Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
jini, dole ai ki zagemu." "Zagi kuma Mamma, ni wallahi ban zageku ba, Amma kuyi haƙuri idan ranku ya ɓaci, haba dai Mamma ta, haba INNO ta, kune fa gata na, taya zan zageku, bakin nawa ne babu sakata duk sanda gaskiya tazo sai na faɗa, amma dai na tuba bazan sake ba, kinga Mamma ki rufa min asiri ki taimakeni ki taimaki rayuwata, ki zamo jagorata na auri Oda ta, ya Garkuwa na, idan na auri ya Garkuwa, Mamma katan katan zan dinga saya miki sigari, kuma babu shege ɗan iskan da zai raina min ke, kamar ƙwai haka zan dinga lallaɓa ki, ke kuma INNO duk shekara saina kaiki Makka, har Mamma ma sai ta koma duk da ta taɓa zuwa, dariya Jummo tasa tana kallon INNO tace, Cap wayaga INNO a Makka." Ai kuwa take Mamma ta sauƙa tana wage baki tana dariya tace. " Allahu Akbar ƴar albarka, kinji yarinyar kirki INNO, Oh kinji fa ƴar kirki, Makka zata dinga kaimu duk shekara, kuma fa wallahi akwai kuɗin da za'a kaimu Makka duk shekara a gidan Buba kuma kuɗin bazasu girgiza ba bare su san an ɗebe su, wannan tsinanniyar matar tasa zainabu ke hanasa min alkairi" sai kuma ta fashe da kuka tana mutstsuka idanunta ta cigaba da cewa " Sai gashi ƴar albarkatun jikata tana son ta auri jikina Garkuwa saboda kawai ta share min hawaye na, ko dan wannan niyyar taki ta alkairi, Jummo sai na tabbatar kin auri Garko kafin na mutu, ai dai da arziki a garin wasu gara a garin ku, a garin kuma a ɗakin ku, nayi miki alƙawari Jummo ko bayan raina sai Garko ya aureki ƴar albarka." INNO ma fashewa tayi da kuka tana cewa Mamma. " Ke dai bari Mamma nine da kuka ba ke ba, Allah sarki ƴar albarka, kaf cikin haulata babu wanda ya taɓa maganar zai kaini Makka sai Jummo ƴar albarka, Allah sarki yarinyar kirki, Allah dai ya nuna min wannan Auren, shiyasa nake sonki kaf cikin haulata, idan kin ɓatawa Mutum rai kinsan yanda zaki faranta masa Allah karka kasheni da wuri." Dariya ce ta ƙwacewa Jummo ganin daga ambaton zata kaisu Makka har sun manta tsiyar da ta shuka musu ita kuwa INNO Uwar rashin so mutuwa, harda roƙon karta mutu da wuri, cikin ranta take cewa (Ko Gombe bazaku bari ba, bare Makka, ina ma zaku ƙara ganina ina Aure ya Garkuwa na, yasin ban sanku ba, ni wannan rugar ma ba sake zuwanta zanyi ba) a fili kuma dariya tayi tana kuma tsarasu tace. " To kuma idan ban kaiku Makka ba, waye zan kai, kune fa gatana Mamma nifa da zaki dage ayi wannan Auren nan da sati ɗaya, da nai miki alƙawarin sai na kori Wannan zainabun da ta dameki daga gidan duka har abada bazata dawo ba, kuma dai kinsan zan iya" Zaro idanunta INNO tayi ta cewa Jummo. " Ke Jummo kanki ɗaya kuwa, surikar taki kike cewa zaki kora, eh lallai baki da hankali." Mamma ce tace. " Wannan ma shine hankali yarinya za tayi abun arziki kike ƙoƙarin dakatar da, ita, Jummo daga yau na ɗaura ɗamarar aura miki Garkuwa muddun zaki yayanki yaƙin tumɓuke Zainabu." Tsalle Jummo tasa tare da furta. " Za kuwa aga tsiya yasin na rantse da Allah muddun kika aura min ya garkuwa sai na fidda miki da Zainabun." Ta ƙarisa Maganar tana ficewa da gudu cike da farin ciki, INNO ce ta kalli Mamma tace. " Kinsan me kike cewa kuwa, kina nunawa yarinya hanyar tsiya ta kori matar da ta, shekara talatin a gidan mijinta, to wai ma ina ruwanki da matar nan ne, tana gidan ta, kina gidan ku, garin ku ma ba ɗaya ba, amma kinbi kin ɗaga hankalinki a kanta." Murmushi Mamma tayi tana kallon INNO tace. " Haba kema kinsan abinda Zainabu ta tare min, kuma kin san alƙawari na ɗauka kafin na mutu sai murƙushe Auren Zainabu da ɗana Buba, kuma na samu wannan damar yanzu da nayi shekara talatin ban samu ba, zanyi amfani da soyayyar da Jummo take yiwa Garko na kawo ƙarshen Zainabu kuma nasan Jummo zata iya, kin sani INNO mugayen laifukan da Zainabu da danginta suka min, dole na ɗauki fansa ta hanyar raba Zainabu da farin cikin ta, kin san a rayuwar mace babu abinda za'a mata taji haushi ta shiga cikin damuwa da tashin hankali, irin a raba ta da gidan Auren ta, da yaranta wannan yafi komai ciwo, INNO harta yaranta sai nasa sun tsaneta, ki saka ido kiyi kallo kawai." Numfashi INNO ta sauƙe tare da cewa. " Mamma meyasa ke baki da yafiya ne, meyasa bazaki manta abinda ya faru shekara talatin baya ba, nasan ba a kyauta miki ba, kuma an tozarta ki, an nuna miki iko da fin ƙarfi amma dan Allah Mamma ki manta kiyi hkr tunda har anyi shekaru ya wuce haka." " Hmmm!!! Sai dai idan kene zaki nuna min iko akan jikarki, ki hanata tayani ɗaukar fansa, amma idan ba haka ba, baki da ikon hanani ɗaukar fansa." " Ko ɗaya bazan nuna miki iko akan Jummo ba, yanda take jika a wajena haka take a wajen ki." " To ki samin ido kawai." Numfashi INNO ta sauƙe tare da ɗauko wani zancen daban suka ɗaura a kai. Almajirai ne cike ƙofar gidan, kowane riƙe da Allo suna ta karatu, Baffa dake zaune a gefe ne ya miƙe ya shiga cikin gidan, Sikayel na zaune tana tankaɗen garin dawa, Baffa ya shigo, zama yayi gefen Sikayel tare da cewa. " Ina Jummo!!! Yau satin ta ɗaya bata zo ta biye karantun ta ba, ido na zuba mata amma naga alamar bata jin zuru yau idan na riƙe Jummo sai ranta ya ɓaci na fara gajiya da munanan halinta......." Baffa bai rufe bakinsa ba, almajiransa ya shigo da sallama sunkuyawa yayi tare da cewa. " Malam Yanzu Lamiɗo yayi aika, wai kaxo fada yanzu yana neman ka." Cike da mamaki Baffa yace. " Lamiɗo Kuma to Allah yasa lafiya, Sikayel bari naje kiran lamiɗo." Da a dawo lafiya Sikayel ta amsa Baffa ya fice darect fadar lamiɗo ya nufa. A gefe ya zauna yana gaishe da lamiɗo cike da girmamawa gefen sa ya kalla Yako da innar sa ne zaune sai dogari, lamiɗo gyaran murya yaya tare da cewa Baffa. " Malam Yaya kaji na aika ayi kiranka ko.?" Ɗaga kansa Baffa yayi alamun eh, lamiɗo ɗaurawa yayi da cewa. " To ganan Yako shine ya kawo min ƙarar jikarka Jummo" yanda Yako ya faɗawa lamiɗo haka ya mayarwa Baffa yanda akayi, shuru Baffa yayi babu musu duk abinda akace Jummo tayi zata aikata duban yako Baffa yayi tare da cewa. " Dan Allah Yako kuyi haƙuri na sani Jummo zata aikata fiye da abinda ka faɗa ina mai baka hkr insha Allah kuma zan mata faɗa bazata kuma ba, Inna kiyi hkr kiyi hkr." Darajar Baffa yasa innar Yako jin jikinta yayi sanyi, cike da girmama Baffa innar Yako tasa Yako ya yafe maganar lamiɗo sosai ya yiwa Baffa ƙorafi akan Jummo, shi dai Baffa hkr kawai yake bayarwa cike da ɓacin rai Baffa ya koma gida, cikin dace kuwa ya samu jummo ta dawo ai kuwa cike da faɗa Baffa ya ke yiwa Jummo magana. " Wato Jummo baki da hankali ko, ke kam sai yaushe zaki nutsu ki zamo cikakkiyar Mutum kullum kina nan tamkar marar hankali, wallahi ki nutsu ki fahimci rayuwa, idan bakiyi hankali da duniya ba, wallahi wata rana sai kinyi kuka da idanunki domin muddun akace baka da nutsuwa da tunani wata rana sai kinyi danasanin halayyar ki, yanzu ki faɗa min kwanan ki nawa rabonki da kizo ki biya karatun ki, yau sati guda, saboda rashin hankali da nutsuwa, kiyi hankali da rayuwa, karatun Alkur'ani shine gatan bawa, wawiya kawai dubeki kin girma har yanzu baki san kin girma ba, kin haɗa hankalinki da tuwo kin cinye, idan banda ke wawiya ce waye yake faɗa da namiji, mema zai haɗaki da Yako, to wallahi daga yau karna kuma jin kinyi faɗa da wani namiji idan kuma naji wallahi sai na bata miki rai shashs." Tunda Baffa yake wannan faɗar Jummo ta cuno baki sai ƙunƙuni take sanda Baffa yayi shuru sannan Jummo ta hau. " Haba dai Baffa shikenan dan lamiɗo ya kiraka ya gaya maka ƙarya da gaskiya sai ka yarda, ni dai wallahi wannan lamiɗon na tsanesa munafiki ne ga............" Bige bakin ta Baffa yayi bata ƙarisa Maganar ba yace. " Shi lamiɗon ne munafiki, kinga rashin hankalin naki ko, Allah ya shirye ki Jummo Allah ya kimtsa miki bakinki, shige ki bani waje." Juyawa tayi tana cuna baki ta shige bukkar INNO. *ABUJA CITY* Da sauri yake haɗa takaddun sa daga cikin office ɗin kasancewar time ɗin tashin sa yayi, gashi kuma gobe yake son ɗaukar hutu, na wata ɗaya yaje ganin gida sanye yake da kakin soja fuskarsa zagaye da saje farine tas dogo mai ɗan kauri, wayar sa dake gefe ce tayi ringin, a hankali ya maida kallon sa ga wayar *My Zarah* ya gani rubuce jikin screen ɗin wayar murmushi yayi tare da zama yana ɗaga wayar. " Hasken Khalil, ina shirin tashi daga office kina kira, ya akayi." Zarah dake kwance ruf da ciki taci kukanta ta ƙoshine ya sata ƙara sakin kuka ta kasa masa magana. Shuru khalil yayi yana sauraron kukan ta, cike da tashin hankali yace. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Oh Zarah wai yaushe zaki kirani ba tare da naji sautin kukan ki ba, kullum ke kina cikin ɗaga min hankali, burin ki kawai ki sani cikin damuwa haba Zarah." Zarah share hawayen ta tayi tare da cewa. " Haba Ya khalil meyasa bazaka tambaye ni damuwata ba, sai kawai ka hauni da mita bay........" " Dan Allah rufe min baki tambayar me zan miki bayan baki da wani ƙorafi da mita sai akan mahaifiyata, to na fara gajiya daga yau idan kinsan zaki kirani saboda ki kawo min ƙarar mahaifiyata ne, karki kuma kira na, idan kinga bazaki iya haƙuri da Momy ba, ki tafi gidan ku, domin kuwa bazan jure ƙorafi akan Momy ba." Yana faɗar hakan ya katse wayar sa, yana tsuka, yana mungun jin takaicin Zarah akan mahaifiyarsa, bata da wani aiki sai ƙorafin Momy, tashi yayi ya ƙarisa haɗa takaddun ya fice daga office ɗin *MAJOR IBRAHIM KHALIL BUBA* kenan cikakken Jami'in Soja......... Zarah tana jin ya katse kiran ta saki kuka mai cin Zuciya, " shikenan sai a dakeka a hanaka kuka, mahaifiyarsa ta min shi kuma ya kasa rarrashi na, rana zafi inuwa ƙuna, Momy tana cuta na a cikin gidan nan, amma bani da gatan da za'a bi kadu na, Allah kaine gatana Allah ka kawo wanda zai bimin haƙƙina.............." *Akwai waɗanda suka min ƙorafi dan Allah nabar littafin akan 100 saboda yanayin yau, to naji ƙorafin ku na barshi akan 100 ɗin* *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal ga masu TRANSFER ta account number na 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank* *Idan kuma katin waya zaku turo mtn card ne na 100 ta wannan numbern 08147537180* *Da zarar kin tura kuɗin sai kiyi screen short ki turo shaidar biya ta wannan numbern 08147537180 kuyi hanzarin biya domin kuwa araha yafi bashi, ina jiran masoyana su nuna min soyayya ta haƙiƙi nasan nafi ƙarfin 100 a wajenku, ina jiran masoyana na haƙiƙa.* Vote Share and comments *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah*✍🏻 [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *11 to 12* *Ƙauyen Tulde* Tunda Mamma tayi sallar asuba ta sammaka gidan INNO, a bukkar INNO ta sameta tana tasbihi, zama Mamma tayi sai da INNO ta ajiye carbin tace. " Lafiya Mamma kika doko wannan uban sammako haka." Taɓe baki Mamma tayi tare da cewa. " Hmmm!!! Ke dai INNO bari, zuwa nayi na sami mijinki Mlm yauta akan maganar da mukayi na tafiya da Jummo birni, jibi nake son mu tafi idan Allah yasa ya yadda." Murmushi INNO tayi tana gyara zaman ta tace. " Har shakka kike, aini bana tantama zai baki ita tunda yasan gaban Buba zata zauna, sannan daɗi da ƙari idan kika ce masa za'a sata a makarantar Boko, kinsan yana son Jummo tayi ilimin BOKO mai tsawo, da wannan zamu ruɗesa ya baki Jummo, amma fa Mamma ki cika alƙawari idan kunje kisa Buba ya saka Jummo makarantar Boko." Dariya Mamma tayi tace. " Haba INNO har kina tantama a kaina ai dole Jummo ta shiga makaranta." Tayi Maganar tana leƙo tsakar gidan ko zata ga Baffa, ta ɗan juma suna taɗi da INNO kafin Baffa ya shigo gidan, INNO da kanta ta masa magana, ya shigo ya sami Mamma a gefen gadon karamnon INNO ya zauna tare da cewa Mamma. " Inbali jam Mamma" Mamma itama cikin harshen fullanci ta amsa masa. " Sai jam, Mlm Yauta wajenka nazo da wata buƙatar, ina son zan koma can birni wajen ɗana Buba, shine nayi tunanin mai zai hana ka bani Jummo na haɗata da ƴar marigayi Sayoji A'illo mu koma can Birnin tare idan munje burina shine nayiwa Buba magana ya saka min su a makarantar Boko, suma su sami cikakkiyar ilimin BOKO, amma me kace." Shuru Baffa yayi yana nazarin maganganun Mamma tabbas yana son Jummo tayi karatun Boko dana addini, sai dai yana tsoron haɗa Jummo da Mamma sanin rashin kyawun halin Mamma, sai dai yana da tabbacin kuma idan har Buba yana nan bazai bar Jummo ta lalace ba, tabbas wannan ce kawai damar da yake da ita wanda Jummo zata samu cikakkiyar ilimin BOKO, numfashi ya sauƙe tare da cewa. " Mamma zan baki Jummo amma da sharafi idan har kin amince." Murmushi Mamma tayi tace. " Faɗi sharaɗinka insha Allah ni kuma zan ɗauka." Baffa duban Mamma yayi tare da cewa. " Muddun Jummo zata zauna dake, dole ne ki saka mata ido, kina hanata aikata wani aiki mummuna, idan kinga zata kauce hanya ki jawota ki nuna mata daidai, kuma dole ne tayi karatun addini bayan na boko, idan kin yarda da wannan sharaɗin na amince ki ɗauki Jummo ku tafi, Allah yasa inda zatayi hankali zataje." Cike da farin ciki Mamma tace. " To ai alhamdulillah!!! Duk waɗannan abinda ka lissafo, koda baka faɗa ba haƙƙine a kaina na sauƙesa karka damu na amince da sharuɗan ka." INNO ce tace. " To alhamdulillah!!! Hakan yayi, Allah yasa haka yafi alkairi, yaushe ne zaku tafi." INNO ta yiwa Mamma tambayar tamkar bata sani ba. " Jibi Lahadi zamu koma insha Allah.'' Baffa cewa yayi. " masha Allah Allah ya nuna mana zan sanar da uwar yarinyar." Yayi Maganar yana tashi ya fice, itama Mamma bata wani juma ba ta koma gidan ta, koda Baffa ya sanar da Sikayel, ranta baiso tafiyar ba, sai dai batayi jayayya ba jin Baffa ya amince da tafiyar, fatan alheri kawai tayi, farin ciki da murna kuwa wajen Jummo ba'a magana sanda INNO ta sanar da ita tafiyar murna kawai take zataje taga Garkuwanta, da gudu ta bar gidan, duk inda ta ga mutane sai ta faɗa musu zataje birni gidan su mijinta, haka ta wuni cike da farin ciki. A kwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau ta kama ranar Lahadi ranar da Jummo da Mamma zasu koma Birni tuni Mamma ta shirya, Tasiu mai taxi ta kira dake yasan har gidan Buba, ta ɗaukesa shata zai kaita har a gida, Jummo dangwalin kayanta ta ɗauka tare da kallon INNO sai kuma idanunta suka ciko da hawaye, shikenan yau zata rabu da INNO, itama dai INNO ranta duk babu daɗi, hanun Jummo ta kama tare da cewa. " Jummo yau zaki tafi ki barni ban sani ba ko zamu sake haɗuwa, sai dai zan sanar dake abu ɗaya a cikin rayuwa, karki taɓa wasa da addinin ki Sallah azumi yawan ambaton Allah, duk da kallon marar mutunci da ake min bana wasa da addini na, kema kin sani, ki riƙe Mamma tamkar ni, Allah ya miki albarka ya kareki daga sharrin shaidan da mutane." Ta ƙarisa Maganar tana share hawayen ta, Sikayel dake gefe ne cikin sanyin murya tace. " Jummo dan Allah idan kinje karki dinga musu rashin jin da kike anan ki riƙe mutuncin ki, babu ruwanki da rashin ki bi Rayuwa a hankali karki yadda ki zalunci kowa, idan kika kiyaye wannan zaki zauna da kowa lafiya Jummo haka duniya zata miki daɗi, idan kuma kika cuci wani babu shakka kema sai an cuceki Allah ya sa zuwan ki can sanadiyyar ɗaukakarki ne Allah ya miki albarka." Ameen Jummo tace tana kuka duk da son zuwa birni da take sai da taji bata son rabuwa dasu INNO babu wanda zata yiwa SALLAMA dama ba kawa bace da ita a cikin garin, koda ta samu Baffa ma a waje shima sosai ya mata nasiha da faɗa, INNO da kanta ta raka Jummo har gidan Mamma, a camma sabon shafin kukan suke, ita da Mamma, SOSAI suka sha kukan su suka godewa Allah, INNO na kallon Jummo da Mamma da A'illo suka shiga motar Tasiu, suna ɗaga mata hanu har suka ɓace, tun da suka kama hanyar cikin Gombe A'illo bata ko kalli inda Jummo take ba, haka ita Jummo kasancewar basa ko ga maciji akan Garkuwa. *GOMBE STATE* Wani irin Hom hom!!!! Ake dannawa get ɗin, da sauri baba mai gadi ya wangale get ɗin, jerin motoci ne sun kai 15 gabaki ɗaya sojoji ne a cikin su, sai wata baƙa wacce tasha tintak baka iya hango wanda ke ciki, yana ganin motocin ya tabbatar KHALIL ne ya shigo cikin garin, danna hancin motar sukayi, cikin compaunt ɗin gidan a parking space sukayi parking cikin sauri suka fito daga cikin motocin nasu, kowannen su hanunsa riƙe da bindiga, baƙar mota mai tintak ɗin suka zagaye ɗaya daga cikin su ne ya buɗe motar a hankali KHALIL ya fito daga cikin motar yana ɗaga musu hanu alamun su sauƙe bindigoginsu, cike da nutsuwa ya basu umarnin cewa kowa ya koma gida ya huta, Bala da Joseph ne kawai zasu tsaya, sannan ya shige part ɗin su, Momy dake zaune cikin falon ne taji sallamar KHALIL da sauri ta tashi cike da farin ciki, kasancewar tana mungun son khalil, cike da farin ciki shima ya rungume Momy yana cewa. " Welcome Momy nayi missing ɗinki." Murmushi Momy tayi tana ɗan buga bayan sa tace. " Welcome my love, sauƙar yaushe baka sanar damu zaka dawo yau ba, nasan Garko daya taro ka." Murmushi yayi yana zama cikin kujerun falo tare da zuba ido yaga ta inda Zarah zata fito sai dai babu alamun ta, (ko dai ta koma gidan nasu ne, da nace idan bazata iya ba ta koma) zuciyarsa ne ta tsinke, duban Momy yayi yace. " Momy ina Zarah ban ganta ba." Taɓe bakinta Momy tayi tace. " Tana can bedroom ɗinta tana baccin asara, yanzu na gama cin ubanta akan aiki ayi yarinya mai shegen son jikin tsiya, ke ba haihuwa ba kice bazaki aikatu ba, sai dai a baki kici ki kwanta, haba me za'ayi da macen da bata haihuwa." Runtse idanunsa Khalil yayi yana jin zafin maganganun Momy sai dai babu yanda ya iya kasancewarta uwa a garesa, shuru yayi baice komai ba, sai ma miƙewa yayi yace. " Bari na shiga Momy." " A fito lafiya" Momy tace tana jingina kanta jikin kujera. KHALIL kuwa haurawa yayi bedroom ɗin Zarah, tana ya hangota ruf da ciki sai shashsheƙar kuka take, ƙarasawa yayi jikin bedroom ɗin ya zauna a gefen ta, tare da saka hanu ya birkito ta jikinsa idanu ya ƙura mata cike da tausayinta domin kuwa yasan matsalarta duk akan mahaifiyarsa ne, numfashi ya sauƙe tare da saka hanu ya share mata hawayenta,a nutse yace. " My dear, kin san fa na hanaki wannan kwanciyar na ruf da ciki, Saboda haramun ne a musulunci babu kyau ki daina, wannan kukan naki shima bana so yana ɗaga min hankali, kuma zai iya sa miki ciwon kai, nasan matsalarki bata wuce tsakanin ki da Momy ne,zuwa yanzu yaci ace kin saba da damuwar Momy, ki daina saka damuwarta a ranki, ki share hawayen ki, dan Allah ki cigaba da haƙuri insha Allah komai zai wuce, ana son ɗan Adam ya kasance mutum mai yawan haƙuri, da apuwa, my dear ina miki wannan tunatarwa ne domin karki sha'afa ki kasa ɗaukar ƙaddarar ki, nine na kawoki gidan nan, kuma ban taɓa ƙuntata miki ba,. Kiyi hkr da abubuwan da Ammi take miki, bani da ƴancin dakatar da ita ko bata umarni, domin kuwa mahaifiyata ne, itace mai iko dani, dole na mata biyayya muddun ina son na gama da duniya lafiya, dan Allah Zarah ki tayani neman aljannata daga mahaifiyata ki daina nuna min damuwarta akan fuskarki bana jin daɗin hakan, kar wata rana ki tunzurani nayi abunda zai zamowa rayuwata matsala dan Allah my dear." Tashi Zarah tayi daga jikin sa tana jan majina cikin muryar kuka tace. " Ban taɓa manta waɗannan tunatarwar taka ba, saboda abune da ko yaushe kake tuna min, koda karatu ne yaci ace na haddace, bazan taɓa zama silar da zaka samu matsala da mahaifiyar ka ba, sai dai ya kamata ka dinga min adalci, ta hanyar nunawa Momy hanyar gaskiya Ubangiji da kansa yace ku faɗawa iyayenku gaskiya idan kunga sun kauce hanya, amma kai ko da sai ɗaya ne baka taɓa nunawa Momy rashin kyautawar abubuwan da take min ba, Ya Khalil na far............." Hanu KHALIL ya ɗaga mata fuskarsa a haɗe yace. " Ya isa haka my dear, nafi ƙaunar mahaifiyata fiye da komai a rayuwata ta duniya zan iya rabuwa da duk wanda zai nemi zamo mata matsala, ko ya nemi faɗa mata Magana, ciki kuwa har dake, Momy uwata ce wacce tayi ɗawainiya da rayuwata tun ina cikinta taci kashina da fitsarina, ta jure duk wata wahalata bata taɓa gajiyawa ba, dan haka bazan taɓa zama a gabanta na nuna mata bacin raina akan abinda take miki ba saboda kawai kina matata, hakan ba yana nufin kinfi uwata bane, daga Yau karki kuma cewa na nunawa Momy rashin facewar abinda take miki, ki cigaba da haƙuri insha Allah komai zai zamo tarihi." Wani irin baƙin ciki ne ya tokarewa Zarah wuya, wannan rashin ganin laifin Mahaifiyarsa da KHALIL baya yi yafi komai ƙona mata rai, kanta ta mayar ta kwanta, cike da damuwa, tsabar takaici ko ruwan wanka kasa tashi tayi ta haɗa masa, wannan wani irin baƙin ciki ne, mijinta yana da gidan sa, ta hanasa zama a ciki ta ajiyesa a gabanta saboda kawai ta ƙuntata mata, shima KHALIL ganin halin da take ciki baice mata komai ba da kansa yayi komansa ya gama, kasancewar zafin da ake ya sashi saka best da gajeren wando falo ya fito wajen Momy................ 😆😆😆😆 Naso na jira isowar Mamma CIKIN wannan gidan, da zai tara cakwakiya, nasan akwai Magana😆😆 bari dai muyi haƙuri sai gobe😛 🥰🥰 Ina fa ƙaunar ku masoyana sai sayan BOOK ɗin nan kuke, gaskiya ina mungun sonku irin sosai ɗin nan. *Naira 100 kacal zaku turo ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank, ko mtn card ta

Chapter 3 of 9