result dinsu yafito doctor ahmad ne ya dubo musu, yayi murna sosai don sune gaba da kowa, haka su abba da ummi sunyi murna sosai, ansaka ranar da za a rintsar da su a skull din su, wato ranar lahadi, su baraka sun sanar da yan gd can, abban rumana yace ba sai sun xo ba sbd idan aka gama xa su taho gabaki daya, uban dawaki yace bari kawai muzu sbda mamin su tana son zuwa taga yadda za a rintsar dasu, don wannan ranar farin cikine sosao arayuwata da sauran yan uwana, ace su mamana sun zama likitoci dama ranar dana keson yaxo kenan, to shikenan yaya sai kunxo din , mami da taji batun rintsar dasu tayi murna tayi kuka, sbd ta tuna lokacin daza a rintsar da su ahmad ninta, kuma gashi tacika mawa ahmad dinta burinshi akan mama taxama likita allah nagode maka, umma itama tayi murna sosai haka ma su abdulrahman.
Wannan karan kowa da kowa zaije india, sakamakon samu likitoci guda uku acikin yan uwa. Can ko india suna murnar ganin yan uwansu, amm kuma suna gudun abunda zai faru.
TAKU UMMU RUMAN ( NUSNIM)JANI MERA TUMSE KHA HAI YE DIL ASHIQANAA💘🌺
[10:49AM, 1/24/2017] +234 806 448 1931: 🍒🍒🍒LABARIN NI'IMAH🍒🍒🍒4⃣0⃣Baraka tace tab wannan shine ana murna ana tashin hankali, mama tace bari kawai bansan yaza ayi ba, ni mami ma nafi ji wlh, bansan wani irin reaction xatayi ba kuma dole ne su hadu da ahmad rumana ta nunfasa kai wannan abu da ban al ajabi yake kuma gashi dole sai annu nashi amatsayinahi na babban likita, kunga ko dole su mami su ganahi wannan haka.
Suna cikin surutansu ummi tashigo tasa mesu me kukeyi kunsan zakuje min aike ko, ummi wlh muna tunanin zuwan su abban ahmad ne bamu san ya za akare ba, tace haka ne nima abun da muka tattauna da abbanku kenan, amma bayadda aka iya dole ne suga ahmad, sai dai fatan allah yasa komai dai yaxo cikin sauki ameen, abban rumana yasa angyara gdanshi sosai har da bangaren baki, gdan y kawayay tu, don yana murna kuma yana bikin ciki, amma kuma yana rokon allah daya kawo mishi sauki cikin lamuran.
Su nawawarat ne da nawwaran suka rugu aguje nawwarat ta biyo nawwaran abba yace lafiya kuke gudu haka, nawwaran yace abba ai nawwarat ce tace bazan mata allura ba idan na girma don nace zan zama doctor irin na yaya ahmad da su aunty rumana, shine take jin haushi abba yayi murmushi, su nawwarn manya wato kana so kazama kaman yayanka ko, eh abba ko baka so nazama ne indinga maka allura kaida ummi, mana so mana sai ka dage da karatu, nawwarat ta zumburo baki abba nifa, baka so inxama likita ne, haba bbyna ina so mana sai tayi murmushi, abba ni zan zama kamar aunty ni'imane tunda tafi su aunty rumana iya aiki gashi kayan likita yana mata kyau, bare in tafito tana dan takawan nan abba, abba ya tun tsure da dariya, kai nawwarat ashe haka kike da surutu, wato harkinsan yadda mama ke tafiya, ahmad dake bayan su duk yana jin su yana dariya, barema yadda nawwarat tafara tafiya irin na mama sai ya lumshe idonshi.
Nawwaran na juyawa yaga ahmad la abba ga yaya ahmad nan kamar yasan muna maganarshi ya karaso yaja kunnan su shida nawwarat kuncika shegen surutu, sannan ya gaishar da abba, yadai ahmad daga ina haka na ganka wujiga wujiga, wlh abba daga asibiti ne munyiwa wata mata aiki ne tasamu yan hudu, abba yace to madallah haka ake so, nawwaran da nawwarat duk sun bude ido da baki suna kallon yaya ahmad, kamar sun hada baki ya ahmad yankata kukayi ko, yayi dariya eh mana kama haka watarana zaka yanka mutum, nawwaran yace tab wlh bazan iyaba, nafasa zama doctorn tunda dama yanka mutane akeyi, abba yace amma anyi malalaci.
Yaune su uban dawaki zasu iso su aliyu baki har baka, da abdulrahman anshirya musu komai, su baraka sunje gidan amarya sumayya dauko nummbern site din su don ranar da aka bada ba suje ba, bayan sundawo daga karba ko wacce tafada gado, baraka tace oh yanxu munefa likitoci gashi anaji damu, rumana tace bari kawai ta dalilin yaya ahmad nace ni likita zanxama, amma tace gashiko kinxama, baraka tacewa mama nasan abbanki sai yayi kuka dan murna da kuma yaya ahmad, dasu mami, oh allah gashi nima adalilinki nazama likita mama, suka godewa allah.
Su uban dawaki sun karasoana ta murna su mama basu wani zauna ba domin su sami suyi hira dasu mami, sai zirga zirga sukeyi don saida suka gayyaci sharukhan da kajol da salmankhan wajan taya su murna, da aliya batan, shima ahmad baisamu yagana da bakin ba saboda gujiba gujiban aiki, su mama sunje sun sami doctor hibba da doctor adnan sai ahmad sunfada musu tarone sosai su sake jikinsu suyi abu mai kyau dayawan likitocin india za su hallara kubasu mamaki amatsayinku na yan nigeria, kuma daga kasarmu ma akwai wayanda aka gayyata manyan likitoci, kunga sai kudage, mama tace inasha allah we will do our best, yauwa good girls may god help you, hall yacika sosai kowa da kowa ya hallara wannan bikin yaya likitoci masu hazaka, shigowarsu ake jira, su mama ansha kaya ha daddu ga lapcout din nan fari tas sun axa asaman kayan su gashi sunsha glass din do fari, sunyi roling din farin gyale akai yayi masu kyau sosai komai nasu iri naya jira suke akirasu sushiga, su uban dawaki sun xuba ido suga ta ina zai hango maman shi, hakama mami, har tana goge yar kwallarta.
TAKU UMMU RUMAN( NUSNIM) (08064481931) BARI BAHAT KUSHI NI'IMAH💘🌺
[10:50AM, 1/24/2017] +234 806 448 1931: 🍒🍒🍒LABARIN NI'IMAH🍒🍒🍒4⃣1⃣Suka kara so ciki su mama ne agaba bayan sun zauna sai gasu doctor hibba da doctor adnan, sannan doctor ahmad, mami ne tayi saurin taba abban ahmad duba can kagani bayan wancan mutumin kamar na ahmad din mu wlh, sai dai kice mekama dashi amma ahmad ba mutumin daya dade da rasuwa, mami sai tunani kawai azuciyarta, wata bangaren zuciyar tata cewa tayi haba yau kusan shekara 8 da dori da rasuwan ahmad amma ace yana raye, ai inda yan raye daya dawo gaban ku, sai takawar da maganar, yayin da taji anfara speach direactor din makarantar yake magana akan hazakar daliban shi, inda yake cewa baitaba wani yaye sate nalikitoci masu kokari ba kamar wannan sate din kuma, yawan cin su yan nigeria ne ma ina alfahari da wannan sate din, yanzu zamu kira wace tayi na uku, yar india ce anuska raizada, tafito tana daga hannu.
Taxo tayi jawabinta aka bata kyautar tar mota da kuma aiki da aka dauke ta aka tafa mata, ta kuma tazauna sanna ya cigaba da magana, yace the next position sunyi bracket kuma yan nigeria ne suka dauka na biyu, aka kira baraka yusuf and rumana adam suka taso ana musu tafi sosai, inda suma sukayi jawabinsu da godewa wannan skull din nasu, yan gd ko sai murna sukeyi suna hawaye, suma anbaso kyautar mota da gida sannan, suka dauka hotona da directocin su, sai tafi aketayi bayan wajan ya nitsa sanna yaciga ba dacewa and the 1 first position is NI'IMAH U DAWAKI, duk wajan ya dauki tafi ana so aga wacece wannan mai sa'ar, ni'ima tafito duk jikinta rawa yakeyi ta kalla wajan su doctor adnan yanuna mata hannu alamun taje mama na hawa kan stage din ta daga ido taga dunbin mutane kowa sai kallonta yakeyi, takai idontan kan babanta yayi mata alamun tafara, takawo idonta daidai kan ahmad yayi mata murmushi da alamun haka👍🏻go on, sannan tayi wani ajiyar xuciya.
Tafara magana cikin harshen turancinta mai dadin sauraro kamar mai raira wakan india, sai da ahmad ya lumshe ido kowa sai mamakin speaking dinta akeyi yadda kasan kamar tafi kowa iya speaking, bayan tagama jawabinta, sannan take cewa nagodewa allah daya nuna min wannan ranar sannan kuma ina godiwa skull dina data bani ilimi sosai ina godewa lecture rorin mu da direactor din mu, allah yasaka da alkhairi, kuma ina godewa iyayena, sai ga hawaye ya zubo mata tacigaba da cewa, sannan tace ina godewa yayana A----- ahmad da kyar takarasa, mami tafara kuka shiku ahmad yana mamakin.kukan mama, yawan cin kowa nawajan sai da zubda hawaye, ubadan dawaki ya tauasayawa diyarshi, hakama baraka, axuciyar mama tace allah sarki naso ace wannan taron da akayi kana cikin habkalin ka.
Bayan tagama, sai shugaban makarantar su yazo yabata kyauta haka manyan mutane suna tazuwa bata kyauta sai karan camera kakeji ana ta daukanta hoto SHARUKHAN ma yazo ya bata gift dinshi tare da cemata, ni'ima u dawaki BARI BUHAT KUCHI MENE APNA HAI YE DIL HAI DUNYA CONGRAT, tasamu kyautar motoci har biyar da gida sannan kudi kuma ba amaga aka kira su rumana da anuska sai daukan hoto suke tayi da india wa, sannn akaba mawa sauran yan department din nasu kyautar dama su ashirin ne, suka dauka hoto in group inda suka sa su mama atsakiya, sun kashe hotona sosai harda su doctor hibba, ahmad da mama ma sun dauka tare sunyi masifar kyau, gwamnatin india suna bukatar suyi musu aiki, sannan gwamnatin nigeria ma haka, akafara ciye ciye sukaxo wajan iyayen su suna murna suka rungumesu shimanan suka dauki hoto mama ta rungume abbanta, abba yau gashi nazama cikakkiyar likita ko sai ga abdul rahman yace doctor ni'ima sai kinyi autar mu suka tafa.
Taro yayi taro kowa ya dawo gda wujiga wujiga duk gajiya ajiki su mama sundawo da tarin dukiya gda, agda ma sunyi kwarya kwaryan su nan ma gda sunsa mu kyaututtuka sosai, har yanxu ahmad baixo sungaisa da yan gda ba, bayan kwana daya kowa ya huta abban rumana yatara kowa a babban falonshi, yace musu yana son nuna musu babban danshi, ranar su mama gabansu sai faduwa yake tayi barema rumana, dama ahmad y kosa ya ga yab uwan abban su, kowa na zaune, sai abba yace MY SON shigo ka gaida iyayenka suko sai murna sukeyi amma banda ummi da baraka da rumana da mama wanda duk hankalin su atashe duk su tsurawa kofan ido yayi sallama ya shigo cikin murmushi.
TAKU UMMU RUMAN( NUSNIM) (08064481931)zindage hai mohabbat hai💘🌺
[10:50AM, 1/24/2017] +234 806 448 1931: 🍒🍒🍒LABARIN NI'IMAH🍒🍒🍒4⃣2⃣yayi sallama yashigo cikin murmushi gaba ki dayan su tashi sukayi tsaye hade dayin salati shiko yana yinayin ido hudu da mami yaji kanshi yafara juyawa, take anan yafadi kasa sumamme, ita ko mami tuni ta sulale kasa su rumana sukayo kanta da gudu, abban ahmad kuma sai ya kulle ido ya bude, yana cewa wannan wani irin mafarki nakeyi ne, yanxuma amafarki ahmad sai kazo mun, sai ya mara kanshi sai ya tsaya shiku uban dawaki na mijin kokari yayi ya jawo abban ahmad dake sun batu.
Shiko abban rumana tuni dama yakira motan asibiti ya sanarwa da doctor hafiz, su abdulrahman da su umma sai kalle kalle suke tayi kamar sun zare sai, mama kam sai kuka takeyi ganin halin da iyayensu suka shiga, sai ga doctor hafiz da su doctor adnan aka basu tai makon gaggawa amma antafi da mami da ahmad asibiti, amma su abba rudune yasa su kidimewa, amma anyiwa abban ahmad allura ta bacci, shiko ubandawaki sai kallon kanin nashi yakeyi, tare da tambayoyi abakinshi daya wa, duk su umma sundawo haiya cin su, amma suna ganin abunda ua faru kamar mafarki ne bare ma su umma, abban rumana yacewa yayanshi, nasan kana da tambayoyi sosai abakin ka ko, tabbas haka ne, bari abban abban ahmad ya farfado sai ayi maganar bayan kowa hankalin shi ya kwanta, manga yake cewa inafa hankali zai kwanta yanxu, har sai kasanar mana da amsoshin zuciyar mu, yayi murmushi insha allahu yaya zakuji komai, su abdulrahman dai basu ce komai ba ganin abu ya zarce tunanin su.
Uban dawaki ne yace tashi muje asibitin don muji lfyar su dama rumana ne da mama sai ummi wanda suka bi motar asibitin, su abban rumana suntafi aka bar baraka da su umma da su aliyu da abdulrahman, su umma suka tashi suka wuce masaukin su aka bar baraka da su abdulrahman, dama allah allah yake su umma su tashi yayiwa baraka tambaya, baraka wace take kallon su tana murmushi aliyu wanda ya shiga damuwa yace baraka wannan bashi bane ahmad din mama ba, abdulrahman yayi saurin amshe zancen, baraka yanaga ku banga kungirgiza yayin da yashigo ba sai tayi murmushi, meyasa zamu girgixa, tace hmm yaya abdulrahman kenan, aliyu yace mekike nufine baraka, sai murmushi kike mana mai makon kibamu amsan tambayen mu, tace yayi aliyu dole inyi murmushi mana, yau kusan shekaranmu 5 muna tare da ahmad, to saboda me zamu girgiza, abdulrahman yace WHAT kun dade kuna tare kikace, kenan kuna rayuwa agida daya kenan, eh wannan hakane, kuma harda mama tace eh har ita, tab di amma tayaya wannan al"amari mai daure kai yafaru, mutumin da yamutu tun dadewa? To meyake yi araye? pls ki fahimtar damu sai magana kike mana tsugul tsugul, shuko aliyu idon shine ya kada yayi jajir, azuciyar shi yace yanzu nakara rasa mama arayuwata to ya zanyi da raina, lallai kam ajalina ne yazo, don bazan iya rayuwa ba mama ba, ita kadai nake so.
Baraka tace muma ranar da muka fara ganinshi sai da muka kwanta a asibiti, mamace tafara ganinshi, tashiga damuwa sosai, sai take fada mana nida doctor adnan wato abokin ahmad kenan tun a nigeria yadawo nanna yana aiki na dan wani lokaci, lokacin da tafada. Mana mun karya tata har muka ce tasamu tabin hankali, har doctor adnan yasa aka duba mata kwakwal warta akaga bokomai. Muka share zancen kullum mama cikin kuka take tabi ta rame tayi baki kamar mai ciwon shekara daya.
Har abun yazo yana bamu tsoro daga muntambaye ta sai tace mana taga ahmad mukuma sai mu batsar da maganar, ana haka har allah yasa nima naganshi, sai da nasuma hakama doctor adnan shima, yashiga yanayin kidimewa sosai, wanda za ace ya za'ace mamaci yadawo, shuko ahmad mamakin mu yakeyi wanda abun nada munshi, sosai har yana cewa me muke gani awajanshi wanda yake bamu tsoro.
Mukayi shawara bawanda zamu fadawa abunda ke faruwa damu tundaga lokacin muka kasa sukuni, ranar da mujazo nigeria ne da zamu dawo abba yayi mana maganar aure tundaga lokacin hankalin mama yatashi, shine da muka dawo mukace zamu samu abban rumana da wannan zancen ko ya amsa mana tambayoyin dake zuciyar mu, don rumana tace mana yayanta ne kuma shi zata aura suna matukar son junan su shida rumana.
Abdulrahman yace kina nufin ahmad bai sanku ba eh bai san muba, aliyu yace dama shine wanda akace zai aure rumana tace eh, aliyu yace to tayaya yazama dan uwan rumana din? Sai baraka tace shi jikan kaka na ghana ne,, abdulrahman yace hmm wannan abu da daure kai yake, ya kuma cewa kuma suna soyayya agaban ku, tace sosai ma, yace allah sarki autar mu allah kadai yasan abunda takeji azuciyarta, baraka tayi murmushi me hawaye, hmm bara nafada muku wannan ahmad din bajikan kaka na ghana bane yaron mami ne shi, baraka ta kwashe komai da komai har ixuwa yau tafada musu, sun girgiza sosai, saida suka zubda hawaye, ashe dama bai mutuba, yana wajan abban rumana, amma allah yasaka mishi da gdan aljannah, aliyu suka ce ameen amma kuma su rumana sun bani tausayi sosai aliyu yace hakane, ko yaza ayi yanxu, abdulrahman yace nasan abban mu zaice mama tabarwa rumana ahmad, aliyu yace haka ne, amma da ba ayi mata adalci ba baraka tace kaima dai kafada yaya aliyu, don mama tace zata barmawa rumana ahmad, ita zata hakura.
TAKU UMMU RUMAN ( NUSNIM)08064481931, PHYAR HAI🌺💘
[10:50AM, 1/24/2017] +234 806 448 1931: 🍒🍒🍒LABARIN NI'IMAH🍒🍒🍒4⃣3⃣&4⃣4⃣Abdulrahman yace sai yadda manya suka yanke kam, wannan hakane, amma kuma yadda mama tayi hakurin jure rashin ahmad, bana jin rumana zata iya, baraka tace sai takoya ai itama maman koya tayi. Abdulrahman yayi dariya wato ke mama kikafi ji bama rumana ba, aliyu yace kyaleta naga alama bata son insami mama ce shiyasa take ta wani zaqewa.
Ai za mugani nasan abban mama ni zai bamawa mama ahmad kuma rumana, tace tab wlh bazai yuba, kai kafi dacewa da rumana wlh, yayi dariya haka kike gani niban masan ya kamannin rumana yake ba wlh,tace zaka sani idan nahada ka da ita, karki kuskura wlh don ni inba mama ba to bani son kowa, to sai ka dau dangana mama ta maka nisa. Suna cikin hira sai ga inna tazo tana kiran baraka, au hira kukeyi ne, aliyu yace eh inna to ku baza kuje asibitin bane, zamuje inna to maza kutashi kudubo mana lfyar su.
Can asibiti an gwada kwakwalwar ahmad ta dawo daidai abban rumana yayi murna, amma ahmad din bai farfado ba sbd an mishi alluran mai karfine, rumana da mama sunsha kuka sosai, su biyune awajan mami, itama bata fardado ba, rumana ta kalli mama da jajayen idonta, tace mama yanxu idan ahmad yadawo cikin hankalinshi, bai sanni ba ko, kuma bai san su abba da ummi ba, ko dasu nawwaran ko, ku kadai kawai yasani tana magana tana hawaye mama taji tausayinta sosai, kuma ya manta soyayyar da mukayi abaya ko, tayi dan murmushi me hade da kuka, mama ta dafa kafa dunta tace, rumana kar ki damu ahmad nakine ni mama nabar miki ahmad, rumana tana girgixa kai tana cewa a'a mama ahmad bazai taba yadda yasoni ba, saboda tun asali bani ke zuciyar sa ba, kece kadai, kema haka yake azuciyarki, zamana dake yasa nagane baza ki iya rayuwa ba ahmad ba, tashare hawayenta, naga irin soyayyar da ahmad yake miki acikin kundin sa dana karanta, sboda haka ahmad is yours only, mama tace no rumana nakine ahmad suka rungume juna suna kuka, sai ji sukayi ana ahmad dina dama kana raye, da sauri suka karasa wajanta, idonta arufe yake amma sai surayai take tayi, mama tace mami mami, sannan ta bude idonta wanda yarine tafara kallon siling, sannan idonta ya sauka kan su mama da rumana, tana magana ahankali tace da gaskene naga ahmad mama, tace eh da gaske ne ahmad dinki naraye, mami tace a'a ahmad dina yarasu pls kufada min gaskiya.
Rumana tace mami wlh ahmad dinki yana raye sai ta kara kallon mama, tana kokarin ta tashi ta zauna, suka taimaka mata suka samata pillow abayanta, ta zauna da kyau ta kalli rumana ta kalli mama ta hade fuska tace to kufada min tayaya yake raye, sai sukace abba yace kar afada komai so ake idan kunsamu sauki sai afada muku, abunda ya faru, tayi shuru tana hawaye, mami kidaina kuka dan allah, suka rungumeta suna kuka sosai sai ga su abba sunshigo, kukuma menene haka kunsata agaba sai kuka kuyi, sai kunsa mata wani ciwon ne, sukayi shiru su abba suka cewa mami, ya jikin tace da sauki, to allah ya kara sauki sai gasu baraka da abban ahmad sunta ho dashi don yace bazai zauna agida ba, sai ankawoshi asibitin,uban dawaki ya juya da mamaki yace har katashi ai da kazauna agida ka kara hutawa, ai ina banga taxama ba, ina so ku fahimtar dani da abun dana gani shin da gaskene ahmad dina nagani ko mafarkine, mami tayi saurin cewa tabbas ahmad dinka ka gani ba mafarki kake yiba sai ta fashe da kuka taci gaba dacewa amma bansan tayaya ahmad yana raye tsawon shekaru dayawa, yakasa waiwayo gda, abban rumana yace dan alla ku saurara kubar maganar nan, idan munje gida zan fayyace muku komai game da ahmad. Abban ahmad yace shikenan ba matsala, yanxu shi ahmad din yana inane, yan dakin hutune anmasa allura kuma ba ason kowa yashiga wajan ne ok, to shikenan, sai ga doctor adnan yazo yagaishar da su mami ya umarci da rumana tacirewa mami drip din da akasa mata, ya mika wa mama allura tayiwa mami, sannan aka salla mesu daga asibitin, sun so mutum daya ya tsaya kusa da ahmad, amma doctor hafix yace ba sai kun tsayaba akwai me kula dashi, to shikenan, abban rumana yacewa adnan yabiyoshi gda don su fayyace musu duk abunda ke faruwa da ahmad, yace to. Bayan sun koma gdane suka kara xama afalon da suka bari, duj kowa ya kagu da yaji abunda abban rumana zai ce, don duka zuciyoyin su cike yake da tambaya.
TAKU UMMU RUMAN(NUSNIM) akele tum akele ham🌺💘
[10:50AM, 1/24/2017] +234 806 448 1931: 🍒🍒🍒LABARIN NI'IMAH🍒🍒🍒4⃣5⃣&4⃣6⃣Abban rumana ya gyara murya yafara basu lbrin da baraka da mama suka bashi dashi ma yadda yasami ahmad din da zaman shi agidanshi da rayuwan da sukayi da ahmad.
Da rasuwan danshi ahmad da soyayyar da sukayi da ahmad, har zuwa yau bai boye musu komai ba, kowa na fallon sai da ya zubda hawaye, bare ma mami da take kuka, gashi kuma abunda ya daure musu kai yadda rumana ke son ahmad, abban ahmad dake share kwalla yazo gaban adam wato abban rumana ya durkusa agaban shi yana hawaye,, yace bansan wani irin godiya zan maka don kamin halacci sosai wanda aduniyar nan bakowa zai maka wannan abun ba sai mai imani, samun irinku aduniya basu dayawa, nagode sosai, kuma na tausaya maka rashin danka dakayi ahmad allah ya jikanshi ya gafarta mishi yasa aljannace makomar sa, duk da ahmad ne kadai dana aduniya bazai hana in mallaka makashi tunda ina da yara yan mata uku ga baraka ga rumana ga mama sun ishene, sai.ka zabarma wa dan naka mata acikin su, tunda ba damar ya aure su duka.
Suka rungume juna suna hawaye, abban rumana yace nagode sosai sosai bansan wani irin godiya zan maka ba a gaskiya muna son ahmad sosai, bakomai duk anaza daya, kowa na dakin yayi murna y suka goge hawayen su, amma fa banda rumana da mama wanda hamkalin su atashe yake, mami ma tazo wajan ummi ta rungumeta mami tana mata godiya irin son da tamunawa danta tilo, itama ta sadakar musu da ahmad din.
Uban dawaki yayi gyaran murya yace mungodewa allah subuhanahu wata ala da ya bayyanar mana da ahmad cikin koshin lafiya tare da kulawar adam,, adam allah ya biyaka da gidan aljanna firdausi allah yakara hada kanmu baki daya, sukace ameen, kuma kadauka kamar kai ka haifi ahmad kadauka kamar ahmad dinka bai mutu ba, yana raye, duk da nasan ahmad inyadawo cikin hankalinshi akayi mishi bayani bazai ki