tayi murmushi inadashi duk surutun da sukeyi, Ni'ima bata ce komai ba saidai kawai ta dinga na natawa azuciya, miji kuma wato kenan wannan kamshin turaren na mijinta ne? to taya ya wannan kamshin yaje dakin da suka kama? wannan abu da daure kai yake,, kuma meyasa tun farko bata cemana tana da miji ba?wazai bani duka amsana, kamarko rumana tasan tunanin Ni'ima na karshe, na rashin cemusu tana da miji ba, Ni'ima kina mamakin don nace ina da miji ko. tayi murmushi.
Kuyi hakuri kawayena naboyi muku wani abu, shi ba mijina bane amma inasa ran xaixama mijina don ina sonshi sosai dan uwa nane gidan mu daya, kuma likita ne sosai ana ji dashi acikin likitoci, shiyake kawoni kuma yake dauko ni, dafatan kun gamsu da maganata.
Sukayi murmushi amma mama kam murmushinta bai kai ciki ba tarasa dalili baraka tace kicaba rumana kice kin kusa zama amarya sukayi murmushi, sunkama hanyan zuwa department dinsu. sunshiga bada dadewa ba saiga lecture ra, mama taga ashe Doctor adnan ne shima yayi mamakin ganin ta kasancewar bai san anan take karatu ba, bayan yagama masu lecture suka kebe da mama suna magana, ashe nan kuke eh kaima kana koyarwane, eh amma basosai ba na dan wani lokaci ne nafi aiki a asibitin can ok ayya ya kwana biyu, ya iyali ka kuma ko gida tunda kazo kuwa eh nakoma ayya.
Sai ga rumana tazo tagai sheshi ita da baraka ya amsa, sukayi sallama da mama yawuce sai rumana tace Ni'ima wannan guy din yayi ko shine gwanin naki? a'a abokin mijina ne au dama kina da miji, eh amma ya rasu allah sarki allah ya jikanshi sai ga hawaye a idon mama, ameen rumana tace kiyi hakuri allah zai sanyaya miki da wanda yafishi baraka tace ameen.
Bayan sunkoma gidane sukayi waya da su mami har da umma da inna da yaya abdulrahman duk sun hadu waje daya anata gaggaisawa da yan makaranta, suka shaida musu sunan zuwa, suma sai murna, uban dawai yace umma kadai taje dasu mami kasan cewa kudin jirgin yayi yawa inbadon hakaba da dukan su za suje. abba yake cewa uban dawaki aiyakamata kaje kamanta da batun kudin jirgi nina dauki nauyin biya, harda abdulrahman za'aje da su inna ma, abdulrahman sbd tsabagen murna sai da ya rungume abba yana godiya, amma yace shi da kanshi zaiyi kudin jirginshi yana dashi, abba yace a'a. uban dawaki yace kayi hakuri alhaji zaiyi da kanshi badamuwa, to shikenan tunda haka kace.
Matan gdan su mama sai tsaigumi suke tayi aliyu ji yake kamar atafi dashi amma bahali yana so yaga abar sonshi, yana matukar son mama, har uban dawaki yana tausaya mishi, yakira aliyun kayi hakuri aliyu yau un allah yace mama matarkace matarkce, bawanda ya isa yahana sai allah ka kara hakuri kacigaba da addu'a, kana d sakone gun maman eh ina dashi wasika yaciro yabawa uban dawaki yayi murmushi yace kuma agaisheta.
Sai abban Ahmad yace zataji cikin murmushi, allah yasa mama ta amince maka kazama suri kin, ameen abba yana murmushin jin dadi. su mama ana shirin tarban iyayensu, rumana taga sai zumudi sukeyi, wai lfy baraka naga mama tana ta zumudi lfy haka wlh iyayenmu ne zasu zomana, ayya kice nima zangan su. eh to bari atashi mushiga kasuwa muyi sayayya ko, to allah ya kaimu bayan suntashi saiga yayan rumana din yazo a mota, motan tayi parking yana jiran rumana, sai gasu ko sunfio yana kallonta, tace yauwa ashe yazoma ba rabon zansha wahala, kuxo muje kugaisa sai infada mishi zamuje kasuwa, kamar sun hada baki sukace a'a jeki kekadai watarana zamu gaisa ok, duk yana kallon su amma su basa ganinshi.
TAKU UMMU RUMAN ( NUSNIM)MUCH OF PHYAR NI'IMAπΊπ
[10:49AM, 1/24/2017] βͺ+234 806 448 1931β¬: πππLABARIN NI'IMAHπππ1β£9β£
Rumana takarasa wajan yayan nata, tafada mishi tana son zuwa kasuwa ne yin siyayya"iyayen kawayenta ne za su zo gobe in allah y kaimu, ok zani kuma bank incire kudi ok to sai kindawo zanfadawa umma bye take care my one.
Yayi ribas ya wuce tagaban su baraka, yana kallon su, ta karasu wajansu kuyi hakuri nabarku atsaye a'a ba komai, to muje tashiga motarsu Ni'ima, dan allah mufara biyawa ta bank incira kude ok amma sai dai kimin kwatancen banka din to dinga nunawa mama hanyar kasancewa itace me tuka motar, sun isa banka tacire kudin suka joya kasuwa, suna tafiya tana basu labiri kuma tace yau sai sunje gidan su, sugaisa da umminta. baraka ta ware ido gidanku fa kikace eh mana ko baza kuje ba, duk fa mutanan gidan sun san da labarin ku har abbana, dakuma wannan yayan nawa kuma suna son ganin ku. please Ni'ima and baraka kuje mana dan allah, ok shikenan karkisamu da muwa zamuje.
Yauwa nagode muku sosai kawayene wlh ina sonko sosai, shiyasa abbana yake son ganin ku ganin nadamu daku, ashe ke yar lele ce sosaima ai suna ji dani bare ma yayana da abbana, ummina kuma tafiji da autarmu, waini katuwace kai rumana wlh kincika surutu inji baraka, ni'ima tace ina ruwanki baraka, yauwa yauwa ni'imata wannan barakar naga alama batasona kamar yadda kike sona, tana sonki mana ita kawai tacika zolaya ne.
Ai naga alama tana murmushi, Ni'ima kinsan wani abu kuwa, sai kin fada rumana. sunan mu daya dake, cikin mamaki suka juyo kai dan allah, shine baki fada mana ba, nikawai sunan bai min bane sunan kakata akasa min, shine nakejin kunyar fada ni aganina sunan mutanan dane, amma kuma dana hadu daku naji sunanki Ni'ima sai naji ina son sunan.
Mahaifina yana matukar sunan Ni'ima kasancewar sunan maman sace,rabonsa da mahaifiyarsa da yan'uwansa tun yana shekara shahudu saka makon saceshi da akayi ya gan shi aghana, shine wani mutum mai kudi ya tsince shi, kuma alokaci anbatar mai da tunaninshi don kar yagane gida har sai da ya girma yayi aure ya haifemu, kwasam sai yatuna da sunan unguwan su,, FANTAGORI, fantagori kuma dama mahaifinki dan fanta gorine ai garin mu kenan, dan allah tab di. shine fa yanxu yakeson zuwa yaje yanemo yan uwanshi, tunda allah ya mishi arziki yana so yan uwanshi su samu suma.
Jiyama yadawo daga gana gunkakanmu wanda yarikeshi da kuma yabashi ilimi yazama mai kudi kuma don ya daukeshi amatsayi babanshi sosai, allah sarki natausayawa mahaifinki, shiyasa ma yake sonku dana cemishi nayi kawaye yan nigeria, sboda cibiyarshi kenan,, ina kuma yanzu dana cemishi ku yan fantagori ne. shiyasa nakeso muje gidanmu daku.
Cewar baraka kar kidamu zamuje sunshiga kasuwa sunyi sayayyan su sun gama, suka wuce gidansu rumana ita tayi driving din motan, har suka isa gidan su mama sunga kudi kam gidane hadadde na ajin karshe sunyi parking da mota suka fito ni'ima tace kuzo mukarasa ciki to baraka sai kalle kalle takeyi sai da mama ta mintsileta tukunna ta daina.
sunshi falo sukaga wasu yara kyawawa sun rugu da gudu suna oyoyo aunty rumana muna ta jiranki baki dawaba sai yaya ne kadai yadawo, to kuyi hakuri munje kasuwa ne dakawaye nane,, sai alokacin sukaga su mama, Lah aunty rumana ina kikasamu me kama dake, sai tajuya tana kallon su mama cikin murmushi, wacce daga ciki take kama dani. suka nuna Ni'ima lah haba dai ai tafini kyau.
Ina ummi ne tana sama tashiga wanka to rumana tacewa su Ni'ima su zauna,tana zuwa bara ta kawo musu ruwan sha bayan ta tafi ne, nawwaran da nawwarat suka zo wajan Ni'ima suna gaisheta, nawwara tacewa aunty menene sunanki mama tayi murmushi tace sunana, ni'ima, la sunan ku daya da aunty rumana allah ko, Eh, suka cewa baraka kema aunty ya sunanki, tayi murmushu sunana baraka, aunty baraka ai aunty rumana suna kama da aunty ni'ima ko sai ta kalli mama taga kuma gaskiyan yaranne tabbas suna yanayin kama amma mama tafita kyau sosai, eh hakane kanina suna kama.
Kaima kana kama da yar uwarka ai amma ku yan biyu ne ko ,eh tare aka haife mu amma nafita tsayi, sai nawwara tace a'a aunty nadai fishi ko, to to to, dukan kuma kuna da tsayi da kuma kyau, aiko suka fara murna da tsalle suna ihu sai ga rumana, kai dalla lafiyan ku kuna mana ihu, a'a kyalesu inji mama muna hira ne dasu, sai ga ummi tasauko a'a har kindawo daga kasuwan eh ummi gasu Ni'ima nan da baraka, allah sarki yau kinkawo mana su suka durkusa kasa suna gaida ummi, a'a kutashi yarana bana son haka"ya karatu lfy kalau ummi y muka same ku lafiya kalau, ai muna tashan labarinku wajan runa ashe dara bon zamu ganku, eh ummi.
Rumana tace wa ummi wlh iyayen sune zasu zo gobe shine mukaje kasuwa mukayi siyayya ayya ashe baki zamuyi"allah ya kawosu lfy ameen ummi, ummi abba fa ya nan eh yana falonshi yana kallon news, ki kaisu sugaisa da abban naku toh ummi. baraka kutashi muje suna isa sukayi sallama suka shiga falon dukan su suka zauna akasa, a'a rumana har kundawo ai dazo yayanki yake fada min kunje kasuwa da kawayenki, eh abba shine ma nakawo makasu sugaisheka Ni'ima da baraka, suka gaishe kansu aduke yake baiga fuskar suba. ya karatu lfy lau abba da fatan ana bada himma eh abba to allah ya taimaka ameen, to rumana nikam wacece mai sunan maman tawa gatacan Ni'ima tadago kai sukayi ido hudu da abban ya yaji kanshi yafara juya mai ya meke shirin faruwane, gizon fuskarta yafara tunowa wanda bazai taba mantawa ba.
TOFA NIMA NACE MEKE SHIRIN FARUWA NE HMM BAKANTA FA. .
TO KUBIYONI AGABA DON MUJI MEZAI FARU AWAJAN.
TAKU UMMU RUMAN( NUSNIM)πΊπmuch of love my dostis
[10:49AM, 1/24/2017] βͺ+234 806 448 1931β¬: πππLABARIN NI'IMAHπππ2β£0β£
Rumana tace abba lafiya,bakomai rumana fuskar kawar kice yake min gixo dana hajiyata, ayya abba, ita kuma mama shi take kallo yayin da kamanshi yake mata fisge dana abban ta uban dawaki, tayi murmushi abba suma fa yan fanta gori ne yayi zumbur yagyara zamanshi kai dan allah, ashe garin mu dya allah sarki.
Dama abba iyayen su ne za su zo musu gobe, shine muke son mushirya musu abincin tarba. dan allah abba kabarni na kwana agidan su kaji abba, to ai bakomai sai ko dauka su larai masu aiki biyu su tayaku ko, yauwa abba na ashe kagane allah yaja zamanin ka abbana allah ya hadaka da yan uwanka, ameen uwata nagode da addu'arki.
Suka tashi za suwuce yace kudan dakata ina zuwa yashiga daki yadauko musu kudi masu yawa" ya mika musu suka ki karba rumana ta hade rai suka kalleta yace aini nabaku kyauta ba wani ba, kuma kamar ya'yana ne, to abba mungode allah ya kara budi ameen sannanfa rumana tasake rai, suka fita tafadawa ummi yadda sukayi da abba zataje ta kwana gidan su Ni'ima to shikenan, ummi ta basu kayan kwalliya da dankunnaye masu bala'in kyau irin na india wa, dakuma kayan ciye ciye.
To kiji kifadawa yayan naki mana, ummi sauri mukeyi yauwa abba yace aturo mana su larai gobe da sassafe sai driver yakawo su sai inmusu kwatance, toh allah ya kiyaye ta daukayen ta suka wuce.
A mota mama take cewa rumana gaskiya gidanku yayi min ki kalla yadda aka karbemu hmm sai ma kunxo kwana agidan namu ma zakusani, dan dayar yayata bata nan ne, sun isa gidansu barakan lfy, ruma na sai murna suna shiga sukayi wanka suka fara wani aikin daga ciki, washegari sai gasu larai sunzo sunfara aiki.
12 nayi su mama sungama shiri zasu je dauko su a airport kowaccen su tasaka kayan india kuma duk coulour daya RED yayi matukar yimusu kyau kasan cewar farare ne su, kuma riga da sikwt ne, sunsha dogon takalmi.
Rumana tace ita zata tuka motan, aikuwa haka akayi har sukaje airport din sun fito sunshiga wani waje sun zauna sai kallon su akeyi kasan cewar sunsa kaya iri daya gasu kansu daya kuma farare, daidai lokacin su uban dawaki da abba suka fito sai gasu umma da inna da mami da abdulrahma, kan kace kabo mama tazura aguje kawai baraka da rumana su kaganta aguje tafada jikin mamin ta da umma sai inna kuma, baraka naso itama tayi gudun amma rumana tariketa sosai allah baza ki tafi kibarni ba, allah allah take taje ta rungume innar ta da mami amma rumana ta riketa gamgam.
umma da inna sukace kedai mama baki girma wlh, mami tace don taxo ta rungumeku tana murnar ganinku, to nikam ku kyale min yata, mamina nayi missind dinki yaya abdulrahman da abba da uban dawaki suna kallon shirmen mama, saida ta rungume kowa, subaraka suka karaso rama tarungume su da gudu kema haka xakiyi kinxa ma mama ne, abdulrahman sai kallon masoyi yarshi yakeyi itama tagaida iyayen nasu, dukan su suka juya kallon rumana wanda take tsaye tana kallon su suna ta faman murna,, itama ta karaso ta sugunna gaban uban dawaki da abba ta gaishe su dasu mami ma, tazo gaban yaya abdulrahman. tace yayan mu ya hanya yace lfy lau mami sai kallonta cikin sha'awa take yaxo yata ya sunanki,mama tace kawar muce, kuma sunan mu daya amma ana ce mata rumana.
ayya gashi kunyi anko kamar wasu yan uku ta rungume rumana hakama umma da inna, rumana sai kallon uban dawake takeyi tana ayyana wani abu aranta.
DAN ALLAH KUMIN HAKURI SAKAMAKON WANI ABU DA YA TARENI,,
TAKU UMMU RUMAN (NUSNIM)πΊπ
[10:49AM, 1/24/2017] βͺ+234 806 448 1931β¬: πππLABARIN NI'IMAHπππ2β£1β£
Sai kallonshi take tayi sai da baraka ta tabata lfy rumana kuwa, naga kina ta kallon.abban mama ne, bakomai wlh natuna dawani abune, naga wani babban al'amari ne yake son faruwa, ko menene shi rumana, kedai bari kawai inmunje gd sai muhadu muyi magana ok, mama ta karaso inda suke wai me kuke tattaunawa ne haka naga kundade kuna tsaye, kema zakiji ai bari mukoma gida ok.
Suka karasa wajan motocin daman rumana tasa akawo mata mota daya daga gida da mami da inna da baraka sai yaya abdulrahman, suna mota daya baraka ita take tukin"sai kuma dayan motan da abban Ahmad da uban dawaki da rumana da mama adayan motan rumana ke tukawa ita, suna tafiya suna hira abinsu"rumana sai kallon uban dawaki take ta madubi, mama kuma tana ta basu labarin makarantar su da kawancen su da ruma harda zuwan su gidan, duk tafadawa su abba.
Hakama baraka itama tana tabasu labarin india da kuma skull da kuma kawancen su da ruma, mami tace a' lallai kice abun naku azeeman ne gashi ko kanku daya kamar jini daya"abdulrahman yace dafatan dai ba'ayi sau.....? sai baraka ta galla mai harara yayi shiru, mami tace aida ka karasa mara kunya kawai . sun isa gidan su mama dukan su suka fito, mama nabude gidan taga abun mamaki yadda aka canxa tsarin gdan da decrotion din yayi masifar kyau baraka tace lfy kikayi turus dake tajuya , tace kema xo baraka zoki ga abun da nagani tana karasawa itama mamaki ya daure ta.
Ita ko ruma tana jingine jikin mota tana jallon su cikin murmushi, suka jiyo so kalli ruma tadaga musu gira tare da murmushi, ta karaso wajen su mami tace kushigo mana mami, har su abba suka shiga suna kallon wajen" kowa yaxauna a falo, mami tace kai wannan falo haka, abban ahmad yace badai saboda xuwan mu kuka kashe kudi haka ba dongyara wajan, ubandawaki yace sai kace ana bikin india wa, abdulrahman yayi dariya ai abba murnan zuwanmu suke sukayi. su baraka dai basu ce komai ba don mamaki har yanxu afuskar. sai ga larai sunfara kawo kayan ciye ciye daban daban abun yawuce tunanin su mama.
Abdulrahman yakasa shiru don ganin abun ya girmama kai wai aina kuka samu kudi haka kukayi wannan abun. suma sukace bamusan da duk wa yannan abun ba, illa muma mamaki mukeyi, umma tace kamar yaya sai alokacin rumana ta amshe magana, kuyi hakuri, duk abun da kuka gani bada kudin su baraka bane sukayi, illama suma basu san konai akan hakaba, duk wannan shiri nane dana mahaifina bayan munje dauko kune akazo akayi wannan abun cikin kankani lokaci, don intaya kawayena murnan ganin ku. dafatan banyi laifi ba sai ubandawaki yace bakomai rumana allah yasaka da alkhairi abba ma haka yace harda su umma.
Ni'ima da baraka suka zo suka rungumeta suna mata godiya da murna, bakomai wlh ku kawayena ne ba har abada ina matukar sonko shiyasa namuku haka, wannan kadan kenan daga cikin aikina, abba yace bara mugama zamuje gidanku wajan mahaifinki don yimashi godiya. yauwa abba dama inaso kuje gidan mu, inna tace kar kidamu zamuje.
sun basu waje su ci abinci don suna so sutattauna akan wani abu, sunkebe mama takara yi mata godiya, nace kudaina gode mun, rumana tace akwai abunda keshirin faruwa mama ma tace tabbas da akwai , suka gayyace komai, kowacce ka gani tahada gumi, tare da farin ciki mara misultuwa, abdulrahman yazo yasa mesu shima yazauna yaciro wasikan da aliyu ya bamawa abba aba mama, gashi mama inji aliyu yace akawo miki. ta karba tare da hade rai, rumana tace waye aliyu baraka saurayinta ne kuma yayanta yarwa da kani suke yana matu kar sonta ita kuma bata sonshi tunda ahmad dinta ya rasu, ahmad shine mijin nata eh allah sarki sunanshi daya da yayana kuma wanda zan aura ayya.
Mama tace kumin shiru dawannan suratan naku tabude lettern takaranta, sai kuma yabata tausayi,, tarasa irin aliyu tafada
mai bata sonshi amma yaki ji.
Rumana ta kalle abdulrahman tace yaya amma kayi dacen mata fa don tana matu kar sonka, kai don allah amma nagode miki rumana, a'a nima kace min kanwarka, to kanwata suka kwashe da dariya vayan su abba sunshirya, daman rumana tafawa abban ta zancen xuwan su, sun kama hanya zuwa, suna isa tayi horn mai gadi ya bude" sukawu ce ciki aiko sunga inda ake narka dukiya a india. tayi musu iso cikin falon abban nata taje takira ummi suka gaisa, sai shima abba yasauko, yana saukowa suna ido hudu da uban dawaki, uban dawaki ya mike tsaye dan ba xai taba manta kamannin ba, abban rumana jikinshi sairawa yakeyi yana fadin ππ»y....?
TAKU UMMU RUMAN ( NUSNIM) MUCH OF MISSING NI'IMAHπΊπ
[10:49AM, 1/24/2017] βͺ+234 806 448 1931β¬: πππLABARIN NI'IMAHπππ2β£2β£
Yaya kaine kuwa ko gizau nakeyi, ubandawaki cikin karkar wa yace adam dama kana raye anya kaine kuwa yayi sauri ya karasa wajan shi suka rungume juna suna hawaye sosai, kowa na falon sai da yaayi hawaye barema ruman da mama sun tausaya musu sosoi,, yaushe rabon da su hadu shekaru aru aru.
Abban ahmad ne yaje ya lallashe su yace su zauna ayi magana duk sun xauna, sai abban ahmad yake cewa uban dawaki kasanshi ne Eh dan uwa nane uwarmu daya uban mu daya shine autar mu, tun yana karami ya bata ba aganshi ba, gashi iyayen mu na matukar sonshi sosai, mahaifin me nadin sarauta, asalin uban dawakin kenan" yazo ya kwanta ciwo yarasu, hakama mahaifiyar mu itama tarasu duk sun rasu da tunanin adam aransu, munyi neman adam ta koina bamu ganshi ba har addu'a mukasa akaimana shima amm shiru na labari.
Abban rumana sai kuka yakeyi saboda rashin iyayenshi da yayi har saida Abdulrahman da abba suka lallashe shi da kyar sannan yayi shiru, abban Ahmad yace allah ubangiji ya gafarta musu da rahmar sa Ameen kowa yafada.shima abban rumana yafada musu yadda akayi har ixuwa rayuwan shi india. allah ya tsare gaba kafin mukoma sai muje ghanan ko Eh, yatambaye shi sauran yan uwan shi yace duk sunana dayaran su, duk gida daya muke allah sarki, kai yaya yaranka nawa.
Yarana hudu biyu maza suna gida tare da iyalan su sai da ukunne wannan abdulrahman kenan sai kuma autana mama mai sunan mahaifiyar mu Ni'imah, kaifa babban dana shine Ahmad sai rumana itama sunan mahaifiyar mu nasa mata Ni'ima sai kuma laisu sai yan biyuna nawwaran da nawwarat, kai amma allah ya raya mana su ameen , ana tahira cikin nishadi basa son rabuwa. uban dawaki yanunawa adam abban ahmad sirikinshine amma allah yayi ma dan rasuwa shine wanda mama zata aura ayya.
Su umma da mami da inna, ummi tajasu sama sasanta don su huta abba kam suna ta hirar su su rumana ma anja kawayenta kuma yan uwanta suna ta murna sosai.
TAKU UMMU RUMAN(NUSNIM)πΊπ
[10:49AM, 1/24/2017] βͺ+234 806 448 1931β¬: πππLABARIN NI'IMAHπππ2β£3β£
Labari ya barke tsakanin su, abban rumana yace dole sai dai sukwana agidanshi aiko hakan tafaru abinci kala kala yasa an musu, washe gari suka dag zuwa ghana wajen marikin adam danttijo dashi mai kamala, yayi farin cikin zuwan su kuma yamika godiya gurin allah dayasa yau'uwan shi suka bayyana tun yana raye.
kwanan su biyu aghana suka koma india, suma sai yawo ake tayi agari asiyo wannan asiyo wancan barema rumana, ummi ma ba abarta abaya ba itama ta kwashe su mami akafita siyayya, sunji dadi sosai mami tacewa ummi nikam kema zan kwace miki yar taki rumana, sai in hada da yan matana biyu sai su zama ukun kinga shikenan nazama.maman ya'ya mata uku ko umma da inna suka ce aikowa hakama ummi.
Satin su daya a india sukace za su koma