Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai mai nera dan ba zasu siyar da akuya ba,  ta dawo tana ci musu danga. Kasancewarta yarinya mai hankali da jin maganar iyaye, yasa bata tsallake maganarsu ba. Koda ta kammala karatu zata tafi bautar ƙasa, ta sha jan kunne sosai. Koda aiki ya fito mata bata wani yi na'am ba haka ta ci gaba da zaman gida, tunda babu abin da ta nema ta rasa, A sanadin kasuwanci Alhji Aliyu ya haɗu da mahaifin Ma'aruf, lokacin ya zo da su Hajiya mama siyan kayan sallah, daga nan suka ƙalla abota mai ƙarfi, har sukayi musayar numbobi, a zahirin gaskiya mahaifin Ma'aruf ya fi Alhji Aliyu kuɗi, nasan zakuyi mamaki... Mahaifin Ma'aruf. Asalinsu noma da kiwo shi ya karɓesu, ta haka suka tara ɗumbin dukiya tun iyaye da kakanni, tun duniya na kwance suke siyan filaye, iyayensa shi kaɗai suka haifa, asalinsu Fulanin jihar Yola ne, duk shekara suna shirya gagarumin taro nasu na Fulani, wanda ilahirin mutanen ƙauyen suke halarta, a wannan shekarar ma mutanen da suka halarci taron bazasu ƙirgu ba, saboda gabaki ɗaya yankin suka tafi, sai dai Allah mai iko babu wanda ya dawo a raye duk sun mutu, sai mahaifin Ma'aruf shine kawai a raye, shima duk ya ji rauni ta ko ina, Bayan ya warke ya ci gaba da tafiyar da kayan iyayensa, kasancewarsa mutum me gaskiya da amana yasa ya samu al'umma masu ƙaunarsa, alhmdulilah yayi boko dai-dai gwargwado kowa na alfahari dashi, ga taimakon talakawa, ko bayan rashin iyayensa be hana shi ci gaba da noma da kiwo ba, Kasancewar lokacin Ma'aruf yana ƙaramin, shi kaɗai suka haifa, mutum ɗaya ne ya rage a danginsu wato Inna, wacce take ƙauyen Kano, aure ne ya kai ta can, Allah yayiwa mijin nata rasuwa amma ya jima sosai tun bayan da ta haifi Talatu, wannan kenan. After 3days Hajiya ta ji sauƙi sosai, se dai har yanzu ta kasa kiran  momyn Saudart saboda takaici, A ranar Inna ta shirya komawa ƙauye, Hajiya mama da Anty Jamila suka ce mata ta turo musu Talatu suna son ganinta, sai da tayi musu alƙawarin idan ta koma zata sata a mota drivern su ya kawota, kaya da yawa Hajiya mama ta haɗa mata, anty Jamila ma ba'a barta a baya ba gurin zaɓo mata hijabai da sikel ɗin ciki. Ƙarfe 9:am Inna ta bar Abuja, suka kama hanya sai Kano.. Sun sha tafiya sosai saboda sunyi awanni kana cikin hukuncin Ubangiji sai gasu a cikin garin Kano, sun sake yin tafiya mai nisa kafin suka Iso ƙauye. Shugowar motarsu ke da wuya, yara da ƴan mata suka cika gurin, kai kace biki akeyi,  can na hango Talatu sai tuture mutane takeyi, tana cewa hegu ƴan ƙauye, tana rattaba motar, Inna ce ta fito tana murmishi, Talatu ta je da gudu ta rungume ta tana cewa " kun higa uku kudai, to Inna aka kawo a mato se kowa ya watse ƴan cusa kai.. Parking ɗin motar yayi a gindin bishiyar dake ƙofar gidan su Talatu kana ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya ciro waya yana dannawa, Suna shiga gida, kafin su kai ga shiga ɗaki kaka tayi sallama, suka amsa, a tsakar gida ta zauna tana yiwa Inna Barka da dawowa, ganin anata fitowa da jakar kaya ya sanya ta cewa "ina kuma ja a kai su?" wallahi su Hajiya ne suka ce Talatu taje tayi musu kwana biyu shine na haɗo mata kaya" "Alhmdllh na gode musu, wallahi dama ta isheni taɓɓ duk wanda ya kwashi wannan yarinyar to ya kwasar wa kansa" Kaka ta ƙare maganar tana riƙe haɓa, "Ni ki dena yimin baki, wataran na ga me tare miki faɗa wallahi" Kaka ta raɓe baki, gami da cewa "kafin ki taremin faɗa kin bani wuya" Inna ko ta kansu bata bi ba, sbda idan sun haɗu sana'arsu kenan da kaka da talatu, Talatu ta ruga gidansu Gudidi, a tskar gida ta sameta tana cin rogo da ƙuli, Gudidi na ganinta ta ɗora ƙafafu a saman kwanon tana wulli wulli da idanu, "keee" Talatu ta faɗa a hankali, Yi mata alama da ta taso tayi, ta taso tazo gurinta, lokacin Ramma tana ɗauki tana sallah, "Ki faɗa min menene ko kinzo sake dukana ne?" "Ke dalla can binni zani hine nace bari inzo in gaya miki, al'kur'an idan zaki ki ɗibo kayanki ki watso min ta katanga sai in kwahe mu wuce kinga mun zamo ƴan binni" Cikin sanɗa taje ta miƙa mata kwanon abincin nata, tace ɓoye maci a mato, Talatu ta juye a ɗankwalinta ta cukuikuye guri guda, ɗan zirine mayafie da taci ɗammara dashi ta ɗaura, har gudidi ta gama tattaro kayanta ta watsa su ta baya Ramma bata sani ba, ashe barci ma takeyi, Gudidi ta kalli ƙaramar ƙanwarta wacce bata wuce shekaru biyar ba, tace "ke Atika ki ce wa Ramma na tafi binni ni da Talatu" Yarinyar sam bata ma gane me Gudidin take nufi ba, ta amsa da "toh" suka wuce, Tunda driver ya san tare da Talatu zai koma ko me ta kawo baya yi mata musu, har kayan Gudidi sai da ta saka a boot, Daga ƙarshe suka raba rogon tare, Talatu ta tura gudidi a boot kana ta rufe, dama kafin Gudidin ta shiga,  Talatu tace mata ta daure, idan suka je can kilihi zasu dinga ci" Talatu ta koma gida tana tsalle, Inna tace "dan Allah talatin ki nutsu ban da yawan magana, Kaka tace "ban da mugunta, hannan ban da  idan ayi maka ka rama" "Wallahi duk wanda ya nuna min yatsa he na karyehi kohi waye" Talatu tai maganar tana tsalle. Horn ɗin da driver yayi ne, yasa su fitowa, Inna ta miƙawa talatu wani babban buhu mai ɗauke da daddawa da kuka da su barkono, Har za a saka a boot, Talatu tace "za'a sace a hanya a bata a hannunta, sbda asirinta zai tonu. Koda driver ya tada mota su Inna suna ta ɗaga masa hannu da yaran dake gurin har suka ɓace wa ganinsu, Sunyi nisa sosai dan sun bar garin Kano, zamu iya cewa sunyi ra bi a tafiyar tasu, Talatu tace "me mato dan Allah ka tsaya zanyi fitsari" Gefen hanya ya samu yayi parking ta fito ya miƙa mata gorar faro "yace gashi" karɓa tayi, bayan tayi fitsarin tana dawowa ya fito shima, cewa take "Gudidi zan buɗe ki yanzu ki dawo cikin mato idan kuma kin mutu hikenan maci naman kaza babu ke" driver yace "Kee! Waye Gudidi? kinada hankali kuwa, a jeji muke da zaki dinga kirawo mana wasu mutane wanda sunan ma babu daɗin ji, daga cikin Boot ya ji ance "me mato ka buɗe ni in fito yasin na gaji da zaman kurkuku" Driver ya zaro idanu tare da matsawa a jikin motar, ya tsorata sosai, tunda a iya saninsa mutum ɗaya ya ɗauko, Talatu tace "kiyi hakuri idan mukayi mihi rabine kunya ze zubemu a nan bari in lallaɓa hi" Ta durƙusa har ƙasa tace "kayiwa darajar gyatumarka ka fito min da ƙawata" A tsorace ya buɗe Boot ɗin sai ga Gudidi tasha kuka ta gaji har da majina, Driver yace "ke ai ke kadai aka ce in ɗauko wannan kuma wacece?...! Sharhin ku shi zai bani damar yi muku typing da yawa. Wanda suke karantawa basa magana karku damu zan tafi hutu kunji?. Mom Islam 08141799224 *NA KASA JUREWA*        🪻🪻🪻 Page 21-22 Talatu na matsar ƙwalla tace "ƙawata ce" Kai tsaye ya zagaya ya shiga mota bai sake bi ta kansu ba, koda suka shiga mota basu kulle murfin motar ba, driver ya ce "ke rufe murfin motar mana" Talatu tace "da ƙarfi ko a hankali?" Driver yace "idan kika rufe a hankali kika faɗo mutuwa zakiyi" Ai da sauri Talatu ta buga murfin motar gaaaam!!! , A tsorace ya ambaci sunan Allah, suka ci gaba da tafiya, Suna gaf da shiga Abuja dan har sun wuce Keffi, Gudidi tace "me mato ka dakata yasin rogo ya sa ni gudawa" Wani dogon tsaki yaja mtswww, kafin yace "ni fa na gaji da ɓatamin lokacin da kukeyi, mun kusa isa gida sai kuyi acan. Gudidi sai cije baki take alamun kashi ya matseta, suna hawa gargada ta sake kashin tsuuuuu, wanda ya fara cika gurin da ɗoyi, ba driver ba, hatta Talatu toshe hanci tayi, sai kuma ta dinga sake tusa tana cewa "na higa uku ni gudalle Allah ka sa ban ɓata musu mato ba" Talatu tace "Hegiya ance miki ki bari aje can gidan amma kin ƙi, saboda taurin kai irin naki" "Talatu kinsan idan naci rogo cikina yana lalacewa, yanzun ma wani kahin nakeji" Driver yace "wallahi idan kika sake yin kashi zan sauke ku duka" Tsit sukayi babu wanda yayi magana, sbda sunga babu wasa a tattare dashi.    Zaman ta a gidansu ya fi mata kwanciyar hankali a bisa zamanta a gidan Ma'aruf, satin ta ɗaya amma ta fara murmurewa, abin mamaki har yanzu momy ba ta sanarwa da Dady Saudert ta dawo ba, Sai da suka kwashe one month a can kafin Dady ya biyo jirgi ya dawo, ya bar Anam acan kasancewar tana karatu ne, Wacece Anam?, Anam ƙanwar Saudart ce, shakarunta 18yrs a duniya, Dady ya ɗora buri a kanta, sbda ita ce alkawarin su na ƙarshe da oga akan itama ze kai ta can wato ya bar musu,kamar inda ya bada ƴar uwar Saudart. Girke-girke momy ta shirya masa masu rai da lafiya, ita da ƴan aikinta biyu da Saudart suke ta ƙoƙarin girkin, 5:pm driver ya ɗauko Dady daga airport zuwa gidansu, Momy Saudart, duk sun ci kwalliya sunyi kyau sosai suna jiran shigowarsa, sallamar Dady ne ya karaɗe parlon, Saudart ta miƙe da gudu tana oyoyo dady, bubbuga bayanta ya ɗan yi kai kace wata baby kafin ta koma ta zauna tana murna, ya buɗe hannayensa ma me momy ta taho ya rungumeta, suna sakarwa junansu murmishi, Bayan ya zauna aka kawo masa abinci saman table, sbda a ranar da ya dawo baya zuwa dinning cin abinci, farfesun naman rago ne da tuwon shinkafa miyar egusi sai lemon abarba da kankana wanda aka zuba masa peakmilk, sai da Dady ya cika cikinsa kafin ya wuce bedroom ɗinsa, acan ya samu momy tana ƙoƙarin fito masa da kayan da zai sa, ta baya ya rungumeta tare da cewa "Hajiya Zee meye sirrin komai nawa yana sake haɓɓaka" cike da so da ƙauna ta juyo tare da kwantar da kanta a faffaɗan ƙirjinsa, gami da shafo gashin gemunsa wanda ya fara zama fari da baƙi sbda ya fara manyanta, Habiby any time kana sake zamowa kamar saurayi" Cikin shauƙin so ya wani zagaya da hannayensa zuwa wuyanta kafin yakai bakinsa kumatunta ya sakar mata hot kiss, kafin Dady ya shiga wanka an sha love fa. A tare da momy suka shiga wankan sbda wannan umarninsa ne, idan har yana gari tare suke wanka, bayan ya fito yana tsane jiki, momy ma ta fito ɗaure da towel milk color, Habiby yau  zanje anguwa wata ƙawata ta aihu walhi yau 4days ko zuwa banyi ba" Momy na gama rufe baki Dady ya sanya hannunsa a saman lips ɗinta kana yace "shiiii" wannan ranar tawa ce dan haka a bata haƙuri a tura mata da 100k, babu inda momy ta iya dole ta haƙura. Duk wannan maganganun da suke yi a kunnen Saudart, tazo wucewa taji suna magana ita kuma ta tsaya, nikam nace Saudart ki rufawa kanki asiri, jin shiru yasa ta bar gurin ta wuce bedroom ɗinta, fashewa da kuka tayi yayinda ta tuno soyayyar da suka kwasa ita da Ma'aruf, daga ƙarshe ta juye ta koma ƙiyayya mai muni. Lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallahar magriba, Dady ya fito sanye da jallabiya, zai wuce ya kalli Saudart kafin yace "daughter yaushe kikazo?" fashewa da kuka tayi kana ta miƙe ta bar gurin da gudu, wucewa yayi masallaci sbda idan ya koma ciki yana iya rasa sallah. Lokacin da su Talatu suka iso Abuja ana kiran sallahar isha'i, saboda tsayuwar da suka dinga sa driver yayi, Tunda suka doso bakin get Gudidi take ƙwalalo idanu ita da talatu, koda aka buɗe get ɗin bayan yayi horn sakin baki sukayi, a parking space ya ajiye motar kana ya zare key ya fito suna gaisawa da mai gadi, Boot ya buɗe kana ya firfito musu da kaya ya wuce dashi side na su Hajiya mama, suma bayansa suka bi . Hajiya mama na ganin driver ta hau washe haƙora ita a dole yarinyarta tazo, duk da ganinsu su biyu be sa ta ɓata ranta ba, sai ma rungumesu da tayi, tace a shigar dasu ciki suyi wanka sai suci abinci, driver yace "Hajiya har da kashi fa a mota, Talatu tace "to me tonon silili anji ai he ka wuce ko?" Hajiya tayi dariya ta shiga ciki. Sai da sukayi wanka suka sauya kaya, wata koɗaɗɗiyar atamfa Talatu tasa, ita kuma gudidi zani daban riga da ban ɗankwali daban haka ta saka, ga wata kwalliya da sukayi iri ɗaya, sun lafka janbaki ja a leɓensu anyi jagira da koren pencil, Koda suka fito ƴan aikin gimtse dariyarsu sukayi, sbda suma dai a gidan aka wayar dasu, a parlo suka zauna yayinda Hajiya ta sanya a kawo musu farfesun naman kaza, da soyayyen dankalin turawa da kunun gyaɗa, sai ruwan gora a gefe, Talatu ta kwaso kulolin duka gabanta, kafin tace "Gudidi bari kiga idan bamu raba shi ba, ƙur'ani zasu ce mana ƴan ƙauye, Talatin ta yago cinyar kaza takai baki, tana cewa "ungo wuya da gurin ɗuwawu kinsan bana cin su" Gudidi tace "kai Talatu me makon ki raba mana tare hine zaki nuna min waraki?" Murguɗa mata baki tayi, yayin da take sake yago naman kana tace "tausaya miki fa nayi hi yasa nace kizo mu tafi, idan ba zaki ci ba to hikenan cinye wannan na kwanon dan ban san meye ba, ga dukkan alamu zai iya tsurar da mutum" Gudidi ta karɓi wuyan kazar da kwankwaso ta koma gefe, dama a saman Capet suke zaune, ta buɗe kular dankalin turawar da aka soya da ƙwai, ashe har da dambun nama a gefe, ko gayawa talatu batayi ba ta dinga ci hannu baka hannu ƙwarya, bata cinye na bakinta take sa wani, sallamar da Ma'aruf yayi ne yasa Talatu da gudidi suka juya a tare....! Idan ana comments in sauya taku idan ba'ayi muci gaba da tafiya a haka, idan na gaji in dena posting Mom Islam ce 08141799224 *NA KASA JUREWA*        🪻🪻🪻      Mom Islam Page 23-24 Sanye yake da blue jeans da t-shirt milk color, fuskarsa tana ɗauke da annuri, hannunsa na riƙe da wayarsa yayinda ya tsunsa suka kasance da tsadaddun zobuna masu kyau, ko da yaga babu kowa a parlo ya tsaya bai ƙarisa ciki ba, ƙare wa su Talatu kallo yakeyi, yayin da suma shi ɗin suke kallo, Talatu ta wani ƙwalalo masa idanunta, Gudidi na suɗe hannu tace "Talatu idanunki sun gano miki abinda na gani kuwa?" A hankali tace "wa Gudidi, zo ki dangwali romo muyi kamar zamu wuce ta gabansa se mu hyafa mai" Kamar inda Talatu ta tsara haka sukayi, kafin zuwan su yana ta, ƙare musu kallo sbda bai taɓa ganin irinsu a gidansu ba, yayi nisa da tunani ya ji sun ruga waje da gudu suna dariya, sai yanzu ma ya gani wa shi suke yiwa dariyar, ashe ɓata masa jiki sukayi, Cikin zafin zuciya ya kalli kulolin da suka ci abincin kafin yace "su waye waɗannan kamar ba mutane ba?" Kai tsaye ya wuce room ɗin Hajiya mama, ya sameta tana shafa mai, kasancewar ta fito daga wanka, "Hajiya su waye a parlo kamar mahaukata?" "Mahaukata fa kace Ma'aruf?" "Yarinyar yayar mahaifinka ce" waro idanu yayi cike da wulaƙanci kafin yace "gaskiya Hajiya suyi gaggawar barin gidannan" Inda yai maganar ta gane Bama shawara yake bata ba, umarni yake bata, "Ma'aruf  ka nutsu kasan me kake yi, yarinyar nan da ka ga tazo zama daram a gidannan babu inda zata je" "Yara dai, Hajiya ki daina cewa yarinya ai su biyu na gani kuma wallahi da su da mahaukata duk tafiyar su ɗaya, Hajiya ki duba rigata ki ga wulaƙancin da sukai min" Yai maganar yana zuba hannayensa cikin aljihu rai a ɓace. Ɗayar ƙawarta ce tare suka zo ɗazu, Beyi abin da ya kawo shi ba ya fice, sbda haushi da takaici, a rayuwarsa ya tsani ƴan ƙauye. Rai a ɓace ya fito daga side na Hajiya yana ƙwalawa anty Jamila kira Hajiya tace ta fita har yanzu bata dawoba" Yanke shawarar ya fice a gidan yayi, ya fito parlo kafin ya buɗe, ƙofa yaji an cakumeshi tana cewa "yasin na kamaki kuma mintsini sittin zanyi  miki" Idanunta a ɗaure take maganar. Ƙare mata kallo yayi up and down, kafin ya fara kiciniyar fincike hannunta a jikinsa, cikin ƙyanƙyami yake ƙwace hannun nata, har ga Allah bata san ba gudidi ta kama ba, ita kuma gudidi tana can corridor tana jiran Talatu ta kira ta, abin ya matukar bashi mamaki wai namiji kamar shi ya kasa cire hannun talatu a jikinsa? meye hakan yake nufi?" wani gigitaccen mari ya zabga mata kafin yace "ba kisan wa kika riƙe ba ko?" Ya ƙara da cewa "wawuya ƙazama me warin awaki" Jin shigar marin tayi har cikin ƙwaƙwalwar ta, lokaci ɗaya taji zafin na shigarta sosai, tai saurin cire ɗankwalin da ta ɗaure idanun nata, buɗe idonta ke da wuya ta ɗora su a na Ma'aruf, hannunta a saman kumatunta tana sosa gurin tace "me nayi maga mugu kawai, na ɗauka ma Gudidi ce ashe Garba ne" Tai maganar tana murguɗa baki, hannunsa yakai bakinta ya ɗanne sai da taji zafi sosai ta ruga da gudu idanunta sun cika da hawaye tace "mugu basamude" Babu hali ya bita sbda sai ta rai nashi haka dai ya fice a gidan zuciyarsa babu daɗi. Kai tsaye gidansa ya wuce, bayan an buɗe masa ya shiga, kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce,  kallon kansa yayi a mirror kafin ya ja dogon tsaki mtswww, sai kuma ya hau ɓaɓɓalle bottoms ɗin rigar, lokaci ɗaya faffaɗan ƙirjinsa ya baiyyana, wanda ke ɗauke da kwantaccen gashi baƙi gunin birgewa, gashin yayi lufff kai kace an tace shi, Har yanzu yana cikin ɓacin rai, ya zauna saman bed ko me yake tunani oho, ya ciro wayarsa ya fara gwada number anty Jamila, ringing ɗaya zuwa uku ta ɗaga, cikin katseta a maganar da takeyi yace " Anty kina da labarin mahaukatan da suka zo gidan Hajiya kuwa?" Anty Jamila ta zaro idanu kafin tace "shine babu wanda ya kirani, Ma'aruf yace "dan girman Allah ko sun zo yin kwana biyu ne ki fitar dasu anty naje rai na a ɓace na dawo gida. Sallama sukayi ya ajiye wayar, sai yanzu hankalinsa ya kwanta a tunaninsa Anty Jamila bata da masaniyar zuwan su Talatu. A gurguje ta koma gida hankali a tashe, tun daga harabar gidan take ƙwalawa drivers da mai gadi da ƴan aiki kira, da gudu suka taho dukkansu suka durƙusa a gabanta, cikin zafin rai da ɗaga murya tace "waye ya bari mahaukata suka shigo gidannan?" A ƙalla ƴan aikin gidan zasu kai goma, kuma ko wanne a wata ana biyansa albashi mai tsoka. Ƴan matan da suke aiki da mai bawa flowers ruwa da mai gadi da ɗan aikan gidan da sauran ma'aikatan suka rantse da Allah basu ma ga mahaukata ba" Anty Jamila ta ɗibi sauri sai cikin gida, tana shiga tun daga parlo take cewa "Hajiya wai gidannan lafiya kuwa?" Lokacin ma sallahar magriba tayi, ta fito parlo ta samu anty Jamila na ta haɗa gumi tace "lafiya Jamila?" "Au Hajiya lafiya fa kike tambaya ta, ni da aka kirani musamman wai mahaukata sun shigo gidannan" Hajiya ta riƙe haɓɓa kafin tace "injiwa?" "Son mana" Anty Jamila tai maganar tana kallon su talatu da suka fito sunata tsotse ƙashi, Hajiya ta nemi guri ta zauna kana tace"Jamila ki fita harkar Ma'aruf wallahi, ƙanwarsa ya gani ita da ƙawarta shine yake kiransu mahaukata, Hajiya tace "ai su biyu suka zo?" Kafin tai wata magana Talatu tace "ai dama kema anan gidan kike?" Anty Jamila ta gyaɗa mata kai. Bayan anyi sallahar isha'i, Hajiya ta nuna musu ɗakin da zasu dinga kwana, babban ɗaki ne, haɗaɗe kai kace ɗakin amarya, ga gado makeke ga katifa mai laushi, wani tangamemen tv ne a manne jikin bango, yayinda remote ya kasance a cikin drowa dake gefe, acan, tsakiyar ɗakin yana malale da grass Capet, yayinda can saman pop ya kasance akwai wasu ado kusa da ƙwanlantarki a taƙaice dai ɗakin yayi kyau over, Koda suka rufe ƙofa, talatu ta fara jin kashi, ta tashi gudidi da ta fara barci tace "ke tahi ki rakani banɗaki alƙur'an kahi nakeji" cikin barci gudidi tace "unn ke komai kahi Allah hi ƙara ai romon da kika hya ne" "Nidai ba wannan ba ki tahi muje in yaso idan muka dawo sai ki ci gaba" Tana maganar tana tsalle, dole gudidi ta tashi suka murɗa handle na ƙofar toilet ɗin suka shiga, "lalala na higa uku wannan aljannar duniyar haka?" Talatu ta faɗa tana ƙarewa toilet ɗin kallo, "kinsan meye gudidi?" Gudidi tace "a'a amma dai yasin sun cucemu ga guri me sanyi da ni'ima sun wani sa mu cikin ɗumi, " "Ke har na ji kahin ya koma, yanzu dai zo mu kinkimo katifa mu kawota nan" Talatu ta nunawa Gudidi toilet, Yasin bazamu iya ba, kafin mu kinkimo ina jin ƙihi, yauwa ka kofi, ta ɗauko wani cup wanda yake ajiye a can sama dan har da abin ajiye shi, kai idan ka ga cup ɗin kamar ka cinye amma wanka akeyi dashi, babu wani datti a jikinsa sai sheƙi yake, Gudidi ta fara dube duben inda zata samu ruwa, "lahh ga rijiya kuma ga dukkan alamu ruwanta ze yi sanyi sosai" Gudidi ta faɗa tana buɗe p-toilet, dumbulo ruwan tayi kafin ta kurɓa cikin jin daɗin sanyi da ya ratsa ta tace "ahhhh" Talatu ta karɓe cup ɗin tare da ɗibowa itama tasha, har tana wani lumshe idanu, sai kuma ta sake ɗibowa, kowaccensu ta sha ya kai cup biyar biyar, daga nan suka fito bedroom sukayi ta kiciniyar ɗauko katifa tafi ƙarfin su, dole suka hakura suka kwanta, "wayo daɗi Talatu ƴan binni suna morewa wannan katifar kamar lallausan burodin hyagon Lado" Gudidi tai maganar tana bubbuga ƙafafunta, da haka har barci ya ɗauke su. Acan ɓangaren Hajiya suna zaune da Anty Jamila, Hajiya tace "Jamila ina son zumuncin mu yaci gaba da ɗorawa da yaɗuwa ta hanyar haɗa auren Ma'aruf da A'isha" Anty Jamila ta ja gauron numfashi kafin tace "Hajiya wato Hajiya wani hanzari ba gudu ba" Hajiya mama tace "ina jinki" Anty Jamila tace "da farko dai a mayar da ƙawar A'isha daga nan sai mu fara tunanin abubuwan da ya dace muyi mata" "Hakane gaskiya banyi tunanin hakan ba sai yanzu, kinga idan ta ga ita kaɗai ce zata fi kintsuwa, akwai wasu kuɗaɗe da zasu shigo end of this month za'a cire wasu daga ciki ayi mata siyayya, Jamila kinsan abu na gaba wanda nake tunani?" Anty Jamila ta bata amsa da cewa"a'a ,ya za'ayi soyayya ta shiga tsakaninsa da Aisha? kinsan dai halin Ma'aruf miskilanci da jinkai, babbar damuwar ma ya ce yana ƙyanƙyamin ƴan ƙauye" Momy na gama maganar tai tagumi, Cikin kwantar mata da hankali anty Jamila tace "karki damu A'isha ƴa mace cefa, sannan wallahi tallahi sai Ma'aruf ya so A'isha fiye da ko wacce mace, amma kafin hakan ya yiwu sai an sha wuya, Hajiya in ba'a haɗasu aure ba, to bamusan wacce zai jajiɓo mana ba, tunda duk ƴan matan ba zama da shi tsakani da Allah zasuyi ba, saboda dukiyarsa zasu so shi, duk da cewar shi ɗin ba mai kule kulen ƴan mata bane" "Hakane, Jamila amma A'isha zata sha wuya sosai" Hajiya ta faɗa tana gyara pillow ta kwanta, "Hajiya na ɗan lokaci ne, bari Allah ya kai mu gobe insha Allah a kuɗin business ɗin a zan ware mata 50k kafin ragowar su zo" Anty Jamila tai maganar sbda tana son kwantar wa da Hajiya hankali. Fans nasan kuna son ku ji waye anty Jamila ko? Anty Jamila ƙanwa ce ga Hajiya mama, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, bayan rasuwar mahaifin Ma'aruf ta dawo gidan Hajiya, tana business ɗin kayan kitchen sbda har babban shago ne da ita, shekarunta 37yrs  kafin zuwanta  tayi aure a Niger, mijin ya gudu Mali ya barta, yakai shekaru 7 bai dawo ba, daga ƙarshe ya aiko mata da takardar saki, shine ta dawo gurin Hajiya mama. Asalinsu ƴan Bauchi ne, dalilin haɗuwar Hajiya da mahaifin Ma'aruf, ta fita anguw a yayi tozali da ita, daga nan magana tayi ƙarfi har akayi aure ga Ma'aruf ɗin mu nan na A'isha komai dozin🤣, wannan kenan. Ko da Dady ya dawo daga masallaci ya samu saudart tana zaune saman

Chapter 5 of 22