An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too.😘😍😀
Bismillah
Page 1~5
Cikin sassarfa ta fito daga bedroom ɗin nata,hannuwanta riƙe da ƙaramin hijab tana ƙoƙarin sakawa ga scul bag goye a kafaɗanta ɗaya.tsayawa nayi tare da ƙare mata kallo sanye take cikin unifoam farare ƙal wando ne jikinta sai riga wacce bata ƙaraso gwaiwarta ba mai tsaga a duka side na rigan .farin socks ne a ƙafanta sai black tom's yayin da hannun hagunta ke sanye da agogon apple black itama hakan yasa na tabbatar da cewa tana karatun likitanci kenan. NIHLA UMAR kenan yarinya mai ƙananun shekaru dan ba zata haurawa shekaru goma sha bakwai a duniya ba.Nihla irin matan nan ne mararsa jiki sai dai tana da shape daidai misali mai kuma matsakaicin tsawo tana da kyau idan nace kyau ina nufin kyau sai dai bata cika haske ba.Nihla ƴa ɗaya tak ga Alhaji Umar.
"NIHLA!,NIHLA!"shi ne abinda AUNTY ke faɗa tana ɗan ɗaga murya taci gaba da cewa"ba xaki fito ba sai kinyi latti?".
Lumshe dara-daran idanuwanta tayi yayinda dogayen eyelashes ɗinta suka kwanto akan kyakyawar fuskarta cikin siririyar muryarta mai daɗin sauraro tace"Aunty ina xuwa".gyara hijab ɗin kanta tayi tana kuma janyota danta rufe mata gashin kanta dake kwance lub akan goshinta ta fito tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta.kai tsaye gaban Abbanta ta isa wanda yake zaune a chair hannunsa riƙe da jarida,ƙafafuwanta ta ajiye a ƙasa tare da ɗaura kanta akan cinyarsa tace"Abbana barka da safiya".
Jaridar hannunsa ya ajiye gefe tare da zare eyeglasess din idonsa cike da so ƙauna ya dafa kan NIHLA fuska ɗauke da murmushi yace"barka dai Ammin Abbanta .kin tashi lafiya?".
Itama fuskarta da murmushi tace"lafiya qlau Abbana".
Kallonsu Aunty tayi tana kuma kissima wani abun a ranta kawar da tunanin hakan tayi ta matso dab dasu tana faɗin "tunda an manta da ni to yanxu na tuna da kaina".
Waro ido NIHLA tayi tace"kiyi haƙuri AUNTY ganin Abbana yana mantar da ni komai a rayuwa."
Dariya Abban yayi hakan yasa dukansu saka dariya kafin ya miƙe yana riƙe da hannun NIHLA har zuwa diniing area.zaunar da ita yayi tare da haɗa mata tea ya miƙa mata.karɓa tayi tare da soma sha sai da ta shanye tas sannan ya soma bata chips da kansa bataci da yawa ba ta miƙe da sauri tana faɗin"Abbana i'm full kuma xanyi latti".
Hannu ya ɗaga mata tare da cewa"to Allah ya tsare sai kin dawo".
Da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa AUNTY ta bisu dashi tare dayin ƙwafa tace"tau yanzu kazo kayi break tunda an samu ta tafi scul ɗin".
Shafa ciki Abba yayi yace "bari na gama shiryawa ,yau baxan fita da wuri ba".
Tankamemen filin da NIHLA ta fito na tsaya kallo lallai an tara dukiya dan gidan yafi ƙarfin ka kirasa da hause sai dai mantion.iya tsaru gidan ya tsaru tana fitowa Sale driver ya ƙaraso da sauri ya buɗe mata bayan motar ƙirar KLK ash colour ta shiga kafin ya zagaya mazaunin driver yaiwa motan key yabar gidan kai tsaye yahau titin dazai kaisa i zuwa makarantar tasu.
Tunda Abba ya shiga Bedroom Aunty ta rumtse ido da ƙarfi tana jin zuciyarta kamar xata fasa ƙirjinta ta fito dan takaici,a duk duniya tana matuƙar kishin kulawar da ALHAJI UMAR ke nunawa akan NIHLA sam takan kasa jurar hakan duk da ta kasance ƙanwar Alhaji umar din kuma matarsa ta ko wanne fanni xata ansa sunan uwa ga Nihla saidai sam hankalin baya akan nan.
Kamar ko yaushe Sale a bakin gate ya ajiye NIHLA inda ko ina ka duba ɗalibaine birjik yaran masu dashi ga duk ta in da ka duba danƙara dankaran motoci ne ke xagaye da wurin.kai tsaye cikin scul ɗin ta shiga ta isa cikin class ɗinsu.bag ɗin dake goye a kafaɗanta duka yakaiwa MIEMIE dake kwance akan desk,cike da masifa MIEMIE ta ɗago ganin NIHLA yasa ta saki murmushi tace"ae dama masan sai ke".
"eh sai ni ,shine kika taho kika barni"NIHLA ta faɗa tana zama.
Yatsina fuska miemie tayi tace"ta ina zan jiraki bayan dana shigo gidan babu alamun tashinki ma.
Buɗe baki NIHLA tayi da niyar yin magana amma sai tayi shiru ganin har ana shirin fata lecture.
Cikin takun ƙasaita da isa na zaratan maza yake safkowa daga stairs ɗin saboda sauri har haɗa bibbiyu yakeyi ga hannunsa dake akan rigarsa yana gyara bottons ɗin rigar black suit din dake jikinsa.Dogo ne sosai fari tas yana da faffaɗan kirji ga kansa dake ɗauke da tulin suma sai sheƙi takeyi tana ɗaukar hankali,yana da long face in da take ɗauke da ɗan ƙaramin pink lips sai sirirn hanci sai kuma eyes ɗinsa masu matuƙar ɗaukar hankali wanda idan ya kalleka dasu zaka ɗauka baccine be ishesu ba yarda suke a lumshe wannan ne ya taimaka wurin rage masa girman idanuwan nasa, DR ZAFAR MUHAMMAD KOFA kenan matashin saurayin da bazai gazawa 32 ba kuma shahararran ɗan kasuwa mai tudin tukiya daji da kansa...cikin sassarfa ya safko cikin babban parlon wanda tsayawa faɗan tsaruwansa ma ɓata lokacine,kai tsaye dining area ya nufa ya kuma kutsa kansa cikin kitchen bai tsaya wata wata ya rungume matar dake tsaye a gaban gas ta baya.
Murmushi ta saki cike da so da ƙauna ta ɗago hannunta ta shafa gefan fuskarsa tace"masha Allah Muhammad ya fito ,barka da safiya farin cikin AMMINSA!"
Nannauyan numfashi ya sauke tare da cewa"Ammin Muhammad barka da safiya,ina kwana".
"lafiya Alhmdllh yaron kirki,muje kayi break nasan ka kusa yin latti"Ammi ta faɗa tana kashe gas ɗin dake gabanta.
Tsadaddiyar agogon hannunsa ƙirar gucci ya lalla tare da ƙwaɓe fuska yana jan hannun AMMI suka fito wurin dining ɗin.xama yayi kafin ta fara haɗa masa tea ta miƙa masa.ƙarɓa yayi ya kumayi bismillah yakai mug ɗin baki,idanuwansa ya lumshe kafin ya waresu a fuskar Ammi yace"Ayyah Ammina sugar bai fito ba".
Waro ido Ammi tayi kuma a lokacin na samu damar ganin fuskarta nan naga tsantsar kamar da sukeyi da Zafar kamar tayi kaki ta ajiye.baki buɗe tace"Muhammad bazaka daina san zaƙi ba kaikam".karɓar mug ɗin tayi ta ƙara sugar ta jujjuya kafin ta basa tas ya shanye sai dai duk yarda yaso yaci wani abun hakan ta faskara a dole ta haƙura ta barsa ya fita.yana fitowa Kabir PA ɗinsa ya tashi tare da ƙarɓar kayan dake hannunsa suka wuce mota,Masha Allah shine na faɗa lokacin da idona ya sauka akan tanƙameman haɗɗiyan gidan lallai dukiya tayi kuka a wajen.
Zagaye tsakar parlon takeyi tare da bubbuga hannu tana huci yacce kasan tayi gasar tsere wani zazzafan huci ta sauke tace"never hakan bazai taɓa yiwuwa ba,Kamal bazan taɓa dauka ba,lallai dole kasan abunyi na gaji da ganin wannan baƙin cikin da nake kan kwasa a kullun".Aunty ta faɗa.
Ɗago kyawawan idanuwansa yayi tare da ciza lips ɗinsa da suka ɗanyi duhu kaɗan murmushi ɗauke a fuskarsa yace"duk meye na zafin kan Hajiyata?,kinsan ko me kike buƙata a kuma ko ina yake xan aiwatar maki dashi fatana dai na daina ganin ɓacin rai a kyakyawar fuskar nam taki,karkiji komai Alhaji yana dab da fita daga hanyarki,ki kuma juya komai yarda kike so,wannan alƙawarin Kamal ne ga Auntynsa".
Wani ajiyan zuciya Aunty ta sauke tana murmushi da kuma gamsuwa da kalaman Kamal tasan ko meye xai aekata ɗin tunda ya ambata.
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN KARSHE*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 6~10
Jin muryar Abba yana ƙwala mata kira yasa ta juyo da sauri tana roƙon Allah yasa baiji abunda suke faɗa ba,da matuƙar fara'a Kamal ya tashi tare da sunkuyar da kai yace"barka da fitowa Abba".
Sosai Abba yaji daɗin ganin Kamal dan sosai yake son yaron saboda yarce yake ganin natsuwarsa da kuma hankalinsa,hannu ya bashi sukayi musabaha kafin yace"Madallah Kamal ya aiki kuma?".
Nanma ƙasa kamal yayi da kansa yace"lafiya qlau Abba zaka fita ,Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya".
Shafa kan Kamal Abba yayi fuskaraa ɗauke da murmushi yace"ameen ameen Kamal."
Wani kallo Aunty kebinsu dashi ƙwafa tayi kafin tace"Abba kada kayi latti".
Juyowa yayi tare da dubanta yace"to Aunty sai na dawo".karɓar jikkar hannunsa tayi tare da rufa masa baya suka fita.
tunda lokacin tashin ɗaliban yayi kowa ke ƙoƙarin haramar fita dan ya samu yaje gida ya kawar da yunwa da kuma gajiyar dake tattare dashi wanda hakan yakan kasance ga duk wani ɗalibi hakan kuma ta faru ga Nihla wacce take kwance akan desk kamar mai bacci, kallo ɗaya zaka mata kagane tsantsar gajiyar dake tattare da ita.tsallake desk ɗin Miemie tayi tana saɓa bag ɗinta a kafaɗa tace"idan kin gama baccin kya taho ".
Tsuka Nihla taja tana kuma saɓar bag dinta tana miƙewa tabi bayan Miemie.a hankali ta soma jin zuciyarta tana mata dukan ukku ukku kamar zata daka tsalle ta fito da ƙarfi ta matse hannun Miemie dake riƙe cikin nata da maganarta mai in'i'ina tace"Mi..e..mie ina..jin wannan faduwan..ga..gaban".
Cike da tausayi Miemie ta kalleta tace"kiyi haƙuri kiyi addu'a kinji komai zai wuce soon zaki daina jin hakan".
Gyaɗa kai Nihla tayi dan a lokacin batajin zata iya furta koda kalma ɗaya ne.a haka suka ƙaraso bakin gate ɗin.kamar daga sama Miemie taji anja bag ɗinta .tun kafin ta juyo ƙamshin turarensa ya sanar mata cewa shine saboda haka ta juyo fuska a sake cike da zumuɗi ta langwaɓar da kai gefe tace"Yaya Kamal sai yanzu?,ni gaskiya nayi fushi"ta ƙare maganar tana harɗe hannayenya a ƙirji tare da juya masa baya.
Ta gabanta ya zagayo tare da kama kunnuwanaa ya ɗan duƙa ko kadan be damu da tarin ɗaliban dake kallonsu ba yace"affuwan farin cikin zuciyata wani abunne ya tsare maki mijinki da safiyar nan".
hararan wasa Nihla tawa Kamal cikin sonyin magana tace"bah..ta..haku..ra ba".
Dariya ya saka yace"in dai tiri zaki mun tab zanje na tiraki da naki gwanin IRFAN".
Jin ambatar sunan IRFAN da kamal yayi yasa aji kab ta nemi damuwarta ta rasa wani sanyayyen ajiyar zuciya ta ajiye kafin ta kalli Kamal tace"ba za..ka taɓa iya...shi.shiga tsakanin anta da ji..jini ba kamal".
Dukan wasa Miemie tayi mata tace"ƴar rainin ƙwalwa to nanma baki samu shiga ba dan tuni na daɗe da yafe masa".
"Muje na ajiyeku gida,dan yau babu wacce driver ɗinta zai zo".haka suka tafi suna fira gwanin burgewa Nihla zai fara ajiyewa dan gidansu ne farko kafin ya shiga bayan gidan wato gidan su Miemie,tunda Nihla ta shiga motar tayi shiru abunta kamar bata cikin motar kwatakwata bata cika surutuba ko dan lalurar da Allah ya daura mata wato in'i'ina takan taƙaita magana shiyasa ba kowa ya fahimci tana da in'i'na ba.
A ƙofar gate ya ajiyeta kafin sukayi banƙwana .wani iska mai tsananin ɗaɗi da daddaɗan kamshi taji yana ratsata kame jikinta tayi tana murmushi har jerarrun fararen haƙoranta suka bayyana kafin ta juya daidai inda tasan zatayi tozali da farin cikin nata,kuma cikar burinta wato Irfan.
tsaye yake fuskarsa ɗauke da murmushi kamar kullun sanye yake cikin riga da wando na ƙananan kaya wandon black jeans sai blue t-shirt an mata rubutu da zanen baƙi,wasu haɗaɗɗun safarars ne a ƙafarsa wanda suka hau har akan wandon hirami ne rataye a kafaɗarsa ga yalwataccen gashin kansa da yasha gyara iska sai busashi takeyi ,IRFAN kyakyawan namiji ne wanda ko wacce mace xata yi burin samu a matsayin miji fari ne tas irin farin ibonnan mai daukar ido yana da tsayi sosai ga faffaɗan kirji duk da ya kasance ba mai kuɗi ba amma yana da rufin asiri ga tsabar iya gayu dole idan kayi masa kallo ɗaya sai ka sake.hannuwansa zube a cikin aljihu ya fara takun zaratan maza ya ƙaraso gaban Nihla hannusa ɗaya ya zaro daga aljihu ya shafa tulin sumar kansa yana kuma tsotsar baki ,ranƙwafowa yayi tare dayiwa Nihla rumfa ya kashe ido ɗaya yace"NIHFAN yada kallo haka?,sai kin gano munina?".ya ƙare maganar murya cike da shagwaɓa.
Lumshe kyawawan idanuwanta tayi sai yanzu ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana kuma karajin soyayyar IRFAN na ratsa duka wata kafa ta jikinta kallon soyayyah take masa kafin tace"NIHFAN ɗina..ba..bashi da muni...koda akwai shi ba..bazan...taɓa gani ba kuma".
Girgiza kai yayi alamar gamsuwa da hakan yasa hannu ya karɓa bag din tata yace"muje na rakaki nasan yanzu gajiya,yunwa da kuma ƙishi sun tarunmun a kanki kuma bazan taɓa lamunta da hakan ba.kai tsaye ƙofan gate ɗin suka nufa a tare gateman ya buɗe masu suka shiga har wurin wata kyakyawar rumfa mai cike da iska da tarin furanni .ta haɗu sosai kafin su zauna ne kuma Aunty ta fito cikin shirin fita,da wani irin kallo tabi IRFAN mai wuyar fassaruwa da azabar ƙarfi zuciyarta kuma ta buga saboda yarda kyan yaron ya tafi da ita .ganin kallon da Aunty kebin Irfan dashi yasa NIHLA cewa "AUNTY fi...ta za..zakiyi ne?".firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula cikin son kawar da tunanin da takeyi tace"eh Nihla amma bazan jima ba,waye wannan?".
ƙasa NIHLA tayi da kai cikin jin kunya tace"AUNTY Ya..ya IRFAN ..ne".
Ɗan duƙawa Irfan yayi tare da cewa"barka da fitowa Aunty,ina wuni".
"lafiya qlau Irfan yaudai Allah yayi zan ganka,ku shiga daga ciki mana zakibar baƙo a waje haba NIHLA".
murmushi tayiwa Auntyn suka mata sai ta dawo kafin suka wuce ciki.tafiya Aunty keyi tana kuma waigen IRFAN harda tuntuɓe.wani irin sanyin ɗaɗi ya kamata tana ganin matsowar cikar burinta tabbas IRFAN shine irin namijin data daɗe tana mafarki ta yaya tana xaune har Nihla ta samu irin wannan guy ɗin?tayiwa kanta tambayar da bata da ansa.dariya ta saki kafin tace"lallai dole na baxa komata na kuma raba ƙafa duk kuma wanda yake niyar hanani FARAUTAR FARIN CIKINA to tabbas ba tantama zan kawar dashi,ka saurareni muradina IRFAN!".
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 11~15
Hannu yasa tare da shafa kansa yanajin matsananciyar gajiya a tattare dashi shigowarsa asibiti kenan yau kam bayajin zai iya aikata komai zagen companies ɗinsu yaje jin wayarsa na ringing yasa ya mayar da kallonsa gareta AMMI shine sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar fesar da iska yayi kafin ya ɗauki wayan bakinsa ɗauke da sallama.
Daga ɗayan ɓangaren AMMI tace"Muh'd kana jina?".
Lumshe kyawawan idanuwansa yayi tare da ciza laɓɓansa yace"na'am Ammi".
"duk abunda kakeyi ka bari kazo gida,Hajiya Kaka tana nemanka kasan kuma idan ka daɗe meye zai iya faruwa"cewar Ammi.
Damm damm haka zuciyarsa ta buga da ƙarfi yanajin kamar zuciyarsa zata fasa ƙirjinsa ta fito waje kasa furta komai yayi kashe wayan yayi tare da miƙewa tsaye ya tattara abubuwan buƙatarsa ya fito ganin Kabir ya taso ne yasa ya ɗaga masa hannu kawai tare da wucewa.a gurguje yaja motar kai tsaye ya nufi unguwar Nasarawa bai wani daɗe a hanya ba kasancewar babu nisa a tsakanin hospital ɗin nasa da kuma gidansu.horn yakeyi kamar zai huda kunnuwan mutane da gudu Idi mai gadi yazo ya buɗe masa gate ɗin yana kuma masa sannu da zuwa.ko kallonsa beyi ba hakan yasa Idi saurin ja da baya yana tunanin komai ya samu ZAFAR duk da yasan bashi da yawan fara'a amma yana da son mutane da kuma haba-haba dasu.
Ko gama daidaita parking beyi ba ya fito da sauri tare da nufar tanƙamemiyar main entarance na gidan ,cikin takun ƙasaita ya ƙarasa cikin babban parlon gidan tsaye ya tsaya tare da riƙe ƙugu yana kuma juya brown eyesball's ɗinsa da suka soma tara ruwa sama sama suka ƙara haske.kanshi ya ɗaga yana kallon stairs ɗin ganin AMMI na safkowa yasa ya kawar da kansa dan bejin ayau zai iya sauraran hakurin da AMMI zata bashi.jin muryar Hajiya kaka a bayan Ammi yasa ya ɗago tare da ƙura mata ido.
har gaban ZAFAR Hajiya kaka ta ƙaraso .Hajiya Kaka macace bamai haske ba sosai tana da kyau daka ganta zakasan irin gogaggun matan nanne da suka sha zaman duniya .Fuskarta dauke da murmushi kafin cikin iko da gadara tace"ZAFAR ga ƴar aminiyata nan a part ɗina sunanta Aysha bana son wata magana ko jin ƙorafi kaje ka ganta na gama maganar aurenku da iyayenta,sannan ina so ka sani wannan karon ba wasa nake ba.
Wani irin kallo marar fassaruwa Zafar yabi Hajiya kaka dashi,numfashi yaja tare da shafa tattausan gashin kansa murmushi ya saki tare da cewa"ko a zamanin da tsohuwa anbar hakan,balle a wannan zamanin,ina maki gargaɗin daina yomun rakice-rakice wai na aura ni Zafar bana da lokacin mace ma bare kuma harna tsaya kallon xaɓinki".
"Da uwarka Maryam kake gata nan tana jinka,to ko ibanka AL-AMEEN yayi kaɗan nasa doka ya karya balle kai karan kaɗa miya ba'a karyamun doka, ba kuma za'a fara a kanka ba Zafar dole kabi abunda nake so".Hajiya kaka ta ƙare magana tana huci.
Lumshe idanuwansa yayi tare da waresu akan Hajiya kaka "idan kin tashi ki daina sakamun mahaifiya a ciki,ki sani a yanzu bazan iya ɗaukar wani cin zarafi a kanta ba,shi kuma ae Ɗanki ne dole yabi abunda kike....."
"ZAFAR" da masifar ƙarfi Hajiya kaka ta kare kiran sunan tana huci,nuna shi tayi da yatsa tace"nasan uwarka ce ke gaya maka duk wannan to ina so ka sani ita kanta a ƙarƙashin ikona take bata da wani zaɓin daya wuce yimun biyayyah".
Buɗe baki Zafar yayi da niyar ƙara yin magana AMMI tayi saurin shiga tsakiyarsu tace"Muhammad kada na sake jin bakinka a wurin nan".
Juyowa tayi tana maida kallonta akan Hajiya Kaka tare da haɗa hannuwanta biyu tace"kiyi haƙuri Mama insha Allah zaiyi biyayyah akan zaɓinki".
Da wani irin kallon mamaki Zafar yabi Ammi dashi kamar ƙwalwar kansa zata fashe haka yake ji bakinsa na rawa"not at this stage Ammi,bazan sadaukar da rayuwata akan wannan ba,bazata taɓa samun abunda take so ba never".
Kallon Ammi Hajiya kaka tayi tace"kisan yarda zakiyi".bata jira cewarsu ba tayi hanyar part ɗinta kamar zata tashi sama.
"Zafar meyasa kakeyin hakan?ko ba komai Kaka itace mahaifiyar Abbanka ya kamata ka mata biyayyah kodon darajar haifar Abbanka da tayi".
Matsowa yayi tare da kama hannuwan Ammi yana kallonta yace"akan komai Ammina amma banda akan ƙuntata maki da kuma akan rayuwata,dan Allah kada kisa kanki a cikin lamarin dazan kasa maki biyayyah".
Shiru Ammi tayi tama rasa abun cewa kafin tace"kaidai kayi addu'a,muhammad bana son rigimar nan dan Allah".
Kai kawai ya iya gyaɗawa kafin ya zare hannuwansa daga na Ammi ya wuce sama.Ammi kam zamewa tayi akan chair ta zauna tare da dafe kanta dake barazanar tarwatsewa tana zancen xuci!shin sai yaushe farin ciki zai wanzu a rayuwarsu ada tasha wahala da ƙalubale kala-kala yanzu kuma akan yaranta?innalillahi wa'ina ilaihir raju'un shine abunda Ammi take maimaitawa harta samu taji saukin nauyin abunda ya danne mata zuciya.
tunda Aunty ta fita wuri ta samu ta laɓe a mota tana jiran tsammani kamar daga sama ta hango IRFAN yana fitowa daga cikin gida,wani irin murmushin nasara ta saki take daɗi da kuma annashuwa suka lulluɓe duka jikinta a hankali ta taka mota tabi bayan IRFAN sai da taga yayi nisa da gidan babu mai hangosa sannan tayi saurin shan gabansa da mota.soma rage glass ɗin motar tayi,tsaye cak IRFAN ya tsaya yana so yaga waye wannan ya tsayar dashi,ganin Aunty ce yasa yayi ƙasa da kansa kafin yace komai ta fito daga mota fuskarta ɗauke da murmushi tace"sannu dai IRFAN ka fito?".
Shima murmushin ya mayar mata yace"eh Aunty sannu da dawowa".
Lumshe ido tayi cike dajin daɗi tace"eh IRFAN muje na saukeka naga akwai rana".
"a'a Aunty na gode sosai zan ƙarasa"ya bata ansa.
"bana son gardama Irfan kamar dai baka yarda dani bane,to kaga tunda ni ke baka son bi ga key ka tafi in yaso anjima da dare ka dawo da ita ,idan kuma kana da abubuwan yi ka iya barin motar a wajenka".bata jira cewarsa ba ta ajiye masa key ɗin tayi gaba abunta.
Sake da baki haka Irfan yabi Aunty da kallo kasa cewa komai yayi a dole ya shiga motan ya wuce gida da ita,sam a ransa be kawo komai ba.
Zaune a dining Aunty ta samu NIHLA chocolate's ne kala-kala gabanta tana sha.jin maganar Aunty saya Nihla juyowa da sauri tana ɓoye chocolate ɗin dake hannunta.
Matsowa kusa da ita Aunty tayi tare dajan kunnenta ta tasheta tsaye tace"watau da kikaga ba kowa gidan shine zaki zauna ki soma shan zaƙi haka Nihla?kinsan matsalarki fa,kin dawo scul da kici abinci sai ki ƙare akan zaƙi ?idan bakya son kanki mu muna san lafiyarki".
Kama kunnuwa Nihla tayi da alamun ɓata fuska kamar zata saki kuka tace"I'm sorry Aunty bazan sake ba.kiyi haƙuri dan Allah karki gayawa gawa Daddy".ta ƙare maganar tana faɗawa jikin Aunty.
hannu biyu Aunty tasa tare da rungume Nihla a jikinta tana kuma sakin murmushii mai wuyar fasaruwa bare kuma gane in da ya dosa,a fiki kuma tace"that's mah gal,Allah yayi maki albarka".
Da ameen Abba ya ansa yana kuma ƙarasa isowa in da suke cike da so da ƙauna yake kallonsu shafa kan Nihla yayi yana kuma kallon Aunty yace"haƙiƙa Fatima ke macace ta gari kuma ta kirki ina rokon Allah ya cike rayuwarki da dukkan haske ya kuma dubeki yarda kika dubi marainiyar ƴata kika riƙeta da kyau tare da bata tarbiya ta gari,irinki a cikin mata kaɗanne Fatima