sake ta dawo mata gida babu kuɗi"
"Ko bin maza zanyi kenan?" Tai maganar tana tura kuɗaɗen cikin ɗankwalinta.
Da sauri ta miƙe tsaye kana ta fara tunanin meye mafita a gareta,
Tafiya tayi mai nisa wanda ita kanta bata san inda zataje ba, tabbas akwai wani abu da yake birgeta da rayuwar ƴar binni, tana bala'in son ilimi a rayuwarta bugu da ƙari tana son itama ta zamo kamar ƴan gayun da ta gani lokacin da suka je binni, tuno, rayuwar da Talatu zata ci gaba da yi tayi, hakan ya ƙara mata ƙwarin gwaiwar son taga ta fita a ƙauyensu, tana tafiya tana tafiya sai gata a tashar mota, gabaki ɗaya ta riƙiɗe sosai, bata ma san inda zata nufa ba, duk a tunaninta idan ta shiga mota, kai tsaye gidansu Anty Jamila za'a kaita, hakan yasa ta kwantar da hankalinta tare da zama daram a mota, har ta fara hango idan har ta je suka haɗu da Talatu zasu zuba yanga, tana tsaka da tunani karen mota yace "ta kawo kuɗi, ta tambayeshi nawa ne yace mata dubu "uku" ta ƙirgo ta miƙa masa ya rage saura dubu biyu kenan, ta ƙullesu da kyau, kana ta zubawa masu zirga-zirgar wucewa idanu,
Ta ɗan ɗauki lokaci a tasha motar bata tashi ba, dan har adu'ar kar Allah ya haɗata da wanda ya santa ta dingayi har motar ta tashi, ...
ANGUWAR ME GISHIRI
Dake cikin Ƙauyen Saminaka.
Wani gida na hango wanda aka gina shi da jar ƙasa, ko da yake yawancin gine ginen haka suke, gidan zagaye yake da katangar buhu, kasancewar katangar gidan ta fadi, malam Habu na Lami tsoho ne amma ba irin tukuf ɗin nan ba,, yanada matarsa ɗaya, Baaba Lalai, Baaba Lalai itama ta tsufa, saboda ko girki bata iya yi, sai dai surukarta wato matar ɗanta idan tayi take zubo mata, yawancin cimar tasu ma daga kunu sai fate, sai tuwo, duk da arziƙin dabbobi da Allah yayiwa malam Habu bai sa ya azurta iyalansa ba, a lissafin mutanen ƙauyen idan aka tashin lissafa masu tarin dukiya har dashi a ciki, saboda ko wacce shekara idan ka ka tayi lokacin da ake kwashe amfanin gona, Allah ya albarkaci nomansa, hakan yasa koda yaushe a cikin siyo dabbobi yake, wato ya siya ya siyar,
Yauma kamar kowane sati, kasancewar duk ranar Laraba ake cin kasuwar Saminaka, acan yake siyo dabbobin, kama daga Akuyoyi da raguna harda kaji na gida, sannan kuma ya siyar a kasuwar idan har aka ɗora masa riba,
Tun bayan da ya dawo daga sallahar asbha yake ta gyaran igiyoyi wanda zai ɗaure dabbobin nasa, bayan ya gama gyaran igiyar ya ƙwalawa magidancin ɗansa kira, kasancewar a gida ɗaya suke, "wanda ya kira da halliru ya fito yana cewa "hannu baba ka gama gyaran igiyar?"
"Eh halliru na gama, ungo ɗauresu sai mu tafi"
Cikin umarnin mahaifinsa ya ɗaure dabbobin kusan su ashirin, suka wuce kasuwa a ƙafa, koda suka isa babu wasu mutane sai dai shi malam Habu ƙa'idarsa ne zuwa da wuri, dan sai dai aje a sameshi badai ya sami wasu ba, bayan ya gama gyaran rumfarsa, ya ɗaure ko wacce dabba a tirke kana ya nemi gurin zama ya zauna.
8:am, lokacin ne mutane suka fara halartar kasuwar, kasancewar anata hidimar babbar sallah dabbobi sunyi tsada sosai, dabbobin malam Habu Masha Allah sunada kyau ga ƙiba shiyasa duk wanda yazo siya ya gaya masa gaskiya kuɗin inhar da gaske yake yi, bazai yi masa musu ba, alhmdulilah kafin ƙarfe sha ɗaya 11:am har dabbobi sun ƙare, saura guda biyu, wani abokinsa dake yawan zama a gurinsa ya ƙare musu kallo kana yace "malam Habu waɗancan dabbobin akwai shiga rai, Wlhi daga ganinsu naji sun higa raina, badan bani da kudi ba ai da siya, sai dai tausayin da nakeyi musu ba zai bari in yarda a yanka su ba" malam Habu ya jinjina kai, kafin yace "Muzammilu kana bani mamaki, wani lokacin idan kayi magana sai kace ƙaramin yaro, to ai naga dai Ubangiji ne ya halasta mana cinsu amma kana wasu maganganu"
Sallamar wani mutum wanda yai parking motarsa acan nesa dasu ne ya katse musu maganar da sukeyi, kallo ɗaya zaka yiwa mutumin ka gane nera da hutu sun samu mazauni, musamman ma idan ka kalli matarsa dake gefensa jajir da ita sai kace baturiya, tanada pink lips mai kyau, cikin shagwaɓe murya tace "Hayati Please kar mu wuce dabbobinnan gaskiya sunyi min" wanda ta kira da Hayati ya ƙare wa dabbobin kallo kana yace "My life ke har kinsan wasu dabbobi ne, ta ɗan ɗora kanta a saman kafaɗarsa tana dariya marar sauti, tunda har my life tayi magana sai shima ya sake ji sun shigar masa rai,
Bayan su Malam Habu sun amsa sallamar suka ƙarasa, matar ta fara shafa macen ragon, macen ragon ta lumshe idanu alamun tana jin daɗin hakan, ko da Matar ta matsa gefe, macen ragon sai ta fara kuka sosai, matar ta sake dawowa kana ta ci gaba da shafa ta, bayan sunyi ciniki mutumin ya siyi dabbobin aka sanyasu a mota suka kamo hanyar dawowa gida,
Yaseen da Yusra, masoyan juna kenan, nickname ɗinsu (Yasra) ko ni soyayyar su tana birgeni bare ku masu karatu da zaku so jin cikakken tarihin masoyan, Yaseen da Yusra a makarantar Jami'a suka haɗu, tun suna yiwa junansu ikirarin abokai, kwatsam sai abota ta juye soyayya mai ƙarfi wacce duk wanda yaga inda suke gudanar da tsaftsracciyar soyayyarsu sai sun birgeshi, kafin yiwuwar auransu sai da aka dinga kai ruwa rana, kafin iyayensu suka amince, Yaseen babban ɗan kasuwa ne, saboda yayi gadon mahaifinsa, mahaifin Yusra kuwa mataimakin gwamna ne, ko wanne iyayensa na damawa da nera sosai da sosai,
Anyi shagali sosai a bikinsu dan sai da aka shafe sati biyu ana shagali, a ranar bikin kuwa ɓangarorin iyayen biyu sun nuna bajintarsu, duk inda ka shiga a kafafen sada zumunta posting ɗin hidimar bikinsu kawai zaka gani.
Bayan anyi aure, burin masoyan biyu ya cika, nan fa rayuwarsu ta sauya cike da farin ciki da ƙaunar juna, a halin yanzu watansu tara da aure, suna zaune a Kaduna iyayensu ma duk acan suke.
Sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso Kd, kai tsaye gidansa ya wuce, bayan an buɗe masa get ya kutsa hancin motar ciki, motocin da akayi parking ɗin su sunkai biyar, kuma duk mallakarsa ne, sababbi fil sai sheƙi sukeyi, yana yin parking motarsa ya fito, Yusra ma ta buɗe ta fito, damuwarta bai wuce Yaseen ya buɗe dabbobin nan taga lafiyarsu ba, kamar yasan tunaninsu takeyi, yana ɗaga murfin Boot ɗin dabbobin suka fara kuka, Yaseen ya fito dasu tare da cewa "gidan gona za'a kaisu tunda dai kwanakin sallahar da saura" Yusra ta matso kusa dashi kana ta yi hugging ɗinsa cikin sanyaya murya tace "Please Hayati ka barni a tare dasu" mamaki ma ta bashi, ita da take ƙyamar dabbobi yau take maganar ya barsu?,
Hannunta ya kama yana cewa "kinga my life muje ciki, Ɗan Lami ka shigar da awakan garden kafin zuwa gobe a haɗasu da ragowar dabbobin"
Cikin bin umarninsa ma'aikacin gidan ya amsa, sukuma suka wuce ciki,
Suna shiga ta fashe da kuka mai cike da shogoɓa tana wani mannewa a jikinsa, a duniya idan akwai abinda ya tsana bai wuce kukan Yusra ba, sai kuma iyayensa, da sauri ya ɗagata sama kasancewar ita ɗin irina ce siririya, kai tsaye ya haura da ita upstairs yana yi mata waƙa, murmushi takeyi wanda ya sake ƙawata pink lips ɗinta, tana ta ƙoƙarin zillewa shigo ya riƙe ta gama.
Har ɗakinta ya kaita tare da direta a saman bed, lokacin ƙarfe 4:pm basuyi sallah ba, a hankali ya matso da fuskarsa kusa da nata, suna jiyo numfashin juna kafin ya kai hannunsa ƙasan mararta in Cold voice yace "mai yasa kike yawan ɓata ranki, shin baki san yin hakan illa bane ga babynmu?" bakinta ta matso dashi kusa da nasa, tare da yi masa hot kiss har sau uku, tana dariya, cikin shogoɓa tace "uhm ba kaine ba ai kaine"
"Am sorry my life sai inda kikace duk abinda kikeso shi za'ayi, yanzu dai tashi muje muyi alwalah, yai maganar yana miƙa mata hannu, alamar ta taso...!
Afuwan masoya masu karanta littafin NA KASA JUREWA, jiya baku ga update ba, ina mai yi muku albishir da gobe Asabar zanyi muku posting ranar Lahadi kam bazan samu yi ba sai Monday, ga wannan babu yawa kuyi manage.
Wanda suke son shiga group ɗin da nake posting suyimin magana WhatsApp only 08141799224.
Mom Islam
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_
Page 49-50
Wunin ranar dai Yaseen bai je ko ina ba a gidan ya ƙare shi.
Ko da ya dawo daga masallaci ya samu Yusra tana tsaye a parlor, ta yane jikinta da mayafi marar nauyi, ba taji shigowarsa ba, bare ta san da cewar yayi sallama, tunda ya lura da hakan ya, taho a hankali kana ya zagayo ta bayanta, ba tare da ta sani ba, ya sanya tafin hannuwansa biyu kafin ya rufe mata idanu yana murmushi, tabbas badan tayi nisa a tunani ba, da tuni ta san da shigowarsa, saboda ko bataji motsinsa ba, iya ƙamshin turarensa ya isheta sanin shi ɗinne,
WASHE GARI
Bayan Yaseen ya tashi Yusra shikuma ya wuce masallaci, koda ya dawo ya sameta tana saman sallahya tana ta rusa gyangyadi, tafin hannunsa ya kai saman fuskarta, ya shafa a hankali, ta buɗe idanu, lokacin gari yayi haske, cikin sassanyar murya tace "Hayati Barka da safiya, "my life dafatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya ya babyna"
Tai murmishi idanunta a lumshe da alamu gyangyadin yayi mata daɗi, ɗagata yayi kana ya ɗora ta saman bed ya kwantar da ita, shi kuma ya wuce parlo bayan ya ɗauki system ɗinsa,
Ƙarfe 9:am ta tashi a barci lokacin har Yaseen ya tafasa shayi already sunada bread ya soya ƙwai, sai da tayi wanka kana taci kwalliya sannan ta fito.
A hankali takai lallausan tafin hannunta kana ta ɗora su a nasa, sannan tace "Hayati" cikin sanyin murya tayi maganar, My "life" ya faɗa yana kamo hannunta, a hankali suke tafiya har suka zo inda kyawawan kujerun da suka ƙawata parlorn suke, ya zaunar da ita, kana shima ya zauna a kusa da ita, "my life" ya kira sunanta, bata amsa ba, sai ma zuba masa idanunta da tayi tana kallonsa, "mai yasa ba zaki rage tunani ba, kinsan yin hakan yana barazana ne da lafiyarki?" hankalinta ya kasa kwanciya, burinta bai wuce ta je ta gano waɗannan dabobi ba, taga a wane hali suke.
"Hayati dan Allah ka kaini gurin dabbobin nan"
Alƙawari yasa ta ɗaukar masa, na sai taci abinci, Bai kaita gurin dabbobin ba, har sai da taci abincin.
Ya sani sarai idan ta so abu tana iya fashe masa da kuka, har yanzu mamaki take bashi, any time zancen dabbobi, daga ƙarshe dai yace "tashi muje" ta miƙe tana ɗan yatsina fuska, tare da sanya hannu a mararta, cikin bai wani girma ba, sai dai sauyin yanayi da takeji, hijab ɗinta ta ɗauko zumbulele kana suka wuce garden kai tsaye,
Bayan ya gaishe su kana ya buɗe musu sannan suka ƙarasa ciki,
Lumshe idanunta tayi, lokaci guda taji wani sanyi mai ni'ima yana shigarta "Masha Allah" ta furta a hankali, wanda ita Yaseen dake kusa da ita ne zai iya jiyo hakan, sosai taji tana son taji ɗumin mijinta sabda wannan sassanyar isar dake ratsa kowanne kafar ɗaidaikun gashin da yayi luf a fatar jikinta, a hankali ta ɗan matsa kusa da Yaseen tare da saƙalo hannunta cikin nasa, ta rungume kana suka ci gaba da tafiya har suka iso garden ɗin.
"Alhmdllh, suna cikin ƙoshin lafiya"
Yusra tace tana faɗaɗa fara'arta.
Sake hannun Yaseen tayi kana ta ƙarasa gurinsu da sauri, tana shafa musu jiki, suka fara kuka a tare.
Neman guri tayi kana ta zauna, tana son cewa Yaseen ya shigar da waɗannan dabbobin corridor tana tsoron amsar da zai bata sbda tasan ma ba yiwuwa maganar Tata zatayi ba,
"Yusra tashi mu shiga ciki yamma tayi sosai, jiki babu ƙwari ta mike, tare da bin bayansa shi yana gaba, tana tana tafiya tana waigen dabbobin.
Bayan tafiyarsu, dabbobin suka koma gefe su biyu, da rago da tinkiya, ragon yace "Najma gaskiya mutanen gidannan sunada kirki, musamman ma matar Wlhi tana da mutunci, wacce ragon ya kira da Najma tace Yaya Majeed, yanzu babu inda za'ayi mu koma kamar inda muke a da?" Majeed ɗin yace "Najma Ubangiji shine wanda zai iya yi mana sakaiyya, saboda babu wanda yasan mu mutane ne, kinga kuwa babu mai taimakonmu, Najma ta fashe da kuka irin na dabbobi kafin tace "Yah Majeed mun shiga uku, Baaba Lami ta cutar da rayuwarmu, wayo Allah"
Majeed yace "inasha Allah zata ga sakaiyya fiye da abinda ta aikata mana" cikin Muryar kuka Najma tace "yah Majeed nidai na gaji da cin dusa da harawa dan Allah kazo mu gudu ko zamu sami abinci mai kyau muci" Majeed ya girgiza mata kai alamar a'a, kafin ya fara magana "Najma kiyi hakuri ki rungumi ƙaddara idan Allah ya taimakemu sai waɗannan mutanen su gane muma kamar su muke"
Da wannan kalamin yai galabar kwantar mata da hankali.
Waye Majeed?
Wacece Najma?
PLATEAU
Jos
Ɓukur park
Akwai wani danƙareren gida mai kyau da tsari, amma mamallakan gidan basa zama a Nigeria sai ƙasar Egypt, Alhaji Abdullahi shine mahaifin su Majeed da Najma, Hajiya Salima itace mahaifiyarsu, shekarar Majeed 28yrs shekarar Najma 18yrs sun taso cikin gata da nuna kulawa, kasancewar mahaifin nasu yana da tarin arziƙi mai yawa, basu cika rayuwa a Nigeria ba, a Egypt sukayi karatu dukkansu,
WATA RANA
Sun dawo hutu, dukkansu har da iyayen, suna zaune a parlor, Dad yace "Majeed, ya kamata ka fara kasuwanci bawai ka dogara da karatu kaɗai ba, bance maka bazaka ribata da ilimin ka ba, amma yana kyau ka kasance mai hanyoyi da yawa" Dad yai maganar yana kallon Majeed, Kan Majeed a sunkuye cike da girmamawa yake cewa Dad ɗin, hakan ma yayi Dad Nagode ina alfahari da kasancewarka mahaifina, Allah ya albarkaci dukiyarka Dady"
Dady yayi murmishi kana yace "Nagode da adu'oinka a gareni ɗan albarka"
Najma ta kwaɓe fuska kafin tace "Dad nifa?" Dady da Momcy sukayi dariya, Momcy tace "ai ke yarinya ce" Majeed yace "wannan rawar kanta ma yafi ƙarfin ta,
Washe gari
12:pm anty Asabe tayi sallama, cikin farin ciki Momcy ta tarbe ta, kasancewar a parlor ta samu Momcy tana shan Black tea, bayan Momcy ta tsiyayo mata, suka gaisa Anty Asabe tace "Alhajin ya fita ne?, Momcy tace "eh ya je anguwa Najma ta bishi daga nan zai sauketa a gurin wankin kai" anty Asabe ta taɓe baki tare da cewa "ya kamata ace Najma ta fitar da gwani duba da girman da tayi sosai" Momcy ta jinjina kai kana tace "anty Asabe ai Najma ƙaramar yarinya ce, dudu du ma guda nawa take?"
Anty Asabe ta gwalo idanu kafin tace "ai kuwa tunda kun ɗauki rayuwar yahudawa dole ki faɗi haka"
Momcy tayi dariya tare da cewa "ɗazu ma dadyn yake yiwa Majeed faɗa akan rashin sana'a, yace zai buɗe masa babban shago, Najma dai sai ta gama karatu, Anty Asabe ta zaro idanu, ita kam Momcy ma bata san tanayi ba, saboda idanunta suka kan wayar dake hannunta, anty Asabe ta miƙe cike da takaicin labarin su Majeed da Momcy ta bata, ta tsani taga Dad yayiwa wasu alkairi bayan ita, kasancewarta ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya, ta kasance itace gaba dashi, bata ƙaunar Momcy da yaranta, shiyasa ta ɗauki alwashin sai ta haukatasu..."
Afuwan please yau dai kunga pegin babu yawa, da naso in bari gobe sai nayi muku mai yawa, masoyan Na KASA JUREWA suka ce a turo musu haka, ayi haƙuri Please 👏
Mom Islam 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_
Page 51-52
Bayan sun gama waya da Zayden ta wani lumshe fararen idanuwanta, tare da yin murmishi mai sauti, "gaskiya duk wanda ya faɗa soyayya zai samu farin ciki, amma ake ƙoƙarin a hanata, Wlhi yin waya da Zayden ko ta halin ƙaƙa ne sai ta yi"
Duk wannan surutan a zuciyarta takeyi, lokaci guda ta rikice akan bawan Allahan nan, gabaki ɗaya ta kasa control ɗin kanta, babban burin ta a halin yanzu shine ta sake yin tozali dashi.
Tayi nisa a tunani, Umaimah ta sake kiran sunanta, a karo na biyu, da sauri ta buɗe ido tana cewa "anty ta dawo ne?" Umaimah ta taɓe baki, kafin tace "wace anty wancan dai Sarkin nacin ne ya dawo wai kizo, nifa na fara zargin sonki yakeyi"
Talatu ta zaro idanu kana ta sauko daga saman bed ɗin tana cewa "Umaimah yah Arman bazai yi soyayya dani ba, taɓɓ ki kalleshi ɗan gayu ina ni, ina shi?"
Tai maganar tana kama haɓa.
"Uhm kije dai kiji ko meye"
Sai da Talatu ta kashe wayar, kana ta mayar da ita cikin kwalinta kafin ta ɗauki siririn mayafi kana ta fice,
A parlor ta sameshi kamar ɗazu, yana zaune yana danna wayarsa, "sannu da dawowa yah Arman" ta faɗa tana yi masa murmishi,
"Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da yayi wannan Kyakkyawar halittar" ya faɗa lokacin da ya ɗora idanuwansa a kanta,
"Zauna" yah Arman yace yana yi mata nuni da saman couch, zama tayi kana ta sunkuyar da kanta ƙasa, sannan ta fara tunanin ko tayi wani laifinne, sbda ita ba shi take kallo ba, kanta a sunkuye yake, shi kuma idanunsa a kanta yake, shi kadai yake magana da zuciyarsa "anya zan iya jure ɗawainiya da soyayyar Aysha, kodai in sanar mata ne?, idan har na sanar mata zata yimin wata fassarar, gara in bari idan ta mallaki hankalin kanta, saboda a yanzu kam Aysha batasan meye SO ba".
Jin shirun yayi yawa, yasa tayi gyaran murya gami da cewa "yah Arman ko kana buƙatar wani abunne?"
"Ah..ah..a'a" Maganar ta fito masa ba tare da yaso durbur burjewa ba, tana zaunen har yayi mata hoto bata sani ba, sai da ya gama ikonsa kana yace ta wuce" ta tashi ta bar gurin, dama abinda take jira taji daga bakinsa kenan, ƙarfe 5:pm anty Tasneem ta dawo daga gidan biki, lokacin Umaimah da Talatu suna kitchen suna yin abinci, ko da ta shigo babu kowa a parlor TV ma a kashe yake, ta fara ƙwala musu kira, Umaimah ce ta fito, Talatu na markaɗa kayan miya, sannu da dawowa Umaimah tayi mata, kafin tace "Aysha ma na kitchen"
"Anty Tasneem na dariya tace "wato yau girkin ƴan mata zamu ci" Umaimah ma dariyar tayi kana ta koma kitchen.
Not. Afuwan, yanzu zan daina kiran Talatu da sunanta na ƙauye, zan dinga kiranta da sunanta na asali wato, Aysha.
Bayan anty Tasneem ta cire mayafinta, ta fito zuwa kitchen, lokacin Aysha na zuba farar shinkafa da wake a kula mai kyau, Umaimah kuma tana zuba miyar Stew a ƙaramar kula, anty Tasneem na shigowa ƙamahin miyar ya yi masa iso, cike da murmishi tace "Aysha wannan miya nasan ba iya ƙamshinta ba, dole sai tayi daɗi" suka kwashe da dariya dukkansu, Ayshar na yiwa anty Tasneem sannu da dawowa, ciro latas Umaimah tayi a fridge tare da tumatur da dafaffen ƙwai, ta zauna a kujera kana ta zuba a mazubi ta fara yankawa, anty Tasneem kam komawa ciki tayi dan ta watsa ruwa sbda anyi rana sosai, lokacin da suka kammala girkin har an fito sallahar magriba, Umaimah ta kai dinning ta jeresu, kana ta dawo tace "Aysha babu ɗan wani juice ne?,kinsan anty Tasneem sai tayi magana, tunda an saba yi"
Aysha tace "Umaimah dare da yayi, yanzu wane irin juice kike gani za'ayi a wannan time ɗin?"
Umaimah tace "ko watermelon juice da milk kawai"
Umaimah ce ta haɗa juice ɗin, kana ta jefa ice block a ciki,kana ta zuba a jug mai kyau, shima aka kaishi can dinning"
Sai da akayi sallahar isha'i dukkansu sukayi, lokacin da anty Tasneem ta fito parlor su Umaimah suna ɗakinsu, ta ƙwala musu kira suka hallara a dining kana table kana aka fara hidimar bawa ciki haƙƙinsa.
Umaimah ce ta sa musu shinkafa da miyar kifi, ko wanne da plate ɗinsa,
Bayan sun kammala cin abincin Aysha ta kwashe takai kitchen kana ta wanke sannan ta kifesu,
Parlor suka koma suka ɗan taɓa hira, anty Tasneem tace "zata wuce ɗaki sai da safe"
Suma ɗakin suka wuce, inda Umaimah ta haye gado, wayarta ce ta fara ringing ta ɗaga tare da maƙale murya suka fara hira ita da saurayinta, sosai Aysha ta nutsu tana sake karantar kalamai daga gurin Umaimah, sun daɗe suna waya, daga ƙarshe sukayi sallama har tana wani yiwa wayar kiss, Aysha ta sheƙe da dariya, Umaimah ta harareta, "Aysha Wlhi ga dukkan alamu idan kikayi zurfi a cikin soyayya zakice mu yara ne, dariya kawai tayi kana taje, kunna TV kafin ta haye bed, wayarta ta ɗauko kana ta kunna, kamar jira yake sai ga kiransa nan, babu ƙara saboda wayar a silent take, Aslmu alaikum my Omri (My lifetime) Babu wanda zai iya bayyanar da yadda zuciya ke ji idan ta kamu da so. Na mallaka miki zuciyata domin ki leƙa cikinta, ki ga irin yadda na kamu da son ki!, Wadannan kalaman da ya gaya mata, sai ta fara jin ta a wata duniyar ba wannan ba, sosai ta kamu da son Zayden saboda shi gwanine gurin iya tsara kalami, My Omri please kice wani abu, idan har kika hukuntani da rashin jin sautin muryarki bazanji daɗi ba, my Omri please" yai maganar yana sanyaya muryarsa, "I love You" tana faɗa ta katse kiran, saboda taji kunyar kanta, kalmar da tunda tasan meye a boko bata taɓa furtawa ba, a bakinta, amma ga shi yau itace take gayawa wani wanda take jin zata iya rayuwa dashi duk tsanani duk wuya, Umaimah kam mutuwar zaune tayi, sai kuma ta tuntsure da dariya, tana cigaba da kallon Aysha, in one time ta fashe da kuka, ita kanta bata san kukan me takeyi ba, sannan kuma bata da muradin Umaimah ta tambayeta wani abu dangane da kukan, gaba ɗaya ta kashe wayar tana jin ƙirjinta na bugawa Dum..dum..dum,
Daga can ɓangaren Zayden, yana kwance a haɗaɗɗiyar doguwar kujera mai zaman mutum uku, miƙewa yayi da sauri fuskarsa yalwace murmishi ya fara rawa yana juyi cikin farin ciki, ya rasa a wane yanayi yake ciki, saboda tsabar farinciki ya fice daga room ɗinsa kai tsaye ya nufi side ɗin Umma, suna zaune a parlor ita da Abba, Zayden ya shigo cikin zunuɗi, tare da sallama, ya zauna kusa da Umma yanata murmishi, Umma dai ta kasa haƙuri tace "Zayd lafiya naga sai fara'a kakeyi kamar wanda aka yiwa kyauta?"
Anzo dai dai inda yakeso, dan dama yanason ayi masa magana, da sauri yace "umma Wlhi budurwata ce tace tana sona, umma na jima ina jiran wannan ranar"
A sukwane ya silale yabar ɗakin, saboda ya mance Abba na zaune can nesa dasu,
Sosai kunya ta ƙamashi, a ƙasan zuciyarsa kuma yaji daɗin hakan, saboda Abba zai san da cewar yana neman aure.
Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta share hawaye, Umaimah tace "wow wannan soyayyar ta birgeni, kenan irin anyi zurfi a cikin soyayyar nan ne ko?"
Ta kwashe da dariya.
Aysha ta kasa ce mata komai, sai ma kwanciya da tayi barci ya ɗauke ta, itama Umaimah ganin babu abokiyar hira yasa tayi barci.
KEFFI
Ido biyu sukayi da Hajiya Zaliha, Saudart tayi mata kallon up and down kafin tace "waye ke?"
Sosai tambayar ta ƙonawa Hajiya Zaliha rai, cikin fusata tace "ni uwarki ce, munafuka kawai wawuya wacce bata san muhimmancin rayuwarta ba" Saudart ta zaro idanu gami da cewa "kinga mama ina jin nauyinki, ki fitar min daga gida kar in yi miki abinda har ki mutu bazaki mance dashi ba" Hajiya Zaliha ta bugi ƙirjin Saudart kana tace "dan ubanki kiyi min abinda ubanki be yiwa uwarki ba ma kinji", sosai munannan kalaman Hajiya Zaliha da ta dinga yiwa Saudart suka tsorata ta, tabbas bata iya faɗa ba, ko musayar yawu da mutane, hakan yasa mayar da maganar ya zamo mata baƙon abu, hayaniyar ce ta tashi alhaji daga barci, dama yasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, ya fito da sauri tare da wucewa ta gefen Saudart, rai a ɓace yace "Zaliha mai ya kawo ki, mai kikazo yi, Ban sallameki ba?" In one time ya jero mata waɗannan tambayoyin,
Sosai tambayoyin da yayi mata suka ƙona mata zuciya, ji tayi kamar ya watso mata ruwan zafi, musamman da yake shirin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 22