Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gane girman gidan saidai abin mamaki kamal ya zuba komai babu abinda bai zuba musu ba. Dade da kayan kitchen ya zuba musu wasu sai yan tsitstsinen da ba'a rasa ba. Umayma harda kukan ta a lokacin da danjinta dana malam ke sanar dasu abinda kamal din ya musu. Dama yar gudun mawar da yan uwa da aboka nan arziki suka hada musu zasuje su mata kayan dakin, kayan kitchen kuwa dama basa lissafi dashj lallali kamal ya zo busu da wani babban al'amarin da bazasu taba mantawa dashi ba, zuwa yamma aka shiga jibje musu wasu shegun akwatuna masu shegen kyau da tsada. Wannan aikin nabban abokinsa ne ZAYD suraj. Wanda wani aikine ya taba hadasu a wata cout akan shariyar wata yarinya da akayi raping nata kuma kamal ne dan sandan daya jagoranci case din har zuwa sanda yayj winning ta hanyar mikasu ga cout din da anan ne suka hadu da Zayd din wanna shine wanda ga karasa aikin ta hanyar jajircewarsa harka aka yaron senetor na garin kano a prison. Kunsan magana ake ta sarauta a wurin. Akwatuna saida aka sauke musu set uku ko wacce da kolonta. Yaufa ake yinta dan fulani yaje asibiti dubiya an bashi lemo da kaji akace kado fito yace ahhhhhhh ai nikam naga makwanci. To hakace ta kasance da iyayen mariya Hakika duk wanda yayi hakurin dafa dutsi to asannu zaisha romansa. Sunci wuyar sun shanye dakan da dukan sai gashi sama taka allah ya basu dami a kala. Duk wasu abubuwan al'ada suma saida sukama kamal suka mika a hannun danginsa. Dare nayi aka mika amarya mariya wa gidan mijinta a yanzu kamaal suraj rano. Sosae tasha amarya mariya tasha kukanta kasancewarta mutum bame hayaniya bane ya sanya sammm babu wani batun tada hankali akan maganar auren. Haka dai al'amura ke wakana cikin kwanciyar hankali komai yaci gana da tafiya. ★★Lagos★★ Gidansu salman kuwa mahaifiyarsa da yayar mahaifiyarsa ganin dai tabbas auren na shirin tabbata ya sanya hankalinsh tashi matuka, yanzuma zaune suke itada yayarta me suna Aunty mariya sai kuma yarta sury idon nan yay hulu hulu dashi nashan kuka. Ran kowa a wurin a bace yake, cikin kuka sury ta rarrafa gaban mom salman ta kama kafafunta fadi take. "Mom don allah ki taimaki rayuwana wllh ni salman nake so shi kadai nake kauna a matsayin abokin rayuwata! Mom taya kuka min haka bayan kunsan cewar ni shi kadai nake so" Ta fadi tana sake rushewa da wani kukan Salman da shigowarsa kenan yaja tsaki "Mtsss ni kuma uban wa yace miki zanso mace kamarki babu baya babu gaba, ki sani rayuwar ma da kikai dani costa risca ba ason raina bane. Don dai kawai muna gida daya ne kuma babu wata beb din a kusa shi yasa ma har na nemaki nayi maleg dake". Yana fadin hakan yay haurawansa upstsaid nashi.da wani mugun kallo umma mariya ta bishi kafin da dubi mam ta mike a fusace tace aidai kina jin abinda wannan watsatstsan yaron naki yake fadi a gabana, amma kikai shiru to wllh idan har ina numfashj a duniya babu wanj shegen daya isa daura wannan auren alkawarinane wannnan kuuma kinfi kowa sanin daukan alkawarina daidai yake da bi takan kowanne shege ne, koda kuwa za'a zan bada da kisa ne to kuwa saina cika wannan alkawarin..... Fuuuuuuhhh taja hannun yarta suna fucewa a gidan Zeey dake kitchen a lafe ta share wasu hawaye tana jizar labbanta. Tare da fadin "ai wallh inda numfashina na gangar jikina ahalin wannan gida kuda kwanciyar hankali kuma kunyi sallama". Tana fadan maganar tabar kitchen din tare da laluben wata number a wayar da kawai wata jar alama ta mata babu suna. Woyar na shiga ta zube akan gwawowinta tare dayin sujjada daga inda take.ta furta "Ran uwar gijiyata ya dade". Daga cikin woyar kuw wata kakkarfar tsohuwa ta wagaje wargajejen bakinta ta hakwaran sukayi tsatsa ta kwashe da wata dariya me kama da kukan jaki. Kafin ta shiga fadin "An gaida kura me dauke da fatar akuya Birinya baki jelen banza kedin kamar hadari kike malafar duniya ba shirgi maganin bari ta wajena, meke tafe da wushuwatu na?" "Alfarmar kamar ba alfarma bace a badini da za'a juwa gabansu zuwa bayansu bayansu ya koma gabansu nake ga hakan kawai zaifi, domin naga kamar ba masu ganewa da fahimtar bane" "Hhhhhhhhhhhhh Hhhhhhhhhhhhhhh Hhhhhhhhhhhhhhhhh Rainon shegu karki damu dumuwasi na tare dake yar shegiya uwar tsinannun, jaraba a cikin jarababbu makata a cikin makatattu annoba a cikin al'umma hinge kike babu me iyawa dake wushuwatu, dan daukar fansa aka yiki" Wata iriyar dariga zeey data koma wushuwatu ta barke dashi tana saisaita yanayinta ya koma normal daga na mummunar halittar data koma zuwa zeey din asalin da muka sani.. Shi kuwa salman saman lafiyayyan gadonsa ya fada tare da fiddo wayarsa kai tsaye data ya kunna tare da kiran dolly video call. Fitowarta daga wanka kenan tana daure da wani guntun towel ga wani bature kwance akan lafiyayyen gadon hotel din, ya tukun kune jikinsa da tattausan farin duvet daga shi sai wani transpared pyjamas. Woyanta da dama alread datanta yake a bude ta dauka, ganin me kiran saida ya sanya tadan bata fuska kana ta dauki woyar zama tayi akan stool na mirror'n. Kallonshi tayi yana kwance daga shi sai longsleev pant sleek wani irin numfashi ta sauke cikin muryan yar shogwaba ta furta. "Ohhhh my babyna I miss you somuch mua" ta bashi wani kyakykyawan kisses ta cikin woyar. "I miss you so much dee" ya fada yana gyara kwanciyarsa yana dan lumshe ido domin tunda ya baro poland bai sake mu'amulantar wata mace ba, domin shi ba da kowacce mace yaje iya mu'amularsa shi ne ma dalilin daya sanya ya ware dolly ita kadai dinta. A hankali ya shiga bude idonsa sai ya hango wani kakkarfan bature yana nufo dolly'nshi, Wani irin shafarta baturen yayi wanda hakan ya zoma dolly a bazata domin ita har tama manta cewar tare take da wani.da karfin masifa ya rumtse idonsa yana jin jijiyoyin jikinsa na tashi na tsantsan bacin rai. Me kenan?Amananshi dolly taci kenan kome? Meye wannan yake yi a tare da bai karasa maganar zucin saba wannan baturen ya finciki mitsil towel din dake jikin dollyn tare da wani irin hugging nata. Wata kara salman ya saki cikin tsawa ya mike tsaye a fusace tare da ambatar. "Dolly!!!" Wani irin mikewa tsaye dolly tayi babu wata² ta dauke fuskan baturen nan da mari cikin tsawa tace "I hate yhu Vham I hate that" Salman kuwa tuni ya datse kiransa wani irin dafe kansa da hannuwansa yayi kansa na wani irin sara masa lokaci guda, bathroom ya fada ya sakarma kansa ruwa kozaiji dan sausauci jin zuciyarsa yake tamkar yankar naman kirjinsa take tana zazzabowa kasa. Da bathrobe ya fito sanye a jikinsa sai kamshin shower gel yake da sauri sauri ya shirya ya fito da nufin xuwa club haka ko park,don ragema kansa takaicin dolly..... Mom nashi ce zaune a parlon har lokacin laptop ne a gabanta dana famar sarrata cikin kwarewa, sai zeey dake dan matsa mata kafafunta sama sama. Har yakai gab bakin kofa mom bashi ta tsayar dashi ta hanyar ambatar sunan shi. Cakk kuwa ya tsaya tare da juyowa yana kallonta "Dawo inason magana dakai ne" ta fada cikin rashin wargi. Dan yamutsa fuskarsa yayi yana fadin ta jira yanzu zai dawo cikin muryan no nonsense ta furta "Dawo nace" Dan dole ya dawo yana zama tare da tankwashe kafafunsa a gabanta yana fuskantar cikin yanayin jin haushi. Kallan shi mom nashi tayi tana ajje laptop din dake kan cinyart zuciyarta na quna tace. "Se yaushe ne zaka daina kuntamin da rashin daukan maganar mahaifinka fiye da nawa, sai yaushe zaka me amfanin dazanyi alfahari dakai amatsayin dana Salman? Kullum mahaifinka shine a samana akan dukkan wasu lamuranka!. Menene yake faruwa acikin kanka ne da kwata kwata babu ranan da zakasa nayi alfari dakai a matsayin dana? Ban isa dakai ba ban isa sakaka abu ka yimin shi ba cikin dadin rai.... Hannuwanta ya kama yana hadewa cikin nasa tafin sai kuma yadan rausayar da kansa yana sakar mata murmushi. " Mommah me yasa kullum kike ganin tamkar baki isa sani abu nayi ba? Kullum maganar kenan sabanin ra'ayine kawai muke samu dake. Shi kuma daddy so tari ra'ayinmu kanzo daidai dashi so shiyasa zakina ganin kamar bana bin umarnin, pls my mommanah kimin afwa Ina matukar son Meerah ne har zuciyata wllh" Wani irin rumtse idonta tayi tare da zare hannunta dake cikin nashi zuciyarta na mata daci kalamansa na kona zuciyarta. Ya zama dole tayi wani abu akan wannan auren da har cikin zuciyarta taji bata kaunarsa kwata². Tashi tayi tana barin parlon da kallo ya bita domin tsaff ya gama sanin so take taga ta dakatar da auren nan kota halin kaka, ficewarsa shima yayi a parking space ya dauke daya daga cikin manyan motocin dake shake da wurin ya cilla saman kwalta tare da daukar hanyar hotel din Asas rayallerh. ★★KUWAIT★★ Duk inda ka wulga bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar. kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasunsu kuma a kakkame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar. Musamman entrance din da sashin me martaba sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT yake, Wasu mahaukatan Samudawane kewaye da sashen baki daya. Kallo daya zakama dukkaninsu ka gane ko wannensu yana cikin yanayi na tashin hankali ne. Wani irin shiru ne ya ziyarci wurin tamkar wanda mutuwa ta gimla ta wajen.Kowa a take ya shiga nutsuwarsa Wanda suke a daidai hanyarta suna rabewa gefe tareda sunkuyarda kai kasa don bata hanya saboda takun tahowar gimbiya ADEENERH. Wanda sautin anklets din zinarin dake kafarta shine yake ankarar ma duk wani hadimi isowarta ko tahowartar tundaga nesa. Wannan sautin sarkar shine ke sanarda tahowartatahowarta tun daga yarinta harzuwa yanxu data manyanta saboda mulki a jinin jikinta yake. Macece me takukar izza dajin kai kagata yar zafin kaice ba komi ake mata ya burgeta. Tana da wani irin boyayyen hali na tsananin jin dausayi, idan akace kowa ya tsani abu to ita kuma zai kasance tana yi ma wannan abun ko maye wala mutum wala sabanin hakan. Idan kuma aka daukaki abu to kuwa zaka tarar ne sammm wannan abun beyi mata ba koda kuwa kyansa ace yakai zinare kyaune. Tana karasowa hanyar dazata shigarda ita bangaren mai martaba sarki ta tsaya cak batare da tace kala ba saima juyowa da tayi ahankali tadan kalli gefenta. jakadiyar dake gefen tace tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su shida, kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suna tsaya tareda sunkuyarda kai domin sun san ma'anar hakan... *BY AMMEY LAYLERH* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 43&44 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅✅✔✴✳❇ Boyayyar ijiyar zuciya tasauke ahankali saida nu'ura ta tantanceta kana ta sanya kanta zuwa kayataccen parlon. jakadiyart na mara mata baya Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs gold and golden kamar zinari sai kyalli da daukar ido suke. sai komai daya kawata parlourn yazamto shima gold and golden colour dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama parlourn tako ina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a parlourn. Wanda tsabar haduwa da girman parlourn yasan ya sammm alkalamina yayi kankanta daya rubuta muku irin kayatuwar parlour kuyi emaging kawai aranku yadda parlourn zai kasance. Babu kowa parlourn kasancewarsa parlourn farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki. Saima wani irin shiru da parlourn ya dauke. Sake tsayawa cak tayi tareda sake sakin wata nannauyar ijiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren da jakadiyar ke binta ta mata alama data dakata. Ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi kwawan idonta sun rikide sun koma jajaye. Hakan na sake bata tabbacin jikin Mahaifin nata ya matsa kenan da gasken?. Adeenerh ta fada acen kasan makoshinta kafin ta tattaro duka jarumta da karfin gwiwanta. Ratsa dogon palon tayi kai tsaye kofar da zata kaita ainihin parlourn mahaifin nata ta tunkara zuciyarta na neman karyewa. Saida ta runtse jajayen idonta kana tayi kundunbalar tura kofar bedroom din. Wani bedroom ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali. Zaune yake cikin shiga ta alfarma saidai Kallo daya zaka masa kasan bama ya a hayyacin sane, jin motsin shigowane ya sanya Zaid dago da kansa kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa ya dauke kansa. Duk da taso rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da karfin halinta baki daya. Duk da kasancewar Zaid kani yake gareta amma ba karamin kwarjini yake mata, kasancewar kwarjin mahaifinsa ne ya dauka reality shida Biyuninsa Maleek. Karasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa tana durkushewa gaban zaid din. murya na rawa tace "Me martaba! Paapana zaid Ya abana" Idanuwan daya sake watso matane yasan ya jikinta sake daukan mazari ga shirun daya mata shi kansa babban tashin hankali da azabtarwane wa zuciyarta. Sake dukar da kanta tayi saboda gudun ganin yanayinsa. ko dagajin yanda ya dauke wuta yaki ya magantu ya sanyata rushewa da kuka wai ko zai magantun, domin ita wllh tsoro take! Tsoron dunkarar dakin sirrin me martaba take gudun abinda ka iya zuwa yaje. Gudun kar tayi gamo da abinda zai sanya zuciyarta bugawar lokaci guda. A kalla sai da dauki tsawan wani lokaci tana rairai kukanta nan ma shiru yaki kulata. Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace. "Me martaba me mutuwa paah yana nan da ransa, domin mikiyansa ba zasu taba iya kaishi kasa ba. Kimin shiru anan domin wannan kukan naki sake fusata zuciyana yake, ki sani Sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR dashen Allah ne hadari ne shi malafar duniya duk wanda yace zaiyi dashi yaja da ikon Allah ki shiga idonki ya kalla miki shi. Dole wannan karon dan zaki ya bayyana akan mikiyansa. Lokacin dawowarsa yayi Masu gudu su gudu domin kowa yasan karon ba dadi!!!" Ya karasa fadar maganan nashi a fusace. Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin dan uwan nata. Tare da zubo da wasu kwallar zafin da zuciyarta ke mata, tana jin tsananin kaunar yan uwanta a ranta duk da kasancewar ba uwa dayace ta haifesu ba. Adeenerh itace babbar yar me martaba mahaifiyarta ta rasune a lokacin tana yar shekaru shida xuwa bakwai. Ba tare data sake kallon inda zaid din yake ba ta mike tana nufar daking room din data tabbar anan me martaba yake. Tamkar yadda ya bata umarni haka ta ratsa ta shige cikin parlourn. Duka wadanda suka dace ne a cike tare da dakin kowa rannan bace babu me alamar sassauci. Kowa ta shiha bi da ido anan ta itama nata idon suka kallar mata Mutanen dake ma paah dinta kallon ka mutu kawai muhuta din nan. Zaune takai ta bangaren da Oummey ke zaune, shiru ne yaci gaba da wakana a dakin zamanta da kamar mintuna biyar MOH JIDDOH ta dubi Oummey tare da furta. "Wannan karon saiki kira lalataccen dayan dan naki, dan wannnan jinyar tasha banban da sauran, mebi ta ajalinsa ne tazo kuma ta gaskiya da gaskiyar kenan. Wani irin mikewa tsaye Adeenerh tayi cikin furyar fusatar zuciya da dacin murya ta furta. "Wannan kalmar marar kan gado fa JIDDOH! Ki sani gudun hatsaniya ne ya sanya mutanen da suka kasance mugwaye a cikin zuriyarki ya sanya mutumin daya kasance shiru shiru ya fusata!. Inason ki sanarma azzaluman cikinku cewar idan har akaci gaba da fusata shi to ki sani tarwatsa masarautar zaiyi kinsan da hakan?. Uwa uba kuma Zakin da kika dade kina ikirarin ya dawo to ki sani yau sai adda'arki ta karbu dole ya dawoooo........ Kowa da yake daking room din babu wanda jinsa da ganinsa basu tafi hutun wucin gadi ba. Kai tsaye Adeenarh ta zari wayar Oummey directly numbern da tayi lakabi da *Willion gargalion* ta dokama kira tare da manna woyar da kunnen oummeyn "kima danki magana a gaban kowa ki sanar dashi ya isa haka paah dinsa da kasar shi na bukatarsa suma, har wadan da ba'a gayyata bama na muradi da dawowarsa mahaifarsa EMAAR's kai tsaye ABDOUL-MALEEK HASSAN AL-HASSAN EMAAR's take da bukata!” Tana fadar hakan ta juya a fusace tabar dakin. ★★NIGERIAN/ LAGOS★★ Fitowarsa kenan wayarsa ta fara ringing ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba daya. Domin tunda yayi waya da zaid komai ya gama kwance masa. Saiya sami kansa da tsurama woyan nashi ido ganin sunan dake yawo akan screen na woyan *_Sweet Oummey_* wani iri rintse idanunsa yayi ransa nakuma dakulewa. Saida woyar ya katse kana ya sake calling nata againt. "*GARGALION*" Kai tsaye sunan ya tafi ya ratsa har cikin tsakiyar zuciyarsa. "Paah! Dinka EMAAR's na bukatar Tsayayyen matashin zaki majinginarsu. Ka sani shi marar jin magana sai ammasa hukuncin jaki yake ganewa. domin kawo gyara acikin al'umma kuwa dole sai wasu sunsha duka dole wasu sai sunsha jijjiga, maza ka dawo GARGA!!! Kai kadai ne mafaraucin da zaiyi wannan farautar” Wani irin fesar zazzafan numfashi yayi tabbas duk Wanda yake da hannu a poisoning na paah dinsa sai yayi dana sanin saninsa arayuwa. Babu ruwansa da wani yar uwa, dan uwa, dangi domin babu tsoro ba fifitawa ba kara ba alfarma ,zai hukunta duk wanda yake da hannu akan paisoning na paah dinsa. cikin suyar zuciya data ruhi ya Wani irin kaima glass di car din da yake shirin shiga naushi. nan take glass ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba. Cikin dakakken sautinsa ya furta, “tabbas kafin suga bayan paah ni zanga nasu bayan oummu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba! Saina wulakanta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy oummey numfashina fansa ne akan mahaifina!!”. Dole saida oum tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Ak ke magana cikin matsananciyar tsawa. Buga wayar yayi da kasa batareda ya katse kiranba. Nan take ta tarwatse wata uwar tsawa ya dakama security'n akan suje. Gaba dayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abude masa baiyi ba yabude yashiga. Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin boss in nasu, sunsan ba karami abune kesa ran boss ya baci haka ba. Saida suka fita daga gidan suka hau kwalta kana suke tambayar ina suka nufa?. Tamkar bazai tankaba sai kuma furta "airport" dake arms yana cikin dayar motarne ya sanya baima san abinda ake ba. Sai dayaga sun dauka hanyar airport din ne ya gane tafiyan nasu ashe na yanzu ne. Domin dama tunda yayi waya da zaid ya shirya tafiya amma sai washe gari. Cike airpot din yake da tarin security na tashin hankali tamkar irin wanda suke gadin gidan mutuwar nan. Sanya yake cikin normal cashmere me tsananin taushi da laushi wanda tsadarsa yake a baiyane, kafafunsa sanye cikin wasu tsadaddun shoe cambot bleim. Kasancewar yau babu komi a face nashi hakan ya bayyana hasalin kyakykywar fuskansa ga jama'a kai tsaye. Nan securityn suka shiga bashi wani irin tsaro na musamman. ★★★★ A hankali Maleek ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar sa da suka iso tsakiyarta. Haka nan yake jin wani irin abu a cikin jinin jikinsa. Ji yake tamkar ya tafi yabar wani abu mai muhimmanci nashi ne a kasar ta 9j. Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙkara ware manyan idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ke hautsinawa bugunta na sake bugu. Misalin karfe sha biyun dare Jirginsu yayi saukar angulu a cikin babban Airport din kasar kuwait. Din na Hammad international airport. Da sauri arms ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙkofar jirgin. A hankali ya fesar da sassayan numfashi dai-dai lokacin daya fara taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin kuwait yana shakar yancin iskar kasarsa. “Yah Salam” Ya furta Sabida wani irin ni'imtaccen iskar kasar sa mai dadi mai cike da salama da ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake. Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauke ajiyar zuciya ya shaka like irin Wanda baya tare da natshwar nan yau kuma ya samj cikakkiyar nutsuwar. A hankali yaci gaba da taka steps din yana sakkowa kasa. Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙkafarsa akan kasarsa. A take yaji naman jikinsa na wani irin tsuma tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin abu na kokarin fusgar numfashinsa. "Subhanallah!" Ya furta a saman lips inshi yana karasawa ware eyes nashi sosae akan kasar sa. Bawai baya zuwa bane yana yawan zuwa kasar saidai zuwan yana kasancewa na sirru ne. Dan baya cikakken 5Months bai leko kuwait din ba. Wasu shegun hadaddun dunkulallun luzury car's ne suka kutso kansu cikin airprt din. Wanda ko wacce bayan mota me makaon lamba dauke suke da sunan *GARGALION*. Ba'a taba ganin mitocin idan harba mamallakansu ne yaso a gane hakan ba. Duk wata shekarar da zata shude tana shudewane da duk samfurin sabuwar motar data fito na GARGALION din. Wanda kai tsaye kowa yasan mamallakin sunan. Zaid ne da kansa yazo daukar biyuninsa airport din ba tare da sanin kowa ba a cikin masarautar. Da yar sassarfa zaid ya karaso tare da hugging dan uwansa hana sumbatar shi a goshi. Tare da fadin "Ur well come 2 u in my country twin" Dan bubbugawa bayansa Ak yayi tare da furta "Well come back againt daya na" Sake hugging nashi zaid yayi kana ya isa ga arms daya kasance amini a gareshi shima yayi hugging nashi. Sake hugging Ak yayi kafin su nufi wurin dunkulallun motocin dake jiransum Da sauri daya daga cikin tight security's din wanda ke gefen damar motar ya kai hannu jikin handle din ƙkofar ya bude Ak. A nutse ya fada cikin motar kana sauran suka shishshiga, saida fadawan suka tabbatar da cewar ya rigada ya shiga kafin su shiga wani irin busa sarewar dake ma duk wani mahaluki cewar GAGALION ne a wurin. Domin busar da ake may ta daban ne irin me sanyin nance dake ratsa zuciya ya tsuma namomin jikin dan adam. Wani irin lumshe

Chapter 15 of 18