tun daga bakin ma shigar gidan ka ake wulaƙantani ana cemin wai ni mabaraciya ne nazo bara wajenka, Buba har bindiga suka samin zasu kasheni, dana tsallake wannan siraɗin wannan ɗan albarka Garko ya shigo dani, sai na kuma samun wata masifar a cikin gidan nan, ina shigowa wannan shegiyar matar taka tana ganina sai ta haɗa fuska tamkar hadari ranta ya ɓaci tamkar taga masifa, na taƙaice maka da ita da wannan ja'irin ɗan naka mai baƙin hali suka zageni tas, ko abinci Zainabu bata bani ba, shi kuwa kalilu bindiga ya ɗaura min yace na kuskura na faɗa maka sai ya kasheni, tunda nazo matarka da ta haura sama ta barni a yashe a nan har yanzu bata fito ba, bare na samu darajar ta bani ruwa sai wannan ƴar kirkin zara'u itace ta ciyar dani ta shayar dani gata kuma tazo muna hira, dan haka yanzun nan ba sai anjuma ba, Buba tashi ka maidani ƙauye tunda ana neman rayuwata a nan, bazan zauna ba."
Ta ƙarisa Maganar fuskarta shakaf da hawaye harda shashsheƙar kuka, khalil zaro idonsa yayi yana mamakin Mamma yanda ta ƙarawa yanda akayi gishiri, Garkuwa ma zaro idonsa yayi yana sauraron Mamma, duk da yasan halin Mamma zatayi sharrin da yafi wannan ma, idanun suka haɗa da Jummo, wani ras yaji zuciyarsa ta tsinke, "wannan kamar Jummo" ya furta cike da mamaki tare da taɓe baki ya kawar da kansa gefe, Daddy wani irin ɓacin rai yaji idanunsa sukayi jajur, " taya za a ci mutuncin mahaifiyarsa a cikin gidan sa, ina Wallahi bazai yiwu ba, dole yau sai ran kowa ya ɓaci a cikin gidan nan idan ana son zaman lafiya dole ne abi umarnin mahaifiyar sa............."
*Biya Naira 100 ki ƴar uwa ki cigaba da karatu cikin nutsuwa, ki gaggauta biya domin kuwa akwai kwanakin dana ɗebawa wannan BOOK ƊIN da zarar kwanakin ya cika LITTAFIN zai tashi daga 100 ya koma 300 gara ki biya da wuri kafin wannan damar ta wuce ki biya ta wannan hanyar👇🏻*
*0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sannan kiyi screen short ki turo shaidar biya*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*FREE PAGE*
➰➰ *23 to 24*
" Oh na gane Aunty, bari na shige bedroom na watsa ruwa."
Da to Aunty Zarah ta amsa Sadiya ta shige tana hararar Jummo, Jummo kuwa da kallo ta bita tare da sauƙe numfashi itama ta shige bedroom ɗin Mamma, yana zaune kusa da Mamma sai zance suke suna dariya, itama Jummo Zama tayi tare da tura bakinta tace.
" Ni fa Mamma na fara gajiya wallahi, shi wannan Ya Garkuwan sai ta shareni yana kau da kansa gefe, baya ma son ganina, ni dai Mamma kice kawai ya soni tunda gani gashi yanzu a gabanki."
Dariya ce taso ƙwacewa Garkuwa, sai ya haɗa fuskarsa tamau, Mamma kuwa gyara zama tayi tare da cewa.
" Allah dai ya miki albarka, ai gara da kika tuno min da zancen Soyayyar nan taku, kai Garko kalleni da idanun da Allah ya baka sosai dan ubanka."
" To fa " Garkuwa ya furta yana zubawa Mamma Ido yace.
" To Uwata Mamma na kalleki faɗi kafin ta kasheki."
" Ai kuwa sai dai ta kashe uwarka ba dai ni ba, kaga Garko ka sota dan ubanka, kuma dole zaka aureta."
Murmushi Garkuwa yayi tare da nuna Jummo da yatsa yace.
" Wannan mahaukaciyar zan SO harna aureta, (Allah siddimo asiri Mamma) me zanyi da wannan jakar, hmmm!!! Naga alamar kina son shiga min hanci da ƙudunduno fa Mamma, to ki dakata haka dan dai wallahi nafi ƙarfin wannan jakar ƙauyen."
Wani irin zogi da raɗaɗin maganar sa Jummo taji, ta rasa meyasa Garkuwa yake kiranta da waɗannan mugayen sunayen jaka mahaukaciya, miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
" Ya Garkuwa na rasa meyasa kake kirana da wannan mugayen sunayen, amma ka sani koda na fito daga ƙauye ba baƙin ƙauye na fito ba, da ɗan wayewarsa, kuma ban shigo Birni da jahilci ba, bare ka kirani jaka, kowa yasan kakana cikakken malamin addini ne, haka kuma yayi ƙoƙarin bani ilimin addini alhamdulillah bokon ma nayi primary, kaga kuwa nafi ƙarfin ka kirani jaka, wannan kalmar tana min ciwo a duk sanda ka ambata min ita, Garkuwa indai nice wallahi daga yau na yafe Soyayyar ka har abada, ba kuma zan ƙara ambata maka ita ba, amma ka sani idan ba'a kiraka mahaukaci ba, ni baza'a kirani mahaukaciya ba."
A fusace Garkuwa ya miƙe zai shararawa Jummo mari Mamma ta daka masa tsawa.
" Karka fara dan ubanka wallahi kana saka hanu a jikinta, sai kayi nadama, wawa marar hankali to ka sani Wallahi baka da wata mata bayan Jummo ka ajiye a ranka, ko na mutu sai na barwa ubanka wannan was.......
.."
" Aa Mamma ki daina wannan maganar ki barshi yaje ya rayu da wanda yake so yaje ya auri ya Birni, karki shiga haƙƙin sa, ina sauraron Baffa sa'i da lokaci yana cewa, Annabi Muhammad (saw) yana cewa ya haramta Auren dole, me zaisa shi a masa, ki barsa Allah ya haɗa kowa da rabonsa"
Tana gama faɗin haka ta juya ta bar bedroom ɗin da gudu, nasu bedroom ɗin ta nufa ta faɗa saman bed kuka mai sauti ta saki, tana jin zuciyarta na mata nauyi tana mungun son Garkuwa sai dai shi sam babu ita a ransa, bata san menene aibunta ba, ko dan saboda ita ƴar ƙauye ce, Sadiya dake zaune gefe ne ta taɓe bakinta, tare da wirgawa Jummo mungun kallo Sosai Jummo tasha kukanta ta godewa Allah har sai da idanunta suka kumbura amma abun baƙin ciki soyayyar Garkuwa dai-dai da gutsure bai ragu a zuciyarta ba, miƙewa tayi ta shiga tollet ta wanke fuskarta, alwala ta ɗauro tazo ta hau Sallah.
Karfe tara na dare khalil ya shigo cikin gidan duk suna zaune a falo har Daddy da Momy sai Garkuwa ne kawai baya nan, a kusa da Daddy khalil ya zauna tare da cewa.
" Sannuku da hutawa, Sadiya yaushe a gari."
" Ɗazun nan na shigo, jiya ai Doctor Naseer yake cemin ka dawo kana gari."
" Eh na kwana biyu ma da dawowa, amm Daddy ɗazu naje gombe high school, wajen Mlm Nuhu nayi Magana dashi ina son na yiwa Jummo registration ta cigaba da zuwa school ɗin, amma na tambayi Mamma tace min tayi primary school, so yanzu yace nan da 3month zasuyi jsce so yace tayi jsce ɗin kawai idan yaso sai ta joining daga ss1 so yayi min bill ɗin kuɗin na biyasa 50k sannan ya min magana da wata malamar su Esther zata fara zuwa gobe tana yiwa Jummo da A'illo extra lesson, ita kuma A'illo gobe zamuje a mata registration na Junior secondry school sai ta fara zuwa.
Murmushi Daddy yayi cike da jin daɗi tabbas yaji daɗin abinda Khalil ya masa, itama Mamma sosai taji daɗi saboda burin Baffa kenan yaga Jummo tayi karatun Boko mai zurfi, ni sawa Daddy yayi kafin yace.
" Alhamdulillah!!! Allah ya maka albarka Khalil Allah ya biya maka buƙatun duniya da lahira kaima Allah ya baka mai rama maka, Allah ya azurtaka da mai rama maka, Allah ya tsare maka gabanka da bayanka, tabbas yau ka faranta min rai."
Dariya Mamma tayi itama cike da farin ciki tace.
" Khalilu ada ina maka kallon marar hankali, ashe dai kai mutumin kirki ne, yau kayi abinda banyi tunanin zaka yisa ba, Allah ya maka albarka."
Da ameen khalil ya amsa cike da farin cikin albarkan da iyayensa suka saka masa Momy kuwa haɗa fuska tayi tamau sosai ranta ya ɓaci da abinda khalil yayi ba tare da shawarar ta ba, sai dai ba tace komai ba, Jummo kuwa tsabar jin daɗi tamkar taje ta rungume khalil take ji, Aunty Zarah ma Sosai taji daɗi abunda take ta son bawa khalil shawara kenan sai gashi ya aiwatar da kansa tabbas mijinta mutumin kirki ne, cike da farin ciki suka kasance har kowa ya watse ya kwanta.
Momy kuwa sanda tasan yanda ta yiwa Daddy ƙarya ya barta zatayi sammako su fita da Asabe, a daren ta kira Asabe ta shaida mata cewa an barta.
Zarah cike da farin ciki ta rungume khalil tana dariya tace.
" Naji daɗin abinda kayi min sosai naji daɗi, daka saka Jummo a makaranta da alamu tana da basira zata iya zama wani abu a duniya wanda al'umma zasu amfana da ita, naji daɗi sosai."
Dariya khalil yayi yana daɗa rungumota jikinsa a kunnenta ya raɗa mata.
" Kaina na yiwa ba keba My dear, nayiwa Jummo wannan zumuncin ne saboda dalilai guda uku, dan haka ki daina gode min babu godiya tsakanin mu."
Murmushi Zarah tayi tana sakesa ta zuba masa ido tare da jefa masa tambaya.
" Ya khalil saboda dalili Uku kuma, wani irin daliline wannan.?"
" Hmmm!!! Zan sanar dake idan lokaci yayi, kije ki kaimin ruwan wanka."
Ɗaga kanta tayi alamun to tare da juyawa ta shiga tollet ta haɗa masa ruwan wanka, kwanciya yayi yana sakin murmushi tare da lumshe idanunsa, tabbas yana jin wani abu dangane da Jummo a zuciyarsa sai dai bai san menene fassarar abinda yake ji ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Washe gari da safe*
Sassafe Momy suka fita da Asabe ba tare da kowa yasan fitar ta ba, ko sanda Daddy ya tashi ta fita, shima breakfast kawai yayi ya fice.
" Saurin me kike haka SAFREENA ina zakije ki.?"
Juyowa SAFREENA tayi tare da kallon Zee tace.
" Zanje *ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* ne"
" *ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* kuma me zakije kiyi?"
" Bai kamata ki tambayeni abinda zanyi acan ba, tunda kin sani, amma tunda kina buƙatar na maimaita miki, zanje na haɗu da wannan azzalumin ne Garkuwa."
" Karkije ko kinje ba samun sa zakiyi ba, meyasa akwai fansa cike cikin zuciyarki, amma baki da mission akan fansar ki, jiya naje Asad airport nayi bincike akan Garkuwa, a binciken dana samu, baya aiki yanzu ya tafi hutun tsawon wata biyu, amma dai ya kusa cinye hutun saura sati biyu ya dawo kan aikinsa, amma a yanzu zaki iya samunsa a I'j'j hotel zaije can yau da misalin ƙarfe huɗu na yamma, shida ƙanwar matar yayansa mai suna Sadiya wacce a yanzu haka itace take cikin tarkon sa, da ita yake hole rayuwarsa, ina da tabbacin itama zai iya rabuwa da ita da zarar ya gama samun abinda yake so daga jikinta, a nawa tunanin karki nuna masa kanki yanzu kiyi amfani da wannan damar wajen razana Garkuwa ta hanyar bibiyar duk wasu gurɓatattun ayyukan sa wanda bayaso duniya ta sani a yanzu haka maganar da nake miki na bawa ma'aikacin hotel ɗin 30k ya ajiye mana camera a cikin bedroom ɗin wacce zata ɗauki duk abinda zasu aikata a hotel ɗin da zarar sun gama zaije ya ɗauki Camera mu kuma sai muje mu karɓa sauran aikin shima zan sanar dake idan camerar tazo hanun mu."
Da fe kanta SAFREENA tayi tare da zama a daya daga cikin kujerun dake falon tare da furta.
" Har abada shi ba zai daina saka mata a matsala shegen kwarjini ne dashi da wuya mace take iya tsallake tarkon sa, bashi da burin daya shige lalata Rayuwar mata ya saka su a cikin matsala, shiyasa nake son kawo ƙarshen sa, Garkuwa bashi da imani innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Zee sai yaushe Garkuwa zai daina lalata Rayuwar mace ya dauki mace tamkar rigar sawar sa, ya saka a lokacin da yaga dama ya kuma cire sanda yake so, idan banga Garkuwa a wulaƙance ba, bazan taɓa yafewa kaina ba wallahi."
" Safreena za kiga ƙarshen Garkuwa Da yardar Allah zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe ni da ke wajen ganin bayansa, zan tayaki wannan yaƙin safreena sai dai abinda nake so dake dole ne ki bawa Abdul kulawa Saboda shi bashi da laifi baisan komai game da matsalar ku ba, safreena karki kuskura haƙƙin Abdul ya fara bibiyar ki, ki farka daga ƙiyayyar da kike nuna masa."
" Ba ƙiyayya nake nuna masa ba babu Uwar da zata haifi ɗa ya tsaga jikinta ya fito ace bata sonsa wallahi ƙarya ne, zafi da suka tare da raɗaɗi nake ji a ƙirjina a duk sanda na ɗaga idanuna na kalli Abdul naga kamansa da Garkuwa, ko na tuno ƙaddarar samunsa ta jefani a cikin halin da nake ciki yanzu sai idanuna su rufe naji ƙiyayyar mahaifinsa ya dira a kansa amma wallahi ina son ɗana."
Numfashi Zee ta saki tare da jingina jikin kujerar tana cewa.
" Ki cire hijabin naki, babu inda zaki fita yau, a duk sanda kikaji zafin Abdul a zuciyarki to ki anbaci innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allah zai sanyaya miki, ina mai baki tabbacin cewa daga gobe zaki fara razana Garkuwa, zaki saka masa ruɗani da tsoro cikin zuciyarsa wallahi a gobe tsoro da fargaba zasu kasance abin tunaninsa, safreena Garkuwa bazai ga fuskar ki shida kansa zai fara nemo ki dan haka hankalinki ya kwanta ina da tabbacin zakiga karshen sa na miki wannan alƙawarin..................."
*Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi Naira 100 kacal babu yawa ki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko kuma ki turo hoton Mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sai ki turo shaidar biya*
*Ki hanzarta ki biya Free page saura 3 page ya ƙare idan kuma ya ƙare book ɗin ya koma 300 dan haka hanzarta ki biya ƴar uwa*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*Ina YINKU over masoyana, tabbas kun nuna min ƙauna a wannan book ɗin, kun nuna min kuna tare dani ko da kuɗi ko ba kuɗi 🥰🥰🥰🥰🥰 Love You masoyana muah😘😘😘😘😘😘*
Mu kafta🤾🏻♀️🤾🏻♀️🤾🏻♀️
*FREE PAGE*
➰➰ *25 to 26*
" Da zanfi kowa farin ciki, idan naji labarin zuciyar Garkuwa ta fara shiga cikin ruɗani, Zee babu abinda zance miki sai godiya, Allah ya bar zumunci domin kuwa kina nuna min ƙauna yanda ya dace na gode sosai."
" Ba sai kin min godiya ba, ki dai tashi kije ki bawa Abdul nono nasan ya farka yanzu haka."
Miƙewa Safreena tayi fuskarta a haɗe ta shige bedroom ɗin ta, ya tashi kuwa sai mitsilmitsil yake da ƙafarsa, zama tayi a gefe tare da ɗagosa ta saka sa kan cinyarta, nonon ta ta ciro tare da saka masa a bakinsa, saurin capka yayi ya fara tsotso, zuba masa idanu safreena tayi idanunta na cikowa da ƙwalla, tsoro da fargabarta ranar da yaron nan zai girma ya tuhumeta waye mahaifinsa, a wannan ranar bata san wacce irin amsa zata basa ba, hanunta ta saka tare da goge hawayen daya cika mata idanunta, sanda ya sake nonon dan kansa sannan ta ajiyesa ta shiga tollet haɗa masa ruwan wanka.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tun ɗazu yake zaune cikin motar yana jiran fitowar ta, yayin da yayi parking a bayan gidan nasu, yafi 30 minute a zaune cikin motar sannan ya hango Sadiya tana nufo motar murmushi ya saki mai sauti tare da sakin murmushi, gaban motar ta buɗe ta shiga, idanu suka haɗa ya sakar mata murmushi, motar yaja suka harba titi, murmushi Garkuwa ya saki tare da cewa.
" Nayi zaton kinyi zuciya ne dani ba zaki ƙara kulani ba sai kuma naga saɓanin haka, kin ajiye zancen auren a gefe kenan."
Kawar da kanta gefe Sadiya tayi ba tare da ta kallesa ba tace.
" Ai ka sani bazan taɓa iya rayuwa ba tare da kai ba, ina sonka sosai Garkuwa dalilin da ya saka rabuwa da kai zai bani wahala, a yanzu ma so nake ji shin zaka iya aurena a duk lokacin da ka tashi yin Auren idan har zaka aureni to ni kuma na amince zanyi zaman jiran ka.?"
Shuru Garkuwa yayi yana jan motar kafin zuwa can yace.
" Bana alƙawari Sadiya Saboda alƙawari yana da matuƙar hatsari, sai dai maybe zan iya auren ki, amma fa ban miki alƙawarin Aure ba."
Yayi Maganar yana saka hanunsa ya kamo nata yana Murza cikin tafin hannunta, shuru Sadiya tayi tare da cewa.
" Amma meyasa kafi son mu cigaba da lalacewa a waje bayan kana da halin da zaka aureni a gaskiya daga Yau mukayi wannan ni bazan sake ba, kawai gara mu haƙura sai munyi Aure."
Bakinsa ya taɓe irin ko ohon nan, bai bata amsa ba har suka isa hotel ɗin.
Ita kuwa Momy ƙarfe huɗu na yamma ta dawo cikin gidan fuskarta cike da fara'a hijabin ta kawai ta cire tare da duban Mamma da Aunty Zarah dake zaune tace.
" Mamma sannu da hutawa."
" Sannu uwar iya gantali tambaɗaɗɗiya, yo Idan banda tambaɗaɗɗe waye zai bar gidan sa tun kafin kowa ya tashi daga bacci, ke de bi duniya a sannu wallahi idan ba haka ba sai ta miki atishawar tsaki, wani wai sannu da hutawa Mamma, to ina ruwana da sannunki, ni kina gabana ne ma shasha kin girma har abada baza kiyi hankali ba."
Momy bata ce komai ba sai ma cewa tayi.
" Kiyi haƙuri Mamma, Zarah kin ɗaura girki ne.?"
Aunty Zarah cewa tayi.
" A'a yanzu dai nake so na tashi na ɗaura."
" Okay to ki barshi yau ni zanyi girkin."
Zaro idanunta Zarah tayi cike da mamaki Momy kuma zatayi girki da kanta, to meyasa anya kuwa muryar Jummo da sukaji daga bayansu ne ya sasu juyawa suna kallonta.
" Girki kuma ke da kanki Momy, meyasa bazaki bari mu muyi ba, haba dai ai kekam yanzu kinfi ƙarfin shiga madafi Momy, kije kawai ki huta zamuyi nida Aunty Zarah.?"
Murmushin yaƙe Momy tayi tare da miƙewa tsaye zatayi magana Mamma ta rigata.
" Yo ina kuwa zata zauna ta huta tunda taje bokanta ya bata wanda zata barbaɗa a girki, ke zainabu karfa ki mayar dani shasha, idanuna a buɗe suke tar duk abinda zakiyi ina sane sarai sai dai na zuba miki idanu, dama zaki saduda ki sawa kanki nutsuwa dama yafi miki domin Ni ɗin nan da kike gani Kainuwa ce dashen Allah, murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya na rantse da Allah da zaki shekara kina min asiri babu abinda zai sameni domin kuwa a tsume nake, karki manta daga inda na fito dan haka ki kiyayeni."
A matuƙar gigice Momy take kallon Mamma zaro idanunta Zarah da Jummo sukayi, cike da matuƙar ƙara razana da lamarin Mamma tace.
" Asiri kuma Momy, ni kuma mai zai haɗani da miki asiri, haba Mamma........"
Ɗaga mata hanu Momy tayi alamun ya isa tare da tashi tabar wajen ranta a matuƙar ɓace.
Murmushi Jummo tayi tare da matsowa gaban Momy tace.
" Kiyi haƙuri Momy tabbas wajen boka kikaje, nine na sanar da Mamma saboda jiya naje zan shiga bedroom ɗinki Aunty Zarah ta aikeni na ɗauko mata kayan wankin ki, har zan tura door ɗin bedroom ɗinki sai naji muryar ki, kuna zance ƙasa ƙasa da wata mata, sai na tsaya na saurari dukkan hirar ku, wanda kike da burin cutar da Mamma, ni kuma bazan iya jurar abinda zai cutar da ita ba, shiyasa na bayyana mata ƙudurin ki akanta kiyi hkr ba laɓe na miki ba, naje aiken Aunty Zarah ne na jiki dan Allah Momy ki sauya hali ki daina ƙoƙarin cutar da Mamma, Momy Mamma tasha bani labarin yanda kuka wulaƙanta ta, lokacin Auren ki da Daddy har yanzu wannan abun yana cin zuciyar Mamma meyasa baza kiyi ƙoƙarin kyautatawa Mamma ba, domin kawo masalaha a tsakanin ku, ki goge laifin ki daga zuciyarta na tabbata Mamma zata manta da komai ku zauna lafiya."
Wani irin sanyi jikin Momy yayi, take gumi ya keto mata kunya duk ya lulluɓeta juyawa tayi ta kalli Jummo tare da zama baki kujera ta kalleta cike da tsana ta nunata da yatsa.
" Wato laɓe kike min, hmmm!!! Yau naji wata ƙaddara yarinya ke gida bana ubanki ba, bana dangin ubanki ba, bana dangin uwarki ba, babu dangi tsakanin mu dake amma ki shigo cikin gidan mu ki nemi hanamu sakat, to bari kiji muddun baki fita a harkata ba, na rantse da Allah sai na kawo ƙarshen ki a cikin gidan nan, shegiya mai kama da buzuwa, to bari kiji baki isa ki wargaza min shirina ba, YANDA na ɗauki alwashin ganin bayan Mamma a cikin gidan nan, wallahi sai na gani, dole sai kun barmin gidana ko koma can ƙauye kuje kuta fama da dawa da baƙar kuka mtss."
Momy tayi maganar tana juyawa tayi taku ɗaya taji muryar Jummo.
"Muddun ina numfashi bazan taɓa bari ƙudurinki ya cika akan Mamma ba, na rantse da Allah yanda Mamma ta shigo gidan babu wanda ya isa ya fidda ita a gidan ɗanta, tazo kenan, Momy ki dawo cikin hankalinki ki fahimci cewa kina kan kuskure ne, da Mamma munguwa ce mai bin doka irinki wallahi da ta juma da ganin bayanki koda bataxo birni ba, domin kuwa ƙauyenmu mun fiku matsafa, amma ita zuciyarta a tsarkake take bata iya mugunta ba, faɗan kawai ta iya dan haka ki kwana da sanin zan tseratar da Mamma daga duk wani sharrin ki, Sai dai ke ki fita kibar Mamma a cikin gidan nan wannan alƙawari na ɗauka."
Kunkumin ta Momy ta riƙe tana huci yayin da Aunty Zarah ta daskare tana kallon Jummo, bata taɓa zaton JUMMO tana da baki haka ba, Momy ɗauke Jummo tayi da mari tana nuna ta da yatsa tace.
" Ni kike kira munguwar, ehh lallai ɗan zaki ya girma, gaskiyar hausawa da suka ce idan ɗan ƙauye ya shigo Birni ya waye sai yafi ɗan Birnin iya shege, to bari kiji ni ba kanwar lasa bace, nafi ƙarfin ki, kuma ki sani nice ƙalubalenki."
Tana faɗin haka ta haura da sauri tana huci, Jummo dafe kuncinta tayi tare da kallon Aunty Zarah, zatayi Magana Aunty Zarah ta ɗaga mata hanu tare da cewa.
" Karki cemin komai, na fahimci komai, tabbas Momy bata kyauta ba, amma bai dace ki mata rashin kunya ba, komai tsiya dai Momy ta haifeki, na fahimci kinzo gidan nan ne domin ku fitar da Momy daga gidan ta, wannan kuskure ne, kuma bazan taɓa bari hakan ta faru ba, Farko ɗaukar mutumiyar kirki nake miki ashe ba haka kike ba, ashe munguwa ce mai fuska biyu kin bani mamaki Jummo."
A matuƙar firgice Jummo take kallon Aunty Zarah da ta mata munguwar