kowa ya san labiba bata da mutunci kona miskana zarra.
Nan akaci gaba da shagalin biki kowa be tsinke da lamarin ba Saida Anne ta fito cikin wata rantsatstsiyar shigar farin less. Howowo zanso ku hango yadda Anne ke walainiya cikin danyen leshin data dautsa.
Mu kuwa muna can uwar ɗakan Anne wajajen lassar la'asr Aunty labiba ta shiga tare da aunty adawiyya da baby autar Hajiya umma suka shiga niki niki hannuwansu dauke da wasu shegun bags har guda uku. Badan kar ace na fiya kyauyanci ba dana rantse ban taba ganin kome kala da bags ɗin ba. Zama suka yi fuskar ko wannensu dauke da murmushi a fuskarsa.
"Amarya ya kamata ki sanjà shiga ga sabbin kayanki da Anne'nki ta sai miki na fitar biki su zaki sanya"
Ijiyar zuciya na ɗan sauke inajin yanayin bugun zuciyana ya sanjawa tare da cinkushewar yanayin dana tsinci kaina a ciki.
"Amma aunty adawiyya wannan shigan na jikina ma ai babu laifi nake ga, nifa bana gayyar kayan zafin nan!"
Meerah ta fadi tana miƙewa tsaye banɗakin cikin dakin ta shiga alwula ta dauro kamar yadda aunty labiba ta faɗa. Nan kowa ya shiga yin alwular muka gabatar da sallar la'asr. Bayan mun idar aunty baby ta shiga tsara min kwalliya a fuskana duk da banso hakan ba. Gashin kaina da shi kansa nasa gyaran na daban ne aunty baby tama wani irin style. Ta raba shi biyu ta kai har karshen ƙeyata wanda ya sauka har gadon bayana wasu shegun style ta shiga yi da gashin. Saida ta kammala kana ta sake nado shi da ribom's. Wata fitinanniyar riga da sket half bubu na wani shegen luxury catton less, irin me haɗe da jakar nan ta tamarmi sai mayafinsa. Wasu shegun barima me kama da diamond ta sanya min tare da zobenta da agogon hannu. Ya subhanallah a take wani irin kyalkyali ya shiga tashi a jikina. Ga wasu Mayun turarukan da ban taɓa jin koda irin ƙamshin su ta shige ɓarinsu a jikina. A take dakin ya ɗauki sowar kawayena jan hannuna aunty labiba tayi tana faɗin ALHAMDULILLAH sai gaban Anne da baffa har dama wanda basu so ganin wannan babban rana ba, namu ba irin nasu bane.
Ina sanyo kafata tun bai kai ga fitowa ba duk wata jama'a dake tsakar gidan suka zubo idanuwansu a kan bakin kunshin daya wani irin sake fidda kyawun kaɗana. Kwallace take kokarin zubo min ganin tabbas waɗan nan mutanen sun taru ne a yau domin ni, hannuna aunty labiba ta janyo tana karasa fiddo ni zuwa tsakar gidan. Wani irin tsitt duk hayaniyar data kacame gidan a ɗazun sukayi. Ko wanne idonsa na kaina, harda masu sake mitsirtsike idanuwansu.
Wata babbar guda Hajiya umma ta saki tana cira hannuwana sama tare da sake ranbada gudarta tana faɗin.
"ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! Yarinya tayi goshi Ubangiji ya baki zaman lafiya tabbatacciya a gidan aurenki MEERAH, Allah ya kare ki daga dukkan sharrin masu sharri. Allah ya tsoka ne idon makiya akan wannan auren da Allah ne ya hada shi, bawai mutum ba saidai Allah Wllh kuwa mutum din zaija da ikon Allah to bismilla!"
Duk wannan abin ciki daga murya Hajj umma tayi nan fa wasu suka sha jinin jikinsu domin kaff ya'yan baffa mata babu wanda yaba Anne ko gudun mawar nera biyar. A cewarsu a gudun mawa karin ƙarfin biki.
Nan marasa kunyar cikin su suka shiga amshe Hajj umma suna shiga tare da jeruwa da meerah ɗin aka fara buga photuna na garari. Babu kunya Anne ta rungume DIDI'ƊINTA aka musu photos da yawa. Nan manyan yayye maza ma suka shigo akaci gaba da hotunan Raiha ce nanuke da meerah duk inda ta yi cikin tata shigar na cotton less.
Nan fa gida ya sake ɗaukar hayaniyar data fi ta ko yaushe kawayena kuwa sunyi cannn ta bayan kewayen gidan sun kafa party tare da shan disko harda mardiyya da bama shiri, dake dama rashin shirin akan hayatuddeen ne saita sauke ta shigo ake shan shagalin da ita. Wajajen sallar magariba kawaye suka fara mitar basu ga ango yazo ba bare ayi zancen photo dake baby na tare dasu sai tace musu ai suma suna da party'n da suke yine da an daura auren shi yasa bai zoba.
OHO nidai bansan abinda ake ba domin ina cennn ɓangaren baffa wani zazzafan zazzabi ya rufe ni tun ina dauriya har Saida ya kaini ga kwanciya. Nan baffa kuwa ya sameni da nasiharsa na komai naga ni a lamarin aurena tabbacecce ne tun daga rabbi izzati, karna yadda nayi jayayya da hukuncin da Allah yay min. Kana karna taɓa butulcema zabinsa na zama mace mai tsananin haƙuri da biyayya a gidan aure na Insha Allah zanga sakamakon auren nan ko bayan babu ransa. Abinda ya sake sanyaya jikina kenan sai kaina ma ya soma sara min.
Ana idar da sallar magariba ƴan daukar amarya suka zo, tun kamin suzo nake wani irin kukan daya sanyaya jikin kowa dake gidan, kira nake Ni Wllh nama fasa wannan Auren dama ai banaso don karnama baffa musu ne ya sanya ni amincewa toni Wllh na fasa. Nan na tayar da hankalin Anne'na da baffa dama duk wani masoyina, wata irin nasihar dahar nabar duniya bazan taɓa mancewa ba Anne na tamin haka ma baga Hajiya umma ba, domin nasihace irin me ragargaza zuciya harma da ratsa gangar jiki. Nidai kuka na nake a haka har dangin ango suka zo tafiya dani.
Nan fa na ce bansan zance ba na rike hannun Anne na kakam ina risgar kuka.
"Ki sani wannan tafiyar itace mabuɗin bude abubuwa da yawa meerah! Bawai kuka nace kimin ba jarum taka yaka mata ki nuna, yanxu an dena kuka dan anyi aure. Bare ma ki sani naki auren yasha banban da saura, Ki nuna musu ke kibiyar ajali ce wacce sulke baya iya ratsata! Ki nuna musu kedin jinin da...........
Wata farar dattijuwoce tayi saurin damkar hannuna da nata lallausan hannun, wanda ya hanani karasa jin me Anne na take nufi a gaban da ɗin nan?, Motocin da baka ganin iyakarsu wanda tsadarsu kaɗai kan iya juyarma dame ƙaramar ƙwaƙwalwa kai. Cikin kuka nake don haka ban tantace ya kamanni da kalansu yake ba nadai san ban iya hangar iyakarsu. Kar kuce wai bana lura a ah ina lura da komai domin idan naji ana magana har wani sake leƙo da kaina nake. Da bismilla wannan matar ta sanya na shiga cikin wata narkakkiyar Toyota Highlander 2024/2025 bugun American.
Ido a rufe yake amma sanda kamshi da sanyin daya ratsa ko ina na jikina ne ya tilas tamin buɗe jajayen idona da sukaci kuka.kallo ɗaya nama motar na furta.
"Allah ya isanmu" na faɗa kasa kasa ɗan nasan da kukaden mu talakawan kasa aka siya wadan nan shegun motocin.
★SALMAN POV★
Sabo da tsabar farin cikin da yake a ciki jinsa yake tamkar an yimay bishara da gidan aljanna, wai yau shine ya mallaki meerah a matsayin matar sa shi kuwa me yafi wannan daɗi a duka cikin tarihin rayuwar sa.
"BABU!"
Ya fadi a fili lokacin da jerin abokan sa suka yo masa rajiyar angwaye. Haka ya kemashe idanunsa yace babu me shigar masa gida wai shi a matse yake don haka kowa ya kama gabansa. Nan fa suka shiga masa tsiya suna cewa zasu rama ne. Shi dai bai damu ba kansa ya mayar da get ɗin gidan ya rufe dan yasan zuwa yanzun kowa ya kama gabansa.
Har wani sassarfa yake haɗawa da ita wajen isa ga muradinsa meerah wacce kullum sai yayi mafarkinta suna sheka soyayyar su...
Jiki har mazari yake sanda ya ƙarasa shigowa palon gidan da yaji wasu shegen kujeru na alfarma. Da dai yaga saurin kamar bazai masa ba sai kawai ya kwasa da gudu sama kai bedroom ɗin daya tabbar da anan aka ajje masa amaryarsa ya tura.
Tana zaune cikin lullubinta har yanzun kuwa ga wani kamshi dake tashi daga jikinta, wata kakkaurar ijiyar zuciya ya saki yana jingina da jikin kofa domin gani yake kamar bazai zo yagan taba. Amma yanzu ALHAMDULILLAH hankalin sa ya kwanta. Ajje ledar da abokanan sa suka bashi yayi saman stool.
Zama yayi kusa da ita ba tare dako sallama ya mata ba, kai tsaye ya sanya hannunsa yana janye lullufin fuskarta zuwa kan shoulder nata.
Wani irin zabura yayi yanaja baya idanunsa na firfitowa wanda suka bayyanar da tsoronsu a fili muraran.
"Sury miya kawoki nan? Ina Meerah? Ina aka kai min Matana!?"
Sune tambayoyi uku a jere daya jefa mata lokaci daya bakinsa na rawa.
Wani irin murmushi sury ta saki tana gyara zamanta tare da duban shi kaɗan, sai kuma tadan shiga jujjuya idonta tana faɗin. "Uyummm wacce mata kuma kake da ita bayin Ni! SURAYYERH MOUSSA CANJI?"
A matuƙar tsawace Salman yace.
"Malama ina magana kina maida min amsa zaki buɗe baki ki bani ina matana? Ina meerah ɗina take?"
Wata shegiyar dariya sury ta sake saki irin ta rainin hankalin nan sai kuma ta mike tsaye tana ɗan juyi a gaban sa. "Yanzu dame wannan kodaddiyar yarinyar ta fini?, Kyau?, Dirin jiki?, Ko kuma wayewa eyeeee Salman?, Ka faɗamin ka bude baki kamin magana"
Wani irin kwafka yakai mata yana damkar wuyanta cikin tsantsan ɓacin rai ya furta .
"Tambaya ta karshe ina meerah ɗina take? Wllh³ sau uku kenan idan har baki bani amsana na rantse saina rabaki da numfashin ki sury"
Tari ta shiga da kakari da hannu ta masa alamar ya sauke ta zata yimay bayani. Sakinta yayi sai gata dagwash a kasan tiles ɗin dakin tari ta shiga yi tana rike wuyanta har saida numfashin ta ya ɗan dawo daidai. Cikin muryan daya jigata ta soma d fadin.
"Wllh ³ Dani aka daura maka aure ta hanyar sanja sunan meerah da Mommah tasa akayi a masallacin! Babu wanda yasan yanda akayi sai a wurin fadar sunan amarya kowa yaji bada meerah aka daura maba tunda Mommah ta rantse dama tace Wllh wannan auren naka da meerah ba a isa anyi saba sai idan bata numfashi, shine ta rufe bakin kowa har aka daura auren babu wand ya lura daba daidai aka daura ba Ata danginmu sai daga dangin amaryar ne suka farga, dama daurin auren biyune a lokaci guda Shine shine shineeeee...........
Ƙasa ƙara sawa tayi sakamakon uwar shaƙar da Salman ya mata, cikin huci da tafarfasar zuciya ya ke faɗin.
"Wllh yau saina kashe ki a wurin nan kafin naje ka uwar taki dama duk wani shegen daya wuce gaba wajen tarwatsa min farin ciki na, Wllh saina nuna muku kalar zallar haukar dana iya. Saina nuna muku Ni rikakken Mahaukacine inda akan meerah ne, saina tada hankalin kowa kafin naga shegen madaurin auren da idonsa baya gani na karasa lalata masa shi ta hanyar kwakule sa tunda baya da wani amfani"
Numfashin tane ya fara seezing amma duk da haka cikin karfin hali take faɗin ya tsaya ta karasa faɗa mar komai amma ina Salman yayi riga da yayi nisan da baya jin kira, domin baya cikin duniyar mutane ya tafiyar sa irin tasu duniyar ta zararru.
"Zaki faɗamin ina meerah take ne kai tsaye ko sai na karasa kashe ki na bisne gawarki a cikin wannan ɗakin?"
Cikin muryan da ko fita bayayi sosae ta shiga faɗin
"Tana wata duniyar ta daban! Ta maka nisan dako hange daga nesa ba zaka iya mata dan an riga an daura mata aure d dh daaaaa.......
sai kuma ta tafi gaba daya luuuuuuu tana zubewa a jikinsa yarabbbbb..
★_ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH 🙏 🙏!!! Anan zamu dakata a book One na wannan littafi mai suna MIKIYA sai kuma Allah ya haɗamu da masu rabo a book two_
★Tofa masu karatu yaya take ne?.
★Mike shirin faruwa?.
★Ina Meerah amarya?.
★Mi kalaman sury suke nufi?
★Shin da waye aka ɗaura wa meerah aure?
★Waye AK?
★Miye haɗin Nigeria da kuma KUWAIT ?
★Tofa wata daban su waye KAMAAL da kuwa MARRIYERTOU?
★Magana fa ake ta an kawo amarya meerah ta rikiɗe ta koma sury. Taya taya ya hakan ta faru?
★ANNE ZATA SAN ASALINTA?
★SHIN MIYA KAWO MADINAH?
_★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba'a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 bamu ko tsoma kafa ba a cikin masarautar Kuwait ko nace EMAAR's_
_★Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakude cikin wannan littafin_
_Duk zamu samu amsoshin wad'annan tambaya idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo k'arshen BOOK 1 NA MIKIYA Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin MIKIYA Naira 500 ne kacal babu yawa_
_Ga duk mai son biya zai tuntub'eni a wannan number_
👇
08104493215
Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin
👇
3206656358
Maryam Nasiru
First Bank
A turo shedar biya ta wannan number
08104493215
*_Kardai ku manta this one ma is not for free zaku Antayo darinku biyar ta Asusun banki na 3206656358 Maryam Nasiru first Bank ko katin mtn ta wannan number 08104493215 vip suma is 700 kamar yanda kuka sani masoya I no kuna bani goyon baya fiye da yanda nake tunani don haka ina ma kowa fatan Alkhairi don haka kar ku tsaya jiran ayi posting a sato muku na BABA NA BATI ku Antayo kuɗin ku karanta Cikin farin ciki da salama yanda kuke so sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na MIKIYA BA TARE DAKE BA HAJIYATA by AMMEY'N LAYLERH'NKU me ƘAUNAR KU FAKA FAKA_*
*Byeeeeeeeee my Re@l f@ns sai mun sake haduwa a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗinka Saida rabonka littafin MIKIYA ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo? Ko zamu dana rihazal ne na littafin SANYI YA HAIFI WUTA _PRINCE SAPWAN_ kenan ba hhhhhhhhh
A gimtse kawai baaaaa.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 18