dan ita kadai tasan me takeji a ƙahon zuciyarta,kamata Aunty tayi ta kaita toilet ta hada mata ruwan wanka bayan ta gama ta taimaka mata ta shirya kafin ta tsareta tayi breakfast ta kuma bata drugs,tuni taji daɗin jikinta sai dai rashin ƙarfin jiki.
Jib dib dib haka zuciyoyinsu ke bugawa a duk lokacin da suka zo kusa da juna,tsayawa yayi jikin ƙofar tare da runtse ido da ƙarfi kafin yayi ƙarfin halin tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Aunty ce ta ansa sallaman da ido ya bita yana kuma yin kicin-kicin da fuska ya rasa me yasa yakejin tsanar matar nan duk lokacin dazai ganta sai yaji kamar ya haɗiye zuciya saboda tsabar takaici da ƙunci.ɗaure fuska yayi kamar an masa sanarwar mutuwa ya ƙarasa shigowa kai tsaye gaban gadon Nihla ya isa cikin murya da sai ka saurara sosai zakaji me yake fada yace"akwai in da yake maki ciwo ne?".
Ɗago dara-daran idanuwanta tayi ta kalleshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta tayi narai narai da fuska kamar zata fasa ihu.wani irin haushi da takaici suka saka ZAFAR a gaba hannu yasa ya bige mata ɗan ƙaramin bakinta da take turowa ya kuma ɗaga hannun da niyar kama kunnenta.
Kuka ta saki tayi saurin kaucewa tana faɗin"ni ba abunda yake mani ciwo".
Harara ya watsa mata tare da sakin siritin tsaki yayi waje abunsa .bayanshi tabi da harara tana guni ƙasa ƙasa.sarai yana jinta amma beko juyo ba ya fice abunsa.
Kai tsaye gida ya wuce,Kabir ne yake jan motar har suka karasa gida bece komai ba a motan yanata dannar labtop din shi,a parking lot ya ajiye motar sannan suka fita a tsaye ya samu Idi mai gadi yana masa sannu da xuwa,fuskar shi kadaran kadahan ya basa hannu cike da girmamawa yana fadin "BABA IDI barka da ƙoƙari".
"barka dai magajin Alhaji,,,,sannu da wowa".
Ansawa yayi tare da juyawa yana kallon jerin motocin da aka ajiye ,kafin ma yayi magama Idi yace"yanzu ba dadewa Dan uwanka yaje ya dauko ALHAJI basu daɗe da shigowa ba".
Jinjina kai yayi tare da cewa"bara na shiga ciki"a fito lafiya suka masa kafin ya wuce cikin gidan.
murmushinsa mai kyan gani ya saki lokacin da idanuwansa suka sauka a kan wani farin kyakyawan Dattijo dake zaune cikin shiga ta alfarma gefansa Ammi ce sai a ƙasa Ramadan da Miemie kowa fuskaraa cike da fara'a.cikin takunsa mai ɗaukar hankali ya ƙarasa gaban Daddy tare da ajiye gwaiwowinsa a ƙasa tafukan hannayenaa ya ɗaura akan cinyar Daddy murya a disashe yace"ko dai nayiwa Daddyna laifi ne,da zai shigo gari ba tare da sani na ba?kuma be nema naje ɗaukosa ba"
Janyo hannunsa Daddy yayi ya miƙar dashi ya kuma zaunar dashi a kusa dashi,,hamnunsa ya ɗaura akan kafaɗar Zafar fuska cike da fara'a yace"bana tunanin Zafar zaimun laifin dahar zan kasa saka shi ɗakko ni,naga kana da ayyuka da yawa ne shiyasa nasa Ɗan uwanka ya ɗauko ni".
Gaɗa kai Zafar yayi alamar gamsuwa kafin yace"ina fatan ka dawo cikin aminci kuma lafiya qlau?"
"lafiya Alhmdllh,ku tashi muje mu gaishe da Hajiya dama jiranka nakeyi ka dawo".
Kicin kicin da fuska Zafar yayi tare da danne jajayen lips ɗinsa kamar zai huda amma ya kasa faɗin komai.
Miƙewa Ammi tayi tace"to sai kun dawo bara na shirya dining kafin ku dawo".
Miƙewa Miemie tayi tana sharara dariya ganin Ramadan yana ta cin magani shima.
Wani banzan kallo ya mata yace"hala na zama taaran wasan ki?".
Buɗe baki tayi da niyar fara surutun nata,"kada ku dame mu a nan"sukaji Zafar ya faɗa kafin kace me duka kowa ya adana maganar da yake niyar yi suka yi gaba.
Tsaki yaja kafin ya miƙe sukabi bayan su Miemie zuwa parr ɗin Hajiya kaka.
Sallama ɗauke a bakinsu suka shiga ,zaune yake akan capet tayi ɗaiɗaya ga apple a hannunta tana ci yayin da ƙafarta ke miƙe akan tum tum sai cika take tana batsewa.kallon su ta soma yi ɗaya bayan ɗaya sai da kowa ya gama zama sannan ta saki fuska tace"a'a Aminu sannu da shigowa,ya hanya?yanxu nake cewa na shigo sai ka rigani kuma sannu da zuwa".
Kan Daddy a ƙasa yace"yauwa Hajiya,barka da gida ".
Ramadan da Miemie ne suka haɗa baki wajen gaiaheta fuska a sake ta ansa tace"ke uwar kilbibi me kila dawo yimun a gida?".
Dariya miemie ta saka tace"da kika samu nazo ko?ina nan zaki zo nemana"
Sai a lokacin Zafar yace"barka da hutawa".
Kamar jira take ta ɗago tana zabga masa harara cike da masifa tace"da ban wuni ba da zaka ganni sarkin mararsa kunya?tun ranar daka gama ɗebemun albarka ka kara shigowa ka gaishe ni ne?to bari kaji dama na tsaya ubanka ya dawo ne sai in ji ta ina ya samoka da har zanaa doka kabi ka take,shege labcecen banza".
Wani irin takaici ya turniƙe Zafar yace"dama gudun wannan faɗan naki yasa bana shigowa ɗin,zancen gaskiya kuma a zamanin nan ba'ayin haka ,ido kika fini ne da zaki min zaɓin mata?".
Hararan da Daddy ya zabga masa ne yasa ya miƙe da sauri yana ficewa daga part ɗin,KAKA na ƙwala masa kira amma ko juyowa beyi ba bare tasa ran zai ansa mata.
"Aminu kana gani,akan idonka Ɗanka ke wulakantani amma ka saka ido kana kallo to ina so kaje ka gaya masa har gidan nan sai nasa ka koreshi dan be isa ya gaya mun maganar banza ba".
ƙasa Daddy yayi da kai yace"Hajiya dan ALLAH kiyu haƙuri insha Allah zan masa magana hakan bazai kuma faruwa ba abunda kike so kuma shi za'ayi".
Tsaki taja tana faɗin "yadai fi maku wallahi"ta ƙare maganar tana cin apple ɗin dake hannunta.sallama suka mata kafin suka taho.
Zafar kam yana shigowa parlo yaci karo da glass jug na ruwa ƙafa yasa ya halbasa ya tarwatse akan tayil lafin yabi ta ciki ya wuce yana huci.
Ammi dake tsaye hammunta riƙe da kula ta bisa da kallo ita kam ta rasa wacce irin zuciya Zafar ke gareshi kuma ina ya gadota ita lamarinsa ma har tsoro yake bata,girgiza kai tayi tace"Allah ya shirya,Lantana kizo ki gyara parlon nan"ta ƙare maganar tana ci gaba da harkokinta.
Tsaye take da waya a kunne shiru tayi alamar tana jin abunda ake faɗa kafin tace"komai ya daidaita Kamal yanzu shiri na gaba kawai ya kamata,banga dalilin sake ɗagawa ba kuma ina so nan da kwana huɗu komai ya tafi mun yacce nake so".
Dariya sosai Kamal yayi kafin yace"da kyau giwar mata cika burinki yana burgeni zuwa gobe zan shigo sai ayi komai yarda ya kamata amma ina so ki kula da kyau".
"baka da matsala da wannan"abunda Aunty ta fada kenan tare da kashe waya.
a ranar aka sallami Nihla daga asibiti danta warke dama haka ciwan mai sikila yake kamar bugun aljannu.
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
*Gobe bazanyi typing ba dan zanyi tafi*
JORDERH✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 31~35
Da matukar karfi Zafar ya fizgi kofar dakinsa ya shiga ,jujuya kai ya soma yana jin kamar zuciyarsa zata fasa kirjinsa ta fito dan takaici,hannuwansa duka biyu yasa yana cukuikuya sumarsa,fadawa yayi akan chair yana fesar da numfashi,jiki a sanyaye Ammi ta gama jera abincin ta fito ta haura sama dan duba Zafar.
Bakinta dauke da sallama ta shiga dakin,tsaye tayi tana kare masa kallo yacce ya hada kansa da gwaiwa daga gani kasan kwata-kwata bashi cikin hayyacinsa karasowa tayi tare da zama gefansa cikin sanyayyar murya tace"Muh'd?
A hankali ya dago rinannun idanuwansa wanda suka soma sauya kala ya zubawa Ammi su ,hannuwansa duka biyu ta runtse cikin nasa tana furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni khairan min ha".
Kamar mai koyon magana ya soma maimaita duk wata addu'a da Ammi ke karantawa cikin kankanin lokaci yaji zuciyarsa ta masa sanyi kwantar da kansa yayi akan kafadar Ammi yana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi tayi cikin san jan hankalinsa tace"kada ka sake fushinka ya rinjayi tunaninka muh'd,ko wanne irin hali ka kasance a ciki karka manta da neman dauki daga mahaliccinmu nasan ka sani kuma ka iya amma wannan zafin zuciyar naka ya daina rudarka kaji".
Ido ya zubawa Ammi kafin ya dauke tare da furta"insha Allah Ammi zanyi kokarin yin haka".
Hannu ta daura a tulin sumar kansa tace"Allah yayi maka albarka muh'd,Allah ya zama gatanka ya kyautata mun rayuwarku kai da y'an uwanka".
Wani kyakywan murmushi ya subuce masa tare da furta"ameen ameen Mamana".
Janyeshi tayi daga jikinta ta mike tare da kama hannunsa tace"muje kaci abinci".
Bai iya mata musu ba haka yabi bayanta har suka safko,a dining suka iske su Abba suna zaune Miemie harta zuba masu abinci suna niyar fara ci.
Karasowa sukayi Ammi tace"Affuwan Daddy bansan kun shigo ba".
Murmushi yayi yana kai spoon cike da shinkafa a bakinsa yace"don't u worry,ae kara a lallaso sarkin zuciya ,kafin ya gama fushin yazo kuma yayi biyayya akan zabin kakar tasa".
Wani irin kwalalo dara-daran idanuwa Zafar yayi baisan lokacin da yace"Daddy badai ka aminta da abunda Kaka ta fada'a ba?".
"sam ko daya bana nufin hakan,amma dai ina so ka sani mahaifiyata ce ita dole zan bata duk abunda take bukata daga gareni,aiki ya rage naka sai kai kokarin nusar da ita zabinka final".Daddy ya fada.
Shiru wurin yayi babu mai cewa komai kafin Ammi ta zaunar da Zafar ta saka masa abinci,wasa kawai yayi da spoon ya tashi ya kama gabansa ba tare da ya wani ci abin kirki ba.
Zaune take yayinda kanta ke jikin kafadar Abbanta mug ne a hannunta na kunu tana sha a hankali,murmushi ya mata tare da shafa gefan fuskarta yace"sarkin rigima ki mayar da hankali ki shanye kunun nan tas kinji,ko kya kara karfi karfi".
Zunburar baki tayi gaba kamar tuguhwar tsire tace"Abba nasha da yawa fa ka tambayi Aunty".
"sosai kuwa y'ata kinsha da yawa kuma kin kara karfi,ni murnata daya da kika samu lafiya kinga gobe sai school ko?"cewar Aunty
Jijjiga kai Nihla tayi tana ansawa da alamar eh.
Sallamar Kamal ya katse masu firansu,fuskarsa cike da fara'a ya shigo tare da zama a daya daga chairs na parlon yace"Abbana sannu da gida".
Fuska fal fara'a Abba ya mike tare da gyara zamanshi yace"lafiya qlau kamaladdin ya kokari da hididdimu?"
Kansa sunkuye yace"lafiya alhmdllh Abba,ashe Nihla bataji dadi ba?dazun nan Aunty take fada mun".
Kallon Nihla Abba yayi yace"alhmdllh ai taji sauki sosai ma,a jiya ne jikin nata yadan motsa".
Jinjina kai Kamal yayi yace"to Allah ya kara lafiya ya kara tsarewa".
Da ameen suka ansa ,sai lokacin Kamal ya gaishe da Aunty sannan Nihla ta gaishe shi tana mikewa tare da barin parlon.
mai aekin Aunty ce ta karaso wurin tare da dukawa tace"Hajiya an gama jera abincin".
Da to ta ansa ta bata izinin tafiya,sannan ta mike ,kallonta Abba yayi yace"Aunty badan karna baki wahala ba aeda nace kin zubo abincin kin kawo mana a nan,ki hadamun tare da Yarona muci tare".
Murmushi dukkansu suka saka kafin Aunty tace"As u wish ranka ya dade".
Mikewa kamal yayi tare da fadin bari na tayaki da tattaro wani kayan,be jira ansar kowa ba ya karasa dining din,bin bayansa tayi ta soma harhada abubuwan da zasu bukata,jujjutawa Kamal yayi ya tabbatar babu mai kallonsa kafin ya ciro wani karamin kulli a aljihu cikin bakar leda ya bawa Aunty.Wani irin murmushi ne ya subuce mata kafin ta soma hada abincin ,ta kuma shiga kitchen ta barbada abun a daidai in da tasan zata ajiye a gaban Abba.Kafin ta fito ta kawo masu abincin a lokacin Kamal harya dawo parlon yana jiranta.
Cike da fara'a tace"sorry Abbanmu na barka a zaune kai kadai amun afuwa dan Allah mai gidana".
"karki damu,ai baki laifi,idan ban jinjina maki ba to bazanga laifinki ko gazawarki ba a wurin kula dani da y'ata sai dai nace Allah yayi maki albarka ya kuma saka maki da gidan Aljanna".cewar Abba.
da ameen ameen suka ansa kafin ta kalli kamal tace"bismillah"tare da kashe masa ido daya.
Spoon Abba ya dauka ya soma juya lafiyayyar julluf din shinkafa da wake dake gabansa wacce taji zallar naman kaji,ya iba tare da bismillah yakai bakinsa,tuni dadinta da dandanonta ya gauraye bakinsa ya soma taunawa a hankali.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Aunty ta sauke yayinda zuciyarta ta cika da tsantsar farin ciki wanda take hangosa bazai taba yankewa b,a lokacin ne natsuwa kwanciyar hankali da hango ta farautaro farin cikinta da cikar burinta wanda ta dade tana saka da kwancewa a ranta tun lokacin y'an mataka.Ko kadan fara'a ta kasa daukewa akan farar kyakyawar fuskarta.a haka tana kallo sukaci Abincin Kamal bai wani ci da yawa ba ya tashi,kasancewar anwa Abba abincin da yafi so yasa ya saki jiki yaci sosai.Bayan kammala cin abincin nasu Kamal yadan jima kafin ya tashi zai tafi,Aunty na ganin fitar kamal ta mike da sauri tana cewa"Abbanmu na manta ban basa sakon nan ba,bara nayi sauri kada ya fice kuma".
Da to ya ansa mata ya kuma mayar da hankalinsa akan kallon news,itakam ta fite a balcony ta samu Kamal tsaye yana jiranta ,a baranda suka karasa kafin ta kallesa fuska kunshe da doki da fara'a tace"aikinka yana kyau kamaladdin ka sani tukuicinka sai yafi karfin tunaninka".
murmushi yayi yace"sai ki fara kirgar awanni da mintina dan yaci,kwanaki sun gajarce ki kumayi sallama da fatan bude sabuwar rayuwarki cikib salama da farin ciki,hakika ina matukar son mata irinki wanda zasu iya sadaukar da komai nasu dan farautar farin cikin su ta ko wacce hanya,badan ina da Miemie na ba da tuni na kutso kaina a sahun manemanki hajiyata".
Far da idanuwa Aunty yayi tace"nikan ae ka zama matattakalata zuwa ga farin cikin nawa,kaine Garkuwata kuma sirrina bana yi sai da kai kuma kaima baka yi sai da ni,ko a hakan ae akwai alakar da bazata taba rabamu ba,kaje sai munyi magana".
Be kuma cewa komai ba ya juya ya wuce ita kuma ta dawo parlo suka ci gaba da kallo.
A daidai wannan lokaci Nihla ta gama yarda da shawarar da zuciyarta ta bata,mayafin dogon rigar jikinta ta janyo ta yane kanta dashi ta kuma janyo bag dinta da phone tayo waje a lokacin tayi sa'a babu kowa a parlon hakan ya kara bata dama da karfin gwaiwar ficewa da sauri daga parlon Idi driver na ganinta ya taso da gudu ,hannu ta mika masa tace"bani key bazan dade ba Zan dawo"sai kin dawo yayi mata tare da bata key din,taja motar tabar gidan.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 36~40
A hankali take tukin motar kamar babu in da take san zuwa har ta iso kofar gidan su Irfan,ta dan jima tana sakawa da kwancewa kafin ta bude motar tare da zuro kyakyawan fararen dogayne kafafuwanta kafin kuma ta fito gaba daya,lumshe idanuwanta tayi tana mayar da lumfashi a lokacin da iskar wurin ta buso iska mai sanyi,cike da natsuwa kamala ta soma daya zara-daran eye lashes dinta da suka kwanta akan kyakyawar farar fuskarta .Tun daga kafa ta soma kallon butt shoe din dake sanye a kafarsa ta dago zuwa ga black jeans dake jikinsa ,ga red shirt mai karamin hannu daya saka a gaba anyi rubutu da bakin kala an rubuta handsome a kafadansa kuma hirami ne rataye kamar ko yaushe haka har ta sauke idanuwanta akan fuskarsa ,wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin sanyayyan murmushi ta kuma hada haruffan bakinta wajen furta"Yayana!"
Kallonta kawai Irfan yakeyi kafin ya kawar da kansa gefe tare da fadin"yan mata Nihla sai ina❓"
Dam dam haka kirjinta ya bada sautin bugawa da matukar karfi,zata iya rantsuwa da Allah wannan karon shine karo na biyu da Irfan ya kirata da sunanta.Wani irin faduwar gaba ne ya dirsan mata a matukar tsorace tace"Yayana ka daina kirana,ka kuma daina zuwa in da nake,ka kuwa san hakan irin cutarwar daya haifar mani❓,ko nayi maka wani laifi ne❓".
Daga gira daya sama Irfan yayi yana kuma sakin kyakyawan murmushinsa yace"Maryam matsawa nayi na baki wuri kidan sha iska,kinsan idan ka tsaya wuri daya baka hangen abunda zai zo a gaba hakan yakan zama cutarwa ga rayuwar mutun! ke babu abunda kika nema kika rasa,shiyasa nima na fita neman abunda zan rufawa kaina asiri".
Kallonsa kawai take kamar idanuwanta zasu fado,a iya dan karamin tunaninta na shekarunta da fahimtarta ta tsaya ta auna kalamansa amma sam ta kasa fahimtar in da ya dosa,kawar da tunanin tayi a ranta tare da cewa"ban fahimceka ba".
Fuskarsa ya shafa kafin yace"is a matter of time,soon zaki fahimta yarayen gwari-gwari,excuse me"Irfan be jira cewar Nihla ba ya juya yayi cikin gida tare da zuba hannuwansa duka biyu a cikin aljihu yana wata tafiyar kasaita.Wasu irin hawaye ne masu matukar zafi suka samu nasarar gangarowa daga idanuwanta zuwa kan fuskarta,dan bubbga kanta tayi taga ko mafarki takeyi,lallai ilaihi kam idonta biyu haka ta raka Irfan da idanuwa harya karasa shigewa cikin gida,dafe kanta tayi tare da fadin"me yake shirin faruwa ne da ni❓"tayiwa kanta tambayar da babu wanda zai iya ansa mata ita.Fizgo marfin mota tayi da sauri ta shige ta kama hanyar gida zuciyarta cike da tunani fal.Wani irin fargaba mai cakude da tsantsar gangariyar tsabtatacciyar soyayyar Irfan ke kuma taso mata ,lokaci zuwa lokaci takan share hawayen dake zubo mata a haka harta isa gida,damuwa ta dabaibayeta ko abincin dare kasa fitowa taci tayi a haka ta kwana tana kallon babu dare mai cike da kunci da tsawo irin na wannan rana data riska,sai wurin asuba kafin wani wahalallan bacci mai cike da mafarkai mararsa dadi iriri data yi.Juye-juye takeyi da kanta kallo daya zaka mata kasan cewa tana cike da tsananin tsoro ga wata irin zufa dake keto mata a duk ilahirin jikinta,duk ACn dake dakin hakan bai hanata hada uban gumi ba,hannuwanta duka biyun rirrike suke da tattausan farin blanket din dake shimfide a gadon,idanuwanta dake rufe sai kyarma sukeyi yayinda hawaye suka yowa gefan kunnuwanta saukar aradu suna zuba babu kakkauta,da matukar karfi ta furta Abba,tare kuma dayin zumbur ta farka daga baccin wahalan daya dauketa,da matukar karfi kirjinta ke bugawa ,da rairafe ta safko daga bed dinta tayi waje da gudu.
Zaune yake a chair yana karatun jarida kamar yacce ya saba duk safiya,duk da yau ya tashi bai jin dadi sam balle kuma karfin jiki ,a guje ta fada a kansa tare da rungumesa da matukar karfi tana rawar sanyi tana fadin"Abb...Abba,Abbana".Abba kam sakin jaridar hannunsa yayi tare da rungume Nihla da karfi a jikinsa a tsorace yake duba bayanta ko wani abu ya biyota ne,babu komai hakan yasa ya soma bubbuga bayanta ganin sam bata cikin natsuwa bata ma san me takeyi ba,addu'a ya soma tofa mata kafin a hankali ta fara dawowa daidai ,yanajin yarda zuciyarta ke bugawa da karfi,dagota yayi tare da zuba mata idanuwa hannu yasa ya tattara mata tulin sumar kanta data baje duk a fuskarta yace"menene❓meke damunki haka❓".
Numfashi ta mayar tare da zaro kwala-kwalan idanuwanta ta daga hannu tana shafa fuskar Abba,wani sanyayyan ajiyar zuciya ta sauke murya na rawa tace"Abbana kai....Kaine❓"
Murmushi ya sakar mata tare da cewa"kwarai kuwa y'an matan Abbanta ni ne da kaina Abbanki farin cikinki maganin matsalarki,meye ya rudani haka❓".
Kasa tayi da kai tare da share hawaye tace"Abbana nayi ma..mafarki ka...Katafi ka barni".Cewar Nihla
Jan kumatunta yayi yace"kice yau da rigima kika tashi dai,gani a zaune babu in da zan tafi na barki,idan ma zan barki sai na tabbatar na baki Garkuwa wanda da taimakon Allah zai kula mun da ke,bana son maganan maza tashi kije kiyi shirin scul you're running out of time Dear,and look at your body".
Sai lokacin hankalinta yakai akan shigarta,sanye take da trouser ash colour iyakarsa rabin cinyarta sai vest,sam ta manta yarda ta fito sai a lokacin taga jikinta,mikewa tayi ta soma tafiya tanayi tana waiwayen Daddy wanda fuskarsa ke dauke da murmushi,tana shiga bedroom ya kuma yin murmushi tare da dafa saitin zuciyarsa wanda yake jinta kamar an daura masa dutse kuma take shirin daina aeki yanzu.
Aunty dake tsaye a baya tana kallonsu ta saki dariya ciki-ciki tare da cewa"naga in da karshen soyayya zata kai,duk wannan iskancin zaki daina shi ne nan da lokaci kadan kizo ki fuskanci duniya,katuwar banza da ke amma kina rungumar ubanki har yanzu".Ganin Abba zai juyo yasa Aunty saurin karasa cikin parlon tana fadin"ranka ya dade an shirya komai kazo kayi wanka bana so ka makara a office".
Gyadawa Aunty kai kawai yayi ya mike ya wuce daki yayin da ita kuma ta raka bayansa da harara tare da jan siririn tsaki.
30mnt later.
Parlon ta fito tana saka agogo a hannunta kamar kullun sanye take cikin white unifoam dinta tayi masifar kyau ga scul bag dinta goye a baya,zaune ta samu Daddy yana zaman jiranta shima sanye cikin farar shadda malum-malum murmushi ne ya yalwata akan fuskarta ta matso kusa dashi da sauri tace"Abba ka...Kayi kyau...So..Sosai".
Dariyace ta kwace masa yace" A dan tsoho dani mai sunan Matana❓"
Hannu tasa a baki tace"shiiiiii Aunty zata jika"ta fada bayan tayi kasa da muryarta.
Dariya yayi kafin ya mike yace "mujr kiyi break,girgiza kai tayi tare da fadin"a'm not hungry yet Abba".
Ba yarda ya iya haka sukawa Aunty sallama suka fita ba wanda ya karya a cikinsu,yau Abba da kansa yakai Nihla scul,farin cikinta kam yaki misaltuwa dan zama da Abba ya kawar mata da duk wani kunci da tunanin Irfan.
Cup din tes yakai bakinsa tare da surfa kadan ya ajiye cup din ya mike ya tattara keys dinsa yana shigowa parlon "Ammi i'm going" ,shine abunda ya fada.
Wani banzan kallo Hajiya Kaka ta masa tace"kai karka damemu da wata shakakkiyar muryarka a wurin nan,ina uwarka❓".
Abu ya hadiye da kyar kafin ya raba ta gefen kaka zai wuce,cukuikuyishi tayi tare da janyo shi tace"kutumar uba! dan kaza -kazanka ko Aminu zai mun haka ne❓bare kai lafcecen banza marar mutunci".
Runtse ido da matukar karfi Zafar tayi yasa hannu tare da cire hannun Kaka daga jikinsa a kausashe yace"wannan ya zama na karshe da zaki kara rikeni! nasha fada maki Daddy haifarsa kika yi while Zafar a santa kuka hadu,wallahi ina dab da yi maki rashin mutunci a gidan nan"
Zaro ido da karfi Hajiya Kaka tayi ko kadan babu alamun mamaki a tattare da ita tace"yau ka fara ne❓ae bazanji komai ba danka wulakanta ni tunda haka uwarka Maryam ta koya maka,ina so ka sani yau zan gwada maka isa da iyawata zanga me zaka iyayi"
Murmushi kawai yayi yace"gulmarki da mulkinki su tsaya kan abunda kika haifa da wanda yaji zai iya dauka,ina binki ina maki biyayyah amma tunda kin zaba mu barar da darajar tamu to bismillah,ina kara tunatar da ke ba'awa Muhammad Zafar dole".Be jira cewarta yayi gaba abunsa.Da kallo Kaka ta bisa kafin da karfi ta soma jiran "Aminu,Al-ameen".
Da sassarfa Ammi ta fito daga kitchen tana dukawa gaban Hajiya kaka tace"Hajiya ya fita tun safe".
"eh dole zaki gaya mun ya fita,shiyasa ashe kika zugo danki yazo ya karemun rashin daraja da tarbiya a kaina❓to bari Aminun yazo gidan ,sai kin gaya mana in da kika samo wancan marar tarbiyar yaron dan ni kam ba jinina bane sam"ta juya ta fice da sauri.
Mikewa Ammi tayi tana jin kuna da zafi a ranta,ita kam ta rasa yaya zatayi da matsaltsalun dake dosota,yanzu kam bata san meye Kaka zata kuma zuwa dashi ba.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 41~45
Kallon time Miemie tayi a agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,kallonta ta mayar ga Nihla data zabga uban tagumi ta lula duniyar tunani,buga desk din da suke zaune tayi da karfi,firgigit Nihla ta dawo daga duniyar tunanin data lula a tsorace,kallonta Miemie tayi tare da cewa"malama ki kalla agogo 5mnt da tashi amma ina tsaye a kanki kina tunani".
Murmushi Nihla tayi jiki a sanyaye ta mike tare da saba bag dinta a baya tace"muje".
Juya ido Miemie tayi tare da fadin"Allah ya sawake,amma kima cirewa kanki tunani akan wannan gantallan yaron".
Saurin juyows Nihla tayi fuska daure tace"yanzu Miemie Yayan nawa ne gantalalle❓"
Tsaki kawai miemie tayi tace"ko nayi rantsuwa baxanyi kaffara ba,tabbas wannan iskancin daya tsiro akwai dalilinsa gara maki ma ki farka daga mafarkin da kikeyi ki gane a gaske kike".
Shiru Nihla tayi batace komai ba taci gaba da tafiya abunta zuciyarta cike da tunani,bin bayanta Miemie tayi suka karasa gate,yau kam Drivern