ma waiwaya shi ba ta wuce daki ta shirya cikin uniform nata, dan ta yanke shawarar zuwa din, ko abinci bata waiwaya ba tayi waje, hatta gaisuwa me gari be samu ba yau, ballantana wata goggo karamar alhaki su isuhu kam ba'a maganan sa ma.
Bata lura da hadarin da ya taru ba tayi ta tafiya har Seda ta ganta a cikin makarantar su na sabon Garin Nangere, tsirarun dalibai ta gani daga alama saboda hadarin da ya taru ne, dan ita kanta ta dauka ruwa ze same ta a hanya ne.
Ajin su ta wuce taga da malami a ciki, directly bencin su ta wuce, shima kuma malamin se be mata magana ba sbd sanin halin ta,
'Wayam' ta kalla bencin nasu ba kowa, seda ta bari an fita break kamin ta tambaya en ajinsu whereabouts din Sadiya dan gabaki ɗaya bata fahimci darasin da aka musu yau ba ma.
Amsar da wani ɗan ajinsu ya bata ne ya sata jin wani iri dan kamar jiri jiri ta kama ji ma, ce mata yayi wai an cire ya'yan sarkin gabaki ɗayan su daga makarantar, aikuwa ana tashi bata zarce ko ina ba se fada dan bata yadda da abinda ya fada mata ba, su Hanne daman duk basu je ba ƙila dan sunga garin da hadari ne.
Fatima na hango a gaban fada sede wani abun mamakin shine fadawa sun hana ta shiga, yo mamaki mana tunda dai last ma tazo ta, sede a mota ta shiga a mota ta fita , kuma gashi hadiri ya mugun haduwa sosai ko wane lokaci ruwa ze iya saƙƙowa, kuma gashi juyin duniya tayi musu sun hana ta shiga, karshen ta ba kalar tijaran da bata musu ba amma ko gezau, abun ya taru ya ma Fatima yawa se kawai ta zauna a kofar masarautar daidai inda mota ze wuce ta kama ihu tana kuka, a daidai lokacin ne wata mota tazo fita daga cikin masarautar, da gudu drivern ya taka birki dan saura kadan ya hau kan yarinyar da take zaune a bakin hanyar fita ɗin, jin an dakata na cikin motar ya tambaye lapiya aka tsaya?, shi kuma drivern se ya fada masa halin da ake ciki daga nan ya nemi izini ya fita dan ya duba ko lapiya, fitar sa keda wuya yaga yarinyar da ya ganta a sashen uwargidan Me Nangere tare da Sadiya, karasawa gun masu gadin yayi yana tambayan su lapiya? Suka ce masa wai wannan yarinyar ne tazo shiga su basu santa ba shine suka hana ta shiga, sannan tace gun gimbiya sadiya tazo, koda jin haka se Bodyguard ɗin yace su barta ta shiga, Fatima ko koda jin haka a take ta tashi ta runtuma cikin masarautar ko godiya bata tsaya yi ba, shiko Bodyguard shigewa motar yayi yayi driving zuwa wajen masarautar.
Seda tasha tafiya kafin ta iso gidan su Sadiyar, da buɗe kofar ta ta hadu da kuyanga
"Wa kike nema?".
Kuyangar ta tambaye ta dan ba ita bace sanda tazo ta wuni
Fatima kuwa jin tambayar renin wayon nan yasa ranta ya ɓaci, wato an wulakanta ta a bakin kofa shine za'a maimaita anan, wlh suma na bakin kofar ba kyale su tayi ba, zata dauki fansa, sannan wannan itama da alamu tana so ta koya mata hankali ne
Fatima na shirin bata amsa cike da renin hankali Sadiya ta fito daga dakin ta sanye da wani kalan abaya yasha stones, baki Fatima ta sake tana kallon Sadiya, can ta ɓata a cikin tunanin ta taji Muryar Sadiyar a kusa da ita
"Fatima yau kece a gidan namu?"
Ta karashe tana jan hannun ta izuwa kan sofan hadadden falon nasu
Fatima kasa magana tayi se mamaki, me ya hau kan Sadiya take mata haka, idan har bata manta ba Sadiya bata fiye san mu'amala da ita ba, amma yanzu shine hadda riqo mata hannu da janta?, bata ce komai ba ta zuba wa Sadiyar idanu.
"Kinga Mama bata nan da kinje kin gaishe ta"
Sadiya ta karashe zancen ta da alamar shagwaba.
"Ina taje?, Daman matan sarakuna suna fita ne?"
Ƴar dariya kadan Sadiya tayi kana ta bata amsa
"Ehhh basa fita amma wannan fitar nata, na yasu yasu matan sarakuna ne ai, ta tafi Damaturu taron matan sarakuna da aka saba yi ko wane bayan watanni shida"
"Ayyah Allah ya dawo da ita lapiya"
Fati ta karashe cikin ranta kuwa zallar farin ciki ne dan ita sam bata wani san mamar Sadiyar nan.
Suna a haka aka tsinke da wani mugun ruwan sama me karfi sosai, Fatima ce ta tambaye ta
"Sadiya meyesa baki je makaranta ba, na tambaye wani ɗan ajinmu wai an cire ku, shiyasa nace barin zo in tambaye ki da kaina, sannan da nazo shiga fadawanku na gate suka min wulakanci, da badan wannan basamuden ranan ba da wallahi har yanzu ina bakin kofa ƙila ma da ruwan nan a kaina ze ƙare"
Fatima ne ta ƙarasar da maganan ta cike da mugun ɓacin rai tana hasaso irin wulaqancin da zata ma masu gadin nasu
"Ehh da gaske ne an cire mu, An maida mu Turkish dan nan babu karatu gashi WAEC zamu fara shiyasa Babanmu yace a maida mu Turkish tunda Kinga daman mazan gidan namu can suke yi.
Jin haka Fatima ta hantsilo daga kujeran da take
"Kina nufin Turkish na mamudo?"
Ta jefa mata tambayar tana kallon ta
"Ehhh wlh can, jibi jibin nan ma zamu tafi, dan Kinga lahadi ake komawa makarantar
Jikin Fati ne yayi sanyi jin ƙarashen zancen Sadiya, Allah Sarki ba komai, duk sanda tazo zata dinga zuwa gidan su tunda ita baze yiwu taje nasu gidan ba kasancewar ta yar sarki.
"Ki tashi muje kici abinci"
Sadiya ta katse mata tunanin da take, babu musu kuwa kamar jela ta bita kan dinning ta zuba mata abinci taci, bayan ta gama tace mata zata tafi, in ta koma can Turkish din Allah ya basu sa'a
Ita kanta sadiya jikin ta sanyi yayi, se taji Fatiman ta bata tausayi, shigewa dakin ta tayi ta kwaso mata su biskit da kaya kala biyu tare da uniforms nata ta bata, karba tayi ba wani doguwan magana suka fita ta raka ta, lokacin an gama ruwan sama gari yayi mugun dadi se kuma hanya da duk ya ɓaci da ruwa, abubuwan da ta kissima zata ma masu gadin kofar ma kasawa tayi amma tana sane dasu kawai dai bata da karfin yin tijara ne
Kayanta ta riqo a hannu ta fara tafiya hanyar garin su a hankali, tunani take tayi a ranta akan makarantar da su sadiya zasu koma, taji ance kaf Yobe babu makarantar da ya kaishi kyau, itama zata so a kaita sede makaranta ne sam be dame ta ba, sannan tasan babanta me gari ne kawai bashi da halin da ze kaita wannan makarantar, tana tafe tana sake sake a ranta taji an doka sallama a kunnen ta, ɗaga idan ta tayi taga iliya ne a gefen ta, karban kayan hannun ta yayi ita kuwa bata masa musu ba ta miqa masa
Suna tafe yana ta mata surutu ita ba ma jinsa take ba, ganin haka se yayi shiru suka ci gaba da tafiya, lokacin har anyi sallan la'asar
Suna isa garin Gabur ta wuce gidan su, tazo shigewa iliya ya mata magana ta juya ta kalle sa, kayanta ya miqo mata tasa hannu ta karba tayi shigewan ta
Tana shiga ta hango goggo akan sallaya tana lazimi, aje kayan nata tayi a kasa taje ta dauro alola tazo tayi azahar da la'asar kamin ta koma ta samu gefe guda ta rabe, goggo dai sai mamaki take, sharewa tayi ta cigaba da harkokin gabanta, suna a haka isuhu ya shigo, be zarce ko ina ba se dakin sa, can kuma ya fito yayi alola ya fice, shine be dawo ba se bayan mangariba ba, shigowar sa ba dadewa akayi isha, fita yayi waje yaje yayi Ishan ya dawo duk yana mamakin sauyin da ya gani a gun mutumiyar tashi, kodanma yasan zuwa safe zata wartsake, can har ze fita ya tuna da dandali, yace tazo ta raka shi ya siyo ƙayau ƙayau, da kaman baza taje ba se kuma ta tashi suka fice, a bakin gidan nasu suka hango majalisar me Gari an ajje musu abinci se ci suke suna taɗi, har ƙasa Fatima ta tsugunna ta gaida su, wanda hakan ya baiwa kowa dake gun mamaki especially baban ta me Gari, miqe wa suka yi suka wuce dandali daga nan.
Mu haɗe a shafi na gaba
Fadrees.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
6
Free Page
Filin gaɗan a cike yake kamar kullum, direct gurin me ƙosai suka wuce sun kuwa taradda dogon layi, isuhu ne yace wa fatima bari yaɗan je can yayi waya, bata ce masa komai ba ta cigaba da jiran layin, can da taga kamar layin baya tafiya ta samu guri ata wani ɓari ta zauna, tana hango su Hanne suna ta hiran su da alamu basu ganta ba ma, itama kuma se bata nemi yi musu maganan ba, tana nan zaune a gun ta fada cikin tunani taji tsayuwar mutum akan ta, tana daga ido taga Iliya
Muryar shi ta tsinkaya yana me mata magana
"Tunanin me kike haka ina ta sallama bakiji Ni ba"?
"Babu komai"
Ta basa amsa, dan zuwa yanzu ta fara gundura da shishshigin da yake mata
Zama yayi a gefen ta hakan sai ya sake tunzura ta, gashi sam bata da karfin yin rigimar ma, ɗaga kanta tayi dan taga ko layin yana tafiya taga kamar ma baya tafiya, sake juya kanta tayi gefen da yayanta isuhu yake waya ta hango sa shi da yarinyar da ta gansu jiya se murmushi suke, yarinyar se wani sadda kanta ƙasa take wai ita ala dole kunyan shi take ji, ba abinda yafi bata mata rai kamar ganin yadda isuhu ya zage se kalamai yake zubowa yarinya, wato shi ko ajikinsa ya ganta wani iri memakon ya tambaye halin da take shi ta soyayya ma yake, wallahi dan bata da karfin yin fada ne, da wallahi se taje ta kakkarya yarinyar can, sannan hadda wani ce mata waya zeyi ashe dai ƙarya yake, wani dogon tsaki taja ta juyo da niyyan tabar gun gabaki ɗaya taga isuhu a gefen ta, wato be tafi ba kenan, se kace wani jela? lalle wannan ko me yake damun sa dai daga gani kansa ba daya ba
Muryar sa ce ta sake tsinkaya yana me ce mata
"Wai me yake damun ki ne Fatima, naga duk kinyi shiru, dazu ma ina ta Miki magana naga hankalin ki baya ma kaina, sannan gashi yanzu ma kamar tunanin wani abun daban kike, nidai jiya ba haka na ganki ba, Allah ya sa dai lapiya?"
Ya ƙarashe maganar sa, muryar sa na cike da tsantsan rashin jin daɗi
Shiru tayi ta ɗanyi jim, se kuma ya sake maimaita mata tambayar, can kamar baza tayi magana ba se kuma ta zayyane masa tsakanin ta da Sadiya da labarin barinta makarantar
Can bayan ya gama sauraronta yace
"Komai da kike gani a duniyar nan yana da sanadin sa fati, sannan rabuwa ai ba mutuwa bace, wataran ai zata zo hutu sannan zaku haɗu, kuma according to yanda kika min narrating ita da kanta zata neme ki ma idan ta dawo, kar ki sanya ma ranki damuwa kinji, a madadin hakan kamata yayi ki kara himma kiyi karatu kıyı passing WAEC da NECO Naki, Kinga se ki gama da sakamako me kyau, inma kina so kici gaba da karatu zaki samu dama da zaran result Naki yayi kyau, inma bakya son karatun Kinga ba se a Miki aure ba?"
Ya karashe yana me kallon ta
Dariya ma ya bata, dan Seda ta ɗan dara, wai aure, çapdi jam, ai ita yanzu bata ga abinda zesa ta aure yanzu ba, dama dama dai karatun sannan gaskiya zata iya cewa bata taɓa zama tayi maganar fahimta da wani ba se yau, mafi akasari tsokana ne da ita da taran fada, ita zata iya cewa abu ma be taɓa damun ta kamar yau ba kuma duk akan zancen barin Sadiyar ne, toh ita dai ba rashin mahaifiya tayi ba, tun sanda ta girma ta gane ba goggonta bace ta haife ta hakan be taɓa damun ta ba, domin goggo ta mata duk abinda ya dace uwa tama ɗiyar ta, bata taɓa banbance ta da Isuhu ba, duba da shima yayi rashin nashi mahaifin, sannan ta koya musu yadda zasu so junan su a matsayin en uwan jini, ta ma fi santa akan isuhun a yadda ta lura, sannan an sangarta ta ɗan hatta wasu masu uwayen ma ta fisu sangarta, sannan Yayanta da me gari ma suna matuqar santa. Kawai dai wataran takan yi tunanin dama ace taga mahaifiyar ta ta ainihi, ta san da kullum zata kasance a manne a jikin ta ne, a hoto kawai ta san mamanta sannan hoton ma guda biyu ne, amma ba komai a hakan ma tana jin dadin rayuwar ta, tana matuqar son goggonta da yayanta hatta da me gari ma, ba komai....
"Fatima lapiya kika yi shiru? Ko auren kike so ne?"
Iliya ya karashe da tsigar tsokana, yaqe tayi tana me sake kallon sa
"Wane makaranta zaki tafi in kin gama sabongari"
Iliya ya sake jefa mata tambayar nan
"So nake inje College ɗin Potiskum Nima, sbd labarin da yayana yake bani akan makarantar"
Ta ƙarashe tana me miqe wa tare da ce masa zata je ta siyi ƙayau ƙayau ɗin dan taga layinta yazo
Tafiya ta fara yi shiko yana Binta a baya, share sa tayi ta karasa gun ta siya ta juya da nufin tace masa ita zata wuce gun yayanta se taganshi da wata suna tsaye, se taji sam bata ji dadi ba, hango yayanta tayi yana zuwa, yana ƙarasowa suka kama hanyar gida, tana jin wasu ƴammata na gulman Iliya da yarinyar da ta gani,
"Gaskiyan ki ne ladidi Iliya yana da kyau da zubi sosai gaskiya yarinyar can tayi dacen saurayi"
Ta jiyo muryar ɗaya daga cikin yammatan ta fadi, sannan tana jin sanda wacce aka kira da ladidin ta saka dariya harda cewa
'Da bata da saurayi da se ta jawo hankalin sa'
Shi kuma isuhu mamakin shirun Fatima yake, can kamar ze mata magana, se kuma ya fasa yana sake nazartar ta sosai.
Sun isa gida suka tarar da har yanzu Me Gari na tare da muƙarraban sa, shigewa abun su suka yi, suka taradda goggo ne a zaune ata verandar kofar dakin ta, ga Zulai a zaune a gefen ta na dama Musa kuma a na hagu, suna ganin Fatima suka gudu dakin mamansu, Fatima a ranta tace
'Yafi muku'
Zama suka yi ita da Isuhu a gefen Goggo, miqo musu abincin su tayi da ta zuba musu a gu daya, karba suka yi suka suka fara ci, kowa da abinda yake dasawa a zuciyar sa, suna gamawa ta cinye ƙayau ƙayau ɗinta.
Zuwa karfe goma Fatima ta shige daki taje ta kwanta, tunanika take tayi, sannan so take tayi bacci sede ta kasa yi, abinda ya wakana ɗazu a dandali take ta hasasowa, maganar Allah ba? da taga iliya da wata abun ya mata zafi, ita a rayuwarta bata san reni, idan yarinyar taga yana kula ta sannan itama yana kulata ai hakan ze iya janyo mata reni ma, gobe inshallah zata masa magana akan ya kama kansa, tana wannan saƙe saƙen taji shigowar goggo dakin.
Can kuma se bacci yayi awon gaba da ita.
Yau ta kama asabar, kamar kullum Fatima ta tashi a fatimanta, bayan irin wahalar da ta baiwa goggo a gun tashin ta, Seda rana ta fito ras kafin taje tayi asuban ta, a lokacin da ta sake fitowa ta hango isuhu ya fito daga wanka, da kamar baza ta masa magana ba saboda haushin sa da take ji se kuma ta canza shawara ta gaishe sa, shiko amsawa yayi yana washe baki dan ganin yau ta tashi a yadda ya santa.
Can bayan an gama karyawa me gari ya shigo inda suke, bayan sun gaisa shida goggo yace mata ta turo masa Isuhu su tafi gona ganin damuna na kan shigowa, goggo kuwa tsabar yanda Fatima ta ɓata mata rai tun daga asuba yasa tace zata koya mata hankali, da ta tashi isar da sakon me gari se tace yace su dukka su fita hadda Fatiman, Fatima tana kumbure kumbure ta fice suka shige bayan akori kura, bayan an jibge musu abincin da zasu ci acan
Da isar su me gari ya saka su noma Fatima kuma shuka, daga sun nome zata zuba iri a gun, Fatima kuka ne bata yi ba tsabar haushi musamman in ta daga kai taga masu yi musu aiki suna mata dariya isuhu kuma yana gun me gari suna bada direction, wato ita aka rena ga isuhu namiji shi beyi ba se ita mace, ba yanda ta iya haka ta dinga yi tana kumburo baki, shi kanshi me gari Seda ya dara a ransa da yaga yanayin Fatima, can kuwa aka zuba abinta fati aka kama zubawa a ciki kamar wanda Allah ne ya aiko ta, cin mugunta tayi kafin ta kyale.
Basu suka bar gonan ba se bayan azahar, suna zuwa ita da yaya isuhu suka kama rige rigen shiga banɗaki dan yin wanka, karshen ta hakura yayi ya batta tayi, tana fitowa ta kwanta bacci cike da jin haushin goggo, yanzu da ta saka baki ai da baza taje gona ba, goggo kuwa ba abinda take se dariya.
Koda la'asar tayi goggo ta dinga tashin ta akan tayi sallah amma tayi kunnen uwar shegu da ita, tana tsakiyar baccin nata taji abinda ya firgita ta ya katse mata baccin, muryar goggo taji tana fadin "toh tunda kin ƙi tashi ganan kawarki sadiya ai tana sallama daga waje"
Firgigit Fatima tayi ta tashi tana me zare idanun ta, taso taqi yadda da zancen goggon sede kuma ai goggon ba wani sanin sadiya tayi da zata ce mata itace tazo ba, bata gama saƙe saƙen zucin nata ba ta hango Sadiya ta shigo bayanta wata kuyanga ce da wani leda a dauke a hannun kuyangar, baki da hanci ta sake har seda Sadiyan ta karaso daidai inda take.
To say that she is shocked is an understatement, a rayuwarta bata taɓa tunanin Sadiya zata taba zuwa gidan su ba, toh me ma ya kawo ta, daman ya'yan sarakuna suna yawo ne?
İkon Allah
Mu haɗe a na gaba
Fadrees.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
7.
Free Page
Maganar da sadiyan tayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa
"Ko dai bakya farin ciki da zuwa na ne?"
"A'a Sadiya kawai nayi mamakin ganin ki ne"
Ta ƙarashe tana me jan hannun sadiyan ganin tazo dab da ita
Dakin goggonta ta kaita suka zauna kowa yayi shiru, can kuma se masu aikin gidan nasu suka shishigo musu da abinci, bayan sun fita goggo ta shigo dakin, Sadiya har ƙasa ta tsugunna ta gaida ta, amsawa Goggon tayi tana me sake fita daga dakin dan ta basu waje, Fatima ta matuqar jin daɗin ganin yadda sadiyan ta gaida goggonta dan har Seda fuskan ta ya nuna, duk da ita kanta wataran ba gaida Goggon take ba, ita kuma Sadiya a nata bangaren mamakin yanayin gidan nasu tayi, wai a haka nan ne gidan me gari? Amma kuma ta lura kaf garin ma babu ya nasu a kyau, Fatima ne ta katse mata tunanin ta ta hanyar jefa mata tambaya
"Nikam Sadiya ɓatan hanya kika yi ne kika zo gidan mu? Ko kuma dai hanya ne ya biyo dake kika ce bari kizo mu ɗan gaisa a tsattsaye?"
Ta ƙarashe har yanzu tana me mamakin ganin Sadiyan
Dariya sadiya ta ɗan yi kana tace
"A'a kawai dai gani nayi yakamata Nima inzo gidan ku, saboda in miki sallama duk da kema jiya kinzo, shine na tambaye me Nangere, se dazu ma na sake tuna masa sai yace Bodyguard ɗin yaya ya kawo Ni
Ta ƙarashe hankalin ta kwance
Ganin haka, se Fatima ta miqe ta buɗe kwanikan taga duk tuwon dawa ne da na alkama se kuma su miyar kuɓewa da karkashi, ji tayi baza ta iya bawa yar sarki wannan tuwon nasu ba, ganin haka se sadiyan tace mata
"Ya kika tsaya ne Fatima, ki zuba mana mana"
Ganin haka se ta zuba musu tuwon alkama da miyar kuɓewa da man shanu suka kama ci, duk da abincin be ma sadiya wani dadi ba haka ta daure taci musamman ma ganin hadda man shanu akai, suna tsakiyar ci ne Inna larai tayi sallama ta ajiye musu wani kwano tayi gaba
Budewa Fatima tayi taga zabi ne a soye sunsha mai sai ɗaukar ido suke, take ta zuba musu suka kama ci suna ci suna hira sama sama, Sadiya ke ce mata gobe ai da wuri zasu kama hanyar mamudo, Allah ya sa alheri ta mata sannan tace dan Allah in ta dawo ta aiko mata zata zo su gaisa ana haka suka tashi suka yi la'asar, se can sadiya ta miqe akan zasu wuce, ledan hannun ta ta sa kuyangar ta ajiye a ɗakin, suka yi waje, abinda Fatima ta gani ya bata mamaki, gani tayi an jibge wa su sadiya goma na arziki, su ƙoyaye ne, su man shanu da kuma nono me ɗan karan yawa, ita kanta Sadiya seda tayi mamaki dan har ƙasa ta durqusa ta sake godewa goggo, suna isa bakin motar su sadiyan, Sadiya tace da Fatima tayi wa me gari godiya, hango su Hanne da su harira tayi suna zuwa, suna ƙarasowa suka tsugunna suka gaida su, Fatima kanta har rawa ya soma yi, ba abinda ma taji daɗin sa kamar Sadiyan da suka gani a gunta.
Ana haka sadiya ta shige mota suka tafi tana me dago mata hannu
Su Hanne kuwa daman gaisawa suka zo yi, sannan suka ce mata jiya sun ganta a dandali amma bata dade ba ta tafi Allah ya sa dai lafiya, ce musu tayi lafiya ƙalau daga nan suka ce zasu wuce sannan dan Allah taje gun gaɗa.
Gyaɗa musu kai kawai tayi kafin tayi shigewan ta gida.
Sadiya kuwa koda ta koma gida se ta iske mamarta ta dawo, sannan me Nangere na sashen nasu, tayi matuqar mamakin ganin hakan dan se ya shafe watanni beje sashen ko wacce mace ba sede matan su iske sa a turakar sa, gani yayi ana ta shigo da kaya hakan se ya basa mamaki,
Muryar Mamarta ta tsinkaya
"Ke sadiya daga ina, sannan wannan tulin kayan suma daga ina"
"Mama kin dawo? Sannu da zuwa ya hanya, Gabur na tafi gidansu wannan ƙawar tawa Fatima wanda tazo shekaran jiya, acan aka bani kayayyakin nan ma"
Taɓe baki maman nata tayi, shiko me Nangere se yaji sun burge shi har yace zeyi ma me Garin Gabur din sakamako.
Can bayan Isha kaɗan isuhu ya tisa keyar kanwarsa se dandali, yau anyi wasanni sosai da sosai anyi su gasa kala kala, emmata sun kekkeɓe da samarikan su suna ta hira aka sake barin fati ita daya bata da ko mashinshini ne, hakan kuwa se ya ɗan ɓata mata rai, ta dinga jujjuyawa ko zata ga Iliya taga wayam, daga karshe se ta dangana, ta samu guri ta zauna wai dan ta hushe haushi kawai se ta hango isuhu da yarinyar da take ganin su tare kwanan nan, gani tayi yarinyar na kokarin taba masa fuska ai bata san sanda ta miqe tayi gun ba, tana zuwa ta shaqo wuyar yarinya
Ganin haka yarinya ta fara numfashi dakyar, dakyar aka samu aka raba Fatima da yarinyar me suna jummai.
Fatima kuwa se cewa take
"Kar ki sake in sake ganin ki da yayana inba haka ba sena babballaki'', ai tuni yarinya ta arce