ya rage mana yau soran 6 days kenan daurin aurena ni Maryam Abdullahi gwani.
A sautari wasu lokutan mutanen da muke musu kallon bango ko jigojin rayuwar mu suna iya zama sune masu nisantar mu, mutanen da bamu san sun damu da mu ba kuma su iya zame mana bango majingia. Ba zan iya bama kowa amsar da take cunkushe a cikin rai da rihuna da kuma zuciya naba!. Domin Sunan shi kadai shine ya sanja zanen kaddarana, kuka na ya kasance a boye bayan murmushina. tambarin da kaddara ta bani ya sani kara ninkaya a cikin tafiyar zanen wata ƙkaddarar izuwa wata alkaryar ta daban.
Kaddara wata abace wacce bawa baya iya tsallaketa kowa da kalar nashi salon ƙkaddarar haka kuma kowa da akwai silar nashi ƙkaddarar.
Haka ba'a iya guje mata domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tamkar zanen dutse a cikin kirjin ko wanne bawa. haka take duk yanda zakayi bazaka iya gogeta ba no matter who are you or what you have nobody can change her destiny either good or bad.
Ayau daya kasance ranar lahadi 1 ga watan takwas na OGUSTA dangin salman suka kawo jibgin kayan akwatunansu gidan. Kayane iyaka kaya wanda mutanen gidanmu harma da yan anguwa zancen kayan ake, media kuwa babu inda zancen be zaga ba domin magana ake ta Ajebor irinsu salman.A lakacin dana budi ido naga yadda pisc nawa suke yawo a media Raina ba bakaramin baci yayi ba, domin abu na farko danafi tsana kenan yada photo's nawa ya media.
Martanin kowa wannan lokacin shine ashe dama shine dalilin daya sanya kullum nake makale a cikin nikaf.
Ashe nasan abinda nake ma kaina tanaji tunda gashi ata sanadiyar auren dan shahararre kuma tycoon isa manu empire pisc nawa sun gama karade ko ina.
Masu iya magana sukance ba iyaka yaudinka shike tabbar maka da nasarar goben kaba, haka zalika yau dinmu ba itane madubinmu goben mu itane madubinmu abin alfarinmu...
Nayi kuka, Nayi kuka Nayi kuka wanda ni kaina bansan iyakar shiba a wannan rana.
Karin wani abin mamakin kuma idan nace muku Anne sammm bata farin ciki da wannan auren karkuyi mamaki ko al'ajabin hakan.domin memakon kaga tarin farin cikinta saidai kaga akasin hakan, Ko yanzu ma kwance nake tarin abubuwa sunbi sun cunkushe a tsakiyar kirji. Ganin dumuwa na neman sanya ni a wani halin ne ya sanya ni bude DATA na, WhatsaAp nawa na fara lekawa bayan sakwannin mutane dana dan dudduba saina koma kallar status na mutane. Bear man shine status na karshe dana kalla wanda ya bani mugun haushi sosae, Pisc ne marasa kan gado yayi status dashi nace kunsan waye me wannan sunan Salman!.mutumin dake dab da zama mijina shine me wannan sunan, don ni a zahirin gaskiya idan na kalleshi da dan biri yake min kama karfa kuce wai don bana son shiba.
A ahh bawai don bana son shi bane har zuciyana da gwaggon biri yake min kama.
Fita nayi daga whatsaAp din na koma Facebook nan na dan dubba abubuwan da suke wakana a median kana nayi search na sabon littafin *SPECIAL*
_TA DABAN_
Na AMMEY LAYLERH da zata fara domin kullum saina duba amma haryau bata fara ba, tun akan litattafanta uku dana karanta na mato akanta Wato litafinta na.
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*KAUNA BIYU*
Sai kuma wani dana fara karantashi amma be zama complete ba wato *PRINCE SAPWAN*
{Sanyi ya haifa wuta }.
Saidai kash yau din ma banyi dace ba har yanzun bata fara ba mebi domin tun daga dandanon kadan daga cikin labarin na gane zai bada fire sosae.
Haka na hakura na sauka tare da kashe data na ammafa ban sauka ba saida na ajje mata message a facebook dinta don bana da whatsaAp number nata.
Sallamar da Hajiya umma ta rafkone ya sanya ni tashi zaune ina amsata tare da kashe data na. Karasa shigowa tayi gaidata nay ta amsa ni tare da tambayar inda Anne take, ganin bata parlon kallonta na danyi sai kuma na sunkuyar da kaina da hannu na mata nuni da bedroom dinta.
Meeting room
Wani irin hadadden parlon ne mai mahaukacin girman gaske parlon ne mai kamada wata fadar kana ganinsa kasan wasu ishasshun mutanene ke rayuwa a ciki, akalla mutanen dake zaune a cikin parlon sunkai wajen su ashirin da biyu, ko wannensy zaune yake akan street table din gaban ko wannensu dauke da juice da gorar ruwa sai dangin su snack.
Manyan masu kuɗin mu kenan manyan kuma yan siyasarmu ne ake magana. A tsakiyarsu ga system jone da dukkan alamu video call suke, wani babban mutum ne kwance jikinsa sanye da uniform irin na marasa lafiyar nan. Zaune ya tashi cikin tsananin fushi kafin cikin miryan fusata ya ce.
"Na rasa mema kuka tsaya yi dahar yanzu baku kawar da wannan shegen yaron ba, tsananin fusata kukeson ta bayyanane kawai manu!, in banda haka ace yarona yana wurinsa duk kaninku babu wanda yayi wani yunkurin kwatar shi daga cikinku Right?"
Tambuwal ne ya dube shi shima cikin nashi kalan bacin ran ya furta
"Kafi kowa sanin wanene wannan yaron bashasha kai a tunaninka zuba ido mukay kenan kome, toba shiru mukay ba karka manta cewar governor da minister da kyar suka sha, zafin kan yaron ni kaina na bani tsoro
ɗan zafin kaine dabi'arsa kuma kan firgitar dani sammm baka taba gane alkiblarsa baka taba sanin koshi ainihin wanene shi!?”
" Saime! Nace saime dan dabi'arsa na firkita zafin kansa kuma kan baka tsoro toni sammm kwata² bana tsoron haka, nima dan zafin kanne aiiiii ko ka manta waye Audu bashasha na tuna maka"
Ya fada a fusace cikin fusatar kanta.
"Duk ba wannan bane ya taramu muyi zaman daya taramu kowa ya kama gabansa, yanzu abu tsaye a raina shine bikin yarona idan an gama komai ya biyo baya. Kuma idan baku manta ba ji ina mun kashe wancen maganar tunda ita kanta yarinyar tana dab da zama tamu ne"
Ijiyar zuciya duka suke saukewa kafin ya dago kaida ganinsa kaga wanda baya cikin hayyacinsa, "To wai ma bikin saura kwana nawa ya rage mana ne ma?" Ya tambaya yana komawa kwance domin yar hayaniyar nan harya fara hawar masa kai.
Daga nan suka shiga tattauna manyan maganganunsu na sirri daga haka zaman nasu ya tashi. Domin tanbuwal har Allah Allah yake su tashi domin yana da wajen zuwa karfe taran dare.
A slowly katuwar bakar jeep din ya parker a wurin adana motoci na cikin Park din, Sanye ta fito cikin riga da wando bakake sai wata falmaran Ash color data dora saman riga sa wandon. Idonta toshe cikin bakin glass tayi rolling da siririn vail din riga da wandon wanda suka kasance disigners ne.
A hankali ta shiga karema wurin kallo, Kallon wajen kawai Riyya keyi lik kamar irin bata san wurin nan ba. iyaka haɗuwa wajen ya haɗu park ne mai girman gaske ko wanne passege yana da nashi kalan kyaun, basarwa tayi tana jingina da jikin motornta babu dadewa kuwa wata arniyar Rolls {R} Rayce blue black ta sanyo kanta cikin park din. Har dab da idan take tsaye motorn ya faka kafin matashin alhajin dake zaune cikin motar ya fito.
Jikinsa sanye cikin wasu shegun Cashmere me laushin tsiya da tsadar gaske wanda kai tsaye bazaka taba iya zartarma da kayan kudin da suka lashe ba.
Tun daga kan motarn ta fara kallon shigar shi da irin makudan kudaden da suka lasa.
Bvl $15, 000
Cartier $5, 000
Rolex $35, 000
Rolls {r} Rayce $250, 000
Wani irin numfashi ta sauke tana dauke kanta a kallonsa, yana karasowa dab da ita ya sakar mata wani tsadadden murmushi yana mata nuni data biyo shi.
Bayanshi tabi suka bi wata hanya cikin wani kayataccen special gun shan iska suka tsinci kansu, kan wasu kujeru wanda suke zagaye da wajen suka karasa zama yayi tare da mata nuni data zauna itama.
Kujerar dake facing dashi ta zaune suna zama wata waiter ta iso wuin tana basu jotter na jerin abubuwan da suke dashi. Shine ya zabi tarin abubuwan da yake so tare da bata umarnin taje ta kawo, babh jimawa ta kawo katon nrey tray xuwa kan table din dake gabansu.
kallon ice-cream ɗin merrah ta yi amma bata ɗauka ba saima wayarnta da take famar latsawa, Dan gyaran murya yayi tare da fadin "Baby ya kamata ace kinsha ko wani abune"
Ya fada cikin Kasa da murya sosae ba karya kamm jijinsa sai fidda daddan kamshi yake.
Ajje woyanta gefen tray din tayi sannan ta ɗauki ice-cream ɗin guda ɗaya ta fara sha. Har wani lumshe ido take saboda daɗin da ice-cream ɗin ya mata, hakan yasa tambuwal binta da wani shu'umin kallo kana ya sanya hannunsa ze ɗauki ɗayan, dan buge hannunsa tayi kamar irin bata sani din nan ba. Dan kadan ne ya zube a jikinsa dan sunkuyawa yayi da nufin daukar tishu tayi saurin jefa masa kwayar dake dunkule a hannunta. Dan turo baki ta yi iri cikin shagwaɓar nan ta ce
"Ayya beby ban kula bane sorryy" tayi maganar tana tura masa robar Ice cream din gabansa. Dauka yayi tare da fara sipping a nutse har wani dan lumshe ido yake domin gardinta na kai may har inda ya dace.
Cikin abinda bai wuce 5 mint ba ya tafi luuuuuuu, Arms dake tsaye bayansa ya taroshi zuwa jikinsa hannunsa ya sanya ya sakali kafadar tanbuwal din tare da ziro hannuwan tanbuwal ta cikin wuyansa. Dashi ya fara tafiya a jikinsa Riyya ta mara musu baya tamkar dama cen a taren suke.
Har bakin motarsu sukaje ba tare da kowa ya farga da abinda yake faruwa ba. Shigowarsu kenan cikin park din idonta ya sauke akansu kasancewarta mutum me tsananin karantar yanayin halayyar dan adam ya sanya kai tsaye ta gane cewar kidnapping ne sukayi, Duka sauran yan tafiyar nasu babu wanda ya lura da hakan sai ita kadai, "xcuse mee!"
Ta na fadar hakan tayi kamar mantuwa tayi ta jikin motar tawuce tare da manna musu wani abu dake hannunta, A kuma daidai lokacin suka tayar da motar suna barin wurin.
Ciki ta koma tana sake gyara zaman jakarta da daidaita nikaf dinta da taji kamar yana kokarin sarkafe numfashinta.
Kano
National Police Headquarters.
_Criminal Investigation Department (CID
Inspector kamal ne dake tsaye yaci gaba da kwararo bayanai yana mai nuni da welpaper screen din.
Hoton wani farin wani dattijone ne na'urar ta haske. Cikin tsananin sanin makamar aikinsa yaci gaba da fadin.
"wannan al'amari ba abinda za'aji ai shiru bane, tunda harya cutar da daruruwan mutane ta hanyar amfani da karfin iko hakan babban zunubi ne yallabai!. Be kamata mutum irin wannan yaci gaba da shakar yantacciyar iskar duniya ba.
Kamata yayi ace zuwa yanzu numfashinsa baya tare da gangar jikinsa, ko ace yana cen prison yana girbar abinda ya shuka! Yana yin duk wasu haramtattun harkalloli kwatsam kuma ace ya zama babban commondi of soldier's?"
Wata iskar bacin rai ya fesar tare da dora hannuwansa biyu saman desk din dake gaban yallabai din yaci gaba da fadin. " A koda yaushe damar shan iska muke basu!, shine babban kuskuren da mukeyi yallaabai a koda yaushe tazarar itace zarrarsu a garemu"
"Uyummmmm na fahimceka kamaal baka sanshi bane shiyasa mutum ne shi me matukar hadari"
Wani irin tirjiya yayi tare da yowa baya ya fuskanci yallabai din kafin kuma ya saki murmushin takaici ya furta.
"Kace bansan waye shi ba? Shiba Aihuwarsa akay kamar sauran mutane ba? Aiba daga sama ya fado ba, ka sani kotu zata iya amince da maganarka, doka zata iya amincewa. Amma Allah bazai taba amimcewaba! Idan kana ganin yafi karfin hukuma to kasani Allah ne zai iya hukunta duk wani mugu dake mulkar bayinsa. A yayinda shirun Al'umma zai zamto tsawa hawayensu yayi ambaliya tamkar tekun maliya. Ko kuma tarin radadin dake bisne a cikin zuciyar kowanne bawa ya koma makamin da zai ceci rayuwaesu Allah ne kadai zai iya hukuntawa Allah daya"
Ya fada a tsawace tare da bugar desk din yana barin dakin taron. Baki daya da kallo suka bishi officer Hassan Arwai ne ya dubi yallabai tare da fadin.
"Zafin kansa yayi yawa! Jin kansa yake a matsayin da bai kawo ba, haka daukar kansa take a matsayin zarrarsa"
"Stop!!! "
Yalaabai ya fadi domin yanzu bai bukatar su sake hargitsa tunaninsa.
"Pls every body get out"
Ya sake fadi a tsawace tare da dafe kansa da hannuwansa.
Kai tsaye gidansa ya nufa zuciyarsa na masa tsananin zafi da suya, Allah ne kawai ya kawo shi gida lafiya bawai don iyawarsa, dan yadda ya bama motar wuta kawai idan ka kalla ka tsoratama.
Ganin wata siena fake a kofar gidan shine ya sanya shi tunanin su waye kuma domin shidai yasan baya da wanda zai kawo masa ziyara, tunda danginsa sun jefar dashi gudun kada susha wahalar dawainiyarsa, Allah ne kadai ya raya shi in banda haka da bai kawo wannan lokacin ba.
Ruwa iska sanyi tsananin rana duk akansa suke karewa baya da matsugunni duk inda ya raba korarsa ake kamad kare koma yace annoba. Ijiyar zuciya ya sauke domin sammm bama ya bukayar ya ringa yawan tunano rayuwanshi na baya domin hakan tafarfasa zuciyarsa yake, kirjinsa kuma ya masa nauyin da yake gaza sarrafa kansa da fushinsa idan har beyi fashe².
A nutse ya bude motarsa ya fito yana fitowa baban mariya na fitowa daga cikin gidan kamaal din, hannunsa dauke sa tray.
Tsaiwa yayi ya fasa tunkarar gidan. Fuskansa da fara'a ya karaso har ganan kamaal din yana cewa.
"Yan uwanka ne na rano da yan gwarzo suka zo wajen ka" ya fadi yana kama hannun kamal din. "Yan uwa dai baba?, ni kuma a ina nake da yan uwa ai bana da kowa....mebi mistake sukayi ne bara na karasa daga ciki"
Ya fadi yana yin gaba.
"Harda Malam Haruna rano shima baka san shiba?" Baban mariya ya jeho masa tambayar data sanya kamal tsayawa cakk da kafafunsa. Wata zubar bacin rai na karyo masa, wato sai yanzune ma suka dashi a jerin yan uwa, kenan raina masa hankali sukai tunda har suka san inda yake zaune kai tsaye.
Cikin bacin rai yayi cikin gidan yana fito da yar karamar pistol din dake sakale a jikinsa, da karfin gaske ya tura kofar parlon wanda hakan ya sanya jama'ar dake zaune a parlon firgira.
Ganin wani matashin bazaraten saurayi tsaye a gabansu me tsananin kamanni da Suraj din sune ya sanya jikin wasu fara rawa. Da sassarfa wani dattijo ya karaso inda yake tsaye da nufin tabashi, wani irin jaaaa baya yayi cikin fushi ua furta. "Me kuke nema?wannan yaron da kuka jefar kuka guda dan kimanin shekaru goma ko wa!?, to ku sani inma shi kuke nema wannan ya dade da mutuwa, wannan dake gaban ku ba kowa bane niba kowa bane face bawan Allah wanda ya raya shi bisa tafarkinsa na gaskiya da kuma bashi kariyarsa acikin duka lamuransa don haka I say get out in my house tun kafin ku fasata wannan bawan allah"
Hawaye sosae suke suna rokonshi daya yafe musu sunsan sun aikata kuskure amma ya taimaka ya yafe musu, wani da suke kira da kawu ilu ne ya rarrafo gabansa cikin kuka ya shiga fadin.
"Tabbas munyi kuskure!, munyi kuskure kamaludden amma ka yafe mana kowa a lokacin ya guji daukar kane sabo da gudun dawainiyarka, duba da tsananin azabar da talakan kasa yake sha. A namu banzan tunanin gani muke ba zamu iya ba kaidin zaka zame mana nauyin da bazamu iya dauka ba!, a jikin takarda naga hotonka ina gani na nemo shamsu nace ya karanta min. Kamal rano kadai daya ambata ya bani tabbacin kamal dinmu ne kamal din da kanina yamutu yabar min!, kamal din da talauci yasa na gaza daukarsa a matsayin.........
Sai kuma wani irin kuka ya sarke shi janye kafarsa Jamal yayi da karfi tare da daka musu tsawa a karo na biyu yana fadin su fuce may a gida.
Wani kyakykyawan bahagon mari baban mariya ya dauke fuskar kamal dashi. Cikin fushi ya furta " Idan har ba karya kamin ba da kace a matsayin mahaifi kake kallona to ban yarda ka kare furta ko wacce iriyar magana wa danginka ba inhar bame dadi bace! Kana ka basu masauki me kyau naji kuma wani abu ya biyo baya kaga yadda asalin fusata take.
Fuuuuuuuu ya fice a parlon yabar kamal da hannu rike da fuska, sunkuyar da kanshi yayi domin hakan da baban mariya yayi na masa nuni da cewar tabbas beyi rashin mahaifi ba Wani irin girma da kuma darajar baban mariyane ya sake dabaibaye kamal. Domin a wannan zamani samun wanda zaiga kana aikata ba daidaiba ya tsawatar ma kanyi matukar wuya. Wani idan yaga kana aikata ba daidai memakon ya hana ka saima ya sake ingizaka da ingiza fushinka
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 39&40
# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration
🤍🔥✅
_______________________
Suuuuuuu suuuuuuu suuuu haka Lafiyayyun baƙaƙe motocin ke sura uban speed saman shimfiɗeɗiyar kwaltar. Tun daga anguwar Victoria island har zuwa fitacciyar anguwar banan island duk inda suka gifta zakaga basu hanya ake, domin kuwa kallo ɗaya zaka ma motocin da irin uban speed ɗin da suke bayarwa ka gane bana lafiya bane.
Cikin dan kankanin loƙaci sai gasu a gaban wani haɗaɗɗen plat house ,sannan kai tsaye suka fada danna hancinan motocinsu gidan wanda uban security'n suka wangale musu ƙaton get ɗin. dukka motocin suka shige ciki suka kuma samu wajena gurbin da aka tanada don ajjiye motoci suka faka. Kafin mutanen dake ciki sanye da baqaqen suit suka firfito suna bada tsaro wa na cikin motar. dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya gaba ɗayansu manyan bindigune a hannayensu.Cikin da zafin nama ɗaya daga cikin security'n ya isa ga motar dake tsaye dukka qofofinta a kulle yayi knocking baqin glass din motar tare da ma arms magana, yar ƙaramar magana sukayi kafin ya bar wajen.
sannan ya sake zagayawa right side na seat ɗin bayan motar ya buɗe qofar,yaja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin motar fitowa.
Saida yaja wasu ƴan sakanni kafin kyawawan sawayensa su fara fitowa, sai daukar idanu suke saboda tsananin kyau da tsafta, Saida ya sake ɗaukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara yatsun hannunsa ya sanya yana qoqarin cire wayar dake maqale a kunnensa,kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati a dinke tsaf babu alamun fara'a ko kadan tattare da ita.
Kyakkyawar soft fatar jikin san nan me murjajjen jiki da babu wani waje da yake a rame ko ya nuna alamun qashi,saima kakkarfan siffarsa da cikakken zatinsa daya nuna kansa da kansa ta jikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na combat Reva net. Sai wani haɗaɗɗen luxury Rolex watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Lallausan sumar nan kuwa da tasha uban gyara daure a kasan ƙeyarsa ya kwanta yayi luf luf saboda wani irin gyara na musamman da akayi masa,
Baqar sumar da baƙaƙen kayan dake jikinsa suka haɗu suka sake haskaka farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Shade ɗin daya toshe idansa dashi shine ya sake saka kyawawan qwayar idanunsa dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali,idanun dake cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata. Sai nose mark daya sanya wanda kai baka isa gane waye shi ba.
Wani irin daddaɗan ƙamshine ke tashi a jikinsa irin me ɗaukar hankalin nan. Ko yaya ka qara taqi kaɗan kusa dashi kana iya shaqar daddaɗan ƙamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaƙeshi ya kuma ƙara kwarjini ga ma'abocin ƙamshin.
Kyawawan fararen hannuwansa zube cikin aljihun tsadaddun riga da wandon dake sanye a jikinsa,Sake gyara zaman bindugunsu security'n sa suka sake yi a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Wata zazzafar Iska ya ɗan furzar kafin ya taka zuwa gaba. Arms tare da wasu mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi. Cikin takun cikakken gwarzon namiji yake takunsa har zuwa cikin ƙayataccen Royal parloun da yake ƙawace da wasu irin Italian Wikipedia chair. Daga nan duka bodygourd nashi suka tsaya a parloun shida arms ne kaɗai suka nufi entrance door ɗin da sai sadasu da duka sassan gidan.
A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce 5 mint ba ya tsaya a parlou 3. Saida yayi scanning card a bakin qofar tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga.
Palace tenpor room ɗin suka nufa kai tsaye Wanda ko ina na gidan Gellary odyssey ke walainiya tako ta ina.
Saida ya buɗe deep freeze ɗin dake makale da dab shiga asalin living room ɗin ya ɗauka kwallar wine ɗin sa. Nan ma Saida Gellary odyssey dpy ɗin yayi on locking up nashi kana ya suka shige Mahaukacin katon parloun da ma'adanar cctv footage ɗinsa yake. Wani irin matakan tsaron na'urori ne kawai ke magana a wurin.
Tanbuwal da tun da aka jeho hi aka garkamesa jiya be kuma sake jin motsi ba sai yanzu. Da wani irin sauri ya sanya hannunsa yana kare Mahaukacin hasken daya kusan ɗauke ganinsa, jikinsa rawa ya fara na tsabar azabar yunwar dake kwakular cikin sa.
Zaune yakai kan Chiar silinder caution ɗin dake facing da wannan mutumin. Ƙafarsa ya sanya tare da mirza ƙafar tanbuwal babu shiri ya saki wata ƙarar azaba cikin tsananin wahala ya furta.
"Pls kuɗin su waye ku? Me kuke nema daga gareni?, Kuɗi!?, Suna?, Mulki?, Ko kuwa ƙarfin Iko kuke da buƙata?"
Ya faɗa cikin muryan jigatuwa da wahala.
Shiru babu alamun amsa hakan ya sanya shi sake faɗin "please let me know waye kai?"
”Makwamishin guba! Mashekin rayuka matunzirin ruhi. Sannan kuma mai kare mabuƙata! Ni dabaibaiyi ne me harɗe duk kan wani azzalumi na kaishi har kasa ÆK”
Ya furta a fusace tare da kwance ɗaurin da akama tanbuwal ɗin. Wani irin mugun shock ne ya ziyarci ƙwaƙwalwar tanbuwal, AK AK AK haka sunan shi ya shiga masa amsa kuwa a tsakar kansa. Cikin Wata iriyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 18