Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
Nihla ya fara zuwa."muje "cewar Nihla. "a'a zan jira Driver nasan yana hanya"Miemie ta bata ansa.Daga kafada tayi alamar ba komai ta shiga mota idi yaja suka tafi.ji tayi wata irin masifaffan yunwa na kartar mata ciki dan duk yau babu abunda ta saka a cikinta ko a lokacin da bata lectures ta gagara cin komai,runtse ido tayi tare da daura hannu akan cikinta ji takeyi kamar ta bude ido ta gansu a gida ,shiru tayi ta soma sauke ajiyan zuciya har suka iso gida,Alhmdllh shine abunda ta fada kafin ta bude motar ta zuro kafarta sannan ta fito gaba daya,tun a bancony ta cire hijab da bag dinta tana shigowa ta jefar dasu akan chair zare shoe da sock tayi ta wuce kitchen ,Murmushi tayi tare da gaishe da Aunty Lami.Dafa kanta Aunty Lami tayi tace"yau an dawo da yunwa ,kin koyi sa'a yau na maki abunda kika fi so". Rungume Aunty Lami tayi tare da cewa "na gode ,yau zanci Danwake". "keee meye kikeyi haka Nihla ❓watau bazance ki daina abuba ki daina,meye na wani rungumarta❓,your'e the princess and u will always be ki kama kanki fice mun a nan". Rau-rau da ido Nihla tayi alamun zatayi kuka murya na rawa tace"Aun...Aunty zan....Zu..Zuba Danwake ne". Shiru Aunty tayi mata ta dauki knife ta wuce waje abunta....Kasa cewa komai Nihla tayi ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dauki plate ta saka Danwaken ta raba ta gefen Aunty lami ta wuce. Da k'yar ya iya karasowa gida,yana tangadi ya samu ya shiga parlon,dafe kansa yayi da karfi wanda ke barazanar tarwatsewa ji yayi lokaci daya komai nasa yana niyar dainawa,a hankali ganinsa ya soma daukewa hakan yayi daidai da tsayawar bugawar zuciyarsa ya kuma zube akan gwaiwowinsa yana jujjuya kai lokacin da wani tari ya turnukeshi,Fitowarta daga kitchen kenan idanuwanta suka sauka akan Abba wanda ke niyar karasa faduwa.Plate din hannunta ta saki ya tarwatse abincin ciki duk ya bata mata fararen kayan dake jikinta da matukar karfi ta furta"Abba" a guje ta kuma karaso garesa ya fado akan cinyarta.Rirrikesa tayi tana bubbuga gefan fuskarsa tare da kiran sunansa.Ganin komai nasa ya tsaya idanuwansa a rufe yasa ta fashe da kuka tana girgiza shi,beko motsa ba hakan ya kuma tayar da hankalinta janye kansa tayi daga kan cinyarta ta mike tare dayin waje da gudu har tana neman kifewa kai tsaye gate da taga an bude tayi a guje,gashin kanta data nannade duka ya tarwatse a bayanta da fuskarta har bata ganin gabanta.Da matukar karfi ya taka burki ganin ta dososa a guje,duka ya kaiwa sitiyari tare da rikesa da karfi yana kallon yarda jikinta ke jijigawa juyawa yayi yana kallon su Idi driver da sauran masu aekin gidan da kowa ya tsaya kamar an dasa shi yana so yaji meke faruwa a cikin gidan,wani irin zafi da kunci ya ziyarci zuciyarsa lokaci daya,da karfi ya runtse idanuwansa da suka soma sauya kala ganin tayi taga-taga zata kife duk rabin breast dinta a waje baisan lokacin daya fizge murfin motar ba ya bude ya fito da sauri,a lokacinne Nihla take neman gittashi ,hannu yasa tare da fizgota da karfi beyi wata-wata ba ya wanke fuskarta da mari cikin kausasshiyar murya yake fadin"ke mahaukaciyar ina ce❓ki kalli jikinki a haka kike fitowa kina gudu maza na kallonki❓"ya kare maganar tare da girgiza kafadunta da karfi. Wasu taurarin wahalane suka gitta mata,ta hadiye busasshen yawu da kyar ,sai lokacin hawaye ya samu damar gangarowa daga cikin idanuwanta ta soma fadin"Abba...Ab...Abbana ka taimaka ..M..Mun" Sai lokacin Zafar ya kuma binta da kallo farar rigar jikinta shara-shara har bra dinta kana kallo,wani takaicin ya kuma rufesa ji yayi kamar ya shakareta uban kowa ya huta a tsawace yace"tsayuwan me kuke a nan kuje kuci gaba da aikin ku mana"sai a lokacin ma'aekatan gidan suka watse jin maganar Zafar cike da fushi. Tsaki yaja yana kallon yarda jikinta ke rawa sam bata cikin hankalinta yasan kome zaiyi ba fahimtarsa zatayi ba,button din black suit din jikinsa ya balle ya zare rigar daga jikinsa ya kama hannunta tare da saka mata,gashin daya bazo mata ya tattare baya tare da daurewa yaja hannunta da karfi har tana had'a steps yayi cikin gidan da ita,sai da suka shigo parlo kafin ya saketa aeko har rige-rigen isa wurin Abba dake kwance suke,sai lokacin Aunty ta fito "innalillahi"ta fada tare da fashewa da kuka tayo kansu da gudu tana fadin"Maryam meya samu Abban❓yaushe ya shigo❓" Tsaki Zafar yaja tare da kuma tamke fuska kamar an aeko masa da mutu yace"ke saka hijab dinki ki taimaka mu saka shi mota" Mikewa Nihla tayi tare da share hawayen dake ambaliya akan face dinta ta soma juye-juye ta rasa ma ina zatayi.Haushine ya kashe Zafar a tsawace yace"wai hauka ne ya shiga kanki ko uban meye❓ga hijab dinki a chair malama" Sai lokacin ta kallah inda ya nuna mata da sauri ta fizgi Hijab ta saka a juye tazo da sauri ta kama Abba,bata da karfi bana da abunda zata iya taimakawa amma a haka ta rike Abba dan daukar gaba daya Zafar ne yayita a haka suka isa mota,shiga tayi ya daura mata kanshi a cinyarta ya rufesu ,be jira cewar kowa ba ya figi motar ya nufi asibiti. Tun kafin ya isa yasa an hada masa komai,mintoci kadan suka kaisu asibitin saboda irin gudun da yayi,a gadon daukar mararsa lafiya aka dauki Abba,a guje Nihla tabi bayansu har suka isa kofar emergency a nan ne Nurse ta tsayar da ita suka wuce da Abba ciki,akan gwaiwowinta ta fadi she's hopeless and spechless ji takeyi kamar ba'a duniyar take ba,gaba daya hankalinta bai kanta da kyar take fitar da numfashi sai haki takeyi,sai lokacin Zafar ya karaso wurin yana gyara xaman handgulofs a hannunsa da gefen ido ya kalleta ya wuce ciko abunsa. Da sassarfa Aunty ya karaso wurin fuskarta tab da hawaye,Nihla na ganinta tayi jikinta ta fada tana fadin"Aunty...Ab...Abba Aunty kice ya ta..tashi kada ya barni". Bubbuga bayan Nihla ta soma yayin da ta saki wani kayataccen murmushi sai kuma ta daure fuska cike da damuwa take fadin"kiyi hakuri insha Allah zai samu lafiya,bazai tafi ya barmu ba a lokacin da muke tsakanin bukatarsa,zai dawo garemu shine Garkuwarmu kuma nasan Allah bazai dauke mana shi ba,ki daina damun kanki kinsan baki da lafiya,bansan ya zanyi da rayuwata ba idan kema wani abu ya sameki ba,bana so ku barni bana da kowa sai ku dan Allah ki kwantar da hankalinki kiwa Abbanki Addu'a". Karar bude kofar emergency yasa Nihla saurin sakin Aunty ta juyo,tsaye tayi tana kallon Zafar da yake tsaye fuskarsa cike da tsananin damuwa ,da matukar karfi kirjinta ya buya ta fara raba ido,cikin sanyayyar murya yace"well Allah yayi ma...."Da karfi ta ingije Zafar tayi cikin dakin a guje..... *Allah ka gafartaws iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 46~60 Runtse idananuwanta tayi da karfi tana karanto duk wata addu'a da tazo q bakinta,gyaran murya yayi tare da cewa"ki shiga Abba naso ya ganki"be jira cewarta ba ya raba ta gefanta ya wuce da sarsarfa da kuma rokon Allah ya bashi nasara akan abunda zai tafi nema.da gudu Nihla tayi cikin emergency din kai tsaye gadon da Abba ke kwanta ta isa gabansa ta duka fuskarta na zubar da hawaye hannun Abba ta riko, Idanuwansa dake lumshe ya soma budewa a hankali kallo daya zaki masa kisan ya jigata ciwo yaci karfinsa,sanyayyan murmushi ya sauke tare da daura hannunsa akan Nihla ya shafa muryarsa bata fita sosai yace"kina matukar kyau idan kina fushi musamman idan kika tura gakin nan a gaba kina hawaye"ya kare maganar tare da dan tura bakinsa a gaba.Murmushi sosai Nihla ta saki tare da share fuskarta ta daura kanta akan kirjin Abba tare da cewa"Ab...Abba ka...ka tsorata ni sosai,..Bana so ka...ka tafi ka barni". Dogon hancinta yaja yace"ita dai Maryam dita da kika gaji sunanta ko kadan ba ragguwa bace,takan tunkari komai ya taso mata takanyi addu'a kuma bata yawan kuka har Allah ya bata nasara akan abunda take nema".Yunkurawa Abba yayi da niyar tashi,tashi Nihla tayi ta taimaka masa ya zauna tare da jingina a bango,gefansa ta zauna hannuwanta cikin nashi tare da tsura masa dara-daran idanuwanta wanda suka sauya launi saboda tsabar kuka. Kallonta Abba yaci gaba dayi tare da cewa"Maryam! bana so ki zama ko yaushe a cikin kuka da kunci,ki sani Allah baya jarabtar bawansa da abunda yasan bazai iya dauka ba,kuma duk abunda Allah ya tsara bashi da mahani Maryama,kiyi kokari wurin bin dokokin Allah ,ki kula da kanki ,Faduwa bashi ke nuna rashin nasara ba a rayuwa,hasalima shine matakin da zaki kara dage damtse ki kuma fuskanci kurakuren ki har ki samu daman gyarawa,ki zama mai gaskiya a rayuwa duk halin da kike ki zama mai gaskiya da rikon amana,babban shawarata a gareki shine a duk in da kike,yanzu ne ,anjima ne,gobe ne jibi ne ko a wanne lokaci ki kasance mai hakuri". Matse hannun Abba tayi da karfi tuni hawaye sun wanke mata fuska kyarma ta kwace mata cikin muryar kuka tace"Abba ..Kana mun ..Ma..Magana kamar Ka..Kana mun wasiyyah...Idan ka ta..tafi waye zai kula dani❓waye zai za..zauna dani❓" Dayan hannunsa ya daura akan nasa yace"ba wasiyyah nake maki ba ,ina baki shawara ne a matsayina na mahaifinki kuma masoyinki mutuwa kam zata iya zuwa ko wanne lokaci ba babba babu yaro,gare ni ko gareki,kina da wanda ya fini Maryam,Allah shine gatanki kuma shine zai yi yanda yaso da rayuwarmu ,Allah baya daukewa bawa wani abun ba tare daya basa wani abun ba". Aunty ce ta shigi dakin hakan yasa Abba kura mata idanuwa da wani irin murmushi a fuskarsa mai wuyar fassaruwa,maido da kallonsa yayi ga Nihla yace "kije gida ki canza kayanki ki taho mana da abubuwan bukata".Shiru tayi girgiza hannunta yayi tare da cewa "ba abunda zai faru kije kinji".Gyada kai tayi tare da mikewa ta fita daga dakin. Hannuwansa zube a cikin aljihun wandon suit dinsa ya shigo parlon nasu,tafiya yakeyi cikin kasaita,izza da isa tafiyar yakeyi kamar marar lakka a jiki sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin Ammi da Daddy zaune a parlon sosai yaji dadin ganinso rufaffun takalman kafansa ya zare tare da karasawa cikin parlon a kasa ya zauna gaban Ammi da Daddy kansa na kallon kasa. Dafa kafadunsa Daddy yayi tare da cewa"meke faruwa Zafar❓ yanayinka ya nuna kana son wani abu" Dago jajayen idanuwansa yayi tare da hada hannuwansa biyu kamar zai fashe da ihu yace"Daddy ,ina matukar sonka! ina kuma alfahari da kai,kaine daya wanda nake da zan nuna a duniya nayi kuma alfahari da duk abunda na nema kana kokarin bani,Shin Daddy kana sona kuwa❓ kuma a shirye kake da sadaukar da komai a kaina❓" Matsowa Daddy yayi daga jingine a jikin kujera da yake cike da matukar mamaki da tarin tambayoyi yake kallon Zafar sannan yace"me yake faruwa da kaine Zafar❓ wannan wacce irin tambaya ce❓" Kasa yayi da kansa yaci gaba da cewa"Daddy ka ilmantar dani ,kuma ka koya mun tarbiyyah babu ta in da ka rageni ,kai ka biyamun islamiyyan da nayi karatu nasan abunda Allah da manzon sa suka ce,ina neman alfarma a gareka da rokonka akan ka taimaka ka tashi muje asibiti kaga Babban Amininka Abba Umar,tabbas yana cikin matsanancin hali da babu wanda ya kamata ya zauna tare dashi sama da kai,ina rokonka ka manta baya ka manta komai kaje ka rungumi amininka ko da sau daya ne komai zai faru dashi ya faru a gabanka,Daddy ina mai takaicin gaya maka Abba Umar an ciyar dashi guba mai tsananin karfin data kwana biyu a jikinsa tana yawo,ina mai gaya maka yanzu haka yana matakin karshe da bazai iya haura y'an awanni ba a duniya,munyi iya yinmu sauran kuma yin Allah ne Daddy". Tunda Zafar ya fara magana komai na jikin Daddy ya tsaya cak,kallon Zafar yakeyi kamar yau ya fara ganinsa da matukar sauri ya mike tsaye tare da furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,hasbunallahu wani'imal wakeel".Ammi kam tuni fuskarta ta jike jagab da hawaye gaba daya ta rasa natsuwarta ganin Daddy yayi hanyar fita yasa ta figi mayafin dake kusa da ita ta bisa baya harda dan gudu-gudunta.Da sauri Zafar ya mike shima yabi bayansu kafin ya fito har su Daddy sunbar gidan,motarsa ya shiga shima ya rufa masu baya,sosai ya tsorata da yarda Daddy ke driving din ikon Allah kawai ya kaisu asibitin,ko daidaita parking beyi ba ya fito da sauri Ammi tabi bayansa,wata Nurse ya tambaya ta fada masa in da yake be jira komai ba ya wuce emergency din.Yana shiga idanuwansa suka sauka akan Abba dake kwance tamkar gawa idanuwansa a lumshe ga Aunty zaune a kusa dashi sai magana take masa amma ya ki kulata,gaban bed din Daddy ya karasa tare da daura hannunsa a hannun Abba,wani sanyi ne ya ratsa shi tun daga kasan kafarsa har izuwa tsakiyar kwakwalwar kansa wasu sanyayyun hawaye ne suka soma zuba ta gefan idanuwansa ko be bude ido ba yasan Al-ameen ne,haka kuwa akayi Daddy yace"Umar ka gaya mun wanda yayi maka haka,na maka alkwari ko da komai nawa dana tara zai kare zan kare rayuwata wurin nema maka hakkinka". Sai lokacin Abba ya bude idanuwansa tare da kallon Aminin nasa ya saki murmushi,idanuwansa ya sauke akan Aunty sai lokacin ya kulata yace"ki bamu wuri".Jiki a sanyaye ta mike tare da bin gefan Ammi ta wuce waje tana sharar kwalla.Murmushi Abba ya saki tare da cewa"wannan farin ciki kawai ya sakani Al-ameen ta dalilin hakan yau gashi tsawon shekaru ka dawo gare ni,ni hakan ma ya isheni ina kuma so kamun alkwari ko bayan raina kaji wanda yamun hakan ka barsa kada kayi kokarin daukar mataki balle tona asirinmu". Zama Daddy yayi tare da cewa"bana da wanda yafi mun kai,kuma kake kokarin sakani yafewa wanda ya cutar mun da kai❓" "ka yafe mani"shine abunda Abba ya fada.Saurin rikesa Daddy yayi yace"a kullun rana bana da burin daya wuce kasancewa tare da kai,bansan da wacce fuska bane zan iya kallonka ni ya kamata na baka hakuri,nikan na manta komai na kuma yafe maka". Hawaye ne ya zubo masu su dukkansu,dariya sosai Abba yayi tare da cewa"ta yaya ni da kaina kuma zan iya fushi da farin cikin rayuwata! kullun cikin Farautar sa nake da neman ya dawo a rayuwata".Tashi yayi zaune suka rungume juna,sosai farin ciki ya ziyarci zuciyar Zafar dake tsaye yana kallonsu,hannu ya tafa tare da sakin dariya ,sosai dariyan tayi masa kyau,kasancewar yaune rana ta farko da fuskarsa ta kasance da yalwatacciyar dariya haka..... Da saurinta ta dawo tsaye tayi a bakin kofar emergency din ,jikkar hannunta ta saki tuni jikinta ya kama kakkarwa ta tsurawa Daddy da Ammi ido da suka fito fuskar Ammi duk hawaye yayin da Daddy ke goge idanuwansa da gefan babbar rigarsa. A guje tayi cikin dakin,tur kashi nan ake yinta tsaye tayi kamar statue ganin Zafar yaja zanin gado tare da rufe Abba dashi cikin sanyin murya yana fadin"Allah yaji kanka Abba,Allah ya kama rahma". Wata irin gigitacciyar kara Nihla ta saki tare da fadin"Abba"da matukar karfi,kafafuwanta kasa daukarta sukayi kyarma suke mata da rairafe ta karasa jikin bed din ta jaje zanin gadon ,fadawa tayi a cikinsa tare da sakin wani irin kuka mai ciwo,cin rai da kuna zuciyar mai sauraro,gaba daya ta firgice ta gama fita a hayyacinta. *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 61~65 Runtse ido da karfi Zafar yayi,dan ko kadan baya son hayaniya yanzu zata sauya tunaninsa gaba daya,hannu yasa tare da dago Nihla daga jikin Abba ido cikij ido ya kalle tare da cewa"pray for him,banga amfanin kukan ba"yana gama fadin hakan yayi waje da ita yayin da aka hada gawar Abba zuwa gida,tun daga wannan lokacin wani ciwan kai mai tsananin zafi ya dirarwa Nihla ko kadan ta nemi hawaye ta rasa wata irin kuna zuciyar keyi shiru tayi sai raba idanuwa takeyi kamar wacce tayiwa sarki karya a haka take zaune kamar wacce aka dasa har suka isa gida,da kyar ta samu damar taka kafafuwanfa saboda wani irin kyarma da suke mata ta samu ta shiga parlo tare da fadawa akan kujera ,sam bata gane komai bare kuma hakurin da Ammi ke bata,da ido tabi gawar Abba da kallo wanda Alhaji Al-ameen wato Daddy da Zafar da wasu ma'aekatan asibiti da suka dauko har suka bacewa ganinta.Aunty dake jikin window dakinta tana leke tabe baki tayi tare da fadin"saboda wulakanci da neman sababi wai sai an kawo man gawarsa a gida ,uban meye zai mun in ba salan a bata ma mutane tayil da carpet din gida ba,ko kadan basu kyautata mani ba wallahi". Murmushi kamal dake jinta a waya yayi tare da cewa"duka minti nawa zaiyi a gidan da har zaki damu kanki Hajiyata❓yanzu ae farin ciki ne naki kin rabu da Allah kakai sai kuma ayi shirin fara sabuwan rayuwa"dariya suka saka Aunty na fadin"wallahi Kamal baka da dama". "kice bama da dama dai ,gani nan shigowa gidan yanzu kin sanmu akwai saurin rakiya kabari"Kamal ya kare maganar yana kashe wayar hannunsa. Sai lokacin ta zira Hijab ta fito parlon ita ma,a hankali gidan harya fara daukar mutane dan parlon babu masaka tsinke,tana fitowa kowa hankalinsa ya koma kanta bata san lokacin da ta kakaro hawayen dole ba,anan masu kuka suka fara masu bada hakuri suka fara zama tayi kusa da Ammi tana sharar kwallah,Nihla kam da ido kawai take binsu ko kwakwaran motsi ta kasa yi. Cike da natsuwa ya shigo cikin parlon tare da cewa"Nihla kizo kiwa Abba addu'a,sai kuma iyalin shi"Zafar ya kare maganar yana komawa ciki,zumbur Aunty ta mike tayi gaba har hada steps takeyi.Girgiza Nihla Ammi tayi tare da mata alama da ido akan tabar damuwa.Jijjiga kai tayi tare da mikewa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tayi hanyar dakin Abba har ta iso bakin kofar,tsaye tayi tana jin yarda bugun zuciyarta ke tsananta,kokarin tattaro sauran kuzarinta tayi tare da daga kafarta ta shiga dakin tare dayin sallama ciki ciki,karasa tayi a in da gawar take ajiye tare da durkusawa akan gwaiwowinta. Kuka rurus Aunty keyi tare da fadin"Allah kajikan mijina,hakika nayi rashi wanda bazai musaltu ba ,bani da wanda ya fika ba kuma zan taba samu ba,tunda nake da kai baka taba cuta mani ba,halinka na gari ya bika Abbanmu,ka tafi kabar mani y'ata marainiya,insha Allah zan rike Nihla kamar nice na haifeta Allah ya maka rah..."maganarta ta sarke sakamakon wani sabon kukan daya kubce mata mikewa tayi da sauri tare da barin dakin tare da toshe bakinta.da kallo kowa ya bita.Hannun Nihla na kyarma ta dauka tare da daurasa a jikin Abba,trying had not to cry,da kyar ta iya bude baki tare da fadin"Allah yayi maka rahma,Allah yakai haske kabarinka,zanta yi maka addu'a kai da Momyna"hannunta ta janye tare da dukar da kanta kasa.Saurin dagowa tayi tana kallon su Zafar da suke kokarin daga Abba daga dakin,Tashin hankalin da ba'a saka masa rana tuni ganinta ya fara komawa dishi-dishi yarda numfashinna ke fizga,shakar iska na kokarin kubucewa hunhuna,ashe ko bayan dara akwai wata caca,tirkashi,bugun zuciyata sai kara jaddada mani rashin kwarin daukar nauyin dake shirin hawanshi,hawaye ne dana dade ina farautar su ruwa a jallo,a mamakina sai ga su suna tsiyaya tamkar idaniyar ruwa mai wuyar toshewa,sai lokacin ta fara hasko tsantsar tashin hankalin rasa Abbanta da tayi,sanadin idasa fitar da akayi dashi yasa ni saurin mikewa tare da fara tafiya da sassarfa,yayin da gabobin jikinta ke nuna tsantsar gajiyawa wurin tafiya.Tafiyata baya rasa nasaba da jarumtar dana dauko na saka wa kaina.Dole kanwar naki.Wani irin zullumi tare da karyewar zuci suka dirsan mun nayi faduwar kasko akan kafata ragab haka na fada,lokacin da aka ida fitar da gawar Abbana daga cikin gidanmu,sunkuyar da kai nayi tare da bude busasshen bakina na furta"ya Allah".Tari ne ya turnike Nihla kan kace me? cikin kuka ta furta"yauce rana mafi muni a gare ni,tunda na ga fitar Abbana ta karshe daga gidan mu".Ban kuma sanin in da kaina yake ba saboda tsantsar ciwo da kuncin da zuciyata take ciki,tuni Sikila tace mun salamu alaikum da sauran ciwa ce ciwacen da ba'a rasa ba,sai ranar sakadakar ukku na dawo hayyacina na fara rarrabe tsakanin mutuwa da rayuwa.Na fahimci Mahaifina yamin gatan da ba ko wacce y'a ke samu a wurin mahaifinta ba.Nayi kuka nayi kuka in da Yaya Zafar ne kawai ya kasance mai lalashina,ban kuma sanin gidanmu ya tashi daga gidan farin ciki ba ya koma mana kamar makabarta sai bayan sati daya da kowa ya gana watsewa duk da a lokacin na dawo hayyacina bana jin ciwo sai dai tsananin fargaba da damuwan da suka yiwa ruhina kawanye tare da lullube ni,kewar Abbana da fargabar sabuwar rayuwa wanda take cike da duhu da kuncin rasa mahimman mutanan da nafi so fiye da kaina a rayuwata dan a yanzu kam na ida tabatarwa Irfan ya gama sallama rayuwata gefe. Parlo na fito duk da tsananin raman da nayi hakan be boye tsakanin kyawuna ba,saurin nemawa kaina burki nayi tare da kwalalo dara-daran idanuwana kamar zasu fado kwakwalwata na niyar juye mani sakamakon ganin Irfan da Aunty da nayi zaune akan kujerar parlon mu tana mika masa lemu a kofin tangaram. Murnushi Aunty ta saki tare da cewa"yauwa Nihla sannu da fitowa ,karaso ki gaishe da sabon Abban naki". Dam dam haka zuciyata ta buga kamar fashewar bomb na tattaro kalaman Aunty cikin rashin fahimta nace"wa..Waye Ab..abbana kuma❓"na jefa mata tambaya. Cikin takun kasaita da isa ta iso gareni tare da dafa kafaduna tace"Nihla Irfan shine wanda nike so a yanzu ko nace muke son juna,kuma shine dana gama takaba zamuyi aure insha Allah,kinga kuwa shine sabon Abbanki wanda zai kula dake". Saurin ture hannun Aunty nayi daga jikina,ina mata kallon da ni kaina bansan ma'anarsa ba cikin kyarmar baki nace"Aunty...Ir..Irfan fane...Masoyina...Ko kin ma...manta shine ke zuwa wurin y'arki❓" Shafa gefan fuskata tayi tare da cewa"na sani mana,tunda ba aurensa kike ba ae hakan bai haramta ba". Dafe kaina nayi da karfi tare da nufar hanyar dakina a guje ina dafe da saitin zuciyata dake barazanar tarwatsewa. Aunty kam wurin Irfan ta koma tana fadin"kasan sha'anin yara sai a hankali,amma cikin lokaci komai zaiyi daidai" Dariya yayi tare da fadin "hakane matata" *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 66~70 Nihla kam tana shiga dakinta ta banko kofan da karfi,saman bed ta fada tare da sakin wani irin kuka,,,gaba daya jijiyoyin kanta sun fito rudu-rudu,tashin hankali! tsantsar tsoro da fargaba sune sukayi nasarar tasiri a cikin zuciyarta gaba daya,ji tayi kamar a yanzu ne ta fara son Irfan jin soyayyarsa na kuma bijiro mata,tashi zaune tayi da sauri tana bubbuga kanta da jujuyawa tana karewa dakin kallo,gani takeyi kamar mafarki take yi,ina! komai yake faruwa da ita a zahiri ne,dafe zuciyarta tayi da karfi naji kuma jin gazawan zuciyar nata wurin daukar gaggarumin nauyin dake shirin hawanta,soma karanta duk wata addu'a da tazo bakinta take yi,a hankali hawaye masu dumi suka soma zarya akan kyakyawar fuskarta. Shigowarta gate din gidan kenan,fuskarta fal fara'a ta kalli Irfan dake shirin fita,cike da zolaya tace kaga Nihfan ,halan an zo ganin masoyiyar ne ❓ku da bakwa iya rabuwa da juna ko yaushe ana mak'ale. Yaken dole Irfan ya saki tare da cewa"Miemie baki da dama,hali dai na nan". Dariya tayi tare da cewa"in dai halinku na nan ae muma na mu da soyayyar ke burge mu ba zai tafi ko ina ba".ta kare maganar tana wucewa ciki.Da Sallama ta shiga parlon babu kowa sai Aunty dake zaune tayi daya kan daya tana kurbar lemu a hankali ,ajiye cup din tayi fuska fal fara'a tace"a'a yau Miemie ne a gidan namu❓tun bayan rasuwa rabon ki da gidan nan kenan" Kasa Miemie tayi da kai alamun jin kunya,sosai take jin kunyarta dan tana ganinta kamar mahaifiyar Kamal ce cikin sanyin murya tace"Aunty makaranta ne bata bari,yau ma na dawo da wuri ne shiyasa na samu damar zuwa"sosai suka gaisa kafin ta tashi ta wuce dakin Nihla,tura dakin tayi tare da shiga,kwance ta hangota a bed tayi rub da ciki,tausayinta ne ya

Chapter 4 of 9