Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
ɗauka harya mutu cikin wa'azi yake mata, bayan mutuwarsa mahaifinku ya ɗaura daga inda Malam ya tsaya amma Mamma taƙi ji, akwai aminiyarta INNO itace take ƙara kangarar da ita, domin kuwa INNO gagararriyar tsohuwa ce mai taurin kan masifa, duk wani wa'azi da zaka yiwa Mamma sai INNO ta koresa, domin kuwa dalilin INNO Mamma taƙi dawowa cikin gari, muddun ba INNO bace ta daina shan sigari ba, Mamma bazata daina shan sigari ba." " Hmmm!!! Lallai kuwa naga alama domin kuwa ko yau dana bata kuɗi cewa tayi sai ta tsakurawa INNO wani abu a ciki tasha sigari, yama kamata fa mu tambayoyi malamai game da bawa Mamma kuɗi kinga dai sigari take sha dashi, kar muje ta dinga ɗiban zunubi da kuɗin mu tana yaɓa mana, amma dai wannan INNOn Allah ya kasheta mu huta." Murmushi Momy tayi tare da cewa. " A'a karka kuma kira mata mutuwa ka mata fatan Allah ya shiryesu duka, ya kamata kaje kayi wannan tambayar domin kuwa nima yana cimin tuwo a ƙwarya." " Shikenan Momy insha Allah zanje, kunyi waya da Khalil kuwa." " Eh ya kiran da safe yace ya nemi layinka baya tafiya." " Network ɗin Tulde gaskiya ba kyau ba lallai bane ya sameni, amma zan kirasa anjuma." Da to Momy ta amsa kafin Garkuwa ya tashi ya fice daga bedroom ɗin yayi nasa. Aunty Zarah cikin awa biyu ta gama girkin 9:00pm dai-dai, dake Sadiya ta tayata da miya, a daining ɗin suka jera sannan Zarah taje ta sanar da Momy ta gama da to Momy ta amsa sannan Aunty Zarah ta shige nata bedroom ɗin tsabar takaici da haushi da take ji yasa bazata iya cin abincin ba, haka ta kwanta da yunwa. Da misalin tara da rabi dai-dai Daddy ya shigo cikin gidan a gajiye sannu da zuwa Momy ta masa sannan ta kai masa ruwan wanka sai da yayi wanka sannan ya sauƙo falo, a tsakiyar falo aka shimfida masa darduma kasancewar baya cin abinci a daining, abinci Momy ta ɗauka ta kawo darduman ta ajiye, malmalar tuwo biyu ta saka masa da miyar ɗanyar kuɓewa, kasancewar Daddy mutum mai son tuwo ko dan ya tashi a ƙauye ne, cike da nutsuwa Daddy yake cin abincin Momy na gefen sa harya gama ruwa yasha sannan ya wanke hanunsa, idanunsa ya dago ya kalli Momy tare da cewa. " Zainab Garko ya dawo kuwa." " Eh ya dawo tun ɗazu yana bedroom ɗinsa." " Jeki kira min shi.?" Da to Momy ta amsa tare da tashi ta haura tare suka dawo da Garkuwa kusa da Daddy ya zauna tare da cewa. " Sannu da dawowa Daddy" "Yauwa sannu Garko ya ka samu Mamman tana lafiya dai ko.?" " Tana lafiya Daddy sai dai hali ne har yanzu bata fasa ba, ya kamata ka dawo da Mamma gidan nan idan akayi dace sai ta daina shan wannan sigarin." Girgiza kansa Daddy yayi tare da cewa. " Mamma bazata yadda ta dawo ba, ni na sani ka rabu da ita kawai mu cigaba ba da mata addu'a idan da rabon zata gyara ko a ina take zata gyara, gobe da safe ka tuna min zan aikeka kasuwa bakin Cross zakaje min shagon Alhaji yawale akwai saƙon da zaka amso min." " To shikenan Daddy Allah ya kaimu." Da ameen Daddy ya amsa yana miƙewa tsaye yace. " Bari naje na kwanta na gaji sosai." Kansa Garkuwa ya ɗaga sannan Daddy da Momy suka haura. Ko da misalin 12 na dare Sadiya bata tsallake umarnin Garkuwa ba, sanda ta tabbatar ƙafa ta ɗauke babu kowa ta faɗa bedroom ɗinsa, itace bata fito ba sai wajen 2 na dare, bedroom ɗin da take sauƙa idan tazo ta faɗa, tare da shigewa tolet, wankan tsarki tayi, sannan ta dawo bed dinta ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka mai cin rai, a hankali cikin shashsheƙar kukan take cewa. " Meyasa na kasance mai saɓon Allah meyasa bana iya kaucewa umarninsa, na kasan cikin mutanen da Ubangiji yake fushi dasu, ina ji ina gani na maida kaina karuwa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Meyasa na kamu da matsananciyar soyayyar Garkuwa, duk halin dana shiga sonka shine ya jamin, meyasa meyasa dole sai kayi zina dani, innalillahi!!!" Ta ƙarisa Maganar tana kuma sakin kuka, sosai take kukan idanunta suka bushe, har sai da aka yi sallar asuba sannan ta samu bacci ya dauketa, ko da gari ya waye da jikinta a sanyaye ta fito falon, Daddy ta fara gaishewa cike da sakin fuska ya amsa yana ce mata. " Halima kinzo mana hutu kenan, ya gidan naku, kika baro su.?" " Duk suna lafiya Daddy, suna gaishe ku" Momy ce tace. " Sadiya meya sameki idanunki suka kumbura, kuka kikayi ne." Ras zuciyarta ya buga, ɗan murmushi tayi tace. " Ciwo idanun suka kwana suna min shiyasa suka kumbura" Ta ƙarisa Maganar tana kallon gefe da gefe ko Garkuwa yana wajen wayam babu shi a wajen, numfashi ta sauƙe tare da zama aka cigaba da breakfast da ita, itama Aunty Zarah yau bata zauna anyi da ita ba da alamu fushin jiya ne bata huce ba. Bayan sun gama breakfast ɗin ne Sadiya ta haura bedroom ɗin Aunty Zarah tana zaune tayi shiru kusa da ita Sadiya ta zauna tare da cewa. " Good morning Aunty" '' morning Sadiya, Sadiya, jiya ƙarfe biyu na dare nagan ki bakin bedroom dinki zaki shiga, ina kika fita kikaje" Zuciyar Sadiya ne ya tsinke cike da tsoro muryar ta na rawa tace. " Ina kuma naje Aunty, daga ina kika ga na fito."? Tsurawa Sadiya ido Aunty Zarah tayi tare da cewa. " Banga inda kika fito ba, amma dai na ganki sanda kike ƙoƙarin shiga bedroom dinki, ina kikaje." Numfashi Sadiya ta sauƙe cikin zuciyarta tana godewa Allah da Aunty Zarah bata ga fitowar ta da bedroom ɗin Garkuwa ba, cike da waskewa tace. " Kitchen naje na dan ɗibi abinci naci yunwa ce ta tashe ni." " Okay,am dan Allah Sadiya kije ki gyara min falo da bedroom ɗin Momy kafin tazo ta fara min mita." Dariya Sadiya tayi tana miƙewa tace. " Kai Aunty Momyn ce mai mitar." " Eh mana!! Ayi mata kullum cikin takura mutum ita jikinta bazai taɓu ba, sai jikin wani, Allah dai ya dawo da khalil lafiya, dole ne fitar dani daga wannan gidan na gaji wallahi." Dariya kawai Sadiya tayi tare da ficewa taje ta hau aikin da Aunty Zarah ta sakata. *TULDEN FULANI* "INNO da Mamma zaune a cikin gidan Mamma gefen su Jummo ce, dukkan su hanunsu riƙe da sigari sai busawa suke, tagumi Jummo tayi tana kallon su, yanda suke busa sigari suna tauna goro, kamar ba Fulani ba, Jummo kasa shuru tayi tace musu. " Ikon Allah, duk wanda Allah ya shiryar shine shiryayye, umhm!!! Wasu dai wallahi su jira mutuwar su, muddun suka yadda suka mutu a haka babu abinda zai hana Allah babbaka mutum, ku zauna kuna haƙar sigari kuna tauna goro tamkar ƴan bariki, ya Allah kasa INNO da Mamma su................." Saurin yunƙura Mamma tayi tana bige bakin Jummo tace. " Kiinci kutumar ubanki, kaji min shegiyar yarinya dan ubanki sai kizo ki fara kona mu, Kafin Allah ya kona mu, shegiya mai bakin tsiya baki iya gani kiyi shuru, a hakan zan baki jikan nawa ki aura shegiya mai kai kamar ƙoƙiya." INNO ce tayi carap ta karɓa. " Barni da ita shegiya mai shegen baki, ke dai Jummo kin shiga Uku da bakinki bazai gani yayi shuru ba, to shan sigari yanzu muka ɗaura ɗamara sai muga shegen da ya isa ya hanamu a CIKIN garin nan, ko a ɗakin uwarki muke Shane, kaji min jaraba da nacin tsiya kekam Jummo da mayya ce wallahi sai kin cinye mutum ko kashin shi bazaki bari ba." Turo baki gaba Jummo tayi cike da jin haushi tayi tsalle ta dire tace. " Sai kuta zagina kuta zagina saboda kawai na faɗa muku gaskiya, kuma wallahi ko zaku kasheni bazan fasa faɗa ba, idan yaso ku tsire Ni, kuji Mamman nan dai har wani cewa kike (a haka zan baki jikan nawa ki shegiya mai kai kamar ƙoƙiya) tayi Maganar tana kwaikwayon Mamman ta ɗaura da cewa, da wani magulallen bakin ki, a wajen da ba hakwaran kirki, yo nida ke ɗin waye mai kai kamar koƙiyar, ai gara kaina ma da naki, ke naki kuma ai sai dai ace kamar ƙwallon goruba, ko kina so bakya so, ko zaki mutu karshen baƙin ciki sai na auri yaya garkuwa, ke kuma INNO na juyo kanki, mai ƙunnen ƙashi, idan aka barni dake ɗin me kika iya dani, dan Allah idan kuna so randa kuka mutu ma, a kunna muku sigarin a asa muku a bakinku ku je kabarin ku dashi ni ina ruwana waye Allah zai babbaka walakiri ya jibgi banza, ni ina nan duniya ina gaɗa da nanaye mun rage iri.........................." *Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne ku HANZARTA ku biya domin kuwa kuɗin babu tsada* *Ga masu TRANSFER to account number na zasu turo 150 kacal ta wannan account ɗin 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank* *Ga masu turo katin waya kuma zasu turo mtn card na 200 saboda idan an sai dashi yana rage farashi ta wannan numbern 08147537180* *Da zaran kin tura sai ki yi screen short ki turo shaidar biya ta wannan numbern 08147537180* Vote Like Share and comments *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah✍🏻* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata ƙawar sirri ƙawar amana *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. https://chat.whatsapp.com/E72lrz6syKr4CNvD9usiuA *Ga waɗanda suka min magana kan cewa wancan group ɗin ya cika sunyi joining yaƙi to ga wani amma fa ki sani iya Free page kawai zaki samu a ciki idan kina da ra'ayi biya kudinki kawai ki wuce wajen* *Dan Allah kar namiji ya shiga mata ne zallah, dan Allah karku shiga wannan gidan* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* Free page. ➰➰ *3 to 4* " Haba Mamma wai yaushe zaki gane Annabi ya faku ne wannan ba mutuncin ki bane wallahi shan sigari, da mutuncin ki, wallahi wannan da'a cikin gari ne da sai kin jawo mana abun gori, ya kamata kinsan kin girma, kusan 86 kike da shekaru yanzu amma ace har yanzu baki daina saɓon Allah ba, haba ya kamata ki daina shan wannan sigarin haka ki duba kiga yanda bakinki yayi baƙi tafin hannunki taɓin ƙafarki kaf ya rine ya koma baƙi saboda shan sigari shiyasa Khalil baya zuwa wajenki saboda ya tsani yazo ya ganki a wannan halin, wallahi idan kika mutu a haka wuta zaki shiga gara tun w......." Dakatar da Garkuwa Mamma tayi itama tana sauya fuska tace. " Dalla rufe min baki dan ubanka, shan sigari ne saɓon Allah, to ai mutuncin nawa ya juma da zubewa idan shan sigari shine rashin mutunci tunda tun kafin na haifi ubanka nake sha banga kuma shegen da zai hanani shanta ba, idan na shiga wutar ina ruwanka kabarin mu ɗaya ne da kai da zaka damu, dan ubansa shi kalilun Allah yasa kar yazo har abada ina ruwana dashi, ni mantawa ma nake dashi jikana ne a duniya, dan haka ka kiyaye i ko ubanka Buba bai isa ya hanani shan sigari ba, ni da sigari mutu ka raba takalmin kaza, dalla!!! Bani ashanata ai ba ubanka bane ya sai min ita, gacar wanda zakaje ka yiwa faɗa wacce bata da mutunci bata ƙaunar dangin mijinta bata ƙaunar wani ya raɓesa yaji sanyi Uwar ka, Zainabu nake faɗa ita zaka je ka yiwa wannan wa'azin ba niba da na gama da iyayen mijina lafiya." Ta ƙarisa Maganar tana wafce ashanar ta daga hanunsa ta kunna sigarin tana zuƙa, tare da wulla masa harara, sosai garkuwa yaji zafin maganganun Mamma akan mahaifiyarsa ya rasa menene tsakanin ta da Momy, basa shiri, haɗiye ɓacin ransa yayi tare da miƙewa tsaye yana kwalawa A'illo kira, A'illo dake cikin bukkar Mamma taji kiran Yaya Garkuwa ai kuwa da gudu ta fito tana. " Oyoyo Bandirawo!! Yaushe kazo ɗazu nake cewa, Ya Jalo yaushe zaka zo yace min bai sani ba sannu da zuwa." Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa. " Yanzu shigowata Ai ina Jalon yake zai shigowa da Mamma kaya a cikin mota ni zan koma ne yanzu." Ɗan murmushi tayi, harga Allah bataji daɗin tafiyar da Garkuwa zaiyi ba da wuri haka, kallon sa yana kwantar mata da hankali, duk da tasan ya garkuwa yafi ƙarfin ta, amma zuciyarta na mungun ƙaunarsa, cewa tayi. " Ya Jalo yanzu ya fice kasuwa, amma dai banji daɗin tafiyar da zakayi ba, yanzu fa kazo meyasa bazaka kwana ba." Mamma ce tayi carap tace. " Saboda naci ubansa na faɗa masa gaskiya, shi kuma ga ɗan masu ido da kwalli wanda ba'a masa faɗa idan kaga dama ka dawo tsuntsu sai ka bar garin da wuri, kai ga isasshe malakakke baza'a faɗi lefin uwarka ba, to ka buɗe waɗannan fala falan kunnuwan naka masu kama da ƙosai kaji, Uwarka bata kirki bata da mutunci ubanka kuma ya zama hotiho, idan kaje ka faɗawa gagararriyar Uwar taka cewa nice na faɗa har kana wani haɗa min rai dama ya fuskar taka take kullum a haɗe tamkar hadari, kaga fice min daga gida ka koma inda ka fito." Dariya ce ta ƙwacewa Garkuwa har haƙwaransa suka bayyana dimple ɗinsa ya loɓa yace. " Dan Allah dubeki ko kunya bakya ji, kinsa surikar ki a gaba tamkar zaki kasheta itako bata ma san kinayi ba, waima ke da kinyi zaton wannan ɓaɓatun da kike shi zaisa na tafi, to bashi bane dama can banzo da niyar kwana ba, a yau zan juya, kuma wallahi bazan fasa faɗa miki shan sigari haramun bane kuma zai kaiki ga wuta idan baki daina ba aljanna sai dai kiga muna shiga, kin wani tsareni da mitsimitsin idanunki tamkar ƙwarƙwata wai ke ga masifaffiyar tsohuwa, ki gyara ko ki shiga Uku." Ya ƙarisa Maganar yana zaro dubu talatin a cikin aljihunsa ya ajiye mata yana cewa. " Da alamu talauci ke saki faɗa yau ga wannan na taimaka miki badan halinki ba, kuma idan kika sha sigari da kuɗina ban yafe ba." A'illo dariya tasa ganin dramar Mamma da Ya Garkuwa dama sun saba da wannan faɗan duk sanda yazo sai sun rikito suke dawowa dai-dai Mamma haɗe girar sama data ƙasa tayi tana ƙarewa kuɗin kallon wulaƙanci tace. " Ka faɗawa ubanka Buba, domin kuwa har idanuna sunso sufi na ubanka girma , ubanka Buba shine mai ido kamar ƙwarƙwata kuma dan uwarka zainabu, da wannan kuɗin naka zan sayi sigari harsu ƙare, kai har aminiyata INNO sai na tsakura mata wannan kuɗin itama ta zuƙi koda kwali goma ne da kuɗin idan ma zunubin ne kaima sai ka samu naka tunda ka bamu gudumowa." " Hmmm!!! Wannan tsohuwa INNO wannan INNOn ina mungun jin haushin ta, duk harda ita a cikin wanda suke daɗa kaiki ga hallaka, Allah dai ya shirya ku, amma dai mun haɗu da jarabawa tunda Allah ya haɗamu daku." Fesar da hayaƙin sigarin Mamma tayi tace. " Oho dai munfi ƙarfin ku, waima ya maganar Auren naka da Jummo, dan dai wallahi sai ka Aure ta." Tsuka garkuwa yaja yare da haɗe rai yace. " Har kina wallahi Saboda kece ubana, to idan kin isa kimin Auren dole, amma Allah ya isa tsakanina dake Mamma wannan jakar yarinyar kike dangantani da ita dan kawai ina wajenki mtsss." yayi tsuka yana kallon A'illo yace. "A'i muje ki shigo da wasu kayan idan naga yara a waje sai su tayaki ko." Yayi Maganar yana ficewa ba tare da ya yiwa Mamma sallama ba, ya tsani koda sunan yarinyar a kira masa, ba ƙaunar ta ko kaɗan, A'illo bayan sa tabi tana murmushi, Mamma kuwa mita ta hau tana cewa. " Kaji ɗan ƙwal Uba to dan ubanka idan ban haifeka ba, ai na haifi ubanka koma wallahi tunda kace sai na nuna maka na isa, baka da wata mata sai Jummo kaji min yaro dai mai baƙin halin tsiya, kai kullum cikin hali mtsss!!!" Ta ƙarisa mitar tana fesar da hayaƙin sigarin, shi kuwa Garkuwa fitarsa ya samu yara a waje ya basa 5k suka shigo wa da Mamma kayan abinci, dubu goma ya bawa A'illo sannan yaja motar sa ya tafi ba tare daya haɗu da Jummo ba. " Wayyo Allah na shiga Uku!!!! Wayyo na shiga Uku na lalace, wayyo Allah na!!!" Jummo ce ta shigo gidan su da wannan ihun ta zauna a ƙasa sai rafkar kukan take, Sikayel da gudu ta fito tare da ƴar Jummo Boɗɗo a tsorace, INNO kuwa tana can banɗaki tana gudawa tunda Jummo ta mata zance mutuwa da rayuwar kabari take sintirin jawo, da sauri INNO ta fito daga bayin ko butar bata ɗauka ba, tana cewa. " Wani shege tsinannan ne ya saki kuka, wani shegen ne?" Tayi Maganar tana karisowa wajen Sikayel jikinta na ɓari take cewa. " Menene ya sameki Jummo, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Kiyi magana mana Jummo keda waye."? Ƙin yin magana tayi sai da taga INNO ta iso wajen ta fara cewa. " Bazai aureni ba INNO yace baya sona, jikan Mamma na binni, wallahi shi nake so ɗan gaye ne, kuma kyakkyawa, ni dai na shiga Uku mutuwa zanyi INNO zan mutu idan bazai aureni ba." Wani ƙuwƙuw cikin INNO ya yi jin Jummo na kiran zata mutu, cikin rawar jiki tace. " Ke dalla ki daina kirawo wannan mutuwar bazaki mutu ba, ehe, badai Garko bane to kwantar da hankalin ki, kamar kin aure shi, ai dai jikin Aminiya Mamma ne, karki damu zamu kitsa mu haɗa, karkaɗe jikin ki ki tashi kije ki sayo min sigari." Wage yalon hakwaranta Jummo tayi tace. " Da gaske zai Aure ni INNO ni dai wallahi shi nake so." " Kwarai kuwa zai aureki." Dariya Jummo tasa cike da murna ta miƙe tsaye tana cewa. " Bani kuɗin sigarin na sayo miki, Allah ya barni dake INNO ta, ki daɗe kiyi ƙargo kiyi shekaru irin na dabino." Sikayel cike da takaici da haushi tace. " Amma Jummo baki da mutunci baki da kirki wallahi, yanzu tsabar ɗaukar alhaki akan wannan shirmen zaki shigo da ihu tamkar an kasheki ki tsinka mana zuciya, kekam wacce irin mutum ne Jummo wawiya marar lissafi." INNO ce ta hau kan Sikayel da faɗa tana cewa. " Kul kul ɗinki!!! Kiyayeni wallahi, karki kuskura ki ɓata mata rai ina ruwanki wani gulman ne yace ki fito, tayi ihun ai dai akan rayuwarta take ihun yau naji tsiya a daki mutum ace za'a hanasa kuka to baki isa ba wallahi baki isa kisa min jika a gaba ba." Shuru Sikayel tayi idanunta suka ciko da hawaye tana mungun jin zafin Rayuwar da INNO take ɗaura Jummo akai, domin kuwa ita macece gidan wani zata idan har ta tafi a haka tabbas akwai matsala, juyawa tayi cike da ɗacin rai suka koma bukkar su, Jummo kuwa cuno baki tayi, INNO kuɗi ta ciro naira hamsin ta danƙawa Jummo tace. " Rabu dasu jeki sayo min sigari ƴar kwali yanzu ki dawo muje gidan Mamman." Ai kuwa da gudu Jummo ta fita sayowa INNO sigari. *GOMBE LOCAL GOVT* *NEW G R A* wani makeken get Garkuwa ke dannawa Hom hom!!! Gaban gidan kansa abin kallo ne bare kuma idan an shiga ciki mai gadi ne ya wangale get ɗin danna hancin motar Garkuwa yayi cikin gidan wohoho kuzo kuga kyawu cikin gidan, kana kallon gidan zaka tabbatar da gidan attajirin mai kuɗi ne, parking space yayi parking a hankali ya fito daga cikin motar, ya nufi part ɗin mahaifiyar tasa, babban falo ne mai cike da kayan alatu wanda aka ƙawata sa da adon Black and White, sosai falon yayi kyau babu kowa cikin folon shuru, kansa ya ɗaga ya zubawa babban elagement ɗin dake manna a falon kallo, wani dattijo ne fari kyakkyawa gefen sa wata dattijiwar mace ce caculate color ita ba fara ba ita ba baƙa ba, sai a hanun damanta hoton wani kyakkyawan saurayi da kakin soja a jikinsa fari sol gefen Wannan dattijon kuma garkuwa ne, sai wata ƙaramar yarinya Black beauty a tsakiyarsu, a ƙasan hoton anyi rubutu da manyan harufa *ALHAJI ABUBAKAR BUBA TULDE FAMILY* murmushi Garkuwa yayi yana ƙarewa ahalin nasa, muryar Zarah yaji tana cewa. " Bandirawo!! Yaushe ka tafi harka dawo"? Murmushi Garkuwa yayi tare da komawa ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna yana cewa. " Daman ai a yau zan dawo matar Babban yaya, ina Momy naji gidan shuru."? " Momy tana bedroom ɗin ta da alamu ma wanka ta shiga, mutumiyar ka tazo Sadiya tun ɗazu take tambayar ka." Murmushi Garkuwa ya saki cikin zuciyarsa ya furta, (Yau akwai holewa kenan, hmmm ita a nata tunanin zan aureta ne, daga ranar dana gama da jikinta daga ranar zan shafe babin rayuwarki.) A zahiri kuma sai ya haɗe fuska gudun kar Aunty Zarah ta fahimci akwai wani abu a tsakanin su, domin kuwa a hankali yake takunsa yamutsa fuskarsa yayi tare da cewa. " Ayya ta tafi kenan." " No bata tafi ba, kasan sunyi hutu, anan zatayi nata hutun, nina roki mama tabar min ita muyi hutu a nan." Da okey garkuwa ya amsa ya tashi ya haura bedroom ɗinsa, ita kuwa Aunty Zarah ko a zuciyarta bata kawo Garkuwa yana lalata da ƙanwarta ba, ɗauka kawai take shakuwace na zaman tare a tsakanin su................. Wannan kenan muje zuwa mahaukaci ya hau kura yanzu aka fara labarin. *Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne* *Wanda zaiyi TRANSFER to account number na 150 zai bada 0006064512 Rashida Usman jaiz bank.* *Ga masu turo katin waya kuma zasu turo da 200 ta wannan numbern 08147537180* *Sannan ku turo da shaidar biya ta wannan numbern 08147537180* *Ga ƴan Niger kuma naji ƙorafin ku, karku damu kuma baza'a barku a baya ba, kumin magana ta wannan numbern 08147537180 zan faɗa muku yanda zaku biya kuɗin ku* *Masoya naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin hanu biyu, dayawa daga cikin ku sun fara biyan kuɗin su, naji daɗi sosai Allah yabar ƙauna* Vote Share and comments. *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah✍🏻* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *Free page* ➰➰ *7 to 8* Sake baki da hanci su INNO sukayi suna duban Jummo, takalmi Mamma ta ɗauka ta jefa mata tare da cewa. " Eh lallai wuyanki ya isa yanka Jummo kin isa, to tashi ki bar bukkar nan kafin ki dake mu, tunda kin balaga ƙirjinki ya cika, kin fara zubda

Chapter 2 of 9