bazan gaji da gode maki ba dan kinyimun abunda har abada bazan taɓa mantawa da ke ba,na gode sosai".
Gyara rungumar datayiwa Nihla tayi cike da nuna zallar soyayya tace"Abbanmu ai ɗa na kowa ne,ni baka ganin Allah bai bani ba?koda ma ya bani meye ribata idan na ƙuntatawa Nihla?ae bansan me riƙeni ba a duniya,fatana dai Allah ya bani cikar burina akan Nihla".
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 16~20
Kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka Zafar ya gitta Miemie da Ramadan dake tsaye a ƙofar ɗaki,da kallo suka bishi Miemie taja hannun Ramadan sukayi ciki,dafe kanta tayi cike da ɓacin rai tace"Yaya Ramadan kana gani?wacce irin sabuwar rigimar ce wannan tsohuwar ke niyan janyo mana?".
Zama gefen bed Ramadan yayi yana sauke numfashi yace"bata so a xauna lafiya ne,and i'm very sure Yaya Zafar baxai taɓawa Hajiya biyayyah akan hakan ba"
Hawayen baƙin ciki Miemie ta share tare da cewa "i wish ace Yaya Zafar zaiyi aure amma bana so a tursasa shi akan hakan kasan halinsa".
Miƙewa Ramadan yayi tare da dafa kafaɗun Miemie yace"kada ki damu da yardar Allah komai zaizo cikin sauki,Allah zai kawo mana mafita,Allah maji roƙon bayinsa ne,a ko wanne yanayi nasan yana jin addu'armu kuma ina da yaƙinin ya ansa mana danshi a koda yaushe mai ƙarɓawa bayinsa roƙo ne".
Murmushi ta saki tare da goge fuskarta tana kuma ƙara jin daɗin kasance tare da Ramadan.
Zagaye ɗakin takeyi fuskarta fal damuwa ta rasa meke mata daɗi balle kuma tasan ta ina zata ɓullowa wannan al-amarin dake niyar doso ta,tabbas tasan ba ƙaramin rigima ce tafeba tunda Hajiya Kaka ta kawo wacce take so amma Zafar yaƙi amincewa,ita kanta tasan babu ta hanyar da Muhammad zai amince da wannan shigar danshi kab rayuwarsa bashi buƙatar wani ya masa kutse a cikin rayuwa.tana kuma gudun wahalar da kuma kuncin rayuwar data zauna hakan ya fuskanci yaranta musamman ma Zafar.hannu ta ɗaga sama tare da cewa"ya Allah ina roƙonka ka kare mun yarana ,ka kuma basu ikon jure duk wani abunda zai doso su,yh Allah na roƙeka ka dawwamar da farin ciki a cikin rayuwarsu Allah ka tsaremun Zafar".ta ƙare maganar muryarta a raunane kamar wacce take dab da zakin kuka.
A hankali ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga kamar marar lakka haka yake taka tausassan capet ɗin daya mamaye tanƙameman parlon nasa,ɗakin gyare yake tsab sai fitar da masifar ƙamshi yake kamar ɗakin mace komai na ɗakin blue and white ne sosai ɗakin ya tsaru ga ɗaukar hankalo,kai tsaye kan sofa ya faɗa tare da shafa tulin sumar kansa yana kuma furta"hasbunallahu wani'imal wakeel ya Allah".shine abunda Zafar yake maimaitawa tare da runtse dara-daran idanuwansa da ƙarfi wanda harsun fara canza launi saboda tsananin ɓacin rai dake tattare dashi,zamewa yayi ya kwanta yana kuma sauraron bugun zuciyarsa wacce take matuƙar bugawa da ƙarfi,ji yakeyi kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito ga wani irin zafin da take masa.
Books ɗin dake gabanta take dubawa da alama tayi nisa cikin zurfin karatunta har Aunty tazo ta gitta bata ganta ba,murmushin nasara Aunty tayi tare da ficewa cikin filin gidan kai tsaye ta nufi parking lot,tafiya takeyi tana rawa da jiki ko ina na jikinta yana ansawa sanye take da red atamfa mai zanen yellow da black sosai riga da siket ɗin suka mata kyau gashi sun matuƙar kamata sai fitar da ƙamshi takeyi ko mayafi babu a jikinta.da fara'a ta ƙarasa wurin motonta tare dasa hannu ta buɗe marfin Driver seat.da kallo yabi Aunty shima fuskarsa ɗauke da murmushi ya ziro ƙafafunsa ya fito tare da cewa"barka da dare Aunty ga aro na maido".
Murmushi tayi tare dayin far da ido tace"call me NAFISA "tasa hannu ta ƙarɓa key ɗin da yake miƙo mata.
Cike da mamaki ya kalleta tana ta wani rawa da jiki basarwa yayi yace"Aunty ina Nihla".
Lokaci ɗaya farin cikin dake fuskarta ya ɗauke juyawa tayi kamar zata tafi sai kuma ta tsaya tare da cewa"IRFAN meka gani a jikin wacce siririyar yarinyar daka maƙale mata?hasalima baka da kuɗin kula da gurguwar rayuwarta me zakayi da Sikila ga tarin in'i'na cike da baki,Nihla baxata iya ɗaukar buƙatunka na yau da kullun ba IRFAN ita kanta neman taimako takeyi a duk lokacin da cutarta ta rinca ɓe mata,IRFAN kayi tunani a shekarunka na yanxu shin ƙuɗi kake da burin nema ko Soyayyah?kayi tunani gobe ina jiran ansarka".ta ƙare maganar tana ajiye masa bandir na dubu ɗaiɗaya guda biyu ta wuce abunta.
Da kallo Irfan ya bita kamar mai son koyon magana haka ya soma buɗe baki amma harshensa ya masa nauyi ya kasa furta komai face tsare bayan Aunty da ido kamar idanuwansa zasu faɗo ,sai da yaga shiganta ciki sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana bin kuɗin data ajiye ɓasa da kallo.yakai kusan 5mnt yana saƙawa da kwancewa kafin ya ɗauki kuɗin yabar gidan.
Jin motsi a bayanta yasa ta juya da ido tabi Aunty da kallo harta ƙaraso gabanta murmushi Nihla ta saki ganin Aunty na binta da murmushi tace"Aunty da..da...daga ina?".
Zama tayi tare da janyo Nihla a jikinta,tasa hannu ta soma naɗewa Nihla tattausan dogon gashin kanta dake baje har tsakiyar bayanta tace"na leƙa na karɓi key ne,Nihla ki daina xama ba hula bare kinga yanzu dare ya soma kinji ko?".
kai Nihla ta ɗaga ba tare da tace komai ba,kallonta ta mayar ga agogon dake liƙe a bangon ɗakin 8:59pm ta gani kasa ɗauke idonta tayi tana nunanin shin ina Irfan?yau kuma meya hanasa zuwa kuma be kirata ba.
Hannu Aunty ta tafa a daidai saitin fuskar Nihla tace"kina tunanin IRFAN ko?".
Saurin yin ƙasa tayi da kanta sannan tace"tunda ɗa...ɗazu be ki..ki..kira ba kuma bexo ba".
Matsowa Aunty tayi sosai kusa da NIHLA tace"kada ki damu ,may be wani abunne ya tsareshi,kinsan yarda Irfan ke sanki ya kuma damu dake nasan ba ƙaramin abu bane zai tare maki shi harya hanasa zuwa gareki".
Murmushi Nihla ta saki kafin ta miƙe ta kwashi books ɗinta ta wuce sama zuwa ɗakinta.harta soma tafiya Aunty tace"ina wayanki?".
Juyowa Nihla tayi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta wuce dining area tare da dakko wayan akan table ta miƙawa Aunty.
Karɓa tayi ta fake kamar zata tura wani ta shiga contact JININI JIKINA shine sunan da Nihla tayi saving a number IRFAN ,cikin hikima ta kwashe number kafin ta bawa Nihla wayan ta mata sai da safe.
Nihla kama ƙarban wayan tayi ta wuce abunta.
Dariya sosai Aunty ta saki tana kallon number IRFAN tace"kaine duk wata hanyar kuma bango abun jinginata Irfan,ma damar ka shigo hannuna to ko wanne aiki zai wakana da nasara,kiyi haƙuri Nihla baxan iya bar maki Irfan ba gani ɗaya zuciyata ta kamu da matsanancin son shi na fiki buƙatarshi shiyasa bazanyi jinkiri ko jin kunya wajen FARAUTAR FARIN CIKINA ba Nihla".
IRFAN kam tunda ya fita daga gidansu Nihla sam ya kasa gane in da ya dosa tafiya kawai yakeyi yana kuma haɗa step kamar iska zata ɗaukesa ta jefar haka yakeyi babu abunda ke masa yaso sai maganganun Aunty sam ya kasa gane ta yaya zai iya ɗaukar wannan al-amarin,lokacin daya shiga gida yayi sa'a mahaifiyarsa harta kwanta dan haka ya wuce ɗakinshi shirin bacci yayi kafin yazo ya kwanta yana kallon silin saurin miƙewa yayi yana faɗin"zanyi tsaɓi tsakanin soyayyah da kuɗi?,tabbas ina buƙatar kuɗi domin nima rayuwata tayi kyau na kuma taimaki kaina,sai dai kuma itama NIHLA wata ɓangarene ta labarin rayuwata soyayyah ta tsawan shekara 6 ko kuma tulin dukiya?".wani murmushi ya saki har jerarrun fararen haƙoransa suka bayyah lafin ya juya ya kwanta zuciyarsa fal farin ciki.dandanan bacci mai daɗin gaske yayi awan gaba dashi.
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
JORDERH CE
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 21~25
Wani irin sukuku haka Nihla ta shiga Ɗaki a bedside drower ta daura book's ɗin data shigo dasu,ji takeyi gaba ɗaya jikinta babu ɗaɗi ko ina ciwo yake mata a hankali ta ɓalla drugs ɗinta ta sha sannan ta ɗauro alwala tayi shirin bacci ta kwanta idanuwanta na kallon sama ta lula duniyar tunani,a hankali wasu zafafan hawaye suka soma gangara ta gefan fuskarta,waya ta ɗakko ta dannawa number Irfan kira amma a kashe taji.wani irin mumunan faɗuwa gabanta yayi hakan yayi daidai da wani irin sarawa da kanta yayi take taji wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta ta soma kyarma da rawan sanyi...
Next day
Da ƙyar Nihla ta soma buɗe lumsassun idanuwanta wanda suka sauya kala saboda tsananin azabar ciwon da tasha da dare,da ƙyar ta iya taka ƙafanta ta shiga toilet wanka tayi tare da ɗauro alwala kafin tayi sallan asuba ,tun lokacin ta soma kiran numbern Irfan amma still har time ɗin a kashe ji tayi wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirjinta take ta fashe da wani matsanancin kuka mai cin rai,ji takeyi a ranta kamar tayi shekara bataji muryar Irfan ba,fatan ta dai ya kasance yana lafiya da ƙyar ta rarrafa ta koma akan bed ta faɗa rubda ciki tana jin ƙasusuwanta kamar zasu karye ko ana buga mata gatari a duka sassan jikinta.
Sai 7:30am Aunty ta fito daga bedroom ɗinta sanye da tattausan jan dogon riga na less rigan tayi matuƙar ƙarban jikinta ga ɗaurin zara buhari ta murza a kanta sai wani sanyayyan ƙamshi ke tashi a jikinta,riƙe take da bag ɗin Abba a hannunta shi kuma yana bayanta cikin shiga ta kamala da alama shirin fita aeki yayi,kai tsaye dining area suka wuce fuska ɗauke da murmuahi taja masa kujera ya zauna tare da cewa"sannu da ƙoƙari Nafisa Allah yayi maki albarka"." Ameen ameen Abbanmu,bara na duba naga ko Nihla ta shirya".gyaɗa kai Abba yayi yana kuma ƙarajin ƙaunar Aunty a ranshi yace"ba damuwa".juyawa tayi kai tsaye ta wuce part ɗin Nihla,tura ƙofan ɗakin tayi ta shiga wani sanyayyan ƙamshi ya bigi hancinta ɗakin na gyare kamar ko yaushe kallonta takai ga ɗan ƙaramin pic ɗin Irfan dake ajiye akan ƙaramin fridge ɗin dake ɗakin da kuma tabkeken pic ɗin mahaifiyar Nihla da Abbanta,wani ƙululun takaici yayiwa Aunty tsaye a rai,ji tayi kamar ta kurma ihu dan ganin pic ɗin Umman Nihla,kallonta ta mayar ga bed ɗin da Nihla ke naɗe cikin bed tana faman juyi da murƙusoso.murmushi ta saki cikin ranta tana cewa indai damuwa kika saka a ranki lallai yanzu wannan shegen ciwan sikilan nayi ya fara tashi.da takun sassarfa ta ƙarasa akan bed ɗin tana kiran "Nihla ,Nihla subhanallah meke damunki?baki da lafiya ne?"ta ƙare maganan tana yaye duvet ɗin dake lulluɓe a jikinta tare da kai hannunta akan wuyanta saurin janyewa tayi saboda jin wani irin zafi kamar garwashi ga hawaye nabin kefan fuskarta da ƙyar ta iya buɗe rinannun idanuwanta tana nishi a hankali tace"Aunty ,Aunty Ƙafana zai cire,dan Allah ki ciremun wannan ciwon Aunty bayana kaina hannuna duka ko ina ciwo yake mun Auntyna".saurin janyo Nihla Aunty tayi a jikinta tana mata sannu a rikice tace"kinsha magungunanki kuwa Nihla?"
Cikin ciwan azaba ta gyaɗa kanta tana kuma yin goho dajin kamar bayanta zai cire gaba ɗaya.
"Abba,Abba,Abba Umar"shine sunan da Aunty ke ƙwallah kira iya ƙarfinta kamar a gaske,rungume Nihla tayi a jikinta sosai wanda a lokacin idanuwanta ke kakkafewa.
Kamar daga sama haka Abba yaji muryar Aunty na ƙwala masa kira a rikice,da sauri ya miƙe yayin da duk takun da zaiyi kuma zuciyarsa ke bugawa dib dib dib da sassarfa ya shiga ɗakin Nihla,ganin Aunty rungume da Nihla kuma tana kuka yasa yayi saurin isa a gadon jikinsa har kyarma yake yasa Hannu ya janyo Nihla jikinsa wanda a lokacin jikinta komai ya gama sakewa alaman ta suma,da sauri ya rungumota kamar ya ɗauki baby ya fito da sauri a rikice yake jiran Bala Driver ,da gudu Bala Driver ya iso gaban Abba ganin Abba rungume da Nihla yasa ya nufi mota da gudu ya buɗe masa baya ya shigar da ita,key ɗin ya fizga a hannusa ya tashi motan da kansa tun kafin ya ƙarasa gate ya soma sakin horn a rule mai gadin ya buɗe masa gate ya fice da wani irin masifaffan gudu yanayi yana juyawa baya yana kuma suban Nihla dake kwance tamkar gawa.
Tsaye Aunty tayi tsakiyan parlo tare da goge hawayen dake zubo mata tace"Allah dai ya baki ikon cire tunanin yaron nan a ranki dan bazan iya haƙurin bar maki farin cikina ba,ina da yaƙinin na fiki san IRFAN,idan kam baki sakawa ranki haƙuri ba tabbas kin riƙa tashin ciwanki kenan"ɗakinta ta nufa ta ɗauko key da mayafinta ta fice tare da bin bayan Abba itama ta ɗauki hanyar *ZAFAR SPECIAL HOSPITAL KANO*.
Bangaren Abba kuwa ikon Allah ne kawai ya kaishi asibitin yana isa ko daidaita parking beyi ba ya fito tare da buɗe bayan ya rungumo Nihla tare da nifo cikin asibitin da ita.Nurses ne biyu suka zo da gudu tare da ɗaura Nihla a bed ɗin mararsa lafiya suka turata zuwa cikin emergency Abba na biye dasu sai da sukaje daidai kofan shiga sannan daya daga cikin nurses ɗin ta tareshi tare da cewa"ƴallaɓai kayi hakuri insha Allah zata samu lafiya ka jiramu".tsaye Abba ya tsaya yana furta kalmar"hasbunallahu wani'imal wakeel,yh Allah ka bawa Maryamata lafiya,Yh Allah yarda ka jarabceni da rashin mahaifiyar Nihla Maryam na roƙeƙa a yanzu ka rayamun ƴata maryam kada ka jarabceni da rashinta a yanzu"ya ƙare maganarsa cike da rauni.
Da ɗan sassarfa yake taku cikin ƙasaita da zallar izza sanye yake cikin ash suit sai inner lite blue,yayinda rufaffun tsadaddun takalmansa suka kasance blue hannunsa na hagu sanye yake da tsadaddiyar agogo ta kamfanin gucci,idanuwansa kam suna sanye da siririn farin glasses sai fitar da sihirtaccen ƙamshi yakeyi yau ta kasance ranar Talata kuma rana ɗaya ɗaga cikin ranakun da yake zuwa duba mararsa lafiya a asibitin nashi ,DR ZAFAR shine kuma likitan dake duba Nihla duk lokacin da ciwanta ya tashi idan kaga wani ya dubata to sai wanda ya aminta da aikinsa idan bashi garin kenan sannan hakan take kasancewa.kai tsaye ƙofar emergency ɗin ya nufa ganin Abba yasa ya isa wurin da sauri tare da cewa"Abba kada ka damu kanka insha Allah zata dawo daidai".
Gyaɗa kai kawai Abba ya iyayi tare da ɗaura hannunsa akan tulin sumar gashin Zafar murya bata fita sosai yace"Allah yayi maka albarka Muh'd".
Da ameen Zafar ya ansa kafin ya shiga ciki dan duba Nihla.yakai tsawon minti 20 kafin ya samu damar Nihla ta dawo cikin hayyacinta allurai yayi mata tare da ɗaura mata drip ya kuma saka mata allurar bacci,nannauyar ajiyar xuciya ya sauke yana kuma jin tausayin Nihla na kamasa yana kuma ƙara mamaye dukkan wani jini,jijiya da ɓargonsa umarni ya bada a mayar da ita ɗakin hutu sannan ya fito shima,hakan yayi daidai da isowar Aunty tana tambayan Abba ya jikin Nihlan,kafe Zafar tayi da mayun idanuwanta wani irin mumunan kallo ya jefa mata wanda yasa hantar cikinta juyawa ta kuma ɗauke fuska da sauri, Zafar kam gaban Abba ya tako tare da duƙawa gabansa yace"Alhmdllh Abbana yanzu tana cikin koshin lafiya tana ɗakin hutu".
Hannu Abba ya ɗaga yana godewa Allah daya bashi lafiyar ƴarsa kafin ya ɗaura da godewa Zafar.murmushi yaɗan saki tare da cewa"Abbana ka daina godemun yiwa kaine itama ae kamar ɗaya take da Miemie a wurina".
"DR mun gode ƙwarai,Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci ya kuma ƙara ɗaukaka".
Wata irin juyowa Zafar yayi yana taune lips ɗinsa kamar zai huda iska mai zafi ya fesar kafin ya tashi yabar wajen.da wani irin mayataccen kallo Aunty tabi Zafar tare da haɗiye yawu muƙuttt kamar a yau ta fara ganinsa kullun idan zata gansa da irin kallon da take binsa dashi kenan.
Miƙewa Abba yayi tare da cewa"Hajiya Nafisa muje mu ganta".
Firgigit Aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana kallon Abba tare da sakin murmushi kafin tabi bayanshi suka shiga ɗakin da Nihla take,drugs Abba ya gani duka an siya kallon nurse ɗin dake ɗakin yayi yace"Muhammad bai gajiya shine ya siya maganin ko?"
Fuskarta ɗauke da fara'a tace "eh ƴallabai".
Sosai Abba ke jinjina karamci da tausayi irin na Zafar wanda daya biye mahaifinsa da yanzu baya tare dasu balle har ya zama Garguwa ga cutar da Allah ya ɗaurawa Nihla.
Ganin Nihla nata baccinta hankali kwance yasa Abba cewa zaije ya dawo amma nazai jima ba,sai da Aunty tayi masa rakiya har ƙofar ɗakin kafin ta dawo ta zauna tana saƙawa da kwancewa a rai.
Wayanta ta ɗauko tare da dannawa number Irfan kira,zaune yake a gefan katifarsa yana ɗaure igiyoyin takalminsa da yake sakawa yaji wayarsa na ruri,hannu yasa tare da ɗaukowa,tsurawa number ido yayi ganin besanta ba tana kuma niyar tsinkewa yasa ya ɗauka tare da faɗin "hello"
Wani irin lumshe idanuwa Aunty tayi tana jin muryar Irfan na ratsa duka wani lungu da saƙo na sassan jikinta cikin salo da jan hankali ta langwaɓar da murya tace"barka dai farin cikina! haba ya kake son wahalar da zuciyar da tunaninka ya riga ya gama hudata Irfan? haƙiƙa bana da wani sukuni ko farin ciki idan har ka kasance da yiman rowar kanka ko muryarka,ina fatan ka gama tunani dayin zaɓi mai amfami akan tayin dana maka Irfan ina matuƙar sonka kuma na maka alƙawarin yi maka komai sa sadaukar da komai akan soyayyarka,kaine namiji na farko dana fara so ,ina fatan bazaka taɓa bani kunya ba".
Tunda Aunty ta fara magana Irfan ya rasa wacce duniya yake shin sama yake ko ƙasa?,duk yanda yake ji sai dai hakan bazaisa ya cutar da kansa ba ko ya kori alkhairin daya doso shi cikin ƙaramin lakaci.
Murmushi ya saki yana jin wani sanyi har cikin ransa cike da ɗauki da daɗɗan murya yace"ki ɗauka a ranki cewa IRFAN nakine Auntyna kece mai sarrafa farin cikinsa da duk wani akalar rayuwarsa,Irfan bazai taɓa kaiwa ko ina ba in har babu ke Masoyiyata ,waye zai zaɓi wahala da soyayyah akan kuɗi da tsaleliyar Hajiya irinki,ke kyajyawace danni idan ina kallonki ina maki kallon ƴar shekara 18 ne dan zan iya cewa kin fisu komai ma Hajiyata".
Wani irin daɗi farin ciki,natsuwa suka dirarwa Aunty lokaci ɗaya baki na rawa tace"na gode farin cikina,nayi maka alƙawarin sauyawar rayuwanka tun daga yau"
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*wannan page din sadaukarwa ne ga farautar farin ciki fans,ina jin dadin comments dinku dan haka ga kyautar page kuyu yacce kuke so dashi*
Page 26~30
Sauke wayan AUNTY tayi tana jin farin ciki na ratsa duka sassan jikinta,ji takeyi kamar duk duniya tafi kowa gata da samun dace,wani irin murmushi ta saki tana cewa"yesss sora kuma plan b yanzu ne lokacina yayi".Jin tarin NIHLA yasa tayi saurin juyowa tana fadin"Alhmdllh sannu Nihla ya kikejin jikin naki?".
A hankali ta soma bude lumsassun idanuwanta wanda suka mata nauyi,kallonta takai ga Aunty kafin tayi kokarin sakin murmushi mai kama da kuka cikin nishewan murya tace"ruwa".
Karasowa tayi tare da taimaka mata ta tashi,sannan ta zuba mata ruwa a glass cup ta dauka tare da kaiwa bakinta,biamillah tayi ta daura hannunta akan na Aunty ta soma shan ruwan tasha da yawa kafin ta janye bakinta daga cup din tana mayar da numfashi.sannu cewar Aunty.kai kawai ta gyaɗa mata kafin tace"AUNTY Irfan".
Wani kallo mai wuyar fassaruwa Aunty ta jefa mata kafin tace "meye ya faru da IRFAN din kuma?".
ƙasa NIHLA tayi da kai ta kasa cewa komai ta fara wasa da ring ɗin dake sanye a zara~daran fararen yatsunta.dafata AUNTY tayi kafin tace"Maryam kin ɗaukeni kamar mahaifiyarki,munyi zaman lafiya da Amminki hakan yasa tana haiguwarki ta bani ke a matsayin amana,baki buɗe ido kika ga wata ba matsayin uwa sama dani kuma Allah yasan nayi kokarin riƙeƙi amana Maryam,ki ɗaga ido ki gaya mun damuwanki tun jiya nake lura dake baki da sukuni".
Hawayen da suka soma zubo mata a fuska tasa hannu ta share cikin dishewan murya tace"A..a...Aunty sh..shi..shine inata kiransa wayan bata..ta..ta shiga".
Murmushi Aunty ta saki tace"na farko dai da zan bawa ƴata shawara ta ɗauka yau dana gaya mata ta kwantar da hankalinta ta daina tashin ciwanta akan IRFAN,duk abunda yake naka ne zaizo gareka duk daɗewa,Maryam bana so ki riƙa raunata kanki akan soyayyar da bata kamace ki ba,kisa ranki a inuwa ki kwantar da hankalin ki in Allah yaso komai zaiyi daidai ,ki daima tashin hankalinki".
Gyaɗa kai kawai NIHLA tayi dan ita kadai tasan me takeji a ƙahon zuciyarta,kamata Aunty tayi ta kaita toilet ta hada mata ruwan wanka bayan ta gama ta taimaka mata ta shirya kafin ta tsareta tayi breakfast ta kuma bata drugs,tuni taji daɗin jikinta sai dai rashin ƙarfin jiki.
Jib dib dib haka zuciyoyinsu ke bugawa a duk lokacin da suka zo kusa da juna,tsayawa yayi jikin ƙofar tare da runtse ido da ƙarfi kafin yayi ƙarfin halin tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Aunty ce ta ansa sallaman da ido ya bita yana kuma yin kicin-kicin da fuska ya rasa me yasa yakejin tsanar matar nan duk lokacin dazai ganta sai yaji kamar ya haɗiye zuciya saboda tsabar takaici da ƙunci.ɗaure fuska yayi kamar an masa sanarwar mutuwa ya ƙarasa shigowa kai tsaye gaban gadon Nihla ya isa cikin murya da sai ka saurara sosai zakaji me yake fada yace"akwai in da yake maki ciwo ne?".
Ɗago dara-daran idanuwanta tayi ta kalleshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta tayi narai narai da fuska kamar zata fasa ihu.wani irin haushi da takaici suka saka ZAFAR a gaba hannu yasa ya bige mata ɗan ƙaramin bakinta da take turowa ya kuma ɗaga hannun da niyar kama kunnenta.
Kuka ta saki tayi saurin kaucewa tana faɗin"ni ba abunda yake mani ciwo".
Harara ya watsa mata tare da sakin siritin tsaki yayi waje abunsa .bayanshi tabi da harara tana guni ƙasa ƙasa.sarai yana jinta amma beko juyo ba ya fice abunsa.
Kai tsaye gida
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*wannan page din sadaukarwa ne ga farautar farin ciki fans,ina jin dadin comments dinku dan haka ga kyautar page kuyu yacce kuke so dashi*
Page 26~30
Sauke wayan AUNTY tayi tana jin farin ciki na ratsa duka sassan jikinta,ji takeyi kamar duk duniya tafi kowa gata da samun dace,wani irin murmushi ta saki tana cewa"yesss sora kuma plan b yanzu ne lokacina yayi".Jin tarin NIHLA yasa tayi saurin juyowa tana fadin"Alhmdllh sannu Nihla ya kikejin jikin naki?".
A hankali ta soma bude lumsassun idanuwanta wanda suka mata nauyi,kallonta takai ga Aunty kafin tayi kokarin sakin murmushi mai kama da kuka cikin nishewan murya tace"ruwa".
Karasowa tayi tare da taimaka mata ta tashi,sannan ta zuba mata ruwa a glass cup ta dauka tare da kaiwa bakinta,biamillah tayi ta daura hannunta akan na Aunty ta soma shan ruwan tasha da yawa kafin ta janye bakinta daga cup din tana mayar da numfashi.sannu cewar Aunty.kai kawai ta gyaɗa mata kafin tace"AUNTY Irfan".
Wani kallo mai wuyar fassaruwa Aunty ta jefa mata kafin tace "meye ya faru da IRFAN din kuma?".
ƙasa NIHLA tayi da kai ta kasa cewa komai ta fara wasa da ring ɗin dake sanye a zara~daran fararen yatsunta.dafata AUNTY tayi kafin tace"Maryam kin ɗaukeni kamar mahaifiyarki,munyi zaman lafiya da Amminki hakan yasa tana haiguwarki ta bani ke a matsayin amana,baki buɗe ido kika ga wata ba matsayin uwa sama dani kuma Allah yasan nayi kokarin riƙeƙi amana Maryam,ki ɗaga ido ki gaya mun damuwanki tun jiya nake lura dake baki da sukuni".
Hawayen da suka soma zubo mata a fuska tasa hannu ta share cikin dishewan murya tace"A..a...Aunty sh..shi..shine inata kiransa wayan bata..ta..ta shiga".
Murmushi Aunty ta saki tace"na farko dai da zan bawa ƴata shawara ta ɗauka yau dana gaya mata ta kwantar da hankalinta ta daina tashin ciwanta akan IRFAN,duk abunda yake naka ne zaizo gareka duk daɗewa,Maryam bana so ki riƙa raunata kanki akan soyayyar da bata kamace ki ba,kisa ranki a inuwa ki kwantar da hankalin ki in Allah yaso komai zaiyi daidai ,ki daima tashin hankalinki".
Gyaɗa kai kawai NIHLA tayi