Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
haka tayi cikin gida a guje, Goggonta ta iske a zaune tana lazimi, zama tayi a gefen ta ta fara gaya mata komai tun daga sanda ta samu wayar, tana me buɗe wayan.
Wayar keypad ne na itel hadda tsallan ta na murna kuwa
Muryar goggo taji tace
"Ba wai tsalle ba, saura ki dinga rashin ji, sannan idan yayan naki ya shigo ki masa godiya idan ba haka ba zance masa ya ƙwace wayar sa"
Fatima ne tace
"Kai goggo, godiya na nawa kuma, ko danma zan sake gode masa godiyar meye ma duniyar?"
Daga haka ta kunna wayar ganin harda sim a ciki tace gobe da safe zata kira sadiya ta fada mata tayi waya, daga haka ta shige dakin Goggonta ta kwanta akan ƴar katifar ta tayi baccin ta tare da rungume wayar hadda kwalin a jikin ta.
Wannan kenan.
Da safe ta ƙira Sadiya suka gaisa tace mata ai tayi waya yayanta ne ya siya mata, bayan sun ɗanyi magana tace mata se anjima ta kashe
Banɗaki taje da niyyan tayi wanka se ta sake ganin ruwa an ajiye a cikin bokiti, har ta dauka zata yi wanka ko dan ta tsokani Tala ma sai ta sake shawara, fita tayi ta ɗebo wani tayi dashi se ta juye na cikin bokitin a cikin wanda tayi wankan ta ajiye sa a bakin ƙofa yanda za'a dauka da na cikin banɗakin tayi ta fice a banɗakin, tun kafin ta isa ta hango babarta Tala ta fito da daura ƙirji tana dariya ƙasa ƙasa tayi hanyar banɗaki, ganin tabbacin Fatima tayi wanka da wanda ta ajiye mata se ita kuma tayi da na bakin ƙofan, a tunanin ta dan Fatiman ta tsokane tane tayi da nata se ta ɗebo mata wani.
Fatima kuwa bata bi ta kanta ba tayi shirinta ta fice zuwa gidan Hanne, anan ta tadda su saude da Barira, nuna musu wayar ta tayi suka dinga taya ta murna, su Hanne se sheqin amarci ake
Se can bayan azahar ta koma gida, anan take jin labari a bakin Iro wai an tafi da Tala asibitin nangere wai jikin ta sunyi ƙuraje manya manya se fashewa suke suna sake fitowa, dariya kamar ze kashe Fatima dan har seda ta kwanta a ƙasa, sallaman Isuhu taji, dena dariyar tayi tayi hanyar dakin su ba tare da ta masa magana ba, gani tayi ya karbo abinci a gun Inna Larai, daga nan ya tisa keyar ta suka kama hanyar Nangere, hawa kan mashin ɗin da ya karbi tayi suka kama hanya, dariya kamar ze kashe Fatima a hanyan musamman idan ta tuna yanzu fa zata je ne ta kalla kalan ƙurajijjikan da suka fitowa Talan, ganin dariyan nata yaqi ƙarewa isuhu yace ze jefar da ita in bata yi masa shiru ba, shine fa tayi shirun
Koda suka je direct emergency suka wuce, ɗaki ne da gadaje kusan sha biyar a ciki, idanunta ta fara waiwayawa, me gari ta fara hangowa a tsaye goggo kuma a zaune akan wani kujera, sai Tala dake kwance akan gado kamar gawa fuskan ta da kuma hannayen ta da ƙafafuwan ta an naɗe su da bandeji tayi kalar abun tausayi, tun daga nesa Fatima ta fara dariya, da ta iso dab kuwa seda ta tsugunna dan dariya, Me Gari Kamar su make ta shida goggo, isuhu kam seda ya ranqwashe ta kafin ta tsagaita.
Gaida su Me Gari suka yi sannan suka tambaye jikin nata aka ce da sauki.
After A While
Bayan kwanakin nan abubuwa da dama sun faru, na farko dai Tala ce da ta jima da warkewa ta ƙullaci Fatima, dan ƙurajijjikan jikin ta seda suka yi sati biyu suka warke kafin aka sallame ta wanda ta ɗora laifin akan Fatima ne, da Fatima tayi wanka da ruwan da yanzu ita ce a cikin condition din da itan take ciki, na biyu kuma tunda Fatima tayi waya hankalin ƴan garin gabur baki ɗaya ya kwanta, yaro se yayi kwanaki dayawa abinsa ba'a taɓa shi ba, alaqar ta da iliya kuwa yayi gaba sosai dan ko wane lokaci ze iya turowa duk da a ranta ba san hakan take ba, shi kuma Isuhu ido kawai ya zuba yana ganin ikon Allah.
Bayan wata ɗaya
Amfanin gonan me gari yayi matuqar kyau sosai, ya siyar da na siyarwa ya kyautar da na kyautarwa da na Zakka sannan ya kuma yi sadaka da na sadaka, ana cikin haka kwatsam, sega Iliya da tawagar sa
Zuwa suka yi suka tattauna ran da yakamata a sanya biki, da alƙawarin nan da satika uku suka yi tafiyar su
Bayan sati uku kuwa suka dawo
A fadar me gari suka iske shi shida jama'arsa, saɓanin wancan lokacin da suka zo da fara'a, wannan karan fuskokin su a matuqar ɗaure suka zo
Su Me Gari suna ta mamakin wannan lamarin sede basu ce komai ba
Ko gaisuwan arziƙi wannan karan basu yi ba, Me Gari dai zuciyarsa se tsinkewa take, magana suka fara yi wanda faɗar ko wacce kalma daidai take da bugawar zuciyar Me Gari, be tsinke da lamarin ba seda Iliya ya matso gaba shima fuskar sa a murtuƙe yana me cewa
"Nidai Baba ayı haƙuri na fasa auren Fatima, hakanan na fasa dan gashin kaina ba wani bane ya saka ni ba, ji nayi bazan iya auren yarinya marar tarbiyya da rashin nutsuwa ba, amin afuwa dan Allah", daga haka ya miqe ya ɗan ja baya, karo yayi da Isuhu, fuskar isuhu kamar na hadari saboda ɓacin rai, fisabilillah wannan wanne kalan tozarci ne? Tun tuni yasan ba auren ta zeyi ba yake kula ta? Shi daman tunda yagan sa be yadda dashi ba, yasan daman wataƙila dan kyanta yake santa toh bari ya koya masa hankali, duk da ba me gari bane ya haife shi shi ɗin Uba ne a gare sa, saboda haka ba ze bari wani ya tozarta shi ya ƙyale shi ba, daga haka ya kama kaiwa Iliya naushi a fuska, rirriqe sa su Baba Liman suka yi da ƙyar, ba'a ankara ba aka ga me gari ya faɗi warwas a ƙasa, da gudu isuhu ya sake Iliya yayi kan Me Gari
Kansa yayi yana me jijjiga sa amma Me Gari baya ko motsi, cikin tashin hankali yayi cikin gida da gudu, ɗakin Me Gari ya shiga ya fara dube dube, yana ta dubawa be samu ba, se daga karshe ya zaro makullin motar Me Garin da yake aljihun rigar sa yayi waje da gudu, duk abinda suke babu wanda ya sani a cikin gidan, koda ya fita kama Me Gari suka yi suka sa a cikin mota, ya fara driving, su Baba Liman ne suka cire ma Me Gari malum malum din jikin sa dan da alamu ya shaqe sa gashi dakyar yake numfashi, Allah Sarki waifa kayan ya saka ne saboda a saka auren ƴa mafi soyuwa a gunsa se kuma ga abinda ya faru.
Tafiyar minti 15 ya kai su asibitin nangere saboda yanda isuhu yake tsala gudu, Ana zuwa aka yi emergency dashi, koda likitoci suka ga irin condition din da yake ciki suka fara bashi taimakon gaggawa, bayan haka suka fara dube dube, su gwada wannan su gwada wancan ganin fa sun kasa shawo kansa yasa suka ƙira ambulance da wuri aka wuce dashi asibitin Potiskum Baba Liman a gefensa Iliya kuma na binsu a baya da motar Me Garin, jiniya se tashi yake duk inda motar tabi har aka isa General Hospital babban asibitin Potiskum kenan, can ɗinma hakan ne ta kasance, duƙufa suka yi akansa suma suka dinga gwaje gwaje, ganin dai sun kasa gane matsalar nan da nan akayi referring nasu zuwa 'Yobe State University Teaching Hospital' dake cikin Garin Damaturu.
Ayyah, Me Gari Babu lapiya, toh Allah ya basa Lapiya Ameen.🙏
Mu Haɗe a shafi na gaba.
Fadrees che.🤍😉
Dan Allah Follow my Account and Vote and Share.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
❥♡👸ME GARI FATIMA.!!👸♡❥
(The Female Village Head) 🦋 🦋🤍

Na Fatima Idriss Bello🤍
FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
20. ME GARI'S SUDDEN SICKNESS/DAMATURU PALACE
Cikin matuqar tsala gudu ambulance ɗin ya dauki hanyar Damaturu, dama daga Potiskum zuwa Damaturu tafiyar awa guda ce dan haka cikin mintinan da basu wuce arba'in ba suka shigo garin Damaturu me albarka, suna isowa direct Teaching Hospital ɗin suka wuce, asibiti ne babba sosai da sosai wanda yana ɗaya daga jerin asibitoci manya manya a faɗin ƙasar nan namu ta Nigeria domin kamar asibitin ƙasar waje mutum yake, lokacin da suka shiga ciki sallan la'asar ake, ana zuwa aka wuce dashi emergency nan da nan likitoci suka duƙufa akan sa, ganin numfashin sa yana seizing ya sanya aka saka masa oxygen daga haka aka fara bincike akan matsalar sa, wanda matsalar tasa ta basu tsoro da sagewar gwiwa dan basu saba ganin irin case ɗin ba
Saboda complication na case nasa seda suka sha baqar wahala dan se bayan Isha suka samu mafita, alluran bacci suka masa kamin suka fiffito suka zazzauna dan su tattauna akan mafitar.
Shidai cutar da yake dauke dashi Blood Cancer ne, wanda yake a matakin stage na uku wanda hakan is very rare and high, and if care is not taken he might lose his life, duk da a binciken da suka yi ya nuna musu ba'a taɓa treating ɗin cutar a jikin sa ba, which means akwai probabilityn be ma jima da kamuwa da cutan ba
Se daga ƙarshe suka yi coming to conclusion akan mafita ɗin, mafitar dai ɗaya ce Tak, cutar da Me Gari yake dauke dashi ba kowane likita bane ze iya treating ɗin case ɗin face Dr. Shettima Bukar Goni II Ibn El-Kanemi wanda aka fi sani da (Ba Prince), wanda ya kasance ɗa ne agun Mai Damaturu, wato Sarki Muhammad Goni II Ibn El-Kanemi.
____________
A can Gabur kuwa, koda Tala ta leqa taga guri ya hargitse ana ta kace nace nan da nan ta saki murmushin jindaɗi dan takai kusan minti biyar tana kallo kamin ta koma ciki ranta fari sal, domin burin ta ya cika a duniya, ta tarwatsa farin cikin Fatima.
Da farko bata so ta mata haka ba, sede kuma ta lura yarinyar tun tana ƙarama ta gane cewar ita tayi ƙulle ƙulle har ta auri Me Gari kuma hakan ya faru ne a dalilin jin hirar ta da tayi da wata ƴar uwarta, dan tun da ta taso bata da mashinshini, kowa baya santa sobada munin ta, daga haka kuma zuciyarta ya bude har ta aikata abinda ta aikata ta auri Me Gari saboda kuɗinsa, dan a ganin ta ba jimawa zeyi ba a doron ƙasa duba da yanda ya tsufa, shiyasa tun Fatiman tana ƴar ƙaramarta ta aikata abinda ta aikata aka maida yarinya marar ji, dan su Me Gari rana daya suka ga yarinya ta koma me ƙiriniya sosai
Murmushin jindaɗi ta sake saki tana ne shigewa cikin dakin ta gun yaranta.
Su Fatima kuma suna zaune aka kai ga an kira azahar kuma suka ga shiru dan a cikin Isuhu da me gari ba wanda ya shigo, daman ita tunda ta samu wayan nan take buga game abinta musamman idan ba waya zata yi da Ilıya ko Sadiya ba, goggo kuwa daman lazimin ta take, daga lazimin bacci ya kwashe ta akan sallaya,sefa yanzu da suka ga shiru.
Hankalin su be ƙara tashi ba seda suka ga an kira la'asar nanma shiru, nan da nan Fatima tayi waje, hango fadar Me Gari tayi babu kowa a gun, mamaki ne ya kama ta, tsayawa tayi tana tunanin a ina zata samu Isuhu, komawa cikin gida tayi ta kira layinsa baya dauka, wucewa gidan Baba Liman tayi ganin haka duk da bata da tabbacin zata same sa shima tunda bata ga Me Gari ba dan kusan kullum suna tare da Baba Liman ɗin, sannan hakanan take ji hankalin ta ya kasa kwanciya akan al'amarin nan, se take jin jikin ta a sanyaye, sallama tayi a kofar gidan ta fara zura ƙafar ta a ciki, tun kafin ta ƙarasa taji ana mayar da abinda ya faru a ƙofar gidan nasu a cikin gidan Baba Liman ɗin, wanda su sam basu da masaniya akai.
Daskarewa Fatima tayi a gun jikin ta ya kama karkarwa.
Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji'un, abinda take ta maimaita wa kenan dan bata san wane kalan tashin hankali take ciki ba (abinda ake san ko wane cikakken musulmi ya fada kenan idan ya tsinci kanshi cikin tashin hankali).
Shin da faduwar Me Gari zata ji ko kuma da fasa aurenta da Ilıya yayi?
Duk da cewar ita kanta ba san auren take ba sam abin se ya tsaya mata a ƙahon zuci, se yayi mata zafi ƙwarai.
Wannan wannan kalan tashin hankali ne?, wannan wane kalan ƙaddara ne fisabilillahi?
Lahaula Fi Sha'atillah, daga haka ta durqushe a wajen😭.
___________
BONUS
MAI DAMATURU’S PALACE
Kamar dai yadda aka sani, Masarautar Damaturu ya samo asali ne daga Babban Masarautar Jihar Bornon nan wato 'Kanem Borno', wanda shi kuma Kanem Borno shine masarautar Maiduguri a yanzu, ita kanta Kanem Bornon ta samo asali ne daga Lake Chad, sannan sun amshi musulunci tun a ƙarni na tara wasu kuma suka ce a ƙarni na goma sha shida.
Sannan ana ƙiran sarki da 'Mai' ne a duk gidajen sarautar jihar Borno da Yobe, (shiyasa yawanci zaku ga ina cewa Mai Nangere, Mai Fika and so on, sunan title ɗin kenan, a matsayin ace Sarkin Nangere.)
Masarautar Damaturu masarauta ce very Modern wato na zamani, me bala'in arziƙi, idan nace arziƙi ina nufin kuɗi, kudin ma masu bala'in yawa, wanda ba'a ma san ya za'a yi dasu ba saboda tsabar yawa shi yasa in ka duba zaka ga babu talaka a garin, sannan idan abun neman taimako ya taso sune zaka ga sun bada gudunmawan zallar kudi, wanda yawan kudin da suke badawan ze haukata tunanin mutum.
Masarautar Damaturu Wani hargitsattsen girma ne dashi wanda ni Fadrees bazan iya misaltashi ba, abu ɗaya kawai na sani, itace masarautar da Sarkin wancan zamanin ya saka turawa da kansu suka gina shi, an kuma gina shi ne da tsantsar ruwan gold, wato gold aka narka kamin aka gina masarautar.
Idan ka shiga farkon masarautar rubutune zaka ga an rubuta da kalmar Larabci.
A gefen masarautar kuwa wani tangamemen masallaci ne shima ginin nashi kamar yanda aka tsara na masarautar ne wato da ruwan gold ɗin.
Cikin masarautar kuwa akwai gurare daban daban kama daga sashen kowa na cikin gidan ma'ana daga kan Sarki yayi ƙasa, akwai gardens akwai museum(ɗakin tarihi) da kuma manya manyan corridors, akwai car parks a kowane sashe har gurin parkıng helicopter akwai a ciki amma ta bangaren Shehun Damaturun ne (Sarkin Damaturun, ko ace Mai Damaturu), sannan akwai stable (barga, gidan dokuna) a almost ko wane sashe na palace ɗin, dan ba kowane masarauta keda yalwar dokuna kamar su ba duba da yanda dokuna suka yi bala'in tsada, amma su ‘yan nan masarautar daga ƙasashen Larabawa ake kawo musu dokunan su ma kuma ƙosassu.
Masarautar Damaturu
Fada
Royal Museum
Royal Corridor
Parlourn Mai Damaturu
Parlourn matar Mai Damaturu
Ba Prince Bedroom.
Royal Dinning Hall.
___________
Toh fa jama'a kamar dai yadda kuka sani a yau yau Ni FADREES na kawo ƙarshen Free pages din littafina me suna 'ME GARI FATIMA'
SHIN;
ME GARI ZE SAMU LAPIYA KUWA???
ME FATIMA ZATA YIWA ILIYA DAN TA HUCE WULAKANCIN DA YA MATA???
ISUHU FA??
YAYA GOGGO ZATA JI AKAN RASHIN LAFIYAR ME GARI DA KUMA FASA AUREN FATIMA DA ILIYA YAYI???
INA BABARTA TALA FA??? SHIN DAƊI ZATA JI GAME DA RASHIN LAPIYAR ME GARI KO A'A, SANNAN YAYA ZASU JI IDAN SUKA GANE IRIN TUGGUN TA???
TUKUNNA MA, YAUSHE NE WAI FATIMA ZATA ZAMA ME GARI???
WAYE BA PRINCE MENENE HALAYYAR SA???🤷
KUNSAN DAI DOLE FATIMA BA PRINCE ZATA AURA TOH TA YAYA HAKAN ZE KASANCE BAYAN ITA ƊIN ME GARI CE, SANNAN BATA MA SAN DA ZAMAN SA BA SHIMA KUMA HAKA ƊIN NE??
TA YAYA ZASU FARA SOYAYYAR MA???
ME ZATA JE TA TARAR A MASARAUTAR DAMATURU???
KUNA SO KUJI KOH???
Toh Dai mafitar ɗaya ce TAK, ki biya Nairan ki ɗari uku 300 kacal domin ki cigaba, Zaki saka kuɗin ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan anyi completing kuma it'll be 500.
Ɗari uku kam ai yayi arha dayawa koh ƴar uwa???.
Ina so idan kun biya Ku biyo domin kuji
Labarin soyayyar Me Gari Fatima da kuma Dr. Shettima Bukar wanda aka fi sani da Ba Prince.
FADREES 🖋️🖋️.

Chapter 9 of 9