ne, na dangin NoNo" Ruqaiyya kam bata gane wannan Hausar ba, ta ce "jekiyi wankan kawai"
Ta miƙe ko ina nata kyarma yake, saboda a duk tunaninta Tana shiga banɗaki Ruqaiyya zata kasheta, ko da Ruqaiyyan ta nuna mata toilet ta shiga sai da tasa saƙata, kana tayi wankan a gurguje, bayan ta fito, taci karo da tsadaddun kaya wanda Ruqaiyya ta ajiye mata, sai dai duk masu gidan sa nono ne, itakam da babu komai a ƙirjinta, wata doguwar riga ƴar kanti tasa, tayi mata yawa, saboda Ruqaiyya tanada tsayi kuma shekarunsu ba ɗaya ba, sabda Ruqaiyya zatayi 23yrs,
Ruqaiyya na fitowa tayi murmishi, kana ta ƙara so ta sanya maɗaurin rigar ta ɗaure mata, hakan ya taimaka mata gurin rage tsayin rigar, ta kawo mata man shafawa ta shafa, sannan tace "zan shiga bedroom ɗin Mom zanyi waya, duk wanda ya shigo kice bana nan, amma idan Mom ce kimin magana"
Gudidi ta amsa mata da cewa "to" bayan shigar Ruqaiyya, sai da Gudidi ta tabbatar da Ruqaiyya ta rufe ƙofar, sannan ta fara shirye-shiryen guduwa, saboda tana ganin Ruqaiyya zata iya kasheta.
Acan bedroom ɗin Mom, Sabeer ne ya dameta da kira, wai sai dai tazo Gidansa kokuma su haɗu a hotel shi bazan iya jure rashinta ba, haƙuri ta dinga bashi, yace sai dai suyi video call idan ta yarda, dole ta yarda tunda tana tsananin sonsa, ya sata ta cire komai na jikinta ta kafe wayar inda zai dinga kallon komai nata, sunata baɗalarsu, shima hakan yayi, yasata tayi wannan ya sata tayi wancan daga ƙarshe dai ta kwanta tana mayarda numfashi, dama da biyu yayi hakan yasan dole sai ta buƙaceshi, tana sauke wani fitinannen nishi tana cewa "Sabeer NA KASA JUREWA bazan iya jurewa ba, Please kazo da mota ka ɗaukeni Please my Sabeer" ransa fess dama abinda yake jira kenan, kasancewarsa mai wayo da dabara, ba wani jimawa sai gashi a ƙofar gidansu, ya kirata a waya, tace masa gata nan fitowa, sai da ta sake yin wanka kana ta sauya kaya, sannan ta fito, "ina kuma yarinyar nan ta shiga?" Ruqaiyya ta tambayi kanta tana ɗaura ɗankwali, ta fito ta zagaye ko ina bata ganta ba, ta tambayi mai gadi yace shima bai ganta ba, hankalinta a tashe ta dinga zagaye anguwarsu, tana dawowa ne ta hango motar Sabeer, ƙara sawa gurinsa tayi, ba tare da tunanin komai ba, yaja mota sukayi gaba...
LAYLA
Rai a ɓace ta ƙarasa shigowa gidan, da kuka ta shiga ɗakin mamanta, mama na zaune tana ninke kaya, Layla ta sameta, cikin Muryar kuka take cewa "mama zan ajiye aiki wallhi bazan iya ba, mama bazan iya JUREWA ba"
Maman bata fahimci komai ba, ta matsar da kayan da take ninkewa cikin yanayi na damuwa tace "Layla meke faruwa? Dan Allah kar in sake ji kince zaki bar aiki"
Hawaye na bin kumatun Layla tace "mama na kamu da soyayyar wanda bai san inayi ba, mama na furta masa yana ƙoƙarin hukuntani, Wlhi har wulaƙanci yayimin, mama bakiga korar karen da yayimin ba, ƙarshe cewa yayi ya tsaneni" Mama ta zaro ido, kana tace "kina nufin yace karki sake zuwa gurin aiki "Layla na kuka tace "eh" maman tace "inko haka ne ai bamu ga ta zama ba, Wlhi tallahi sai inda man mu ya ƙare, amma fa kinsan malam mai yanzu-yanzu aikinsa akwai tsada abinda nakeso dake yanzu, kiyi hakuri ki bar min komai a hannuna tunda yace "abinda zeyi kenan kawai ki ƙyaleshi, ni zan ji da komai" mama ta kai ƙarshen maganar tana kwashe kayan ba tare da ta ƙara sa ninkewa ba ta kaisu uwar ɗaka, ta ɗauko hijabi tana cewa "yanzu nawa ne a gurinki?" Layla tace "dubu biyar, amma ai yau za'ayi mana albashi, mu jira zuwa anjima mama"
Maman ta ajiye hijabin, ta shiga kitchen kana tace mata "idan kuɗin ya shigo kiyimin magana"
Kai tsaye ta wuce ɗakinta tare da tunanin idan har bata mallaki Ma'aruf, ba zuciyarta tana iya fashewa, tana tsaka da tunani ƙarar alert ya shigo wayarta, ihu ta kurma tare da duba alert ɗin, ware idanu tayi tana cewa "Allah na gode maka, zan mallaki wannan haɗaɗɗen gayen ko ta halin ya ya" da gudu ta nufi inda mama take, cikin farin ciki tace mama kuɗi sun shigo 100k yanzu ya za'ayi?"
Mama tace "jeki ciro dubu talatin, kinsan ance komai ayishi da zafi zafi yafi, ke ƴar nan idan har kika auri wannan mutumin ba ni kaɗai ba, har dangina sun warke da nera, mama ta janyo hijabi ta fice tana kiran Layla, a tare suka tafi, Layla na cire kuɗin a POS ta miƙawa mama 40k ta riƙe 10k dama 50k ta ciro ya zamo tanada 15k a hannunta, kai tsaye mama ta wuce bakin titi, nan ta wuce baban Layla a majalisa, mashin ta hau ta gaya masa anguwar da zai kaita, bayan sun iso ta sauka, kana ta sake hawa wani mashin ɗin da zai kaita ƙauyen da take son zuwa, daga gefen hanya mai mashin ɗin ya ajiyeta, ta bashi kudinsa kana ta ci gaba da tafiya, tayi tafiya mai nisan gaske har haɗa gumi takeyi, tana tafe tana ta saƙar inda bikin Layla zai kasance idan har tai nasarar samun Ma'aruf,
Tana isowa gurin wata tsangaya ta tsaya tare da ɗagawa malamin hannu, sbda yana tare da almajirai,
Malamin na ganinta ya washe haƙora, saboda yanayi mata aiki sosai tana kawo masa mutane, aikin mallakar baban Layla ma ita tayi masa,
Tashi yayi daga inda yake zaune, kana yace suci gaba da karatu, iso yayi mata zuwa ɗakin da yake karɓar baƙi, bayan mama ta zauna suka gaisa, ta ce masa "dan Allah ya taimaketa yarinyarta tana kwance babu lafiya ta kamu da soyayyar wanda take yiwa aiki a Company ɗinsa, sun rasa gane kanta" malam yayi murmishi kafin yace "Hajiya wannan duk mai sauƙi ne, wato matsalar shi wanda takeso shine...
Bayi da ra'ayin soyayya, sannan bai sanya mace a lissafinsa ba, amma idan har tace zata iya zama dashi a haka, zanyi mata aiki mai ƙarfi wanda zan janyo hankalinsa ya karkato gareta"
Mama tayi shiru, kafin tace "malam bari in kirata kar ayi abun da ka"
Malam yace "babu network anan, ki fita can waje zakiga wani ƙaton dutse anan muke samun network"
Mama ta fita tare da hawa saman Dutse kana ta fara lalubar number Layla,
Layla na ganin kiran mama tai saurin ɗagawa, cikin farin ciki take cewa "mama an dace ko?"
Mama tace "Layla kina jina?" Layla ta amsa da "eh, "
Tayi mata dukan bayanan da malam yayi mata, kana tace "kin amince ayi aikin?"
Layla tace "eh na amince"
Mama ta katse kiran ta koma gurin malam, tace ayi aiki kawai, malam yace "yanzu ma kuwa, tambayar sunan wanda Layla takeso malam yayi, mama tace "Ma'aruf"
Malam ya zuba wani irin ruwa a ƙwarya kana ya fara ƙwalawa Ma'aruf kira da ƙarfi, sai ga Ma'aruf a cikin wannan ruwan ya baiyyana, gashi a zaune a office yana shan coffee, malamin ya fara wasu surkulle wanda ni kaina ba riƙe su nayi ba, daga ƙarshe ya ɗibi ruwan a gora ya miƙawa mama, kana yace a kaiwa Layla tayi wanka dashi babu sabulu, sannan ga wannan powder idan zataje Company ta shafa, ko wani saurayi ya ganta babu damuwa ai da sunan wanda takeso akayi aikin" mama tace "to malam mun gode sai dai baka faɗi abinda za'a baka ba?"
Malam yayi dariya, kana yace "kuɗin aikinku dubu talatin da biyar" mama ta ƙirgo ta miƙa masa, kana tayi masa sallama, ta fito.
Cike da fatan nasara ta ƙara so bakin titi inda zata samu abin hawa, mai mashin na zuwa ta hau suka wuce anguwarsu, kasancewar idan daga nan zaka tafi ana samun mashin direct zuwa unguwarsu,
Har ƙofar gida mai mashin ya sauketa, ta shige gida zuciyarta fal farinciki, lokacin anata kiraye-kirayen sallahar magriba, sai da tayi sallah kana ta zauna bawa Layla labari, har suna tafawa saboda farinciki, ta miƙawa Layla ruwan maganin da Powder tayi mata bayani, kana tace "bata son mahaifinta ya sani, cikin sirri sukayi abin, har baba ya shigo bayan an idar da Sallah, ya tambayi mama ina taje, tace masa gidan wata ƙawarta, bai sake cewa komai ba.
Washe gari Layla ta ɗau alwashin bazata je aiki ba, zata gwada ta gani maganin yana aiki, kwanan ta biyu babu wanda yai cigiyarta a gurin aikinsu, sosai ta fara damuwa saboda gani takeyi maganin ma baya aiki, ƙarfe 10:am ta kwanta barci mai cike da mafarki mai daɗin gaske, wayarta ta fara ruri, tsaki taja saboda mafarkin masoyinta takeyi gashi wanda yake kira ya katseta, da sauri ta ɗaga kiran cikin tausasa murya tace "Sir Barka da safiya da fatan kana cikin ƙoshin lafiya" ya Subhanallah ji yayi kaf duniya babu Muryar da takai ta Layla daɗi, bayan sun gaisa shine har da ce mata wai yayi missing ɗinta, sannan yana son tazo office idan bai ga kyakkyawar fuskarta ba bazai iya yin aikin komai ba, sosai ta dinga furta masa kalamai masu tsayawa a zuciya cikin sanyin murya wacce ta sake Ratsa zuciyarsa da zallar soyayyarta,
Bayan sun gama waya, shine har da ce mata I love you, da wasu hote things.
Tana ajiye waya ta shirya cikin sauri tare da baɗa powder har taso tayi mata yawa,
Koda taje gurin kayanta ta jima tana zabar kayan da zai dace da shigar da takeson yi, saboda yau ranace ta musamman a gareta, wata baƙar doguwar riga ta ciro wacce akayi mata tattara ta gaba, anyi mata ado sosai da pink and golden ɗin zare, kana an yalwata ta da stone masu walwali, ga wasu tutoci a zagayen jikin rigar, mayafin rigar tayi rolling dashi kana taje gaban mirror ta ƙare wa kanta kallo, ko ba'a gaya mata ba, ta sani tayi kyau sosai, tasa pink lipstick tare da fesa turaruka masu ƙamashi.
Hand bag ɗinta ta ɗauka kana ta rataya, sannan ta ɗauki farin mayafi ta ninkeshi a kafaɗarta, ta fito parlor sai zuba ƙamshi takeyi, Mama ta kalleta cike da ƙauna irin ta ɗa da uwa, tayi murmishi kafin tace "har na hangoki a gidan Ma'aruf, suka kwashe da dariya, Layla tace "mama inasha Allah, adu'arki ai karɓaɓɓiya ce a gurin Ubangiji".
Mama tayi mata Allah ya kiyaye ta fice zuwa company.
Afuwan kuyi hakuri baku samu update da wuri ba, Wlhi nayi baƙi ne, sannan ina jiran shar'hi, wanda suke son shiga group ɗin da nake posting suyimin magana WhatsApp 08141799224
Mom Islam ce...🤙
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_
_SANARWA_
Aslamu alaikum masoya makaranta littafin NA KASA JUREWA, kuyi haƙuri da tsaikon da ake samu gurin posting, jiya na samu matsala da WhatsApp, yau kuma yarinyata ta tashi babu lafiya, alhmdulilah jiki yayi sauƙi, akwai wata sanarwa da naga ya dace in yiwa masu bibiyar labarin, idan har na kai page 50 zan dinga posting ƙarfe 12:pm insha Allah, sannan inayi muku albishir da cewar, daga yanzu zaku dinga samunsa akan lokaci da izinin Ubangiji, masu Arewabook posting ɗinku special ne.
Page 55-56
Washe gari sunada makaranta dan haka ta shirya da wuri, anty Tasneem da Umaimah ne suka ƙara sa aikin gidan, tana fitowa harabar gidan ta hango motar yah Arman, mamaki ne ya kamata sai ta ci gaba da tafiya, har ta iso inda motar tasa take, "yah Arman ina kwana" ta gaishe shi tana ɗan sunkuyawa, "lafiya lau ƙanwata da fatan kin tashi lafiya" ta gyaɗa masa kai, tare da buɗe gidan gaba ta shige, bayan ta rufe murfin motar, yayiwa mai gadi horn suka fice, tunda suka fara tafiya take ta kalle-kalle, shi ko idanunsa suna kanta, duk wani motsi nata akan idanunsa takeyi, ikon Allah ne kaɗai ya kaisu makarantar, domin kuwa bai mayar da hankali ga tuƙinsa ba, mai gadin makarantar nasu na ganin mota ta taho, ya miƙe da sauri yana buɗe get, har cikin makarantar yah Arman ya shigar da ita, bayan ta fito yace "Aysha.." ta amsa da cewa "na'am.."
Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma yace "kinzo da kuɗi ne?"
"Eh yaya" ta faɗa tana kama hanyar tafiya zuwa ajinsu, tunda ta fara tafiya ya zuba mata idanu, har ta ɓacewa ganinsa, sannan ya ja motar kana ya fice daga cikin makarantar.
Da sallama ta shiga class ɗin, wasu ƴan mata guda biyu suka amsa mata fuska cike da fara'a, suna ce mata Aysha Barka da zuwa" duk da bata wani daɗe da shiga makarantar ba, ta fara sabo da ƴan matan ajinsu, sosai ta sake wayewa idanunta suka sake buɗewa, sabda ƴan matan ajin nasu duk wasu sun girme mata wasu kuma ta girmesu, alhmdulilah karatunta yana tafiya inda ya kamata, tunda wasu ma gurinta suke zuwa su tambayeta abinda basu ganeba,
Ko da aka fita break ƴan ajin nasu basu fita ba, kasancewar suna meeting akan inda zasu yi birthday ɗin ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Laurat, ko wacce tana faɗar abinda zata kawo, dai-dai ƙarfinta,
Aysha tayi murmishi kafin tace "nikam zan zo ayi aiki tare dani, idan har na samu abin kawowa zan kawo"
Nan fa suka kaure da ihun murna, suna class har aka dawo break, a ranar malamai huɗu ne, suka shigar musu aji, kuma alhmdulilah duk wani malami da ya shiga ajinsu yana alfahari da basirarsu saboda suna ƙoƙari sosai, bayan sunyi sallahar azhar suka koma aji, yau kam da wuri aka tashesu dan basukai 6:pm ba, saboda ankai wata Malama Hospital,
Ta rasa inda za'ayi ta koma gida, ga shi tsakanin makarantar da anguwarsu akwai nisa sosai, shawarar taje office ko akwai mafita ne ya faɗo mata, bayan tayi sallama shugaban makarantar ya amsa kafin yace "yarinya lafiya?"
Aysha tayi rau-rau da idanu kafin tace "Dama number wayar dreban gidanmu ko ta yayana nake nema.."
Shugaban makarantar ya buɗe wani babban littafi wanda suke ajiye number saboda irin haka, kasancewar ita bata jima a makarantar ba, yasa ya gane sunan yah Arman, ya ɗau number tare da kiransa, ringing ɗaya wayar yah Arman tayi kana ya ɗaga, bayan sun gaisa shugaban makarantar yace "dama mun tashi ɗalibai ne, sakamakon wata Malama babu lafiya an wuce da ita asibiti, Yah Arman yace "okay ta jirani gani nan zuwa"
Kallon tulin file's ɗin dake gabansa yayi, saboda ya fara cikewa kenan aka kirashi, shi kuma bayajin zai iya haƙura ta hau mashin ɗin wani ko adaidaita, yana tsaka da tunanin tafiya makaranta, PA ɗinsa ta sake shigowa a karo na biyu, "Sir dama nazo in gaya maka ne, ya kamata a cike takardunnan a yau saboda yin hakan yanada muhimmanci sosai"
"Naji..."
Shine amsa da ya bata, koda tayi masa godiya ta fita, tsaki yaja mtswww, tare da tashi tsaye, ya ɗauki key car ɗinsa, cikin sauri dan baya buƙatar wani dakatar dashi, ya shiga mota kana ya fice da a guje, yayi gudu sosai kafin ya iso makarantar, a waje yayi parking motarsa kana ya fito ya shiga cikin makarantar, tana zaune ita da ƙawarta, Laurat kasancewar itama bata da number kowa na gidansu sannan bata je office ta tambaya ba, sukan ɗanyi fira jefi-jefi kafin Yah Arman ɗin ya iso, yana isowa inda suke Laurat ta gaishe sa, kafin Aysha ta gaishe sa itama, amsa musu yayi a lokaci ɗaya, tare da cewa "Aysha wacece wannan?"
Aysha tayi murmishi kafin tace "yah Arman ƴar ajinmu ce"
"Me yasa bata tafi gida ba"
Laurat ta karɓe da cewa "drivern mu ne bai zo ba"
Yah Arman yace "okay muje sai in saukeki a hanya"
Laurat tace "ai sai na rigaku sauka ma"
Suka wuce zuwa mota,
Yah Arman da Aysha suna gaba, Laurat tana baya, sunyi tafiya ba mai nisa sosai ba, suka iso ƙofar get ɗin gidansu Laurat, kasancewar gidan yana bakin hanya, tayi musu godiya kana ta fita tare da ɗagawa Aysha hannu tana murmishi,
Sunyi tafiya mai nisa kana ya waigo ya kalleta sannan yace "Aysha ana karatun kuwa?" Ta gyaɗa masa kai,
Cikin yanayi na bada umarni yace "karki kuskura wani namiji ya fara wata magana dake, a school ko a hanya ke ko a ina ne, wlhi idan har kika fara soyayya Aysha kin cuci kanki, sbda inaso kiyi karatu sosai ki zamo wa iyayenki abin alfahari"
Aysha tace "insha Allah yah Arman, Nagode sosai"
Koda suka iso ƙofar gidan anty Tasneem, bai shiga ba, ya ajiyeta a bakin get, tayi masa Allah ya kiyaye hanya, kana ya wuce.
Kafin ta kai ga shiga gidan, sai da ta daɗe a tsaye tana tuno faɗan da Yah Arman yayi mata, lokaci ɗaya zuciyarta ta kasu gida biyu, ɗaya tana ce mata, tabbas Aysha kinyi ganganci, ɗayar kuma tana ce mata "inda kika fara samun farinciki bai kamata kiyi wasa da damarki ba, ga shi Zayden yana mugun sonki kawai ki mance da batunsa,
Ko wacce shawara ta yanke oho, kai tsaye ta wuce cikin gidan tare da yin sallama, sai da ta gaishe da mai gadi kana ta shige ciki.
A parlor ta samesu da Anty Tasneem da Umaimah suna zaune a saman kujera suna hira, sannu tayi musu kana itama tayiwa kanta mazauni tana cewa "wash na gaji"
Umaimah tasa dariya tare da cewa "haka muma muka sha fama da wannan zirga-zirgar" Aysha ta turo baki gami da cewa "anty bakiga na dawo da wuri ba?" Anty Tasneem tace "wlhi kinga tambayar tana bakina, amman dai lafiya ko?"
Aysha tace "ai wata Malama ce babu lafiya"
Sukayi mata adu'ar samun lafiya, Umaimah tace "barin taimaka in kawo miki abinci, Aysha ta washe haƙora tana dariya.
SINGAPORE
Buland island
Wani haɗaɗɗan ɗaki Reed ya shigar da Thabit, cikin kakkausar murya yake gaya masa ɗakin sirrinsa ne, saboda kaf duniya bashi da kamarsa, ɗaki ne wanda aka gina shi da zinare, ko ina walwali yakeyi, sai dai shima ɗakin a tsafe yake sosai, a saman wata kujera mai zaman mutum biyu suka zauna, abin mamaki, a hankali kujerar ta fara tafiya har ta kaisu ga wani rami mai kyau, ramin an sarrafashi da gwala-gwalai, sannan komai na cikinsa gold ne, Oga Reed ya kalli Thabit kafin yace "wannan guri da kake ganinsa, idan har mutum ya shiga ba tare da amincewata ba, gawarsa za'a gani, sannan waɗannan gwala-gwalai da ka gansu mallakina ne, yau ma za'a sake kawomin wasu a cikin dare" Thabit ya jinjina kai, kafin yace "baka da matsala dani shugabana ni mai biyayya ne ga duk wasu abubuwan da ka sakani zanyi maka" Oga Reed yai murmishi kafin yace "yayi dai-dai, yanzu ya kamata mu koma ɗakin da buka baro, sbda inason mu tattauna wasu muhimman abubuwa" Thabit ya jinjina wa Oga Reed kai tare da binsa suka koma ɗakin da suka baro a da,
Thabit ya ɗauki school bag ɗin da ya shiga gurin Oga Reed da ita, zuge zip ɗin baya yayi kana ya ciro wani ƙaton mangwaro jajir dashi, sai dai jan da yayi bai hanashi yin tauri ba, Thabit ya miƙawa Oga Reed, Oga Reed ya miƙa hannu tare da cewa "Me ya kawo mangwaro cikin shirin da muke son aiwatarwa?" Thabit yai murmishi kafin ya juya bayan mangwaron kana ya sanya hannu ya tura ɗan yatsansa sai ga shi ya ciro sabon memory card, ya miƙawa Oga Reed,
Kana yace "wannan memory card ɗin da kake ganinsa akwai abubuwan da zasu amfani tafiyar da zamuyi kawai ka tsaya ka kalleshi daga farko har ƙarshe,
Da sauri Oga Reed ya janyo system ɗinsa kana ya jona memory card ɗin, ya buɗe, videos ya gani sunkai kala uku, ya kunna na farko, sosai videon ya ja hankalinsa, sakamakon tare wasu jiragen ruwa da akeyi, abin takaicin ma, nasa ne, jiragen ruwan sunkai su biyar, amma duk an riƙesu, wasu a cike da ƴan mata, wasu kuma an cika shi da miyagun kwayoyi, wani an cika shi da magunguna masu cutarwa, wasu kuma an cikosu da ma'adanai na ƙarshen shine wanda aka cika shi da wasu manyan kwalaye ko meye a ciki oho..,
Kafin Oga Reed ya kai ga kallon video na biyu, hankalinsa in yayi dubu ya tashi, rai a ɓace ya miƙe tare da kashe kallon, kana ya juya ga Thabit sannan ya marairaice idanu, ya sani idan har waɗannan jiragen ruwan suka salwanta, tabbas kashinsa ya bushe har gida za'azo a ƙamashi, sboda bashi da tarin ƴan matan da zai biyasu dashi, a yau yau ɗin nan ya ƙuduri aniyar ɗaukar ƙwaƙwaran mataki akan wannan ɓarna da ake shirin yi masa, Yace "ɗan uwa Thabit Please I need your help, kaima zaka more duniya idan har ka taimakamin wannan lamari bai faru ba, Thabit yace " Oga baka da matsala dani, dama kuɗi na fito nema saboda talauci ya isheni tabbas idan na zauna baƙinciki zai kasheni" sosai hankalin Oga Reed ya kwanta, ya matso kusa da Thabit kana yace "yanzu me kake ganin ya kamata muyi?" Thabit yai shiru da alamu yana nazari ne, ya daɗe bai cewa oh Reed komai ba, daga ƙarshe dai yai gyaran murya kafin yace "Oga kuɗi zaka fitar masu yawa, saboda mu siye manya manyan masu ruwa da tsaki a ƙasarnan, ta inda ko me zaka shigo dashi babu mai yi maka magana, ya kasance duk wata kana biyansu lafiya lau fa" Oga Reed yace "tabbas na daɗe ina tunanin hakan amma kasan me?, ya za'ayi su fahimceni?" Thabit yace "karka damu zasu fahimta"
Cikin ƙoƙari irin na Thabit ya fara ƙoƙarin gwada number Prime minister, abin mamaki shine oga Reed yace "Thabit ya akayi ka samu numbersa kai tsaye?" Thabit yayi murmishi gami da cewa, idan har kanason dukiya dole ka yi faɗi tashi gurin ganin ka cimma manufarka" Oga Reed ya jinjina kai tare da cewa, amma kana ganin Prime minister zai iya gyara komai?" Thabit yace "eh amma fa sai ka saki kuɗaɗe"
Iya Reed ya gyara zama kafin yace "indai kudi ne babu matsala nidai fatana komai ya tafi dai-dai kar a samu matsala".
Daga nan suka fara shirya yanda komai zai tafiyar musu dai-dai,
Agogon sanarwa ne ya buga daga ɓangaren hagu, Reed ya kai dubansa ga agogon kafin yai tsaki, tare da cewa "shagali za'ayi bana jin zan iya aiwatar da komai saboda wlhi ina cikin wani hali, bana jin daɗin yanayin da nake ciki a yau"
Ya kai ƙarshen maganar yana miƙewa tsaye kana ya fara zagaye ɗakin,
Thabit ya miƙe tsaye shima, kana ya tako har kusa dashi sannan ya dafa kafaɗarsa, cikin ƙarfafa masa guwaiwa yace "Oga Reed ka kwantar da hankalinka, waɗannan ƴan mata da ka tara, kamar inda kace idan an tashi siyar dasu akwai kuɗi sosai, bai kamata mu saka musu fargaba, ni Thabit zan jagiranci shagalin ina fatan zaka goyamin baya" oga Reed yayi murmishi kafin yace "gaskiya Thabit bani da kamarka, ina alfahari da kasancewar mu tare, fatan alheri abokina"
Thabit ya koma ya zauna tare da fara latsa wayarsa,
Acan ɓangaren su Misha, ita da Neria suna zaune a parlor ko waccensu da glass cup a hannunta table ɗin dake gabansu an jereshi da faifan wainar ƙwai da chips na dankali da Biryani, hankali kwance suke cin abincin, kasancewar lokacin bai wuce 7:pm ba, cikin yanayi na jin daɗi da annashuwa Misha tace "Neria ya kamata ki tashi mu shiga boutique mu zaɓi kayan da zamu sa, kinsan time yana tafiya fa"
Wacce Misha ta kira da Neria, wato ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya da bata sani ba, tace "anty Misha Please muje ki zaba min" suka tashi kai tsaye suka wuce gurin zaɓar kaya, akwai wani tsari da gidan nasu yake da, duk wanda zai karɓi kaya sai an bashi wani kati, sai ya wuce gurin karbar kayan, kasancewar gurin akwai kasuwanni kuma duka domin waɗannan ƴan matan, sannan duk wani motsi na kowa yana tafin hannun OGA Reed, hakan yasa babu wanda yake yunkurin cutar dashi, CCTV tsaf zai nuno kowa.
Ƙarfe 8:pm ilahirin ƴan matan dake cikin wannan gida suka fito, ko wacce da kalar adon da tayi, amman duk cikinsu babu wacce ta sanya rigar da ta kawo mata gwaiwa, daga iya cinya ne, sai wacce da kaɗan ta wuce mazaunanta, cikin taku na isa da sarauta kai kace wani Sarki yake takowa, tun da ya fara idanun ƴan matan dake estate ɗin ya dawo kana Thabit dake takowa cikin hall ɗin, yana sanye da kaya irin na sarakai, tabbas duk wani mai fahimta ya fansa yasan shi ɗin musulmi ne, domin kuwa bai yi kama da kalar kafirai ba,
Yana tafe securities na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 22