Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9

"Ki fito kici abinci"
Ta tsinkayi muryar sa, ɗaga ido tayi da niyyan tace masa baza taje ba se taga yasha murrr
Biyo sa tayi taje falon, already goggo ta zuba musu a plate daya, nan suka zauna
Fati se ci take tana hararar ƙasa, dan tasan ze iya bige idon nata.
Suna gamawa tayi Isha ta kwanta, se bacci yaqi daukan ta, tunanin club ɗin dazu take, gaskiya duniya nada matuqar faɗi, bata taɓa tabbatar da hakan ba se yau kuwa.
Toh Allah Ubangiji ya kyauta, sannan Allah ya shirye su in masu shiriyar ne. Daga haka tayi bacci.
Me gari ne da ya leqo ya kashe mata wutan dakin yana me jinjina kansa, cike da mamakin halayyar Fatima, wato ita baza tayi sharing daki daya da sa'ade ba kenan, ta gwammace ta kwana ita daya.
Daga haka ya koma dakin sa shima ya kwanta dan dama daga gate yake yaje ya rufe gidan ne ya hango ɗakin da take ciki da haske.
Isuhu ma bacci gagara zuwa idonsa yayi, tunani yake shin ina Fatima suka je da wannan yarinyar da bata ma santa ba se yau, gaskiya da ayar tambaya dan yanayin da ya gansu dukkanin su kamar jikin su a ɗan sanyaye, bari ze sake sa mata ido sosai gaskiya
Daga haka shima barawon yazo ya sace shi.
Zan ɗan dakata daga nan😌
Se mun hade a shafi na gaba🤗
Ayi liking da sharing Please.😥
Taku ce har kullum👌🤍
FADREES 🖋️.😘😘
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
10. MAIMUNA AGAIN
Free Page
Da safe sai wajen bakwai hajjaju makkatu tayi asuba, tana gamawa tayi wankan ta tare da maimaita kayan da ta cire, a cewar ta se ana dab da fita zata je ta sako kayanta masu bala'in kyau ta cancaɗa kwalliya abun ta.
Tsaya! Toh ai ita bata da kayan kwalliyar ma, da taga dai ba inda saƙe saƙen ze kaita se kawai ta fice zuwa falo ta tararda Babarta Tala ne kawai da yara, yi tayi kamar bata gansu ba ta wuce ɗakin goggonta, ganinta tayi a kwance akan nata katifar ta rufe ido tana lazimi, ƙare ma ɗakin kallo tayi, ilai kuwa, hasashen ta ya zamo gaskiya dan ɗakin sak irin nata ne har direction ɗin yanda katifar take.
Can kaman baza tayi magana ba tace
"Goggo İna kwana"
Bude idonta goggo tayi tana me kallon Fatiman dan bata ji sanda ta shigo ba kana ta amsa da
"Lapiya qlau"
"Goggo ina abinci na?"
Fatima ta sake mata magana a karo na biyu
"Yana tsakar kaina"
Goggon ta bata amsa
Matsowa tayi kusa da Goggon tace
"Goggo ayyah dai, nidai yunwa nake ji gaskiya, ke ko tausayi na bakya ji, ina matsayin yar autar ki kamata yayi ai kisa yaya isuhu yaje ya siyomin"
Washerere goggo tayi da baki tana kallon ta, ta bude baki zata bata amsa taga an bankado kofar
Musa ne ya shigo cikin dakin yana ɗar ɗar saboda ganin Fatiman a ciki
"Goggo inji Baba wai yana jiran ki a falo"
Yana gama faɗa yayi ficewar sa
Miqewa goggo tayi tana me mara masa baya fatiman na take mata baya, sunzo daidai fita daga kofar falon Goggo ta watsa ma Fatima harara akan ta dena binta, a memakon ta koma se ta laɓe dan so take taji me zasu tattauna da me gari, koda taga baza taji komai ba se ta koma falo ta samu kan kujere ta zauna tare da saka su xulai aiki, itama kuma babarta se bata tanka mata ba dan tsoron rigimar ta take
Ita kuma goggonta tana fita ta gansa ata ɗan gefe, ya zauna a kan wani kujera, karasawa tayi ta zauna akan kujerar da take fuskantar tasa
"Yauwa sa'ade daman so nake mu ɗan tattauna kafin Isuhu ya ƙaraso da abin kari tunda daman maganar ba wata me tsayi bace, daman akan matsayin da aka ƙaramin a fada ne, yanzu gaskiya ba kamar da bane dole ne zamu dinga raka Me Martaba gari gari domin halartar taron da ta shafi jaha baki ɗaya, yanzu zancen da nake miki, gobe goben nan zamu tafi Damaturu da Me Nangeren amma a goben zamu dawo saboda haka tafiyar mu ta tashi daga gobe ta koma jibi tunda Kinga bansan a wane lokaci ne zamu dawo goben ba, shine nace daman zan fada miki kinsan sha'anin karfe se a hankali, yanzu dai kuje ku shirya kafin yaron nan ya dawo in yaso da an karya se a kama hanyar zuwa ziyarar dan anjima dole zan shiga fadar mai Fika na samu ganin sa domin tattaunawa akan cigaban kauyen namu"
Koda me gari ya gama magana, se goggo tayi ta masa addu'ar nasara tare da nuna jindadin ta bisa ga wannan alkhairin dake binsu daga nan suka miqe kowa yayi cikin gidan, a falo ta iske su su duka, da ta dora idonta akan su Tala se taga duk sunyi wanka sun shirya Fatima ne da kayan jiya a jikin ta,
"Fatima kije kiyi wanka da Isuhu ya dawo zamu fice"
"Goggo nayi wanka fa, kawai ƙin sakawa nayi se zamu fita zan canza"
Daga nan ko uffan bata ƙara ba tayi shigewan ta ɗakin ta, can se gata ta fito ta canza wani kayan daidai sallamar Isuhu kenan.
Amsawa su babarta suka yi itakam Fatima taqi ko kallansa ma, se ma plate da ta gani a gefe da ta janyo ta fara zuzzubawa, doya da ƙwai ne da shayi da bredi se su madara, doyan kuwa yana da ɗan karen yawa gashi ya soyu gwanin ban sha'awa, bayan ta gama zuzzubawa kowa ta dauki tray ta ɗora plate daya da kofi da flask din shayin tare da madara da bournvitan tayi hanyar dakin me gari, sallama ta doka, me gari na kokarin saka kayan sa da hanzarin sa ya ida sakawa ya juya ya kalli kofar daidai shigowar ta cikin ɗakin.
Har ƙasa ta durqusa ta gaida me gari wanda hakan da tayi ya matuqar basa mamaki amma se be nuna ba, shidai se kawai ya amsa
"Baba daman zuwa nayi ince maka nidai gaskiya bazan koma gabur ba, kawai ka dauki Baba Tala dasu Musa ku koma dan daman sune suka yi kalar en kauye, in yaso se ka barmu da goggo da Yaya Isuhu anan se ka dinga zuwa kana gaida mu"
Kallon kanki daya kuwa me gari ya jefa wa fatima, amma se ta maze tace
"Baba baka ce komai ba, nidai gaskiya baba bazan koma kauye ba"
Ta ƙarashe tana me haɗe rai
'Allah Sarki A'isha, da kina nan da zaki ga ƴar ki me matuqar kama dake sede sam Fatima bata biyo halin ki ba,'
"Baba kayi shiru"
Me gari ya tsinkayi muryar Fatima a cikin kansa
"Naji zanyi tunani akai"
Ya samu bakinsa da furta mata haka, yayi hakan ne dan ta sanya masa salama amma ba wai dan yana nufin hakan ba
Ita kuwa koda jin haka se ta kaiwa me gari wani wawan runguma, da badan yana da ɗan saurin karfi ba da ta jefar dashi ƙasa
Ficewa tayi tana me cewa
"Baba kaci abincin ka kar yayi sanyi"
Murmushi ya sanya ganin yau sun rabu lafiya ƙalau da Fatima
Koda ta koma falo taji su babarta se santi ake ana yaba garin Potiskum
Su Musa kuwa basu taba zuwa inda suka ji dadin rayuwar su kamar nan Potiskum ba dan ana cin bredi da shayi.
Koda ta daga kanta se bata ga isuhu ba, zama suka yi suka karya kowa ya miqe ya fice ita kuwa ta runtuma zuwa cikin dakin ta ta canza kayi ta wuce toilet tana kallon kanta a mirror
Sake ganin fatalwar yayanta tayi a cikin mirrorn, se wannan karon bata yi maganar zucin ba dan ta san ƙila shi ɗin ne, ilai kuwa, shi ɗin ne.
"Baki iya gaisuwa bane?"
Kamar baza ta gaida shin ba, ta tuna da anjima fa ze iya siya mata tsire tunda ba'a siya Jiyan ba sannan kuma yanzu ai ta girmi ƙayau ƙayau
"Ina kwana Yayana"
Amsawa yayi cike da mamaki yace ta fito ita ake jira.
Fita tayi suka shige motar me gari shi kuma isuhu ya bude gate ya cire motar ya rufe sannan ya fita yaje ya rufe gate ɗin tare da rufe gidan.
Tunda  suka fita ziyara Fatima take leqe leqen gari, duk gidan da suka je se ansan Fatima tazo dan isuhu duk wanda yasan shi to ta tabbata yasan Fatima, gidan Uncle nasa na jiya suka je, lokacin la'asar tayi, daga nan me gari ya fice shida isuhu ba sune suka dawo ba se dab mangariba.
Suna isowa kuwa aka shiga sallah, bayan sunyi sallah Isuhu yaje ya samo musu abinda zasu ci da dare, ana yin Isha me gari ya shigo tare da wasu baƙi, se kawai ya musu tayin abincin da aka siyo suka baje a tsakar gidan daga nan ya kirawo isuhu ya kara aiken sa ya siyo wanda za'a ci a gida, anan ne Fatima tace se taje yace baza taje ba, suka yi tayi me gari ganin yana jin tashin hayaniya se ya shiga ciki, bayan yaji bayanin kowa yace isuhu ya tafi da Fatima, fati daɗi kamar ya kashe ta, ji tayi kamar ta goya me gari a bayanta isuhu kuwa se zungurin ta cike da jin haushinta kuwa ta share sa tana ta kalle kallen ta
Tsabar mugunta Isuhu yaqi yabi inda suka bi juya wai kar Fatima ta haɗa baki da maimuna, canza layin da suka yi se Fatima sam bata ji dadin sa ba, dan tana so ta hadu da maimunan kwarai dan tana da tambayoyi da take so ta amsa mata
Koda suka isa restaurant din se isuhu ya shige ya siya abinda ze siya yazo biyan kudi suka ce POS nasu ya samu matsala sedai ya ciro cash, shine suka fita shi da Fatiman, gun wasu shaguna suka je suka tsaya a lokacin se taji an janyo ta har ta kusan faduwa, dagowa tayi da niyyan da danqarawa koma uban waye ne ashar tayi tozali da maimuna, idan har tace bata ji dadi ba to tayi karya, Isuhu ganin su tare se yaji mugun haushi ya kama sa, gefe suka ja se maimunan take ce mata
"Ai tun daga gidan ku na biyo ku nan, naso inje gidan naku in jira se kun dawo se naga yafi dacewa in biyo ku kawai, wai dan kar mu hadu ne yayan ki ya canza layi?"
Gyada kai Fatima tayi cike da mamaki
Dariya maimuna ta saki ganin yanayin Fatiman kana tace Tou ai jiya ban koma gida ba seda naga gidan ku, naso Nazo yau na fasa zuwa
"Ai kuwa da kinzo baza ki same mu ba, amma maimuna Ni ina da tambayoyin da nake so na Miki yanzu ya za'a yi?"
"Sede kizo gidan mu gobe".
"Wai kina nufin masarautar ku?"
Fatima ta tambaye ta
"Ehhh"
Maimuna ta bata amsa, zaro ido tayi da nufin ta sake magana Isuhu ya kama jan hannun ta ita bata ma san sanda ya karaso gün ba, shigewa cikin restaurant din suka yi ya biya kudin ya karbo abincin suka fito suka sake iske maimuna
"Yaya zanci tsire"
Ya jiyo Muryar Fatima
Daman yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, shi yasan ba dan Allah ta biyo sa ba daman.
"Bani da kuɗi"
Isuhu ya bata amsa
"Ni ina da kuɗin" suka tsinkayi muryar maimuna
Share ta yayi ya cigaba da jan hannun Fatima,
"Nidai yaya se Naci tsire bazan koma gida ba yau"
Ganin zata tara masa jama'a suka wuce hanyar gun me tsiren jiya, yana tafiya yana zungurin kanta sam ya hana ta samun daman magana da maimuna ita kuma bata dena binsu ba
Ganin haka se ya fawwalawa Allah ya kyale su ya wuce gun siyan tsiren
A lokacin ne kuma maimuna ta gaya mata process din da zata bi taje gidan su.
Daga haka ta juya, su kuma suka koma gida.
Washegari da misalin karfe sha biyu Fatima tayi shirin ta na zuwa fada, lokacin me gari ya jima da tafiya Damaturu, a falo ta iske su goggo tace musu tana da tsohuwar dari biyu zata je ta siyo biscuit, goggo de ce mata tayi karta jima tunda bata san kan gari ba, ko karshen zancen Goggon bata tsaya jira ba tayi hanyar gate tazo fita ta hadu da yayanta Isuhu a kame a bakin gate din.
Littafin nan na kudi ne akan Naira 300 kacal.
Zaki saka kuɗin ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan kina so tun yanzu zaki iya biya, in kuma se an gama free pages ne ma dukka daidai ne.
Idan anyi completing kuma it'll be 500.
FADREES 🖋️.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
11. FATIMA'S VISIT TO FIKA PALACE
Free Page
Abinda Fatima bata taɓa yi ba tayi yau, wato rissinawa in zata gaida Isuhu
Shi mamaki ma ta bashi, wai yau Fatima ce ta durqusa har ƙasa tana gaida shi? Gaskiya something is fishy, daman tunda ya hango yanayin yanda take ta sauri sauri sannan take ta tambayan lokaci yasan ba lafiya ba, kamar kuma bata da gaskiya
"Ina zaki je ne Fatima?"
Ta jiyo muryar Isuhu na jefa mata tambayan da yasa ta sake duburburcewa,
"Amm amm dama shago xanje in siyo biskit"
Zancen ta be dauki hankalin sa ba amma se ya kyale ta yace mata
"In kinje ki zauna" tare da shigewa cikin gidan, daman abu yazo dauka zeje abokan sa suna jiran sa, wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dafe kirjin ta, ashe daman tana tsoron Isuhu?
Share zancen tayi ta fice daga layin su ta hau kan kwalta daman tasan sunan unguwar, yanzu dai abinda ya rage mata shine ta nemi gidan sarkin
Wani shoeshiner ne yazo wucewa ta tsayar dashi ta tambaye sa, shi kuma ya mata kwatance, indai har ta yanda ya mata kwatancen ne toh gidan ai ba nisa ma
Ai kuwa be wuce tafiyar minti 20 tayi ba ta fara hango wasu dogin gini masu karfi da tsari, bakinta a hangame har ta karaso bakin kofar shiga ta cikin masarautar
'Wai wai wai, garin dadi na nesa, wai hausawa suka ce ungulu ta leqa masai'
Yanzu wannan wawakeken gurin ne za'a ce masarauta? Wannan ai sede wani garin, bar ma batun wani garin ai ko gabur za'a iya hada shi da nan
Tana ta saƙe saƙen ta tana ƙara ƙarato palace din, sede tazo kusa ne taji tsoro ya kama ta, musamman da ta hanzo fadawa hannun su riqe da zuqa zuqan bulalai ai se taji hantar cikin ta ta motsa, nan dai ba Nangere bane ballantana tace zata je ta musu tijara dan taga alamun ubanta zata ci anan
Har tayi kaman ta juya se taga baza ta iya hakan ba, ko ba komai ai tana so taga ya yanayin cikin nasu gidan yake
Can se tayi kamar ta shiga se kuma ta fasa, lokacin har ana ta kiraye kirayen sallan azahar
Daga karshe se kawai tayi shahada ta doshi babban gate din
"Yarinya daga ina?"
Wani basamuden bafade ne ya jeho mata wannan mummunan tambayan, to mummunan tambaya mana tunda shima mummunan ne, tunani ta fara yi a ranta, tunanin be wuce na jinjinawa da take jefa ma maimuna ba, lalle itan ba karamar hatsabibiya bace, yo hatsabibiya mana, idan ba hatsabibiya zata ce ba me zata ce, yarinyar da zata iya fita da dare a irin wannan gidan kuma da irin wadannan uban tsaron kam ai hatsabibiya ce.
"KE?"
Taji an sake zabga mata wani mahaukacin tsawan, karkarwa ta kama yi, bakin ta na ɓari tayi shahada tace
"Nazo gün Maimuna ne"
Dariyan renin hankali suka saka, wanda hakan ya kona ran Fatima, gashi nan ba irin fadawan Nangere bane ballantana ta musu rashin kunya
"Ki ɓace anan ko kuma jikin ki ya gaya miki"
Ta tsinkayi muryar bafaden
Rai a ɓace ta juya da nufin tabar gun, wato maimunan ta rena ta shine yasa tace tazo dan ta tozarta ta ko? To ba komai akwai Allah.
Har ta juya ta fara tafiya, se ta tsaya cakkk tace
"Gun Gimbiya Ƙarama nazo"
Koda jin haka se dayan mutumin yace
"Dazu ba naji ance gimbiya ɗaya ta aiko akan zata yi bakuwa ba? Kodai wannan ce baquwar?
Dayan ne yace.
"Inaga itace a tambayi Bala mana, ba a shi aka baiwa saƙon ba?"
Daga nan aka ƙira balan a waya aka tambaye sa dan dutyn safe yake yi kuma ya tafi
Koda aka tambaye sa se yace sunan baquwar Fatima.
Tambayan sunan ta suka yi tace musu 'Fatima', daga nan suka ce mata ta shiga
Wani ne yace tabi bayan sa, bin bayan nasa tayi har suka iso sashen su maimunan, wuyan Fatima kuwa kamar lagwani, da lagwanin ne ma da ya jima da lanƙwashewa saboda yadda ta dinga juya shi da sunan kallo, Gashi dai a yanayin sutura da yadda take su tafiyar ta baza kace zata aikata ba sede kuma, a lokacin ne ta fito a matsayin ta na ƴar kauyen Gabur, sunyi tafiya me nisa ƙwarai dan ƙafar ta har ya gaji, suna isowa mashigar side din su Maimunan wanda ya rako ta ya juya, knocking tayi wata kuyanga ta buɗe, ce mata tayi tana neman maimuna se tace ta shigo, tana saka ƙafar ta se taji ƙafar ya lume cikin wani abu kamar kulya, wani laushi ne me bala'in santsi ya ziyarci ƙafarta, tsabar dadin da taji har hajijiya kusan kama ta yayi ga kunnen ta ya kama motsi, ƙarasa shiga tayi ƙafarta se fada wa cikin santsi take, zama tayi akan wani royal sofa cike da fargaban kar azo ace mata ta tashi daga kai, can se taga an bude wani kofa maida hankalinta kan kofar da se yanzu ta lura da shi tayi, kofofi biyu ta gani a gun, ko wannen su yana fuskantar juna, ganin maimuna tayi ta fito sanye da wani leshi kalar vanilla cream yasha adon pink pink, bakin Fatima a sake har ta karaso tace
"Ki rufe bakin mana"
Jinjina kai Fatima tayi tana me kara kallon ta da kyau
Ba abinda ya fito daga bakin Fatima sai;
"Maimuna se yau na tabbatar da ke ɗin hatsabibiya ce, duk wannan uban tsaron gidan naku a haka kike satan hanya ki fita wajen masarauta"
Ta ƙarashe cike da dimbin mamaki
Dariya ta saki sai can ta tsagaita tace mata
"Kaf gidan nan babu me hankali na da kirki da biyayya a zahiri, amma a baɗini ai ke kinsan koni waye ce"
"Nikam ya kuka ƙare da masu tsaron kofar shiga?" Maimuna ta jefe ta da tambaya
"Ohh daman kinsan da haka kenan, kinsan za'a min tsawa kan a barni in shigo kenan?" Fatima ta ƙarashe ranta a haɗe tuna yadda ta muzanta kafin ta shigo
"No ba haka bane, tunda safe fa na sa ace ma wani wai Bala yake ko wanene? akan zanyi baƙuwa me suna Fatima, toh bansan ya suka yi ba, kinsan mu haka ake a gidan sarauta idan ba sanar da zuwan mutum muka yi ba, ba barinka za'a yi ka shigo ba
Jinjina kai Fatima tayi cikin gamsuwa
"Ni kam tashi muje muci abinci"
Ta jiyo maimunan ta faɗa
Se a lokacin cikinta yayi ƙaran yunwa, wato gidan su Maimuna aljannan duniya ne, ashe shi yasa ake jin masu kuɗi sunyi miqit ashe sunsan irin daular da suke ɗiba.
Miqewa tayi suka yi kan dinning, tayi serving nasu varieties of mouth licking dishes, ai kuwa yawun Fatima se reto yake, se da ta fara afkawa bakin ta taji hankalin ta ya kwanta, sede kuma wataqila gobe iwar haka tana gabur tana gabzar tuwo da miyar kuɓewa ko kuka, amma kuma ai me gari ya mata alkawarin zama a nan ai.
Daga haka da suka gama suka dinga hira, Fatima na tambayan ta ina iyayen ta ta ganta ita kadai, sai tace mata ai nan sashen ta ne na ita kadai, da ita da yayar ta ne toh yayar tayi aure yanzu ita kadai ce, sannan mamanta yanzu hutawa take kuma in tana hutawa ba'a tada ta, mamaki kamar ya kashe fati jin wai nan sungumemen sashen wai nata ne ita kadai ikon Allah, kuma bata jin tsoro?
"Yayanki haka yake da sa ido da masifa"?
Maimuna ta jefa wa fatima tambaya
"A'a wlh, kawai dai ke ɗin ne baya so, musamman da yaga juya ya neme Ni be same ni ba kuma kece sanadi"
Taɓe baki maimunan tayi nan suka cigaba da yin hira akan makaranta, maimuna take ce mata ai itama tana Turkish sede Day take ba boarding ba
Ko da jin haka seda ta zabura, bakin ta na rawa tace
"Kin san Sadiya Muhammad Ibn Alƙali"?
Na santa mana, ai set namu daya wannan Term din aka kawo su sannan tana science Ni kuma Art, ko ba ƴar Me Nangere kike tambaya ba?"
Itace wallahi, ai ƙawata ce, dan Allah in kinje ki gaida ta"
"Gaskiya bazan iya ba, sede ki rubuta mata letter in bayar a bata, dan mu acan kowa ji yake da kansa, sannan Ni Kinga matsayi na yafi nata, da Ƴaƴan Mai Damaturu kawai nake alaqa, ke ɗinma sa'a kika ci dan da ko kallo baki ishe ni ba kin sani"
Maimunan ta ƙarashe tana yatsina cike da yauƙi dan har ta hasaso girman ta ya zube.
Tsaki Fatima tayi tace,
"Ai kinsan da hakan kika gayyace Ni gidan naku, duk da babana be kai matsayin baban Sadiyan ba, Ni idan bakya san mu'amala dani kiyi sauri ki bani paper da biro in rubuta mata lettern in kama gaba na
Ta faɗa cike da jin haushin abinda aka fada akan Sadiya da kuma kanta, ita sam bata san reni
"Ke ba wai ina nufin na rena ta ba, ba ma wani having good times da ita ne, besides, class namu ba ɗaya da ita ba nace miki, sannan naga ita ba ruwanta da ƴan uwanta take yawo ma"
Se anan Fatima ta saki ranta suka cigaba da hira har maimunan ta dakko mata jotern ta ta rubuta lettern tace dan Allah ta bata hand in hand
Sai can anjima ta tashi zata tafi, Maimunan tace mata gobe ƙila tazo gidan su, Fatima kuma tace gaskiya ba lallai ta same ta ba zasu iya komawa kauyen su, da haka se Maimuna ta rubuta numbern ta ta bata tace ta samu layin isuhu ta kira ta dashi.
Da mota Sadiya tasa aka maida ta bayan dimbin abubuwan da ta haɗa mata, a haka Fatima tana ji tana gani ta ƙi karba wai tana gudun reni.
Tun suna hanya da ta tuna yanzu fa zata je gida ta taradda da su hankalin su a tashi, nan da nan taji hankalin ta ya ɗunguma ya tashi.
FADREES 🖋️.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘Romantic Love Story.
Na Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
12. BACK TO GABUR
Free Page
Ta so tace ma drivern ya sauke ta a hanya se kuma ta canza shawara, roqon sa tayi akan ya taimaka ya cece ta in suka koma gida suka tarar da problem, nan da nan ta zayyano masa komai, daman mutum ne me yanayi da natsuwa, yace ze temaka mata amma Seda tasha faɗa a gunsa, share sa kawai tayi dan taimakon ta zeyi amma ji tayi kamar ta make sa, wai ita ze gani yace zewa wa'azi, koda suka isa kofar gidan nasu kuwa ta hango goggo duk ta firgice su Babarta Tala kuma hankalin su a matuqar tashe, daga zuwa shago har yanzu shiru? asirinta ɗaya da Allah ya rufa shine har lokacin Isuhu

Chapter 5 of 9