kuma kara fadada fara'arta dan wannan shi ne ganin Zafar na biyu da tayi kuma tun ganin farko ya tafi da dukkan tunaninta da wata farin cikin rayuwarta,tun daga ranar take jin babu wanda ya cancanta da ita sai shi"kura masa ido tayi ta kuma kasa janyewa,lokacin daya tayi saurin runtse idonta da matukar karfi sakama kon idanuwan Zafar da suka shiga cikin nata,wani irin suck taji wanda yasa ta kasa ci gaba da kallonsa tayi sakama kon kwarjin daya yi mata.
Karasa shigowa yayi tare da zama akan chair dake fuskantar Kaka cikin natsuwa ya furta"Ga ni!".
Lumshe idanuwa Aisha tayi yayin da so da tsantsar kauna suka soma daukar mata daddadar muryarsa tana mata yawo a kai.
"wannan itace Aysha matar dana zaba maka Zafar,ka ganta dan ita ta riga ta ganka kuma ka fara shirin biki "Kaka ta fada.
Shiru Zafar yayi tare da dago kai ya kalli Kaka yace"ki bamu waje to".
Alhmdllh shine abunda Hajiya kaka ta fada tana kuma cewa"nasan ai dole kaso zabina ,kaine jika mafi soyuwa a gare ni kasan bazan maka zabi marar kyau ba,ku zanta da kyau,Allah yayi maka albarka".Ta kare maganar tana wucewa bedroom dinta.
Murmushi kawai Zafar ya saki,wanda hakan ne yasa Aysha shagala da kallonsa dan ba karamin kyau yayi mata ba.Yana juyowa da kallonsa tayi saurin yin kasa da kai zuciyarta na bugawa.
"a wannan zamanin ban tunanin akwai wadda za'awa zabin miji ko mata haka kawai ya amince,shin ke sanina kika yi ne da kika amince da zabin kaka ta❓ Aysha ba abunda kika rasa bare nace bana sonki,ko a ina babu wanda zai kushe halittarki,sai dai ina mai matukar baki hakuri ,bana da ra'ayin yin wani aure a yanzu".
Saurin dagowa tayi tare da dubansa cikin sarkewar murya tace"ni naga kayi mun,kuma zan iya jiranka ko yaushe ne"Cewar Aysha.
Hannu yasa tare da shafa tulin sumar kansa kafin ya bata ansa da cewa"ki gane bana da ra'ayin son mace biyu danni ina da wacce nake so kuma na riga na zama mallakinta i'm sorry"ya kare maganar tare da mikewa ya yi hanyar fita.
Da kallo tabi bayansa dashi ,sai da ya kurewa ganinta sannan wasu hawaye masu dumi suka samu basarar gangarowa akan fuskarta....
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
81
Da kallo Aysha tabi bayan Zafar harya bacewa ganinta,dukar da kai tayi tare dasa hannu ta soma share zafafan hawayen da suka gama wanke mata fuska,sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dagowa tana kallon Hajiya kaka dake tsaye gabanta ta kureta da ido.
"me yake faruwa❓,ina Zafar din❓,Aysha kina jina fa"cewar Kaka,"Kaka ya tafi"Aysha ta bata ansa tare da mikewa tana kokarin barin wurin.Rike mata hannu kaka tayi tace"ki gaya mun me lalaceccen ya yi maki❓".
Dayan hannunta ta daura akan na Kaka fuska cike da murmushi tace"kaka beyi wani abunda ba daidai ba,ya fada mun yana da wacce yake so,kuma kinga ni bazanyi kokarin raba masoya ba ko Kaka❓".
Saurin janye hannunta Kaka tayi daga rikon da Aysha ta mata"ke dai Allah wadanki,nafa gaya maki halin yaron nan kab,to karya yake yayi haka ne dan ki rabu dashi,ke baki san ciwan shi na gudun mata ba❓wallahi karya yake,bakin hali ne irin nasa,amma kab kinfi ban haushi da bata mun rai wallahi"kaka ta fada.
Murmushi kawai Aysha tayi tare da daukar jakarta ta bar bangaren kaka.Da matukar sauri kaka tabi hanyar harda tuntube ta shiga main part na gidan,da Miemie taci karo janyota tayi tare da cewa"ke ina wannan labcecen banzan ❓".
Dariya Miemie ta kunshe tana kallon Zafar dake niyar ficewa ta bayan Kaka wanda fitowansa daga dakin Ammi kenan.
Carab kaka tayi da belt din Zafar ta rike da karfi "au guduwa zakayi Zafar❓kai duk duniya lamarinka babu albarka a cikinsa❓ko kadan baka da gaskiya "cewar kaka
Kamar safkar mutuwa haka Zafar ya daure fuskarsa babu alamun annuri a tattare dashi hannu biyu ya hada tare da cewa"Kaka ki daina damun kanki dan Allah,badai aure ki ke so nayi ba❓insha Allah ranar satin zan kawo maki wacce nake so,amma dan Allah ki tsayar da wannan rigiman bana so ya koma wani abu na daban".
Shiru kaka tayi kamar mai tunani sai kuma ta saki murmushi tare da dafa kan Zafar tace"kayi alkawari zaka kawo mun❓".
Ajiyar zuciya Zafar yayi tare da sakin yalwataccen kyakyawan murmushin shi mai wuyar ga ni ya janyo kaka jikinshi sosai ya riketa tare da cewa"eh nayi alkawari Nanima!".
Dariya kaka tayi tare da rungumar Zafar tana saka masa albarka kafin ya fita daga gidan,wani irin dadi ne ya kwaranya a zuciyar Ammi tabbas tasan Kaka na matukar son Zafar da duk rigimarta shi kadai ke iya mata a gidan,sai dai ta wani bangaren cike take da matukar tsoro da firgicin ranar da Kaka zata gane gaskiya akan abunda suke boye mata,hannu ta daga tare da cewa"ya Allah ka bamu mafita akan wannan al-amarin". karab idonuwan Ammi suka sarke cikin na Hajiya kaka,tsaki taja tare da cewa"maryam bansan gulma tsayuwar me kike a nan❓ ko baki so aurem Zafar din bane,to ahirdinki wallahi" Kaka ta kare maganar tana fita daga part din,dariya Miemie ta kwashe da shi tare da yin sama da gudu gudun kada Hajiya kaka ta jiyota ta tayar mata da balli.
4 days later
Sanye take cikin riga da siket na material red colour,daurin zara buhari ne a kanta sosai dinkin yayi matukar yi mata kyau duk da kasancewarta marar kiba amma ko ina das ,simple make-up ne a fuskarta sai baza kamshi take ta tako a hankali zuwa cikin tabkeken parlon nasu,kawar da kai tayi saka makon ganin Irfan da Aunty zaune suna sheka dariya kasa-kasa Aunty ke fadin"ai duk wasu takardu na yawancin dukiyar na dauke in gaya maka,sora wanda ba'a rasa ba shima tare za'a raba mana gado,bakin cikina daya takardun dukiyar da uwarta ta mallaka mata duka suna hannun Dr Zafar kuma kasan ansarsu bazai taba yiwuwa ba".
Dariya Irfan ya yi tare da mikawa Aunty ledar hannunsa yace"kinga ga IV na auren mu nan nan da sati ukku masu zuwa,maza tattaro mun takardun na fita dasu daga gidan nan".
Wani irin sanyi,farin ciki,natsuwa gami da annashuwa na jin dadin cikar buri yasa hawayen farin ciki safkowa a fuskar Aunty bakinta ta bude tare da furta"Alhmdllh,ga kuma takardun duka a jakkar nan Baby".Hannu Irfan yasa tare da karbar jikkar a hannunsa.Ganin Nihal na niyar wucewa tasa Aunty cike da dauki tace"Nihal kizo kiga abun farin cikin daya doso Auntynki dan Allah".
Cak Nihal ta tsaya tare da dago kanta dake duke,saurin kawar da hawayen dake kokarin zubo mata tayi ta maye fuskarta da Murmushin data kakalo ta dawo kusa da Aunty tare da cewa"menene wannan ya samu Auntyna❓".
Janyo hannun Nihal Aunty tayi tare da zaunar da ita suna fuskantar juna ta dafa kafadunta "Nihlal yaune ranar farin ciki a gare ni tun bayan rasuwar Mahaifinki,Nihal yaune na fara ganin cikar burina na tun yarinta,Nihal ki kallah katin aurena da Irfan!"
Dam dam haka kirjin Nihal ya bada sauti cak numfashinta ya tsaya na wasu seconds,kamar statue haka Nihal tayi hucking,wani irin ajiyar zuciya ta saki wanda hakan ne yasa ta soma rarrabe yanayin da take ciki,saurin kawar da damuwarta tayi tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo ta kuma soma bude bakinta dake kyarma ,sai da tayi da gaske wurin harhado kalamanta cikim tsananin tsoro da firgici tace"Au..A...Aun...Aunty na ta..ta..taya ki farin...Ciki"shine kawai abunda ta iya furtawa ,bude hannuwa Aunty tayi da niyar Rungumar Nihal itama jikinta ta shiga suka rungume juna,idanuwa Nihal ta lumshe tuni hawayen da take boyewa sun samu damar bayyana a sarari a yanzu sun kai lokacin da bazata iya controlling nasu ba,rokon Allah ta keyi yasa ta farka daga mumunan mafarkin da take yi,sai dai kash ko da ta bude ido hakan ya kuma kara tabbatar mata da cewa a gaske ne ,samu tayi ta janye cikinta daga na Aunty ta mike zata wuce.
"ba zakiyiwa Abban naki murna ba Nihal❓".Kalaman Aunty suka darsu a kunnuwan Nihal,saurin dafe zuciyarta ta yi dake dab da tarwatsewa saboda tsananin tashin hankali cikin sarkewar Murya tace"i..I..Ina taya ka murna,Allah ya..yasa alkhairi,A ko da ya..ysushe zan kasance mai maka fatan al...alkhairi da addu'a"ta kare maganar tana tafiya i zuwa dakinta,key tasawa kofan tare da silalewa kasa ta fadi akan gwaiwowinta tare da sakin wani irin kuka mai kuna da cin rai,Dan kwalin kanta ta cire tare da jefarwa tasa hannu tare da barbaza yalwataccen dogon gashin kanta,kanta ta dafe da karfi tana kuma fashewa da kukan ,da gudu ta mike ta isa gaban hoton Abba da Mummy dake ajiye a dakin,rungumesa tayi a kirji cikin muryar kuka ta furta"yau na cika kuma na tabbata cikakkiyar Marainiya ni Marya,da ace zai yiwu zan iya bada komai nawa ko da na sati daya ne a dawo mun daku duniya,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,yau na tabbata cikin tashin hankali Abbana lallai kamun gata Abbana nayi kewarka,Abba bazan iya daukar wannan ba ko kadan,Abba nima yau na roki mutuwa fiye da rayuwata,idan na zauna nan zuciya zata fashe bazanyi mutuwa mai sauki ba Abba,Abba ka g..ga...gafarce ni...Yau zan bar ..Gidan nan".Da gudu ta nufi wadrope ta janyo hijab da akwati ta dinga jefa kayanta tamkar sabuwar zautacciya,kudi ta zuba a ciki ta rufe ta janyo shi zuwa kofan daki ta bude wani irin jiri da tari ne ya turniketa dafe kirji tayi tare da sulalewa a kofar dakin a sume......
*Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
82
Da matukar sauri Irfan yakai hannunsa da niyar taba Nihla wanda isowarsa wurin kenan,wani irin riko yaji anwa hannunsa tun daga kasa ya fara kallon wanda ya rike masa hannu har i zuwa akan fuskarsa ,fuska daure babu alamun murmushi Zafar ya gyada wa Irfan kai kafin ya jefar da hannun nasa,dukawa ya yi akan gwaiwowin sa ya tallafo Nihla yana girgizata ganin ko kadan bata motsiya yasa ya dauketa zuwa mota,da matukar gudu ya figi motar zuwa asibitin shi,kai tsaye emergency ya tafi da ita,ja da baya yayi tare da dafe kansa da karfi wanda yake jin kamar zai tarwatse masa,Dr Aminu ne ya karasa gareta ya fara kokarin ceto ranta.Zafar kam da tsananin firgici ya gama kama shi ga zufa da taketa keto masa ta ko ina,saurin fitowa ya yi daga dakin,kamar an saukar masa da mutuwa haka ya zaro dara-daran idanuwansa yana jefawa Aunty da Irfan mugun kallo kamar idonsa zai fado.Saurin ja da baya Aunty tayi tana mayar da nunfashi saboda tsoron daya gama bayyana a tattare da ita,hannu ya daga tare da nu na su cikin tsananin hassala yace"we don't need u here,get lost,billah Irfan idan na bude idona na ganka a nan tabbas za'a baka gado".
Kafin Irfan ya yi wani yunkuri tuni Aunty yaja hannunsa da karfi sunyi baya,cijewa yake yi a tsawace Aunty tace"kayi hauka ne Irfan❓,kai baka san waye Zafar ba❓na tabbata tun da akan Nihla ne bazaiyi tunani so biyu ba wajen illataka".Dafe kansa yayi yana jin wani iri saurin kawar da damuwar ya yi tare da kallon Aunty tare da sakin murmushi yace"muje Baby,tunda kina tare da ni meyasa zan damu da abunda ya damu da Nihla".Tafiya suka yi suka bar asibitin.
Zama akan chair dake bakin emergency din Zafar ya yi yana jin zuciyarsa kamar zata fasa kirjinsa ya fito,dukar da kai ya yi tare da daura hannuwansa akai yana cakuda yalwataccen gashin kansa.Fitowar Dr Aminu yasa ya yi saurin dago ido yana kallonsa yana so ya yi magana amma sam ya kasa furta komai,gane abunda yake nu fi yasa Dr Aminu dafa kafadarsa tare da cewa"Relax Dr,Alhmdllh ta dawo a hayyacinta,amma kasancewar firgicin da take ciki yasa kwalwarta na bukatar hutu yasa na mata alluran bacci,later on sai ka dubata akan ciwonta daya tashi".
Rinannun idanuwansa da suka gama rinewa ya dago tare da kallon Dr Aminu Murmushi kawai ya masa a matsayin godiya tare da gyada kai sannan ya mike tare da shiga dakin da Nihla take ciki.
Kamar wanda be son taka kasa haka yake tafiya harya karasa a kusa da gadon da take,hannunsa ya daura a kanta dake baje babu dankwali janye mata gashin kanta daya rufe mata fuska ya yi,kallonta ya soma yi kamar wacce xata bace masa,a hankali ya soma magana "Mamana bazan taba bari wani kuncin ya sake shigarki ba,kin sha wahala a rayuwa,kinga jarabawa kala-kala ko ince kina cikin gani Nihla,tabbas zaki samu y'ancin da ko wanne Dan adam ya kamata ya samu,zaki samu y'ancin karbar abunda yake naki ne amma ake ta faman boye maki an kasa fito da hakan saboda tsoro,insha Allah wannan alkawarina ne gareki,kisa a ranki wahalarki tazo karshe yanzu babu abunda ya rage gareki face ki karbi kaddararki da hannu bibbiyu ki karbi ki kuma yarda da canjin da Allah ya yi maki Nihla".Kallonta yake ci gaba da yi kallo daya zaka mata kasan baccin wahala take kuma ko kadan bata cikin natsuwa,hannu yasa ya goge mata hawayen dake bin gefan idanuwanta suna zubowa kafin yabar dakin.Nurses ya saka su kula da Nihla zaije gida ya dawo.
Tunda ya shigo gida bai ansa ko gaisuwar da masu aikin gidan suke masa ba ,ya wuce ciki da ido Ramadan ya bisa da kallo kafin yace"Yaya lafiya kuwa❓".Dafa kafadar Ramadan ya yi tare da gyada kai ya karasa shiga tsakiyar parlon be wani yi tunani sau biyu ba yace"Ammi ki shirya Nihla ba lafiya taba asibiti".Zumbur Miemie ta mike har idanuwanta sun kawo ruwa tace"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Yaya meya sameta❓dan Allah ka kaini in ganta".
"babu wanda zai fita a gidan nan bare yaje ganin wannan yarinyar da na ciga na cireta daga cikin wani da zai iya rabarmu".Cewar Kaka dake shigowa Parlon fuska a matukar daure.
Ras ras haka plate din dake hannun Ammi ya fadi ya tarwatse hawaye ne suka kawo idonta da sauri ta iso gaban Kaka tare da hada hannuwanta biyu tare da cewa"Kaka dan Allah kada kice haka,Kaka in kinso zaki iya mana komai amma kada ki hana mu zuwa duba abunda yake dawainiya a kanmu,na rokeki ko sau daya ki sassauta zuciyarki akan Nihka kaka ,Nihla bata da laifi in ma Mahaifinta yayi laifi kaka ba itace mai laifi ba".
"ya ishe ki haka Maryam"kaka ta fada a tsawace,wanda ya haifarwa wanda ke wurin kullewar ciki.
Da sauri Daddy ya iso gabata tare da cewa"Hajiya dan Allah".
"ni yau har ta kai kuna fada mun abunda ya kamata nayi❓Maryam ke da kanki❓a yaushi kika dauki alhakin kula da waccan yarinyar ba ni da labari❓yarinyar da cuta duk ta gama kanainayeta❓"Kaka ta kare maganar tana kallon Ammi.
Runtse ido da karfi Zafar ya yi yana kuma jin zafin kalaman Kaka akan Nihla,juyowa ya yi tare da cewa"har ke xakije ganin Nihla ba iya y'an gida kadai ba".
Cakumar kwalar Zafar tayi tare da girgiza sa da karfi tace"kayi hauka ne❓ko kuma ka fara shan wani abu ban sani ba❓to ka bude idonka da kyau bazan taba taka kafata ba da sunan naje ganin jinin Umar har abada"
"shin da sauran kakannin mu ne zasu goyi bayan hakan daga gare ki❓,idan da Kaka Aysha kika barwa Abba shin zaki tsammaci hakan daga gareta❓haka ne rikon amana kaka❓Abba Umar amanarki ce ya tashi beda uwa bare uba baida wasu dangi da suka wuc naki sai lokaci daya ki fitad dashi❓kuma harki mayar da hakan akan y'ar daya haifa ❓yau dai ko sau daya Kaka ki bude idonki ki kalli gaskiya,ina so ki biyoni na nuna maki wani abu idan yaso daga baya zaki iya yanke hukunci da kanki komai kike so shi zaki yi".
Hannu yasa tare da cire hannun Kaka daga rikon data masa,kallonta yayi ganin akwai mayafi a jikinta dama kuma bata taba zama ko a cikin parlo ne yasa yaja hannunta ya fara tafiya da ita,bata musa ba ta soma binsa,ganin hakan yasa duka yan gida rufa masu baya mota biyu sukayi,Zafar kam bai tsaya ko ina ba sai cikin harabar asibiti.Kashe motan ya yi ya zagayo ya budewa kaka mota ya taimaka mata ta fito nan ma still hannunta ya kama har zuwa cikin emergency tsakiyar dakin ya tsaya cak hakan ce ta faru da duka yan gidan da suka biyo su,hannu ya daga tare da nuna Nihla,tare da cewa"Kaka ki kallah".Kamar bata son juyawa hakan ta juya tare da kallon in da Nihla ke kwance duk na'u'rori a jikinta,cikin tsanannin raunin murya ya fara magana"shin kaka akan waccan kike fada❓jikarki da take gwagwarmaya da rayuwarta❓yarinyar da ko sau daya take fatan ta rayu,kaka Nihla bata taba karaya ba duk da yarda ta taso cikin maraici wanda kuma yake bango abun jingina a gareta shima Kaka ya kauce,Nihla bata da kowa sai mu,wanda take so kuma take burin kasancewa da shi ya cuceta a yau nake fada maki ya fiddo katin aurensa tare da Aunty wacce ta taka matsayin uwa a gareta".Ba kaka kadai ba kowa na dakin ya firgita da shiga tsananin tashin hankali sabanin Miemie dako a jikinta dan tasa a ranta Aunty zata iya aikata fiye da haka ma.
"shin yanzu wannan bata cancanci tausayawarki da yafiyarki ba❓,kinsan Nihla dawainiyata ce a yau nake shirin kara gaya maki wani dawainiyar data rataya a kaina,ba kina so kiga matar da zan aura ba❓".
Gyada kai kaka tayi dan bata jin zata iya magana a wannan lokacin ita kanta ta rasa gane meke damunta❓ko wanne irin yanayi take ciki,abunda ta sa ni kawai shine dai kunnuwanta na sauraran kalaman Zafar.
Rike hannuwanta biyu ya yi sosai a cikin nashi,kafin yace"ina mai fada maki cewa Nihla Umar Matata ce ta sunnah da aka aura mun yarda musulunci ya tana da na biya sadakinta da kuma shaidu sun tabbatar Nihla ta zama Matata ta sunnah"
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*MARUBUCIYAR*
*SANADIN GATA*
*YAUDARA KO BUTULCI*
*DALILIN SO*
*SO DAYA*
*ASALINA*
*ADDININA*
*SHI NE AJALINA*
*RUHIN FANSA 1&3*
*HANAN* paid book
*ABU BILAL* Paid book
*FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻♀️
83
Tsurawa Zafar idanuwa Kaka ta yi ko kibtawa bata yi jin jiri na neman daukanta ta tafi tagal-tagal zata fadi yasa Ammi saurin riketa,hannu Kaka tasa tare da rike Ammi ta kuma sauke wata nannauyar ajiyar zuciya,kwatakwata ta kasa yarda ace yau jinin Umar shi ne matar jikanta,jika mafi soyuwa aduk jikokinta,ko a mafarki bata taba tunanin hakan zai iya faruwa ba,shin ashe duk yarda ta yi hakan bazai iya nesanta yaran ba,dafa kai tayi tana kuma kawai da kai jin Zafar ya kuma rike hannuwanta tare da cewa"shin Kaka zaki iya gudun Nihla❓ Zaki iya rabani da abunda na rayu da soyayyarsa❓Kaka na rayune saboda Nihla,na canza duk tsarin rayuwata saboda Rayuwarta,ina mata son da bana yiwa kaina".
Ja da baya Kaka tayi tare da zama akan kujeran roban dake kusa da ita cikin dushewan murya tace"ka gaya mun lokacin da ka auri Maryam".
Akan gwaiwowinsa ya tsuguna ya daura kansa akan cinyar Kaka yana jin zuciyarsa na suya yace"na Auri Nihla ne a ranar da Abba ya rasu,kuma akan yarda addinin mu ya tanada,Daddy ,Ramadan da Dr Aminu su shaida ne,na biya sadakin Nihla an kuma daura mun aurenta,hakan ya faru ne ta dalilin Amanar da Abba ya kuma daura mun mai girma ta zamowa Garkuwan Nihla ,shi ne suka yanke hukunci akan cewa Aura mun ita shi ne kadai zai ba ni tabbacin kula da ita ta ko wanne fanni,Sannan kaka ko kadan Abba bashi da hannu akan zargin da kike masa,idan lokaci ya yi zan sanar da ke hakan da duk wasu sheduna idan kina bukata".
Hawaye suka zubo akan fuskar Kaka kasa furta komai ta yi.
"Hajiya Dan Allah ki bar zubar da hawayen ki ,nayi maki alkawari idan kika nuna bakya so zan saka Zafar ya sawwakewa Nihla tunda bata san da auren a kanta ba,amma ina rokonki da kada ki hana mun rikonta a matsayina na wanda take kallo uba gareta"Daddy ya fada.
Dafa kan Zafar Kaka ta yi tare da cewa"wacece ni da zanja da hukuncin Allah Zafar❓duk iya kokarina na nisanta ku amma sam ba haka Allah ya so ba,gashi ya yi ikonsa a kanku wanda ba ni da yarda zanyi,ni bazan dauki alhakin kowa ba,ba kuma zan kashe aure ba rabo ya kashe ni,itama wani sauyi ne Allah ya yi mata na wancan algunguman da ke son cutar da ita,duk da ba ita na so ka aura ba amma kuma ita Allah yaso maka,Allah ya bata lafiya,ku mayar da ni gida ina so in huta".
Sanyi,dadi,farin ciki mai cakude da sanyayyar annashuwa ce fa dirarawa duk wani Dan Adam dake cikin dakin asibitin musamman ma Zafar sai dai sam beji mamakin abunba tabbas yasan Kaka kamar kwakwa take wajenta akwai matukar tauri sai dai cikinta ta fi komai laushi da kuma tausayi,hamdala ya yi ga sarki Allah kafin ya furta"Alhmdllh,ni da Kaka fada ya kare kuma".
Dungure masa kai tayi tace"da'allah labcecen banza ni ba ni wuri na wuc....."kasa karasa maganan tayi jin Muryar Nihla na kiran "Yaya...ya...ya"idanuwanta a rufe gq hawaye na gangarowa da ga cikinsu,saurin mikewa Zafar ya yi ya karasa kusa da bed din ya rike hannuwanta yana cewa"Nihla,ga Yayanki a kusa da ke,me kike so❓"kamar wacce ta yi mumunan mafarki firgigit haka ta mike ta rungume Zafar da iya karfinta kamar za'a kwace mata shi a hankali sautin kukanta ke tashi yana zagaye ko wacce kusurwa da lungu na dakin,ta yananayin kukan nata kadai ya isa ka gane kuka ne mai cike da tarin kunci,takaici da kuma tsananin kewa.
Runtse ido kaka ta yi tana kuma jin wani irin yanayi yana shigarta,lokaci daya jikinta ya dauka tsam kamar wacce aka soka da allura,hanyar waje ta yi hakan yasa Ramadan da Ammi suka bi bayanta don mayar da ita gida.
Miemie kam a guje ta iso wurin gadon ta hada Zafar da Nihla ta rungume tare da fashewa da kuka.
Jin muryar Miemie na yawo a kanta yasa ta dago idanuwanta da suka gama rinewa tare da yi mata nauyi ta zuba su a cikin na Miemie"ki..ki daina..Ku..kuka"ta fada.
Murmushi ne ya subucewa Miemie taja Dogon hancin Nihla tana cewa"kukan farin ciki nake in law".
Zumburar baki Nihla ta yi tare da murgudawa Miemie baki ta juyar da kai,ba Miemie ba hatta Zafar sai da ya murmusa sosai hakan ya yi mata kyau duk da tana cikim jinya.
Karasowa jikin bed din Daddy ya yi yace"y'ata❓sannu kinji,ina yake maki ciwo❓".
Jin muryar Daddy yasa ta tashi da sauri tace"Daddy".
Da na'am ya ansa mata yana kara matsowa kusa da ita.
Ganin Daddy a kusa da ita yasa take ganin kamar Abbanta ne a kusa da ita tace"Abba,kaina kafana ,hannu Abba da ko ina ciwo yake mun".
"Allah ya baki lafiya,sannu insha Allah zai daina kinji,kiyi hakuri haka Allah ya kaddara maki,sannu"Daddy ya fada.
Dr Aminu ne ya shigo bayan sun gaisa da Daddy ne yace"Dr muje a iba jinin".
Kai Zafar ya gyada tare da gyarawa Nihla kwanciyarta kamar jira take ta lumshe ido sai bacci.
Daddy ne yace"jinin za'a kuma saka mata❓"
Da eh Zafar ya ansa "kamar ko yaushe jinin nata ya kone ne ,tana bukatar kari".
"Allah ya baka lada Zafar,Allah shine kawai xai biyaka akan kokarin rike amanar da ka ke yi,Allah ya dafa maku ya kuma biya maku bukatunku na alkhairi".
Da ameen ameen suka ansa sannan Daddy ya tasa keyar Miemie gaba suka wuce gida,dan yasan idan tana nan ba zata taba bari Nihla ta huta ba.
A harabar gidan su Daddy suka iske Kamal yana jiran Miemie a mutunce Kamal ya gaishe da Daddy sannan suka zauna shi da Miemie kallonta ya yi tare da cewa"yan matana wannan fara'a haka❓duk ta mecece❓ke da kika dawo daga asibiti nasa xan ganki fal fa damuwa shiyasa nazo rarrashi tunda tabin ranmu ba lafiya".
Kallonta ta maido gareshi tace"ya akai kasan muna asibiti❓".
"Aunty ce ta gayamun Nihla ba lafiya"ya bata ansa.
Wani irin hade fuska Miemie tayi tare da jan dogon tsaki tace"matsiyaciya kenan,wallahi hakki baxai taba barin Nafisa ta zauna lafiya ba da ita da duk wani mai goyon bayanta cikin tarwatsewar rayuwar yar uwata,sai dai kuma wani hanin ga Allah baiwa ne,cin amanar da zaluncin da tayi hakan be hana Allah zabawa Nihla zabi na gari