girgiza kai tare da ɗauko wani kaskon wuta kana ya zuba wani abu hayaƙi ya tashi, sannan ya matso kusa da su ya ɗibi wani ruwa mai warin gaskiya ya watsa musu, kafin ya sake ɗibo wani garin magani ya kaɗa a ruwa ya basu suka sha, sannan yayi kabbara Allahu Akbar... Allahu Akbar.... Allahu Akbar, sau uku, abin mamaki sai ga Majeed da Najma sun baiyyana cikin kayan da suka fito dashi daga gidan tun watanni takwas da suka wuce, dukkansu a durƙushe suke, sai da tsohon ya sake ɗibo wani man shafawa ya shafa musu a guwaiwar hannu da ƙafa da wuyansu, kafin ya umarcesu da su miƙe tsaye, suka miƙe tare da fara rarraba idanu, dukkansu sai suka fashe da kuka a tare, tsohon ya ɗaga musu hannu kana yace "godewa Allah ya kamata kuyi, bai kamata kuna kuka ba, ya ƙwalawa yarinyarsa kira wacce bata wuce sa'ar Najma ba, sannan ya ƙwalawa yaronsa wanda Majeed ma zai girme masa kamar da shekara ɗaya, yace "a basu ruwan wanka da abinci, shi namjin ya bawa Majeed kaya, ita kuma macen ta bawa Najma kaya, suka amsa da cewa "to"...
KANO
ana gobe birthday party ɗin Laurat, Aysha ta gayawa anty Tasneem da Umaimah, bata hanata zuwa ba, hasali ma har tambayarta tayi mai zata kai wa ƙawar Tata a matsayin gift, Aysha tayi shiruuu, sboda bata sam mai ya dace ta kai mata ba, anty Tasneem tace "gobe idan Allah ya kaimu sai in baki abinda zaki kai mata, "Umaimah zakije koh?" Aysha ta tambayeta,
"Eh man zuwa sosai ma"
Umaimah ta bata amsa, wunin ranar dai sunata tsara irin shigar da zasuyi, kai kace sune masu yin birthday ɗin, yau kusan kwananta uku bata kunna wayarta ba, Umaimah tayi tayi akan ta kunna saboda kar Zayden yayita tunanin ko bata cikin ƙoshin lafiya amma fur taƙi sai yau, kamar jira yake yi, ta kunna wayar, aiko sai ga kiransa tare da text message, kiran nasa ta ɗaga, cikin sanyaya murya, "amincin Allah ya tabbata ga masoyiyata abin alfaharina, ina fatan dai kwana biyu lafiya?"
"Uhm lafiya lau"
"Mai yasa wayarki bata shiga,"
"Haka kawai"
"Kinason ki azabtar dani ne?"
Ta fashe masa da kuka mai sauti, da sauri ya kalli wayar dake hannunsa kana ya kara a kunnensa kafin yace "Please beauty ki gayamin meke faruwa?"
"Zayd ina sonka, bani da damar da zan iya furta maka hakan"
Ta katse kiran tare da ajiye wayar, dariya ta farayi ga hawaye na, zuba, ta share hawayen, tare da kallon gefenta taga babu kowa, hamdala tayi kana ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwalah kana ta shimfiɗa sallahya sannan ta kabbara sallahar magriba, tana cikin yin Sallah sai ga Umaimah ta shigo, da alamu daga can parlorn ta ɗauro alwalah, itama ta kabbara sallah, bayan sun idar sunyi addu'oinsu, Aysha ta kalli Umaimah, kafin tace "kinsan me?" Umaimah ta girgiza kai, Aysha tace "wlhi har tunanin ranar da zan koma gidan Hajiya nakeyi, babbar damuwata yah Ma'aruf, bashi da mutunci ko kaɗan"
Umaimah tace "uhm na taɓa ganinsa sau ɗaya a wata hira da akayi dashi a TV, wlhi bana fata in ganshi a zahiri, saboda Guy ɗin akwai kwarjini sosai, ga shi Ubangiji ya haɗa masa komai duka, ance ɗan adam tara yake bai cika goma ba, nikam a ganina wannan bawan Allahan ya cika ɗari ma, ga kyau ga kuɗi ga izza wow amma fa tsoronsa nakeji" Aysha tayi murmishi kana tace "wato Umaimah, babbar damuwata komawa gidan, kamar dai yadda na gaya miki, dalilin da yasa na fara tunani, hamm uncle Junaid ya kusa dawowa kinga anty Tasneem bazata barmu a gidannan ba, i swear" Umaimah tace "faɗi ki ƙara barinma kekam da zaki sace zuciyar duk wani lafiyayyen namijin da yayi tozali dake" Aysha ta zaro idanu tare da cewa "wlhi sharri dai babu kyau"
Umaimah tace "wlhi gaskiya nake gaya miki lokaci ɗaya kika wani cika, ƙila baki ga hips ɗinki bane ko? One Month nazo gidannan lokacin ma ƙirgen dangin da kika farayi ƙanana ne, ga shi yanzu har ana saka bra, uwa uba 3 weeks ago kika fara period, hmm ai dole ki fara tunanin makomarki, amma ya maganar makarantar ki fa?" Uhm Umaimah, alhmdulilah insha Allah na koma Abuja zan ci gaba, amma nafison mai haɗe da islamiyya" Umaimah tace "ai karatun addini yanada kyau sosai, haɗuwarmu zatayi wuya sai dai a waya, wlhi zan gargaɗeki karki kuskura ki nunawa wani wayarnan, idan ba haka ba, wlh sai kin shiga tashin hankali" Aysha tace "hauka nakeyi Umaimah?"
Aysha ta faɗa tana riƙe baki,
Sunsha hira a daren, bayan an kira sallahar isha'i sunyi suka kwanta, wayar Umaimah ta fara ringing, tana dubawa taga Zayden, ta zaro idanu, tare da cewa "Aysha ga masoyinki ya kira, tayi kamar bazata karɓi wayar ba, ta miƙa hannu ta karba tare da karawa a kunnenta, "aslmu alaikum"
Tayi sallama,
"Wlkslm" Zayden ya amsa, daga jin muryarsa ma ta nuna yanayin damuwar da yake ciki,
Kafin yace "beauty dan Allah ina son in roƙeƙi wata alfarma, sannan inason ki gayamin iya gaskiyarki saboda bana son ƙarya.."
In Cold voice tace "ina jinka"
"Aysha kina sona, tsakaninki da Allah?"
"Tayi shiru, kafin tace "eh sosai ma"
Yace "good"
Ya sake cewa "Aysha bana son idan muna magana ki dinga katse min kira"
Cikin sanyin murya tace "bazan sake ba"
A karo na uku ya sake cewa "yanzu meye yake damunki?"
Ta marairaice murya tare da cewa "babu komai"
"Yaushe zamu haɗu"
Kai tsaye tace masa "ko gobe"
Yace "a ina zamu haɗu?"
Ta jujjuya idanu kafin tace "zan kiraka, ƙawata ce zatayi birthday"
Yace "okay, Allah ya kaimu"
Tunda ya katse wayar Aysha, tunani iri-iri ya dameshi, sakamakon sonta da yake neman zautar dashi, duk inda ya zauna sai ya yi maganarta har cikin danginsa da abokansa, shi kasansa ya kasa misalta son da yake yi mata, wanda bai taɓa yiwa wata mace a faɗin duniya ba"
Itama a nata ɓangaren haka ne, soyayyar Zayd ta fara nisa a zuciyarta.
Har Umaimah tayi barci tana rungume da wayarta...
Washe gari
Tun bayan da sukayi sallahar asbha suka fara aikace-aikace, daga nan sukayi wanka, already dama babu school sboda malamar su anyi wa wata Malama cs headmastern su shima yana Hospital,
A gurguje sukayi breakfast sukuma masu aikin sukayi moping,
Ƙarfe 9:am abinci ya kammalu aka jere a dinning, sai da suka shirya tsaf, cikin Abaya baƙaƙe, sunyi matuƙar kyau, saboda abayar ta amsa sunanta, duba da ƙyaleƙyalen dake jikinta, duk wanda ya kallesu tabbas sai ya sake kallo, saboda har wani walwali takeyi sukayi rolling veil ɗin a kansu, ba wani abinci mai yawa sukaci ba, tsabar ɗoki da murna, anty Tasneem ta kawowa Aysha wata haɗaɗɗiyar sarƙa mai zobe, da turare mai tsada harda su ribom masu kyau, Masha Allah sunyi kyau sosai, Aysha tayi godiya tare da cewa "anty bakice munyi kyau ba"
Anty Tasneem tace "wlhi kunyi kyau sosai, sukayi hoto,
Tare da yi mata sallama, kasancewar ko wacce ta fito da hand bag ɗinta, anty Tasneem ta miƙawa Umaimah 10k tace ko zasuyi siyi wani abun, sukayi mata godiya kana suka wuce.
Kai tsaye parking space suka nufa, sukayi wa driver kwatancen anguwar da zai kaisu, suka shiga backside yayiwa motar key bayan an buɗe masa get.
Cikin ikon Allah suka iso anguwarsu Laurat har ƙofar gida ya kaisu, suka gaya masa time ɗin da zai dawo ya ɗauke su, ya wuce.
Nocking sukayi a get na gidan, mai gadi ya leƙo tare da cewa "sannunku daga ina?"
Umaimah tace "nan ne gidansu Laurat?"
Da sauri mai gadi ya gyaɗa kai gami da cewa "eh nan ne, amma daga ina kuke, kuyi hakuri wannan tambayar da nakeyi muku tana ɗaya daga cikin sharuɗan shiga wannan gidan"
Aysha tace "babu komai, ta buɗe hand bag ɗinta kana ta ciro wata ƴar takarda sannan ta miƙa wa Umaimah, tace ta kira mata lambar, ringing ɗaya Laurat ta ɗaga tare da cewa waye?" Aysha tace "gamu a ƙofar gidanku"
Cike da murna Laurat ta katse kiran tare da fitowa harabar gidan tana yiwa mai gadi magana akan ya buɗe musu get, bayan ya buɗe musu suka shigo, wow, hmm masu karatu gidan fa Masha Allah komai yayi, hatta motoci biyar ɗin dake jere a gurin ajiyar motoci duk na yayi ne masu tsadar gaske, Laurat tana sanye da gown irin ƴar kanti, kanta yasha gyara sai sheƙi yake yi Masha Allah, daga nan tayi musu iso zuwa cikin gidan, babu kowa a gidan, saboda an ɗaga birthday ɗin, sakamakon Dad ɗin ta yace ta bari sai next week, Aysha kuma bata sani ba shiyasa suka zo, kai tsaye ɗakinta ta kaisu, ɗakine babba kai kace ɗakin wata macen, Masha Allah ɗakin yayi kyau, bayan sun shiga suka zauna a wasu ƙawatattun kujeru, Laurat ta fita zuwa kitchen, ta kawo musu sakwara da miyar egusi, da kunun gyaɗa mai ɗumi wanda ya ji coconut da milk,
Bayan ta ajiye musu a saman table ta koma ta zauna, kafin suka fara gaisawa, nan take gaya musu ai an ɗaga birthday ɗin, Aysha ta ciro kayan da Anty Tasneem ta bata ta miƙa mata, sosai Laurat tayi farinciki da wannan tsaraba, saboda a halin yanzu sun shaƙu da Aysha sosai,
Basu wani ci abincin sosai ba, Laurat ta ƙurawa Aysha idanu, A'isha dai da ta gaji da kallon da Laurat keyi mata tace "ke ya dai lafiya?"
Laurat ta sauya mood zuwa na damuwa, kafin tace "Ƙawar Aysha Please sunanki fa?" Umaimah tayi murmishi kafin tace "sunana Umaimah, ni ƴar uwarta ce" Laurat tace "alhmdulilah"
"Dan Allah Umaimah ki taimakeni akan manufata Please ku fahimceni dan Allah"
Sosai ta jefasu cikin alhini duk da basu ji me take son cewa ba,
Laurat ta sakko ƙasa tare da durƙusa guwaiwoyinta ƙasa, ta haɗe hannayenta kafin tace "dan Allah Aysha kiyimin wata alfarma dan Allah"
Aysha tace "Laurat wace irin alfarma ce hakan, da har kika durƙusa min?"
Laurat ta shiga gallery na wayarta ta nuno wani kyakkyawan hoto, wanda wani matashi ne a jikin hoton, shi ɗin ba fari bane, baƙi ne, sannan baƙinsa ba mai muni bane, yanada gashin baki mai kyau, sannan ya gyare sumar kansa, ta nunawa Umaimah, kafin tace kinsan wannan?"
Umaimah ta gyaɗa kai, tare da cewa "wannan ai yayi ambassador a ƙasar waje, kuma har yanzu ana damawa dashi dan na gaban goshi ne, ga kuɗi kamar zai kasheshi" dukkansu basu san me take nufi ba, tace "kuyimin alƙawarin duk abinda nace zaku amince" a tunaninsu wata maganar ko neman shawara takeyi, cikin haɗin baki suka amsa da cewa "zamu amince"
"Laurat tace "Aysha dan Allah ki auri Dad ɗina, shine a jikin hotonnan, ni kaɗai nake zaune a gidannan sai masu aiki, sannan shi bai cika zama a Nigeria ba, sannan yana dawowa Nigeria baya cin abincin waje ko na masu aiki nice nakeyi masa, tun bayan rasuwar mahaifiyata, tana aihuwata ta rasu, wlhi tallahi Aysha baki da matsala da Dad, ƴan uwansa sunyi masa maganar aure har sun gaji dan Allah ki taimakeni"
Laurat ta ƙarshe maganar tana, sake cewa "karki manta keda Umaimah kunyi min alƙawari, sannan Ubangiji yana girmama alƙawari"
Kuka take yi sosai, yayinda Aysha ta daskare a gurin, Umaimah kam ta kasa koda motsa bakinta ne, tsabar firgici, saboda basuyi tunani ko tsammanin jin waɗannan zafafan kalaman daga bakin Laurat ba, ta sake fashewa da kuka tana cewa "Please nasan zaki iya kinada hankali nutsuwa tausayi da duk wani hali na gari da namiji ya kamata ya samu gurin mace, Please say something...!
Tofa, 2days nayi talauci, rashin data yasa banyi muku posting ba, kuyi hakuri dan Allah.
Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
Mom Islam
Page 61-62
"Innalillahi wa inna ilahir raji'un"
Hajiya Lubabatu ta ambata, cikin yanayi na damuwa, kana ta ci gaba da tafiya tana jimamin Gudidi, babbar damuwarta ina zataje..sannan da su wa zata hadu...a wane hali zata kasance?"
Har ta iso gurin get ɗin gidanta tana ci gaba da tunaninta, nocking tayi mai gadi ya buɗe mata, kana yayi mata sannu da dawowa ta amsa tana shigewa ciki, tun kafin ta kai ga shiga cikin gidan ta fara ƙwalawa Rukaiyya kira, amma shiru, kamar babu kowa a gidan, sosai ranta ya ɓaci ta shiga ɗakinta tare da duba ko ina babu Rukaiyya babu alamarta, wasu kaya ta gani a saman kujera sunkai kala tara, duk na Rukaiyyan ne, ta nemi guri kana ta zauna tare da tunani iri-iri kwance a zuciyarta.
Hotel
Tun ƙarfe 10:am Rukaiyya ta bi Sabeer ga shi yanzu har ƙarfe 4:pm bata dawo ba, hankalin Hajiya Lubabatu ya tashi sosai, saboda bata san Rukaiyya tana yawace-yawace ba,
Astagfirullah innalillahi wa inna ilahir raji'un, dan girman Allah iyayena mata mu kula, tabbas duk wanda Ubangiji ya azurta da aihuwar ƴa mace, tofa bata da kwanciyar hankali har sai ta ganta a ɗakin mijinta, bawai dan kinada budurwar ƴa ki sake mata komai ba, wlhi tallahi mu kula, ranar lahira sai Ubangiji ya tambayemu, akan tarbiyya,
Suna kwance a saman bed ya rungumeta, ga dukkan alamu babu kaya a jikinsu, hankali kwance suke barcin, Ruqaiyya ce ta fara farkawa, da sauri ta sauko daga gadon tare da wucewa toilet tayi wanka ta tsarkake jikinta, kafin tazo ta fara tashin Sabeer, a hankali ya buɗe idanu tare da cewa "Ruky karki damu fa.."
"Wane irin kar in damu har ƙarfe biyar da rabi tayi, ka kalli agogon dake jikin bango ka gani mana, idan momy tazo ai na shiga uku wlhi sai ta kusa kasheni"
Ruqaiyya ta faɗa tana yayibo ƙaton hijabinta da hand bag ɗinta, da sauri ya tashi, cikin sauri shima ya shiga toilet ɗin, tare da yin wanka kana ya fito, ko mai bai shafa ba, ya sanya kaya yayi mata rakiya suka fito har harabar hotel ɗin, "ban gane ba mai kake nufi?"
Ruky tayi masa magana saboda ta fahimce bazai mayar da ita gida ba, "kinga kiyi hakuri Wlhi barci nakeji sosai, kinga a irin wannan condition ɗin bai kamata inyi driving ba, sai mu samu matsala"
Ya ƙarashe maganar yana ɗaga mata gira,
"Uhm Sabeer ni zaka wulaƙanta, a lokacin da ka buƙaci jikina ɗaukoni kayi har nan, bayan ka biya buƙatarka sai ka watsar dani ko?, kana nufin sai gobe kuma idan ka sake jin wani jarabar sai ka nemeni?"
Tayi maganar tana zubar da hawaye, kafin ya buɗe baki yace mata wani abu, har ta buɗe get ta fice da gudu, tana kuka, tafiya take tana cewa "tabbas Allah ba azzalumin kowa bane, na cutar da kaina wayo Allah, bansan mai yasa Sabeer ya lalatamin rayuwa irin haka ba, innalillahi wa inna ilahir raji'un, ta dinga mai-maitawa tana kuka, sai da ta gaji da tafiya, kafin ta tsari mai adai-daita ya kawo ta har ƙofar gida, koda ta fara buga get ɗin kamar zata cireshi tsabar bugu, saboda gabaki ɗaya bata cikin nutsuwarta, mai gadi ya taso zai yi masifa ya ga itace ai yayi gum da bakinsa, da gudu ta shiga gidan tana ci gaba da kuka, har ta shigo parlon momynta tana cigaba da gunjin kuka,
Momyn ta fito da sauri kana ta kalli Rukaiyya tare da cewa "Rukaiyya ina kikaje me kuma ya faru?"
Bakinta ta toshe da tafin hannunta tana kuka,
Cikin daka tsawa tace "ina kikaje?"
Muryarta na sarƙewa tace "mo..mo...momy, na...na...naje, islamiyya ne, shine malaminmu ya ce ya koremu"
Momy ta nemi guri ta zauna, kafin tace "amma ai baki gayamin zakije ba"
Tana shesheƙar kuka tace "momy Ummu ce tazo bayan fitarki tace wai yau akwai islamiyya, kai tsaye momy tace "toh shikenan"
"Mai ya haɗaki da Yarinyar nan, na ganta a can kusa da bakin titi, ko da na tambayeta, na nemeta na rasa ta gudu?"
Zaro idanu Rukaiyya tayi, kafin tayi yunkurin bata momy amsa, cikin rashin tsammani amai ya taho mata wanda ita kanta bata san da zuwan aman ba, "innalillahi Rukaiyya dama baki da lafiya ne"?
Ta jefo mata tambaya, tana miƙewa da sauri ta kawo ruwa a cup kana ta shafa mata a fuska, sannan ta riƙe hannunta suka shiga toilet, ta wanke baki, acan toilet ɗin ma tayi amai sosai, lokaci ɗaya jikinta ya fara karkarwa, cikin sauri momy ta ɗauko mata rigar sanyi, tare da cewa "Rukaiyya mai yake damunki?"
"Uhm momy wlhi zazzaɓi ne"
Momyn ta fice da sauri tana ƙwalawa mai gadi kira akan ya kira mai mashin,
Bai daɗe da fita ba, sai ga shi nan ya shigo tare da mai mashin ɗin, ta riƙe hannun Rukaiyya suka fito harabar gidan, momy ta miƙa mata hijab ta saka, kana ta hau mashin ɗin momy ta hau bayanta suka wuce Hospital,
Sai da suka fara ganin likita, akayi wa momy tambaya "tun yaushe ta fara rashin lafiyar?" Momy tace "yau ne ta dinga amai"
Doctor yace za'ayi mata test, momy tace babu komai,
Bayan an ɗibi jininta aka bata wata roba tayi fitsari a ciki, kana aka ce suje su zauna kafin su jira result sai asan taimakon da ya dace a bata, sun ɗan jima a saman benci a zaune, doctor ya ƙwalawa momy kira, bayan ta zauna yace "tanada aure ne?" Momy tace "bata da aure yarinyar da ko samari bata da su" doctor ya jinjina kai kafin ya fara sosa kansa, saboda ya kasa yi mata bayanin abinda ke faruwa, cikin tuhuma momy tace "doctor lafiya naga bakinka yana ta motsi kamar kana son cewa wani abu?"
Doctor ya ajiye pen ɗin dake hannunsa kafin yace "Hajiya idan yarinyar ki ce, tanada cikin wata biyu, idan baki yarda ba zaki iya zuwa wani Hospital ɗin.
Tun da ya fara magana momy ta daskare a gurin, lokaci ɗaya jikinta ya fara karkarwa, da sauri ta ce "Doctor ciki fa kace?"
Doctor ya sake gyaɗa kai, "Nagode nawa ne kuɗin?"
Ya gaya mata ta bashi sannan ta fice da sauri, "Rukaiyya tashi mu je gida"
Momy ta faɗa tana kallon Rukaiyyan, kafin ta miƙe, momy ta rigata yin gaba, sboda jikinta babu ƙarfi sosai, momy na fita a hospital ɗin ta iso bakin titi, hankali a tashe, Ruqaiyya na zuwa suka hau mashin suka dawo gida, bayan sun shigo parlorn Ruqaiyya ta nemi guri a 3sitter kana ta kwanta, sboda kasalar da takeji, sai da momy ta wuce ɗakinta tasha kuka mai isarta kafin ta fito parlor, "Ruqaiyya tashi zaune"
Momy ta faɗa a taƙaice,
Ruqaiyya ta tashi zaune kamar inda momy ta buƙata, "waye yayi miki ciki, ashe dama yawon banza kike zuwa?"
Momy ta jefo mata waɗannan tambayoyin, ƙirjinta ne ya bada rass, ta dafe ƙirji kafin tace "haba momy kinfi kowa sanin wacece ƴarki, wlhi bana bin kowa hasali ma ko saurayi bana..."
Momy ta gwaɓe mata baki tare da cewa "wlhi tallahi idan har baki gayamin wanda yayi miki ciki ba, sai na kasheki"
Da sauri ta zabura, kafin momy tayi wani yunƙuri ta ɗauki wayarta ta gudu, kasancewar get ɗin abuɗe yake, ta fice.
Momy ta ɗora hannu a kai tare da kurma ihu, tsananin baƙinciki da takaici yasa ta kasa furta komai, a gurin ta durƙushe tana kuka, a halin yanzu bata san wa zata ta ra da wannan maganar ba, waye zai fahimceta?"...
*****
Har yanzu tana emergency room bata san inda kanta yake ba, shiko yana zaune a office ɗin doctor, kasancewar doctorn abokinsa ne, yayi tagumi cikin wani irin yanayi, sai mai-maita Innalillahi wa inna ilahir raji'un, gabaki ɗaya ya gama rikicewa saboda tunaninsa yarinyar da ya bige bazata rayu ba, mutuwa zatayi, duba da jinin da ya zuba daga jikinta mai yawa sosai, Doctor yace "Prince Murad ka kwantar da hankalinka da izinin Ubangiji komai zai zamo normal"
Prince Murad ya miƙe tsaye, sanye da Kayan sarauta, tsantsar cikar kamala da izza gami da ruwan sarauta duk sun yalwatu a jikin Prince Murad, "Allah ya bata lafiya" ya faɗa yana ficewa a office ɗin, doctor ya amsa da amen"
Dama dogarensa na daga bakin ƙofa, suna ganin ya fito, suka zube a gurin suna miƙa jinjina,
Ransa a ɓace yake, saboda ko kaɗan baya fatan ya ga ya wulaƙanta wani ɗan adam a doron duniya, burinsa kyautatawa al'umma,
Kai tsaye haɗaɗɗiyar motarsa ya shiga, drivernsa ya rufe murfin motar, ganin haka yasa dogarai suma suka shiga tasu motar, Prince Murad yace kaini "gurin Umma"
Kai tsaye suka wuce garin MANDU, har cikin gidan sarki suka shigar da motar, inda sukayi parking a inda aka tanadarwa motoci, bayan an buɗewa Prince Murad murfin mota ya sauko da ƙafarsa ɗaga, kafin ya sake sauko da ɗayar ƙafar, yanayin takunsa kaɗai ya isa ya tabbatar maka da ko shi waye, yana tafe dogarai na biye dashi, ko da yazo shiga babban parlon Sarauniya, tsayawa sukayi daga bakin ƙofa, tafiya yakeyi ko gabansa baya kallo, saboda tsananin ɓacin ran da yake ciki, bai yi tunanin kiranta a waya ba, har ya wuce parlon bai san da cewar Sarauniyar na zaune a parlon ba, hadiman ta suna ganin Prince Murad suka duƙar da kansu ƙasa, "Murad lafiya na ganka cikin wannan yanayin?"
Sarauniya ta tambayesa, tana daga kishingiɗe a saman wata kujera mai kama da katifa tsabar taushi, da sauri hadiman suka fice, suna cewa "Allah ya taimakeki Allah ya ƙara Miki lafiya, mun barki lafiya" a hankali ya juyo cike da sarauta, kafin ya zo gabanta ya nemi guri ya zauna a saman Capet, kana yace "Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Umma na kusa kisan kai, a halin da ake ciki ma, wlhi bansan zata rayu ko bazata rayu ba oho" a ɗan firgice ta tashi zaune tare da gyara zaman alkyabbar dake jikinta, kafin tace "Murad mai kake nufi ban gane ba?"
Idanunsa sun kaɗa sunyi jajir yace "Umma muna cikin tafiya a mota, Umar driver ya kaɗe wata yarinya tana can rai a hannun Allah, Umma yanzu idan har yarinyar nan ta mutu ya zamuyi?"
Sarauniya tace "Murad ka kwantar da hankalinka, komai fa ikon Allah ne, shi yake raya wanda yaso sannan ya kashe wanda yaso, yanzu dai waye a gurinta?"
Kan Murad a duƙe yace "Allah ya taimakeki, Falmata ce a gurinta"
Sarauniya ta jinjina kai, sannan tace "ya kamata kaje kayi wanka kaci abinci, saboda kar ulcer ɗinka ya tashi, idan baka manta ba, doctor ya ɗoraka akan magani sannan yace "ba'a son ka ji yunwa komai ƙanƙantar ta?" ya miƙe tare da fita daga sashen mahaifiyar tasa kafin ya wuce sashen sa, wani haɗaɗen ɗaki ya shiga ko ina walwali yakeyi Masha Allah, a kujera one sitter ya zauna, ya fara tuno irin hatsarin da sukayi, yana tsaka da tunani, Ruma ta shigo fuskarta ɗauke da murmishi, ko sallama babu ta yiwa kanta mazauni, kafin tace "yaya Murad lokaci yayi da zamu fito mu faɗawa mai martaba da Umma cewar mun shirya a ɗaura mana aure.." da sauri ya kalleta, kallo yakeyi mata mai cike da zallar tsana, ransa a ɓace yace "tashi ki fita.. ta wani matso kusa dashi tare da cewa "ko kanaso ko bakaso aurena ya zame maka tilas ragowar jiji da kai da taƙama duk zanji dasu, nidai burina..."
Kafin takai ƙarshen maganar ya wanka mata mari lafiyayyu masu zafin gaske, wanda yasa ta riƙe kumatunta, tare da ficewa da gudu, tayi sashen Fulani...!
Comments and share fisabilillah
Mom Islam ce 08141799224
NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
Book
Page 63-64
Kuyi following ɗina Arewabook
https://arewabooks.com/u/momislam11
_Mom Islam_
A hankali ta fara motsa hannayenta, tare da yunkurin tashi zaune, tsananin zafi da raɗaɗi ne sukai mata sallama, saboda duka jikin nata ciwo yakeyi mata, in ka cire goshinta da ya sha ɗauri, "yi haƙuri insha Allah zaki samu lafiya"
Wata likita tayi mata magana cikin tausasa harshe,
Tabbas tasan lokacin da ta zata tsallaka titi, bayan nan babu abinda zata iya tunawa sai ganinta da tayi a asibiti, meke faruwa da ita?,
Kuka ta farayi tare da mutsu mutsu, wanda yasa ta kusa tsige drip ɗin dake hannunta, likitoci biyu ne a ɗakin hakan yasa suka riƙeta sosai, tana ta kuka, tana cewa "nikam na haƙura da rayuwar binni wlhi gara in koma gurin mahaifiyata wayo Allah na zan mutu waiyyo Allah..."
Duk waɗannan maganganun da takeyi, a kunnen Prince Murad ta yisu, ba kayan ɗazu bane a jikinsa ya sauya wasu, sai dai a sama akwai wata ƴar riga mai tambarin gidan sarauta a jiki, ga dukkan alamu bayan yayi wanka ne ya dawo Hospital ɗin, cikin takunsa mai ɗaukar hankali ya shigo room ɗin tare da amsa gaisuwar likitocin da sukayi masa, "ya jikin?"
Ya tambayeta cikin dakakkiyar muryarsa,
Waro idanu tayi, kafin tace "da sauƙi, kana ta mayar da kai ta kwanta, ammafa abin ya bata mamaki,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 22