kawai take gyadawa Abba amma ta kasa furta komai.
A rude Ramadan ya shigo gidan yana fadin "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Mota ta kade Kamal ko kamanninsa ma baka ganewa wani mumunnn hadari ya faru da shi,kuma a take a wurin ko shurawa beyi ba".Saurin Jan Miemie Ammi tayi ta wuce sama da ita.
5years later.
Fitowarta daga mota kenan sanye take da fararen kaya na nurses sosai kayan suka mata kyau,tayi kiba a bunta murmushi shinfide akan kyakyawar fuskarta.A hankali take taku harta iso kofar da zata sadata da cikin gidan.Da gudu Karami yaro Dan kimanin shekara ukku ya rugo ya rungumeta yana fadin "oyoyo Mummy".Tuni fara'a ta kuma yalwata akan fuskarta ta duka tare da daga yaron sama tace"Faruk sarkim rigima,oyoyo Abbana"Nihla ta fada.Rungumeta yaron ya yi wanda kallo daya zaka masa ka gane tsantsar kamarsa da Zafar kamar ya yi kaki ya ajiye.Da shi a kafadunta ta karasa ciki parlon yana ta zuba mata surutu.Da gudu Famal da Faman yaran Mieme da Irfan suka rugo tare da rungumarta suka rike mata kafafu suna ihun murna.Jin ihun murnar yara yasa Zafar dake zaune yana aiki a laptop ya tureta ya fito da sauri yana fadin"Miemie kina aikin me❓idan kuma suka sakamun mata ciwo fa❓"da sauri ya karaso ya karfi Faruk tare da janye Faman da Famal yana cewa"ku bar Mummy ta huta yanzu ta dawo aiki fa".
Miemie dake zaune tana wa Little Nihla wasa tace"haba Yaya oyoyon ma,to idan ka hana kowa riketa ai baka hana ta dauko takwararta ba,maza karbeta kafin Abban su Famal ya shigo mu wuce".
Dariya Nihla ta sanya tace"kwarai kuwa Abba Irfan ai yamun takwara dole na dauke kayata,ana yayeta ma ko mutun be so dole ya bani takwarata".
Juyar da kai Miemie tayi tare da cewa"kanki ake ji,ni da tun yanzu zaki dauketa ma aida kin faranta mun".
Dariya Aunty Aisha ta saka dake xaune(Aysha yanzu ita ta auri Ramadan dam sam Kaka taki bari ta kubucewa Family dinta),tace"ku kullun dakun zauna musun ku kenan,ni a hada mun duka yara na fiku bukata,kunga Affan(Al-ameen shine yaci sunan Daddy) sai yama yini ban gansa ba daga wannan ya figa sai wannan ya figa".
Tsuke fuska Hajiya Kaka tayi wacce shigowarta kenan parlon ga alamun kara tsufa duk ya bayyana a jikinta tana cewa"Allah kadai zai saka mun Aisha anshi yaron ki tunda baki bani da zuciya daya,daga yauma na gama tabq yaron uban kowa".Ta kare maganar tana ajiye mata Affan akan cinyarta Dan kimanin shekara 1.
Murmushi Nihla ta yi ta daura hannuwanta akan kafadar Kaka tace"rabu da su Hajiya kakata,ga Faruk nan ba baki baki daya ".
"Yimun shiru ko zan dauki kowa banda gadon rashin kunya,wancan yaro tsab ba abunda ya baro na labcecen ubansa,in daukesa Zafar yazo ya kare mani rashin daraja da rashin arziki ba ruwana ni kinga tafiyata".kaka ta fada.
Murmushi Zafar yayi yace"eh ban badawa dai".Harara Daddy ya jefa masa yace"ya isheka haka Zafar,duk yaron da Kaka take so dole ta dauka".Cikin tabbatarwa Ammi tace"kwarai kuwa".
Irfan da Ramadan da shigowarsu kenan Irfan yace"ta dauki kowa banda little Nihla".Sake da baki Ramadan yace"kaima ta baka ansa daidai da kai yanzu ai"duk parlon suka saka dariya cike da tsananin farin ciki da jin dadi.Kallo daya zaka masu kasan cewa lallai farin ciki ,natsuwa da kwanciyar hankali sun gama ratsa ahalin duk da kalubalen rayuwa iri-iri da suka fuskanta amma yanxu ya zama tarihi babu abunda suke fama dashi sama da tarin farin ciki da kaunar juna,bakin ciki ya kau......
Alhmdllh
*kyakyawar gaisuwata ga Maman noor,Hassan Atk,Muhammad kareeem Mk,Sdeen,ina maku fatan alkhairi aduk in da kuke,hakika nayi farin ciki ta yarda kuka bada gudumawa akan yadamub littafin nan har inda banyi tunani ba,na gode sosai Allah yabar zaman tare*
*ina rokon Allah ya albarkaci abunda na rubuta na daidai a littafin nan,wanda yake akasin haka ina rokonsa ya yafe mana,ya kuma bamu ikon yin amfani da darasin dake cikin littafin*
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels