shi kuwa ya saka white ring mai kyau a karamar yatsa.kanshi bai saka hula ba sai baƙar sumar shi data sha gyara gwanin sha'awa kamar ɗan India. kyakkyawar face na mai ɗauke da manyan dara-daran eyes balls ɗin da suke kamar madara.
A hankali ya rufe manya eyes ɗin shi yana sauke ajiyar zuciya.Tare da furzar da iskar bakin shi.Manyan wayoyin shi dake riƙe a hannu ya kalla ga dukkan alamu ƙira ne ya shigo.
Ɗan siririn tsaki ya ja wanda idan ba kana gaf da shi ba ba lallai ka ji ba. A kunne ya manna woyar cikin fusata murya a daƙile ya furta.
"Zanci ubanka Wllh Najeeb akan takura min da kayi!, Wllh idan ka tunzirani zan fasa maka visa'n naga uban da zakay ok”
Datse woyar yayi Cike da taku irin na zaratan maza ya fara taku yana nufar cikin hotels ɗin.da sauri driver'n ya mara masa biya da system nashi da dayar woyarsa.
A room na daban shima ya sauƙa tare da kayayyakinsa suka zube akan lafiyayyan gado. ZAYD SURAJ kenan ɗa ga Sarkin kano mai martaba SURAJ SUNUSU SHUREIM.
*AK*
Cikin bacci yaji ya soma jin vebration na woyarsa, da ƙyar ya iya buɗe lumsassun idonsa. Idanu ya tsurawa screen ɗin wayar dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu haka ya tsira wa woyar kaifafan idon shi.
Duk da cewar yasan ZAID bazai ƙirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu haka nan ya tsinci kansa da faɗuwar gaba. Hannunsa ya miƙa da niyar ɗaukar wayar saidai kafin yakai ga ɗauka ƙiran ya katse.
Ɗin Jim yayi yana me tunanin bin ƙiran saidai sanin da yayi cewar mai ƙiran nasa zai sake ƙira ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya tare da fesar da numfashi.
Anutse ya tashi zaune yana me tunani acikin zuciyarsa, haka nan Idanunsa da suka dan ɗan tara ruwa ya lumshe saboda tunowa da PAAH tare da Momma'n shi da yayi.
”ZAID EMAAR KUWAIT”
Ya furta a saman laɓɓansa woyar ya jawo tare da mannata da kunnensa. Daga cennnnn Zaid cikin yanayin sanyin jiki ya furta.
” ABDOUL-MALEEK PAPA?”
Zaune ya tashi da sauri amma a zahiri ba saurin yayi ba shine a ganinsa yayi saurin.
Cikin fitar sautin da yayi low sosae ya furta.
”Why? Where is my PAAH”
Shiru daga cennn Zaid yayi, Ak kuma jin shirun Zaid shine ya sanya shi furta.
”Ina PAAH yake you will die ko? ka buɗe baki kamin magana Zaid”
Ya ƙarashe cikin sautin tsawa
“Ko ɗaya bai mutu ba anyi poisoning nashi ne agant!, wannan tafi ko wacce iriyar gubar da aka saba poisoning nashi da ita. Domin wannan da wuri zata iya zama sanadiyar rasa shi acikin loƙaci kaɗan, matuƙar akayi wasa to tabbas zamu iya rasa rayuwar PAPA gaba ɗaya”
Wani irin sakur zuciyarsa maganan da Zaid ya faɗa mishi yayi, yana jin daidai yake da bugun zuciyarsa acikin kunnuwansa, haka yake jin maganganun na yankar zuciyarsa.
Saurin fusgo numfashinsa dake ƙoƙarin kwacewa zuciyarsa yayi ta hanyar furta kalman.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju’un!!!”
da sauri saurin dake tafiya da gudun bugun zuciyarsa ya furta.
”what? My papa his under incapable survive in the world at this condition? oh god tell me the Truth I'm very dangerous twin!”
Jin yadda lokaci daya yanayin dan uwansa twins dinsa jininsa ABDOU-LMALEEK AK KUWAIT ya sanja ne ya sanya.
Ya shiga kontar masa da hankali, ganin kamar hankalinsan na kwanciya zai yi bane ya sanya ya shiga fada masa kalma daya takkk.
Wadda bansan ko wacce kalma bace itane ta nutsar da AK da kuma lurar dashi......
*BY AMMEY LAYLERH*
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 29&30
# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# BEST LOVE
🤍🔥✅
*KUWAIT*
Zazzau ne suke a falon maza da mata kowa ran nan a haɗe wasu ido yayi ficin ficin.
Mommah dake dab da ƙafafun MOH JIDDO idanunta sun kaɗa sunyi jazur tana sanye da Alkaybba hannunta rikeda tissue dakuma charbi tanaja, sai wasu daga cikin manyan fada irin su Waziri, Wambai, Makama dakuma Sarkin dawaki, chan kuma saiga wasu Manyan dattawa maza guda biyu sun shigo sun zauna suma, dan faɗuwa gaban Mommah yayi dan haduwan mutanen nan wanda bayan sarki sune masu fada aji a fadan ƙasan Kuwait kasan babban abune, ƙarasowa suka yi tsakiyan ɗakin sannan suka sami waje suka zauna
Zaid ne ya ɗago rinannun eye's nashi tare da duban MOH JIDDO cikin daƙushashshayar murya yace “ JIDDO kene kika aika akirani”?
Girgiza kai JIDDO tayi kafin ahankali tasa tisssue saman fuskanta tashare hawayen tasss sannan tace “Wambai ne ya aika kazo zaka ƙira musu wannan tantirin ɗan uwan naka”
dasauri yadagokai yakalleta tare da sauran jama’an ɗakin dake kallonshi yace “tooh” anatse waziri ya furta “ƴan uwanka duka sun iso na kusa dana nesa”
Sai kuma ya ɗan yi shiru a tare dukansu ƴan ɗakin suka zubama waziri ido duk kuwa da sunsan YARIMA MALEEK zai ambata amma hakan bai hana su binsa da ido ba.
“YARIMA ABDOUL-MALEEK fa”?
Ya faɗa wanda iyaka ambatar sunan shi da akayi Saida zuciyoyin wasu daga cikin su ya buga.
Adan hankali Zaid ya sauƙe ƴar ɓoyayyen ijiyan zuciya yace
“naƙi rashi ba adaddi bana samunshi” salati Al-hussein ya saki cikin babban sauti sosae ya shiga furta
“Ban taɓa ganin gantalallen yaro irin ABDOUL-MALEEK ba ohh Allah Ace mahaifinka na ahalin Rai ko Rayuwa amma baka ma san a halin da yake ba”
MOH JIDDO ce ta tare shi da faɗi
”Dama fa ba jinin MARYAM bane yake yawo a sassan jikinsa, kaima da ɓata baki kake Wllh hussein”
cikin murya mai laushi wamzai ya furta "MOH JIDDO adai yi haƙuri muna a halin ciwo ne" ya faɗa yana rusunar da kansa ƙasss
Wani mugun kallo MOH JIDDO tabi wambai dashi wanda suke ƙira da *RIGA DAKI* a yarensu na cennnnn.
Cikin tsana da jin haushi MOH JIDDO ta furta ”Ni na rasa mecece matsalan ABDOUL-MALEEK da ya gwammace ya tafi yawon duniya har wata uwa Nigeria akan abbinda ba tabbacecce bane. Shi burin daya ɗauka alƙawarin cika tashin”
Ijiyan zuciya Mommah ta sauƙe tana jin wani abu na yawo a dukkan sassan jikinta.
“Yanzu ai idan ya riski saƙon mutuwarsa a yanar gizo ya dawo!, nasan duk inda yake aduniyar nan zaiga news na rasuwan mahaifinshi dan haka zamu ganshi idan ya riski saƙon macewar ubansa”
Yana faɗin hakan ya tashi yayi gaba abinsa yawuce yafita yanajan ɗan ƙaramin tsaki aranshi bayan yakai waje.
Cikeda ɓacin rai MANDOOD ya furta ”MOH ve said this time without number to Mai Martaba he should call ABDOUL-MALEEK to order, duk cikin yaran me martaba babu gantalalle kaman ABDOUL-MALEEK, yaƙi zama ya koyi komi na al’addun masarautar mu, sabo da yana jin kansa shi tantiri ne”
_TUN DAGA HAIHUWA MA KUWA_
Domin Abdoul-maleek hadarine malafar duniya,funkasau babban girki, biri da gatarine shi ajalin me gonna, Jan kasa na bayan daki kowa ya ganshi ya tuna Allah. Shi kadangaren bakin tulune a barshi ya fada ruwa a taba shi kuma ya FASA TULU, Ak ginshikin dutse me kowa yayi karo dashi shika fadi, soja mazan fama namijin mazaje an buga dashi an barshi saidai su buga su barshi kuma domain shi din dashen Allah ne, murucin kan dutse be fito ba saida ya shirya_
ZAID ya furta a cikin zuciyarsa ya miƙe yana ficewa a ɗakin shima domin da biyu yaki sanar musu yayi magana da AK din.
haka suka ringa fita ɗaya bayan ɗaya, ɗakin ya rage daga Mommah sai RAZEENERH mata ta farko ga Me martaba sarki *SARKI HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT*
Wasu irin kaifaffun hawayene suke saƙƙo mata, cikin ƙunar zuciya da irin raɗaɗin dake ƙona zuciyarta ta kwanto da kanta zuwa jikin Mommah MARYAM. Ta fashe da wani gurgegen kukan ɓakin ciki.
”Shin Sai yaushe zamu dena zubarwa da ƙaddara hawayenmu? Sai yaushe abubuwan dake ɓoye zasu bayyana kansu? Na gaji-na gaji NA GAJI MARYAM, inajin haƙuri na na gab da ƙarewa akan abubuwan dake faruwa dani a cikin wannan azzalumar masarautar HABA!”
Ta faɗa cikin sake fashewa da wani gursheshen kukun,
"Haƙuri shine matakin ko wacce nasara RAZEENERH, Ko wacce Nasarar rayuwa da ɗaukaka kuma suna zuwarma baya ne da tarin ƙalubalen rayuwa salo daban daban, me yasa zamu gaza cinye ɗan takin daya saura a cikin rayuwarmu?. Xuwa yanxu AYSHATUL HUMAIRA a bayyane take garemu loƙaci kawai muke zuwa ya bayyana kansa,Ayi walƙiya Allah ya bayyana mana magautanmu na ɓoye dana fili mu gansu su fito suna hawaye anyi walƙiya!!!”
Sosae suka sha kuka me sunan kuka kafin su runguɗa zuwa ga special room donper ɗin da me martaba yake cikin haɗaɗɗen hospital ɗin masarautar.
Dammmmm ɗakin yake tarin ƴan uwa na kusa dana nesa irinsu garin Makka Madina Saudi Arabia dadai sauransu aurarru da ma'aikatan da suke aiki a wojen ƙasar.
Wani gauran numfashin da sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT ya kawo ne ya sanya baki ɗaya katafanin jama'ar parloun, juyowa zuwa gareshi.
ALHAMDULILLAH wasu suka shiga furtawa wasu kuma zuciyarsu na ƙonewa ne tare da yin baƙikirin tun durun da tsabar masifar baƙin cikin da ke soya zuciyarsu ƙurmus.
Ahankali ya shiga bin kowa dake parloun da ido, cike da tsananin ƙarfin hali da kuma dauriya irin ta zaratan sarakai ya saki kyakkyawan murmushinsa me kyau. Wanda exactly tsananin kamfaninsa da ABDOUL-MALEEK KUWAIT AK suka gama bayyana.
”Alhamdulillah Ban mutu ba Allahu Ya tsare lafiyata a kwanana akwai ƙari don haka kowa ya kwantar da hankalinsa” sarki AL-HASSAN EMAAR ya furta
Wanda wannan maganar nashi ya daki wasu ɓoyayyan rufaffun zuciyoyi daga cikin al'ummar denpor ɗin....
Haka kaifafan idonsa yaci baba da yawo har sauke kallonsa akan Ayeshan shi. Kyakykyawara mace karshe a fannin hakuri mace me kamar maza CE ita wajen danne ko wanne irin ciwon cake damun zuciyarta.
Da wani sassayan kallo ya bita yanajin lallai rayuwar idan babu ita to shima babu amfanin tashi rayuwar, a jinin jikinta taji irin kallon da take binta dashi.
★★★
Abuja
Nigeria
Zaune yake yayi crossing kafafunsa sanye yake cikin shigar kananan kaya na shan iska, loptop ne a gabansa kan dan table tonight din dake gabansa, yana faman sarrafata cikin kwarewa yake latsa keyboards din system din.
A nutse zayd suraj shureim ya karaso har inda AK din yake zaune.
Zaman shima yayi ba tare daya furta komai ba, haka suka shiga zaman kurame har na tsawon 30 minutes, A nutse Zayd dubi AK da yama nuna tamkar besan anyi ruwan zayd din bane yadan daki shoulder na AK din.
Sai kuma ya dan saki wani shegen murmushi domin shima karshe ne fagen tashi izzar Wanda shima sarautar kano ta gama ratsa ilahirin Jinin dake gudana a cikin jikinsa.
”Yaryadi baka yadon banza yau kuma dame kake tafe?, ka kirani ka sanya na baro garina zuwa wani garin Right?' Ka kuma shareni abunka to Dan ubanka Wllh zan komawa na domin inada abubuwan yi dana baro ba kamar kai ba”
Wata katuwar harara ak ya sakarma zayd yana fadin.
”Jeka mana dan uwarka ka gani idan Abbu ko ummieyn Momma basu koromin kaiba”
Ya fada a daidai lokacin kuma ya kammala aikinsa na cikin laptop, tashi yayi tare da yin gaba yana fadin.
”Idan kaga dama same ni a room na baka 2 mint domin INA shirye shirye bar muku kasarku ne”
”Look AK karka ma soma hakan, Don munyi woya da mommah tun a daren jiya ta shaidamin cewar jikin Me mar taba da sauki sosae $0 inaga babu bukatar zuwanka!”
Ko ta kanshi ak bai biba saima wucewarsa da yayi room
Bayansa zayd yabi cike da shekiyanci yake tsokanarsa ai dole ya bashi girma tunda shine autan su momman ak din.
Ganin nan din ma ya share shi ne ya sanya shi komawa seriously tare da furta.
”Muyi abinda ya kawo mu kasan akwai Case's da yawa dana tsalallake na baro dude”
Charkkk kuwa ak din ya tsaya tare da juyowa ya fuskanci zayd din.
Zama sukayi a tsakiyan kayataccen palon hotel din, computer'nshi ya janyo tare dayin wosu yan danne danne said kuma ya juyo da fuskar computer system din xuwa gaban AK.
Da wani black beauty guys ya fara cin karo wanda me sanye cikin kaki na yan sanda.
Tsaye yake chark a gaban Cf of the police babu alamun tsoro a tattare dashi.
Gani yayi wannan ceef din ya mike a fusace yana duban wannan tsayayyen matashin, kafin kuma cikin fusata ya furta.
_Akan me zaka harbe shi?, Tambayarka nake me yasa ka harbeshi? Me yasa kai baka Iya sarrafa kankane?_
Gani yayi wannan matashin police din ya furta.
_Bana Iya sarrafa kainane akan irin wadan nan tantiran yallabai!_
_Kenan saika harbe shi kuma?_
Ceef ya sake furta a tsawace.
_Me yasa bazan hukunta wadan da suke barazana wa al'ummarta ba?, nayi rantsuwa da girman Allah zan kare kasata da al'ummata. Akan mene yasa bazan harbeshi bayan shidin gurbatacce a cikin al'ummar?_
Ya fada tare da sarawa a gaban Ceef din.
_To hakan ba shine dalilin da yasa muke nan din ba?, muna kamasu mu gurfanar dasu a kotu domin karbar hukunci daidai da abinda suka aikata_
_Tsawon wanne lokaci ake dauka kan a kammala yallabai?_
Wannan matashin ya fada cikin sigar tambaya shima.
_muna Iya kaiwa tsawon wata biyar ko kuma ma shekara_
_Kafin xuwan wannan lakacin taya kake Iya bacci?,No bana Iya baccin to yallabai_
Yayi maganar cikin tsananin fushi.
_Nima wannan shine dalilin da yasan nake ta bibiyar Tanbuwal, duba wadan nan duka sun aikata manyan laifiku!, duk kuma Wanda ke a cikin wannan kundi suma a kashe su kenan?_
Ye jefawa matashin alamar tambaya.
_Kashe sun shine daidai yallabai idan har muka kare ADALCI to daga nan ne shima ADALCIN saiya zama me bada KARIYA a garemu!_
Daga nan Video'n ya yanke.
”Inspector KAMAL RANO kenan, matashin dake aiki da dukkanin rai da zuciyarsa a jihar kano!. Shi din marayane A karamar hukumar kano yake a garin RANO baya da uwa baya da uba dangin duka mahaifansa sun wofantar dashi. Yanzu haka yana zaunane a garin kano anguwar sharada”
Wani dan banzan murmushi ak ya saki kafin cikin muryar nan na no nonsense ya furta.
”ina bukatar ganinsa a cikin week din nan”
Daga haka ya mike yana barin wurin, bedroom ya shigee shi kuma zayd ya bar dakin baki daya.
Bayan sun tattauna wasu muhimmam abubuwa daga baya.
*LAGOS*
~Meerah~
Sanye take cikin shigar atamfa chiganvy coffee colour ta ɗora dogon shimar din ta har kasa.
Sake kallonta salman ya yi a karo na biyu ganin yanda ta haɗe rai.
"Meerah"
Ya kira sunanta batareda ta kalleshi ba ta amsa da
”na'am”
Wani gauron numfashi ya sauke sai kuma ya furta.
”Naga kamar baki saurarena ai a irin wannan lokacin kamata yayi ace zallar farin ciki kadai za'a gani tattare dake, amma da dukkan alamu ko saurarena ba kiyi bare ki fahimceni ma”
kallonsa tayi da manyan idanunta masu cike da wani irin kwarjini
sai kuma ta dan tabe baki tace
”Ai naga kunnene ki ji kuma ina jinka ko ihu kakeson nata yi kwararo² titi² ina fadin ina jinka?”
numfasawa ya sauke kafin ya furta
”shikenan na baki lokaci kije kiyi tunani da kanki ina fatan za ki yanke shawara mai kyau, kasancewar saura nan da watanni mu zama Ma'aurata”
Wani shegen kallon ta wulla masa yi tayi kamar zata yi magana sai kuma kawai tayi shiru ta juya tabar wajen kawai, domin a ganinta wannnan tsayawa ja'in jar ma aiya sami arzikinta kenan.
Domin a ranta take jin Wannan auren ba tabbatacce bane.
Gefen lips Inshi yadan ciza kadan tare da furzar da numfashi yasan ya shige ajin yarinyan, Bama don ya kadaitu da ita ba har ita wacece da zata dinga wulakanta shi.......
*BY AMMEY LAYLERH
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 31&32
”Amma dai ba har kin dawo daga firan ba Meerah ba?”
Disha ta tambayeta ganin har ta dawo ga ran nan haɗe babu ko sassauci.
Rabuwa da ita tayi taki tanka mata, ita kuma ganin ta mata banza ne ya sanya fadin.
”Haba meerah bakison mutumin nan kawai ki fito fili ki fadama su baffa fine!, amma shi haɗe ran na mene kinsan dai ba maganin damiwa zaiyi miki ba?"
Wata yar karamar kwafa taja tare furta ”wlh idan har bai yi a hankali ba sai na yi masa rashin mutunci nifa banson irin haka, na gaji da wannan takurar haka nan haba!” ta karashe maganar a tsawace.
”So sorry meerah kiyi hakuri kici gaba da kaima Allah kukan ki, Insha Allah zai duba lamuran”
Nooding kanta tayi tana jingina da jikin duguwar kujerar palonsu. Nan suka ci gaba da firansu amma sama sama, domin meerah bata jin kanta a cikin mood me dadi.
Washe gari da misalin karfe Biyar da Rabi na yamma Meerah da disha ne zaune jingune da roiler din dake harabar wurin. Meerah ta dan dubi Rolex watch din dake hannunta ganin shida na kokarin karasawane. Ya sanya ta mikewa tana fadin.
”Inaga lokacin tafiyana yayi zan wuce bye Sis”
”Laaaa kinga ma motar ya Ayaan ta shigo kizo saimu sauke ki gida!”
Cewar disha, Tafiyanta taci gaba dayi ba tare data dakata ba tana gyara zaman bag din dake rataye a shoulder nata cikin muryan no nonsense ta furta.
"I m so sorry Sis to kar kice wani abu please zan fita bakin gate na tara napep then nasan ma Wannan uban yan nacin na dab da shigowa."
Saurin juyowa disha tayi ta kalleta tabbas idan da sabo yaci ace ta saba da halin meerah, saidai ta gaza sabawar har zuwa yanzun.
Parking car din da ayaan yayi a gabansu ne ya katse maganar da disha take shirin yi.
”Yen mata barkanku da hutawa ku shigo mu wuce” ya fada yana sauke glass na motan.
Gaba kawai ta wuce ta bar disha tsaye, domin meerah bata magana biyu kuma dama ta tsani ayaan din Sabo da masifar kallonta da yake yawan yi.
Dan bata fuska disha tayi tare da shigewa cikin motar ta rufo murfin da karfi. Ta gaban ta suka wuce bayan ayaan ya sake mata tayin shiga amma ko kallo be isheta ba.
Idanunta ta dan lumshe a hankali kuma saki wani dan murmushin da ya bayyana akan fuskarta. Ganin yadda fuskar mutuniyar ta tayi taki ko kallar inda take lokacin da suke wucewa.
Tasan cewar hakan da disha tayi alamane dake nuna cewar tayi fushi da ita kenan.
Ci gaba tayi da tafiyanta har takai bakin gate din fita daga gidan jaridar, haka ta ringa ratsa manya manyan motocin dake wurin. Tafiya takeyi amma gaba daya duk bata jin dadin yanayinta amma ko a fuska baka Isa gane yanayin da take a ciki ba.
Hango wani me napep yana zuwa ne kuma yasa da sauri ta soma daga hannu tana son tare mai napep din.
Cikin sa'a kuwa ya tsaya cikin yanayin dan hanzarinta ta yunkura da niyar shiga napep din.wata arniyar Rolls *R* Rayce ta danno kanta, wacce kiyastin kudinta a dalar amurka yake daidai $25,000. kamar ance daga idonki sukayi 4 eyes da duk da yau din ma idonsa rude yake da blue shade.
Wani dan banzan kallo ta cilla masa tare da murguda bakinta, kafin can cikin kasan muryarnta irin na tsiwan nan ta furta.
{MARA GASKIYA DAI KO A RUWA GUMI YAKE}.
Fadawa cikin napep din tayi tayi sai kuma ta shiga furta kalmar
”La ilaha illa anta's subhanaka inni kunti minazzalin!”
A bayyane domin zuwa yanxu dai tasan wannan mugun wani abun yake sake nufi da ita....
”Malam nace don Allah kuwa kasan wancen mutumin na cikin motar cennnnnñ?”
Ta fadi da kokarin nuna masa motar, saidai me? Sama, kasa, haka ta nemi motar ta rasa.
”Hajiya wacce motar fa?”
Muryar dan sahun ya farkar da ita.
Ijiyar zuciya ta sauke tana fadin ”muje kawai anguwar dadin kowa zaka sauke ni farkon layi!”
Ta fada tana me sake kallon inda taga motar da yake ciki.
"To Hajiya zaki biya 400"
Me napep din ya fada yana kallonta.
Nooding kanta kawai tayi batare kuma da ta nemi ya rage mata ba, ta bude bag din ta kudin ta bashi yaja suka tafi.
So kawai take taga sunkai gida don Anne'nta tace mata zata aiketa gidan hajiya umma,amma intai dare ba zata aike tan ba ko kafin ma ta dawo ta aika Raiha.
Wani irin kyakykyawan murmushin daya sanya me napep din kallonta ta tayi.Tuno da Anne da tayi Ita kanta batasan iyaka adadin son da takema Annenta ba, Kawai dai tasan Wani irin so takeyi mata na musamman, son da yake tafiya da tausayi mai tsanani bata da kowa aduniyar nan daya wuce mata Anne'nta itane komai nata Garkuwanta haka kuma farinciki agareta ita da Raiha dinta. Hannuwanta da suke hade wuri guda ta sake dunkulewa, tana matukar tausayin Anne'nta sabo da ta tashi ne ba uwa uba Yar uwa Dan uwa wani nata a tare da ita.. Ahankali kuma ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.
*{INASONKI ANNE NA}*
Ta fadi hakan acikin zuciyarta tana mejin tsananin shaukin son mahaifiyar nata na ratsata.
Uwar da takejin babu irinta a fadin duk duniya, Uwar da take fatan faranta mata akoda yaushe, Uwar da take matukar son farincikinta fiye da kowa da komi na cikin duniyar.
Aikuwa basu wani debi lokaci ba suka iso gidan kuma babbar sa'arta data ko shirin tada sallah ba'aiba.
Da sallamarta ta shiga kota kan mutanen da suke zazzaune bata biba, Da Anne'nta ta fara cin karo a palo tana duddura humrarta me azabar kamshin gaske. Gaida ta tayi dama kuma al'adar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 18