Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iyayena suka haɗoni dashi sun ƙare, me kake dashi da zan ɗin ga ɗiba? ta gyara ɗaurin zaninta taci gaba da cewa "ko yanzu na fita a gidanka zan samu saurayi sabo fil gada gau me jini a jika" Tun da ya ji ta faɗi haka, ya wuce ƙofar ɗakinsa kana ya ɗauki buta ya kuskure bakinsa, har ya nufi hanyar zaure ya juyo yace "Tabaiyye kiji ta tsoron Allah karki ragemin masara" "Da tsoronka nakeji mtsw" Tai maganar tana yatsina masa fuska. Hankali kwance Talatu ke tafiya har ta iso gida, tunowa da babbar baƙuwar da Inna ta gaya mata zasuyi ne yasa ta washe haƙora, a fili tace "na rantse da Allah ina son ganin ƴan binne" da gudu ta shige tana cewa "Inna dan Allah ki biyoni ban ɗaki da buta tsuuuuu (Gudawa) nakeyi" Sam bata ma ga Anty Jamila dake zaune saman tabarma ba, cikin ɗaga murya Inna tace "Talatu zanci mutuncin ki", tana ƙare maganar ta miƙe takai mata buta, "Yauwa Innata idan nai aure zanyi kewarki" Ko ƙala Inna batace mata ba ta dawo gurin Anty Jamila. Murmishi Anty Jamila tayi kafin tace "wallahi A'isha tana birgini" Inna tace "taɓɓ bakisan waye A'isha bane" "Haba Inna ai Kowane yaro da ƙuruciyarsa" "Hakane kam" Inna ta faɗa tana dariya. Bayan ta fito daga banɗaki ta ware idanunta, fess ta ɗora su kan Anty Jamila, washe jajayen haƙoranta tayi kafin ta taho da sauri tace "ahe kin ƙaraso Inna Jumai?" "Na ƙaraso A'isha, amma sau nawa zan ce miki bana son ki dinga ce min jummai?" "To kiyi hakuri yasin mancewa nakeyi, amma dai kinzo kiyi mana wata da watanni ne ko?" Anty Jamila tai dariya kana tace "a'a yanzu ma daga Madobi nake gobe insha Allah zan koma Abuja" Zaro idanu Talatu tayi sai kuma ta matso kusa da Anty Jamila tace "dan Allah ina Hajiyar nan da take zuwa tana raba mana hinkafa?" Anty Jamila tace "Hajiya tana gida, sbda rashin lafiyarta ne ma zan koma gobe" "Ahe bata da lafiya?" Talatu ta faɗa tana ƙara tattaro nutsuwarta, kai kace dagaske, Ita ko Anty Jamila duk tambayar Talatu tayi mata sai ta bata amsa. Koda Inna tazo ta samesu sunata hira, abin yai mata daɗi, Tace "Jamila kuna zantawa ne da ƴar taki?" Anty Jamila tai murmishi. Jollof ɗin dawa da wake Inna ta kawo wa Anty Jamila, ayko taci sosai ba laifi dan kaɗan ta rage tasha ruwa, Wayar Anty Jamila ta fara ringing, Ganin sunan Ma'aruf yana yawo a kan screen ɗin wayar yasa tai saurin ɗagawa, tare da cewa "my Son ya akayi?" "Anty Jamila Hajiya fa bata magana kwata-kwata" Cikin firgici Anty Jamila ta fara mai-maita "innalillahi wa inna ilahir raji'un" Kana tace "son kayi haƙuri yanzu dare ya fara tunda ana shirin kiran sallahar magriba, insha Allah gobe ƙarfe huɗu zan taho, Allah ya bata lafiya" Sosai hankalin Anty Jamila ya tashi, sanda a iya saninta Hajiya ba ta taɓa irin wannan ciwon ba. Nan ta labartawa Inna abin da ke faruwa, Inna tace "itama zata bi Anty Jamila su tafi tare" Talatu tace "taɓɓ wallahi he anje dani kawai ki tafi har binni ki barni hu'um" "Ba fa wani abin daɗi ne ze kaini can ba, rashin lafiya ne, kuma befi in ɗauki kaya kala ɗaya ba" Da ƙyar da lallashi dan sai da Anty Jamila tayi mata alkawarin zata turo me mota ya kawo ta Abuja sannan ta amince, A daren Inna ta haɗa mata kayanta a bako sbda kafin su wuce zata kai ta gidan mahaifiyar babanta. Bayan sallahar isha'i, suka wuce gidan Kaka, da sallama Inna ta shiga kafin tace "zauna mana ai dai kya gaihe ta" "Ina wuni" Talatu ta faɗa tana turo baki, "lafiya lau ƙawata na ganki da jakar kaya?" Inna tace "wallahi na kawo ta ne zamu wuce Habuja gobe saboda Hajiya Habiba babu lafiya" "Ash sha, Allah ya bata lafiya, zaki daɗe ne?" "A'a kwana ɗaya zanyi" Inna taba kaka amsa, kaka tace "to ki ja mata kunne banda rahin kunya, dan ba kowa bane ze ɗauka" Sosai Inna tayiwa Talatu faɗa kana tayi musu sallama, bayan ta miƙa wa Talatu ɗari biyu taba wa kaka ɗari uku, Kaka ta washe haƙora tana cewa "Allah ya tsare, "maiyyar kuɗi" Talatu ta faɗa tana hararar kaka" "Nayi ɗin naga uwarki ce ta bani ko?" Koda taji barci kaka ta hanata hawa gado wai kar tayi mata fitsarin kwance, sai da Talatu ta bari kaka tayi barci kana ta lallaɓa ta kwanta can gefenta, Kaka dai tasan ta hana Talatu hawa gado, gashi fitila ta mutu, tunda su basa ganin wutar lantarki, cikin ihu da kururuwa take cewa "ke Talatu tahi ki gani kwarto" Tunda Talatu taji kaka ta faɗi haka, ayko ta kunce zanin kaka ta cukuai kuyeshi, ta janyo hannun kaka kiiiii ta janyo ta ƙasa, ta haye gadon daga can inda take ta sauya murya tace "ke ƴar tsohuwa jiya naji kina adu'ar Allah ya baki miji hine nazo mu shirya" Haba kaka ta sake rikicewa, bakinta na rawa tace "nifa tsohuwa ce haba kai kuwa baka ga jikina duk a tamushe ba, na roƙeka nidai ban ce haka ba" "Zo nan" Talatu ta faɗa cikin daka tsawa, ganin kaka ta rikice sosai yasa ta koma kan gadon ta kwanta tunda tasan bazata taba komawa ta kwanta acan ba. Ƙarfe huɗu na asbha Anty Jamila ta farka, dan ba wani barci me nauyi tayi ba, ko wanka batai ba, ta shirya cikin leshi Black anyi masa ado da zare golden color me adon duwatsu farare, mai kawai ta mutsika, tayi tunanin Inna tana barci sai taga itama har ta gama shiri, kasancewar basu da wani kaya me nauyi suka fita neman me mashin, sbda masu mashina ba kasafai suke yawo ba, kasancewar ƙauye ne sosai, idan kaga mashin sai na masu zuwa gona, can maƙotansu Inna taje ta roki alfarma, tai sa'a yaron gidan na nan, ya fito da mashin ɗinsa suka hau zuwa tasha, Sai da suka kai ƙarfe shida kafin motar ta cika, sannan suka fara tafiya...! Ayi haƙuri jiya baku ga posting ba, wallahi kuna raina kunsan weekend mutum ba shi da wani hutu sosai. Share fisabilillah 👏 Mom Islam ce 08141799224 [7/16, 8:21 PM] Mom Islam: *NA KASA JUREWA* 💋💋💋 💋💋 💋 _Mom Islam🍹_ Kiyi following ɗina Arewabook zaki samu more pages ga link nan 👇 https://arewabooks.com/u/momislam11 Page 71-72 Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Yaseen, duk cika bakin da ya dinga yi akan bazai barta taje wankan gida ba, yasha ruwa, saboda daga Hospital gidan Momcy aka wuce da ita, dole ya ƙulla ƙawance da zirga-zirgar zuwa gidan Momcy kullum, kaka ce take yi mata wankan jego, Sati biyu Yusra ta samu a gidan Momcy, tayi kyau tayi ƙiba sosai, ita da yarinyarta da suke kira da Mirah, sosai mimrah take kama da Yusra har ɗan ƙaramin bakin, Yauma kamar kullum, koda ya je can gidansu sai ya ga gidan yayi masa girma sosai, acan gidan Momcy yake cin abincin dare kullum, Ƙarfe 7:pm ya kama hanyar zuwa gidan Momcy, ga wani uban hadari dake haɗawa, hakan bai sa ya fasa ci gaba da driving ba, horn yayi a bakin get ɗin mai gadi ya buɗe masa, ya shigar da motarsa, a lokacin har an fara yayyafi, da sauri ya shige gidan tare da kutsa kai cikin parlorn, babu kowa a parlor dukansu suna ɗarin Momcy hakan yasa shikam kai tsaye ya wuce ɗakin Yursa, wayarsa ya ciro tare da danna numberta ya kirata, kasancewar wayar a vibrat take, ta ɗago kai a hankali kafin ta kalli kaka, sai kuma ta kalli Momcy da ita take kallo, cikin ɗan duburburcewa tace "am..dama...um.." Momcy tace "Yaseen ne yazo ko?" Ta ɗanyi murmishin yaƙe tare da cewa "uhm Momcy ya akayi kika gane?" "Kinga tashi kije, wlhi idan har kika biye masa yayi miki daɗin baki ke kika sani, dan ɓatan watanki ya ɗauke ba shi ke nufin ki koma ga mijinki ba, ah to, wallhi ina nan babu ruwana," Kaka ta faɗa tana bin ta da kallo, sake ɗago idanu tayi ta kalli Momcy, Momcy tace "tashi kije amma fa ki kula" Har ta fito bakin ƙofa, Momcy ta ƙwala mata kira ta dawo, "zo ki ɗauki ƴarki" Momcy ta miƙa mata mimrah, Bayan ta karɓeta ta fice a ɗakin kai tsaye ta wuce ɗakin ta, A saman sallahya ta samesa yana ta kwararo adu'oi, bayan ya shafa, ya miƙe yana ninke sallahyar yana yiwa mimrah murmishi, kafin ya matsa inda Yusra take tsaye, ya buɗe hannayensa, ta matso ya rungumesu, tare da cusa kansa cikin jikin Yusra, a wani irin yanayi ya tsinci kansa, wanda yasan idan har bai samu abinda yake so ba, komai yana iya faruwa, sauke wani irin numfashi yayi, tare da zame jiki sa a na Yusra, in Cold voice yace "my life wlhi NA KASA JUREWA, yanzu shikenan an shiga tsakanina dake har sai nan da sati biyu?" Yai maganar murya a sanyaye, Ɗan murmishi tayi, kafin tace "sati Uku dai" ya runtse idanunsa, tabbas tasan abinda yake damunsa, saboda har Hospital sunje watannin baya da suka wuce, hakan yasa take ƙoƙari gurin ganin ta kiyaye dokokin da aka gindaya musu, domin ya zauna cikin ƙoshin lafiya, Cike da kallon tausayi ta bishi, tare da ajiye mimrah da tayi barci tun bayan da ya rungumesu a saman bed, kafin ta matso kusa dashi tace "Qalbi" Lumshe idanunsa yayi yayinda ta ƙaraso garesa, sannan ya ji faɗar sunan da tayi ya sake saukar masa da kasala, saboda cikin sanyin muryarta da take hargitsa tunaninsa tayi maganar, janyota yayi jikinsa, kana ya rungumeta ya sake sauke numfashi, kafin ya zame ɗankwalin dake kanta, "Qalbi bamu da time wlhi su Momcy zasu gane" muryarsa tayi wani irin lokacin da yake ce mata, "yanzu ni da matata ta sunnah sai anyi min iyaka, gaskiya zanzo in ɗaukeki mu gudu" Tai saurin toshe masa baki, tare da taimaka masa ya samu nutsuwa sosai.. A hankali ya ke sauke numfashi mai cike da nishaɗi, hatta mood na fuskarsa ya sauya, kana ganinsa kasan ya samu nutsuwa sosai, Ya rungumeta yana saka mata albarka, da sauri ta miƙe taje tayi wanka, kana ta tsane jikinta sannan ta dawo gurinsa tace "Qalbi.." ya amsa mata da idanu kamar na mai jin barci, yace "wannan sunan yana yimin daɗi" Ta yi masa murmishi tare da cewa "yanzu dai duk ba wannan ba, ka tashi ka sa kaya ka wuce wlhi zaka janyo min faɗa a gurin Momcy" Dole hakan yayi, bayan ya kintsa, ya sa hula ya miƙe tsaye, ta wangale baki tace "wlhi kayanka sun yamutse ya zamuyi?" Ya ɗage ƙafaɗa kana yace "karki damu, da ace ban samu honey milk ba, da ni kaina sai na zarce kayan gurin yamutsewa amma yanzu normal babu abinda ya dameni" Tsayawa kallonsa kawai tayi, a fili tace "wato ma babu abinda ya dameka ko? baka san idan an aihu ba'a zuwa gurin miji sai anyi arba'in ba?, shikenan Qalbi ka sake yimin wani cikin" ta faɗa tana rushewa da kuka, "calm down haba wane ciki kuma, saboda shigar cikin babu wahala? Kinga ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru, ni bari in wuce, me kuke buƙata sai inyi miki transfer?" "Zamuyi waya" ta bashi amsa tana share hawayen dake Zarya a kumatunta.. KD Sosai take gudu har ta fita daga anguwarsu, kafin hankalinta ya kwanta, wayarta dake hannunta, ta kunna da tuni ta kasheta, hankalinta ya gushe tunaninta ya ƙare, ta rasa wa zata kirawo, kai tsaye ta saka number Sabeer, saboda ɗazu ta gogeta kuma ta haddace number a kanta, yana kwance inda ta barshi, yana kwasar barcinsa, gefensa wani glass cup ne mai ɗauke da wine a ciki, da alamu yasha ya bugu saboda wannan barcin nasa kamar ba na lafiya ba, ringing ɗin wayarsa ce ta tashesa, idanu a lumshe da ƙyar yake buɗesu ya ɗaga kiran tare da cewa yaaaa..akaaaayiiii...neeee.., murya dai sak ta mashayi, tana kuka game da toshe bakinta tace "Sabeer kaga abinda ka janyo min ko? Ga shi nan momy ta ce, sai ta kasheni " Da sauri ya tashi zaune tare da ware idanunsa kana yace "akan me zata kasheki, tasan hukuncin wanda yayi kisa kuwa?" Cikin daka tsawa tace "ni dallah rufemin baki, ba duk kai ka jawo ba, na biyewa daɗin baki da kuɗinka, ga shi yanzu ina ɗauke da juna biyu "kai haba, ya faɗa yana washe haƙora" dogon tsaki tayi "mtswww" sannan tace "au na ga kamar murna kakeyi?" Ransa fess yace "nikam karki zubar min da ciki, ai ba shege bane da ubansa gani, ko a ina zan amsa ni ne ubansa" Ta zaro ido saboda lamarin Sabeer ya fara bata tsoro ya daina bata mamaki, "Kawai kizo mu haɗe zan baki gidana dake Tudun Wada karki wani damu, idan ta kasheki ai ni tayiwa asara" jin haka yasa ta ce "yanzu kana inane?" "Ina hotel ɗin da kika barni, dama wlhi ina hungry ɗin..." Ta katse kiran. Mashin ta tare ko mayafi babu a kanta, kana ganinta tayi wuji wuji saboda ta fita a kamininta na ɗazu, wasu ma sun ɗauka Cristian ce, wanda suka santa kuma suyita yi mata adu'ar shiriya, tunda dama an daɗe ana bada labarinta, mahaifiyarta ce kawai bata sani ba. Dan Allah iyaye mata mu kula, dan tayi wannan abin bai kamata, ace mahaifiyarta ta ɗauki alwashin kasheta ba, yanzu dai ga shi mai gari ya waya?, zata koma inda ake gudunta dashi, ya kamata da wani ƙwaƙwaran mataki ta ɗauka a kanta, duk da nasan tayi furucin cikin fushi ne, Allah Ubangiji ka tsare mana imaninmu ka kyautata farkonmu da ƙarshenmu ka bamu ikon riƙe amanar ƴa ƴanmu da ka bamu Amin. Bayan sun iso ta kira Sabeer, ya fito ya bawa mai mashin kuɗinsa ya wuce, Wani irin kallo yake mata wanda ya tabbatar mata da abinda ke cikin ransa, hannunta ya riƙe suka wuce room ɗin da yake, a ranar dai wuni yayi yana aikin Abu ɗaya, tabbas Ruqaiyya ta gane Allah ɗaya yake, a ranar yayi mata kyautar mota, mai kyau, sai dai bata kai tsadar tasa ba, sosai suka kasance manne da juna, kai kace yau ne rana na farko da suka taɓa haɗuwa, kokuma muce kamar wani sabon ango, siyan abinci ne kawai yake fitar dashi daga room ɗin, haka suka kasance babu sallahar azhar babu na la'asar bare na magriba da isha'i, koda dare yayi, haka ta shiga toilet ta dinga kwarara amai, cike da tausayinta ya taimaka mata har ta gama, sannan yace "akwai abinda take buƙata ne?" "Babu tace masa lokacin da take mayar da numfashi" Magunguna ya haɗo mata, tare da su peakmilk da moltina ya bata tasha ya ajiye mata na anjima dana gobe, fitar da yayi har boutique ya wuce, ya siyo mata kayayyaki masu tsada harda hijabai da takalmi, sosai soyayyarsa ta sake samun sabon mazauni a cikin zuciyarta, a ranar dai kwana sukayi farantawa junansu, can dare sosai barci ya ɗaukesu, koda aka kira sallahar asbha babu wanda yayiwa ɗan uwansa magana, basuyi ba, sai ma shiga wanka tare da sukayi suka dinga iskancinsu daga ƙarshe dai suka fito tsirara manne da juna, suka shafa mai suka saka kaya, da yake yau ne zai koma gidansa da yake zaune, suka shirya kayan su, kana suka bada key sannan suka wuce gidansa, tangamemen gidane, idan ka gansa sai ka rantse babu talauci a duniya, bayan mai gadi ya buɗe masa ya shiga, suka fito, tana sanye da dogon hijabi, bayan sun shiga cikin gidan, ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo, saboda tunda take bata taɓa ganin gida irin wannan ba, saboda su ɗin bawai sunada hali irin sosai bane, dan kwananan ma momynta take cewa zata sallami mai gadin, tunda mahaifinta ya rasu komai sai yayi ƙasa, hakan yasa momyn ta nemi aikin gwamnati domin ta ci gaba da taimakon kansu.. Ko me ta gani sai ta ƙura masa ido kai kace makauniya, haka ta dinga kalle-kalle har ya kaita ɗakin da zata zauna, wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da rungumeshi tana murmishi tace "masa godiya nake" Ya zauna saman bed tare da janyota ta faɗo jikinsa, sannan yace "Ruky anan zamu ci gaba da rayuwa babu mai takura mana, sannan inson kisa a ranki ni mijinki ne, ban taɓa son wata ƴa mace ba, bayan ke, wlhi tallahi duk wayar da kikaga inayi a gabanki kawai dan in gane kinaso na ko a'a ne, karkiji shayin yimin biyayya, ko kuma tambayata wani abun da kike da buƙata.. ta amsa da "to" tana sake ƙamƙameshi. Waye Sabeer? Sabeer ɗane ga Alhaji halliru, Alhji Halliru wani attajiri ne mai kuɗi sosai, matarsa ɗaya Hajiya Zainab, ba itace mahaifiyar Sabeer ba, saboda a gidan tazo ta sameshi kuma da wayonsa, sannan tun Sabeer yana ƙarami babu wanda ya isa ya ɗaga masa yatsa, hakan yasa, ko ke shayinsa, sannan mahaifinsa ba basa zabi akan ko ina yakeson rayuwa yayi, sai dai kar ya sake yayi kwana biyu basuyi waya ba, sannan idan har bashi da kuɗi, ko nawa yakeso zai bashi" Wannan matar tasa a iya matsayinta kawai take zaune, tabbas idan har zata kawo wata magana akan Sabeer, to tabbas ranta in yayi dubu sai ya ɓaci, hakan yasa tayi haƙuri ta zauna, taƙi gani taƙi ji. Bayan tafiyar Ruqaiyya Hajiya Lubabatu ta fara numfarfashi sama-sama, wata maƙociyarta da ta shigo suyi magana akan ankon bikin ƴar matar, tazo ta sameta rai a hannun Allah, kai tsaye taje ta samu mai gidanta, ya fito da mota suka wuce Hospital....! Mom Islam *NA KASA JUREWA* 💋💋💋 💋💋 💋 _Mom Islam🍹_ Kuyi following ɗina Arewabook zaku samu more pages acan https://arewabooks.com/u/momislam11 Page 73-74 sai da suka wuni a hospital ɗin ita da matar, saboda har test akayi mata, sannan aka saka mata drip, doctor ya tabbatar musu da damuwa ta saka a ranta shine ya haifar mata da wannan ciwon, ga shi ta kamu da hawan jini, zuwa yamma aka sallameta, mijin maƙociyarta ne ya biya komai, daga nan suka dawo gida, babu abinda take yi sai kuka, hakan yasa mutane suke ta cewa ƙila ta tuna da mutuwar baban Ruqaiyya ne, shiyasa take ta kuka, Ita kaɗai tasan abinda ke damuta a cikin zuciya. KD Ƙauye Bayan sun dawo gida, malam yace "Najma ta miƙa niƙan masara ingi" suka wuce gona shi da Majeed da Haladu, malam na tafiya, cikin daka tsawa Inna tace "zoki miƙa kiƙannan dan ubanki akwai bayinki ne anan?" Najma ta miƙe jiki a sanyaye ta wuce miƙa nika, Acan a gona, zaune suke a gindin bishiyar ɗorawa Haladu da Majeed, Haladu yace "Majeed dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka?" Majeed yayi shiru yana nazarin shi kuwa wace alfarma Haladu zai nema a gurinsa me yake dashi?" Majeed yace "Haladu insha Allah zan yi ƙoƙari gurin ganin na amsa maka tambayar da zakayimin?" "Ina son Najma.." Haladu yai maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, Majeed ya girgiza kai tare da cewa "Najma bata da iyaye taya zakuyi soyayya har takai ga kunyi aure?" Haladu yace "Majeed ka fahimceni, amma inason ka sani iyayena ai sun zamo iyayenku, wai dai tsaya akwai wata tambaya da nakeson yi maka, sannan inason ka bani labarin asalinka, malam dake tsaye a kansu yace "Haladu abi komai a hankali, kasani fa har yanzu ban gama yi masa magani ba, saura kwana biyu mu kammala kuma insha Allah muna saka rai da alamun nasara daga shi har ƴar uwar tashi" Majeed ya sunkuyar da kansa yana sake godewa Malam, daga nan suka ci gaba da aiki, Mai motan da suka haɗu dashi ɗazu ne ya aika yaro gidansu Karima, a kirawo masa Najma, a kwatancen da yayiwa yaron yace farar yarinya, yaro ya shigo gidan tare da cewa "wai wannan baƙuwar tazo" Inna ta yatsina baki kafin tace "kace gata nan zuwa" lokacin har ta dawo daga kai niƙan tana gida a kwance sbda barci ma take yi, Inna tasa Karima ta shirya cikin kayan sallah tare da yin kwalliya ta fito kamar wata dodanniya, ta cika janbaki ja yayi mata yawa sosai, ta fito tana rangwaɗa tare da isa gurin mai motar, yana ganinta ya tuntsure da dariya kafin yace "kwalliya tayi kyau, amma ni ba ke nake nema ba, wannan yarinyar da na ganki da ita ɗazu ita nake nema" ta turo baki tare da cewa "to ai ta koma garinsu, kuma ni kaɗai ce a gidan" ya figi mota ya wuce ba tare da ya sake yi mata magana ba. Da gudu ta shigo gidan nasu tana kuka mai sauti wanda har yasa Najma ta farka, kana ta fara sauraren dalilin kukan Karima, "uhm....um...hum... Inna wai dan nace masa tayi tafiya shine kawai ya wuce ya barni, wlhi Inna ya wulaƙantani" tai maganar tana share hawayen dake zubowa daga indanunta kamar an buɗe famfo, Sai yanzu najma ta gane abinda sukayi, murmishi tayi ko me yasa oho. Haka dai Najma taci gaba da rayuwa cikin tsngwamar Inna da kyarar da Karima take yi mata, tunda yanzu Karima ko cokali bata ɗagawa komai Najma ce take yi. Bayan kwana biyu, malam ya kawo shinkafa mudu biyar wane mudu ɗaya, yasa aka daka yaji sannan yace a dafa masa shinkafar, bayan ta dahu, malam yasa aka zuzzuba a tray kamar guda biyar, ko wanne aka saka mai da yaji, yasa aka fitarwa da almajirai abincin. Bayan abincin sadakar ya ƙare, malam yace a yau ne ya kammala aikin da yake yiwa Majeed da Najma, dan haka ya bawa Majeed wani ruwan magani yayi wanka dashi har kansa, hakama Najma yace har tsarki tayi dashi, dukkansu sunyi yadda malamin yace, bayan sun sanya kaya ya kirasu dukansu zuwa ɗakinsa, suka zo suka zauna saman buhu, yayi bismillah tare da watsa musu wani ruwan magani kana ya fara karanto musu ayoyin Alkur'ani mai girma. Ina one time suka wani sauya yanayi Najma ta sake fari sosai, wato farinta na da lokacin tana gidan mahaifinta ya dawo, shi kuma Majeed shima ya sake haske da fresh fatarsa ta da ta dawo, Malam yayi hamdala tare da sake ɗaga hannu ya godewa Allah, kafin ya sake yin bismillah Sannan yace "ku suwaye?" "Majeed ya fara kallon ɗakin yana waige waige, Najma kam kuka ta fara tana cewa "momyna wlhi karki sake yarda da mugaye" malam ya sake watsa mata adu'a kafin ta natsu, cikin nutsuwa Majeed yace ni ɗan PLATEAU ne, Jos mahaifina sunansa Alhji Abdullahi" malam yace "ko zaka iya bani lambar wayarsa?" Majeed yace "eh malam" Malam ya miƙawa Majeed waya yasa number mahaifinsa, sai dai a kashe, saboda tunda anty Asabe taji wannan maƙudan kuɗaɗen da ake bin bashi ta kashe wayar, Ya saka number mahaifiyarsa Hajiya Salima, cikin sa'a ta ɗaga tare da cewa "waye?" Duk da Majeed ɗin yaso ya yi magana amma sai ya miƙawa malam saboda girmamawa. Bayan Malam ya karɓi wayar cikin nutsuwa da Dattaku yace "sunana Malam Isyaka, ina zaune a garin Kaduna acan ƙauyen ƴan kifi, dalilina na kiranki wani yaro ne ana ce masa Majeed... Hajiya Salima na jin an ambaci sunan Majeed ta zaro idanu tare da sake riƙe wayar da kyau, kana tace "malam ina jinka" yace "siyarsu nayi a gurin wani mutumi a matsayin dabbobi, da yake dai Allah ya bani ilimi dai-dai gwargwado yasa na dinga yi musu magani, har muka yi nasarar karya sihirin duka, yanzu dai inason in kawosu gareku ya za'ayi?" Hajiya Salima tace "malam idan har kuɗi kakeji babu damuwa, ki taho dukkanku da mutanen gidan malam" Malam yace "a'a, zan fara kawosu ni da yarona, daga baya mai ɗakina zata zo, ai kuma zumunci ya ƙullu" Sukayi sallama da Hajiya Salima da niyyar gobe insha Allah zasu taho Jos, Ko da mama taji labarin an ga su Najma har rawa sai da tayi, tare da yiwa Allah godiya, tun a ranar suka fara shirye-shiryen abubuwan da zasu tarbi Malam dashi... MASARAUTAR MANDU A wani ɗaki mai kyau tangameme akayi mata masauki, ɗaki ne wanda yake ɗauke da gado irin na zamani mai kyau, sannan gefe da gefen gadon akwai wani bedsite masu kyau, a gaban gadon kafin ka hau sai ka taka wani lallausan carpet mai taushi sosai, daga hannun hagu wata doguwar drowa ce mai kyau irin kwaliyar gadon ne a jikinta, sai dressing mirror dake can gefe da stool shima mai kyau, Jakadiya tace "nan ne ɗakinki kafin ki koma ga iyayenki " Gudidi ta harareta tare da cewa "yasin baki isa ki koreni ba, zama a gidan nan daram ko mutum yana so ko baya so" ficewa jakadiya tayi

Chapter 20 of 22