kamata dan tasan lallai anwa Nihla rashi,tasan irin tsantsar soyayyar dake tsakaninta da Abba,karsawa tayi tare da zama akan gadon tasa hannu tare da dafa bayan Nihla,lumshe ido Nihla tayi hawaye na safkowa daga cikinsu jin Miemie ta anbaci sunanta yasa ta dagowa tare da share fuskarta,kwabe fuska Miemie tayi kamar zata yi kuka tace"haba Nihla?shiyasa nace ki dawo scul,babu amfanin ki rika zama kina kuka haka kinsan kuma ba lafiya gareki".
Dago blue eye's ball dinta tayi tare da daurasu akan Miemie,wani kukan ke niyar kwace mata tayi saurin rufe bakinta cikin sanyin murya tace"Miemie Irfan ne".
"Irfan kuma?,ina yanzu nafa yabar gidan?kuma na tabbata in dai Irfan yana kusa da ke ba zai bari kiyi kuka ba".
Rike hannuwan Miemie Nihla tayi tare da cewa"Irfan shi ne silar kukana Miemie,ina son Irfan fiye da kaina,zan iya sadaukar da komai dominsa,amma yau shi da kansa ya guje ni Nihla,Irfan ba ya so na ,Miemie Irfan Aunty yake so,ko fitarsa da kika gani daga wurinta yake ba wurina ba".
Saurin janye hannuwanta Miemie tayi daga rikon da Nihla tayi mata da karfi ta mike tsaye tare daja baya tace"anya kina cikin hankalinki kuwa? kin kuwa san me kike fada? wannan ae abunda bazai taba yiwuwa bane".
Murmushin da yafi kuka ciwo Nihla tayi tare da cewa "sai gashi yau ya yiwu Miemie,farin cikina daya tak daya rage yau ya janye mani,abun takaici kuma ya dawo wurin matar babana".
Razana,al-ajabi,tsoro tsantsar tashin hankali da fargaba shine abinda ya dirarwa Miemie lokaci daya.Bugawan da zuciyarta tayi yayi daidai da zubo war hawaye mai zafi akan fuskarta,saurin gogewa tayi tare da fadin"Never,hakan bazai taba yiwuwa ba,ko da shi ne abunda zan aikata na karshe a rayuwata tabbas yarda kika rasa Irfan haka zalika Aunty Nafisa sai ta rasa Irfan".
Kuka sosai Nihla ta kuma sakawa tare da cewa"Miemie ina san sa,bana so na rasa shi,ina so ya dawo gare ni"
Dafe kai Miemie tayi tare da cewa"tunda kina so ya dawo,sai ki tashi kiyi fada akan soyayyarki,kije ki roketa idan hakan be biwu ba sai kisan abunda zakiyi bawai ki zauna kina koke-koke ba".jan hannun Nihla Miemie tayi da sauri tare da fitowa da ita daga dakin,kai tsaye gaban Aunty ta kaita tare da sakin hannunta.
Dukawa Miemie tayi akan kafarta tare da hade hannayenta duk biyun tare da cewa"Aunty ke uwa ce,kada ki watsar da kimarki akan biyan wata bukata naki,Nihla kamar yar da kika haifa ce,Aunty ana barin halas ko dan kunya,a tunanina ko da ke ke son abu Nihla ta nuna tana so zaki iya hakura ki bar mata,dan Allah Aunty na rokeki kibarwa Nihla masoyinta".
Murmshi Aunty tayi tare da mikewa,dafa kafadan Miemie tayi tare da cewa"sirikata kada ki damu,bawai na dauke Irfan daga wurin Nihla bane a'a,shi da kansa yaga ya dace ya canza akalar soyayyarsa,kuma ni bance ta daina son sa ba,tana da damar da zamuyi tarayyah a soyayyah nayi mata alkawari in har ya nuna ita yake so to zan bar mata shi"tana gama fadan hakan ta wuce part dinta abunta.
Zage dakin yake yi hannunsa zube cikin aljihun wandon dake jikinsa,sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da zama akan daya daga cikin fararen kujerun dake cikin wurin shakatawar,langwabar da kai yayi tare da lumshe kyawawan idanuwansa babu abunda yake masa yawo a kai sai kalaman Abba dana Momy kafin rasuwarta furzar da iska yayi tare da sake lulawa cikin duniyar tunanin data zamar masa abun fira......
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderhβπ»
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: ππππππ
*FARAUTAR FARIN CIKI*
ππππππ
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 71~75
17 year's back
Rike hannun Zafar Mummy tayi tana cikin radadin ciwo,sam ta gama fita daga hayyacinta ,gyara zamanta tayi tare da jingina jikin gadon asibitin da take zaune tayi,kallon jaririyar dake kan k'afarta tayi fas kyakyawa da ita,wanda haihuwarta kenan yanzu,hawaye ne suka zubo a kan kyakyawar fuskarta ta dauki y'ar hannunta na rawa ta daurata akan hannun Zafar dake zaune kusa da ita,da ido kowa na dakin yabi Mummy da kallo harta Zafar kasa dauke idonsa yayi daga kallon da yakewa Mummy na alamar tambaya,hannunta ta mike daidai gaban Zafar kafin ta fara cewa"Zafar ga K'anwarka nan na baka iko da ragamar kula da rayuwarta,ka zama Garkuwanta kuma gatanta kada ka bari wani ya wulakantata ,kada tayi kukan rashin mahaifiya,ko Yaya ko kane,,idan harka aminta da amanar dana baka ka mun alkawari ka daura hannunka akan nawa Zafar"ta kare maganar tare da share hawayen dake zubo mata.
Kallon babyn Zafar yake yi,tuni idanuwansa sun gama canza launi ,tsantsar tashin hanlali ne kawai zaka hango a tattare dashi,taya zai iya rike wannan amanar mai girma haka? yawa kansa tambayar da bashi da ansa,ashe maganar tasa ta fito fili.
Murmushi Mummy tayi tare da cewa"zaka iya Zafar kai din adaline kuma mai kula da duk wani nauyin dake kanka,,duk da kana d'an shekara 16 Zafar amma kana da hankalin yan 30 kuma kana yin abunda suka gagara yi".
Jinjina kai Zafar yayi tare da daura hannunsa akan na Mummy yace"nayi maki alkawari Mummy bazaki taba dana sanin Amanar da kika bani ba,zanyi iya yina,zanyi da karfina,da dukiyata da duk wani abun dazan mallaka bazan taba barin Amanata ta shiga kunci ba".
Hadasu duka biyun Mummy tayi tare da rungumewa,tana jin sanyi a ranta,a kan idonta Zafar ya daga babyn tare da mata huduba da Maryama ,murmushi yayi tare da mikewa yabawa Abba babyn yace"Allah ya raya mana mamana taci sunanta Maryama zamuna kiranta Nihla.Sosai farin ciki ya cika zuciyar ,Abba ,Daddy Ammi da kuma Aunty dake tsaye kusa da Abba.
Allahu akbar,Allah akbar Allah mai girma da daukaka maiyin yarda yaso a duk lokacin da yaso,idan da ranka baka gama ganin ikon Allah da girmansa da daukakarsa ba ,lallai mutuwa dole ce,dole duk wani mai rai ya dandana dacin mutuwa, A lokacin da kowa ke murnar zuwan Nihla duniya a daidai wannan lokacin kuma Allah ya karba mahaifiyarta ba tare da tasan dadin uwa ba bare ko da sau daya ta kurbi nonon mahaifiyarta a matsayin abincinta na farko a duni,,,wani tsalelan kuka Nihla ta tsala da matukar karfi a lokacin da ran Mummy maryam ya gama fita,fitan rai mai sauki da dadi babu shure shure babu raki ,mutuwa ba tare da wanda suke daki daya sun fahimci hakan ba,(Allah ka azurtamu da saukakakiyar mutuwa).Sai a lokacin kowa hanlalinsa ya dawo akan mummy wacce ta ansa kiran mahaliccinta.
Saurin mikewa tsaye Zafar yayi tare da shafa gashin kansa tare da fezar da iska mai tsananin zafi yana kuma kara jinjina karfin girman alkawarin daya daukarwa Mummy.runtse idonsa ya kuma yi da karfi maganganun Abba na kuma masa yawo kafin rasuwarsa.
Sati daya daya wuce
Rike Zafar sosai Abba yayi cikin wahalan ciwo yake masa magana"Zafar hakika kai da na gari ne,ka gyara amintakata da mahaifinka ko yanzu na mutu burina ya gama cika Zafar,tunda raina kana kula da Nihla baka taba gazawa ga Amanrka ba,yauma ga wata Amanar daga bakin mahaifi zuwa D'ansa,,ka rike mun Nihla ka kula mun da ita,ko kadan kada ka barta tayi zaman maraici,tabbas bayan mutuwata a lokacinne Nihla zata gane mabanbantan rayuwa,a lokacinne duniya zata mata baki ta kasa gane komai,tana da kananun shekaru Zafar ka kula da kanwarka kaci gaba da zama Garkuwarta a kp yaushe,karka sakarwa Nafisa kula da Nihla domin Nafisa mata ce mai fuska biyu,Nafisa ba zata iya rike mun y'ata ba,hasalima ita ce zata zama bangon bakin ciki da zai ruguzawa Nihla farin cikinta,ka saka ido sosai a kanta daga karshe zaka gano abunda nake fada maka Zafar".I zuwa wannan lokacin kan Zafar wani irin sarawa yakeyi da matukar karfi,duka jijiyoyin jikinsa sun fito radau-radau,saurin dago rinanun idanuwansa yayi yana zubawa Miemie data shigo dakin tana cizgar kuka,akan Zafar ta tsaya cikin tsantsar kuka tace"Yaya anya zaka iya ci gaba da rike amanar daka dauka kuwaβ,a yau Nihla tana cikin tsananin bakim ciki,tayi kuka tayi kewa a yau ta tabbata marainiya wacce ta rasa gata ta kuma rasa wanda zai lalasheta ya tallafeta".
Murmushin takaici Zafar yayi cikin sanyin murya yace"bawai na daina zuwa duba Mamana bane sai bazan iya jurar ganinta tana kuka akan mutuwar Abba ba,wannan kuma nasan bana da ikon hanata yin kuka akan rashin bango abun jingina gareta"bai tsaya takan Miemie ba data fadi akan kafarta tana kuka kamar zata mutu ba ya fice yaja dakin,cikin sanyi ya soma safkowa daga stairs sai da yazo tsakiyar parlon sannan ya tsinci maganar Hajiya Kaka tana fadin"Zafar kai nake zaman jira fa,gashi kana kallona kuma zaka wuce".
Ba tare daya tsaya ba,yace"zan dawo ba jimawa,zan iskeki wurinki".Ba tare da ya jira yaji ansarta ba ya fice da sauri.Beko tsaya ansa gaisuwar da Baba mai gadi ke masa ba ya bude gida ya fice,cikin sassafar yake tafiya tare da zagayawa layin dake kusa da nasu,unguwar shiru kasancewar irin wannan unguwannin baka samun mutane a waje sai yan tsirarin motoci dake gittawa,yana isa yayi sa'a kuwa gidan a bude yake yasa kai tare da wucewa ciki.
Tsakiyar main parlon gidan ya tsaya tare da zuwa hannuwa cikin wandon aljihun jeans dake jikinsa,dara-daran idanuwansa da suka koma red red ya daga tare da watsawa Aunty Nafisa su ,da sauri ta janye idanuwanta data zuba masa kamar tsohuwar mayya.Ta gefan Aunty ya raba zai wuce tare da sakin siririn tsaki,da sauri zuciyarta na matukar bugawa tayi gefe ranta cike da tsantsar tsoro.Tsaye yayi cak,jin an rungumesa ta baya ga sautin kuka mai cunkushe da tsantsar fargaba da tsahin hankali duk mai yinsa kasan ba karamin kuna yake ji a zuciyarsa ba,ya zama kamar wanda ruwa ya kama neman agaji yake kota wacce hanya,runtse idanuwansa yayi tare da kawar da kansa gefe yayin da zuciyarsa ke dukan ukku ukku kansa da tunaninsa na niyar tarwatsewa lokaci daya,ita kam iya karfinta take rungume dashi kamar wacce za'a kwacewa shi kyarma kawai take hannuwansa yasa tare da rabata daga jikinsa ya juyo tare da fuskantarta,batayi wata wata ba ko jinkirtawa wajan kara fadawa a faffandan kirjinsa ta kuma rungumesa,still hannuwansa yasa tare da dagota daga jikinsa cikin sanyin murya yace"Mamana kin girma yanzu,ki daina kokarin rungumata haka".Ganin bata fahimtar komai in ba yarayen kuka ba,be da wani zabin daya wuce karbarta a wannan lokacin riketa yayi sosai a jikinsa yana bubbuga bayanta tare da hura mata iskar bakinsa alamar lallashi.
Wani kululun bakin ciki ya turnike zuciyar Aunty wani mugun kishi ya soma dawainiya da ita,ji take kamar ta shakare Nihla ta cireta daga jikin Zafar ko taji saukin abunda take ji a ranta,hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta da sauri tayi part dinta kafin zuciyarta tayi boosting.
A hankali ta soma yin shiru sai ajiyar zuciya da take saki a kai a kai,a sannu komai nata ya fara sakewa a jikin Zafar alamun bacci ya dauke ta a tsayen da take,hannu yasa tare da janye dogon gashin dayawa fuskarta rumfa,sosai yake jin nunfashinta na sauka a kan kirjinsa,rasa abunda zaiyi yayi a dole ya dauketa kamar ya dauki baby ya wuce part dinta da ita,da kafa ya bude door din kafin ya shiga a bed ya daurata yana niyar tashi daga sunkuyan da yake riganta ta shige cikin aninayen rigarsa har kusan fada mata yayi,da sauri ya dafa gadon yana mayar da numfashi,zare rigan nata yayi daga jikinsa ya samu ya mike,lullubeta yayi ya kashe ACn dake kunne a dakin kafin ya koma akan karamar chair ta dakin ya zauna yana kallon pic din Mummy da Abba sai nashi dana Nihla lokacin tana karama da suke ajiye akan drawan ya lula tunanin rayuwarsu ta baya......
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawsn karshe*
Jorderhβπ»
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: ππππππ
*FARAUTAR FARIN CIKI*
ππππππ
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
76
ASALIN LABARIN
ALHAJI UMAR shi ne asalin sunan Abba ,ALHAJI AL-AMIN shi ne sunan Daddy.Asalin amincin su ya samo asaline tun daga iyayensu haka suka tashi suka ga kansu a wuri daya amincinsu ya zama kamar yan uwa,daya baya zama sai da daya harda kalar kayan jikinsu basa banbantawa,ko a makaranta wajen zaman su daya,iyayen su maza da kuma Hajiya Aysha wato mahaifiyar Umar sun rasu ne ta hanyar hadarin jirgin sama daya ritsa da su.Ba karamin tashin hankali Hajiya Jamila(Hajiya Kaka) ta shiga ba duk da ta kasance jarababbiya kuma mafadaciya amma bata da mugunta haka ta kama Umar da Al-amin ta rike a hannunta har zuwa lokacin auren su in da Al-amin yake auran Maryam yar asalin garin Adamawa ce,mata mai tsanin tsoron Allah da son mutane,a yawon kasuwancin sa ya hadu da ita.Shi kuma Umar a nan cikin garin katsina ya hadu da matarsa mai suna Maryam mace mai tsanin kunya,hankali da rashin son hayaniya.Ko kadan Hajiya kaka bata masu sauki akan yin wani abunda bai dace ba ko kuma wani ya kauce fadanta ma kadai ya ishe ka.Tun bayan auren su Allah ya kara sakawa kasuwancin su albarka dukiya ta habbaka tayi yawan dasu kansu mamalakanta basu san iyakarta ba,a daidai wannan lokacin ne kuma Hajiya kaka ta bijiro da masifar an auro mata ba mai niyar Haihuwa ba kamar matar Al-ameen wato Ammi ba wani jinta take a ranta ba saboda kasan cewarta ba yar masu kudi ba.Wannan dalilin yasa Hajiya kaka cewa dama dan ta kwashe masa dukiya ta aure sa wannan shine asalin rashin shirin Ammi da Hajiya kaka.Ana tsaka da wannan fitanan Maryam(Ammi) ciki ya bayyana,duk da tsananin farin cikin da suka yi hakan besa Hajiya kaka ta sake da Ammi ba.Wata tara ta sanbalo yaronta kyakyawa ajin farko ,saboda tsananin murna maryam(Mummy) tayi kukan murna tayi sadaka ta bayar da abubuwa da dama dan ji take kamar ita ce ta haifi yaron,ganin hakan da take yi a ko yaushe it Ke dawainiya da jaririn yasa Ammi mallakawa mummy jaririn da ko sunansa ba'ayi ba,har ranar suna tazo akayi fatali da dukiya akayi suna na azo a gani ,yaro yaci suna MUHAMMAD ZAFAR wanda Mummy ce ta zaba masa wannan sunan.Sosai Hajiya Kaka ke matukar nuna soyayyah da kulawa ga Zafar sai dai shi sam tun yana jariri baya zama inuwa daya da ita,tana taba shi yake fara tsallara ihu .Ta kasance da yin tsawa da masifa hakan yasa ko kallonta Zafar yayi zai fashe da kuka ko kadan baya son hayaniya da fada.Tunda akayi yayen sa Ammi ta hada kayansa ta bawa Mummy ya koma part dinsa,shakuwar Mummy da Zafar ta wuce tunanin duk mai tunani komai ita ke masa baya cin abinci idan ba ita ta basa ba,bashi bacci idan ba jinta yayi a kusa da shi ba.Haka rayuwa taci gaba da tafiya in da hankalin Hajiya kaka kab ya dawo akan mummy sbd rashin haihuwarta.
5year's later
Zaune suke a babban parlon gidan fira suke yi tare da fara'a fal fuskar su,daukar yankan apple Mummy tayi wanda Zafar ne ya saka mata Mummy ,yake kiran Mamansa Ammi ,Umar kuma Abba ,Al-ameen kuma Daddy,ta kai bakinsa ,bude baki yayi tare da ansa ya kuma mayar da kansa akan kirjinta ya kwanta,a lokacin yana dan kimanin shekara biyar.Gyara zama Ammi tayi tare da sakin nishi tana tallabar katon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe.Fuska daure Hajiya Kaka ta shigo dakin ta zauna a chair tare da yin daya kan daya.Saurin safkowa kasa Mummy tayi tana kara rungume Zafar a jikinta bakinta na rawa fuska cike da tsoro tace"Hajiya ina wuni".Banza Hajiya Kaka tayi mata ta juya tana ansa gaisuwar sauran yaran dake gaisheta a parlon.Mikewa Zafar yayi tsaye tare da jan hannun Mummy yace"tashi,tashi muje daki,kar Allah yasa ta ansa gaisuwan dama ke kike gaisheta".Kafin ,Zafar ya rufe baki Hajiya Kaka ta tangare masa keya,a fusace ya juyo fuska murtuke yace"kar dai kimun ihu a kai".Saurin janyosa Mummy tayi tare da cewa"Muhammad zamu bata kanawa manya rashin kunya".
"har kina da bakin fadin hakan?ae duk abunda Zafar zaiyi laifinki ne ke kika bashi tarbiya kuma sunan da yake ansawa naki ne,dole zaiyi abunda yake so".
"ki daina wa Mummyna fada,babu ruwanta ni ne nake so na gaya maki haka saboda kina takura mata"Zafar ya bada ansa.
A fusace Hajiya kaka tace"zanyi maganin ku kai da uwar rikon tana,Umar ina so kayi aure,Umarni ne na baka ba shawara ba,ina so naga jikanka kafin na rasu,idan kuma bani da iko da kai zaka tabbatar mun ba nono kasha ba sai ka bijirewa Umarni na".
Kasa Abba yayi da kai tare da cewa"Hajiya duk yarda kike so haka za'ayi,insha Allah zaki sameni da bin umarninki a ko wanne lokaci".
"Allah yayi maku albarka "ta fada tare da ficewa yabar parlon.
Wasu zafafan Hawaye masu dumi suka zubo a fuskar Mummy,da sauri Zafar ya tallabi fuskarta tare da cewa"kibar kuka Mummyna ,ki daina biye mata,ita fada kawai tasa gaba,idan na girma zan zana soja in halbe maki ita,Insha Allah kuma zaki haifo mana baby mai kyau kamar ki".Murmushi ne ya subucewa Mummy ta rungume Zafar.Ana cikin wannan yanayin ne Ammi kuma ta sake sanbalo yaronta kyakyawa ranar suna yaro yaci suna Ramadan,duk da tsananin kulawar da Zafar ke nuna masa da tsananin so amma sam bai yarda ya dau lokaci a bangaren Ammi.Watan Ramadan ukku Hajiya kaka ta samowa Abba matar aure,yarinya mai tashe da kyau da halayyah mabanbanta mai suna Nafisa,tayin farko Nafisa ta amince da auren Abba duk da ba wani son sa take ba dukiyarsa kwai take kwadayi,a lokacin Nafisa tana yar shekara 23.Auren Nafisa shi ne dalilin rushewer wannan Familyn ta kasance itace wacce take rike da kaddarar gidan,ita ce asalin kawo bakin ciki da rarrabuwar kan ko wanne a gidan su,tayi amfani da damar zama mata a gidan ta hanyar cika burukanta da dama,sati biyu da haihuwar Ramadan Aunty ta shigo gidan a matsayin matar Abba.
A fuska Nafisa mata ce mai tsakanin kirki,son kowa da kuma kyautatawa duk wani dake gidan.Zafar ne ya taso da tsananin kiyayyarsa duk soyayyarsa da abu data taba shi to ya gama amfanarsa ko menene,ko parlo yake zaune tana fitowa zai tatara kayansa yabar mata parlon.Duk wata y'ar tsamarsa da Kaka ya janyeta ya dawo da ita akan Nafisa wanda su Mummy ke kira da Aunty.Nafisa ta kasance tauratuwa kuma masoyiya ga Hajiya Kaka ta kwacewa kowa fada,komai lamuran Hajiya kaka a wurinta suke,da komai daya shafi gidan. Wannan kenan.
Zagaye daki take yi,maganganu da yawa suna mata yawo a kai.Kwatakwata ta rasa sukuni babu abunda take buri da so daya wuce mallakar dukiyar Familyn gaba daya da kuma babban burinta na raba Mummy da Abba.Kamar wani gunki haka ya iso ta gefanta tare da rabawa zai wuce.Saurin juyowa tayi tare da daga hannu tana kokarin janyo hanun Zafar.Da matukar karfi ya bige hannunta kafin ya karasa a hannunsa,dara-daran idanuwansa ya kuma zazzarosu waje tuni sun sauya kala da kawo k'yalli k'yalli alamun ruwa ya fara taruwa a cikin su,hannu ya daga tare da nuna ta da yatsa tare da cewa"karki kuskura,har abada duk ranar da kika yi gigin taba ni nayi maki alkawari da wanda raina yake a hannunsa a ranar sai na cire maki wannan kazamin hannun naki".Hannu yasa tare da damkar sumar kansa ,da sauri ya karasa ya dauki qur'an din da yazo dauka ya dauka ya wuce Mummy da Ammi dake tsaye cike da tsananin al-ajabi sun daskare da ganin yaro karami yana irin wannan halayyar.Zafar kam ko kallonsu beyi ba yabar parlon yayin da zuciyarsa ke cike da tsananin kiyayyar Aunty tana kuma bugawa da matukar karfi..
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderhβπ»
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: ππππππ
*FARAUTAR FARIN CIKI*
ππππππ
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
77
Mummy ce ta katse shirun da duban Aunty tare da cewa "dan Allah kiyi hakuri,kinsan lamarin yara ba kamar Zafar mai wuyar sha'ani zan masa fada insha Allah bazai kuma ba".
"wallahi Mummy babu komai,kada ki damu kanki waye besan yara ba?komai ya riga ya wuce".Aunty ta bata ansa tana wuce wa ciki.
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da cewa"lallai yaron nan so yake nayi maganinsa ,kiji daukar magana yanzu idan Kaka taji wannan maganar fa?".
Dafa kafadunta Mummy tayi tare da cewa"insha Allah ba zata ji ba,bari naje na same sa"batajira cewar Ammi ba ta bi bayan Zafar kai tsaye dakinsa ta nufa,zaune yake akan prayer mat ga al-qur'ani a gabansa yana muraji'a,shigowa ta yi ciki ta zauna a gabansa,sai da yakai ayar da yake yi karshe kafin ya dago ya kalli Mummy .Ba laifi fuska a sake yace "Mummy wani abun na damun ki ne? ."
Kuma daure fuska tayi kafin tace"ai dole abu ya dame ni Son,yanzu kai ya dace ace matar Abbanka ka ke wa magana haka?".
Saurin ja da baya Zafar yayi dan da nan annurin fuskarsa ya guje, taune lips dinsa ya yi kamar zai huda ya kasa cewa komai."Zafar magana na ke maka fa".
Kallon Mummy yayi tare da cewa"to Mummy ban san me zance ba ae,dan Allah ki daina shiga tsaka ni na da waccan matar na roke ki".
Sake da baki haka ta bisa da kallo,rasa me zata cw ma tayi hakan yasa ta mike tabar dakin.Shikam nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kuma jin tsantsar tsanar Aunty a ransa.
2yrs later
Abubuwa da dama sun faru masu dadi da mararsa dadi,dama rayuwa haka ta gada.
Ammi ce zaune a gado ,kowa na gidan yana parlon a lokacin Zafar yana shekara 16 Ramadan na dan shekara 11 ,ko wanne ka gani cikinsu fuskarsa dauke take da yalwataccen murmushi marar yankewa,cike da fara' Daddy ya mikawa Mummu babyn dake hannunsa tare da cewa"Allah ya raya mana Nana Aisha."
Wani irin murmushi ne ya subucewa Abba yana kallon Daddy cikin hanzari ya karba babyn daga hannun Mummy yana cewa "masha Allah yau Hajiya ta dawo,ina godiya da wannan karamcin insha Allah daga yau zamuna kiranta Miemie ,kuma na mallaka mata kamfanina na gidan Ashana dake nan garin kano".
Wani irin yunkurowa Aunty tayi da karfi har tana niyar fadowa daga kujera tace"haba Alhaji daga haihuwar yarinyar?".
Wata uwar harara Zafar ya afka mata cike da masifa yace"an kasa da ke ne? kiyi kokari ki haiho Aminiyarki Jamila sai ita a bata ta hassada sai ta kare".
Dakuwa Ammi ta masa tare da cewa"ungo nan Muhammad,sai dai ta haifo Maryam badai Uwar mu ba".
Dariya Ramadan ya saka tare da cewa"wallahi Yaya duk ranar da Hajiya kaka ta ji kana cewa a haifota wallahi ka shiga rububi".
Harara Abba ya masu yana cewa"ku kama kanku a wurin nan,bama son shakiyan ci".
Gyara zama Mummy tayi tare da tallabar k'aton tsohon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe tace"mu dai a bamu babyn mu yunwa take ji".
Da sauri Ramadan yace"Mummy wannan babyta ce Ammina ta siyo mun".
Mugun kallon da Zafar ya jefa masa yasa yayi shiru da sauri,tsaki yaja tare da dafa cikin Mummy yace"na raye gori,insha Allah nima Mummyna mace zata haifa mun mai kama da ita,in kuma saka mata sunan Mummy".
Kowa fuskarsa fal fara'a ,kama Mummy Zafar yayi ya tusata gaba da rigima dole sai da suka tafi part din su.
Bayan sunan Miemie da kwana biyu Mummy ta tashi da nakuda,cikin sauri aka tafi da ita asibiti,tafiyar ta karshe,barin gidan nata da ahalinta da rai na karshe,hakika mutuwa dole ce kuma ance sabo ake wa kuka ba mutuwa ba...Tun daga mutuwar Mummy komai na rayuwar Zafar ya gama canzawa dandanan yake kasancewa cikin tsakananin fushi da kunci,ko kadan be son hayaniya magana ma gaggararsa take yi,a ko yaushe yana rike ne da Nihal,saukin sa daya gama zana jarabarwar gaba da secondry ne kullun yana gida,ko daidai da second baya barin Nihal wani irin tsantsar so da kulawa mai cakude da tsantsar tausayi.A bangaren Nihal ma hake ne,tunda ta fara wayau bata yarda kowa ya bata ta daga Abba sai Zafar.Lokacin da Zafar zai tafi makaranta ba karamin daga aka sha ba dan da kyar aka samu ya tafi dan kafewa yayi ya jingine makarantar wai shi ba zeje ba,sai da Abba ya dage kafin aka samu ya koma makaranta...A lokacin ne kuma fir Aunty ta dauke Nihla daga hannun Ammi ta lullubeta da soyayyar karya ,tun Nihla na kukan Zafar harta hakura ta saba da zama da Aunty.A wannan lokacin ne kuma