magana akan babarki, ki dena shiga harkan ta, sannan ki dinga girmama ta ko ba komai matar ubanki ce, dan Allah Fatima ki kiyaye, yanzu dazu abinda kika yi ai be dace ba har ki hau ruwan cikin ta kina mazgarta"
Da 'Toh' kawai ta amsa ta kama bude ledan Iliya, isuhu ne ya fito daga dakin sa ya iso gun nasu yana jiran yaga meye a cikin ledan da iliyan ya bata
Goggo dai bata ce musu uffan ba se cin naman ta take tana santi, har da yi ma Isuhu bismillah yace baze ci ba, wani leda ta ciro a cikin ledan tana budewa taga tsire a ciki me uban yawa dan ze kai na dubu biyu tsabar yawa
Yawunta a take kuwa ya tsinke, zama tayi ta rarraba, ta dauka wa me gari nashi tace isuhu ya zauna suci tare, goggo ce ta tambaye ta wa ya bata wannan uban tsiren sannan meye a ƙasan ledan, gaya mata komai tayi, se taga goggo tana murmushi tana ɗan rufe fuska alamun jin nauyi, ita kam ko a jikin ta ƙasan ledan kuwa da ta zazzage Lip gloss biyu da powder da jambaki da kwalli biyu da su ribbon uku ta gani, harda pad (su iliya ansan pad) da Mirror da comb da kifiya bibbiyu.
Wai goggo ce ke tambayan meye pad din, ita kanta Fatiman da badan a gun Sadiya ba da ba sanin shi zata yi ba
Ajiye musu tsiren tayi a gaban su ita da goggo, daman isuhu yace baze ci ba
Suna kan ci dan sunci rabi da kwata ma Goggo tace a ɗibarwa su Musa mana, daga nan fa Fatima ta dire akan baza suci ba shine itama goggon ta tashi ta wanke hannun ta, ita kuwa ta naɗe sauran akan se tazo kwanciya taci tunda tasan goggon ba sake ci zata yi ba
Isuhu kuwa uffan bece ba ƙarshenta ma ficewa yayi a gidan se bayan Isha ya shigo, lokacin Fatima tayi shiri zata fita dandali, ta shafa powder tasa man lebe sannan ta saka kwalli tana riqe da sabon mirrorn ta tana kallon fuskan ta, se tayi wani irin kyau, kamar wacce zata tafi gasar kyau, gashi ta saka riga da zani sun fito mata da shape nata, se ta zama kamar wata model tsabar kyau.
Tsintar Muryar yayanta tayi yana mata magana
"Ke ina zaki?"
"Ina kuwa banda dandali"
Fatima ta basa amsa tana wani ciccin magani, wannan ma ai tambayar renin hankali ne, ai de yasan tana zuwa dandali shine yake so ya kawo mata cikas? Toh wallahi be isa ba ta Allah ba tashi ba
"Baza kije ba"
Ta jiyo Muryar sa, itama kuwa ta maida masa da tambayar ta hanyar cewa
"Me yasa?"
Ji yayi kamar ya mangare ta se kuma yace
"Saboda kije ki haɗu da wancan yaron ne koh? Toh baza ki ba"
"Nidai wallahi zanje"
Ya sake tsinkayar muryar ta.
Ganin da gaske hana ta zeyi se ta apka a guje ta fice a gidan, a ranta tana faɗin 'ɗan buƙulu kawai'
___________
Littafin nan na kudi ne akan Naira 300 kacal.
Zaki saka kuɗin ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan kina so tun yanzu zaki iya biya, in kuma se an gama free pages ne ma dukka daidai ne.
Idan anyi completing kuma it'll be 500.
FADREES 🖋️🖋️📝.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘Romantic Love Story.
Na Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
15. TROUBLED
Free Page
Tunda ta kama gudu Bata tsaya ba se da ta ganta a filin gaɗa, numfarfashi ta fara saki kana ta koma sakin ajiyar zuciya.
Su Me Gari suna zaune ana tattaunawa a majalisa suka ga mutum ya fito a guje yayi hanyar filin gaɗa, ganin isuhu suka sake yi ya fito a hanzarce Baba Ladan ne ya ƙwala masa ƙira ganin yayi setin da suka ga fatiman ta bi, zuwa yayi ya durqusa ya kwashi gaisuwa
Liman ne ya tambayi ba'asin fitar Fatima a guje se kawai yace musu ba komai bane
Ladan ne yace yaje ya qira Fatiman tazo gaban fada dan ɗazu an kawo ƙarar ta wai ta haɗu da wasu yara sun yi ma wata duka sun faffasa mata jiki, isuhu da jin haka ya saki salati yabi bayan fatima.
Fatima kuwa koda ta hango filin dandali se ta kama taku a hankali dan ta gaji, duk wanda ya kalle ta zece yanga take ita kam bata ma san tana yi ba gashi lokacin wata yazo karshe ɗinnan akwai haskensosai sannan akwai hasken solar a gun irin me haske sosai ɗinnan, tana isa kuwa hankalin kowa ya dawo kanta, dan tayi masifar kyau hasken solar se ya ƙara bayyana farin fatar ta, ƙwayar idanunta kuwa suka sake yin wani kalan haske se ya zama kamar asalin colourn gold ɗin, ılıya dake zaman jiran ta ne ya miqe a mamakance, shi ya dauka baza tazo ba ganin ta jima, ita kuma ta ɓata lokaci ne a dalilin hanata fitan da Isuhu yayi, sake kallon ta Isuhu yayi dan ya kasa motsi ma, tabbas yasan Fatima tana da kyau, kyau irin na sosai da sosai ɗinnan, sede be dauka hakan take ba, lallai kam se ma ya kalla kamar duk abubuwan da ake cewa tana yi kamar sharri ake mata dan gani yayi wannan innocent yet calm face ɗin nata baze aikata rashin ji ba, ɗaga kansa keda wuya kuwa gani yayi hankalin kowa ya koma kanta, se yaji haushi sosai saboda haka se ya miqe ya wuce gunta, yana isa gaban ta ba abinda ya fara fita daga bakinsa sai
"Kinyi kyau sosai Fatime, hasken ki ka iya sa wannan watan dilmiyewa, hakikanin gaskiya keɗin kyakkyawa ce ko a cikin kyawawan da suka amsa sunan su kyawawa".
Daskarewa fatima tayi jin abinda yace, wani kalan feeling taji ya tsarga mata, sannan kuma waye Fatimen? Meye kuma Fatime, ba Fatima bane asalin sunan ta? Ɗazu ma tana ji ya kira ta dashi kawai sharewa tayi dan ta dauka ko kunnen ta ne be ji ba
"Zo muje"
Kawai yace mata
Binsa tayi suka samu waje suka zauna, daga nan hankalin kowa ya koma kan abinda yake
"Meyesa kake cemin ina da kyau, ko baka fada ba ai na sani, sannan ko yayana baya gaya min"
Ta faɗa tana haɗe girar ta
Ce mata yayi;
"Saboda shi yayanki ne Fatime Ni kuma saurayin kine"
"Yaushe ka zama saurayi na, Ittaqillah, banda ƙarya wallahi kar kaga dan kana da ɗan kyau zaka iya gaya min abu in yadda, kodan kaga baka yi kala da ƴan ƙauyen nan bane?, ranan fa kar ka manta na ganka da wata kuna tsaye kuna hira"
Dariya ya saka sosai kana yace
"Haushi kika ji kenan da kika ganni da wata"
"Toh ya bazan ji haushi ba, Ni bana san mutum yana kulani sannan yaje yana kula wata sam bana san hakan, kalen taje ta rena Ni?"
Ta ƙarashe da iyakar gaskiyar ta,
"Toh ayi min afuwa Fatime, bazan sake ba.
"Shikenan ya wuce"
Ya tsinkayi muryar ta
"Daga zuwa Damaturu se ka zauna? Se kuma wasiqan da aiko?, sannan ma, wai meyesa kai baka zama a garin nan ne, ko gidan ku fa ban sani ba"
Ta ƙarashe cike da son jin amsa
"Toh ai Ni ba ɗan garin nan bane, Ni ɗan Potiskum ne, ina zuwa nan ne gidan kakata, wancan yaron da kika daka cousin ɗina ne ita kuma yarinyar da kike kishin ƙanwata ce, tana Potiskum ma, nasan baki sake ganin ta ba ai koh?"
Ya ƙarashe yana kallon idon ta,
'Ehh gaskiyar sa, bata sake ganin ta ba tun ranar ashe shi ɗan Potiskum ne'
"Nima ai naje Potiskum ɗin jiya ma muka dawo, gaskiya ban taɓa ganin gari me kyau a kaf faɗin duniyar nan ba idan ba can ba".
Dariya Ilıya ya saki, ita kuma ta tsaya tana hararar sa
"Abinda yasa kika ce haka ai dan baki san su Kano, Kaduna, Maiduguri da su Damaturu bane"
"Toh kaidin ka taba zuwa can ɗin ne?"
"Ehh duk wanda na lissafo naje Ni, sede ba wanda yakai Damaturu kyau"
Ya ƙarashe yana me kashe idon sa ɗaya
"Dan Allah? kaban labarin Damaturun"
"Okay, Damaturu babban birni ne wanda yake dauke da gurare daban daban, akwai kasuwanni, asibitoci, guraren cin abinci da universities, Ni yanzu Kinga misali Universityn mu......"
Be kai ga ida maganar sa ba isuhun da basu san da zuwan sa gun ba ya kama jan hannun ta, shi kuma ılıya se yabi bayansu yana tambayan ba'asi, be dire ta a ko ina ba se a majalisar Me Gari.
"Gata nan Baba Liman".
Baba Ladan ne da har yanzu ƙeyar sa bata warke ba ya kama magana kamar haka
"Fatima kusan kullum in muna zaman fada se an kawo mana ƙarar ki akan kin tsokani mutum, ko kinyi illa a kadarar mutum ko dabbobin sa, duk da abinda kike bamu taba cewa a hukunta ki ba, ko nan Babanki kullum aka kawo ƙarar ki cewa yake a hukunta ki mune muke ƙi, ƙarshenta kullum shi kike bari da biyan diyya, sede yau kuma abinda kuka aikata keda ƙawayen ki ya saɓa wa shari'ar Muslunci, be kamata kuje har gidan su yarinya babu izini ku mata duka ba, yanzu da wani abu ya same ta a dalilin dukan fa, ko baku san cewa har kotu za'a iya kaiku ba akan hakan?
Tukunna ma, meya aike ku gidan su har ku shiga ku dake ta ba tare da ta muku komai ba?"
Ladan ya ƙarashe yana sake maida hankalinsa kanta
"Gaskiya Baba Ladan wallahi sharri aka mana, yarinyar nan kuɗi na ta sace min Naira na dukan Naira har dubu ɗaya daga in bata jaka na ta riqe, sannan da muka je gidan nasu ƙin bamu kuɗin tayi Seda muka dake ta kafin, kuma ma dari takwas taban dan har ta kashe dari biyu a ciki, shine nace ta kawo min Naira ta ɗari biyun a filin gaɗa toh gashi ko zuwa ma bata yi ba"
"Toh ke wa ya baki dubu ɗayan"
Liman ya jefa mata tambayar
"Ɗazu ne babata da Babanmu ya bata ta jefar wai bata so, shine Ni nace masa ina so na dauka, ai ga Me Garin ma a tambaye shi"
Ta faɗa tana hasaso irin dukan da zata yiwa Barira idan ta hadu da ita, wato shine har zata kawo ƙaran ta bayan ita ce ɓarauniyar wallahi zata koya mata hankali
Ana haka sega Barira da mamanta da babanta sun ƙaraso daman tun da Isuhu ya tafi neman fatima Baba Liman ya aika a kirawo su
Bayan an maimaita musu komai aka tambaye Barira zancen kudin da ta ɗauka
Har zata ce sharri fatiman ta mata kamar yadda mamanta ta umarce ta tace, se kuma taga idanun Fatiman nan da nan shakkar ta ta darsu a ranta
Daga nan akace Fatima ta bata haƙuri
Yi tayi kamar tayi yaya, sede ba yadda ta iya musamman ganin idon isuhu da Me Garin da ya zuba mata ido yana jinjina yanda ta iya haɗa zance, wai 'jefar da kudin Tala tayi' idan beyi karya ba wafcewa tayi naga? Toh Allah ya kyauta, shima Iliya yana ji bede ce komai ba
"Muyi haƙuri"
Aka jiyo muryar fatima, ganin haka se Liman yace Barira ta bata haƙuri
Hakuri Bariran ta bata kamar yadda aka umarce ta, mamarta se dalla mata harara take taqi kallon ta.
Daga nan Me Gari ya sallami kowa, har su Barira sun miqe zasu tafi Fatima tace ita a biya ta ɗarin ta biyu, cike da kunya da danasanin kai ƙara babanta ya ciro ɗari biyar dan baida canji ya bayar, ai kuwa tayi wuff ta dafe kudin ta
Daga nan aka rufe taro kowa ya watse, sallama tama Iliya ta shige cikin gida, Isuhu kuwa da ya shiga seda ya ranqwashe kan ta, can bayan me gari ya shiga, ta dauki naman sa ta wuce dakin sa tayi knocking ta shiga ta kai masa
"Wannan fa? A ina kika samu?"
"Baba Iliya ne ya kawo min, hadda su kwalli da man baki"
"Kije ku cinye keda kannenki"
"Nidai gaskiya baba baza su ci ba, Ni akai na kawo wa, dan Allah dan darajar Annabi Muhammad SAW kaçı, na roqe ka da...."
"Shikenan ajiye min zanci"
"Nidai baba kaci a gaba na"
Budewa yayi ya fara ci, can yace mata
"Kika yi karya ɗazu, kika ce wai jefar da kudin Tala tayi, bayan ke kika karɓe "
"Toh Baba in ba haka nace ba za'a ce Nima satan nayi ai, shiyasa"
Daga nan be sake mata magana ba, ya cigaba da cin tsiren sa yana mamakin wato ko kunyan sa ma bata yi shine zata kawo masa abun saurayi, toh Allah ya kyauta"
Seda Fatima ta tabbata ya gama ci kafin ta masa Seda safe ta fice, ta koma dakin Goggonta, Seda ta gama shirinta ta dauko tsiren ta ta fara ci, kasa cinyewa tayi ta ajiye da niyyan Seda safe ta cinye
Goggo na ganin ta ta share ta, daga haka tayi kwanciyar ta cike da tunanin Iliya.
Wannan Kenan.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋🤍
Na Barr. Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
Ban yadda wani ko wata yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wallahi billahi baza mu wanye lapiya ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.
Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.
Da fatan an fahimta.
Nagode.
__________
16. TROUBLED???
Free Page
Da safe kuwa kamar kullum bayan yin wanka, salla, gaishe gaishe da kuma karya kumallo tayi shirinta ta tafi makaranta
A makaranta se shirye shiryen fara Exams ake wanda ake saka ran nan da sati uku za'a fara
Koda ta dawo daga makaranta ta hango babarta tana ta yaɓa ma Goggo magana, wanda hakan ya jawo seda suka yi cacar baki tayi mata rashin kunya ta gaya mata baƙaƙen maganganu waɗanda dole seda suka saka babartata kukan dole, domin fatima sam bata so taga an rena mata iyaye ita.
Koda me gari ya dawo seda Tala ta faɗa masa har da barbaɗa gishiri, shiko ya ƙira Fatima yana mata nasiha wanda suka shiga ta kunnen damanta suka fice a na hagu dan bata ma san ko maganar me yake ba ballantana ma ya dame ta, ita kuma babar tata ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin yadda Me Gari yake mata nasiha ita kuma tana nuna halin ko in kula, taso ace ya saka Isuhu ya zane Fatiman.
________________
BAYAN WATA ƊAYA
Sati ɗaya kenan da fara WAEC ɗin su fatima wanda kafin su fara Seda me gari ya zaunar da Fatima ya sake tuna mata mahimmancin ilimi da dalilin da yasa yake so taci wannan Exams ɗin, bayan shi ma seda Isuhu ya sake yi mata bayani akai, Iliya kuma ya sake ƙarfafa mata gwiwa akan samun nasara a Exams ɗin, wadanda sune dalilan da ya sa ta maida hankali take karatu bilhaqqi, a makaranta har malamai sun gane ta dan yanzu kusan kowa alfahari yake da ita, ba kamar da ba da ta gunduri kowa
Alaqar ta da Ilıya kuwa babu wanda be sani ba a cikin gidansu hatta da babarta Tala kuwa, wanda tayi mugun baƙin ciki da jin wai a Potiskum yake ba'a gabur ba, ita dai abu ɗaya ta sani, wallahi wallahi baza ta bar Fatima taji daɗin rayuwa ba, ƙwafa tayi ta wuce dakin ta abunta a ranta kuwa cewa take 'Se ayi mu gani idan tusa zata hura wuta'.
Mai Gari kuwa kullum cikin yaba halin Iliya yake, Iliyan kuma kullum yakan zo ya gaida shi duk sanda yake cikin garin, yanzu kwata kwata bashi da shamaki da gidan dan har Goggo ta saba dashi, matsalar dai ɗaya ce, Isuhu.
Isuhu har yanzu be aminta dashi ba, hasali ma baya masa kallon mutumin arziƙi, Iliya yasha bashi hannu suyi musabaha yaqi amsa masa, gani yake Ilıya be dace da Fatima ba sannan kamar dan wani abunta yake sonta.
Yau kamar kullum da wuri ta tashi, bayan tayi asuba wanda yanzu tana ɗan kiyaye sallah akan lokaci se ta wuce banɗaki dan tayi wanka, tana shiga taga ruwa a ajiye me ɗumi wanda ko tantama bata yi ba na Me Gari ne Tala ta haɗa masa dan munafurci, dan tun abinda ya faru ranan ta ɗauka talan zata yi zuciya ta dena haɗa masa ruwan amma kuma seta cigaba da yin hakan wanda it's quite suspicious, bata yi wata wata ba kuwa ta dauki ruwa tayi wanka abinta ta fita, Baba Tala kuwa ganin wanda yayi wanka da ruwan seda ta fadi ta suma, mamaki kamar ya kashe Fatima, daga yin wanka da ruwa se ta suma? Gaskiya akwai ayar tambaya akai, har ta gama shirinta ta fice makaranta Tala bata farfaɗo ba sannan Goggo ce ke gefen ta tana ta mata addu'o'i saboda rashin zuciya, Yo rashin zuciya mana bayan duk abubuwan da Talan take mata har zata wani zo gefenta ta taimake ta? Ita kam wallahi da itace sede Talan ta mutu amma wallahi baza ta taimaka mata ba, tana fita ta hango Iliya akan mashin dinsa yana jiran ta, hawa tayi suka dau hanyar Nangere, daman a cikin kwanakin nan shine yake zuwa ya kaita ya ɗakko ta in har yana gari, seda yabi ta kasuwa ya siya mata abinci wanda hakan ya zama kamar wani responsibility nashi kana ya kai ta da alkawarin ze zo ya dauke ta da yamma tunda Exams ɗin su na yau safe da yamma ne
Su Hanne har sun dena jiranta ma zuwa suke su tafi abunsu in sun haɗu toh a gun gaɗa ne ko a cikin makaranta in an fito break ko kuma sanda iliyan bezo gabur ba.
Yanzun ma haka ta kasance, ledan abincin ta ta dauka ta isa gun su hannen suka zauna suna hira Saude se basu labarai take suna dariya dan suna da awa kusan uku kamin su shiga na farko kuma na yau baida ma wahala shiyasa suka samu sararin yin hiran.
Barira suka hango tana ta leqen su, tana so tazo gunsu tana tsoro, dan tun abinda ya faru bata shiga cikin su tsoro ma take ji, ta koma ita kadai take rayuwar ta babu ƙawaye wanda hakan ke matuqar damun ta, hannu fatima ta mata akan tazo, zuwa tayi ta tsaya a gaban su ta kasa ce musu komai
'Ki zauna mana' fatiman tace mata, zama tayi tana ɗan jin ɗar ɗar
"Ba wai kinga mun dawo dake cikin mu ba ki ɗauka mun manta da satan da kika min ne, a'a, mun dawo da ke ne da sharaɗin baza ki sake sata ba dan mu baza muyi ƙawance da ɓarauniya ba, saboda haka ki saki jikin ki damu''
Daga haka suka fara hira, can kuma Fatima ta ɗakko ledan abincin ta ta bude suka cinye daga nan ta zame taje ta duba littafin ta kamin aka shiga Exams, can bayan an fito suka je gun sayar da abubuwan ƙwalama, waɗanda suke da kuɗin kashewa kamar Fatima suke jin daɗin break ɗin, marasa kuɗi kuma sede su zuba tagumi abunsu.
Bayan an koma break suka sake shiga suka yi Exams ɗin su na yamman, da suka fito Fatima tazo ta same su akan zata bi Ilıya suyi tafiyar su kawai, daga haka tabar gurin.
Tana zuwa bakin makarantarsu kuwa taga Iliya akan mashin dinsa yana jiran ta, ɗaukan ta yayi suka fara tafiya seda suka zagaye garin nangeren kafin suka bi ta ƙofar fada suka bar cikin garin, 'Allah Sarki Sadiya' Fatima tace a ranta, ko me suke yi a nasu makarantar oho, suma tasan sun fara WAEC ɗintunda nationwide ne.
Bayan ya kawo ta kofar gida ya sauke ta suka yi sallama ta wuce domin shiga gidan nasu, karo tayi da Isuhu wanda yake tsaye ransa a mugun haɗe, jan kunnen ta yayi ya kaita gida ita ko se ihu take saki yaqi kyaleta Seda ya kaita gaban me gari da yake zaune a gefen goggonta ya direta kamin ta tsagaita da yin ihun
Gaishe da Me Gari tayi ya amsa mata tare da yin tagumi sannan ta gaida Goggo, Isuhu kam tama ƙi kallon inda yake bare yayi tsammanin gaisuwa daga gareta
"Me kika yiwa babarki ta suma?"
Me gari ya jefa mata tambayar da ya sata a mamaki
"Me kuwa na mata Baba, daman nasan se ta min sharri ai, toh ni ba abinda na mata, kawai daga yin wanka da ruwa a bokiti a banɗaki ta suma se kuma daga dawowata a ɗora min sharri banji ba ban gani ba?"
Fatima ta ƙarashe tana me jin haushin sharrin da ake so a qaqaba mata
Tsintar Muryar goggo tayi tana fadin
"Toh yanzu kin janyo tayi yaji ai, ta kai ƙaran Me Gari wai yana musguna mata ita da ƴaƴanta ke kuma kina mata rashin kunya sannan kina cin zalin ƴaƴanta "
Ko da jin haka Fatima se ta ƙyalƙyale da dariya, 'wato da ta farfaɗo daga suman memakon ta musulunta shine har zata mata sharri koh? Toh wlh ita me bin ta gidan nasu ne taci ubanta', harda cewa wai tayi yaji, shi yajin yaci ƙafar uwarsa, dan Allah in taga dama karta sake dawowa gidan har gaban abada, bari ma zata je har gidan nasu ta koya mata hankali ita zata yi wa sharri?
Shidai isuhu yana zaune a gefe yana jin su bece komai ba
"Yanzu dai ki shirya kije ki bata haƙuri"
Ta tsinkayi muryar goggo
"Nidai wlh baza ni ba, kalen ta dauka an damu da ita ne, sannan ai yaji tayi, idan taji yunwa na neman halaka ta da kanta zata dawo ai"
Daga faɗin haka ta miqe tayi shigewan ta ciki, can ta fito da ɗaure ƙirji abinta, ko damuwa da me gari da Isuhu da suke zaune a gun bata yi ba tayi wucewar ta banɗaki.
Wannan kenan.
Haka dai rayuwa tayi ta cigaba har suka kammala WAEC nasu lokacin damuna na shirin tafiya, basu jima ba suka fara NECO, alaqar ta da Ilıya kuwa kullum se gaba gaba take, dan bama en gidansu ba hatta da en kauyen kusan kowa yasan da alaqar su, se ta zamto ita ce wacce yammatan kauyen ke kishi saboda dacen samun iliyan da tayi kasancewar sa ɗan birni kuma wayayye.
Babarta Tala kuwa da tayi yaji taje taga bata samun abun arziƙi a gidan nasu, daga tuwo se tuwo kuma ma ba'a ƙoshi, gashi alamu sun nuna koda kashe auren ta tayi daƙyar ne in zata samu mashinshini, tuni ta gudo ta dawo gidan me gari cike da sabin ƙudirirrika kala kala, sanda ta dawo kuwa Fatima babu kalan gori da baƙar maganar da bata mata ba, hatta da talaucin gidansu seda ta tuna mata.

FADREES 🖋️🖋️📝
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋🤍
Na Barr. Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
Ban yadda wani ko wata yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wallahi billahi baza mu wanye lapiya ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka