Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
dogon lokaci tsakanin sallolin yanzu saboda sauyawar lokaci, nan ma a zaune Madiyam ta sake yin sallar ishah ɗin jiki a mace, tana gamawa ta koma tayi baya ta jingina da kujerar dake bayanta, ita kuma Mahmah ta miƙe ta je kitchen tana ɗauko abincin da za ayi na dare tana jerewa akan dardumar dake can gefen kujeru inda suka saba cin abinci gaba ɗayansu, Madiyam kuwa tuni baccin wahala ya soma ɗaukarta, tana jin sallamar Abbu ta wartsake tare da fashewa da kukan da tunɗazu take tanadinsa kafin ya ƙaraso, dai dai lokacin kuma aka kawo wutar nefa data haske gaba ɗaya falon dake ɗauke da ƴan madaidaitan kujeru saiti ɗaya masu kyau da kuma fridge a gefe, da sauri Abbu ya ƙaraso wajen don Mahmah bata faɗa masa komai abunda ke faruwa ba ganin yanda ya shigo gidan a gurguje yana so ya samu jam'i. "Madiyam ɗin Abbu! Wa ya taɓa mun ke haka kuma?, me aka yiwa yarinyar nan?" Ya faɗa yana kallon Mahmah ganin yanda idanuwanta suka kumbura, har za tayi magana sai ga Hisham ya shigo haɗe dayin gyaran murya ya ce, "Ba abunda akayi mata Abbu, wajen rashin jin maganarta ta je ta faɗa a kwalbatin ƙofar gida, shine fa ta jima ƙafarta". Ya ƙare maganar tamkar bashi keyi ba haɗe da zaunawa saman kujerar dake facing ɗinta yana jifarta da wani irin kallo dake nuna ki shiga taitayinki, sai data haɗiye wasu yawu masu ƙarfi haɗe da tsaida kukan da takeyi sannan ta tura kanta cikin jikin Abbu daya rungumota. "Haba mamana, meyasa kikeyin abunda zai wahalsheki haka?" "Abbu to ba shi bane!" Ta faɗa can cikin jikin Abbu data tura kanta, "Waye? Hisham ko?" Ya tambayi kansa tare da bawa kanshi amsa yana kallon Hisham. "Eh Abbu". "Ahaf dama ai nasan kwanan zancen, yanda na ji yayi karaf ya amshe zancen daga shigowarsa ya sa nasan shiga taɓa mani ke, ƙyalesa ni dama tunda ya kirani a waya haɗe da cewa yau zai dawo nasan sai anyi ta tsakanin ke dashi, yi haƙuri zanyi masa faɗa bazai sake ba kin ji ko?" "To Abbu, bacci zanyi" ta faɗa a shagwaɓe tana ƙara narke masa a jiki, ɗagota ya yi ya ce, "Kinci abinci ne?" "Ai Mahmah bata bani ba, kuma yunwa nake ji sosai". Ɗago kai Abbu ya yi yana kallon mama dake zaune gefe tana kallonsu haɗe da cewa, "yanzu fisabilillahi kinsan halin da yarinyar nan ke ciki zaki bari ta kawo wannan lokaci bata ci abinci ba, haba maman Hisham wannan wane irin abune haka?" "To ai basu jima da dawowa gidan ba daga wajen Sadi mai ɗori, kuma suna shigowa Sallah muka tsaya yi daga ni har ita, da ina yimata magana ma ƙyaleni tayi balle naji ko zata ci abincin, gata nan zaune agabanka in ƙarya nayi mata". "Wai haka ne mamanah". "Abbu to ƙafar kemun ciwo fa, ALLAH wancan Sadin mugune, dafa reza biyar ya tsaga mun ƙafata". Gaba ɗaya buɗe baki sukayi haɗe da cewa, "Reza biyar Madiyam?" Lokaci ɗaya, in banda Hisham da tun ɗazu takaici ya sashi fiddo wayarsa yana latsa, juyowa Abbu daya gama dudduba ƙafar Madiyam ya yi haɗe da kallon sa ya ce, "Yanzu don ALLAH Hisham a gabanka Sadi zai fiddo reza har biyar ya tsattsagewa ƙanwarka ƙafa haka..." Bai ƙara sa ba da sauri Madiyam ta ɗora hannunta akan bakinsa haɗe da ƙwalo kyawawan idanuwanta ta ce, "Kayi shiru Abbu, ai shine ma ya siyo rezojin fa ya kawo masa, kuma ya riƙeni har ya gama yimun tsagar, baka ji ya yi shiru ba? ai shima yasan gaskiya na faɗa". ta ƙare zancen tana turo baki haɗe da naɗe hannayenta saman ƙirji, ɗago kai Hisham ya yi tare da kallon yanda take maganar tamkar wata sakarya shi Abbu na biye mata, girgiza kai kawai ya yi tare da maida kansa ƙasa yana ci gaba da latsar wayarsa don baya son ya shiga shirginta yanzu, amma yana addu'a ALLAH yasa cikin daren nan ta shiga nasa sai ya koya mata hankali, Abbu kuwa lallaɓa ta ya yita yi har ya samu ya riƙata suka nufi wajen cin abincin yana yi yana yimata sannu. Cike da natsuwa kowa ke cin abincinsa da Mahmah ta zuzzuba masu a plate amma banda Madiyam data karɓi wayar Abbu tana faman buga game tana dariya, a gefe kuwa sai faman mutsunniya takeyi da ƙafar tata mai ciwo ta rasa inda zata ajiyeta, Mahmah tayi magana har ta gaji ta ajiye wayar taci abinci amma ta yi banza da ita, data nemi ɗaga mata murya Abbu ya dakatar da ita da hannu dole ta saka mata idanuwa, ai kuwa kamar an bugo ƙafar Madiyam sai cikin abincin Hisham, dai dai lokacin kuma wani yaro ya shigo ya ce ana yiwa Abbu sallama, dama ya gama cin abincinsa don haka ya miƙe ya fita, Hisham kuwa da tuni ransa ya gama ƙololuwar ɓaci akan abunda Madiyam tayi masa Abbu na fita ya fizge wayar hannunta tare da sakar mata wani mugun ranƙwashi akai yana faɗin, "Ba kya ganin abunda kika yimun ne zakiyi tamkar baki san kinyi ba, halama ke makauniya ina ce? to wallahi na rantse sai kin cinye abincin nan ko nayi maki ɗan banzar duka a gidan nan". Ya ƙare zancen haɗe da juye sauran abincin nasa acikin plate ɗin dake gabanta. "Kamun daidai Hisham, ALLAH ya yi maka albarka". Mahmah ta faɗa haɗe da miƙewa tana tattara kwanonin abincin ta bar falon a fusace, wage baki Madiyam ta yi tana kallon ƙofar fita ko Abbun nata zai shigo ya bala'in daka mata tsawar data sata juyowa a razane ta saka hannu ta fara cin abincin, ci takeyi tana hawaye har ta ci fin rabi, ba tare data ɗago kan ba ta ce, "ya Hisham na ƙoshi" Banza ya yi da ita wanda hakan yasa ta cigaba da cin abincin har saida ta cinyesa tas sannan ya miƙe yabar ɗakin ransa a ɓace, "A'ah, ina kuma za kaje ga wani na zubo maka?" Mahmah ta faɗa dake riƙe da plate ɗin wani abincin data sake zubowa, "Na ƙoshi". Ya bata amsa a taƙaice tare da barin gidan, yana fita ya samu Abbu na sallama da baƙin nasa, bayan ya wuce ya riƙo hannunsa haɗe dayin murmushi ya ce, "Hisham ya bautar ƙasar, angama lafiya ko?" Ya ƙare maganar yana janyo hannunsa suka dawo cikin gida, sai da suka zauna akan wani benci dake tsakar gidan tukuna Hisham ya ce "Lafiya klw Abbu, mun sameku lafiya?" "Lafiya lau Hisham, ya mutuniyar taka? Wato daga dawowa saida kukayi halin, ko dai ƴar gida za ayi Hisham?" Abbu ya faɗa yana kallonsa haɗe dayin dariya, ba tare da Hisham ya ce komai ba ya sadda kai ƙasa, shi kuwa Abbu dama da zolaya ya faɗa don ya san Hisham da Madiyam tamkar wayar positive ne da negative, baza su taɓa haɗuwa ba, wata firar ya ɗauko masa suka ci gaba dayi har kusan sha biyu na dare ya yi sannan sukayi sallama ya wuce ɗakinsa dake can gefe shi kuma Abbu ya wuce cikin nasu ɗakin, ko daya shiga har Madiyam data gama cin duka agun Mahmah saboda kukan banzan data aza mata tayi bacci, ɗaya ɗakin nasa dake laƙe cikin falon ya nufa bayan ya tofawa Madiyam ƴa tilo a wajensa da yake matuƙar ƙauna addu'a haɗe da yiwa Mahmah seda safe. *****. *****. ***** A ɓangaren Haisam kuwa yana jin Hisham ya katse masa kira ya yi dariya haɗe da cewa, "Dama nasan za a rina Hisham, indai kan zancen Madiyam ne bazaka taɓa tsayawa ka saurara ba, na rasa me yarinyar nan tayi maka ka fiye tsangwamarta da yawa, gashi kuma yayanka na masifar sonta, bansan ya zamuyi dakai ba idan kasan haka!" Ya ƙare zancen tare da kwashewa da dariya yana faɗin "case" sannan ya jefa wayar cikin aljihun dake gaban rigarsa ya miƙe ya nufi cikin toilet ɗin dake cikin ɗakin nasa ya ɗauro arwalar magrib tare da ficewa cikin ɗakin, yana fitowa Abbie wato mahaifinsa na fitowa daga cikin ɗakin nasa shima, da alama shima arwalar ya yi ya fito zuwa Masallaci saboda yanda yake ƙoƙarin faman saukar da hannun rigar tasa, ɗan russunar dakai Haisam ya yi haɗe da cewa, "Barka da marece Abba?" "Barka Haisam". Abbie ya faɗa yana miƙa masa hannu tare da saƙalo kafaɗarsa suka shiga saukowa daga kan upstairs ɗin gwanin ban sha'awa, murmushi Ammie dake fitowa daga kitchen ta hangosu tayi tana faɗin, "A'ah, kike father like son, wato dai na fahimci kun haɗewa yarona kai ko tunowa bakwai dashi ko, ALLAH sarki Hisham bawan ALLAH." "Mu kuma fa?" Abbie ya faɗa lokacin da suka sauko tare da janyo Ailat dake kusa gareta ya yi mata kiss a goshi yana faɗin, "Ummina bye bye, munyi masallaci" murmushi Ailat da baza ta wuce shekaru goma sha shidda ba a duniya tayi haɗe da cewa, "ok Abbie bye, ALLAH ya kiyaye." "Amin" Haisam ya faɗa yana mangare mata kai sannan yabo bayan Abbiey dake dariyar Ammie dake faɗar, "kuma bayin ALLAH ne amma ba kamar yarona ba Hisham, shi wannan ja'irin yaron naka ba abunda ya sani inba tsokana da ɗaukar magana ba, duk ya bi ya hana autata sakewa." Ta ƙare zancen tana ƙoƙarin kai masa duka ya yi saurin ficewa daga falon shima yana dariya, juyowa ta yi ga Ailat data turɓune fuska haɗe da dafe ƙeyar kanta da Haisam ya mangare ta rungumota tana dariya haɗe da cewa, "Srry my Baby, ƙyalesa ni nasan hukuncin da zanyi masa kinji ko?" "Ammie ni dai don ALLAH ya Hisham ya dawo nan shi kuma ya Haisam ya koma can gidan Abbu." "Tirƙashi! Kar ma ki sake Hisham yaji wannan zancen a bakinki ku ɓata, ai shi yafi jin daɗin zamansa acan saboda baya son hayaniya, shiyasa tun yana ƙarami yabi Abbunku a can." "To amma ai Madiyam nada rashin ji da karauniya kuma." "Ai shiyasa basa shan inuwa ɗaya dashi, wlh Ni har tausayi take bani don ba ƙaramin takurata yakeyi ba, gashi itama Mahmah ɗin na biyesa suyita takurata." "To Ammie ki ɗaukota ta dawo nan mana, nima kinga na samu ƙanwa muriƙa zuwa makaranta tare ko." "Ai Abbu bazai yarda ba, sai dai tazo mana hutun data saba zuwa, Abbiey ma yaso haka amma idan mukayi hakan kamar munyi amai mun lashe ne." "Ammie to..." Kafin ta ƙara sa Ammie ta katseta haɗe da cewa, "oh my God Ailat, nifa matsalata kenan dake tambaya ta yi maki yawa, maza jeki kiyi Sallah kafin Abbie ya dawo ya iskoki bakiyi ba, kinsan sai kinsha faɗa sosai ko?" Tmɓure fuska ta yi haɗe da cewa, "Ammie idan zan kwanta zan haɗe da ishah duka nayi." "What..?" Ammie ta faɗa tana zaro idanuwa kafin tayi kanta kamar zata doketa, dariya Ailat ta yi sannan ta riga da gudu ta wuce ɗakinta ta faɗa toilet, bayanta Ammie ta bi har sai da taga ta fito ta shimfiɗa abun Sallah haɗe da saka hijab ɗinta ta tayar sannan ta bar ɗakin nata itama ta wuce nata don ta samu ta watsa ruwa kafin su Abbie su dawo don fashin sallah takeyi... *FIL HUB (Acikin so), littafin kuɗi ne, ki biya ₦500 kacal don ki mallaki naki, ƴar uwa ki gujewa cin haƙƙin ƴar uwarki dake neman ci da guminta domin faranta maku👏 ga masu buƙatar wannan littafi sai zaku tura kuɗinku ne ta wannan account no, 0434776437 gt bank Balkisu sani kaura ko kuma katin waya na mtn da shedar biya duka ta wannan lambar, 07040402435* mungode *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* Free page 3 *FIL-HUB*♥️ (Acikin so💘) Paid Book: N500 Written by Billy s fari💎 ______________________________ Ammie na cikin ɗaki tana shiryawa ta jiyo sallama daga falo, amsawa ta yi haɗe da gyara mayafin doguwar rigar data saka ta feshe jikinta da turarukka masu ƙamshi sannan ta fito fuskarta ɗauke da murmushi gani Najlah tsaye a tsakiyar falon. "A'ah wai dama kece muryar taki ta ɓacemun?, zo ki zauna kin wani tsaya anan sai kace baƙuwa". ta ƙare zancen tare da ɗaukar remote ɗin dake kan center table ɗin dake tsakiyar makeken falon ta kunna tv sannan ita ma ta nemi waje ta zauna, murmushi Najlah dake kallon irin kyau da haɗuwar da Ammie tayi ta yi kafin tace, "Ammie ina wuni?" fuskarta a sake ta amsa da "Lafiya klw Najlah, ya su Hajiya Raheema, da Zeenatu duk suna lafiya?" "Lafiya klw suke, gashi suka ce na kawo maku". Ta ƙare maganar tana ajiye mata wata ƙatuwar leda agabanta, sai da Ammie ta ɗan buɗe ledar ta ga abunda ke ciki sannan ta ce, "Ko ƴan ƙasar Parisa sun dawo ne?" "Su yaya Irfan?" "Eh, ko ba satinnan Hajiya Zeenat ta ce zasu dawowa ba?" "Eh wannan satin ne, amma yaya Irfan kaɗai ne zai dawo, shi ya Naufal ya ce sai ya biya ta indiya wajen budurwarsa tukuna, Dady dai ne yadawo". Ta yi zancen murmushi ɗauke akan fuskarta, murmushin itama Ammie ta yi haɗe da cewa, "To angode sosai, ina ruwan Naufal, inaga ai duk sai ya doke yaran nan ya yi aurensa ya huta tunda su sun tsaya shashanci, badai kamar wannan babban kobon Haisam". Faɗaɗa murmushin dake kwance akan fuskarta tayi jin Ammie ta ambato sunan marurun zuciyarta haɗe da sinne kai tana wasa da ƴan yatsun hannuwanta, "Kai Ammie, ai shima zai yi in sha ALLAH, kwana biyu ma na dena ganinsa?" "Ko? Ai kuwa yana nan, halan ya dena shiga wajen su Hajiya?" "Eh, tun bayan tafiyar Dady Umrah na dena ganinsa". "Yanzu nan kina ganinsa shi da Abbie sun shigo tunda angama sallolin ishah, ya Dadyn naku ya dawo lafiya?" "Lafiya lau, yana gaisheku". "Muna amsawa, ai yanzu ne zaki ga Haisam agidan naku tunda ya dawo". Tana rufe baki yana shigowa falon bakinsa ɗauke da sallama, ɗaure fuska ya yi haɗe da kau da kansa gefe ganin Najlah yana faɗin, "Ammie na dawo". Tare da haye upstairs ɗin ya nufi ɗakinsa, "Haisam, ina Abbie naga ka shigo kai kaɗai". Ammie ta faɗa haɗe da juyawa tana kallonsa, ba tare daya juyo ba daga hawan upstairs ɗin da yakeyi ya ce, "Yana can tare da Dady suna gaisawa?" "To halama baka ga Najlah bane zaka wuce baku gaisa ba? Ko baka ji gaisuwar da takeyi maka bane." Oh my God ya faɗa cikin zuciyarsa ganin Ammie na neman kwafsa masa haɗe da juyowa daga kan matattakalar fuska a ɗaure ya ce, "Sannu Najlah banji bane, kina lafiya?" Ƙin amsa shi itama tayi don ya bala'in bata haushi, ko don yaga tana son shi ne shiyasa yakeyi mata haka? Tayi maganar cikin zuciyarta haɗe dajin haushin kanta, shi kuwa ɗage kafaɗa ya yi irin ko ajikinsa tare da juyawa ya ƙarasa hayewa sama abunsa, Muryar Ammie ta ji data dafata ganin yanda fuskarta ta sauya tana cewa "Kiyi haƙuri Najlah, kin san halin yayan naki, ni kaina wani lokacin idan ya yi wani abu sai naga kamar bashi ba, shi da Hisham kamar suna musayar halaye nake gani wani lokacin, don wannan halin na Hisham ne ba nasa ba." "Ai ƙwanda ya Hisham Ammie da Haisam, sam shi baya da wulaƙanci irin na ya Haisam ko don yaga ina son shi shiyasa." Ta ƙare maganar tana share ƙwallon daya zo mata, rungumota Ammie ta yi haɗe da cewa, "Ba haka bane Najlah, kiyi haƙuri zanyi masa magana kin ji ko?" "To Ammie, bari na wuce" Ta miƙe tare da gyara mayafinta, dai dai lokacin Ailat ta fito itama ta watso ruwa earpiece laƙe a kunnenta ta nufi kitchen ba tare data kallin inda Najlah ɗin take ba, "Ke zo nan". Ammie ta faɗa tare da ɗaure fuska, wajen ta ƙaraso haɗe da cire earpiece ɗin dake kunnenta tana kallon Najlah ta ce, "ina wuni Aunty Najlah, Ammie gani". Ta ƙare zancen tana dariya don tasan zancen da Ammie zata yi mata kenan, hararar ta Ammie ta yi haɗe da cewa, "ALLAH Ailat sai na saɓa maki akan Najlah, wannan ai rashin kunya ne ace kana ganin babbanka baza ka gaishesa ba sai anyi maka magana" "Yi haƙuri Aunty Najlah". Ailat ta faɗa tare da ɗan rissinawa tana haɗe hannuwa waje ɗaya tare da rungumo Ammie ta ɗora kanta asaman kafaɗarta ta ce, "Keyi haƙuri bazan ƙara ba kin ji Ammie na". "ALLAH yasa, ni ɗagamun a kafaɗa" ta ƙare zancen tare da ture mata kai, ganin haka yasa Ailat riƙo hannun Najlah tana faɗin "muje na rakaki zuwa gate aunty Najlah, nasan shi ɗai zaisa Ammie ta dena wannan fushin nata". ta ja hannun Najlah da dama tun ɗazu ta matsu ta wuce saboda wani irin ɓacin rai da take ji yana sake taso mata, musamman yadda taga Ailat na dariya sai taga kamar da ita take saboda abunda ya faru, a bunda bata sani ba ma Ailat bata san meke faruwa ba, asalima bata san da zuwanta gidan ba sai yanzu data fito ta ganeta, to kuma dama ba wani shiri sukeyi da ita ba shiyasa ta wuce abunta ba tare data kulata ba, don ita kam ta tsani ɗaukar kai da isar da take nuna mata, "Najlah kicewa Dadyn ku angode, ina na nan shigowa ko zuwa gobene nayi masa sannu da zuwa, ina gaida su Hajiya." "To Ammie zasu ji". Najlah ta faɗa sannan suka fice har lokacin Ailat na riƙe da hannunta, suna kawowa wajen gate ta fincike hannunta daga riƙon da Ailat tayi mata tare da watsa mata wani mugun kallo gami da harara tana cewa, "ALLAH kika sake ƙoƙarin riƙon hannuna kamar haka sai na baki kyakkyawan mari a fuskarnan taki, ni sa'ar kice ko angaya maki ni tsararki ce?" "Easy Aunty Najlah, Nima ai ba son haka nakeyi ba, kawai nayi ne don Ammie ta dena jin haushin abunda nayi maki, amma ALLAH ya baki haƙuri tunda kinji haushi". "Dallah rufamun baki, in sha ALLAH sai nayi maganinki tunda kika rena ni". Ta faɗa tana nunata da yatsa sannan tabar wajen, dariya Ailat ta yi haɗe da tafa hannuwanta kafin tace, "sai da safe aunty Najlah" cikin ɗaga murya, juyowa ta yi shaye da toka haɗe da sake nunata da hannu ta ce "Zanyi maganinki ne very soon". sannan tabar gidan, Ailat na dariya itama ta koma cikin gida tana bin waƙar da take sauraren a kunnenta. Ammie kuwa Najlah na wucewa takira Haisam ta rufesa da faɗa akan abunda ya yi mata bai kyauta ba, ta kuma nuna masa rashin dacewar hakan da yayi tunda baisan inda rana zata faɗin ba tsakaninsa da ita, kuma ko ba haka ba ya ci ace kodon irin alaƙar dake tsakanin gidansu da gidansu ta maƙwabtaka da yanda iyayensu suke ya girmamata, yanda yaga ran Ammie ya ɓaci ya sashi saukowa haɗe da cewa "Kiyi haƙuri Ammie in sha ALLAH hakan bazata sake faruwa ba, kawai Ni abubuwan da take yimun ne yanzu bana so shiyasa na dena bata fuska" "Au, saboda ta nuna maka so shine kake yimata haka?, Ashe da gaskiyarta abunda ta faɗa". "No Ammie ba haka bane, Ni akwai wacce nake so shiyasa bana son sakar mata fuska kar ta zata ko nima ina sonta". "ALLAH Ammie kar ki yadda dashi, shima yana sonta kawai baya son faɗa maku ne." Ailat data shigo falon yanzu ta faɗa tana yimasa dariya, ɗaure fuska ya yi tare da ɗago kai ya ce, "Ke, ina wasa dake ne?" "Sau nawa kuma? Ai saidai kar a ƙara" Ammie ta faɗa tana dariya ganin yanda ya ɗaure fuska yana zarowa Ailat idanuwa, dariya itama Ailat tayi haɗe da ɓuya bayan Ammie tana cigaba da cewa, "kuma wlh Ammie sun bala'in dace wa da ya Haisam, har fa kama sukeyi da juna wlh" Kafin ta rufe baki ya ciro pillow kujera ya jefeta dashi haɗe da yo kanta ta bar wajen aguje tana yimasa gwalo, zagaye falon suka shiga yi tana dariya shi kuma yana biye da ita yana cewa "yau sai kin faɗa mun ta inda muke kama da ita ko nayi maki shegen duka a gidan nan". Dai dai lokacin Abbiey ya shigo tayi saurin ɓuya bayansa haɗe da riƙe shi don har ga ALLAH ba ƙaramin shammatar ya Haisam ta yi ba, don shi kyakkyawane sosai chocculate colour dake da wasu irin narkakkin idanuwa masu matuƙar ɗaukar hankali, Najlah kuwa fara ce sosai ƴar siririya marar hanci da ƙananun idanuwa, sak idan ka ganeta ba tada maraba da ƴan China don har haka wasu ke kiranta (Ƴar china), lokacin da tana ƙarama kyakkyawa ce sosai amma bakin mutane yasa tana girma kamanninta suka sauya, duk da hakan ba laifi ko yanzu tana da irin nata kyau daidai gwargwado, tun suna yara tare suka tashi dasu Haisam da Hisham don makaranta ɗaya ma sukayi karatu lokacin Abbie na aiki a Lagos, sai ya zamana mahaifinta shike kula da kaisu makaranta da ƴan sauran abubuwan da ba'a rasa ba, sun shaƙu sosai dasu Hisham amma kuma tafi shiri Haisam, mahaifinta shahararren mai kuɗi ne, wanda ke da mallakin gaba ɗaya kamfanin NaNa rice da aka fi sani da suna Alhaji Asim mai dala (cikin littafin WASU MAZAN 😍), gidansu laƙe yaƙe dana su Haisam, ma'ana maƙwabta ne, maƙwabtaka ce ta haɗa su da Mahaifin su Hisham wato Alhaji Sani Naira, inda sannu a hankali mutuntaka da sanin yakamata da kuma kyautatawa dake tsakaninsu ta juye izuwa ƴan uwantaka, don dukkanninsu sunsan darajar ɗan adam da kuma haƙƙin maƙwabtaka, shiyasa zamantakewar tasu tayi kyau da kuma ƙarfin da duk wanda ya ganesu zai ɗauka ƴan uwa ne, Najlah itace ƴarsa macce tilo da yake da ita duniya wacce ƙaddara ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarta aka samu cikinta ta hanyar daba halas ba, inda bayan wasu shekaru ya yi tunanin gyara kuskurensa ya nemo inda mahaifiyarta take Hajiya Raheema ya roƙeta gafara sannan kuma ya aureta, a ɗaya ɓangaren kuma yana tare da matarsa Hajiya Zeenat da yake matuƙar so da ƙauna, mace mai haƙuri da kuma kirki da yadda da ƙaddara, sosai ta shiga damuwa lokacin daya labarta mata tsakaninsa da Hajiya Raheema da kuma cikin dake tsakaninsu, tayi kuka ta shiga damuwa ta kuma tuhumi kanta sosai akan wannan jarabawar da mijin nata ya tsinci kansa a ciki, in da ƙarshe ta ɗauki abun a matsayin ƙaddararsa, ta kuma tashi tsaye wajen taimaka masa don ganin ya gyara kurakuran daya aikata na baya, wanda hakan ya sa lokacin daya gano inda Raheema take da cikin data haifa, ta bashi ƙwarin guiwar aurenta ɗari bisa ɗari, lokacin itama tana da ƴaƴanta biyu a gabanta Irfan da Naufal, Irfan ɗan ta ne na cikinta data haifa, shi kuma Naufal ɗane ga aminin Alhaji Asim wato Imran, wanda adalilin irin mu'amalar da sukeyi ta masha'a tare matan banza ya auri wata mata Azeema ta haifa masa a matsayin ɗansa, ya zamana ta ci amanarsa ne ita da abokinsa Imran, wanda sai daga baya da tazo rasuwa ta sanar dashi gaskiya, ko data rasu ta bar Naufal yana jariri wanda hakan ya sa Hajiya Zeenat ta haɗa su duka shi da Irfan ta cigaba da shayar dasu don babu wata tserewa tsakanin su, yanzu haka suna ƙasar Paris sun kammala karatunsu suna shire-shiren dawowa gida nageria. (Ga mai son jin yanda labarin na family ɗin Alhaji Asim Mai dala yake, sai ya biya N300 na littafin WASU MAZAN ta hanyar wannan account namu da muke amfani dashi tare da tuntuɓar wannan lambar 07040402435 domin mallakar nasa). Dariya Abbie ya yi tare da riƙe shi lokacin daya ƙara so yana faɗin, "Haisam nima fa na kusa komawa bayan ummina tunda bazaka bari ta sakata ta wala ba, don haka dole ma satin nan ka fiddo da mata na aurar dakai mu hutu". "Ai Abbie har ma ya fidda, shi da Aunty Najlah ƴar gida za a yi" "Haba ummina! Da gaske kike yi?" Abbie ya faɗa with so much excited akan fuskarsa yana kallon haisam, zancen da suka gama yi kenan yanzu shi da Alhaji Asim, ALLAH yasa hakan ta kasance, da yafi kowa farinciki don Alhaji Asim mutumne, ya ƙare zancen cikin zuciyarsa yana riƙo hannun Haisam daya samu sa'ar kaiwa Ailat ranƙwashi akai ya nufi wajen

Chapter 2 of 9