Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
dining dashi yana faɗin, "Ammiensu zo ki zuba mana abinci muci, ina so mu sakaya nida yarona idan mun gama" ya jawo masa ɗaya daga cikin kujerun dining table ɗin ya zaunar dashi, yanda yaga ya sha toka ya sashi yin dariya tare da cewa, "menene yarona?" "Abba ƙarya fa Ailat keyi, ni Madiyam nake so gaskiya ba Najlah ba" "Common..Madiyam kace fa? Yarinyar dako Ailat ta fita girma, yaushe zaka tsaya zaman jiranta? ka dai san ko way Abbu, bazai taɓa aurar da ita ba yanzu ko ana maza ha mata". "Abbie to ba saina jirata ba har lokacin da Abbu zai shirya aura da ita, nidai gaskiya ita nake so". Ya ƙare zancen yana tura plate ɗin gabansa, zaro idanuwa Abbie ya yi yana maido masa da plate ɗin agabansa haɗe da cewa, "To meye na ture plate ɗin? Ai abun bai kai can ba, indai kwantar da hankalinka in sha ALLAH kamar ka sameta ka gama, amma kuma bazai yuyu kayita zama a haka ba dole kayi aure kafin lokacin tunda kai mijin macce huɗu ne sannan shekarunka ja suke yi ba raguwa ba". "A'a Abbie nidai..." "Ya isa haka". Abbiey ya faɗa shaye da toka yana nuna masa yaci gaba da cin abincinsa da Ammie ta gama zuba masa, sanin halin Abbie ya sa Haisam ɗaukar cokalin ya fara cin abincin ransa a ɓace ba tare daya koma cewa uffan ba, bai wani ci abincin sosai ba ya ture plate ɗin gefe haɗe da miƙewa ya bar wajen, ɗago kai Ammie ta yi zata yi masa magana Abbie ya ɗaga mata hannu, hakan ya sa ta kama bakinta tayi shiru ta cigaba da cin abincinta, "Good night Abbie, night Ammie." Ailat ta faɗa itama tare da miƙewa ta bar wajen ta nufi ɗakinta dake nan ƙasa Abbie na cewa tayi addu'a kafin ta kwanta. Sai da suka gama cin abincin Abbie ya riƙawa Ammie suka kwashe kayan ta ɗauraye shi kuma ya wuce ɗakinsa ya watso ruwa sannan ya sake saukowa ƙasa ya sameta a falo tana kallon drama, gefenta ya zauna tare da amsar remote ɗin ya sauya channel zuwa ta labarai sannan ya mayar mata yana faɗin, "yau dai ya kamata mu kalli labaran nan tare dake. "Ai kuwa bazan kalla ba don bacci nake ji". "Ai tunda na kashe maki drama ɗinki ba?" Ya faɗa yana dariya kafin can ya ɗan riƙe fuska yana kallonta, hakan ya sata natsuwa sosai tana kallonsa itama don tasan tunda ya yi haka akwai maganar da yake son yi da ita mai muhimmanci, murmushi ya saki ganin yanda ta tattaro duka natsuwarta gareshi haɗe da cewa, "Shiyasa nake ƙara ƙaunarki a zuciyata saboda kina fahimtar duk wani yare dazai fito daga kan fuskata, koda kuwa ban furta komai ba a bakina". Sai daya yi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da cewa, "wai me kika fahimta a zancen yaron nan ɗazu, wlh daga ni har Alhaji Asim mun zata suna son junansu ganin yanda suka shaƙu juna." "Nima haka na ɗauka daga farko, amma daga bayan nan sai na fahimci kawai shaƙuwace shi Haisam baya sonta, amma ita tana son sa sosai, gashi ya ɓullo da zancen Madiyam yanzu, kuma kasan Abbu na ji babu abunda zai hana ya bashi aurenta". "Hakan ba laifi bane, amma shekarunsa na ja, idan aka ce ya zauna zaman jiranta tofa yayi mata tsufa alokacin." "Alhaji kenan, ai shi namiji baya tsufa da aure, indai tana son sa ba wata matsala bace, sai ya haɗa su su biyu ya auresu". "Abunda nake ƙoƙarin nuna masa kenan ɗazu yake nema ya yimun gaddama". "Haƙuri za muyi mu lallaɓasa, kuma muyi masa addu'a ALLAH ya zaɓa masa alkhairi, nasan in Sha ALLAH itama Najlah zai amince ya aureta." "ALLAH yasa". "Amin, ya batun yaronki shi kuma, ya faɗa maki yana da wacce yake so?" Sai da tayi dariya sannan ta ce, "Ina ruwan Hisham, ai ni ko ga mafarki banji ba kuma ban gani ba". "Ai shikenan, gashi ga iyayensa su suka san yanda za suyi dashi, don yanzu ina magana Abbu zai ce takurasa nake son yi, kinsan halinsa da son ƴaƴa" "Ai sai ka zuba masu idanuwa, idan tayi tsami ma ji" "Hakane, kindai hanani kallon labaran nan, bari naje na kwanta gobe muna da mitin ƙarfe bakwai na kwamishinoni idan ALLAH yakai ranmu da maigirma gwamna." Ya ƙare zancen tare da miƙewa ya nufi sama yana yimata sai da safe, kayan kallon ta kashe itama ta wuce ɗakinta tana buga hammar dake nuna baccin na cinta itama sosai. Abbu da Abbie wa ne da ƙane kuma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dukkanninsu haifaffin garin kaduna ne a ƙaramar hukumar Giwa dake cikin jahar, sun taso cikin maraicin iyaye lokacin Abbu mai suna Awwal yana da shekaru goma sha tara aduniya shi kuma Abbie Sani yana da shekaru sha biyar, sai ƙanwarsu Fatima tanada shekaru bakwai aduniya, inda tana cika shekara goma bayan rasuwar iyayen nasu itama ALLAH ya yi mata rasuwa ya rage daga Abbu sai Abbie, ganin yanda Abbie ke son karatu ya sa Abbu jajircewa wajen kasuwancin saye da sayarwa na hatsin da suke nomawa da kansu a gonar da mahaifinsu ya bar masu a kasuwanne don taimakawa ɗan uwan nasa ya yi karatu, cikin taimakon ALLAH kuwa Abbie ya maida hankali sosai ya yi karatun da har ALLAH ya kawosa a babban matsayin da yake yanzu a cikin gwamnati na commissioner of health a jahar, sosai ya so ɗan uwan nasa ya dawo su zauna tare amma fir Abbu ya nuna masa yafi don zamansa acan ƙauyen yana ƴan harkokinsa daya saba dasu na yau da kullum, hakan ya sa Abbu ya gyara masa gidansa ya kuma buɗe masa wani ƙaton ma'ajiyar hatsi da yake siye ga manoma idan sunyi girbi shi kuma yana saidawa manyan ƴan kasuwa dake zuwa siye daga birni, shiyasa in ya fita tun safe baya dawowa sai marece, tun da Abbu ya auri matarsa Fatima (Mahmah) bata taɓa haihuwa ba har Abbie ya zo ya yi aure sai gashi cikin iyawar ALLAH shekara na zagayo wa matarsa Amina(Ammie) ta haifi Haisam inda Abbu ya yi murna sosai da samun ƙaruwar ɗan uwan nasa, bayan shekara uku ta sake haifo ɗan ta ya ci suna Hisham har lokacin Mahmah ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, sosai Abbu sukayi zuwa yawon asibiti har cikin Kaduna da taimakon Abbie aka duddubasu akace basuda matsala su dukansu lokacine kawai baiyi ba, hakan yasa Abbu ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da addu'a ALLAH ya kawo masu nasu lokacin suma. Kamar yanda Abbu da Abbie ke tsananin son junansu haka Haisam da Hisham ke matuƙar son junansu tun suna ƙanana, babu mai yadda wani abu ya sami ɗan uwansa ba tare daya tare masa ba, komai nasu iri ɗaya akeyi masu haka ma suna da kamanni sosai, hasken fata kawai ne ya banbanta su inda Haisam ya ɗauko kalar fatar mahaifiyarsa, shi kuma Hisham ya ɗauko ta mahaifinsa don kuwa farar fata ne Fulani ƙauye na asali, sai kuma banbancin halayya da suka samu, inda Haisam keda son wasa da dariya sosai shi kuma Hisham miskiline ko magana bata damesa ba, hakan yasa rana ɗaya yana gama jlc ya daka tsalle Abbu na zuwa ya laƙesa yace shi wajensa zai koma da zama, wanda hakan ba ƙaramin farinciki ya saka Abbu ba tare da jin soyayyar Hisham sosai a ransa, shi kuwa Abbie ya tattara komai nasa ya barwa Abbu shi, komawar Hisham wajen Abbu sai ya zama alkhairi, don kuwa a watan ALLAH ya bawa mahmah cikin Madiyam, murna awajen su Ammie da Abbie ba a magana, lokacin Ailat nada shekara biyu da haihuwa, yanda su Mahmah suka ga su Abbu na son junansu haka suma suke son juna ita da Ammie, shiyasa Mahmah ta zama ƴarlici ta ko ina data samu cikin, don ko yaushe Ammie na kan hanyar zuwa dubota, Hisham kuwa har girki da shara duka yimata yakeyi lokacin da cikin ya tsufa saboda tausayi, watan haihuwarta na kamawa ta haifi kyakkyawar ƴarta taci sunan mahaifiyarsu Abbiey wato hawwa'u amma sai ana kiranta da Madiyam da yake cikin damana aka haifeta, su kuma Fulani sukan kira wacce aka haifa cikin damana da Madiyam musamman ma idan za ayi mata laƙani. Sosai Madiyam ta taso cikin kulawa da soyayyar ƴan uwa musamman Hisham da har goyata yakeyi, yanayin karauniya da irin ƙiriniyar data taso da ita da sangartawar da Abbu keyi mata ya sashi sauya mata saboda gudun kar ta koma ɗaya daga cikin sangartaccin yaran dake lalacewa ana yi masu kallon marasa tarbiya da kuma mafaɗi... *****. *****. *****. Tun da asuba da Madiyam tayi Sallah ta ɗauko madubi tana faman jujjuya fuskarta aciki har safiya ta fara wayewa, don ba laifi ƙafar tayi mata sauƙin sosai, kallonta Mahmah ta yi haɗe da cewa, "Wai lafiyar ki Madiyam, me kikeyi da madubi tun asuba har yanzu" Turo baki ta yi haɗe da cewa, "To ba ya dodo bane ya ce wai ƙarin baki ne dani, shine nake dubawa na gani wai don ALLAH da gaske ne Mahmah? ta ƙare maganar tana wani kimtsa bakinta haɗe da kallon Mahmah, dariya Hisham daya shigo ɗakin da sunan gaishe da mama ya taddata tana wannan shirmen ya kwashe da ita haɗe da ƙaraso wa cikin ɗakin ya karɓe madubin ya ɗora saman chest of drawer ɗin dake gefe haɗe da cewa, "Ai kima hutar da kanki yarinya da dubawa, kowa agidan nan ya san ƙaton baki ne dake, matso nan naga ƙafar taki".. ya ƙare zancen yana ɗaure fuska tamkar ba shi ya gama dariyar ƙera ba yanzu tare da zuba mata kyawawan idanuwansa yana kallon yanda ta fara kyaƙƙyafta idanuwa haɗe da tumɓure fuska za tayi kuka... *FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* Free page 4 *FIL-HUB*♥️ (Acikin so💘) Paid Book: N500 Written by Billy s fari💎 ______________________________ Ɗan murmushi ya saki kafin yace, "Ai kin ji, matsala ta dake kenan, komai naki na kuka ne, zaki matso ne ko kuma nazo da kaina na duba ƙafar?" Jiki a mace ta taso tana goge hawayen da har sun zubo mata akan fuska da hannu ta zauna a ƙasan gadon da yake zaune akai ta tura masa ƙafar tare da kauda kanta gefe, taɓe baki ya yi haɗe da kallon Mahmah ya gaida ita sannan ya ce ta bashi maganin daya zo dashi jiya da za a sake shafa mata, hannu ta miƙa kan madubi ta ɗauko ledar maganin ta miƙa masa tana faɗin, "Ai naga ƙafar ma da sauƙi alhamdulillah." Daidai lokacin wayarsa tayi ringing ya ciro daga gaban aljihu haɗe da karawa a kunnensa ya ce, "Good morning ya Haisam" "Morning Hisham, kun tashi lafiya?" "Lafiya klw, yasu Ammie da Ailat." "Lafiya klw suke, ya jikin Madiyam?" "Ta ji sauƙi?" Ya faɗa tare da saka wayar handsfree ya ajiye a gefen gadon haɗe da riƙo ƙafar tata yana faɗin, "Mahmah sammana kaɗa." Daidai lokacin shi kuma Haisam ya ce "ba Madiyam wayar?" Kallonta ya yi ganin yanda ta washe baki jin muryar Haisam daya ce a bata wayar haɗe da cewa, "Yi maganar ka tana jinka" "Hello Madiyammm.." Haisam ya faɗa yana wani jan sunan cike da shauƙi, ɗan runtse idanuwa Hisham ya yi jin wani abu ya dakar masa a zuciya haɗe da buɗewa ya saukar dasu akan fuskar Madiyam da sai faman dariyar dake nuna jin daɗin Muryar ya Haisam ɗin da tayi takeyi haɗe da cewa, "Laa..ya Haisam ina kwana?" "Lafiya klw ƙanwata". "ALLAH kafi kowa iya faɗan sunana ya Haisam". "Da gaske kikeyi Madiyammm" ya sake daɗi fiye da yanda ya kasa ɗazu, sai data yi dariya sannan ta ce, "Wlh kuwa, kuma ya ma fi daɗi abakinka idan ka faɗa, ina Aunty Ailat da Ammie." "Duk suna nan lafiya suna gaisheki" "Ina amsawa". "Ya ƙafar taki inji da sauƙi?" Sai data kalli Hisham daya riƙo ƙafar yana goge dattin dake sama da kaɗar da Mahmah ta miƙo masa sannan ta ɗan turo baki haɗe da cewa, "Eh da sauƙin ya Haisam ɗazu, amma yanzu gashinan ta fara ciwo." "Ayya srry zata dena kinji ko?, kina dai shan magani?" "A'a shafawa kaɗai akeyi" ta faɗa tare da fashewa da kuka jin yanda Hisham ke shafa mata maganin yana murza wajen sosai, saboda wani abu da yake ji na taso masa azuciya, uwa uba daya ji tana faɗar wai yanzu ƙafar ta fara ciwo tsabar ta rena masa da wayau, kenan don ta riƙa ƙafar shiyasa tafara yimata ciwo?, hakan ya sake tunzurasa ya cigaba da murzar ƙafar yana shafa maganin da ƙarfi, jin kukan ta ya sa Haisam ruɗewa haɗe da tashi daga kwancen da yake yana cewa, "ƙanwata lafiya?, meya faru kike kuka kuma? no kidena pls bana son jin kukanki kinji ko?" "Ya Hisham ne.." ta faɗa tare da kasa ƙarasawa ganin yanda yake wurgo mata wata shegiyar harara, "Yaya Hisham ne ya yi maki me cutie?" "Ba komai" ta faɗa tana sadda kanta ƙasa, "Shikenan barni dashi kinji ko, yi haƙuri ki goge hawayen gobe zanzo na dubaki, me kike so nazo maki dashi." "Ni bana son komai" ta faɗa cikin shagwaɓa tana goge ƙwallan, "Haddani bakya so?" "A'a ina sonka" "To ai Ni zan zo maku da abunda kike so idan kin faɗa". "Kazo mun da Aunty Ailat da ice cream." "A'ahh..Aunty Ailat makaranta take zuwa kinsan gobe monday, sai dai ice cream ɗin, dame kuma?" "Komai ma ina so". "Kin tabbata?" "Eh". "To yimun dariya naji.." kafin ya rufe baki Hisham da firar ta soma isarsa ya ɗauke wayar haɗe da miƙewa ya ficewa daga ɗakin yana faɗin, "Mtsss...wai kai baka gajiya da shirmen waccan yarinyar ne?, to ni fita zanyi sai ka kira wayar mama ku ƙarasa acan." Ya kashe wayar tare da jefata aljihu ba tare daya jira jin amsar da zai bashi ba, Dariya Haisam ya yi jin ya katse kiran don dama ya san za a yi hakan, wani murmushin ya sake saki yana tsinkayo fuskar Madiyam ɗinsa na dariya kafin ya miƙe daga kan gadon daga shi sai ves da dogon wando a jiki, turo ƙofar ɗakin nasa ya ji anyi tare da shigowa an mayar an rufe, juyowa ya yi tare da zaro idanuwa ganin Najlah jingine a jikin ƙofar ta naɗe hannayenta a ƙirji tana jifarsa da wani irin kallo. Tsuke fuska ya yi haɗe da gyara tsayuwarsa yana wurga mata wani mugun kallo shima haɗe da cewa "Me ya kawoki ɗakina Najlah?" "Zuwa nayi inji dalilin sauyawar da kayi mani kwana biyu". Ta ƙare maganar tare da nufo wajensa tana murmushi haɗe da kakkarya jikinta, "stop Najlah." Ya faɗa da ƙarfi tare da kauda kansa gefe yana ɗaga mata hannu, ganin taƙi tsayawa kamar yanda ya umurce ta ya sashi fara ja da baya har ya haɗe jikinsa da ƙofar toilet ɗin cikin ɗakin, wata tsawar ya sake daka mata a karo na biyu yana faɗin "Wai meye haka?" ba tare data damu ba ta matso sosai kusa dashi har jikinsa na gugar nata ta yanda zasu iya shaƙar lumfashin juna tana ƙarema kyawawan idanuwansa kallo, "haisam, kayi iya shouting ɗin da zaka yi ba wanda zai jika a gidannan, Abbie tun safe ya fita, Ammie da Ailat kuma suna gida na baro sunje yiwa Dady sannu da zuwa, hakan yasa na zo inji laifin da nayi maka domin bazan juri cigaba wannan shariyar da kake yimun ba, ko ka manta alaƙar dake tsakani na dakai ne?" ta ƙare zancen tare da ɗora yatsanta a saman fuskarsa tana yawo dashi. "Meye haka kikeyi Najlah, wace irin maganace kike faɗa haka? Dama akwai wata alaƙa ne tsakanin ni dake wacce ban sani ba?" "Yes upcouse Haisam, kafin kowa sanin ta tunda kai ka saba Mani da ita, ka reneni cikinta har muka girma". "No..Ni bansan komai ba kima dena yaudarar kanki?" "Common...ai kai kake yaudarar kanka Haisam, kana nufin duk abota, shaƙuwa, kulawa, da kuma kyautatawar da kake tsakanina dakai ba *A cikin so* bane?, gaba ɗaya shirme ne da kuma tatsuniyar gizo da ƙoƙi?" Ta ƙare zancen tana ƙara shiga jikinsa haɗe da yin wasa da wuyan ves ɗin jikinsa, wanda hakan yasa Haisam ya ji wani irin abu na tsirga masa tun daga ƙasan ƙafafuwansa har zuwa tsakiyar kansa, runtse idanuwansa ya yi haɗe da turata da ƙarfi yana faɗin, "enough Najlah, wai menene hakan kikeyi? Ko kin manta ke macce ce?" "And so what don ni maccce ce Haisam?, sai akace maka bazan so abunda zuciyata ke muradi ba? Ko ce maka akayi bazan iya nunawa abunda nake so so ba?, look Haisam!, tun tashi na ban taɓa son wani namiji a duniya ba kamarka, kuma kaine ka koyar dani hakan tun bansan meye so ba har na fara saninsa, akan me yanzu tsakar rana zaka zo kace ba haka bane kuma kayi tunanin wai zan dena bayan kai da kanka ka tabbatar da irin tarin soyayya da kuma ƙaunar da nake yi maka." "Wannan fa ba soyayya ce irin ta aure na nuna tsakanin ni dake ba Najlah, kawai shaƙuwa kuma ya kamata ki fahimci hakan". "Bazan fahimta ba Haisam don na riga da nayi nisan da bana jin kira wlh, akanka zan iya komai aduniya, don haka ya zama dole ka so ni kaima ko kana so ko baka so" ta faɗa da ƙarfi haɗe da nunasa da hannu, shaƙo wuyanta ya yi cikin ɓacin rai tare da manna ta ajikin bangon ɗakin, zai yi magana cikin ƙarfin hali ta haɗe bakinta da nasa ta fara tsotsa, hakan ya sashi lumshe idanuwa tare da sakinta ba tare daya sani ba yana jin jikinsa gaba ɗaya ya mutu, hannunsa ya sa ya riƙo ƙugunta haɗe da mannata a jikinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya fara mayar mata da martani, tana jin hakan ta saki wani murmushi haɗe da turesa, sake jnyota ya yi jikinsa na rawa zai sake haɗe bakinsa da nata ta turasa da ƙarfi ya faɗa kan makeken gadon nasa, ƙafarta ɗaya ta ɗora akan gadon tare da kallon yanda idanuwansa suka soma sauyawa ta ce, "Shima wannan duka ba A cikin so bane shaƙuwa ce, kada ka cuci kanka Haisam don ƙarya kakeyi kima kana sona, idan kuma kace ba haka ba to ina tabbatar maka da kaɗan kafara gani cikin abubuwan da zan yimaka da zasu sa iyayenmu su aura mana juna ko kana so ko baka so". Ta ƙare zancen tare da kashe masa ido ɗaya sannan ta juya ta bar ɗakin, saida ta leƙa ƙasa ta tabbatar ba kowa sannan ta sauko ta fice daga gidan tana rayawa zuciyarta kota halin ƙaƙa sai ta mallaki Haisam. Shi kuwa dafe goshi ya yi tare da ɗago kai yaga yanayin da Najlah ta jefasa aciki ya koma ya kwanta yana jin wani abu mai kamar shocking na fizgarsa, gaba ɗaya ta jefasa cikin wani irin hali sai numfashi yake fitarwa da ƙarfi da ƙarfi, "ya zan yi?" Ya tambayi kansa don har ga ALLAH bai taɓa jin soyayyar Najlah aransa ba, Madiyam ce tun tana jaririya daya ɗora idanuwansa akanta ALLAH ya saka mashi tsananin sonta da ƙaunarta, gashi Najlah na nema ta takalo masa ciwon da baya da maganinsa a halin yanzu in ba Madiyam ɗinsa ta zama mallaki da ba, jin abu na neman zamar masa alaƙaƙai ya sashi miƙewa ya faɗa toilet ya sakarwa kansa ruwan zafi, amma inaa kamar ya ƙara takalo wa kansa masifar yake ji, wayar sa ya ciro tare da kiran wani abokinsa Dr Ahfan ya sanar dashi halin da yake ciki, tintsirewa da dariya ya yi haɗe da cewa, "Ai kaji abunda ake faɗa maka tuntuni kayi aure amma ka ƙi, kai baban soyayya ka zauna jiran har sai lokacin da ƙwailar ka ta girma, inaga idan baka bi hattara ba zaka tsofe a haka ba aure, don wlh aka ƙara shekaru biyar gaba yanzu ba lallene Madiyam ɗin taka ta amince ta aureka ba." Ya ƙare zancen yana kallon matarsa Nihal data nufo wajen da tulelen cikinta da haihuwa ko yau ko gobe haɗe da miƙa mata hannu ya zaunar da ita akan cinyarsa yana sumbatar cikin, Cikin wata irin kasalalliyar murya Haisam ya ce, "Kai fa ɗan iska ne, bakinka ya sari zuma rock na Abuja, ni ba wnnn na kirak ji ba don ALLAH ka faɗamun ya zanyi, ni kaɗai nasan halin da nake ciki yanzu haka" "To kayi aure mana ka huta, in yaso ko daga baya ne sai ka auri ita Madiyam ɗin tunda musulunci bai hana ba." "Mtsss..nifa gaskiya mace ɗaya ce tsari na, bana sha'awar mata biyu gaskiya". "Aikuwa ka faɗo wlh, mata biyu ai duniya ne Malam". "Naji nidai faɗa mun me zan sha na fita wannan bala'in yanzu". "Kawai nemi ruwan ɗimi da lemun tsami kasha za ka ɗan samu relief, amma maganin wannan ƙwazabar taka kaje kayi aure kawai, wannan shine shawarata, ko ba haka ba Madam?" Ahfan ya ƙare zancen yana kallon Nihal da kallo ɗaya zaka yimata kasan ba ƙaramar wahala take sha ga cikin ba. Tsaki Haisam ya ja tare da kashe wayar yana faɗin, "ɗan iska kawai, ashe agaban matarsa yake mun wannan tsarguwar, zamu haɗu dakai ne". shi kuma Dr Ahfan dariya ya saki yana shafa gefen fuskar Nihal dake kwance saman kafaɗarsa haɗe da cewa "Sannu Madam, ya aka yine?" "Don ALLAH ka mai dani wajen Aunty, ALLAH gani nakeyi kamar bazan iya haihuwar nan da kaina ba" "Kice a gaida Amira data haifamun ƴan biyu, kawai ki daure in sha ALLAH kema lafiya klw zaki haihu, kuma da kanki ba sai an fasa ki ba, ko Amira da kike gani tausayi ƙanƙantarta naji ace zata haifi ƴan biyu shiyasa kawai na bari aka fasata, bodon haka ba bazan yarda a runatamun mata b ta kasa ɗaukar lalurata." ya ƙare zancen tare da ɗagata suka nufi ɗaki don ya fahimci bacci take ji sosai Haisam kuwa ƙasa ya sauko bayan ya saka doguwar jalbiyarsa ya nufi kitchen ya shiga bubbuɗe abubuwa ko zai samu lemun tsamin, cikin sa'a kuwa yana buɗe fridge sai gashi ya gani har kusan ƙwaya biyar da Ammie tasa aka siyo mata tana amfani dasu idan za tayi haɗin drinks, gaba ɗaya ya kwaso ya matsesu a cup ya jefa bayan a bayan window sannan ya tsiyaya ruwan zafin daya gani ajiye cikin flaks ya ɗauki cup ɗin ya nufi falo haɗe da kunna tv yana kallo yana kurɓa a hankali har ya shanye su tas, sannu sannu ya fara jin abun na saukar masa kafin can yana kallon bacci mai nauyi ya yi awon gaba dashi, Ammie kuwa da sai kusan sallar azahar suka dawo don suna fita gidan Dady wajen saloon suka nufa, yanda ta iske shi kwance cikin falon yana baccin ya sa ta bishi da kallo, don tun yana yaro abune mai wahala ka ganesa yana baccin rana sai inhar idan baida lafiya ne, ɗauke cup ɗin dake gabansa ajiye ta farayi ta kai kitchen tana mamakin abunda Haisam ya yi da lemun tsamin da taga kufansa aciki, ba tare data kawo komi a ranta ba ta dawo tare da ɗora hannunta saman jikinsa ta taɓa ta ji ba zafi sannan ta tashesa tana faɗin, "Ka tashi kaje ankusa kiran sallar azzahar, lafiya kake kuwa, wannan bacci haka a takure da kakeyi sai kace wanda al'ada dole?" Sai daya ɗora kansa a saman kafaɗarta sannan ya ce, "Ammie yaushe kuka dawo? Gaskiya kun daɗe sosai". "Mun biya gyaran kai ne Ni da Ailat da kuma Najlah bayan mun fita gidansu". "Shine kuma baku faɗa mun za kuje ba na kaiku? kuka tafi kuka barni cikin gida ni kaɗai?". "Ikon ALLAH, Haisam kai ƙaramin yaro ne ko jariri da

Chapter 3 of 9