bari na samu na ƙarasa abincin ka samu kaci, gashi ka kwaso gajiya".
"Wlh kuwa, bari nima na kwaso kayan dake mota kafin ki ƙara sa Mahmah don yunwa nake ji sosai".
"Ai dole, wannan uwar rana da hanya daka sha". Ta faɗa tare da barin ɗakin shi kuma ya koma waje,
Ice cream da fresh youghout ɗin Madiyam ya fara ɗaukowa ya saka a fridge don duka sun narke sannan ya shiga kwaso kayan ɗaya bayan ɗaya yana shigowa dasu ciki, bayan ya gama Mahmah ta ɗauko makullin ɗakin Hisham data rufe masa ɗazu ta ajiye makullin a hannunta ta bashi haɗe dayi mashi sannu tana sa mashi albarka,
Gyare ya isko ɗakin fes sai ƙamshin turarukkan da Hisham ke sakawa a jiki ke tashi haɗe da faɗawa kan ƙatuwar katifar da ta sha gyara gyara har ta gaji yana faɗin, "Wash ALLAH! Where are you my cutie? Pls come back soon am eager to see you". Ya ƙare zancen yana ƙare wa ɗakin kallo yanda ya sha gyara tsaf komai a tsare sai kace ɗakin macce, wata ƙil Madiyam ke gyara masa, ya faɗa cikin zuciya, da saurin ya girgiza kai a zahiri yana faɗin, "No bazai yuyu ba, Madiyam is belong to me, ɗaki na kaɗai ya cancanci ta riƙa gyarawa" murmushi ya saki yana hasaso zuwan lokacin tare da sha fa quarter million ɗin sa daya zagaye fuskarsa daga nan bacci ya yi awon gaba dashi yana faman saƙe saƙe da tunani akan zuwan ranar da zai mallaki Madiyam ɗinsa.
Bai tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya da kwata Mahmah ta tada shi ya yi sallah, toilet ya fara shiga ya rage cikinsa haɗe da watso ruwa sannan ya buɗe doguwar wadrobe ɗin da kayan Hisham suke ta bango ya ciro kala ɗaya ya sa ya nufi masallacin dake gaba da su Mahmah kaɗan ya yo Sallah, yana fitowa ya ga ɗalibbai sun fara tasowa makaranta, ai kuwa ya dinga baza idanuwa yana jiran hango ta inda Madiyam ɗinsa zata fara fitowa, ganin an kwashi kusan mintuna ashirin bai ga ta inda ta ɓullo ba ya sa ya wuce gida cike dasa ran zai iskota, yana shiga ya ji muryarta a bayansa ta shigo don kusan tare suke tana bayansa bai sani ba, ita kuma kanta sunkuye yake a ƙasa ta faɗa duniyar tunani bata ma san wanda ke gabanta ba har suka ƙaraso, haka ma Hisham shima yana bayanta amma akwai ƴar tazara kaɗan tsakanin su, saurin ɓuya Haisam ya yi a jikin rumfar dake gaban ɗakin Mahmah yanda baza ta iya hango sa ba haɗe da zuba wa tsakar gidan idanuwa yana jiran shigowar ta, "Fatabarakallahu ahsanil khaliqeen" Haisam ya faɗa lokacin da idanuwansa suka sauka akan Madiyam data shigo a gajiye tana faɗin, "Mahmah, Mahmah, na dawo" yana kallon yanda ɗan ƙaramin bakin nata ke motsawa, lumshe idanuwa ya yi haɗe da sake buɗe su ya saukar akanta, daidai lokacin tana ƙoƙarin shiga ɗakin Mahmah ya lallaɓo ta bayanta tare dasa hannu ya rufe mata idanuwa yana dariya ƙasa ƙasa, gabanta ne ya yi wata irin muguwar faɗuwa don bata lura da motar Haisam ba dake ajiye a ƙofar gida da zata shigo, daidai lokacin shima Hisham ya ƙarazo ƙofar gidan gabansa na faɗuwa ganin motar yayan nasa abakin gida, tsintar kansa ya yi da jin haushin zuwan nasa amma sai ya danne hakan tare da shiga ciki, wata irin tsawa ya daka wa Madiyam da tana jin Muryar ya Haisam da ya ce ki cinki ko waye ta juyo da ƙarfi cike da farinciki tana ihu zata rungumesa,
"Wai meye haka ke damunki da gabaɗaya ba kida hankali wani lokacin, wannan ihun na meye sai kace wata ƙaramar yarinya, getout ki ɓacewa mutane da gani in baza kiyi aikin hankali ba, wawiya kawai" ya faɗa ransa duka aɓace ba tare da ma ya san abunda yake faɗa ba, ɓata rai ta yi haɗe da sinne kai ƙasa sannan ta juya ta shige ɗakin tana faɗin, "Ya Haisam sannu da zuwa".
"Yawwa my cutie sister" ya faɗa tare da juyowa yana kallon Hisham daya nufi kitchen wajen Mahmah dake kallon abunda ya yi, wanda ko shakka babu a yanda yake maganar zaka fahimci akwai kishi a ciki, murmushi kawai ta yi haɗe da cigaba da suyar jakin da take yi har ya ƙara so wajen,
"Sannu da aiki Mahmah."
"Yawwa Hisham, a dawo?"
"Eh Mahmah, ina wuni?"
"Lafiya klw, ya ɗaliban naka?"
"Alhamdulillah" ya faɗa tare da juyowa ya nufi wajen Haisam dake kallonsa, hannu ya miƙa masa yana murmushi haɗe da cewa, "Welcome brother, yaushe ka iso?"
"Ban sani ba". Ya faɗa yana harararsa hakan ya bawa Hisham dariya sosai haɗe da riƙo hannunsa ya tafe da nasa sannan ya jasa suka nufi cikin ɗakinsa yana faɗin, "Am sorry my sweet and only brother, ALLAH yarinyar can ba ta jin magana, baka ji yanda ake Jin ihunta ba tun a waje sai kace wata zararra".
"Kai ne dai zararren Hisham baka sani ba, daga shigowa gida ba sallama kawai sai ka fara yiwa yarinya ihu, waya faɗa maka haka akeyi?".
"Sorry pls, mu ajiye wannan zancen ya wuce, ya su Ammie da Ailat, am seriously missing them, ina Najlah dasu Dady, hop kowa yana lafiya?"
"Yes upcouse, kowa yana lafiya unless Najlah?" Ɗan zaro idanuwa Hisham ya yi haɗe da cewa, "Me yake damunta ne?"
"Meke damunta kuwa banda cutar so, kuma wai ta rasa wanda zata ce tana so sai ni..." Kafin ya ƙarasa Hisham ya kwashe da dariya haɗe da cewa, "To sai me? Ai ta kwana gidan sauƙi, dama ina ta addu'a ALLAH ya ceci yayana kar ya tsufa baiyi aure ba, ashe ALLAH ya amsa mani ban sani ba".
Sai da Haisam ya ɗauke fuska sannan ya ce, "Sai kuma aka ce maka ni ina sonta?"
"Amma kuma ai ba ka ƙi ta ko? Look ya Haisam, wlh kun bala'in dacewa da Najlah kuma zaku samu rayuwa mai kyau da ita idan kuka auri juna saboda akwai kyakkyawar alaƙa da shaƙuwa haɗi da fahimta tsakaninku, a yanda ka ɗin nan bana tunanin akwai mace da zata iya baka kyakkyawar kulawa kamar Najlah, just accept her musha bukin ƴar chana da ya Haisam.." kafin ya rufe baki ba Haisam ya ɗauko pillow yana maka masa ganin yanda yake kwasar masa dariyar ƙeta, "kai kaje ka aureta mana, duk shaƙuwar dake akwai tsakanina da ita ai akwaita tsakaninku".
"Nooo ya Haisam ba kamar kai ba gaskiya, be side ma, ai kai tace tana so ba ni ba".
"To ni bana sonta ina da wacce nake so".
"Wa kenan?" Hisham ya faɗa yana caɓe pillown daya jefo masa, har Haisam zai yi magana sai kuma ya fasa haɗe dayin murmushi ya ce,
"Koma waye zaka santa very soon in sha ALLAH". Ya ƙare zancen tare da ficewa ya bar ɗakin, shiru Hisham ya yi kamar mai wani nazari kafin ya miƙa ba tare daya kawo komai a ransa ba ya shige toilet ya watso ruwa,
Ɗakin Mahmah ya nufa ya ci karo da ita bakin ƙofar shiga ɗauke da tray data jerikke kayan abincin akai ya yi saurin karɓar mata haɗe da ƙarasawa dasu ciki, ɗauke kansa ya yi ganin Madiyam da ya Haisam zaune akan kujera ɗaya ya tasa mata kayan daya siyo mata agaba tana ci yana yi mata fira tana kwasar dariya, burger ce a hannunta ta gutsiri wata a baki tana ci a gefe kuma ga ice cream ya buɗe yana yi yana bata abaki tana sha, wani abu Hisham ya ji ya dakar masa a zuciya tare da ajiye trayn ya juya zai fita, dariyar da Madiyam keyi ga gutsiren burger acikin bakinta ya sata ƙwarewa ta shiga yin tari kamar zata mutu, da sauri Haisam ya tsaida shi haɗe da cewa ya miƙo masa ruwa ɗaya a fridge don shi hannuwansa riƙe suke da ice cream ɗin da yake bata tana sha, kuma sun lalace sanadiyar tarin da take yi ya baltsar masa har a jiki, ko kaɗan Hisham bai yi niyar miƙa mata ruwan ba har sai ta wahala amma ganin Mahmah ta shigo ya sa ya buɗe fridge ɗin ya ɗauko ruwa ɗaya ya miƙo mata yana faɗin,
"Mutum ya zauna yayi ta ciye ciye hannu baka hannu akushi ba dole ya ƙare ba".
"Fasa mata mana ka bata Hisham, wai wannan wane irin rashin tausayi ne haka".
"Ita ya kamata kayiwa faɗa ba ni ba ya Hisham tunda bani na aiketa ba". Ya ƙare zancen tare da ajiye masu ruwan ya yi gaba abunsa, ajiye icecream ɗin Haisam ya yi haɗe da ɗaukar ruwan ya fasa mata ya miƙa mata, lokacin tayi tarin har ta gaji tayi liƙis haɗe da relaxing ajikin kujera"
"Am sorry my cutie karɓa kisha" ya ƙare zancen tare da kai mata ruwan a baki, karɓa ta yi ta sha sosai sannan ya janye ruwan ya ajiye tare da kallonta ya ce,
"Sorry cutie".
Murmushi ta sakar masa sannan ta taso ta karɓi sauran icecream ɗin dake hannunsa don kar ya ji ba daɗi tana faɗin, "ya Haisam bari na ƙarasa wannan, wuɗannan zan ajiye a fridge na riƙa zuwa dasu makaranta,na gode sosai"
Hisham kuwa duk da yunwar da yake ji ficewa ya yi daga gidan yana jin wani abu na taso masa a zuciya, ya rasa me yasa baya son kowa ya kusanci Madiyam, ya rasa meyasa yake cin zafin zuciya da ƙunar rai idan ya ganta da wani, gashi dai Haisam ɗan uwansa ne kuma duka matsayinsu guda a wajenta, amma sai yake jin ba daɗi ganin yanda suke shiri dashi.....
_Afuwan not edited_
*FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
Free page 8
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ko da suka isa makarantar har anfara Assembly hakan ya sa bai tsaya bi takanta ba ya wuce gaban Assembly ɗin inda malamai ke tsaitsaya, yana hawa wajen gaba ɗaya idanuwan student suka koma kansa sai maganganu ke tashi sama sama na yanda suke yaba haɗuwarsa da tsarinsa, bayan an kammala duk wasu activities da aka sabayi wajen assembly ɗin principal ta juyo haɗe da kallonsa cikin harshen turanci ta ce yazo ya gabatar da kansa ga student da kuma subjects ɗin da zai ɗaukesu, ganin yanda gaba ɗaya suka zuba mashi idanuwa ya sashi ɗaure fuska haɗe da takowa zuwa gaban assembly yanda zasu ganesa daidai, cike da ƙwarewa cikin harshen turanci daya bala'in zauna masa raɗam a baki kai kace tun asali dama can Bature ne ya fara magana.
"_Good morning student, sunana Hisham s dala, ni ne wanda zanci gaba da ɗaukarku darasin Physics, ina fata kowane ɗalibi zai bani haɗin kai wajen mayar da hankali, ina da matuƙar sauƙin kai ga waɗanda suka maida hankalinsu ga abunda ya kawo su haka kuma ina da zafi sosai ga wuɗan da basu san me ya kawo su ba, thanks to meet you all_"
Ya ƙare maganar haɗe da sakin murmushi yana ɗaya masu hannu, gabaɗaya tafi ɗalibban suka saka tare da haɗa baki wajen cewa, "Thank you uncle Hisham, you're highly welcome to sardauna acadamic science school". Kamar dai yanda aka saba yiwa kowa ne sabon malami idan ya zo makarantar, Nauwara ce ta yi murmushi haɗe da juyowa ta kalli Madiyam da ta yi tsaki ƙasa-ƙasa saboda jin haushin yanda aka wani karrama Hisham ɗin, duk da kuwa ta san cewa al'adar makarantar ta su ce, ta ce "Madiyam ya akayi yau naga kinyi sakkon zuwa makaranta, ko dai aikin ya Hisham ne?" Ta tambaya don ta san halin Madiyam, ba ta shigowa school sai kusan takwas da rabi duk da tsananin da akeyi wajen taron latti, banza Madiyam ta yi da ita don har yanzu haushinta take ji tare da wuce wa class ɗinsu don assembly ɗin ya watse.
SS 2 green nan ne class ɗin su Madiyam a kujera ta biyu layi na farko ita da wani yaro ana kiransa Abdallah, tsarin makarantar kenan macce da namiji ake zama don private school ce ba ruwansu da wata aƙida ko al'ada, ya yin da ita kuma Nauwara ke kujera ta farko duka anan layi na farko, sai da ta zauna sit ɗinta sannan ta ce,
"Nauwara haɗin mun littafaina duka ki bani".
"Wai lafiya Madiyam? Hakama meya faru?" Ta faɗa haɗe da juyowa tana kallonta, kauda kanta gefe ta yi kafin tace, "Ba komai, kawai bana son harka da wulaƙanci ne? Don na fahimci shi ya dodo yake son tata mun cikin mutane ƙara in kama kaina kafin hakan ta faru". To ƙare zancen tare da miƙa hannu ta jawo Jakar ganin ba tada biyar bata sai ma zubo mata idanuwa da ta yi cike da mamaki, ba tare data damu da hakan ba ta kwashe duka littafanta da sauran abubuwan karatunta dake ciki sannan ta miƙa mata jakar tana faɗin,
"Menene wai? Na faɗa maki dalilina to meye na zuba mani idanuwa kina kallo kuma?"
"Babu" Nauwara ta faɗa tare da karɓar jakarta tana tunanin ko me ya sa Madiyam ta yi hakan, don sam bata yarda da hujjar data bata ba.
Math suke da ita period ta farko da ta biyu, sannan Physics period ta uku kafin a fita breakfast, hakan ya sa Madiyam shiga tsoro da kuma tashin hankalin abunda zai faru idan ya Hisham ya shigo, don har ga ALLAH ba tada littafin Physics ma gabaɗaya saboda yanda ta tsani subject ɗin, sama-sama ta saurari fahimci bayanin da mai math ɗin keyi masu har ya fita ba tare data iya komai ba, ko mintuna biyar bai yi da fita ba Hisham ya shigo fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa, bayan sun gaishesa ya sake gabatar masu da kansa sannan ya shiga tambayar sunansu ɗaya bayan ɗaya suna faɗa masa har aka zo kan Madiyam, "You oyonbo, what is your name?" Ya faɗa don kusan tafi kowa haske cikin ajin, wani irin haushi ne ya kamata jin sunan daya kirata dashi haɗe da ɓata rai sannan ta ce, "Hauwa'u A dala". Ta faɗa tana turo baki, dariya ce ta kubcewa Abdallah deke kallonta ya yi saurin rufe bakinsa, "stand up" Hisham ya faɗa yana ɗauke fuska don dama tunda ya shigo ajin ya ji tsarin zaman nasu bai yi masa ba kwata kwata, don sai da ya ji wani abu ya dakar masa zuciya ganin Madiyam tare da wani zaune waje ɗaya, wataƙilma har jikinsu na gugar juna, nan take ya ji wani irin kishi ya rufesa amma sai ya yi saurin tausar kansa, yanzu kuma ganin irin kallon da Abdallah keyi mata yana dariya ya sa abun ya motsa masa, nan take ya shiga sauya masu wajen zama, inda ya tada namijin dake tare da Nauwara a sit ɗin gaba ya maido Madiyam a wajen, shi kuma Abdallah ya maida shi acan sit din baya tare da wani namijin, shi kuma ya ɗauke maccen dake tare dashi ya maida wani wajen tare da macce ƴar uwarta, nan take ya hautsine ajin gaba ɗaya ya canza tsarin zamansu zuwa macce biyu a sit ɗaya sannan namiji biyu a sit ɗaya a bayansu sai kuma wasu mata biyu a sit ɗin bayansu, ya kuma tabbatar masu da cewa daga yau haka zasu riƙa zama musamman idan lokacin period ɗinsa ce,
Ji Madiyam ta yi kamar ta aza hannu ta fashe da kuka ganin ta a sit ɗin gaba, abunda ta fi tsana a rayuwarta kenan amma ya zo ya mai dota a wajen tsabar mugunta, yana ganin yanda take faman turar baki tana wani jajjaye jikinta ga Nauwara ya yi banza da ita haɗe da fara karantar dasu, cikin gwanewa ya fara gabatar masu da topic ɗin da za su fara dashi haɗe da yi masu bayani a taƙaice sannan ya ce su fiddo littafansu su fara rubutu don dictation zai yi masu ba note a board ba, salon d'aya shiga dashi cikin ajin na sassauya masu wajen zama shiya haifarwa da ɗaliban mutuwar jiki haɗe da shiga taitayinsu, inda nan take suka fiddo littafansu ya fara yimasu dictation ɗin suna rubutawa in banda Madiyam da tayi zaunenta tana wasa da bironta a saman benci, "Stand up". Ya faɗa tare da cigaba da abunda yake yi ba tare daya kalleta ba har suka cika paper ɗaya suka juyo, sanin da ita yake ya sa ta miƙe tsaye tana jiran me zai ce mata, bai kula ta ba har sai daya gama sannan ya ɗari kai yana kallonta, cikin harshen turanci ya ce,
"Me yasa bakya rubutu kamar sauran ɗalibai?" Shiru ta yi masa bata ce ko uffan ba har sai da ya sake jeho mata tambaya ta biyu, " ina littafin ki?" Sannan ta ce,
"Ba ni da shi".
"Very good, wato irin ku ne ɗaliban dake cutar da iyayensu bakwa tsayawa kuyi karatu, kuna sa suna hasarar biya maku kuɗin makaranta da kuma na tara, a maimakon haka kamata ya yi ace kun zauna gida kun faɗa masu cewa ku bakwa son karatu wata ƙila aure kuke so, sai su hutar da kansu da kashe kuɗinsu a banza, no matter what kike ganin kina da kyau matuƙar baki tsaya kikayi karatu ba to kyanki na banza ne, beauty is nothing when the brain is empty, yan da kike ganinki a haka ilimi ne kawai zai taimakonki a rayuwa, all this ɗaukar kai da shan toka da fizge fizgen kai da kike yi ba zai taɓa helping ɗinki a rayuwa ba, so you better change before I decided to change you by force, and next time idan bakya da littafi kada ki shigo mun aji, idan kuma kika yarda na shigo bakya ciki to tabbas ki kuka da kanki don bazan ɗauki wannan shashancin a acikin class ɗina ba".
Ya ƙare zancen tare da ɗago kai yana kallon sauran ƴan class ɗin ya ce, "we can hold it next time". Ya ƙare zancen tare da ficewa ajin jin an tashi break....
*FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
Free page 7
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ko data iso gida yana zaune abunsa bakin gate saman kujera yana latsar waya, bata ce dashi uffan ba ta biya mai napep ta ƙarasa gidansu, ko mintuna biyar ba a yi ba sai ga napep ta aje Ailat itama, tana ganinsa ta sha toka haɗe da kallon mai napep ta ce, "Kaje wancan ya biya ka kuɗin ka" ta ƙare zancen tare da kwasar kayanta ta wuce ciki, ɗari biyar Haisam ya taso ya miƙawa mai napep ɗin don ya ji lokacin da Ailat tayi zancen haɗe da cewa yabar canjin da yake miƙo masa, Ailat kuwa data shiga gida dariya Ammie ta aza mata tana juya miyar da take haɗawa haɗe da cewa,
"Da na hanaki binsu ai laifina zaki gani, yanzu kuma kinga abunda hakan ya haifar maki da kanki, banda abinki kina ganin yanda ake ALLAH kama hannuna tsakanin shi da ita meya kaiki binsu? Gobe ai saiki kiyaye hakan".
Sai alokacin itama abun ya bata dariya haɗe da cewa, "kai wlh Ammie ya Haisam baida kirki, haka fa ya baromu wajen tsaye turus sai dai na fito naga ba mota, Aunty Ailat gwanin tausayi har da kuɗi ta bani na hau napep tana dariyar ƙarfin hali, ashe bin nan nasu da nayi itama ya bata haushi, ai kuwa anyi ɗan ba ƙari".
"Da dai ya fimiki, wato kinje ki kwafsa masu ke mai yaya, ai ga abunda yayan naki ya yimaku nan".
"Hmm ya Haisam yasan takan tsiyar, ALLAH da faɗa mun akayi bazan yarda ba saboda na fi sa ran ya Hisham ya yi hakan, ai kuwa ina ganinsa bakin gida na matse fuska na ce mai napep ɗin ya karɓi kuɗinsa hannun sa na shige abina."
"Bayan dai ansha wuya kenan!" Ammie ta faɗa tana dariyar tare da sauke tukunyar miyarta, tare suka ƙarasa aikin Ammie ta bar mata kitchen ɗin ta gyara ita kuma ta kwashe abincin takai kan dining ta jere sannan suka wuce wajen Sallah don ankira sallar magrib.
Da daddare bayan sun gama cin abincin ana falo Ailat sai fushi takeyi tana kumbura fuska don ko Abbie da Ammie ta bashi labarin shima dariya ya aza mata haɗe da kallon Haisam ya ce,
"Baka kyauta ba Haisam, gudan maman tawa zaka yiwa haka? Kƴalesa in sha ALLAH zan saya maki taki motar kin ji ko, amma kam ai game ɗin bata yi daɗi ba kuma ka tabbata ka bawa Najlah haƙuri ko a waya ne don baka kyauta ba ba gaskiya".
"Abbie nifa..?" Ailat ta tambaya tana turo baki, ranƙwashi Haisam ya kaimata akai kafin ta rufe baki haɗe da cewa, "Baza a bayar ba ɗin, bayan kuɗin da kika sa na biya mai napep har wani haƙuri kike so na baki?, to anƙi ɗin?" Ya ƙare zancen tare da miƙewa yabar wajen,
Shine fa take faman fushi da kowa ko magana ba tayi su kaɗai ke firarsu, daga ƙarshe ma bacci ya ɗauke ta wajen sai da Ammie ta tada ta ta koma ɗaki.
Dama tun cikin daren Haisam ya faɗawa Abbie zai je Giwa gobe ya dubo Madiyam da jiki Abbie ya bashi ATM card ɗin sa ya ce kafin ya tafi ya tsaya ya yi masu sayayyar kayan abinci da drinks ya wuce masu dashi, dama kuwa yana tunanin bai san yanda zai yi ba ATM ɗin sa na hannun Najlah, gashi sau biyu yana tura mata text message da
_Am sorry_
Kamar yanda Abbie ya ce yayi amma bata maido masa da amsa ba, hakan yasa ya ji duk ba daɗi, ko ba komai a yanda suke tare bai kamata ace ya yi mata hakan ba, gaskiya ce ya riga daya faɗa mata akan soyayyar Madiyam, to bai kamata ace kuma ya yi fushi ba duk abunda zata faɗa masa don ko waye ma zai iya hakan, watsApp ɗin sa ya hau yaga tana online ya tura mata saƙo da sticker ta ban haƙuri tayi banza dashi, sauka ya yi ya sake tura mata text message saboda ba ƙaramar shaƙuwa ce tsakanin shi da ita ba, just that shi ba soyayyar aure yakeyi mata ba shaƙuwace kawai tsakaninsu.
_I feel so bad about what did, I understand that I made a mistake and I am sorry about that, won't never repeat this again_
Murmushi ta yi bayan ta gama karantawa haɗe da tura masa saƙon itama.
_Ya wuce my feature husband, dama ni nasan kana so na, kawai soyayyar ƴar uwarka da kake ganin ta fini ya sa kake rufe idanuwanka akaina, ban damu ba kowa ma zaka so hakan bazai sauya soyayyar da nakeyi maka araina ba, saboda haka kayi haƙuri abunda ya faru ɗazu, i love you, i love you so much ya Haisam_ ta ƙare saƙon tare da turo kiss aciki, murmushi kawai ya yi haɗe da tura mata _Thank you_ sannan ya kashe wayar ya kwanta saboda ya samu ya yi sakkon tashi gobe.
Kasancewar Abbie zai je Abuja kuma ƙarfe 9:00 na safe jirginsu zai tashi ya sa daya yi sallar asuba bai koma bacci ba