saboda sai ya saukesa acan sannan zai wuce, a gefe ɗaya kuma farinciki ne kwance fal a zuciyarsa zai je yaga abur sonsa kuma abur ƙaunarsa wato Madiyam.
A gurguje Abbie ya gama karyawa don sai daya tsaya cika wasu document a computer sannan ya yi wanka ya gyara ya fito, koda ya fito falon ya yadda har sun gama karywa Haisam na zaune yana jiransa shima, hakan ya sa bai wani ɓata lokaci wajen yin karin ba ya ƙare suka fita, har bakin mota Ammie ta raka su haɗe da miƙawa Haisam ledar sauƙon Hisham data Mahmah don shi har ya manta dasu saboda zumuɗi,
"To Ammie sai na dawo".
"Adawo lafiya Haisam muna gaishesu".
"To Madam mu mun wuce, akula mani da mamana". Abbie ya faɗa shima riƙe da marfin motar, murmushi Ammie ta yi haɗe da cewa.
"A sauka lafiya Abbie, in Sha ALLAH zan kula da mamanmu tunda abun yau ba kara". Ta kai zancen haɗe da tura ƙofar ta rufe masa ganin har Haisam ya tada motar, dama inda sabo ta saba indai akan Ailat ne sam Abbie bai fiye yimata kara ba don itama sunan mahaifiyarsu gareta, sunan su ɗaya da Madiyam wato Hauwa'u.
Tafiyar mintuna ta kai Haisam airport ya ajiye Abbie, ya so ya wuce amma bazai iya ba har sai ya ga jirgin su Abbie ya tashi, ba ajima ba kuwa jirginsu ya ɗaga sannan ya juya ya shiga motarsa ya bar wajen shima,
Sai daya biya wata supermarket ya saisayi kayan abinci irin waɗanda ya san su Abbie zasu fi buƙata kamar su taliya, makaroni, samovita, comflacks, goldenmon, Madara, bonvita, sugar, fulawa da garin alkama aka saka mashi a Boot, haka ma drinks na gwangwani da na kwali duka saida ya siya da kayan kayan ɗin swan, ya biya ta wani bakery ya sayi su cake, dounout, meatfie, da dai sauran snacks da su chocculate sannan ya karɓi ƙatuwar ribar ice cream har guda uku da fresh youghout ƙwaya biyu sannan ya ɗauki hanya, yana tsakar tafiya Najlah ta kira wayarsa, sai alokacin ya tuna cewa basu ma yi maganar da ita ba, "Case" ya faɗa tare da ɗaga wayar da ya yi connecting da Bluetooth ɗin dake kunnensa, "Hello ƴar chana" don haka yake kiranta wata ran idan yana son tsokanar ta, murmushi ta yi haɗe da cewa, "yau wace safiya ce irin haka ka tashi da ita cike da farinciki? Ina kwana?"
"Lafiya klw ya kike?"
"Alhamdulillah, kana ina ne haka naji kamar ƙarar motoci?"
"Am sorry na manta ba muyi maganar dake ba jiya, ina kan hanya Abbie ya aikeni na kaiwa Abbu saƙo".
Wani irin abu ta ji ya dakar mata zuciya haɗe da runtse idanuwa kafin tace, "Ba wani nan, kai dai kace za kaje ka gano zaɓin ranka, wato ciwon son ya motsa maka?, Shikenan ALLAH ya kiyaye." Ta ƙare maganar tare da saka masa kuka,
"Oh my God! Najlah..." Kafin ya ƙara sa ya ji ta katse kiran, sake kira ya yi taƙi ɗagawa har ta tsinke, girgiza kansa kawai ya yi sannan ya cire Bluetooth ɗin dake laƙe a kunnensa haɗe da cigaba da tuƙinsa hankali kwance......
*****. *****. *****.
A ɓangaren Madiyam kuma tun ƙarfe shidda da rabi na safe Hisham ya shirya tsaf yana jiran ganin fitowarta, ganin har bakwai da rabi ta yi bata fito ba ya sa daya fito ya samu Mahmah a kitchen ya gaisheta haɗe da cewa, "Mahmah ina Madiyam ne? Ta shirya?"
"Shiga ka gani, har yanzu tana can kwance inda ta gama Sallah, nayi nayi da ita ta tashi amma taƙi, dama ko yaushe haka nake fama da ita in aka ce maka ana zuwa boko".
Juyawa ya yi ya shiga ɗakin ya iskota kwance a kan abun Sallah kamar yanda Mahmah ta faɗa masa, duƙawa ya yi yana kallon fuskar tata da yanda ta turo ɗan ƙaramin bakinta tana baccinta hankali kwance, kau da fuskarsa ya yi yana murmushi kafin ya juyo haɗe da ɗan bubbuga hannununta yana faɗin, "Madiyam, Madiyam ki tashi haka lokacin makaranta ya yi". Can cikin bacci ta sake turo baki haɗe da buge masa hannu tana faɗin, "Ni ka ƙyaleni Abbu bazan je ba".
"Ki tashi mana Madiyam lokaci na wucewa".ya faɗa da ƙarfi haɗe da cirata zaune, luuuu ta yi ta faɗo a jikinsa cikin muryar baci tana faɗin.
"Don ALLAH Abbu abari sai gobe." Wani irin yarr ya ji ajikinsa haɗe da saurin janye ta ta, ai kuwa ta koma ta kwanta abunta, miƙewa ya yi jikinsa a mace haɗe da buɗe fridge ya ɗauko ledar ruwa ɗaya masu mugun sanyi ya tsiyaye mata a fuska da jiki, wani iri tsalle ta yi haɗe da miƙewa saboda tsananin sanyin ruwan tana buɗe idanuwa, "Abbu..." Ta kasa ƙarasawa ganin Hisham tsaye a gabanta ɗaure da fuska, "ya Hisham ina kwana?" Ta faɗa a firgice tana murzar idanuwa, wata irin tsawa ya daka mata data sata barin wajen yana faɗin, "Kika sake bakwai da kwata ta ƙarasa baki fito ba saina ɓaɓɓallaki agidan nan, wato ke marar kunya abari sai gobe don kin rena mutane?". Ya yi kwafa tare da barin ɗakin, a tsaitsaye ya sha tea ɗin da Mahmah ta haɗa masa a nan waje yana jiran fitowar Madiyam, ko mintuna goma masu kyau ba a yi ba saiga Madiyam ta fito cikin shirin ta tsaf, kallo ɗaya ya yimata ya ɗauke kai haɗe da cewa, "Mahmah mun tafi."
"To Hisham, ALLAH ya tsare adawo lafiya".
Ɗan turo baki ta yi haɗe da cewa, "To ai ban karya ba".
"Comon wuce Malama, wani ya hanaki tashi da wuri ki karya? Gobe ma ki kwanta kina wannan baccin naki sai kace kasa ki gani in zan jira ki kiyi kari ne" ya ƙare zancen yana nuna mata ƙofa, juyawa ta yi ta kalli Mahmah taga gaba ɗaya ma hankalinta baya kanta, hakan yasa dole ta wuce gaba shi kuma ya bita a baya....
FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*
Free page 10
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Yana wannan tunanin kiran Najlah ya shigo wayarsa, da har bazai ɗauka ba sai kuma ya yi sauri ya ɗaga ganin kiran ya kusa katsewa,
"Hello Hisham".
"Na'am Najlah ya kike?"
"Lafiya klw Hisham, ya Haisam ya iso lafiya?"
"Lafiya klw, dama nasan don shi kaɗai kika kirani".
"Ba haka bane, kai ɗin ne ayita kiranka ba a samu, gabaɗaya ka yafe kowa".
"Ba haka bane, ya su Hajiya da Dady?"
"Duk suna nan lafiya, ka faɗa masa na kira wayarsa ban samesa ba".
"Ok. Riƙe wayar bari na kai masa ai muna kusa". Ya faɗa tare da komawa cikin gidan cike da son rabo Haisam a wajen, kamar dai ɗazun, yana shiga ya tadda Madiyam na ƙarashe robar icecream ɗin da take sha Haisam na goge mata gefen bakinta daya ɓata yana faɗin, "Cutie na gano bakin nan naki ya iya shan daɗi". Ita kuma tana dariya, ɗaure fuska ya yi kafin ya miƙa wayar haɗe da cewa,
"Matarka na magana, ta ce ta kira bata sameka ba".
Harararsa ya yi kafin ya karɓi wayar haɗe da cewa, "for where matata, kai ka ɗaura mun aure da ita?"
Yana kallon yanda Madiyam ta ɗan sha jinin jikinta tana kallon yanda Haisam ke magana, "Oh my God Najlah, Wai me yake damunki?" Ya faɗa tare da miƙewa ya bar ɗakin, harara Hisham ya dalla mata ita kuma haɗe da cewa, "ALLAH yasa naji kin ɓarewa mama wannan ƙarin bakin naki kina faɗin cikinki ke ciwo, sai na tattakaki a gidan nan, acici kawai" sannan ya fice shima ya bar ɗakin, cuno baki ta yi haɗe da cewa, "oho dai kanka ake ji" ta miƙe itama tare da har haɗa kayan dake gabanta ta saka cikin fridge.
A can ɓangaren Najlah kuwa kuka ta sakawa Haisam haɗe da cewa, "Duk abunda zaka yimun ya Haisam ba laifinka bane nawa ne don na ce ina sonka, kuma ka sani tsangwama da kyarar da kake yi mani wallahi baza su taɓa sa na sauya ba, ina sonka, ina sonka har iya ƙarshen rayuwata".
"Najlah kenan! ALLAH sheda ne akan ni ban yi maki komai ba, amma dai na faɗa maki gaskiya ni ina da wacce nake so, saboda haka ki bari alaƙar dake tsakaninmu taci gaba da wanzuwa a mutunce, idan kuma ba haka ba..." Tayi saurin katsesa haɗe da cewa, "me za ka yi? Yanke alaƙar ko kuma cire mani sonka a raina".
"Ko wane zai iya faruwa".
"Ƙarya kake yi Haisam domin dukansu ba huruminka bane, ni nake da damar daina sonka kuma na ciresa azuciyata idan naso haka, alaƙa kuma daga iyayenmu ne, matuƙar suna tare kai baka isa ka yanke ta ba".
"Ok! Gaskiya kika faɗa, amma ina so ki sani ba a so dole".
Dariya ta kwashe da ita dake nuna cike take da ɓaci rai kafin tace,
"Tabbas ba a yi Haisam, amma za a fara kanka in sha ALLAH, don sai na zame maka ƙarfe ƙafa ko kana so ko ba ka so, tun wuri ƙara kayiwa kanka ƙiyamullaili ka koyawa kanka da kanka soyayyata, in ba haka ba.."
"Sai kiyi me?" Shima ya katseta cikin jin haushin maganganunta, wata dariyar ta sake yi sannan ta ce, "Oh relax my feature husband, ba abunda zan yi illa ni da kai na in sa kaso ni by force".
"By force!"
"Yes upcouse, ko ka manta cewa ni macece kuma na cancanci a so ni kamar yanda ka faɗa da bakinka".
"Mtss..You are not serious Najlah". Ya faɗa yana ƙoƙarin kashe wayar.
"Kar ka fara, ai ni nakira ba kai ba sannan ko ka manta wayar ba taka bace? Kai mashi abussa akwai maganar da zanyi dashi". Ta faɗa cikin gadara da nuna isa, tsintar kansa ya kasa yi da yimata musu har ya ya kaiwa Hisham dake ɗaki wayar, tana jin alamun zai bashi ta ce,
"Wait my feature husband, yaushe zaka dawo?"
"Wannan matsalar ni ta shafa ba ke ba, saboda haka babu ruwanki da ranar da zan dawo". Ya ƙare maganar cikin jin haushi haɗe da miƙa masa wayar, ba tare da sanin haka ba ta ce "Bye tunda baza ka faɗa mun ba, ka kula mani da kanka sosai i love you" ta ƙare maganar haɗe dayin dariya tana jefo masa kiss a wayar, da sauri Hisham da har ya kai wayar a kunnensa ya yi saurin janyewa yana kallon Haisam da zai fita ya ce,
"Ungo wayarka ba a gama baka saƙonka ba fa".
Banza Haisam ya yi dashi ya fice abunsa yana tunanin yanda zaiyi da Najlah ta raba shi da zancen soyayyar nan ta ta da take iƙirarin tana yi masa, a can ɓangarenta kuma dariya ta yi jin abunda Hisham ya faɗa tare da kashe wayar, duk da a zuciyarta tana jin haushin abubuwan da Haisam ke yi mata amma a zahiri tana matuƙar tsintar kanta cikin nishaɗi aduk lokacin da suke haka dashi, tana da ƙwarin guiwa sosai akan cewa tunda har yana saurarenta to tabbas wata rana zata yi winning heart ɗinsa, musamman idan ta tuna yanda take dashi da yanda tasan wasu halaye nasa na jin tausayin mace, shi yasa baza ta taɓa hasala ko kuma yin zuciya dashi ba don yana faɗa mata maganganu, sannu a hankali wata rana zai daina.
"Wai ni kam baza kuzo kuci abinci ba Hisham? Sai faman yawo da hankali kuke yimun in wannan ya yi nan wannan ya yi can, kun kasa zaunawa kuci abinci kuma nasan dukkaninku yunwa na damunku" Mahmah ta faɗa tsakar gidan ranta a ɓace, hakan ya sa Haisam wuce wa ya zauna yana bata haƙuri, cigaba da faɗa ta yi ganin shi Hisham yaƙi fitowa, tasan halinsa kar tunda bai fito ba to lallai bai da sha'awar zaunawa aci abincin tare, hakan yasa ta ce Madiyam ta zuba masa nasa a plate ta rufe ta ɗauki cokali da ruwa takai masa a ɗaki, shi kuma Haisam ta zuba mashi na shi ta tura masa a gaban shi tana faɗin,
"Ka dena biyewa waccan ɗan uwan naka, zai iya kai dare a haka baici komai ba indai ba nayi masa magana ba, nayi faɗa har na gaji amma ya kasa dena wannan halin nasa".
Murmushi ya yi haɗe da cewa, "A yi haƙuri Mahmah zai dena ne in sha ALLAH, ai yunwa ba uwar kowa bace balle ta raganmasa". Ya ƙare zancen yana kallon yanda Madiyam ke loda abinci cikin plate ɗin tana turo baki har tana sake dannawa, wani murmushin ya saki saki haɗe da cewa, ashe akwai ƙura yau, cikin zuciyarsa,
Har zata fita ya yi tunanin wulaƙancin Hisham ya kira Madiyam ya ce ta rage abincin, "a'a ta kai mashi hakan, tun safe ruwan tea kaɗai ne acikinsa ƙara yaci ya ƙoshi". Mahmah ta faɗa tana ɗauko wani haɗaɗɗen zoɓon data sake haɗa masu ta ajiye mashi a gabanshi, ta ce Madiyam ta jeka takai abincin ta dawo ta ɗaukar masa nashi soɓon da ruwa.
A natse ta tura ɗakin tare dayin sallama sannan ta shiga ta kai abincin ta ajiye masa ta koma ta ɗauko ruwan da zoɓon ta kawo masa ta ajiye, har lokacin ko motsawa bai yi ba daga inda yake zaune yana latsar wayar dake hannunsa, sai daya ga zata fita sannan ya ce,
"Azo mun abincin annan". Ya nuna mata gefensa saman katifar ba tare daya ɗago ya kalleta ba, sai daya ga zata aza zoɓon da ruwan akai sannan ya ɗago kai yana faɗin, "A ina kika taɓa ganin haka?"
"Yi haƙuri" ta faɗa shaye da toka sannan ta saukar dasu ƙasa, abincin dake cikin plate ɗin daya buɗe ya ga yawansa ya ƙurawa idanuwa haɗe da ɗago kai ya kalleta tana ƙoƙarin fita ya ce,
"Zo nan!" Jin tayi kamar ta saka ihu don gabaɗaya ta tsargu da wuɗannan abubuwan da takeyi mata, dawowa cikin ɗakin ta yi haɗe da cewa
"Gani".
"Waya zubo wannan abincin, ke ko Mahmah".
"Ni ce" ta faɗa kanta na sunkuye a ƙasa, ɗago kai ya yi ya kalleta haɗe da sakin murmushin mugunta sannan ya ce, "Saboda gani jaki ko? Shiyasa kika kofi mun wannan abincin haka tunda an faɗa maki ni acici ne kamar ki, to zauna ki cinye sa". Sai alokacin ta ɗago kai kamar za tayi kuka ta ce,
"To ka kawo rago maka, ni na ƙoshi bazan iya ci ba".
"Baki isa ba, zauna nan sai kin canye sa" ya ƙare maganar tare da nuna mata ƙasan wajen shaye da toka, ƙyaƙƙyafta idanuwa ta farayi tana so tayi kuka ya daka mata tsawa haɗe da cewa, "duk kika samun kuka sai na ɓallaki a wajen, meye ɗazu banganki kina ci ba ko gajiya bakinki ba ya yi, ai sai ki ƙara da wannan" ya dangware mata plate ɗin abincin aƙasan, yanda ya yi da huska ba karamin tsoratata ya yi ba, hakan ya sa dole ta zauna tana cin abincin tana ƙwalla, a zahiri za kaga kamar idanuwansa akan wayar suke amma gabaɗaya hankalinsa nakanta, yanda take cin abincin da yanda idanuwanta suka sauya kala cike da ƙwalla ba ƙaramin burgesa ya yi ba, ganin ta ɗago kai ya sa ya yi saurin maida idanuwan nasa ga wayarsa yana sake ɗure fuska, "Ya Hisham wlh na ƙoshi, wlh zan iya yin amai".
Banza ya yi da ita ya ci gaba da latsar wayarsa, hakan ya sa taci gaba da tura abincin yana kallonta ta ƙasan ido har sai da ya ga ya kai daidai yanda zai iya canyewa sannan ya ce,
"Rufe ki tashi ki bani waje".
Ba musu ta jawo ɗayan plate ɗin ta rufe sannan ta fita tana yi masa ALLAH ya isa a zuciya, dai dai lokacin Haisam shima ya gama ya fito, kallonta ya yi haɗe dayin dariya ganin yanda ta fito tana kumbura fuska ya ce,
"Ya akayi cutie!? Ko ke yasa kika cinye abincin?"
"Eh, kuma fa na faɗa masa cewa na ƙoshi, wlh da na sani bazan kai masa abincin ba sai dai Mahmah takai masa".
"Eu'uhm rufe bakinki kar ya jiki, haka yake yiwa Ailat itama, don haka daga yanzu ki kula".
"Kar ma ta kula". Ya faɗa riƙe da plate ɗin ya fito dasu, da sauri ta shige ɗaki Haisam ya bita da dariya yana kafin ya maido kallonsa ga Hisham ya ce, "ALLAH Hisham ka rage mugunta, ina laifin wanda ya baka abinci kaci ka ƙoshi?"
"Babu shi, ai shiyasa kaga nima na sata taci ta ƙoshin".
Mahmah dake tsakar gida ta girgiza kai haɗe da amsar plate ɗin tana cewa, "ALLAH ya maka maganin wannan hali naka, da na sani ai sai a ƙyaleka kayi ta zama da yunwarka tunda haka kake so" ta ƙare zancen tana buɗe plate ɗin, ganin ba komai ya sa ta dena faɗa da takeyi, don a tsammanin ta baici abincin ba, shi kuma Haisam ya zata yanda yake wa Ailat yasa ta canye abincin duka haka ya yiwa Madiyam, abunda bai sani ba rabi ta ci shi kuma ya canye rabin amma ya fito yana wani matse fuska.....
_Afuwan not edited_
*FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
Free page 11
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ɗago kai Mahmah ta yi ta kallesa ganin ba komai cikin plate ɗin haɗe da cewa, "Au ashe ka ci"
"Eh Mahmah" ya faɗa tare da sha fa kansa cike da jin kunya sannan ya wuce ɗakinsa.
Murmushi ta yi haɗe da wucewa kitchen tana mai addu'a ALLAH ya sa hasashenta ya zamo gaskiya, da tafi kowa jin daɗi saboda gabaɗayan su renonta ne kuma tana jin soyayyar kowanensu a ranta,
Yau Haisam ya so wucewa gida saboda ganin Abbie baya nan don kar ya bar su Ammie su kaɗai a gida, amma da ya yi waya da ita sai ta ce indai bai taso ba ya bari sai gobe don ba ta so marece yayi masa a hanya saboda yanayin da ake ciki yanzu na rashin tsaro, sosai hakan ya yiwa Haisam daɗi don dama haka yake so, faɗar kalar farinciki da kuma shauƙin da yake jin kansa aciki kuwa bazai misaltu ba, ko ba komai zai kasance tare da Madiyam ɗin sa daga yau har gobe da safe kafin ya wuce, kuma hakan zai bashi damar bayyana yanda yake fama da dakon soyayyarsa ko da baza ta fahimta ba, ya san sannu a hankali wata rana zata fahimci hakan, yana gama wayar da Ammie ya ga Madiyam ta fito cikin shirinta na uniform za ta wuce islamiya, ƴar gayaran murya ya yi haɗe da cewa, "cutie makaranta zaki je?"
"Eh ya Haisam."
"Bari nazo na raka ki". Ya faɗa haɗe da miƙewa daga kan kujerar da yake sannan ya bi bayanta, Kallonta ya yi tun daga sama har ƙasa yana yaba yanda kayan suka yi matuƙar karɓarta haɗe da cewa,
"Tubarkallah cutie kayan nan sunyi maki kyau, sai kace ba na islamiya ba".
"ALLAH ya Haisam?"
"Sosai kuwa, yayanki bai taɓa faɗa maki ba?"
"Tab..ya Hisham ɗin? Ai sai dai na mutu in sai ya ce nayi kyau, wanda baida aiki kullum sai kushe ni"
"Jininku ne bai haɗu ba shiyasa, ai ni babu wacce nake ganin kyanta da kuma yaɗuwar ta a duniya sama gake ƴar ƙanwata, shiyasa duk lokacin da nake tare dake nake jin wani irin daɗi tare da tsintar kaina cikin farinciki marar misaltuwa". Dariya ta saki haɗe da ce
"ALLAH ya Haisam?"
"Sosai cutie, ke baki ga hakan ba."
"Na gani mana, ai shiyasa nima nake jin daɗi idan ka zo tare da tsintar kaina cikin farinciki sosai"
"Da gaske cutie?"
"Wlh kuwa ya ya Haisam"
"Faɗa mun naji me yake saki cikin farinciki idan na zo" Ya faɗa yana kallonta cike da so da ƙauna, sai da ta yi ƴar dariyarta dake matuƙar tafiya da hankalinsa sannan ta ce,
"Saboda yanda kake sona, kake zauna wa kayi fira dani, kake sake mun fuska, kana siyo mun abubuwa da kuma yanda ba ka sakani kuka, amma shi wancan ya dodo ɗin ba abunda ya gwane kamar ya sakani kuka ko ya yi mun mugunta". Tayi zancen haɗe da turo baki, murmushi ya saki tare da cewa.
"To me yasa yake yi maki hakan?"
"Wai bana jin magana yake cewa, don ALLAH da gaske ne ya Haisam bana ji?"
"Gaskiya a'a, cutie ɗina na jin magana sosai." Dariya ta saka haɗe da cewa, "yauwa, dama na sani kawai yana faɗa ne don baya so na!"
"To ni fa?"
"Kana so na mana shiyasa ba ka cewa haka," shafa kansa ya yi yana kallonta cikin idanuwa haɗe da jin wani irin shauƙin sonta da ƙaunarta na sake fizgarsa kafin yace,
"Tabbas ina sonki sosai Madiyam, duk duniya banda Abbie da Ammie babu wanda nake so sama dake, zan iya ƙarar da rayuwata duka saboda in dinga ganinki cikin farinciki tare da wannan kyakkyawan murmushi akan wannan fuskar taki a koda yaushe". Ya ƙare zancen yana nuna fuskarta da yatsansa, cike da jin kunya ta sa tafin hannunta ta rufe fuskar tana cewa, "kai ya Haisam, kar kasa na fara yiwa ƙawayena kuri akan nafi kowa sa'ar samun yayan da ke matuƙar so na aduniya".
"Ki faɗa da kyau duk inda kika shiga cewa yayanki yafi kowane yaya aduniya son ƙanwarsa, don tabbas zan iya bada rayuwarta ga duk wanda ya nemi taɓa mani ke".
Dai-dai lokacin suka kawo bakin gate ɗin makarantar tasu ya ja ya tsaya haɗe da cewa, "To my cutie, Bari na tsaya anan, ayi karatu lafiya, kuma ki kula mani da kanki"
"To ya Haisam in sha ALLAH"
"Yauwa, na manta ban faɗa maki cewa ba ina sonki sosai"
"Nima ina sonka sosai ya Haisam". Ta faɗa tare da rugawa ta shige ciki saboda kunya da ta ji, wani irin jiri ya ji ya ɗebesa jin kalmar data fito daga bakinta haɗe da jin wani irin farinciki marar misaltuwa na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma ruhinsa, wai da gaske ne Madiyam ɗin sa na son sa? kuma ita da kanta ke faɗar hakan da bakinta? Ya tambayi kansa haɗe da zaunawa daga gefen makarantar yana murmushi, "what a happy moment!" Ya faɗa a fili haɗe da sakin dariyar dake nuna tsantsar farincikin da yake ciki.
Ya jima a zaune wajen kafin ya miƙe ya nufi wajen Abbu da ƙafa, don ba wani nisa ne da inda shagon Abbu yake da makarantar ba, haka ma tsakanin makarantar da gidansu Madiyam ɗin ba wani nisa bane sosai, shiyasa ma da ƙafa ma mutum zai iya zuwa makarantar.
Hisham kuwa tun daya koma ɗaki ya yi kwanciyarsa, babu abunda yake yi illa tunanin Madiyam da yanda take motsa ɗan ƙaramin bakinta ɗazu da yake kallonta da tana cin abinci, dariya ya saki hango lokacin data turo bakin haɗe da janyo wayarsa daya ɗauke ta hoto lokacin ba tare data sani ba, hoton ya jawo haɗe dayin zooming ɗinsa ya sake sakin wata dariya yana kauda kansa gefe ya ce "trouble girl" A hankali Sannan ya gogesa zuwa trash box, dama haka yakeyi duk lokacin da take yin wasu abubuwan dake saka shi dariya, yakan saita wayarsa ya ɗauke ta hoto ba tare da kowa ya fahimci hakan ba, wanda a zahiri idan