Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
sunfi so su sawa yara idanuwa suyita yanda suke so with out any displine or control? Bazai yuyu ba gaskiya, ko da yake gashinan ai naga irin tarbiyar da makarantar tasu ke bayarwa, gaishesu ma ɗalibban nasu baza su iya yi ba". "Wannan wani abu ne daban Hisham, kai dai kawai ka canza in zaka canza kaji na faɗa maka, in ba haka ba wankin hula ya kaika dare". "Na ji zan canza, kuma zan sa a canza dole". "To ai shikenan, gamu gani?" ya faɗa haɗe da miƙewa yana yiwa Mahmah sai anjima. "To Ashafaq a gaida su Umman taka, na gode sosai ALLAH ya yi maku albarka". "Amin ya rabbi Mahmah". Suna fita sai ga kiran Ammie ya shigo a wayar Mahmah, murmushi ta yi kafin ta ɗaga wayar haɗe da karawa ga kunne tayi sallama, Cikin girmamawa Ammie ta gaisheta sannan ta ce, "ina ƴatah Madiyam da ƙafa ta ji sauƙi?" "Ta ji sauƙi sosai har anyi makaranta, ya su Ailat duk lafiya suke?" "Lafiya klw, ai ɗazu da safe Haisam ke faɗamun abunda yaron nan ya yi mata, kuma wai don tsabar rashin kunya har yake bawa ɗan uwan nasa labari, ko da yake ba laifinsa kaɗai bane Mahmah har da naki, fisabilillahi yarinya ɗaya duk anbi an takurata ba tada ikon motsi mai ƙarfi?, Ai zan faɗawa Abbie yazo ya ɗauketa idan anyi hutu, in yaso sai kuyi da wata". "Ikon ALLAH, ai gaki gatanindai Madiyam ce, zaku ganewa idanuwanku yanda ta sake tsargancewa, shiyasa bana hana Hisham hukuntata idan ta yi abu, idan har shi ya'yan naku bazai iya ba kuma ni ya hana nayi ai shi sai ya yi tunda ɗan uwanta ne, kuma ba tada kamarsa aduniya". "Haka ne, amma dai ai sai a sassauta kar aje gyaran doro a kare wuya". "In sha ALLAH lafiya klw za'a gyarasa, ALLAH dai ya shirya mana su za a fata" "To Amin, ai kinga da yake baida gaskiya na nemi wayarsa na rasa don yasan haɗuwa zamuyi dashi". "Kinga, ba ruwanki tsakaninsa ne da ƴar uwarsa, don ALLAH kada ki takurasa". "Au! Amma shi ya takura ƴar mutane?" "Ai laifinta ne". "To ai shikenan.." da haka suka ci gaba da firarsu a wayar har Hisham ya dawo daga wajen rakiyar Ashfaq, yana shigowa Mahmah ta ce "Ɗan halak, gashi nan ya dawo ko na bashi wayar." "A'a Mahmah ƙyalesa". Sanin kawaici irin na Ammie ya sa Mahmah ta miƙa masa wayar tana faɗin, "ungo ga Ammienku tana magana" Karɓa ya yi haɗe dayin sallama sannan ya ce, "ina wuni Ammie?" "Lafiya klw, a gaisheka yaron kirki, kai wato baka san abunda ya dace ba da kawaici ba ko?" "Ammie me nayi?" "Ai har tambaya kakeyi?" "Yi haƙuri Ammie, wlh na kashe wayoyin ne". "Dalili? Kai baka tunanin wani abu zai iya tasowa a nemeka? Shikena duk ka bi ka takura kanka kuma ka takurawa ƴar mutane, kayi rayuwarka yanda kake so baza a hana kaba, amma don ALLAH Hisham ka barta itama tayi rayuwarta yanda take so". "Ammie Madiyam ɗin za a bari tayi yanda take so? Ta fiye sakalci da shirme fa, kuma Ammie girma fa takeyi shikenan sai a zuba mata idanuwa?" "Shikenan ai sai kaci gaba tunda haka kake so, ana dai don kara da kuma halacci, kuma ita uwa da kake gani sai dai ta kauda kai idan ana cutar mata da yaro bawai don tana jin daɗin hakan ba". "No.. Mahmah ba haka take ba, tasan duk abunda nake yiwa Madiyam ina yine don gyaran gobenta, kuma duka a cikin so ne tunda ƴar uwata ce." "Duk da haka dai ka rage takurata for me kaji ko?" "Shikenan Ammie sai anjima" ya kashe wayar tare da komawa cikin gida ya kaiwa Mahmah wayar don dama fita ya yi, "Yawwa Mahmah, ina littattafan Madiyam na boko ne?" Ya faɗa tare da zaunawa kan kujerar falon ya ɗanyi relaxing baya tare da runtse idanuwansa, ita kuwa Mahmah kitchen ta nufa tana faɗin, "ka bari ka fara cin abinci tukuna in yasa zuwa anjima ta dawo sai kasa ta ɗauko maka don bansan takamammen wajen da ta ajiyeta ba". Ko mintuna uku Mahmah ba tayi da fita daga ɗakin ba sai ga Madiyam ta dawo tare da ƙawarta Nauwara, yarinya mai na tsuwa da hankali, zata ɗan girmeta a shekaru kaɗan amma da yake tana da ɗan girman jiki sai ba kowa zai iya fahimci hakan ba har sai in fuskokinsu aka kalla, ALLAH ya haɗa jininsu da ita sosai shiyasa ko yaushe suna tare da juna, musamman a makaranta don makarantar ɗaya suke yi both boko da arabiya kuma duka ajinsu ɗaya, tun a tsakar gida Madiyam ta fara ƙwalawa Mahmah kira tana faɗin, "Mahmah na dawo". kamar dai yanda ƙananan yara keyi, murmushi ne ya kucce wa Hisham da har lokacin idanuwansa ke a rufe jin irin ɗaya daga cikin shirmen nata da har yanzu bata san ya kamata ta dena yinsa ba, jin yanda ta ɗago labulen ɗakin ta shigo ba tare da tasan yana ciki ba ya sashi saurin ɗaure fuskar, "Shigo Nauwara.." ta faɗa daidai lokacin data ƙaraso tsakar falon tare dayin turus ba tare data ƙarasa maganarta ba, "ina wuni ya Hisham" ta faɗa tare da ƙoƙarin ficewa daga falon, "Dawo ki zauna". Ya faɗa har lokacin idanuwansa na arufe, Madiyam da gabanta ke wani irin mugun faɗuwa kamar za tayi kuka ta ce "A'a yaya, tare nake da ƙawata" "Ce ta shigo itama". Ba yanda za tayi dole ta leƙa ta kirawo Nauwara, cike da natsuwa ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, tsaye tayi tana kallon kyakkyawar fuskar Hisham kafin tace, "ina wuni ya Hisham?" Tasowa ya yi tare da gyara zamansa yana murmushi haɗe da cewa, "Lafiya klw, zauna" ya nuna mata kujera fuskarsa a sake, wanda hakan ya sa Nauwara sakin murmushi itama ta nemi waje ta zauna haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, haka kurum Madiyam ta tsinci kanta da jin haushin abun musamman yanda ta ga ya Hisham ɗin na kallon ƙawartata, daidai lokacin mama ta shigo ɗauke da tray da kuloli akai da plate da spoon sai kuma jug ɗin roba data haɗo masa zoɓo aciki, sai data buɗe fridge ta ciro ƙanƙara ta sake masa aciki sannan ta juya tana kallon Madiyam data sha toka tana tutar baki ta ce, "lafiya ke kuma?" Ƙin tankata ta yi saima nufar ƙofa da ta yi zata fice, "Dawo zubawa ƙawar taki ruwa tasha kafin ki fita" ya faɗa yana kallon yanda ta yi kicin kicin da fuska, "Ina wuni Mahmah" "Lafiya klw Nauwara, yasu mamanki?" "Duk suna lafiya." "To madallah, har an taso daga makarantar?" "Eh mun taso." Ta ƙare zancen tana kallon Hisham dake kallon yanda Madiyam ke tsiyaya mata ruwan a cup tana turo baki, Mahmah kuwa suna gama gaisawa ficewa ta yi tabar ɗakin gaba ɗaya ta tafi zuwa nata sabgogin, A gaban Nauwara ta ajiye cup ɗin ruwan data tsiyayo tana faɗin, "kisha ruwa Nauwara bari nazo". "Ki miƙa mata mana, ko bakisan baƙonka annabinka ba". Ɗaukar cup ɗin ta yi ta miƙawa Nauwara tana aika mata da harara tare da jin haushinta, "Yawwa ko kefa? Zo zuba mun abincin nima". Ta ji ya faɗa tamkar ba shi ba. Kallonsa ta yi ya sakar mata murmushin mugunta haɗe da cewa, "ko baki iyawa nasa ƙawarki?, Kinga sai taji daɗin cewa baki girmama yayanki idan ta fita ko ba haka ba Nauwarat". Yanda ta ji ya kira sunan Nauwara ɗin ya sake baƙanta mata rai, wanda ko za a tambayeta dalilin hakan itama bata sani ba, kawai dai ta ji haushine kuma baza ta iya ɓoyewa ba, plate ta ɗauka ta zuba masa abincin sannan ta ɗauka ta miƙa masa tana tuni baki, murmushi ya yi haɗe da amsa yana kallon yanda take faman kumbura fuska haɗe da cewa. "Thanks, zaki iya tafiya yanzu, ko da yake zuba wa Nauwara itama." "A'a yaya Hisham na ƙoshi wlh". Nauwara tayi saurin faɗa tana ɗago kanta, a fusace Madiyam tabar ɗakin ta samu Mahmah a waje tana shara ta ce, "Kawo na ƙarasa maki Mahmah". "A'a Madiyam, barshi na gode". Saman bencin dake tsakar gidan ta koma ta zauna tare da naɗe hannayenta a saman ƙirji kamar zata fashe tsabar takaici, "Waike lafiya?" "Lafiya klw Mahmah". "To meya faru kike faman baƙin rai?" "Mahmah kinga ya Hisham ko?" "Me yayi?" "Ba kiga yanda yake wani sakarwa Nauwara fuska ba har dasu murmushi, amma ni sai yayi ta cin zalina, ɗazu fa har marina ya yi don kawai nayi tuntuɓe na faɗawa abokinsa, amma dubesa har da wani cewa na zuba mata ruwa tasha, ko ina ruwansa ai ƙawata ce kuma wajena tazo ba wajensa ba" "To meye ruwanki aciki? Ai na faɗa maki indai bazaki dena halinki ba babu randa zai shafa maki lafiya, dama shike haɗaki dashi ba komai ba, ita Nauwara baki ga yanda take da hankali da natsuwa ba? Ai koma waye dole ya sake mata fuska tunda batayi abunda zaisa ayi mata magana ba" Turo baki tayi haɗe da cewa, "su suka sani, nima gobe wanda zai sake mun fuska ai zai zo" "Wa kenan?" "Ya Haisam mana". "To ALLAH ya kawo shi lafiya, shi dama ai taya ɓera ɓari yakeyi shiyasa jininku ya fi haɗuwa." Dai dai lokacin Hisham ya fito tare da Nauwara ya fice daga gidan, ita kuma ta ƙara so wajen da suke zaune tana faɗin, "Mahmah sai anjima, Madiyam zo ki rakani" "Magrib ta yi ba a bari na fita, sai dai gobe idan mun haɗu". ta bata amsa a daƙile wanda hakan ya sa Mahmah sakin murmushi haɗe da cewa, "ALLAH ya maki maganin wahala Madiyam, tashi kije ki ɗauko hijab ɗinki ki rakata mana, ai akwai sauran lokaci kafin akira". Ba don Madiyam ta so ba ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab ɗin ta rakata cike dajin haushinta. Da daddare bayan ya dawo sallar ishah yana shigowa falon Madiyam ta ɗauki plate ɗin da take cin abinci ta wuce ƙuryar ɗakin, haka kurum duk haushinsa take ji saboda abunda ya yi mata ɗazu, ya fahimci hakan tunda ta kasa ɓoyewa amma sai ya yi kamar baisan tana yi ba, waje ya nema ya zauna yana gaida Mahmah haɗe da kiran sunan Madiyam, turo baki ta yi sannan ta amsa a daƙile kamar za tayi kuka, ba tare daya damu ba ya ce, "ki fito mun da littafanki na boko idan kin kammala cin abincin". "To" ta amsa masa dashi gabanta na faɗuwa don duk kusan littafan suna can cikin school bag ɗin Nauwara da take ajewa, ta fi mintuna goma yana jiranta fitowarta amma taƙi har sai data ji Muryar Abbu ya shigo sannan ta ɗauko ƙwaya huɗu data zo dasu ranar friday zata copy note da bata yi ba. "Sannu da zuwa Abbu" ta faɗa tare da ajiye littafan a gaban Hisham ta koma inda Abbu yake zaune ta zauna, dafa kanta ya yi haɗe da cewa, "Sannu mamana, ya ƙafar taki? In jin kinyi sauƙi?" "Eh Abbu amm..." Gyaran Muryar da taji Hisham dake bubbuɗa littafan nata ya yi ya sa ta ja bakinta tayi shiru, don da ƙorafi zatayi masa cike da shagwaɓa, sai da Hisham ya gama duba littafan sannan ya ɗago kai ya gaida Abbu haɗe dayi masa sannu da zuwa sannan ya miƙe ya bar falon yana faɗin, "Ki zo na tambayeki wani abu a ciki, don ina ga ni zan ɗaukeku Physics". Zaro idanuwa ta yi jin abunda ya faɗa haɗe da kallon Abbu ta ce, "Abbu dama ya Hisham makarantar mu zai je karantarwa? Shikenan na kaɗe, don ALLAH Abbu ka cireni ita." Dariya abun ya bawa Abbu tare dafata ya ce, "Akan me mamana? Ai indai kika maida hankali ba abunda zaiyi maki, kuma ba gani ba, idan ya yi maki wani abu kuka dawo gida kisanar dani, zan san matakin da zan ɗaukar masa kin ji ko, tashi kije kar tun yanzu ku fara samun matsala". "Abbu..." "Ki tashi kije mana, wi ke wace irin yarinya ce da gardama ta yimaki yawa?" Miƙewa ta yi kamar wacce ƙwai ya fashewa cikin ciki ta fice daga falon, Ganin baya tsakar gidan ya sa ta nufi hanyar ɗakinsa data hango ƙofa buɗe, a bakin ƙofar ta tsaya haɗe da cewa, "Gani" ya yi banza da ita har saida ta sake maimaitawa kusan sau uku sannan ya ce, "Idan baki tashi shigowa ba tafiyar ki gobe sai mu haɗu a school". Har ta juya zata tafiyarta don dama haka take so sai kawai ta tsaya jin ƙarshen abunda ya faɗa, "mu haɗu school" ta maimaita cikin zuciyarta tare da saurin ƙarasa shiga ciki, zaune yake saman ƙatuwar katifar dake cikin ɗakin nasa yana sake bubbuɗa littafan haɗe da ɗago kai fuskar nan ba alamun wasa ya ce, "Ina sauran littafan naki?" "Suna wajen Nauwara" "Me yasa?" "A cikin shool bag ɗinta nake ajiyewa." "Ke ina taki?" "Tana nan?" "Ta lalace ne?" "A'a" "Kenan ta fiki hankali da sanin abunda ya kaita makarantar, ke kina cikin unserious student da basu san abunda ya kaisu makaranta ba, me yasa bakya copying more a class sai kin zo gida?" "Ba komai." "Very good, bakya son makarantar ne na canja maki wata?" Ta girgiza kai tana jin gabanta na wani bugawa da sauri da sauri, gaba ɗaya wani irin tashin hankali take ji yanda yake halbo mata tambayoyin tun kafin azo kan na karatu, "ki faɗa mun gaskiya?" "Eh bana son makarantar." "Shikenan, zan canza maki wata, amma ki sani duk wacce zan kaiki tare za muje saboda wannan hasarar kuɗin tarar da Abbu keyi tayi yawa, dole nasa maki idanuwa yanzu tunda bakisan inda keyi maki ciwo ba." "To kabarni a wannan ɗin." "Ta nawa kike ɗaukowa a class." "Bakwai" "A cikin ku nawa." "Ashirin da biyu." "Nauwara da?" Ɗan turo baki ta yi tare da gyara tsayuwarta sannan ta ce" "Ta ɗaya take ɗaukowa?" "Kina aikin me hakan ke faruwa? Ko da yake dole hakan zata faru tunda ita tasan abinda ya kaita makarantar, abunda nake so dake ki faɗamun duk wani abu dake damunki dake hanaki maida hankali ga karatu domin bazan iya ci gaba da kallon wannan takkwalcin baki ba, so nakeyi this term ya zama ke zaki ɗauko ta ɗaya a ajin ku, idan ko ba haka ba, to zamu saka ƙafar wando ɗaya dake, fice ki bani waje" ya ƙare zancen yana ajiye mata littafan saman katifar, turo baki ta yi haɗe da juyawa zata fita ya ce, "Dawo ki kwashe mun wannan shirmen naki." Dawowa ta yi ta ɗauka sannan ta fice daga ɗakin tana ƙunƙuni taya zai ce ta ɗauki ta farko a class ɗinsu bacin akwai wuɗanda suka fita ƙoƙari, ina laifin ma yace ta biyar koda da satar amsa ne ta samu tayi, ai wlh saidai su saka riga ɗaya ba wando ɗaya ba, don tasan bazata taɓa yin ta dáya ba tunda ƙoƙarin ta bai kai ba, da wuɗannan suruttan ta ƙarasa cikin ɗakin tare da yiwa Abbu sai da safe sannan ta je ta yi kwanciyar ta... *****. *****. *****. Haisam kuwa bai samu ya je wajen Dady ba sai bayan sallar la'asar ya nufi gidan gabansa na faɗuwa, a harabar gate ya taddashi zaune cikin wata ƴar rumfa dake ɗauke da fararen kujeru masu matuƙar kyau yana karatun jarida, footstep ɗin daya jiyo ya sashi ɗagowa tare da zare glasses ɗin idanuwan nasa yana kallon Haisam har ya ƙaraso wajen, cike da jin kunya ya ɗan russuna kai yana gaishesa ya yin da shi kuma ya jawo hannunsa suka gaisa yana faɗin, "have a sit my son, ai na zata an haɗani dakai shiyasa kaƙi zuwa gaisheni". "Wa ya isa Dady? Abubuwa dai ne wlh, an dawo lafiya?" "Lafiya klw ya kake?" "Alhamdulillah Dady". "Masha ALLAH, ai ɗazu Hajiya ta shigo ita da Ailat na bata saƙo, na zata ta manta bata sanar maka ba, to ashe ta faɗa maka" "Eh Dady, ayi haƙuri" ya ƙare maganar yana sinne kai ƙasa, kamar ance ya ɗago kai ya hango Najlah da taga lokacin daya shigo tafe ɗauke da ɗan ƙaramin tray ta nufo wajen, wani irin abu mai kama da jiri ya ji ya ɗebesa tunowa da abunda ya faru tsakaninsu, anya Najlah ba tada aljannu kuwa ya tambayi kansa yana sadda kai ƙasa, tsinkayo muryarta ya yi cikin kunnuwansa tana faɗin "ya Haisam ina wuni? Barka da zuwa" tare da jan kujera ɗaya ta zauna kusa dashi tana kallon mahaifin nata dake ƙoƙarin sake maida hankalinsa ga jaridar, "Dady Barka da marece, me zan zubo maka?" "Duk abunda kika zubo Najlah, amma ki fara da yayanki" ya ƙare zancen tare da buɗo wani shafi a jaridar, ganin hankalin mahaifin nata baya kansu kuma shima Haisam ɗin ya sadda kansa ƙasa ya sa cike da jin haushi ta saka ƙafarta ta ɗan taka tashi dake kusa da ita, yana ɗago kai ta kashe masa ido ɗaya haɗe da cewa, "me zan zuba maka ya Haisam, lemu ko ruwa?" Tare da turo baki alamar kissing cikin ƙasa da murya ta ce, "kayi kyau sosai". Daburce wa ya yi haɗe da ƙoƙarin tashi ta sake take masa ƙafa, wanda ganin hakan yasa Dady ajiye jaridar yana faɗin, "ko wucewa za kayi my son baka sha komai ba?" Da sauri Najlah ta yi yaƙe haɗe da cewa, "No Dad abunda nake tambayarsa kenan, ko ba haka ba ya Haisam" cikin daburce wa da tsarguwa da zaman ya ce, "eh ruwa..ruwa, zuba mun ruwa nasha" shima yana dariyar yaƙen, murmushi ta saki sannan ta zuba masa ruwan ta miƙa masa, shi kuma Dady ta zuba masa lemu ta bashi tana faɗin, "Dady injin kunyi magana da ya Haisam akan maganar dana faɗa maka ɗazu?" Da ƙarfi Haisam ya furzo da ruwan dake bakinsa ba saboda tsananin tsoron wace maganar ce tayi da Dady, kaddai ace zuwa tayi ta faɗa masa cewa ya yi mata wani abun, ɗago kai Dady ya yi yana kallonsa haɗe da cewa "lafiya my son, ko ƙarya takeyi baka ce zaka kaita wajen shopping anjima ba? Shiyasa na ce ta bari sai na tambayeka na ji idan har da gaske ne?" "Eh da gaskene Dady". Ya faɗa haɗe da kallonta yana goge baki, rufe bakinta ta yi tana danne dariyar data zo mata haɗe da tashi tabar wajen tana yimasa dariya... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* Free page 9 *FIL-HUB*♥️ (Acikin so💘) Paid Book: N500 Written by Billy s fari💎 ______________________________ Madiyam kuwa tunda ya fara faɗar maganganunsa ta soma zubar da ƙwalla saboda ba ƙaramin ci mata mutunci ya yi ba a gaban abokananta musamman da taga wasu na faman sadda kai haɗe da rufe baki suna dariya, sai taji duk duniya babu wanda ya taɓa wulaƙantata agaban mutane kamarsa, don ɗai bata yi note ba shine abun cin mutunci da faffaɗa maganganu haka, wannan wace irin tsana ce haka ya yi mata da ya rasa wanda zai fara wulaƙantawa sai ita? Ta tambayi kanta idanuwanta na sunkuye ƙasa suna fidda ƙwalla, har ya yi kusan mintuna biyar da fita bata ɗago kai ba har sai da ta ji Nauwara ta ce, "Madiyam muje muyi breakfast". sannan ta ɗago kai haɗe da sa duka tafin hannuwanta tana share ƙwalla gami da jan majina a hancinta ta ce, "ki je kawai Nauwara bazan je ba". "Saboda me?" "Saboda haka nake buƙata". Ta bata amsa a ɗan tsawace sannan ta ɗauki jakarta ta fice daga class ɗin, can baya ta koma ta zauna ta haɗe kai da guiwa tana ci gaba da kukan da zata iya kira na ɓakinciki biyu, na farko na muguwar yunwar dake damun cikinta, na biyu kuma na walaƙancin da ya Hisham ya yi mata, wanda take kallo a matsayin big Shamless thing to her don babu malamin daya taɓa kwatanta yi mata haka, sake sakin wani kukan tayi tuno wa da abun tana kiran sunan Abbu har aka koma breakfast ba tare data sani ba, ganin bata fito ba daga inda ya hangota ɗazu daga ta shiga daga staffroom ɗin su ya sashi tasowa ya nufi wajen, tana haka ta tsinkayo muryarsa cikin don kunnuwanta yana faɗin, "Kukan me kike yi? Me kuma kike yi anan? Baki ji an koma break bane?". Ba tare data ɗago kai ta kalli inda yake ba tagyara jakarta dake saƙale a kafaɗarta haɗe da raɓawa ta gefensa ta bar wajen, "In dai akan abunda ya faru a class ne kike kuka to ba kiga komai ba, don matuƙar kika maida karatu maƙiyinki kuma kika riƙa saka wasa acikinsa to tabbas yanzu muka fara saka ƙafar wando ɗaya dake, kukan jini idan zaki iya kiyi wannan ke ta sha fa". Ya faɗa kafin ta ƙara sa barin wajen, tana jinsa ta yi banza da shi ta koma cikin aji abunta idanuwa a kumbure tsabar kukan da ta yi, ranar a takure ta ci gaba da zama cikin ajin nasu har aka tashi school gabaɗaya. Kusan ita ce ta farkon fita saboda ba ta ƙaunar ta sake yaɗuwa dashi balle ya tasa ƙeyarta a gaba yace su tafi gida sai kace wacce ake tsoron ta tafi wani wajen ko kuma ta ɓace, yana kallon yanda ta fita da sauri da sauri tana yi tana waiwayen bayanta, wanda ya tabbata tana yine don sa, taɓe baki ya yi haɗe da cewa, "ki gama gudunki ya rinya ai zamu haɗu a gida". sannan ya tattara textbooks da maker ɗin dake gabansa da note book da aka bashi duka as teaching materials ya saka cikin wata side drower dake gefen bencin dake gabansa haɗe da miƙewa ya bar staffroom ɗin ya nufi gida shima. A ɓangaren Haisam kuwa sai daya yi nisa sosai sannan ya tuna da ya yi mantuwa akwai abunda yake son siyawa Madiyam da bai saye ba, don haka ya juya kan motar tasa ya koma ya siyo sannan ya sake kama hanya, hakan ya sa bai iso ba sai wajen ƙarfe ɗaya saura kwata, a shagon Abbu ya fara biya wa su gaisa, cike da jin daɗin ganinsa ya miƙa masa hannu yana murmushi suka gaisa, "Sannu da zuwa Haisam, ai munyi waya da mahaifin naka yake yimun zancen zuwan ka, don ALLAH ku rage gudu akan titi saboda kayi saurin isowa". Murmushi Haisam ya yi yana shafar kansa haɗe da cewa, "in sha ALLAH Abbu". Don shi kanshi ya san ya yi gudu ba kaɗan ba, "Ya mahaifiyar taka da Ailatu duk lafiya suke?" "Lafiya klw Abbu, duk suna gaisheka". "Ina amsawa". "Abbu ya Ailat da jiki?" Sai da Abbu ya yi dariya sannan ya ce, "Ai kai baka gajiya da taya ɓera ɓari Haisam, shikenan daga ji ance ta ɗan jimu a ƙafa sai ka kamo hanya kazo kai mai ƙanwa! To yanzu haka tana makaranta ta samu sauƙi sosai, dama taɓara ce da shagwaɓa irin ta ummina da bata gajiya dasu, amma ciwon ba ai wani ciwo bane sosai". "Har sai da aka tsaga fa akace Abbu!" "To ai gaka nan ka zo Haisam sai kaje ka ganewa idanuwanka, ungo wannan saƙon ka wuce wa maman taku dashi". Ya miƙa masa wata leda daya siyi ɗanyen naman kaji guda biyar a hannun wani maƙwabcinsa da suka gama waya da Abbie ya sanar masa da zancen zuwan Haisam. Har bakin mota ya rakosa sannan ya juya ya koma shago shi kuma ya wuce gida, lale marhabin Mahmah ta tarbesa da ita lokacin daya iso gidan cike da farinciki, Ruwan sanyi da sauran zoɓon data haɗawa Hisham jiya ta fara kawo masa don duk haka suke daga shi har Haisam da Ailat da son soɓo, musamman ma idan akace nata ne ita ta haɗa shi, to fa har rigimar ake yi wajen sha tsakanin su idan ya zo, don yakan ɗan zo wani lokacin shi da Ailat suyi kwana biyu ko uku su koma, sai da ya gama sha sannan ta zauna suka gaisa haɗe da tambayar sa duk lafiya su Ammie suke ya amsa mata da lafiya lau sannan ya miƙa mata saƙon da Abbu ya bashi ya kawo mata yana faɗin, "gashi inji Abbu yace akawo maki" "A gaishe to, halama sai da ka biyo ta wajensa sannan ka wucikke?" "Eh, nasan kona iso gida bazan isko shi ba, shi yasa na fara tsayawa ta wajensa muka gaisa." "To ai ka kyauta,

Chapter 5 of 9