wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya*
*Araha tafi bashi kuyi maza kuyi registration kafin na rufe 100 ce babu yawa🥰.*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*ASSALAMUALAIKUM ALAIKUM MASOYANA BARKA DA DARE, JAMA'A SAI MAGANA SUKE MIN AKAN COMPLETE ƊIN BOOK DIN HATSABIBIYA SAUDE HAR GA ALLAH BAN KAMMALA BOOK ƊIN BA SAURA KAƊAN WANDA NAKE SAKA RAN INSHA ALLAH ZUWA BAYAN SALLAH ZAKU SAMU COMPLETE ƊIN LITTAFIN, A YANZU GASKIYA BABU COMPLETE ƊIN SA, SANNAN INA KIRA GA MASOYANA DA SUYI GAGGAWAR ZUWA SU BIYA KUƊIN WANNAN LITTAFIN NA GELLE ƁINGEL AKAN FARASHI MAI SAUƘI 100 KACAL*
*FREE PAGE*
➰➰ *9 to 10*
Tana cikin wannan halin damuwar Momy ta faɗo cikin bedroom ɗin nata cike da faɗa.
" Oh wai Zarah kwanciya kikayi tuntuni, aikin gidan waye zai miki shi, wai meyasa kika cika son jikine, ki tashi maza kije kiyi aikin dake gabanki."
Cike da ƙunar rai Zarah ta ɗago kanta ta kalli Momy, numfashi mai zafi ta sauƙe tare da cewa.
" Aiki kuma Momy, ai nayi duk wasu ayyukan daya kamata nayi, nayi girki nayi shara da mopping, din falo, to kuma Momy me zanyi bayan shi."
Momy taɓe bakinta tayi sannan tace.
" Sanin kinyi ne yasa na kira ladi mai wanke wanken gidan nace karta zo, sai ki tashi kije kiyi wanke wanken, idan kin gama gacan wanki na, kije ki ɗauka ki wanke min su, kuma ban yarda ki saka Sadiya ba, kece zaki min waɗannan ayyukan, ayi yarinya da shegen son jikin tsiya, baki haihu ba, sannan kice bazaki aikatu ba, a'a dole kiji wahalar aiki tunda bakiji ta haihuwa ba."
Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo daga idanun Zarah, tana mungun jin zafin gorin haihuwa da Momy ke mata, har ga Allah ita ta fara gajiya da wannan rayuwar Auren ta fara ji a ranta gara ta kashe Auren ta zauna bazawara zaifi mata kwanciyar hankali ina amfanin auren da babu jin daɗi a cikin sa, uwar miji ta ƙuntata maka, shima miji ya kasa baka farin ciki, yana ganin tamkar baka son mahaifiyarsa ne, muryar Momy ne ya doki kunnen ta.
" Ko bazaki tashi kiyi aikin bane kike min hawayen munafurci, karya nayi a cikin maganata, ko kin taɓa yin koda ɓari ne, amsar itace a'a, dan haka dole ki bautu muddun kina son zama a cikin gidan nan, gara ki daina kuka zaifi muku, duk wani take taken munafukar ƙanwarki tana son Garko, to ki sani wallahi ko sama da ƙasa zasu haɗe bazan taɓa bari ɗana ya kuma Auren zuri'ar kuba, tunda da alamu baku da yawan ahali ku biyu fa rak iyayenku suka haifa suma su Uku uwarsu ta haifeshi, kinga kuwa ai ya tabbata baku da yawan ahali, ke bari kiji wallahi khalil ma sai ya ƙara Aure domin ya haihu shima yaga jininsa magajin sa a duniya, ki kuma tashi kije kiyi aikin dana saki."
Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, kuka mai cin rai Zarah ta saki, harda majina cikin kukan take cewa.
" Allah kana kallon halin da nake ciki, ya Allah kai kace mu rokeka zaka amsa mana, ya Allah ka bani haihuwa, idan kuma bani da rabon haihuwa a cikin gidan nan ya Allah ka kawo ƙarshen wannan Auren nawa na huta, ya Allah karka bari baƙin cikin Momy ya samin ciwo, Allah ka dubeni da idon rahama da albarkacin karatun Alkur'ani da nake."
Tayi addu'ar tana tashi, ta fito, kitchen ta shiga ta tattara wanke wanken tanayi tana kuka harta gama, ta kuma nufi bedroom ɗin Momy ta ɗauko wanki nata shima taje ta wanke tas ta shanya su, sosai ta gaji jikinta duk yayi tsami, koda ta dawo bedroom ɗin ta, Sadiya ta kira, kafin Sadiya tazo Zarah ta kira aminiyarta Khadijah akan tazo ta sameta, tana nan kwance Sadiya ta shigo a gefen bed ɗin nata ta zauna tare da cewa.
" Gani Aunty."
Tashi Zarah tayi ta zauna tare da tsare Sadiya da ido, cike da tuhuma tace.
" Sadiya zan tambayeki ne dan Allah ki faɗa min tsakanin ki da Allah, wai da gaske kina son Garkuwa, karki boye min komai ni ƴar uwarki ce baki da wanda ya fini.?"
Shuru Zarah tayi zuciyarta na bugawa ta sunkuyar da kanta tare da dagawa Zarah kai alamun eh.
Shuru itama Zarah tayi sosai hankalinta ya tashi lallai akwai Babban ƙalubale a gabanta dole ne, tayi yaƙin raba Sadiya da Garkuwa koda hakan zai kawo ƙarshen aurenta itama bataji daɗin zaman gidan ba, bare ta bari yiwa ƙanwarta sha'awar ta shigo amma bazan yi gaggawar rabasu ba, zanbi komai a hankali insha Allah a ruwan sanyi zan rabaku numfashi ta sauke tace mata.
" Sadiya da zan baki shawara ki ɗauka da nace ki rabu Garkuwa ki nemi wanin mijin Auren."
Da sauri cikin kiɗima Sadiya ta ɗago ta kalli Zarah, ras zuciyarta ta buga.
"na rabu Garkuwa no ina bazan iya ba, Garkuwa tamkar numfashi nane rasa shi yana nufin rasa rayuwata ne, amma Aunty meyasa kikace na rabu dashi.?"
" Nasan a yanzu bazaki fahimce ni ba Saboda zuciyarki tana cikin gigi bazan ce miki komai ba yanzu kije sai na sake neman ki, abinda nake so dake yanzu ki shirya ki koma gida gobe."
" Aunty na kom........"
Dakatar da ita Zarah tayi tare da cewa.
" Karki cemin komai Sadiya, dan Allah na roƙeki ki koma gida gobe, dan Sadiya karki sanar dasu Mama cewa nice nace ki dawo dan Allah kimin wannan alfarmar."
Cike da ɗaurewar kai Sadiya take kallon Zarah ta rasa Gane inda maganganun ta suka dosa sai har ranta bataji daɗin korarta da Aunty Zarah tayi a cikin gidan ba ( ko dai ta fahimci suna lalata da Yaya Garkuwa ne, idan ba haka ba meyasa zata koreni, Allah kasa ba hakan ta fahimta ba) duk cikin zuciyarta Sadiya take wannan maganar, tare da miƙewa cikin zafin zuciya ta fita daga bedroom ɗin, tana fita Zarah ta saki kuka tana toshe bakinta, tana cikin wannan halin Khadija ta shigo da sauri ta ƙarisa tana riƙe kafarɗarta.
" Subahanallah!!! Zarah lafiya meya faru.?"
Zarah tana kuka ta kwantar da kanta a jikin Khadija, cikin muryar kuka tace.
" Kinsan matsalata Khadija, Momy zata kasheni, ina tsoron kar wata rana a wayi gari babu ni na mutu."
Numfashi Khadijah ta saki tabbas Zarah tana cikin jarabawar uwar miji, maimakon Khadijah ta zagi Momy sai cewa tayi.
" Ita Rayuwa tamkar ƙwallon ƙafa take kullum cikin gara bawa take bata taɓa barin bawa ya huta, kana tsallake wannan jarabawar zaka faɗa wata, ki cigaba da haƙuri Zarah ke taki ƙaddarar kenan dan Allah karki dinga sanar da iyayenki abinda Momy ke miki, wata rana zaki iya manta abinda ya faru tsakanin ku, amma su iyaye bazasu taɓa mantawa kullum zasu ke ganinsu dashi."
Numfashi zarah ta saki tare da kai dubanta ga Khadijah fuskarta cike da alamun damuwa tace.
" Khadijah tunda akayi aurena da Khalil zaman haƙuri kawai nake a cikin gidan nan, kullum bani da burin daya wuce na farantawa Momy Amma sam bata gani na rasa meyasa Momy ta tsaneni, bani na hana kaina haihuwa ba Khadijah amma meyasa take ganin laifina, shima kansa Khalil baya ganin laifin Mahaifiyarsa sai nawa, kullum nayi magana sai dai ace nayi haƙuri ana tusa min baƙin ciki, sai yaushe komai zai wuce, ko sai na mutu ne, Khadijah bazan ɓoye miki ba, wallahi na fara gajiya da wannan rayuwar gidan na gaji da wannan Auren na gaji da hkr."
" Zarah ba'a gajiya da hkr, mijinki yana sonki da ƙaunarki dan Allah kar damuwa mahaifiyarsa tasa kibar gidan sa, dama ba kowani ɗan adam bane yake so a dinga yawan kawo ƙarar mahaifiyarsa, kullum ina hanaki kaiwa mijinki ƙorafin mahaifiyarsa domin kuwa maza basa so, hkr da juriya shi zaki riƙe insha Allah zakiga komai ya zamo tarihi babu abinda yazo zama a duniya sai ikon Allah komai yana da farko da ƙarshe ki daure kici wannan jarabawar zarah."
Cike da tsantsar damuwa zarah tace.
" Khadijah kullum abinda kike faɗa min kenan kalma daya kiyi hkr Khadijah sai yaushe wannan haƙurin zai ƙare ne, haka zan cigaba da rayuwa cikin baƙin ciki da ƙunci.?"
Murmushi Khadijah tayi tare da cewa.
" Haƙuri baya taɓa ƙarewa na faɗa kuma na maimaita miki, Asali ma sai dai ya kaiki ga cimma nasara, Zarah dole nace kiyi hkr domin kuwa shine abinda duk wani masoyinki na gaskiya zai faɗa miki, Aure ya gaji ƙalubale duk daɗin da mace take ji a gidan Auren ta dole sai kin samu ta da wani matsala koda kaɗan ne."
" Shikenan Khadijah zan cigaba da haƙuri har Allah ya kawo min karshen matsalata, bari naje na kawo miki abinci."
Khadijah murmushi tayi tace.
" A'a barshi wallahi a koshe nske bani da yunwa yanzu haka gidan kaka tabawa zani na dubo jikinta shine fa dana ga kiranki nace fana fara biyo nan ɗin."
Zarah ce tace.
" Dama kullum kika zo gidana baki cin abinci, ki gaishe da kaka tabawan."
" Khadijah tana miƙewa tsaye tare da ɗaukar jakarta tace.
" Zataji nikam bara na tafi."
Zarah tare suka fito da Khadijah daga bedroom ɗinta a falo suka taradda Momy zauna tana kallo Khadijah har kasa ta sunkuya tace.
" Sannu da hutawa Momy Barka da Rana."
Harara Momy ta watsawa Khadijah tare da taɓe bakinta tace.
" Iyayen munafurci kuma yaushe aka shigo, har kun gama kulla tsiyar ne, baki da aiki sai gulma da munafurci, wallahi ɗana Khalil yafi karfin ku, tun yana yaro nake tsumasa da bauri yafi karfin kaidinki da bokan ku, shige a gabana."
Khadijah bata ce komai ba ta miƙe tsaye, Zarah ranta cike da baƙin ciki ta juya zatabi Bayan Khadijah Momy ta dakatar da ita tare da cewa.
" Ina zaki fita ki bita baƙar munafuka, duk makircin da kuka ƙulla a ɗakin bai isheku ba, har sai kun fita waje kun ɗaura, to koma ɗakinki bazaki bita ba."
Zarah zatayi magana Khadijah ta dakatar da ita.
" Karkice komai ki koma zamuyi waya."
Juyawa Zarah tayi cike da baƙin ciki, ita kuma Khadijah ta fice tana yiwa Zarah addu'ar samun sauƙi, Momy kuwa tsuka taja.
Ita kuwa Sadiya cike da ɓacin rai tabar gidan Zarah babu wanda yasan ta tafi a cewarta Aunty Zarah ta wulaƙanta ta, ta koreta a gidan ta, tana mata baƙin ciki karta auri garkuwa ta huta.
Koda Garkuwa ya dawo da daddare sai da ya nemi Sadiya saboda buƙatar kansa, Aunty Zarah ganin bata gidan yasata fahimtar fushi tayi ta tafi, murmushi Zarah tayi tare da cewa Garkuwa.
" Sadiya ai tun ɗazu ta tafi, Mama ta kirata zasuyi tafiya."
Cike da rashin jin daɗi Garkuwa yace.
" Kuma Aunty shine zata tafi kota nemeni bari na kira wayarta"
Yayi Maganar yana ciro wayar sa, numbern Sadiya ya kira yaji switch off, Aunty Zarah ya kalla yace.
" Switch off."
" Wayar nata, maybe ko chaji."
" Zai iya yiwuwa" Garko ya faɗa tare da tashi ya haura harya taka step ya juyo ya cewa Aunty Zarah.
" Am na manta ɗazu khalil ya ce ya kiraki baki ɗaga ba, so yace a faɗa miki gobe bazai samu dawowa ba sai next week."
" Allah ya kaimu Zarah tace tana shigewa kitchen."
✨✨✨✨✨✨
Rayuwa tana gudu yayin da abubuwa ke sauyawa mai daɗi da marar daɗi, Rayuwar Zarah dai a cikin gidan babu wani sauyi wajen Momy, yayin da daga can ƙauye Mamma take ƙoƙarin dawowa cikin birni gidan ɗan ta tare da Jummo domin kawo ƙarshen Momy, Momy da Daddy har Garko basu da labarin dawowar Mamma ita kaɗai tasan zata dawo, bata kuma so su sani sai dai su ganta.........................
Tirƙashi lallai akwai lauje cikin naɗi shin wani irin rayuwa za'ayi a wannan gidan idan Mamma ta dawo, shin Mamma zata ci galba akan Momy kuwa, Garko zai yadda da Auren Jummo kuwa, shin Zarah zata samu farin ciki, ya Rayuwar Sadiya zata kasance tsakanin ta da garko, amsar tana sanƙame cikin wannan labarin indan kun biyoni da Naira 100 kacal, ba'ama fara komai ba yanzu za'a fara, ku dai masoyana ku biyoni mu jone.
*100 zaki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan kuyi screen short ku turo shaidar biya, karku sake ayi babu ku.*
Masoyana ina alfahari daku, sai na ganku.
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*FREE PAGE*
➰➰ *13 to 14*
Tafiyar awa ɗaya ce ta kawo su Mamma har ƙofar gidan Alhaji Buba Tasiu mai taxi parking yayi a gefen gidan yana duban Mamma yace.
" Allah ya kawo mu, munzo ganan gidan ɗanki Alhaji Buba, sai ki shiga ki karɓon kuɗina."
Mamma zaro idanunta tayi tana leƙo kanta daga tagar motar, tana ƙarewa gidan kallo.
" Kan bala'i wai da gaske wannan tangamemen gidan duk na Buban Mamma ne, kaga wani makeken ƙyaure na gwal yiwa bakin shige, cap!!! Aa dole Buba ya dawo shirgegen ƙato, ina can ina zaune a shegen gidan zana shiko yana nan cikin wannan aljannar, lallai Zainabu ta shanye Buba."
Jummo itama gidan take kallo tana jin wani irin farin ciki, ita fa burinta kawai taga Garkuwanta shine damuwarta, A'illo kuwa uffan bata ce ba saboda tasha zuwa gidan itama Mamman ƙin dawowa tayi tun farko tace sai ƙauye, hanun Jummo Mamma ta kamo suka fito daga cikin motar A'illo bayan su ta biyo, a bakin get ɗin suka tsaya Mamma ta kalli Jummo tace.
" To ni yanzu Jummo ta yaya nasan zan iya buɗe wannan ƙatuwar ƙyaure, ki duba fa yanda yake kame tamkar baida mabuɗa."
" Mamma ni ina zan sani, gashi ba guntuwar katanga ba, bare mu haura, kawai mu ta bugawa harsu buɗe."
Ai kuwa Jummo bata rufe bakinta ba, Mamma ta hau doka ƙofar tamkar zata ɓalle ta, Joseph da keneth sai Baba idi mai gadi cike da tsoro suka miƙe jin mungun bugun da ake yiwa ƙofar, keneth da Joseph bindiga suka ɗaga sama, keneth shine ya buɗe get ɗin tare da saita bindigar sa, dai-dai ƙirjin Mamma bindigar ta tsaya, ai kuwa Mamma bata ankara ba, sai gani bindiga tayi, wani irin ƙara tasa, sai ga fitsari sha ya zubo daga jikin Mamma take ta wanke zaninta da fitsari jikinta ya soma rawa, ta kasa magana sai zufa dake keto mata, Jummo kuwa idanu ta ƙura masa cike da rashin tsoro ko a jikinta, sai kuma ta kwashe da dariya ganin yanda Mamma ta sake fitsari ga famar rawa da take yi, cikin tsawa Joseph yace.
" Kai wanene zaka dinga duka ƙofa haka, kai wawane Mama, ko aikeka akayi.?"
Joseph yayi Maganar cikin bagwariyar Hausar sa da bata nuna ba, Baba Idi ne mai gadi yace.
" A'a Joseph ai ba sai ka tambaya ba, ya wuce irin mabaratan nan ne, masu zuwa bara wajen Alhaji."
Tsawa keneth ya dakawa su Mamma.
" Ku bar kofar gidan nan ko na ɗauke kanku da bindiga, duk na kasheku YANZU."
Ai Mamma bata jira ya rufe bakinsa ba, ta zura da gudu ta koma bakin motar Tasiu, Jummo kuwa batayi motsi ba, tace.
" Bafa bara muke ba malam, ya zaka kalle mu kace mana mabarata, wannan tsohuwar da kake gani Uwar masu gidan ne, itace maman Alhaji Buba, baka san Buban Mamma ake ce masa ba a ƙauye, ku bamu hanya mu............."
Wani wawan mari keneth ya ɗauke Jummo dashi, tare da hankaɗata ya rufe get ɗin, dafe fuskarta Jummo tayi cike da ɓacin rai tunda take a rayuwarta babu wanda ya taɓa marinta da girman ta, sai wannan mai fuskar fir'aunan, juyawa tayi ta dawo wajen Mamma da har yanzu take cikin firgici sai ɓari take, Jummo duban Mamma tayi tace.
" Kin iya kunna sigari ki zarewa mutum ido kuna kunna masa ashar, amma sai tsoron bala'i, ki duba fa yanda kika jiƙe da fitsari Mamma abun kunya, shiga mota mu koma kauye kawai wannan ba gidan shiga bane gidan bala'i ne."
Ita dai Mamma yau bata da baki, ko amsa bata mayarwa Jummo ba, ta faɗa motar duk abinda akeyi, Idi drever yaga koma ba musu ya shiga motar, Jummo tana ƙoƙarin shiga idanunta ya kyallo mata motar Garkuwa yana tahowa, tsalle tasa tana dariya tace.
" Yeee!!!! Mamma ganan Yaya Garkuwa a mota fito ki tsare mana shi aradu."
Ai kuwa but Mamma ta fito, Garkuwa dreving ɗinsa yake, abunsa yana sauraron waƙar auta mg boy, ko kaɗan bai kula da Mamma ba, sai gani yayi ansha gaban motarsa, da sauri garkuwa ya taka burki gudun karya taka ta, zaro idonsa yayi yana kallon Mamma cike da mamakin waya kawo ta, "Lallai wannan tsohuwar akwai rigimar tsiya" buɗe motar yayi ya fito, ras idanunsa suka sauƙa akan Jummo, zuciyarsa ne ta tsinke ras, " dama da wannan aljanar yarinyar tazo, yau kuma mun shiga Uku ai" yayi Maganar a ransa yana haɗe fuskarsa, da gudu Jummo ta ƙariso gaban sa tana.
" Oyoyo yaya GARKUWA na, wayyo daɗi, wallahi sai yanzu naji sanyi dana ganka yaya GARKUWA na."
Tsuka garkuwa yaja yana nuna ta da yatsa yace.
" Ke mahaukaciya, karki kuskura ki ƙara danganta sunana dake, wawiya." Yayi Maganar yana duban Mamma da har yanzu bata cikin hankalinta yace.
" Ke kuma meye haka sai kace wadda aka tsamota a kaskon suya, duk kinbi kin fice hayyacinki, anya kuwa lafiyar ki."?
Jummo baki ta murguɗa masa, Gabansa Mamma tazo tare da kamo hanunsa tace.
" Kaga Garko bana son bala'i yanzu wanda na gani yanzu ma ta isheni, ni dai yanzu biya idi kuɗin sa, sai ka ketarar damu siradin gidan ubanka, tunda kunsa ƙattai masu fuskar fir'auna su dinga ciwa duk wanda zai rabeku mutunci."
Cike da rashin fahimtar zancen ta, Garkuwa yaje, motar Idi ya basa dubu goma, tare da tambayar A'illo meke faruwa da Mamma, fayyyace masa A'illo tayi, sosai Garkuwa yake dariya, tare da barin motar sa a wajen ya jawo hanun Mamma yace.
" Muje masifaffiyar ƙarya."
Tafiyar sukayi har bakin get ɗin Mamma na maƙale jikin Garkuwa, get ɗin a kwankwasa a hankali, jumawa kaɗan keneth ya wangale kofar ganin Jummo yasa zai fara masifa sai kuma yayi shuru sakamakon ganin Garkuwa, gefe ya matsa suka shiga, kafin ya rufe, Garkuwa cike da tahuma yace.
" Wani ɗan iskan ne cikin ku ya nunawa wannan tsohuwar bindiga?"
Shuru sukayi, tsawa Garkuwa ya Kuma musu.
" Magana nake kun min shuru!!"
Joseph ne ya nuna keneth da yatsa, numfashi Garkuwa ya sauƙe tare da cewa.
" Kasan wacece kuwa wannan daka nunawa bindiga, kasheta zakayi ne, Maman Daddy ne fa, uwar da ta haifesa."
Zaro ido dukkan su sukayi cike da tsoro, Garkuwa cije bakinsa yayi tare da cewa.
" To kuwa kun jawowa kanku bala'i ku kwana da sanin cewa yanda kuka shuka mata tijara, wallahi Mamma sai ta jaza muku bala'i dan bata barin bashi."
Yayi Maganar yana jan hanun Mamma suka shige part ƊINSU, Baba Idi mai gadi kuwa, cikin sa sai ƙugi yake cike da tsoro domin kuwa da wannan aikin kawai ya dogara idan aka koresa ya zaiyi da iyalansa, gara su keneth su gwamnati suke yiwa aiki koda za'a ɗau mataki sai dai a musu horo ba dai kora ba, da wannan damuwar Baba Idi ya zauna.
Suna shigowa bakin falon Mamma ta kwace hannunta tare da cewa.
" Dallah cikani!!! Dan ubanka, ke zainabu!!! Ke Zainabu!!! Zainabu!!!"
Momy da Khalil dake zaune suna hirar yaushe gamo ne ya sata saurin juyowa jin ana ƙwala mata kira tamkar za'a tashi sama, shima Khalil dubansa yakai wajen " Mamma!!" Ya furta yana miƙewa tsaye, Momy kuwa kusan suman tsaye tayi ganin Mamma a cikin gidan ta, shikenan ta shiga Uku, Mamma a cikin gidan ta!!! Dakyar cikin nauyin baki Momy ta amsa.
" Na'am Mamma kece tafe, lale marhaban sannu da hanya, kin kwaso rana, Bismillah Mamma ki ƙariso ki zauna."
Kallon sheƙeƙe Mamma ta yiwa Momy cikin masifa take kwaikwayon maganar Momy tace.
" sannu da zuwa Mamma kin kwaso rana, Bismillah ki ƙariso ki zauna!!! Riƙe sannun ki makira bana so, ina ruwanki da hanyar dana kwaso a kanki na taho da zaki min ƙirafi,. Koko ni makahuwa ce da bazan ga wajen zama ba sai kin gwada min, gidan kine kona ubanki ina dai gidan ɗana ne, ai dole na zauna ba tare da iso ba."
Shuru Momy tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa bata tankawa Mamma koda kalma ɗaya bace, Garko kuwa taɓe bakinsa yayi alamun kunfi kusa, shi kuwa khalil tamkar hadari haka ya haɗa fuskarsa a rayuwarsa ya tsani a ƙuntatawa Momy cike da masifa idanunsa sunyi jajur yace.
" Haba Mamma!!! Haba meye haka wannan ai cin mutumci ne, taya zaki samu mata tana zaune ki hauta ba tare da ta miki wani laifi ba, gaskiya wannan bai dac........"
Hanu Momy ta ɗaga masa tare da cewa
" Karna kuma jin muryarkae, baka da hankali ne, Mamman sa'ar kace, ina ruwanka da kai take" kallon Mamma tayi tace " kiyi hkr Mamma Allah ya huci zuciyarki."
" Ai da baki dakatar dashi ba, da kin barsa sai yazo ya dokeni, ya gani idan zai share dan ubansa, tambaɗaɗɗe marar mutunci, yo ni ina ma lissafi dakai a cikin jinina ne, kalilu, shege mai baƙar zuciya tunda ka shiga wannan tsinannan aikin ko zama cikakken Bayahude, to dan ubanka na dawo gidan nan da zama, sai ka shiryawa dukana wata rana tunda kace kai marar mutunci ne" tsagaitawa Mamma tayi da maganar sai kuma tasa kuka tana cewa " yanzu tsabar ba'a daukeni da mutunci ba, nan aka ajiye wasu ƙattin arna masu fuskar fir'auna, suka hanani shigowa gidan ɗana, wai harda bindiga aka ɗaura min saboda ba'a so nazo gara a haɗa baki dasu su kasheni, wai tsabar rainin wayo wai wannan ƙeƙashashen mai gadin ƙyauren naku ya kalleni ya kira ni mabaraciya, wallahi yau ɗin nan sai ya bar gidan nan Allah ya kawo Buba, zan nuna masa nice mai iko da gidan ba Buban ba."
Cike da takaici da haushi Khalil yake kallon Mamma gashi ba halin ya mata magana Momy ta hausa da faɗa, Garko kuwa dariya yasa tare da haurawa sama yana kiran " Mamma matsala" waje ta samu ta zauna tare da saka hanu a lalitar ta, ta ɗauko sigari da ashana,