Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sun riga da sun san da fitar. katafaren unguwar Banana Island suka nufa wadda take nan da manya manyan ƙerarrun gine gine na zamani duk inda ka kalla zaka so kara kallar wurin, tamkar ba'a nigeriyarmu ba, ko ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa kammm anguwar ta gama haɗuwa. Tun da motocin suka hau saman titin babu abinda kakeji sai suuuuuu suuuuuu suuuuuu shine kaɗai sautin dake tashi, har suka nufi wani ƙayatacce fitaccen gini na alfarma, da remote suka yi amfani wurin buɗe ƙaton jibgegen get ɗin. Kai tsaye suka danna hancin motocin nasu zuwa cikin gidan a jere, nan suka ci gaba da tafiya a jere a saman kwaltar, a ƙalla dai Saida suka wuce wajen get huɗu kamin su isa gaban wani ƙaton parking space ɗin da ya gaji da haɗuwa, wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motoci , kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah saboda tsabar tsananin kyau da tsadar motar, kallo ɗaya zaka ma dogon ginin da yafi kama da masarrafin kera motoci. A jere waje guda motocin nasu suka yi parking, ɗaya daga cikin manyan samudawan sane ya fito tare da buɗe masa ƙofar motar, cikin zallar izza ya fito yana ƙara gyara zaman p-carp ɗin dake saman kansa, wanda lallausar sumar kansa ta fito ta ƙasar ƙeyarsa. Ya Ilahi wannan gida kacokam ɗinsa saidai mu ƙirashi da aljannar duniya, ga wasu haɗaɗɗun beneye wajen hawa ashirin da wani abu. Su dukka daga nan suka dakata shi kuma ya soma tafiya cikin tsananin zallar iya sarrafa tafiya, wata rantsatstsiyar ƙofa ya dosa tare da seta ƙofar da ƙwayar tsaƙiyar idanunsa, wanda suke nan exctly irin na mage a take kofar ta buɗe sai gashi cikin wani irin azababben narkakkun parlour, wanda ya linka na gidansa dake Victoria island sau goma a haɗuwa da tsaruwa. Baki ɗaya parlourn ɗauke yake da wasu uban lumtsuma lumtsuman kujeru wajen set huɗu, ga ta ko ina na parlourn kewaye da na'u'rorin sarrafa abubuwa, gaban wata kerarriyar ƙofar glass ya nufa, bayan ya shiga cikin lifter ɗin ya danna Black B Parlour 3 zuuuuuuu lifter ɗin tayi ƙasa dashi idanunsa Lumshe a haka har ta kawo shi parlourn, still wasu kofofin da suka kusa kwance min kai na kuma cin karo dasu, nan ya ringa ratsa parlouna yana wucewa har ya isa gaban wani ɗaki da yafi kama dana masu bada horo. Nan ma Saida yayi amfani da ƙwayar idonsa kafin kofar ta buɗe ya sanya ƙansa cikin ɗakin, tare da ɗan yin baya da blue jacket ɗin dake saman shigar sa, mutane biyun dake a galabaice ne suka yi saurin dago kansu domin tun da aka kawo su wurin ko sau ɗaya babu wani mahalukin da suka kuma gani. Gashi yau wajen kwanaki shidda ake magana, komai na amfan da aka tana jar musu ga ɗan madaidaicin stoor nan a cikin dakin wanda abubuwan da suka shafi rayuwa aka tanajar a cikin sa irin su kayan girki ne, maƙulashe ne kayan tea ne, chocolate cake recipe with milk duka dai abubuwa ne da akayi tanajinsu dama, farar kujera yaja irin da ƴan ɗaurin auren nan yana zama akai tare da fuskantar su. A take suka sha jinin jikinsu sai suka ji duk wani hope na ƙwarin gwiwar dake garesu ya gudu nashi wuri, Cikin haɗiye miyan wahalta governor Aminu Bello ya dubi AK tare da faɗin. "Mine hurumin ka na sacemu?, Wani irin ɗan jujjuya kyawawan ƙwayar idonsa yayi tare da furta. "Kar kayi magana a loƙacin da babu abin faɗa, koda da abin fadanma kasani shuru bai taba zama illaba, rayuwar duniya kamar series film take, episode episode take zuwa amma duk yawan film ɗin dole ne ya ƙare wata rana" Ministan gida ne ya ɗan zunguri Aminu Bello, tare da fara kifkifta masa ido ga jikinsa dake tsuma Shi kuwa cikin aro wata jarumtar ya kuma furta. "Yaro A wasu loƙutan kana ganin kayi nasara shine faɗuwa, haka ma wasu loƙutan ka yadda ka faɗi shine nasara" "Ka sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai ku ɗin nan" "Ita fa Duniya kamar jirgin ruwa take, Zata iya kaika inda kake so, kuma zata iya kaika inda take so. don haka be careful respect your mouse ba lallai a wannan karon ta kaika inda kake so ɗin ba" "Bani da loƙacin ɓatawa loƙaci loƙacinsa,don ba zamane ya kawo niba, a cikin mutanen ku duk mutumin da ya kuskure ya kuma yarda ya haɗa hanyar sa da nawa, saidai uwarsa ta haifi wani badai shiba rayuwata rayuwa tace, haka za rayuwarku rayuwar kuce, kowa ya rufe idanuwansa akan mahaukacin zakin daya fito domin yin farauta, ya kuma toshe kunnuwansa daga hargaginsa" Sosae suka sake rikicewa ba kuma su sake rikicewar ba Saida ya danna wani ɗan abu mai kama da elevator kyawawan kwalaben wine suka bayyana tare da dasu cocaine cigarettes. Wannan cocaine ɗin ya ɗauka tare da walwale ledar yana matso da ita dab da hancinsa, wani irin kyawawan shaƙa ya mata tare da Ciro kwalin cigarette yana zarar guɗa daya lighter ya ɗauka a cikin abun kana ya karsta ya mata zuƙa ɗaya tare da faso musu hayaƙi Sigarin, zuƙa biyu ya mata ya gama da ita kai da ganin yadda yake zuƙar cigarettes kasan ehhhhhhhhh lalle wannan ubanta ne. A take yanayin idanunsa suka jirkice zuwa wasu colourn daban, wannan blue In tuni ya kau yana dawo wa jaaaa sosae ga kuma ƙwayar idon ta tayi wani irin fari tasssss tamkar wanda aka ɗura madara a cikin su. Haka ya tashi yana tafiya irin ta wanda ya bugu har yaje bakin kofar sai kuma ya waiwayosu cikin muryarn maye ya furta. "Duk lalacewan kura a dawa to tabbas tafi ƙarfin kare, haka duk lalacewan mafaraucin zaki yafi karfin alade" Zuuuuuuu kofar ta koma bayan ya gama fita , directly ya hau lifter ta komar dashi har zuwa asalin wannan narkakken parlourn. Cikin mayen daya fara ɗibarsa ya nufi kofar yana fita bayan ya loda mata security. Suna ganin yanayin her boss ln nasu suka tabbatar ba'a cikin hayyacin sa yake ba, axton ne yayi saurin buɗe masa murfin motar, shiga yayi suka ja motocin nasu a guje tare barin anguwar baki ɗaya. Wayar sane ya hau vibrating ring a fusge ya shi ƙoƙarin zaro wayar, *first love* sunan daya bayyana kenan saman screen In wayar, manna wayar yayi a kunnensa bayan yayi picking call ɗin, "My Boy!" Shine sautin daya fita cikin wata irin kamalalliyar murya me sanyi, a take yaji jikinsa yaji ya yi wani irin sanyi rauninsa na ƙoƙarin bayyana. Shirun da taji yamata ne yasanyata ta furta *"William"*  gaban sa ne yaji yayi mummunr faɗuwa jin sunan data ƙira shi dashi. yanzun ma shirun yamata dama tasan abunda zai faru kenan ɗin, dama tasan hakan ce zata kasance duk loƙacin da zata ƙira shi da wannan sunan na William bakin sa yana masa nauyin ne wajen amsata. Da dai taga alamun bazai amsa tan ba ya sanya ta furta "ABDOUL-MALEEK KUWAIT! har yanzu kana nan kan bakarnka na ƙim amincewa na dawowarka gida?, rayuwar da ka zaɓarma kankayanxun William. takai ƙarshen maganar cikin yanayin Sanyin murya da kuma raunin da muryar ta samu, domin maganar harya fara fita da sautin rawa rawa na rarrabe wa. A hankali yaji  jikin sa na ƙara yin sanyi sanyi, ita kuma cikin muryarn dake dab da fara zubar hawaye taci gaba da faɗin. "Kasan irin mikin dake cikin zuciyarmu kuwa William?, kasan irin tsananin ciwon dake galabaitar damu aduk loƙacin da duniya zata haskaka a matsayin criminal kuwa?, do on hey ta yes'ka'rev'nvu ka dawo ƙasarka me ƴanci, Onoyin na nan na maraba da dawowarka tare da sauran ƴan uwanka, harda ma jesra, twin yafi kowa missing naka. MOH tana buƙatar ganin ka William....... Sammmm bazai juri waɗannan maganganun ba hakan yasa hannunsa har rawa yake wajen datse qiran, wayar ya tsura ma lumsasaun Idanunsa tamkar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi,yana ƙara lumshe birkitattun idanunsa. yana jin yadda namomin jikinsa suka ɗauka rawa, daga cenñnn ƙasar zuciyarsa kuwa wani irin mugun zugun masifa yake ji. Kife kansa yayi da tafin hannunsa yana cusa kansa tsaƙiyar cibiyoyin sa. Daga nan bai kuma koda ɗagowa bane har Saida yaji an buɗe masa ƙofar motar, alamun sun iso keñan. Kai tsaye yana fita wajen sink ya nufa alwula ya ɗaura domin anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib ne, hakan yasa suma sauran yaran nufar gaban tarin sink ɗin dake jere reras suka shiga ɗaura alwular suna take masa baya wurin bautama mahaliccinsu. Sune ne basu dawo gidan ba sai wajajen ƙarfe taran dare, a parlourn suka dakata suka fara shirya dining ɗin domin suna buƙatar suyi ɗinner.  A nutsen sa ya shiga saƙƙowa zuwa loƙacin 9:35 ne, ahankali ya doshi kan dinning ɗin nasu yana baza wannan mayataccen ƙamshin nasa cikin shigar short trouser fari da kuma vest blue wadda takara haska farar fatarsa,yau kammm ko ƴar p-carp ɗin babu saman kan nasa, hakan shi ya bama lallausar baƙar sumarsa bayyanu wacce aka yima wani irin kwalliyar dada, gefe da gefen kuma an kitse shi sai tayi shilim a tsakiyar kan sa tare da sakkowa har ƙeyarsa, wani irin shining take yi na tsabar kyau da makudan kuɗaɗen da ake narka mata. zama yayi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tare da buɗe wani kyakkyawan food plask lafiyayyan tuwon semo ne da jar miyan dage dage domin shine abu mafi sauƙi daga cikin jerin abinciccikan boss ln nasu, kuma dama best favorite food nasa kenàn, idan kana son ka birgisa to ka masa tuwon semo. Duk da baya a yanayi me daɗi hakan bai hana fuskarsa nuna jin daɗin saba. Barka da dare suka masa kafin axton ya matso ya fara saving nashi,  tuwon semon ya zuba mishi , ya ɗora masa A gabansa tare da sanya masa spoon a ciki, karamin cup na glass yaja yana tsiyan ya masa win with alcoholic a ciki, A hankali ya fara feeding kansa, ya danci da dama kafin ya ture plate ɗin, wannan glass cup ɗin ya ɗauka tare da fara sipping nashi tamkar wani King. Tsammm ya miƙe yana komawa saman sopa tare da jan shisha ya shiga zuƙar ta yana fesar da hayaki. Suma Abincinsu suke ci hankali kwance, suna kammala cin farar shinkafa da jar miyar suka miƙe tare da zagaye boss ln nasu. tamkar wanda zasu hana zarar ransa idan loƙacinsa yayi. Wayar sa ya ɗauka  kawai yawuce warsa bedroom, cikin tafiyar ƙasaita wadda sarauta tagama ratsa jinin jikinsa. Yau kam babu aikin babu aikin daya tsaya yi kai tsaye kwanciyar sa yayi bayan yayi adda'oin barcinsa kamar kullum. ♥️🤍🤎 *MEERAH* Kamar kullum gidan na nan kamar kasuwa, duk uban sallamar data rinka yi amma babu wanda yayi ƙoƙarin amsata, itafa har mamakin gidan su take yadda abubuwa suke tafiyar musu tamkar irin gidan jahilan nan, kanta kawai ta sanye xuwa barandar da mahaifiyarta take zaune tana aikin zuzzuba humra cikin kwalabe. Zaune takai dab da mahaifiyar nata tana faɗin "AMMANMU sannu da aiki!, ina raiha tayi ne naga ban ganta ba?" Dago kanta wacce ya kira da amman tayi tana cewa "yawwa meerah raiha na ɗan aike ta ne bayan layi, gidan jajiya kareemah zata kai mata humra" Nooding kanta kawai tare da cewa "Ina Affan naga ban ganshi ba..... Kafin ma ta rufe bakin saiga wani ɗan bakin yaro nan a guje irin ɗan shekara shida ɗin nan zuwa bakwai, a guje ya faɗa jikinta tare da faɗin "oyoyo aunty meerah na!" Rungume shi tayi tana sakin dariyar farin cikin nan ta buɗe bakinta kenan da niyar yin magana, gaji an wani janye shi a jikin ta. Cikin haki da masifar dake cin gabjejiyar matar dake tsaye ta rike hannun yaronta ƙammm, "meerah ki fita a harkan Affan fa, ko sai kin iskan tamin da?, duk yaran gidan nan da suke nan ga sunan kamar jamfa a Jos, amma duk babu wanda kika liƙema sai ɗana dalilin ki iskanta min ɗa ko?, to wllh bari malam ɗin ya dawo bazai yiwu ba dole ne yau na datse alaƙar dake tsakanin ki da Affan" Kanta dake mata ciwo ta riƙe domin dama komai take yi dauriya ne kawai sharrrrr wasu hawayen takaicin familynta ya saukar mata, _Wai sai yaushe kan family's nasu zai haɗu wuri guda?, sai yaushe zasu gane Allah da girma yake?, yaushe ne zasu san daɗin zumunci da ƴan uwan taka, gidan mu ya kasance wani irin gida ne me cike da son kai da son zuciya, kowannensu yana tafiya ne ya kife kansa kaɗai ya sani da rayuwar yaran sa. Gidan mu yafi karfin a ƙira shi da ko wanne irin suna, domin kafff iyaka bincike na na gaza samun sunan da yayi daidai da rayuwar gidan mu, kawai zan baku abin a dunƙule ne kowa yaje ya nemi fassara!. Mahaifin mu malam Abdullahi gwani yana da mata huɗu, duk wani haƙki na uba ɗa yana bamu saidai sammmm iyayenmu basa taɓa fashimtar hakan, kullum babban burinsu shine meda gidanmu filin yaƙin sunƙuru dana fili. Ga yawan tarin iyalan da Allah ya bashi, gamu da masifar dangin kamar tsaƙi amma sai ka kasance jajirtacce ɗan zamani zaka zauna da kowa lafiya a sannu a sannu muna tafiya, zaku fashimci halin kowa da kuma manufa na_ Wannan keñan Amma dake zaune tana ci gaba da zuzzuba humrarta cikin kwalabe idan ƙasa tana magana to kuwa tayi ita ma, haka Maman Saude ta karaci bala'inta tayi gaba ita da Affan dake ta kuka, yana miƙo min hannu, sai tallar ƙeyarsa take. Na yunƙura zan tashi keñan ƴar ƙaramar wayata irin tecno common ɗin nan tahau ruri cikin waƙar hamisu breaker me taken _Kada ki bari zuciya ta zuga ki_ saurin kallona Amma tayi tare da tsare Ni da manyan Idonta wanda duka muka gada daga gare ta, Cikin in ina nashi ga faɗin. "M.... MD ne, Ammah wai yana son za'a fira dani, kuma kinji wai dole sai dani za'a yi firarn, bayan duk ga su mardiyya nan su hayatu amman dole sai dani za'a yi wai" Kanta ta mayar taci ga *🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 7&8 🤍🔥✅ Aikin ta ba tare da tace komai ba, haka yaci gaba da ƙiran Ni ban ɗaga ba kuma ban tafi ba. "Ki amsa shi, Idan kuma baki so ki bashi amsa ki dena ja masa rai har haka!" Ganin abinda nake son ta fashimta ɗin bata fashimta bane, ya sani faɗin. "Fuskata za'a haska a yayin firan Ammah!" Saurin ɗagowa tayi tare da dubana sai kuma tamin nuni dana shige ɗakin kawai, alamun bata son maganar. Handbag ɗina na ajje a kan doguwar kujerar dake parlourn mu, dake ciki da parlourn ne dakin namu, kayan jikina na rage ina faɗawa kan kujerar tare da kwanciya bayan nasha maganin ciwon kan. A take nannuyan barci yayi awon gaba dani, ban farka ba sai bayan sallar magrib, daƙyar nake Iya buɗe ido na sabo da nauyin da suka min, Adda'ar tashi daga barci nayi tare da tashi ina fita alwula na ɗauro na data salla ina zaune na haɗe kaina da gwuiwa na abin duniya duk sun gama sanyoni gaba raiha ta shiga ɗakin, zama tayi kusa dani tare da daura kanta saman ƙafafuna tace, "Yaaya kije Inji baffa yana ɗakin zaure" Dammmm gabana ya bada sautin bugu baffa kuma yake ƙirana a irin wannan loƙacin kuma. Jiki babu ƙarfi na miƙe ina fita tare da nufar ɗakin zauren. Da sallama na shiga ya amsani tare da nuna min wurin zama, zaman nayi tare da gaisa shi ya amsani a nutse, "ko miye dalilin daya sanya Maryam ƙin amincewa Md firar da ake son yi da ita?" Kaina sunkuyar ina wasa da yatsun hannuwana cike da ladabi na furta, "Videon kai tsaye ne za'a haskaka ma duniya!, shi yasa sammm naƙi aminta da hakan, domin acikin sharruɗanka babu ɗaukar video!" Wani gwauron Numfashi ya kawo ya sauƙe tare da dubana, "A gaskiya banyi tunanin haka abin yake ba amma kije babu komai kije ayi firar kariyar Ubangijii yaci gaba da tabbata a gareki, Allah Miki albarka tashi kije" Da saurin umman mariya ta ɓoye bayan bishiyar dake kofar fita a dakin, domin dama badai iya laɓe ba, Ni kuwa banma san tanayi ba tunda cikin yanayin dana kasa gane masa na baro dakin. *AK* Ahankali cikin nutsuwar sa yake saƙkowa daga upstairs nashi zuwa wangamemen parlourn gidan, loƙacin sha ɗaya da minti sha biyu, kunga kenan minti uku ya rage masa. Zamani tv Duk da kasancewar yau kwata kwata bata niyar zuwa wurin aiki, amma haka ta danni zuciyarta ta fito tun sha daya saura, gudun kada tayi lettt, sai gashi kuma har yanxun wajen sha ɗaya da minti goma shiru shiru babu labarin zuwan nashi. Ɗan madaidaicin Agogon Rolex ɗin dake hannunta ta shiga dubawa ganin har sha ɗaya da mintinan ashirin da biyar tayi bai iso ba, hakan yasa ta jan ɗan ƙaramin tsoƙi, domin jira na ɗaya daga cikin abinda tafi tsana a cikin rayuwarta. Na miƙe kenan ina fita daga cikin department namu wasu irin fitattun narkakkun motoci guda uku suka sanyo kansu cikin coumpaund na gidan jaridar namu, hakan ya sanya ni ja baya ina komawa cikin dakinmu inda mardiyya ta shiga tsokana wai kwana biyun nan kamar wacce akama turen rashin son magana, nidai ci kanki ban ce mata har zuwa loƙacin da Md ya ƙara so cikin department namu, cikin wani irin rawar jiki sai faman zazzare idanuwa yake ya tsohon maye. A kaina ya fara sauƙe Idanu, cikin rawar murya ya furta, "MEERAH da dukkan alamu wannan baƙon namu wani ƙusar ne ke kinga wasu irin rantsantstsun motocin da yazo dasu?, tare da wasu samudawan escort, baki ɗayan sa tun daga ƙafarsa kamo fuskarsa a rufe suke cikin wasu haɗaɗɗun suit baƙaƙe ke hatta takalmin ƙafarsa abin kallo ne, maza yi sauri ki fito, kana ki tabbatar kin cire wannan liƙabin da kika kwama a fuska" Ko amsata bai ji ya fice harda haɗawa da ɗan gudu gudunsa, yake zai shiga kenan ya kusa cin karo da hancin bindigar dake hannun miles, wani irin zaro Idanu Md yayi, domin shifa sai yanxun ma ya kula da uban manyan bindugun dake hannuwansu, kuuuuuuu cikin sa ya bada sauti, gumi na keto masa, miles dake zuƙar cigarettes Samm bai kula da yanda ya tare hanyar da bakin bindigar saba, hakan ya sanya shi saurin janye wa yana tsare Md da firgitattun idanunsa da suka kada sukayi zajurr. A gujeeeeeeee MD ya zura har yana neman hantsilawa "innalillahi wa'inna ilair raji'un, me yake shirin faruwa damu kodai kidnapped namu aka zo yi " Ya faɗa a bayyane amma sai ya daure yana ƙaraso cikin Office ɗin nasa. A ƙalla Saida na ƙara wajen 10 mint da fitar Md ɗin, kafin na fito, Nima dai ganin wannan samudawan hannuwansu riƙe da manyan bindugun Saida ya razanani, amma na dake don nasan matsoraci baya taɓa zama gwani. Haka na ratsa tsaƙiyarsu na fice cikin takun daya fi kama da a ƙira shi dana yanga, saidai sammm ba haka bane haka Allah ya halicceni, zuwa wannan loqacin tuni wanda yake zaune harya fara fusata da zaman jiran yarinyar da murya ta kaɗai yaji, don ko photon ta bata yarda ta taɓa ɗaurawa a media. Wani irin mahaukacin ƙamshim turare ne ya fara welcome nawa, tun daga bakin ƙofar, a nutse na sanya zara zaran yatsuna ina tura ƙofar Office ɗin, ya ɗago kansa da Nijar yama Md magana yaci karo da zanen jan lallein yatsun hannunta, kafin na bayyana kaina cikin qaton hijjabina da kuma niƙab ɗina. Cikin ƴar siririyar muryata nayi sallama wanda Md ne kaɗai ya amsa ni banda mutumin dake haƙimce saman kyakkyawar kujerarn da nayi tunanin daga ina Md ya samo ta, don dai nasan Bama da irinta cikin kaffff gidan jaridar namu. Banko damu da yadda duk mutanen dake cikin Office zubo min Ido ba, domin duk da ko ina na jikinsa a ɓoye yake amma sai suka gaza samun sukuni. kujerar dake pacing dashi naja na zauna,kasancer nasan shine nawa mazaunin. sai table ɗin dake gabanmu wanda ya raba tsakanin mu, an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan saci kallon sa dan koda na zauna ban tanka musu ba, ban kuma zare niƙa ɗin fuska na ba. Haka naci gaba da ƙare masa kallo duk kuwa da cewar bana iya ganin komi nashi, har yatsun hannuwansa kuwa abinda zan iya faɗi kawai shine da ganinsa ba karamin mutum bane, ko daga yanayin zaman da yayi irin na shahararrun sarakunan nan ba muna sarki ba, sai hujin dake kunnensa ta ɓangaren hagu ya sanya wani diamon ring barima color'n gold. Ɗan taɓe baki na nayi tare da janye idanuna dake kansa, Cike da ladabi Md ya ƙaraso tare da maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima ya miƙomin na maƙala a jikin hijjab ɗina, Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. A nutse na sanya fararen hannuwana ina janye niƙab nawa zuwa saman fuskana, cikin aro jarumta da bada attention Kamar bani ba, sai da na kalla cemara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan loƙaci tare da fatarn sake kasancewa damu a shirin mu na kai tsaye, dangane da wannan bawan Allah dake son bamu ƙarin haske game da AK. (Wama ya sani ko AK ɗin ne) Na faɗa aceñnn ƙasar zuciyar, sai kuma nayi saurin faɗin (kai hakan ba bazai taɓa iyuwa ba, bayan ance shi kamar aljani yake kuma tunda yake babu wata cemara data taɓa haska shi aduk tsawon rayuwarsa, saidai kawai sunan daya karaɗe ko ina sabo da mumman aikinsa) Saurin dawowa cikin hayyacina nayi dan gyaran muryan da aka min a take na dawo da ainihin nutsuwa na zuga ga dubban jama'ar da ke son kallon mu. Cikin tsare sa da Idanuwana duk da cewar bana iya ganin ƙwayar idon sane, na furta. “Assalamu alaika ranka ya daɗe”.        A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam” cikin muryar

Chapter 3 of 18