a ranta kuwa caa take ko isuhu ne autan maza ta hakura dashi, tunda dai kanwarsa halaka ta take san yi
Ganin haka kowa ya fara watsewa a gun, shikam isuhu kasa magana ma yayi, ikon Allah, ji yarinya na kokarin kawo masa cikas?, bari ze gyara lamarin inshallah
Da haka ya kama hannun ta suka yi gida, tsabar kumbura ko tuwo bata ciba tayi shigewan ta daki, hatta da ƙayau ƙayau din nata bata nema ba
Ita kanta in da za'a tambaye ta dalilin da ya sata aikata abinda ta aikata, toh bata da hujja, kawai dai tasan wani abu, deeply haushin rashin ganin Iliya take sannan kuma da tafiyar sadiyan
Washe gari da kanta tabi su me gari gona dan ji tayi gidan ya ishe ta, sunsha aiki kam dan se da la'asar suka dawo gida, suna zuwa wanka tayi ta kwanta bacci cike da tunanika kala kala, washegari ma koda suka je dandali bata ga Iliya ba, se kuma ta dasa ayar tambaya a ranta, toh ina ya shiga, dan abun gaskiya ya soma mata wani kala, sannan ta lura yau sam bata ga yarinyar da ta ganta tare da Isuhu ba watakila ta dauki shawaran nata ne, ai kuwa dai yafi mata kam.
Bayan Mako Biyu
A cikin satika biyun nan Fatima tayi wani kala, domin babu iliya babu dalilin sa, yau ta kama Litinin, da wurwuri ta tashi taje tayi salla tayi wanka da ruwan da aka hada na me gari, tana jin babarta Tala tana masifa tayi banza da ita, goggo kuwa ganin ikon Allah kawai take, dan ko gaisuwa yau bata samu ba wai dan saboda bata cewa me gari ya dena zuwa gona da ita ba, sannan ta shawarci me Garin da ya saka Fatima a cikin wadanda zasu yi aikin gonan sa na nan dake bayan gidan nasu, shiyasa take wani ciccin magani, taɓe bakin ta tayi taci gaba da sabgogin ta dan zuwa anjima ma fita zata yi anyi aihuwa a makwafta zata Barka.
Fatima tana gama shiryawa ta fita ta ga Inna larai ta sauke abun kari, zama tayi ta zuba ta kama ci tana gamawa ta miqe tayi hanyan dakin me gari, me gari yana jin ta kama buga masa kofa ya buɗe ya fito ya bata kudi Naira Hamsin, haushi ne ya kama Fatima ganin Naira Hamsin kacal ya bata, amma a haka ta amsa, har da zata je isuhu ya kara mata ta fasa dan shima yanzu fita makarantar yake gadan gadan semester tayi zafi, ficewa tayi ta tafi makaranta abunta dan yanzu shirye shiryen Exams ɗin gamawa suke sbd haka ne zata maida hankalinta.
Can bayan an tashi ta tiso keyar su Hanne suka kamo hanya, tana jinsu suna ta hiran samarikan su akan suna aiko musu su wasiqa da kayan ƙwalama da dai sauransu, taɓe baki tayi ta cigaba da jagorantar su kawai har suka isa.
Suna shigowa cikin gabur wannan yaron da ta taɓa kwacewa ƙayau ƙayau din sa ya sha gaban su, bata wasiqa yayi yayi gaba abunsa
Su Barira duk mamaki ya kama su, itakam amsa tayi tayi hanyar gidan su, roqon ta suka yi da tazo gaɗa yau, bata ce musu uffan ba ta wuce gidan nasu seda tayi sallah taci abinci kamin ta bude wasiqan
"YA FAƊIMATY
Ya kike, ya gida ya su goggo da kuma Isuhu, da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Nasan kinji Ni shiru ko? Nayi tafiya ne zuwa damaturu, naje ina neman admission a Universityn garin, da na gama zan zo gidan ku inshallah.
Ki kula da kanki
ILIYA MAMMAN".
Ta kula da kanta? Toh daa ɗin bata kula da kanta ne?, ji shi ɗan shishigi kawai, wai ya tafi neman admission, yanzu fisabilillah duk girman san nan se yanzu ze shiga university? Amma kuma taji kwanaki isuhu na cewa ai ya gama College ɗin Potiskum, toh Allah ya kyauta, amma kar ya sake yazo gidan su dan rashin mutunci zata masa, sannan yace Damaturu koh? Idan ya dawo zata ce ya bata labarin Damaturu dan taji ance babban gari ne me matuqar bala'in kyau.
Mu haɗe a na gaba
Fadrees🖋️.
Littafin nan na kudi ne akan Naira 300 kacal.
Zaki saka kuɗin ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan kina so tun yanzu zaki iya biya, in kuma se an gama free pages ne ma dukka daidai ne.
Idan anyi completing kuma it'll be 500.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
*Fatima's Visit to Potiskum.*
8.
Free Page
Da daddare bayan anyi isha sun shirya da niyyan suje dandali me gari yayi sallama, su Fatima sunyi mamakin ganin me gari a wannan lokacin dan sunyi tsammanin ko baida lapiya ne, shidai da ya shigo se ya wuce gun goggo, binsa isuhu da Fatima suka yi dan su gaida shi se suka ga ya ciro makullin mota, gayawa goggo yayi akan me Nangere ya masa kyautar mota sannan an ƙara masa matsayi a fada, wani uban ihu su Fatima da su Musan da bata san da zuwan su ba suka sa, hatta da Baba Tala seda tayi ihun murna jin mijin ta yayi sabuwar mota, goggo ma da Isuhu murna kamar suyi me
Muryar fatima aka jiyo tace
"Toh Baba yaushe zaka ɗana mu da motar sannan muna so ka kaimu Potiskum"
Dariyar farin ciki me gari ya saki ganin duk iyalan sa suna cikin matuqar farin ciki kuma duk ta dalilin sa, tsintar Muryar shi yayi da furta,
"Ranan asabar zamuje dukkan mu, in yaso kowa ya dauki kayan sa kala biyu kwana biyu za mu yi mu dawo"
Faɗin irin farin cikin da Fatima tayi ɓata baki da lokaci ne, a rayuwarta tana so taga itama taje birane sede Allah be yi ba, dan ita tunda take sau daya ta taɓa zuwa Potiskum, lokacin tana ƙarama suka je gidan en uwan baban isuhu daga nan bata sake zuwa ba, ƙarƙarin ta Nangere ne daman, se su Chalimno ƙauyukan dake kusa dasu kenan, sannan a dalilin Sadiya kuma ta shiga cikin gidan me nangeren.
Ranan fitar dandalin da basu yi ba kenan, sannan kwanan farin ciki tayi, ga farin cikin ganin wasiqan iliya ga na motan me gari da kuma zuwa Potiskum ɗin da zata yi, sannan tasan in iliya ya dawo ze bata labarin Damaturu.
In takaice muku tun a daren Fatima ta haɗa kaya kala ukun da zata tafi dasu, biyu wanda Sadiya ta bata ɗayan kuma na sallan tane, tana gamawa taje ta kwanta cike da tunanika da haka bata san ma bacci ya sure ta ba seda taji goggo na tada ta sallan asuba, ba tayi wani dogon musu ba ta miqe taje tayi.
Bayan gari yayi haske taje tayi wankan ta ta wuce makaranta ko karban kudin me gari bata yi ba.
A haka dai ranaku suka yi ta tafiya har yau ta kama asabar, Fatima tunda asuba tayi wanka, karshen ta ita ta tada kowa sallan asuba hatta da goggo kuwa, Goggo mamaki kamar ya kashe ta, haka dai ta kyale, lalle ta yadda da maganar nan ta hausawa da suka ce 'Saa kai ganin dama ne'.
Zuwa karfe goma kowa ya gama shirin sa fitowar me gari kadai ake jira, can kuwa ya fito cikin shirin sa na malum malum yayi kyau abunsa, kana ganinsa za kaga zallar kamar da yake da su Musa, sede shi ɗin tsoho ne tukuf.
Motar tashi babba ce sosai, irin manyan motocin nan ne dan Seda ta dauke su kaf, Isuhu shine a drivers seat, me gari a gefen shi, se tsakiya kuma fatima da goggo da Baba Tala se ƙannen fatiman a cinya.
Ajiyar gidan aka bari a hannun masu aikin gidan kana suka kama hanya, minti goma ya kaisu nangere dan Yaya isuhun tsula gudu yake, Fatima kam se kalle kalle ake, daga nangere suka hau babban titi se garin Potiskum, tafiyar minti 20 ya kaisu Potiskum, Fatima kanta kamar ze ɓalle saboda waige waige, bata taɓa ganin garin da ya burge ta ba kamar Potiskum, Seda taga gidan sarakunan su ma tace ashe Nangere ba komai bane, Ita bata taɓa sanin ana yin sarakuna biyu a gari daya ba seda taje Potiskum, gashi gidajen nasu dukka sun amsa sunan gidan sarauta.
Gidan baffan isuhu suka fara zuwa da yake unguwar race house, sun ɗan jima kafin me gari suka tashi shida baffan isuhun zasu je wani guri, basu ne suka dawo ba se da azahar, daga nan yasa isuhu ya ɗebe su ya kaisu wani gida me kyau dake unguwar Sarkin Fika, me gari da kanshi ya bude gate din gidan isuhun ya shige da motar, koda ya faka motar da gudu yaje ya rufe gate ɗin gudun kar me gari yace shi ze rufe, dan Fatima da Yakamata taje ta rufen ƙarewa gidan kallo take bata ma san wainar da suke toyawa ba.
Gida ne me ɗauke da apartment ɗaya babba sosai me dakuna biyar, gidan ko ina interlock ne a zube, se parking lot da dam me ɗauke da borehole, a falo suka tsaya me gari yace da goggo wannan gidan sa ne da ya saya shekaru biyu baya, daman yayi niyyan duk sanda suka zo da iyalan shi anan zasu dinga sauka, yanzu kowa ya sauka a daki ɗaɗɗaya, nan ya wuce dakin da yake can ciki shi kuma isuhu ya dauki dakin dake cikin parlourn saura dakuna uku, Babarta Tala ce ta shige daki daya da yaranta saura daki biyu
Goggo ce tace da Fatima ta dauki kayan su tasa musu a dakin gefen na Babarta Tala
Budan bakin Fatima tace bata san zance ba, ita a daki daya zata zauna baza suyi sharing daki ba, goggo kamar ta make ta ɗan haushi, daga baya ta kyale ta ta shige dakin aka bar ta ita daya a falon, karewa parlourn kallo tayi a ranta tana jinjina rowar me gari, yanzu fisabilillah yana da irin wannan gidan yabar su suke gararamba a gabur? Yanzu abinda me gari yayi musu ya kyauta musu kuwa, jibi falon nan, wallahi ya kusan nasu Sadiya a kyau, ai wallahi tunda dai haka ne zata ga me mayar da ita Ƙauyen Gabur, ta riga da tazo kenan, dan garin ma gaba-daya ya matuqar burge ta, tana sake saken nan ne taji ƙafar ta yayi tsami daukan jakar kayanta tayi ta shige dakin da tayi wa lakabi da nata
Katifa ta gani a shimfide da pillow akai sai wani drowa madaidaici ata gefe, idon ta ta juyar ta dayan gefen taga wani kofa, tashi tayi taje ta bude kofar, banɗaki ta gani a ciki, wato harda banɗaki ma, yayi kyau kuwa, shigewa tayi ta kunna famfon jikin sink taga ruwa yana zuba, bata san sanda ta sake murmushi ba, ashe dai burinta itama wataran ze cika, tana matuqar san gida me kyau yau gashi Allah ya bata, murmushin jin dadi ta saki, mirror ta gani ata saman sink din data ɗan ɗaga kanta, kallon fuskar ta tayi, kamar ba ita ba, gani tayi ta yiwa kanta kyau, ruwa ta dauka ta watsa a fuskar ta nan ta saki murmushi a karo na biyu, gani tayi ashe tana da dimples ma, ikon Allah ashe haka take da kyau? Tsayawa tayi a gaban mirrorn tana ta shirmen ta, daga tayi wannan style din se ta canza tayi wani, motsi taji seta daga kanta taga isuhu a bakin kofa yana kallon ta
"Yayana zo ka kalle Ni da kyau ashe haka nake da kyau shine baka taba fada min ba?"
Isuhu ya tsinkayi muryar Fatima na jefa masa tambaya cike da lalata
Sharewa yayi yace mata
"Ki fito za'a ci abinci"
Yana karashewa ya juya yabar dakin gaba-daya, fitowa itama tayi taje falon ta iske su duka an zuba abinci, mamakin daga inda aka samo abincin take sedai bata yi magana ba.
Shinkafa ne jollof da kaji da su drinks, bayan an gama ci me gari yace su huta gobe zasu je ziyara gidan en uwan isuhu, sannan shima ana neman sa yanzu a masarautar Potiskum, daga haka ya fice.
La'asar yana yi kowa yaje yayi Sallah, bayan sun kimtsa Isuhu ya kunna musu tv, Baba Tala ido kamar ze fado ƙasa tsabar kallo saboda babu a house, haka zalika su Musa, Fatima kam tsaki tayi tayi shigewan ta ɗakin ta, dan tunda tayi arba da madubi ta koma banɗakin, lura da abinda take yasa goggo take fatan Allah ya sa wani aljanin ma ya wanka mata mari ko zata dawo taitayin ta, su Musa kuwa an kame kai saboda ana tsoron Fatima.
Can bayan sallan Isha lokacin me gari be dawo ba, isuhu suka fita shi da Fatima siyan tsire.
Unguwan a cike yake kowa yana harkan gaban sa, hakan se ya burge Fatima sosai, sun kusa isa gun me tsiren wata tazo wucewa ta gwabje Fatima.
Wani kalan ashar ta lailayo ta janyo rigar yarinyar ta dawo da ita gaban ta, ashe yarinyar itama ba ƙyal bace, nan kuwa suka kama cacan baki, seda isuhu ya raba su kafin nan, se kuma daga baya yarinyar tace mata
"Daman haka kike?, daga ganin mutum ki kama janshi da fada? Ke baki da hakuri ne? Meye sunan ki ma"
Fatima kamar baza ta kula ta ba seda tagama ƙare mata kallon raini kafin tace
"Sunana Fatima, Ni ƴar Me Garin Gabur ce"
Gani tayi yarinyar ta saka dariya sosai harda kama ciki
Ba Fatima ba hatta isuhu seda yayi mamakin dalilin dariyar nata
Matsowa tayi daidai saitin fuskan fatiman yanda zata ji ta da kyau tace
"Ni kuma sunana Maimuna, sannan Ni ɗiyar Sarkin garin nan ne, ina nufin na masarautar Fika.
Ido da hanci isuhu da Fatima suka sake suna mata kallon mamaki
Tana diyar sarki shine zata fito da dare ba tare da jagora ba, lalle kam, ita dai Fatima kamar bata yadda ba amma ganin kalan kayan jikin yarinyar ya sake sata tunani
Maimunan ta juya zata tafi Fatima ta sake janyo rigar ta har tana ɗan yin tuntube
Haɗe rai tayi tana me kallon Fatiman.
Zan tsaya daga haka
Mu haɗe a na gaba.
Fadrees.
Follow me on Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
9. Gidantu Club 🏠
Free Page
"Idan har da gaske kike ke ɗin ɗiyar Sarki ce, meyesa kika fito ba jagora?"
Fatima ne ta jefe ta da wannan jimlar
"Saboda Ni bana san rayuwar kulle, kin ganni nan? Dare ɗaɗɗaya ne bana fita, kullum se nayi ɓadda kama na fito yawo, bana komawa gida se na tabbatar da na zaga kaf garin nan, Kinga can"
Maimuna ta ƙarashe tana me nuna mata wani guri, daga kai Fatiman tayi tana me ɗora idanun ta a gun da maimunan ta nuna mata
Hango wata mata tayi, matar se waige waige take sannan kuma tana juyowa taga direction ɗin inda suke.
Ganin haka se Fatiman ta yarda da batun yarinyar dan alamun matar can ya nuna sam bata da gaskiya
Juyawa tayi da niyyan ta ma isuhu magana se ta ganshi a cikin wasu samari se magana suke tayi, ganin haka se ta juyo da kanta kan maimunan
"Toh yanzu ke ɗin ina kika nufa da kika fito a yanzu"?
Fatima ta sake jefa mata wani tambayan, gundura maimunan tayi ta tambayoyin Fatima se kawai tace;
"Ko danma, banga lefin ki ba, kika ce ke ɗiyar Me Garin Gabur ce, toh daman ina zaki san ire-iren abubuwan nan tunda daga ƙauye kika zo"?
Ta ƙarashe tana dariyar renin wayo wanda hakan ya sa ran Fatima kaiwa kololuwa wajen ɓaci
Ganin hakan se Maimuna ta bata haƙuri se ta sake matsowa dab da kunnen fatiman kana tace
"Wani gidan rawa zanje, naji labarin yau akwai babban show, shiyasa kika gannin"
Zaro ido Fatima tayi cike da mahaukacin mamaki dan tasan ance gidan rawa ba guri bane me kyau, sannan maimunan yarinya ce da baza ta wuce sa'ar ta ba, toh me zata je tayi a gun rawa ma? Gaskiya itama tana so taje taga gun
"Ni zan wuce ko? Sai wata rana"
Maimunan ta faɗa tana me shirin tafiya daga wajen
Ko da jin haka ai sai Fatima tace
"Zan biki Nima"
Kallon ta Maimuna tayi kana tace;
"Ta yaya toh? Ba tare nagan ki da yayanki ba? Ai baze barki ba".
Fatima ne tace;
"Kar ki damu, mu ɓace masa kawai"
Da haka suka kama hanya se gaban gidan rawar.
🍒'GIDANTU CLUB PKM BRANCH'🍒
Fatima ta gani a rubuce a jikin wawakeken gate din gurin
Sake maimaita sunan gun tayi a ranta, daman haka gidan rawa yake? Itafa ta dauka ginin ƙasa da langa langa ne, sannan ƙiran masu kidan molo ake yi suzo su dinga kida ana musu kari ashe abun ba haka yake ba, idon Fatima be rena fata ba seda suka shiga gun ainihin gun, hadda su reception, gani tayi Maimuna tayi gun reception itama se ta bita gun gudun kar ta bace mata, magana taga maimunan sunyi da receptionist ɗin, take ce mata ai ba'a shiga se an biya 5k per ticket, sannan hawa hawa ne akwai kudin da yafi haka, in dai ka siya ticket komai kayi order za'a kawo maka, kudade taga maimunan ta ciro daga wani side bag nata me ƙirar LV ta miqa, ita kuma receptionist ɗin ta miqo musu tickets guda biyu inda Maimuna tasa hannu ta karba, ta baiwa Fatima daya ta riqe daya, mamaki kamar ya kashe Fatima amma duba da cewar yarinyar diyar Sarki ce hakan ba komai bane, shiga cikin club ɗin suka yi inda suka sake iske wani kofa, ita kanta maimunan ba saba zuwa ire-iren gun nan tayi ba, kawai dai curiosity ne ke janta shiyasa tazo, sannan taji dadi da fatiman ta rako ta daman a ranta taji tsoron zuwa ita daya kar wani abu ya same ta duk da bata fatan haka
Bude kofan ainihin gun suka suka shiga, daga nan kafar Fatima ta kama karkarwa ganin mata da maza a cunkushe ana rawa jiki na gugar jiki, ga wasu ɗan banzan shiga dake jikin su, gun dim lights ne kala kala se caccanzuwa suke yi ga wani cool sanyi da kuma cool music ɗin dake tashi a gun, hannun ta Maimuna taja suka samu guri ata gefe suka zauna, daman anyi reserving gun daidai kudin da suka biya, waiter ne yazo inda suke Maimuna ta musu ordern pineapple punch da pizza, Fatima ba abinda take se kallon gurin da ido, a rayuwa tana san zuwa gurare a birane sede ba irin wannan ba, yanzu fisabilillah wannan wane kalan rayuwa ne, dubi yanda suke rawa se kace korarru? Yaya za'a ga daidai a rayuwa dan Allah? Lahaula fi sha'atillah🤦
Koda waitern ya kawo musu abun nasu hankalin Fatima sam baya kansu ma, ita idanunta yana kan en rawa se kare musu kallo take tana ganin fuskokin su ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya, Maimuna ne ta taɓa ta kana ta dawo hankalin ta, daukan pizza tayi kaman yadda taga maimunan tayi, se ta tuno da sadiya, Allah Sarki Sadiya ko me suke yi a makarantar su yanzu?, cin pizzan tayi se taji wani mugun dadi ya mamaye bakin ta, nan da nan ta cinye share nata, ta kora da pineapple punch ɗin, bayan kamar 30 minutes tacewa maimuna gaskiya Yakamata su koma, itama maimunan bata mata musu ba tace su tafi ɗin dan in tayi dare za'a gane bata sashen ta.
Fita suka yi daga club ɗin suka koma daidai inda suka haɗu, ba se kan Fatima ya juye ta rasa hanyan komawa gida ba?
Lokacin kuwa ba neman duniyan da Isuhu be mata ba, bayan ya gama gaisawa da course mates nasa da suke yin College tare se ya dawo daidai inda suke shi da Fatima da farko
'Wayam' ya gani, ba Fatima babu dalilin ta, sannan babu yarinyar da ya gansu tare, waige waige ya kama yi ko ze ganta yaga shiru, nan take yaji hantar cikin shi ya kada, wucewa yayi ya koma gida da sassarfa, daman niyyan sa in yagan ta a gida se ya mata duka, in be ganta ba kuwa ze sake fita ya koma neman ta ne, yana sallama ya iske su goggo a falo, ita tana jan carbi Baba Tala kuwa an kafe tv da ido bata ma lura da shigowar sa ba, ɗaga idon ta goggo tayi ta gansa, tace
"Ya naga kun ɗan jima ne Isuhu, ina ita Fatiman take?"
Rasa ƙaryan da ze mata yayi fahimtar cewar Fatima bata ciki, se can ne yace mata
"Na barta a bakin gate, kudin hannuna ne baze isa ba shine nace ba seta shigo ba ta jirani inzo in dauka ATM dina se mu hanzarta muje mu dawo"
Taɓe baki goggo tayi tace
"Kar dai ku dade kamar na yanzu gaskiya"
Da 'toh' ya amsa mata ya fice ya koma inda suka tsaya da farko, Safa da marwa ya kama yi, daga baya kuma yayi tagumi.
Shi dai yana roqon Allah yasa ba ɓata tayi ba dan be san a ina ze fara neman Fatima a wannan babban garin ba, amma tsaya ma tukunna, ai yaji yarinyar dazun tace ita ɗin ɗiyar Sarki ce, har ma ta nuna wata wai wanda ta rako ta, ɗaga kansa yayi setin matar be ganta ba, ji yayi kamar ya saka kuka, shikam yau ya shiga uku in Fatima ta ɓata dan besan inda zesa kansa ba, sake waigawa yayi, yaga matar ashe canza guri tayi, ta koma can lungu sosai inda hankalin mutane baze je kanta ba, da sassarfa ya isa gunta yace mata ina maimuna ta tafi da Fatima, kame kame ta fara yi yace in bata fada masa ba yanzu yanzu ze kaita masarautar da kanshi yace ta fitar da yar sarki bada izinin kowa ba, ai nan mata ta rikice ta fara basa hakuri
Daga nan ta gaya masa yanda suka yi da maimunan, ce mata yayi ta masa jogara subi bayansu inba haka ba shi yasan me ze mata, tafiya ta fara yi yabi bayan ta har suka zo inda suka tsaya da farko maimunan ya hango tana tahowa da saurinta ba Fatima, ƙarasawa gunta yayi yana tambayan ta ina Fatima, nuna masa wani hanya tayi ta kama hannun matar suka yi tafiyar su, da gudu ya karasa layin ya hango har tayi nisa sosai, karasawa yayi ya janyo ta ya wanka mata wani lafiyayyen mari, dafe kuncin ta tayi ya sake wanka mata a dayan, shima dafe shi tayi ta tsugunna ta kama kuka a gun dan marin ya shige ta sosai, ɗaga ta yayi ya rungume ta a jikin sa, se can yace
"Kiyi shiru Fatima, tsoro kika ban shiyasa na mare ki, na dauka kin ɓata ne, sannan kinsan cewar nan ba ƙaramin gari bane ina kuka je?"
Shiru tayi ita de tana kuka ganin haka ya kama ta suka koma gida, tsiren da ba'a siya ba kenan
Koda suka koma suka hango me gari ya riga da ya dawo, direct dakin ta ta wuce bayan ta gaida me gari da Goggo dan har gobe ita bata gaida Baba Tala.
Kan katifan ta ta hau ta kwanta daman fankan dakin a kunne yake, kukan baƙin ciki da jin haushin Isuhu ta kama yi se daga baya tayi shiru, tana yin shirun kuwa Musa ya shigo a ɗarare yace ta fito taci abinci, tsawan da ta buga masa ne yasa ya ruga ko ƙarashe maganar nasa ma beyi ba dan karta bige shi
Miqewa tayi ta shige banɗaki tayi alola ta watsa ruwa a fuskan ta tana me kallon fuskar ta da yayi shatin hannun isuhu, shafa gun tayi tana me bata rai, wani abun mamakin shine ganin sa da ta sake yi ta madubi, a ranta tace
'In ma aljanin kane wallahi Ni nafi karfin ku'