ka gani zaka ɗauka latsar wayarsa kawai yakeyi, aduk lokacin da kuma ya gaji da kallonsa a wayarsa sai ya goge cike da jin haushin kansa.
Bai fito ɗakin ba har sai da aka kira sallar la'asar, lokacin har Madiyam da Hisham sun fita don tun ƙarfe uku ake zuwa islamiyar, arwala ya farayi sannan ya wuce masallaci, bayan ya dawo ya zauna tsakar gidan yana danna wayarsa, lokaci kaɗan kuma yana yi yana ɗago kansa yana kallon ƙofar ɗakin Mahmah, so yakeyi ya tambayi Mahmah ina Haisam don ya san dole Madiyam ta yi makaranta tunda lokacin zuwa islamiyarsu ya yi har ya wuce amma ya kasa, kallonsa Mahmah ta yi haɗe da cewa,
"Wani abu kake nema Hisham?"
"A'a Mahmah". Ya faɗa haɗe da miƙewa ya koma cikin ɗakinsa, wayar Haisam ya kira har kusan sau uku bai ɗaga ba, hakan ya sa ya sake fitowa yana faɗin,
"Mahmah Haisam fa?"
"Ya fita tare da Madiyam wai zai rakata islamiya".
"Ok" ya faɗa tare da komawa cikin ɗakin ya yi zaune gefen katifar tasa yana ci gaba da latsar wayarsa, ji ya yi bazai iya ci gaba da zaman ba, don haka ya tashi ya fice daga ɗakin haɗe da jawo ƙofar ya fice daga gidan gaba ɗaya, tsintar kansa ya yi da bin hanyar makarantar tasu yana tambayar kansa me yasa ma tun farko baya rakota zuwa islamiyar, gashi yanzu lokaci ɗaya Haisam ya tsiri rakata, wanda hakan zai sa Ammie taga rashin kulawarsa agareta ta wannan fannin, tsaki ya yi tare da ja ya tsaya yana jin haushin kansa, don yanzu idan ya tsiri yin hakan za a ga kamar don Haisam ya yi ne shiyasa shima ya yi, da wannan tunanin ya juya ya koma ƙofar gida ya yi zaunensa, ya yi tsaki tsaki ya fi a ƙirga cike da jin haushin Madiyam ɗin, don a cewarsa ita ta ba Haisam damar hakan amma shi daidai da rana ɗaya bata taɓa nuna masa tana so ya rakata ba, da wannan marece ya yi masa a wajen har aka taddo su Madiyam a islamiya, tunda ya hangota ta doso ƙofar gidan ya ƙura mata idanuwa har ta ƙaraso, kauda kansa ya yi haɗe dayin tsaki ya miƙe ya wuce cikin gida.
A jiyar zuciya Madiyam ta sauke ganin yabar ƙofar gidan don tunda ta hangosa gabanta ke faɗuwa, tana shiga cikin gida ta ji muryarsa yana faɗin, "kizo ki gyara mun ɗakina". Ya ƙare zancen tare da ƙarasawa cikin ɗakin, turo baki ta yi haɗe da cewa,
"Na rantse bazan zo ba, kawai daga dawowar mutum sai a tsiri sakasa aiki".
"To marar kunya, yi niya ya jiki".
"ALLAH Mahmah ni na gaji bazan gyara ba sai dai ya kashe.." kafin ta ƙarasa Mahmah tayo kanta tana faɗin,
"Zaki ajiye ki tafine ko sai na saɓa maki rai, wai ke wace irin yarinya ce haka? Shiyasa sam bana tausayinki tunda ke marar kunya ce, zaki wuce ne ko sai na saɓa maki".
"Mahmah.." ganin ta yo kanta ya sa tayi saurin shigewa ɗaki ta ajiye jakar ta nufi ɗakinsa tana ƙunƙuni, zaune ta iskesa saman doguwar kujerar dake gefe cikin ɗakin ta ɗage labulen ƙofar saboda kar yaci zalinta idan yana hango Mahmah na ka'ida kawo a tsakar gidan,
"Fitarmun ɗaki kuma ki sake mun labule tunda ke ba musulmai bace, in yaso duk randa kika zama musulma sai ki shigo ki gyara".
Sanin inda ya dosa da kuma idan ta tafiyarta me hakan zai haifar mata ya sa bayan ta saki labulen ta yi sallama a bakin ƙofar ɗakin haɗe da cewa, "in shigo?"
Can cikiciki ya amsa sallamar haɗe da cewa, "zaki iya". Ba wani datti ne a ɗakin ba kawai rashin son zama lafiya ne ya sa shi sata gyaran ɗakin tare da son ƙare mata magana, yana kallonta ta fara cire bedsheet ɗin katifar haɗe da kakkaɓeshi sannan ta sake shimfiɗasa da kyau ta gyara filallan ta aza, tana ƙoƙarin shiga toilet ta wanke masa ta ji ya ce,
"Beyi ba".
Juyowa ta yi.ta kalli katifar sannan ta kallesa haɗe da cewa, "meye?"
"Miya" ya bata amsa yana kallon katifar, hakan ya sa ta sake sauke filallan ta sake gyara zanen gadon da kyau sannan ta maida pillows ɗin ta aza, tun kan ta cire hannunta ya sake cewa,
"Bai yi ba shima" ba tare daya ɗago kansa ba a wannan karon, tsaye ta yi tana turo baki haɗe da cewa "to ya zanyi ya Hisham? Ni haka na iya".
"Kina macce baki san yanda zaki gyara common gado ba balle ɗaki, amma kin iya fita anguwa tare da namiji kowa na kallonki, sai kace ba ƴar Fulani ba da aka sani da kunya, fitar mun ɗauki ni na gyara abuna". Ya ƙare zancen tare da ficewa ya bar ɗakin jin ankira sallar magrib, kallon yanda ta luluye katifar ta yi amma don tsabar ganin laifi wai yace bata yi ba, to ya yake so tayi? Ta tambayi kanta haɗe da cewa, "kar ALLAH yasa yayi" ta faɗa a fili tare da haye katifar ta dinga juyi akai har saida ta turmuju zanen gadon tas, kamar ance ta juyo ta gansa tsaye ya zaro idanuwa yana kallon ikon ALLAH, sumui sumai ta miƙe haɗe da raɓawa ta gefensa zata wuce, fizgo hannunta ya yi tare da cewa, "idan na dawo yana haka saina ɓallaki biyu tunda ke marar kunya ce" ya ƙare zancen tare da tura ƙeyarsa sannan ya wuce masallaci, tafe yake yana murmushi haɗe da dariyar yanda ya iskota tana birgima akan gadon har ya kai masallacin, acan ya tadda Abbu da Haisam suma sun dawo sun tsaya yin sallah, tare suka bi jam'i suka gama aka kira sallar isha itama suka yi sannan suka shigo gida tare, abinci suka fara ci sannan Haisam ya je ya buɗe mota ya ɗauko saƙon Hisham dana Mahmah daya manta dashi tare da abunda ya koma ya siyowa Madiyam lokacin da zai zo, saƙon Mahmah ya fara bata sannan ya miƙawa Hisham nashi, kallon Madiyam data takure waje ɗaya ya yi haɗe da cewa, "cutie rufe idanuwanki kema na baki naki sauƙin." Murmushi ta saki tare dasa hannuwa ta rufe fuskarta, wata ƙatuwar tedi fara tas da takusa rabin girmanta ya ɗauko a ƙofar ɗaki daya ajiye haɗe da cewa, "oya to buɗe idanuwanki" ya saita tedin a daidai fuskarta yana dariya, waro idanuwa ta yi haɗe da cewa, "wowwww ya Haisam kamar kasan ina son Baby". Ta ƙare maganar tare da rufe bakinta saboda tsabar farinciki, dariya Mahmah da Abbu suma sukayi ganin yanda ta karɓi tedin ta wani sa a jikinta ta rungume tana faɗin, "Na godiya ya Haisam, babyn so cute". tana wani tattaɓa fuskar tedin,
"Yes she's so cute like you cutie, ta yi maki ko?"
"Sosai ya Haisam ina sonta".
"Ahh..to nifa?" Ya faɗa shaye da toka yana harararta irin da wasa ɗin nan, dariya ta saki haɗe da cewa,
"Kai ma ina sonka ya Haisam sosai"..
Wani irin tsaki Hisham ya ja cike da takaici yabar ɗakin, shiyasa sam baya son wani lokacin Haisam na zuwa don gabaɗaya shi ke ida lalata Madiyam, fisabilillahi yanzu meye na siyo mata wata tedi sai kace ƙaramar yarinya, wannan ai salon ya hanata karatu ne kawai ya sa ya siyo mata ita, ya dinga faɗa shi kaɗai cikin ɗaki haɗe da cilla saƙon da Dady ya aiko masa dashi saman katifar zuciyarsa cike da takaici ba tare daya duba ba.
*FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
Last Free page 12
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
*Alhamdulillah munzo ƙarshen free pages, FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode.
______________________________
A haka Hisham ya shigo ɗakin ya taddashi yan faman kai da kawo haɗe da suruttan da shi kansa ma baisan dalilin yin su ba, kallonsa ya yi cike da tuhuma kafin yace, "Wai lafiya kake Hisham? ko ka manta matsayin da Abbu da Mahmah ke dashi a wajenmu ne? Yanzu ka faɗa mun, me akayi najin haushi awajen da zakayi masu tsaki ka fito?"
"Look ya Haisam, bana son takurawa da damuwa, kaje ka ƙare abunda kake yi sai ka dawo muyi magana, amma ina so ka sani, ni ba Mahmah da Abbu nake yiwa tsaki ba.."
"Oh kenan Ni kake yiwa ko?"
"Akan me zanyi maka tsaki ya Haisam? Saboda bana da abunyi?"
"Yes upcouse, tunda har baza ka iya ɗauke idanuwanka ga abubuwan da nake yiwa Madiyam ba dake saka ka jin haushi to tabbas ba kada abun yi".
"Ok haka kake zato?"
"Eh haka ɗin ne Hisham, ni na rasa me yasa ka ɗauki karan tsana ka ɗorawa yarinyar can, gabaɗaya sam baka ƙaunar farincikinta da walwalarta.." Haisam ya faɗa rai a ɓace yana ware hannuwansa, cikin sanyin murya mai cike da ɓacin rai shima Hisham ya ce,
"Ok, shikenan na ji, kai da kake son farinciki da walwalarta sai kaje ka ci gaba da bata, in yaso ka maidata ciki idan zaka iya". Ya ƙare zancen tare da ɗaukar wayarsa da makullin motar da Haisam ya zo da ita dake ajiye kan gado ya bar ɗakin ransa a ɓace,
Bayansa Haisam ya bi yana kiran sunansa ya yi banza dashi haɗe da buɗe motar da ƙarfi fizga ya bar ƙofar gidan, tsaye Haisam ya yi riƙe da kunkuru kafin ya koma cikin gidan, tsaitsaye ya tadda su Mahmah a tsakar gidan jin ƙarar yanda Hisham ya tada motar haɗe da sunansa da Haisam ke kira ya ƙi saurararsa.
"Lafiya Haisam? Me ke faruwa tsakaninku?" Abbu ya tambaya yana riƙo hannunsa, murmushi ya saki haɗe da cewa,
"Ba komai Abbu, ku ƙyalesa haka yake da baƙar zuciya akan ɗan abunda bai kai ya kawo ba, ya tafi duk inda zai je ALLAH ya kiyaye".
"A'a Haisam kada kace haka, baka ji yanda ya tada motar ba ne?"
"Ba abunda zai faru Mahmah ina sha ALLAH, kuje ku kwanta ni zan jira dawowarsa".
"ALLAH ya kyauta" Abbu ya faɗa tare da komawa ciki, don idan har zai ce bai ji zafin abunda Hisham ɗin ya yi ɗazu ba, to ya yi ƙarya, Mahmah kuwa kallon Haisam ta yi haɗe da cewa,
"Ya kamata kai da Abbu ku fahimci Hisham da kyau, abubuwan da kukewa yarinyar nan ne dake shagwaɓata suna sakata sakalci ne baya so, sai yake ganin kamar yana tubƙa ne kuna walwala, kana gani dai da idanuwanka, in ba shi ba babu wanda Madiyam ke tsoro agidan nan, ga rashin ji da rashin kunya tab cike da cikinta, kuma idan muna da rayuwa gidan wani zata je bai kamata abarta tana cigaba da rayuwarta haka ba..."
"Haba Mahmah! Me yasa kullum kike goyon bayan abubuwan da Hisham ke yiwa Madiyam, shin ita ba ƴa bace da baza a barta tayi rayuwarta yanda take so ba? Wannan takurawar da Hisham keyi mata tayi yawa wlh"
"Na sani Haisam, amma duka yana yi ne don tasan ciwon kanta da kuma gyaran gobenta, ka ga kuwa bai dace a hanasa ba tunda ɗan uwanta ne".
"Koma dai meye abun nashi ya yi yawa Mahmah, shi kansa yana buƙatar a gyara masa saitin rayuwa saboda a wani baibai yake tafiyar da tasa, sai kuma yace yanda rayuwarsa take haka yake buƙatar wasu suyi tasu? Bazai yuyu ba kawai ku ƙyaleni dashi". Ya ƙare zancen tare da koma wa wajen ya zauna, tun suna dubin dawowar Hisham har ƙarfe sha biyu ta wuce bashi ba labarinsa, abun da ya matuƙar tayar wa da Mahmah hankali kenan, don ko ƙarfe takwas da rabi na dare nayi Hisham na dawowa gida, bai taɓa kaiwa ko ƙarfe goma a waje ba inba abokinsa Ashafaq ya zo ba ya je yi masa rakiya, gabaɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye akan rashin dawowarsa haka ma bacci ya gagara ɗaukarta saboda rashin sanin halin da yake ciki, har ga ALLAH tana jin wata irin soyayya da ƙaunar Hisham a ranta da baza ta taɓa iya jurewa wani abun ya samesa ba.
A ɓangaren Hisham kuwa yana fizgar motar bai tsaya ko ina ba sai can bayan gari, ba tare daya damu da dare bane ya yi parking motar haɗa da fitowa ya samu waje ya zauna, ba by abunda yake buƙata a yanzu sama daya ganesa shi kaɗai, shi yasa ya baro gidan ya dawo nan ya zauna saman wani dutsi ko zai samu natsuwar zuciya, don yanzu haka wani irin zafi take yi masa tamkar zata huda ƙirjinsa ta fito, ya fi ƙarfin mintuna goma sha biyar a haka kafin ya miƙe ya sake komawa cikin motar, nan ma wasu mintuna biyar ya sake kwashewa kansa na jingine ajikin kujerarar motar daya zauna kafin ya tayar da motar ya yi gaba, gidansu Ashfaq ya nufa don dare bai wani yi sosai ba ya tadda shi ƙofar gida tare da wasu abokanansa suna fira, motar ya yi parking ya fito haɗe da wuce ta gabansu ba tare da ya ce dasu uffan ba ya wuce tsaye cikin ɗakin na Ashfaq daya gani a buɗe don dama a ƙofar gida ɗakin nasa yake, kallo ɗaya Ashafaq ya yi masa ya girgiza kai tare da maido hankalinsa wurin abokanan nasa suka ci gaba da fira, ɗaya daga cikinsu ne ya ce,
"Mtsss..ni fa gaskiya bana son gayen can Ashfaq saboda girman kansa ya yi yawa". Ya faɗa a hasale haɗe da miƙewa tsaye cikin ɓaci rai, "wallahi ka riga ni faɗa ne kawai Jamil, amma nima sam bana son shi, mutum sai kace ya fi kowa kana ganin mutane amma baza ka iya yi masu magana ba sai dai ka raɓa su ka wuce kana wani cin magani, ko da yake ba laifinsa bane, laifin ka ne Ashafaq da ya ga kana kula shi, shi yasa har yake yiwa mutane wannan faɗin ran tsiya".
"Look Khalid, Jamil kuyi haƙuri, kunsan kowa da irin rayuwarsa, ba wulaƙanci ne Hisham keyi maku ba, kawai haka rayuwarsa take, kuma kunsan baza mu iya sauya masa ita ba". Ya ƙare zancen tare da kallon Khalid da Jamil dake tsaitsaye cikin ɓacin rai, tsaki Jamil ya ja haɗe da cewa, "Dallah gafara, ko haka rayuwarsa take ai ya yi wa mutane sallama idan har bazai iya tsayawa a gaisa ba, kai dake iya wa da halinsa sai kaje can kayi ta haƙuri dashi, Khalid wuce muje". ya faɗa tare da taɓa Khalid suka bar wajen, shiru Ashafaq ya yi haɗe da duba agogon wayarsa yaga ƙarfe goma da rabi na dare, ajiyar zuciya ya saki tare da juyawa ya shiga cikin ɗakin, kwance ya isko shi idanuwansa a rufe ya ɗora hannunsa ɗaya a saman goshinsa ɗaya kuma akan ƙirji tamkar mai bacci, gefen ƙafafuwansa ya zauna tare da kallonsa ya ce,
"Hisham lafiya? Me yake faruwa?". Kusan mintuna biyar ya kwashe yana yi masa magana amma ya yi banza dashi hakan ya sa ya miƙe ya shigewarsa cikin gida don inda sabo ya saba da irin wannan murɗaɗɗiyar halayyar ta Hisham dake bala'in wahalar dashi, musamman akan Madiyam daya yi ta ƙoƙarin fahimtar dashi amma yaƙi fahimta, shi yasa wasu lokutan yake fita batunsa ya saka masa idanuwa, yasan duk ranar da giɗa ta ji gashi ita za tayi ɗaɗo da kanta.
Har ƙarfe sha biyu ta buge Hisham na kwance a wajen bai ce dashi ko uffan ba shi ma kuma bai sake bi takansa ba ya ci gaba da yin abunda ke gabansa, ganin yana shire-shiren kwantawa ya sa Hisham miƙewa yana faɗin, "Sai da safe" ya amsa masa da "mu tashi lafiya tare dayin tsaye bakin ƙofar ɗakin nasa yana kallonsa har ya shiga motar ya tayar ya bar ƙofar gidan sannan shima ya shige ɗakinsa ya rufe ya kwanta yana jinjina zurfin ciki irin na Hisham.
Ganin hasken mota ya nufi wajen ya sa Haisam dake zaune yan latsar wayarsa ya koma cikin gida, "Mahmah to kije ki kwanta ga ɗan renin wayon nan ya dawo" Haisam ya faɗa ganin Mahmah zaune saman bencin dake tsakar gidan ta rafka tagumi lokaci ɗaya kuma tana faman gyangyaɗi.
Bata bar tsakar gidan ba sai da ta ji shigowar Hisham tare da rufe gidan, duk da haka tsaye ta yi har sai daya ƙaraso, ganinta zaune a saman bencin ta zubo masa idanuwa ya sa shi jin ba daɗi haɗe da rashin kyautawarsa, wajenta ya ƙarasa ya zauna kusa da ita haɗe da cewa, "Mahmah baki kwanta ba.." kafin ya ƙarasa ta ɗaya hannu kamar zata maresa ta ce "yimun shiru, taya kake tunanin zan iya kwantawa a yanayin da naji kafita gidan nan, taya kake tunanin bacci zai ɗauke ni awannan yanayin da ka fita ba tare da nasan wane hali kake ciki ba?"
"Kiyi haƙuri Mahmah muje ki kwanta". Ya faɗa tare da riƙata har cikin ɗaki ta zauna a gefen gado, hannunsa ta kamo shima ta zaunar dashi tare da tallabo fuskarta suna kallon juna ta ce,
"Hisham, idan akwai abunda ke damunka ka sanar dani, bana son ganinka cikin irin wannan yanayin da kuma saurin fushin da kake yawan yi, hakan baya mani daɗi sai naji kamar na gaza wajen baka irin kulawar daya kamata ace kowace uwa na bawa ɗanta, a ko yaushe ina yimaka kallon wani haske kuma alkhairi a tare damu, shi yasa bazan iya jurewa ganinka cikin ko ƴar ƙanƙanuwar damuwa bace".
"Kiyi haƙuri Mahmah, in sha ALLAH zan dena, nima bnsan me yasa nake tsintar kaina cikin ire-iren wannan fushin ba, amma zanyi ƙoƙarin nisanta kaina daga abubuwan dake haifar mani dashi".
"Ka tabbata?".
"In sha ALLAH Mahmah". Ya faɗa haɗe da ɗora hannunsa a saman nata dake kan fuskarsa yana sakar mata murmushi, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta gyara kwanciyarta tana faɗin, "ka ja mun ɗakin idan ka fita, sai da safe".
"To" ya faɗa haɗe da juyawa ya kalli Madiyam dake kwance ƙwaƙume da tedinta tana baccinta hankali kwance, ji yakeyi kamar ya fincike tedin daga jikinta ya je ya ƙona amma ya san yin hakan babban kuskurene, don ko shi aka yiwa haka sai ya ji zafi sosai, tsaki ya ɗan ja cike da jin haushin kansa ya kashe wutar ɗakin sannan ya fice haɗe da rufo masu ƙofar, ajiyar zuciya Mahmah ta sauke haɗe da gyara kwanciyarta don tana kallon duka mintunan daya kwashe tsaye a wajen yana kallon Madiyam kafin yabar ɗakin.
Ko daya shiga ɗakinsa kuwa ya tadda Haisam har ya yi kwanciyarsa akan gadon bacci ya soma ɗaukar sa, ba tare daya bi takansa ba shima ya ɗauko pillow ya jefa kan doguwar kujerar dake ɗakin shima ya yi kwanciyar sa, baccin da gabaɗaya rabi da rabi ya riƙa zo masa tsabar tunani har sai da aka kusa kiran sallar asuba sannan ya ɗaukesa.
A ɓangaren Najlah kuwa tana shiga gidan Ammie da ta ji tana waya da Haisam akan idan bai taso ba ya bari sai gobe ya dawo ta ji wani irin zazzaɓi da kishi sun taso mata lokaci ɗaya, kasa ɓoye hakan ta yi har sai da ta ce, "Ammie saboda me zaki ce ya kwana acan, ai ƙwanda ya dawo gida tunda kinga Abbie baya nan".
"A'a Najlah, hanyoyin nan basu da kyau kema kin sani, ALLAH ya kare ba fata ba idan yace ya kamo hanyar nan yanzu ya taho kafin ya iso dare ya yi, kuma zai iya haɗuwa da miyagun mutanen nan da idan har basu kashe mutum ba za su iya garkuwa dashi, to wahala ake gudu ba abunda zasu tambaya ba shiyasa na ce yayi zamanninsa sai gobe kin fahimta".
"Kuma Ammie a gidansu Madiyam zai kwana".
"Eh mana, banda abunki Najlah yana da wani waje ne a can wanda ya fi masa gidansu?"
"Hotel mana Ammie, ba sai yaje can ya kwana ba da safe sai ya dawo". Zaro idanuwa Ammie ta yi haɗe dayin dariya kafin tace,
"Hotel kuma Najlah, ga gidan baffan nasa inda ɗan uwansa yake zai wani je hotel ya kwanta, ai bazai yuyu ba".
Kallonta Ailat dake zaune tana kallo ta yi haɗe da cewa, "Tab..ai aunty Najlah babu hotel a Giwa, kuma ALLAH NI gani nakeyi ɗan iska kawai ke kwana a hotel, sai kuma dole idan ta kama, ai ƙwanda ya yi kwanciyarsa a gidan Abbu wlh, babu wata takura kuma zai ma fi sakewa acan sosai bisa ga hotel.."
"Dalla rufa mana baki, to waya tambayeki ne?" Ta kwatse Ailat ranta a ɓace sannan ta miƙe tana yiwa Ammie sai anjima ta bar gidan.
Dariya Ailat ta saki haɗe da cewa, "Kai! Wlh aunty Najlah akwai kishi, don fa Madiyam ta daɗi hakan Ammie".
"Ina ruwan Najlah, ai akwai aiki gaskiya don matuƙar akayi auren nan nasu da Haisam to fa daƙyar in zata amince ya auri Madiyam, gashi Abbie ya ce sunyi magana da Dady idan ya dawo daga Abuja za a tsaida maganar aurensu".
"Amma Ammie kina gganin ya dace haka? Wlh da gaske ya Haisam keyi yana son Madiyam sosai"
"Na sani Ailat, itama Najlah ɗin zai so ta tunda akwai shaƙuwa da fahimtar juna tsakaninsu, sannan baza mu ci gaba da zuba masa idanuwa haka ba aure ba, kuma daya je ya ɗauko mana bare ai ƙara Najlah ɗin, in yaso daga baya sai ayi maganar Madiyam idan tana sonsa, tunda itama ba a san ra a yinta akan shi ba".
"To ALLAH ya sanya alkhairi, wlh ina son ya Haisam ya auri Madiyam saboda ba kaɗan yake sonta ba".
"Ai abun farin ciki ne idan ya aureta don sake ƙarfafa zumunci ne haka".
Dariya Ailat ta yi haɗe da cewa, "oh ya Hisham, shi kuma ko sai yaushe zai zaɓo matar da zai aura? ALLAH ba don basu shiri da Madiyam ba da ma shiya aureta don sunfi dacewa".
"Kar ki bari ya ji wannan zancen, in ba haka ba zaku ɓata dashi".
"Na sani Ammie, amma dai baisan ya Haisam na sonta ba ko?"
"Zai sani ne tunda kinsan halin Haisam bai iya ɓoye abuba a ransa, inda dai shine to bazai bari kowa ma ya ji ba balle shi".
"Aikuwa, to ALLAH ya bashi ta gari shima".
"Amin ya ALLAH, kema ALLAH ya baki na gari"
"Amin Ammie, amma fa ya Nau..." Sai kuma ta kasa ƙarasawa haɗe da miƙewa ta bar wajen cike da jin kunya, don tuni sun jone da ya Naufal ba tare da kowa ya sani ba sai yanzun da ta yi suɓul da baka, da idanuwa Ammie ta bita haɗe da cewa, "Tooo... Kunji yaran zamani, wato suna can suna sha'aninsu bamu sani ba, kinga ikon ALLAH, to ALLAH ya tabbatar mana da alkhairi". Ta ƙare zancen cike da jin daɗi da farinciki a ranta, don kuwa ta yaba da hankalin Naufal dashi har mahaifiyarsa, ta kuma tabbata ba ƙaramin farinciki ƴarta zata samu ba idan ta auresa, fata dai kawai ALLAH ya sanya alkhairi a cikin lamarin.
*****. *****. *****
Kamar yanda Hisham ya saba ako yaushe idan ya yi sallar asuba bai fiye komawa bacci ba, yakan littafansa ne ya duba ko kuma ya hau karatun ƙur'ani har safiya ta fara wayewa, yauma haka, text books ɗinsa ya ɗauko ya ɗan dudduba topic ɗin da zai yiwa ɗalibbansa sannan ya miƙe ya faɗa toilet yayo wanka, zaune ya samu Haisam shima ya tashi baccin daya koma bayan sallar asuba, "Morning brother". Ya faɗa a daƙile yana goge kansa da ɗan ƙaramin towel daya fito riƙe dashi, "morning Hisham, ka tashi lafiya".
"Fine" ya bashi amsa a taƙaice tare da rataye towel ɗin ajikin ƙofar shiga toilet sannan