Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
anguwar yayo Ahankali ya soma buɗe lumsassun Idanunsa da har yanxu suke cike da barci, santala santalan fararen sawayensa ya fara zubowa kan tattausan carpet ɗin dake gabansa. A nutse kuma ya miƙe yana nufar haɗaɗɗen bathroom nashi, shower ya sakamar kansa sosai ruwan ya dake shi, kana ya tara ruwa masu ɗumi da daɗin ƙamshi a cikin bathtub,Wanda gefe da bathtub ɗin akwai drawers masu yawa da wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower tana wani fidda wani irin ƙyalli, kamar ba'a taɓa amfani da shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu ɗaukar hankali sosai. Yaja tsahon loƙaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe chocolate Colo mai azabar taushin tsiya dan har wani wani maski-maski take yi tsabar taushi da kuma laushinta,da mini towel ɗin dake a hannunsa ya shiga tsane jiƙaƙƙiyar tulin sumar dake kansa mai tsaho, Fuskar nan a tsuƙe Samm babu alamun rahama a cikinta. Gaban ƙaton mirror'nsa ya nufa cikin tafiyar jin kai da kuma isa. Hand dryer dake saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da himilin sumarsa da tafi kama data ƴan India, lotion ɗin dake jere saman mirror'n ya shiga shafa wa jikinsa sama sama. Saida ya mulke jikinsa da spray's nashi masu azabar ƙamshi da tsada, kafin ya nufi gaban wardrobe nashi data kusan cinye bango guda. Tsabbb yayi shirinsa cikin wasu haɗaɗɗaun track suit baƙaƙe, sai glass ɗin daya sakaye idanunsa a ciki tare da facemask ƴar gadon, phone's nashi kaɗai ya diba yana nufar main Parlour, cikin takun cikakkun mazan dake ji da kansu. Kafin ya fito tuni su milse sun gama shirya komai daya dace, jin takun tafiyarsa da baya taɓa ɓuyane ya sanya su risinar da kansu ƙasa, cikin girmamawa suka haɗe baki wajen furta "Good morning Boss!" Saida yaja wasu luƙuta kafin ya amsa "kuna lafiya" iyaka saman laɓbansa. "So boring Boss" Wannan karon kammm da ka kawai ya amsa su, yana zama kan ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun dake kewaye da dinin Area ɗin, A ƙasaitance yaja wata haɗaɗɗiyar kwalba wine Wanda naga ansa with alcohol, zubawa yayi a glass cup ya farasha, bai wani shada yawa ba, yaja plantain chips ya fara cakuta kaɗan yaɗan taɓa ya tashi tare da wine ɗin ya koma kan caution ɗin parlourn ya kafa bakinsa ya fara sha inda saida Ya shanye Kafin ya ajiye bottle ɗin. Laptop ya janyo tare da buɗe mukullan sirrin ya shiga sarrafa abarsa cikin kwarewa. A rikice a kuma ɗimauce Rooney ya faɗo ɗakin cikin tashin hankali ya nufi ogan nasu kai tsaye, system ɗin dake hannunsa ya dire gaban uban gidan nasu. A tare miles axton lani da kuma Vincent suka ja baya suna toshe bakunansu, hankali tashe suka juyo baki ɗaya da nufin Boss ya kalla laptop ɗin, amma ga mamakinsu abinda suka kalla ɗin ya tada musu hankali shine Boss ɗin nasu yake kalla hankali kwance tamkar babu abinda ke damunsa ko kuma ya girgiza shi. A baɗini kuwa wata iriyar tsuma namomin jikinsa suka ɗauka.bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kishin kiɗe jikin kujerar kansa a sama kaɗan, Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima fahimtci kamai dangane da hakan ba, Yaja kusan 10 mint kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe rinannun idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau sai dai a nutsensa yake Samm babu alamun firgicewa a tare dashi,Sudai baki ɗaya sun gaza samun Nutsuwa sai kai da koma suke famar yi a cikin parlourn, suna a cikin wannan alhinin ne kuma get man na gidan ya faɗo parlourn against. "Boss da akwai matsala" Wani irin rumtse idanunsa yayi a duniya kalma mafi muni daya tsani ji itace kalmar yaji an ambaci matsala, ya tsani jin kalmar andaɗe da fice wannan babin, don haka ya kalli get man ɗin tare da ɗunkule hannunsa tamkar wanda zai kai naushi, sai kuma ya kaima iska naushin, yana fesar da wani zazzafan Numfashi, loƙaci kaɗan kamanninsa suka sanja jikinsa ya shiga rawa kana ganinsa zaka san he is not on his mood,musamman yadda yanayin jikinsa ya sanja tare da wani irin tsuma. Cigarettes ɗin dake jere gabansa ya ɗauka a zuciye da sauri Vincent yazo gaban sa tare da kunna masa lighter ya fara zuƙarta a haukace, cikin ƙankanin loƙaci ya har gitsa parlourn da hayaƙin cigarette. Saida zuƙe wajen kara biyar kafin yaji zuciyarsa ta ɗan risina, cikin hosky voice nashi ya furta "A tura saƙon kai tsaye!, Vincent maza a nemo mana biza daga nan zuwa yamma" "An gama Boss" Suma suka haɗe baki wajen faɗar hakan suna fita daga parlourn baki ɗaynsu, Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga parlourn ya nufi bedroom ɗinsa. Zaune yakai saman lafiyayyan gadonsa          Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane Abubuwane kawai suke masa kai-komo a rai da suka wayi gari dasu. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba, domin zai iya cewa kusan a haka ya rayu, Amma na yau ɗin sai yafi ƙona zuciyar sa fiye da koda yaushe,dan duk sunzo masa a bazata ne. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba. Goran ruwan dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na ba adadi yana sake nutsar da kansa. Sosai abubuwa masu yawan gaske suka shiga ƙoƙarin zeroying Brain nashi. Tamkar kuma wanda aka zabura ya miƙe aɗan zafafe yana yin gaban ƙofan Glass ɗin dake a shafe da Pics manya na emeji me hoton lion, babbar yatsar hannunsa ya sanya a take wurin dake a shafe yayi On tamprint na yatsunsa, zuuuuuuu wata haɗaɗɗiyar ultra door ta baiyana. Wasu manyan Computers ne A ɗakin dasu jojjone ta ko wacce kusurwa dake ɓangaren, akan wani ƙayatacce dogon table saikuma macbook akan wani dogon lumtsatsen kujera, Zama cikin hanzari tare da ɗaukar MacBook ɗin dake kan kujerar, buɗewa yayi yafara aiki cikin ƙwarewarsa da kuma baiwar iya sarrafa ko wanne abu, yakai kusan 40min yana danne danne, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya tashi yana barin ɗakin da yafi kama dana bincike. Yana fitowa daga wannan ɗakin ya ciro iphone XR ɗin sa, NO na Vincent yayi dialing NO In, cikin ƙanƙanin loƙaci daga ɗaya ɓangaren ya cira wayar yana faɗin "Boss" "Get ready to go out operations!" Da wannan ƙasaitar nashi yayi maganar yana zare farar Morocco ta mazan dake jikinsa, cikin sauri sauri ya shirya kansa cikin straight leg trim trouser sai black Versace greco hoodie, ƙafafunsa sanye cikin wasu haɗaɗɗaun black hermes cover shoe, sai hannunshi sanye cikin wasu haɗaɗɗun safan hannu, ga kuma facemask ɗin dake saman fuskarsa dake saye cikin sun glasses ɓaki wuliƙ dashi. Yana fitowa coumpaund ɗin tuni wannan samudawan sukayi shiri na musamman sun ɗane cikin rantsatstun baƙaƙen motocin su. Suna ganinsa suka hau fito da shewa suna faɗin "BOSS! BOSS!! BOSS!!!" Cikin wani irin salo da ƙwarewa Miles ya yayi tsalle ya diro yana shirin buɗewa Boss In nasu car, hannunsa dake a rufe ruff ya ɗaga masa yana mashi nuni da power bike ride ɗin da zai hau, sara masa yayi yana komawa cikin motar, shi kuma cikin wani irin taku ya nufi power bike ɗin tare da daura hannunsa akan key na machine ɗin, wani irin tsalle yayi cikin salon daya zam ɗabi'arsa ya haye saman machine ɗin, tare da masa key wani irin kuka yayi machine ɗin ya ɗauka. Kasancewar shine a gaba ya sake daidaita machine ɗin Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama ƙaramin yatsansa ya fara musu wata alamar dasu kaɗai suka san ma'anar kayansu. Suna gama fashimtar haka yaja machine ɗin da wani irin azababben gudu ya fita a gidan baki ɗaya, suuuuuu motocin suma suka rufa masa baya Sosai motocin ke sheƙ uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai ƙara ƙainarsu, Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauƙa suke gefen hanya domin basu fili, ganin yadda suke zuga uban gudu na tashin hankali, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Kai tsaye Lekki suka nufa daidai wani mahaukacin ƙaton luzary suka kutsa kansu, tuni jami'an tsaron gidan suka soma sakar musu wata. Wani irin sakin kan machine ɗin yayi tare da Ciro wasu bindigogi guda biyu kirar berreta M9, tsalle ɗaya yayi ya diro akan power bike ɗin ya fara tafiya kamar irin fusataccen zakin nan, Saida yayi pulling trigger Kafin cikin wani ƙayatacce salo ya soma harba bindigar. A gigice Governor Ibrahim Khaleel Nasara dake zaune irishe irishe acikin mahaukacin parlourn sa yayi wani tsalle kamar mage ya haye saman lumtsememiyar kujerar jikinsa na kerma, minister Zubairu tanbuwal kuwa rasa ma yadda zai yi yayi sai kawai yayi knell down a tsakar parlourn. Acen coumpaund na gidan kuwa Sosae jami'an tsaron suke neman gagararsu su, tuni AK ya fusata kafin kace mene saiga wannan kattin jami'an a ƙasa shi kaɗai ya kutsa kansa cikin ƙaton parlourn, duk wani lungu da saƙo dazai shige saiya haɗu da jami'ai haka yake harbesu. Harse daya danganta kansa da rantsatstsen parlourn minister'n. Fuskarnan yawa kunu haka ya tisa ƙewarsu su duka biyun. Bayan na jakin da suka sha. Tuni suka bama wurin iska suna barin cikin anguwar, suna barin unguwar manyan sojoji da jami'an tsaro harsun ƙaraso, hakan yasa suma jami'an tsaron a fusace suka mara musu baya, nan fa aka shiga fafatawa tsakanin ƴan ta'addar da kuma jami'an tsaro, suna dab dacim musu suka suka saki hayaƙi tuni wurin ya gauraye dama titin baki ɗaya suka harba motocin su tamkar walƙiya haka suka ɓacema jami'an Nan.        Cikin wani mugun jin haushi Ajmaal ya taka birki tare da jan wani mugun tsaƙi tare da cije saman laɓbansa.        Rai ɓace suma sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. "AK!" Wani zazzafan numfashi ajmaal yaja tare da komawa cikin motarsa yana yin reverse, a 370 yaja motar tamkar wanda zai tashi sama. *ZAMANI TV* "MEERAH! MEERAH!! MEERAH!!!" Sunan da suke ta famar ƙira kenan tare da juyi da matashiyar budurwar a tsaƙiyarsu. Ita kuwa wannan matashiyar da suke ƙira da MEERAH, murmushi kawai take saki baƙar doguwar riga ce a jikinta wadda ta yane kanta da baƙin mayafin doguwar rigar sosae tayi wani irin fitinannen ƙyau cikin shigar. "MEERAH ABDULLAHI GWANI!, ana son ganin ki a sashen MD" Aka faɗa daga cenñnn ɗan nesa dasu. Ahanzarce wannan matashiyar budurwar da zatayi irin shekaru sha taran nan, ta juyo tare da nufar office ɗin MD ɗin harda ƴar sassarfarta. Da sallama ta shiga cikin fuska kaɗan kadaran kada han, bakinsa ya baje ba ki ɗaya yana amsa sallamar nata, "Stay here" Ya faɗi cikin ɗan saurin bakin da yake da, zama tayi bayan ta gaida shi, amsata yayi sauri sauri kafin kai tsaye ya shiga rattaɓo mata bayanai. "Amm MEERAH aduk faɗin wannan tasha tamu kusan zan iya bugar kirgi wajen faɗin kece haskenmu, kana Nasarar mu, ɗaukakarmu, yanxu nake samun labarai daga majiya me ƙarbi kan cewa yanzu yanxu wannan babban criminal ɗin ya ƙwamishe gwamna da kuma ministan gida!, SO shine nake son ki haskaka ki faɗaɗa ki ninki maganganun ta yacce wannan tasha tamu zata ƙarayin popular fiye da da, duba da cewa duk wani abu daya danganci wannan babban me laifin son shi mutane suke kamar hauka. Tuntuni nake son samun ɗan firit news akansa ko yayane, saidai sammm babu wata hanya to yanxu ga dama ta samu mezai hana a yanxu kafin wasu gidan jaridun labarain suje musu ke ki fara fitarwa daga wannan tasha tamu ta ZAMANI TV!" (Ɗan azabar son kuɗi dason suna) Ta faɗa a cikin ranta Jin tayi shiru ne yasan MD dan takar teburin dake gabanta cikin marairaice murya yace. "Wannan labari zai jawo hankalin Mutane zuwa wannan tashar tamu uwa uba yanda kowa ke ƙage dason jin sabon News daga AK EAGLE babban ɗan ta'addar da duk duniya sunansa ya kewa ye ko ina" "Pls MD naji!, naji!! Naji!!!" Suna kawai kalaman data furta cikin ƙosawa dajin harmutsatsan zancen MD ɗin. A take aka tattaro duk wasu ƙananun ma'aikata dama manya, cikin 5 mints kowa ya gama halarta a inda ake gudanar da shirin a ɗaki na musamman. Dama tuni Md ya bata doguwar takardar da duk wasu maganganun suka ƙunsa. Murya ta gyara bayan ta maƙala headphone tare da sanya ƴar ƙaramar loudspeaker a bakin ta, Cikin zaƙin Muryarta sautin maganarta ya fara fita kamar haka cikin amsa kuwwa. "_Assalamu alaikum masoya barkanmu da kasancewa damu ayau safiyar juma'a, wacce akema laƙabi da juma'atu babbar rana , karku manta kuna tare da tauraruwar tasharku mai farin Jini wato ZAMANI TV!, Wanda muke tafe muku da zazzafan labari akan wannan babban criminal ɗin nan wato EAGLE, wannan Ni! MEERAH ABDULLAHI GWANI Ni ce jagoranci shirin. A yau safiyar juma'a mun tashi ne da alhinin labarin ƙwamishe governor da kuma ministan gida, da wannan tantirin ɗan ƙunar ɓakar waker ɗan. Ta'adda wato AK EAGLE yayi wanda ahar kullum tazara kaɗan ce tsakanin sa da jami'an tsaro. Bayan karkashe masu tsaron gidan gwamnatin, shin ku a tunaninku miye wannan criminal ɗin yake nufi ne?, yana nufin yafi ƙarfin jami'ainmu kenan, domin dai kunsa tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi YA FECE kamar yadda ya saba dai, kamar kwanaki da labaransa suka game media kan ta'adda cin ɗaya shiga cikin babban hotel ɗin yayi fashin sa ya fice salin alin. Masha yi, maci amanar ƙasa ɗan ta'adda, We want an end to oppression💪. Musaso a kawo ƙarshen zalunci, cin amana, ya kamata jami'anmu su farka daga nannauyar barcin daya ɗaukesu kodan sharen fa gen da wannan babban criminal ɗin ya soma ɗauki ɗai ɗai a cikin al'umma, donjin ra'ayoyin ku zaku iya na ƙara faɗa We want an end to oppression💪 tuntuɓarmu akan wannan number 081----------- ko kuma shafin mu na Instagram, Facebook, dadai sauran tasho shinmu a gimtse 🫰 " Tana kammala shirin ta miƙe jiki a mace tare da barin ɗakin baki ɗaya, Tafi su su majeedah dasu Sairah ɗauka da shewa shi kuwa me girma MD sai faman washe baƙinsa yake domin dai yasan wannan karon zasu shahara, Daga cikin garin Lagos kuwa harda ma ƙetare a take mutane daban daban suka shiga turo saƙonnin jinjina da ƙara buɗaɗama jami'ai hanya, na suna tare da su 100 percent. Kamar yadda al'umma suka saurari wannan labaran na yau haka ma babbar headquarters ta Lagos ta saurara, Cikin ƙanƙan da da ido mr.presiden ya ɗago kansa tare da duban Ajmaal, ƙasss masa da ido, nan suka suka shiga tattauanawa akan wannan batu me girma, cikin ƙankanin loƙaci kuwa duk inda ka gaza labarin KIDNAPPING ɗin ake, saiga ZAMANI TV a sama tana shawagi. A gimtse 🫰 To ai shikenan kooooo ⁉️🚯 Sai na ce sai mun haɗe a next page kanan. Laaaaaa na manta shegun sunyi bannet numbern WhatsApp nawa nefa Shi yasa kuka jini ɗifffff taku ce *AMMEY LAYLERH ✍️* *🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 5&6 🤍🔥✅ " Ita yarinyar da tai labaran lallai ina son sanin wacece ita" Ya faɗa cikin dakakken sauti tare da ɗaukar kwalbar Win yana kafata a baki, bai dire kwalbar ba Saida ya shanye tasss. "Sunanta MARYAM ABDULLAHI GWANI wacce akafi saninta da MEERAH, haifaffiyar garin nan ce suna zaune a unguwar GATAN KOWA. Mahaifinta malami ne sananne wanda daƙyar ya bar yabar yarinyar ta fara aiki da gidan jaridar, acewar aure shine kaɗai rufin asirin dukk wata mace ta gari, Md ɗin ne yaje har gida ya roƙi alfarmar malam Abdullahi don ganin loƙacin da suka je pratical cikin tashar, bayan sun gabatar da pratical ɗinne yarinyar ta ringa samun viaw na jama'a, hakan ya haukata Md, shine dalilin da yasa yaje har wurin mahaifinta neman alfarma ta fara aiki da tashar, nashi kona ɗan loƙaci ne.yana da mata uku tayi karatun ta tun daga kan primary nata har zuwa high school ɗinta ji duka anan cikin garin Lagos, ta fara aiki da gidan jaridar zamani tv watanni shida da suka wuce, tana da tsayayyen saurayin ta wanda za'a yi bikin su nan ba da jimawa, tun ranar da rahotannin ya fita na bibiyi ita kanta yarinyar, don nasan dole zaka buƙaci sanin wacece ita, yanxu haka md ɗin yana ƙoƙarin buga jaridu akan hakan, umarnin ka kaɗai muke jira wajen daƙile faruwar hakan, A yadda nayi kyakkyawarn bincike game da Md ɗin yana da masifar son kuɗin masifa, shi ba ruwansa da inganci abu burinsa kawai kuɗi ɗaukaka sune kaɗai yaren daya fi fashimta" Axton ne duka me wannan maganar kuma tun a ranar da rahotannin suka fita yabibiyeta, harya samu cikakken tarihin ta. Saida ya kuma zuƙar cigarettes ɗin dake hannunsa, kafin ya ɗago rikitattun idonsa ya zuba su akan axton, shi yasa ahar kullum yake kuma alfahari dashi acikin yaran nasa, duk abinda ya kamata kafin yace shi kuma ya aikata. Miles ne ya kuma daidai ta nutsuwar sa cikin gurɓatacciyar hausar sa da baya fita ya furta. "Boss ni kuma bayan na bibiyi rahotannin ta na shiga duka kafofin sadarwarta, kamar yadda ta umarta tabbas tauraronta na haskawa a wannan tashar dama duniya baki ɗaya, duba da yadda take da tarin masoya tako ta ina hakan yasa cikin ƙanƙanin loƙaci wannan ruhotannin ya baza garin Lagos harma da ƙetare, a yadda ma na samu cikakken bayani daga cikin headquarters na A F S, aka bama shi MD ɗin bayanin dukkan abinda ya faru a safiyar juma'ar, kana Saida suka yi duba da yanda tauraron yarinyar yake haskawa kana sukayi amfani da hakan don son cika burinsu, zasuna amfani da ita ne kawai don..... Ɗaga masa hannun da Boss In nasu yayi ne ya sanya shi dakatawa, wani irin killet murmushin gefen baki ya saki tare da faɗin. "A barta taci gaba da buga wasan da dukkan alama zai yi armashi, zai kuma kawo nishaɗi, Nazari muke da ƙwaƙwalwa karku manta!, Sadaukai ne mu tamkar mafarauta!, ba'a taɓa nasarar yaƙi sai in da mayaƙa, don haka ina son a buga wannan game ɗin tare dani"    Wani mugun waro idanu sukayi suna bin boss in nasu da kallo Lallai Boss rigimarka yawa gare ta da ɗaukar abu me muhimmanci da rashin muhimmanci. Kai komai da zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo,in banda taryan Aradu da ka taya ma zakace a bari a buga jaridu akan ka, kana kace a barsu kana son buga wasa akan mutanen dake farautar rayuwarka. Sune kalaman da da axton ya shiga nanatasu cikin zuciyar. Tsammm ya miƙe cikin tafiyar nan na ƙasaita da kuma izzar da yake da yabar main Parlourn tare da nufar upstairs nashi, yana barin su da wasuwasai falll zuciyarsu. Shi kuma Boss In saman sa ya nufa zaune yakai gefen bed nashi tare, da janyo system nashi me ƙirar campanyn apple, engine machine ɗin sa ya jona tare da jan glass cup yana siyanyar coffee tare da fara dan sipping nashi a Ahankali, kana ya shiga wasu ƴan sarrafe sarrafe kafin ya janye ta tare da ɗaukar wani ɗan kit box,, buɗeta yayi a take wata ƙaramar waya ta bayyana irin nokia ɗin nan ta da. A take ya shiga loda Numbern daya gama haddace abarsa ya lodata tare da shiga ɓangaren messages, ya koma yana ajje wasu short mess tare da switch na wayar yana jefata cikin wannan kid box ɗin. *Zamani tv* Jikin MD har mazari yake wajen amsa saƙonnin dake ta famar shigo musu, tun a daren shekaranjiya da da suka bayyana rahotannin babban criminal ɗin, kamar daga sama kuma yaga wani ɗan short mess ya faɗa masa, cikin rawar takashi ya shiga cikin message ɗin, _ Amatsayina na babban masoyin wannan tasha ina so ayi fira dani da misalin 11:15Am na safiyar gobe tare da MEERAH ABDULLAHI GWANI🫨_ "Yesss!" MD ya faɗa da masifar ƙarfin daya sanya sauran ma'aikatan dake dab da Ofishin sa fitowa, dama abinda yake fata da kuma buri kenan ayi ta jan maganar wannan AK ɗin, gashi Alkhairuka suna ta samunsa a sanadiyar iyaka yaɗa labaran sa kawai. Loƙaci ɗaya tashar sa ta kara zama shahararriya kuma yasan duk ata sanadiyyar MEERAH ne. "Kai wannan ƴa kin zama Alkhairi na iyayenki sun iya farar haihuwar ƴar baiwa!" Haka dai Md yaci gaba da zabga surutunsa kafin yasa a ƙira masa mera ɗin. Zaune take gaban me girma Md wanda ya shiga koɗa ta da mata kirari kala daban daban, kafin ya shiga sanar mata da buƙatarsa na wannan bawan Allahn da yake son yin fira da ita. nooding kanta kawai ta yi tare da zuba masa ido tana binshi da wani irin kallo wanda kai tsaye zamu iya ƙiransa da najin haushi. Ganin ba haƙura zai yi bane ya sanya ta miƙewa dare da barin office ɗin, kai tsaye coumpaund na gidan jaridar ta nufa tare da barin gidan baki ɗaya. tana fita kuwa taci Sa'a ta haɗu da me napen, shigewa kawai tayi shi kuma yaja kanta ta kife saman cinyarta, tsananin ciwon kan da take ji na ƙara tsananta, "Hajiya ina muka nufa?" Ɗan adedeta sahun ya tambaye ta. "Daɗin kowa" ta bashi amsa ba tare da ta ɗago kanta ba, babu wata tafiya me zurfi sai gasu har sun ƙaraso, handbag ɗinta ta buɗe bayan ta fita tare da zaro dari biyar ta bashi, canjin ɗari da hamsin ya bata tace ya barshi tana faɗawa cikin gidan nasu. ________★★★________ Cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na campanyn Dior saddle Brook yafito brown se ɗaukar ido yake baƙaramun amsar jikinsa kayan suka yi ba, abinka da cikakken namiji me jini a jika da ɗan sassarfa yake saƙƙowa daga stair ɗin, Zazzaune ya samu su axton suna ƴar firan su , ganin sakkowa Boss In nasu ne ya sanya suka miƙe zumbur tare da rusunar da kansu. Kai tsaye motocinsu suka nufa suna mata key dake dama already

Chapter 2 of 18