Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
a kiyaye.
Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.
Da fatan an fahimta.
Nagode.
________________
17. GRADUATED
Free Page
Yaune ranan da Fatima zasu gama NECOn su, se wani kala take ji musamman idan ta tuna cewar makaranta zata gama, Allah Sarki, Rayuwa kenan, yaushe ma ta shiga? Bata manta sanda Baba da kansa ya kawo ta makarantar taqi zama seda isuhu ya koya mata hankali kafin, yanzu gashi zata gama, ayyah
Yau dai dasu Saude zasu koma domin Iliya baya nan, yau satinsa ɗaya be leqo ƙauyen ba, ita kuma bata je gidansu dan taji yaya ake ciki ba.
Can zuwa karfe uku suka fito daga last papern su wato 'Civic Education', assembly aka musu principal yace musu sati biyu masu zuwa za'a musu graduation ceremony daga nan aka sallame su kowa ya kama hanyan tafiya gida, suna tafe suna hiran yanda bikin Grad ɗinsu da kuma na Hanne ze kasance, wanda a ƙiyasin su na Hannen ya kama saura wata ɗaya cif ayi.
Hanne ta kasa ɓoye farin cikin ta game da hakan, dan ta jima tana san ayi mata auren se yanzu Allah ya kawo karshen nacin nata, suna hanya suna ta maganganun su dai da kuma yanayin yanda graduation ɗinsu ze kasance. Barira ce tace;
"Nikam Fatima yaushe za'a saka ranar auren ku keda Iliya ne? Nifa na ƙagu naga an saka, ga saude da ta haɗu da nata daga baya ma maganan nata ake"
Daga nan fa maganan ita da iliya ya ɓarke a tsakanin su, kowa se cewa yake tayi dacen samun namiji irin sa.
Ita bama jinsu take ba, tunanin ta take yi daban, ita dai gaskiya tasan abu ɗaya, tasan tana san Iliya sede Allah ya gani ba aure take so tayi yanzu ba, bata san meya shiga kanta ba amma sam bata san aure yanzu, inda hali ma karatu take so ta cigaba da yi, so take me gari ya sama mata makarantar su isuhu ta jona dan gani take aure be dace da ita ba.
Suna ta hirarrakin su Hanne ke cewa
"Kema ai Barira yakamata ki tsaida ɗaya a muku auren bana son inxo aurenki da ƴaƴa"
Dariya suka sanya gaba-daya har ita Bariran, cigaba suka yi da tattaunawan su har suka iso Gabur, kowa ya kama hanyar gidan su
Koda Fatima ta wuce gida se taga babarta a gaban murhu wai girki zata yi, da yake harga Allah basa girki Inna Larai ce keyin duk wani abinda ya shafi girke girke a gidan, goggo dai bata ce mata uffan ba, itama fatima ko kallon inda Talan take bata yi ba, wucewa tayi ta canza kaya ta zauna taci abincin ta suke hira da goggo, gani tayi Tala ta ɗakko figaggen ƙatuwar kaza ta kira Baba Larai suka yanka daga haka ta zuba a tukunya ta masa haɗi hadda su manja da su daddawan ta, su dai basu nuna sunma san da zaman ta ba, suna a haka isuhu yayi sallama ya shigo musu da balangu me uban yawa daga haka ya fice, zama Fatima tayi ta sauƙe zanin ta ƙasa ta dinga apkawa cikin ta, tare da ma babarta Tala gwaliyo, gani tayi goggo ta ɗiba naman a wani kwano wai Fatima ta miqa wa Talan, ba'a san ranta ta karɓa ba, ta miqe taje kan Talan tace mata
"Karɓa ki haɗa muku, Kinga yau sallan ku kenan, zaku haɗa naman da kuka yi kwaɗayi aka sammuku da kuma kazar da kika sato a gonan Me Gari kike dafa muku, karɓa dan Allah ni sauri nake"
Ran Tala ne ya ɓaci ta saka kukan baƙin ciki, hango Isuhu Fatima tayi yana doso inda suke, ai da gudu ta zame ta koma bayan goggo riqe da kwanon tana zare ido
Goggo ne ta tsinkayi muryar Fatima tana cewa;
"Goggo wai tafi ƙarfin a bata saura, za dai ta tsammana kaza idan ta gama"
Goggo ko da jin haka bata ce komai ba ta cigaba da harkan gaban ta, isuhu kuma daman biyo ta yayi yaji me take faɗa wa Talan da har ta dade a tsaye a gun ga kwano a hannun ta sannan ga bakinta yana motsi sannan expression ɗin Tala kuma na ɓacin rai ne, koda yaga ta gudu yasan bata da gaskiya, daga haka ya fice a gidan.
Tala kuwa da ta sauke kaza ta zuba wa Me Gari a wani keɓantaccen kwano, daga nan ta zuba wa yaranta sannan ta ɗakko nata tazo gaban goggo tace mata 'bismillah' goggo cewa tayi 'Alhamdulillah' ta gode, memakon ta tashi ta koma kofar dakin ta se ta zauna a gun tana ci tana santi, hakan da tayi ya baiwa Fatima dariya dan seda ta dara, cike da jin haushin dariyan nata ta miqe tabar gun, can da dare Fatima tayi shirinta kamar kullum ta fice dandali, dan yanzu ba kullum suke tafiya da Isuhu ba, musamman ma da yanzu yake rubuta Exams nashi.
Koda taje kamar kullum babu Iliya babu dalilin sa, da sakakken jiki ta dawo gida da wuri, hango su Me Gari tayi a majalisar sa na dattawan sa ta wuce gunsu ta gaggaida su, mamaki kamar ya kashe su Baba Liman hadda goge idanunsa wai ko gizo suke masa, daga haka ta wuce cikin gida, can da Me Gari ya shigo taga babarta ta nufi dakin sa da kwano a hannun ta, ganin bata yadda da kwanon bane' tabi bayanta
Ɗora kunnen ta tayi a ɗakin tana sauraren me babartata take cewa
"Ga wannan nace yau zan maka girki da kaina, aika iro gidan gonan ka nayi ya ɗakko min kaza na sarrafa na baiwa kowa a gidan nan shine na ajiye maka naka, kayi sauri kaci in fice da kwanon"
Babarta ta ƙarashe cike da son taga yaci kazan, sallama Fatima tayi ta gaida Me Gari wanda shi kuma mamakin abinda ya kawo ta dakin nasa yake, ya lura in har Tala ta shigo itama seta shigo, bari ze mata magana in Tala ta fita.
"Baba meye ne a cikin kwanon nan, daga gani abin dadi ne tunda kaci tuwo ɗazu "
Share maganan ta yayi yace mata
"Meya paru naga kinzo a wannan lokacin?"
"Daman Baba zuwa nayi ince maka mun gama exams yau, za'a yaye mu nanda sati biyu ina so kazo, to tun ɗazu nake so in gaya maka naga kuma baka shigo da wuri ba"
Ta ƙarashe tana kallon Tala da take jefa mata harara ƙasa ƙasa
"Toh tunda dai an gama makarantar da se ki bari da safe kizo ki gaya min ai, yanzu tunda kin faɗa zaki iya tafiya"
"Nidai gaskiya baba bazan tafi ba seka min alkawarin zaka sa Baba Tala ta dafa min kaza gobe da safe inci, dan yau gaba-daya da kwadayin kaza na wuni kuma ina so inci girkin ta"
"Toh ki dauki wannan kwanon kici daman kuma faduwa ne tazo daidai da zama, kaza ce a ciki babarki ta kawo min"
Koda jin abinda me gari ya fada Tala ta dire akan fatima baza taci kazan ba
Ita kuma Fatima ta rantse se taci
"Ba a ni kika kawo ma ba?"
Me Gari ya jefa wa Tala tambaya
Tala ta gyaɗa kanta
"Toh meye idan taci".
"Kawai ni baza taci bane....."
Bata ma ƙarashe ba fatima ta buɗe kwanon ta fara ci, dan bata yadda da kazan ba, ji take kamar an barbaɗe shi da magani, ita sam bata yi niyyan ci ba amma ganin take taken Talan yasa take ci ɗin, idan ma magani ne a ciki toh wlh ita tafi ƙarfin su
Ihu Tala ta saka nan take ta faɗi ta ƙara suma, Fatima ko a jikin ta seda ta cinye tas ta juye kashin a cikin kwanon ta miqe tayi waje ko ganin me garin da ya rikice bata yi ba a ranta kuwa caa take 'aniyarki ta biki wallahi' sannan ƙurwar mu Ƙur nida Me Gari.
BAYAN SATI BIYU
Yaune ta kasance Juma'a ranar da aka yaye su daga makaranta, tun ɗazu take sanya idon ganin wani nata amma shiru kake ji, Babu Me Gari babu Isuhu, daman bata saka Goggonta a lissafi dan ba zuwa zata yi ba, Iliya kuma tayi matuqar mamakin rashin ganinsa a gun, bayan duk alƙawarin da ya mata? Amma shine ta ji shi shiru? Allah ya sa dai Lafiya Allah ya sa shirun nasa ya zama alkhairi, bata dai gaji da jiran tsammanin ba dan se leqa hanyan shigowa hall ɗin makarantar take, amma shiru, babu komai, ita ko baza taga Iliya ba, tana so taga Me Gari, dan Iliya har yanzu Exams yake ba lallai ya samu damar zuwa ba, sbd haka ta masa uzuri, tana wannan tunanin ne aka ƙira sunan ta, bata ma ji ba seda aka sake taɓa ta ta miqe taje ta karɓa kyautar ta ita ɗaya, wanda da da hali zata so ta karɓa ne tare da wani nata, Amma ba komai ta musu uzuri duk da a ranta rashin dadi ne sam.
Bayan koke koke da musayar lambar waya suka yi bankwana da ƴan makarantar su suka kama hanyar Gabur ita da su Hanne, ganin daga yau in sun koma zeyi wuya su dawo nangeren se suka yi deciding su zagaye garin, daman da shirin su suka zo domin siyan wasu abubuwan ado na bikin Hanne da za'a yi nan da sati biyu masu zuwa, suna cikin tafiya suka zo ta wurin gidan Me Nangere, a cike maqil suka ga kofar fadar, sunzo zasu wuce Fatima ta hango motar Me Gari na fitowa, hannu ta dinga dagawa alamar ya tsaya, yana hango ta kuwa ya tsaya yayi parking a gaban su, su Hanne ne suka gaida shi shida su Baba Liman, sa'annan itama ta gaida su
Me Gari ne yace da Fatima cike da kulawa
"Yanzu wai nake sauri sauri inje makarantar taku ko ban samu komai ba se mu wuce, dan ina so kiga nayi niyyar zuwa ɗin"
Tuni baƙin cikin rashin zuwan da Me Gari yayi ya yaye a ranta, har tayi zuciya da farko ashe dai yana da muhimmin abu ne a fadar shiyasa
Ganin haka se tace ba komai yanzu ma kasuwa zamu daga nan in mun gama komai sai mu wuce gida zamu, daga haka suka yi sallama da Me Gari ya ɗan bata wani abu sannan ya mata kashedin kar su jima, daga haka yaja motarsa ya wuce.
Kasuwan suka je suka siya duk abinda zasu siya suka wuce garin nasu.
Koda ta koma gida ta tarar yayanta ya ajiye mata kyauta na musamman, wanda hakan ya matuqar sanyaya mata rai taji duk wani ƙuncin da take ciki ya yaye.
Muje zuwa
Fadrees.
.🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋🤍
Na Fatima Idriss Bello
FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
Ban yadda wani ko wata yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wallahi billahi baza mu wanye lapiya ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.
Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.
Da fatan an fahimta.
Nagode.
18. SADIYA'S SECOND VISIT TO HER HOUSE
Free Page
Yau juma'a ne aka daura auren Hanne da mijinta Tanimu, zaune su Fatima suke suna jiran isowar ango da abokansa, amma har yanzu basu ƙaraso ba, tunowa da kashedin da Me Gari ya mata tayi, seda ya ƙara jaddada mata kar ta wuce Isha amma yanzu ƙarfe tara ake magana, sannan dalilin da yasa bata wani ɗaga hankali ba dan ganin layin can bayan su kaɗan aka kawo Hannen, can dai ta miqe tace musu ita zata wuce kawai, su saude ne suka ce mata dan Allah ta sake jira ita ko tace a'a kawai gobe sa haɗu, da sassarfa ta fara dosar kofar fitar, se kuwa suka ji sallamar ango da abokansa sa, koda ɗaga idon Fatima sai tayi ido hudu da Iliya, mamaki kamar ya kashe ta, magana ya fara mata tayi mishi banza ta fice, shi kuwa ya biyo ta, yana ta cewa 'ki tsaya mana Fatima, Dan Allah ki tsaya kiji, amma tayi biris dashi, daɗin ta ɗaya, taku be wuce saba'in tayi ba ta shige cikin gida ta hadu da murtuqaqqen fuskar yaya isuhu banza tayi dashi ta wuce abinta, ransa in yayi dubu ya ɓaci, bari zai koya mata hankali, ita ko koda taje kwanciya se tunanin Iliya ya sake fado mata a rai, ina ya tafi all these while? Sannan daman yana nan shine har ze iya zuwa bikin Hanne amma baze iya neman ta ba? Gaskiya ba ƙaramin mamaki ya bata ba a hakan ne baba yake so ya turo iyayen sa, tun ba'a je ko ina ba ta fara ganin ɗaukewar ƙafar sa?, tayi zurfi a tunanin ta zancen Me Garin ya sake faɗowa ranta, akan tayi sauri ta cire miji ya mata aure tunda ta gama sakandare
Sake hasaso abin tayi kamar yanzu ya faru
'''Da yamma ne lokacin Me Gari ya dawo daga Nangere a gajiye, bayan ya kimtsa yace Musa yaje ya kirawo masa fatima, babu sallama ya fara karanto mata saƙon Me Gari, dundu ta ma masa kuwa har guda uku, nan take ya saka azababben ihu yayi ɗakin mahaifiyar shi, wanda hakan yasa ta fito tana ta zage zage, kamar ba ita bane suka gama rikici sati uku baya har me gari ya musu tsakani
Sallama Fatima tayi kana tace
"Baba ina wuni, Musa yace min kana kira na"
"Ehh ni nace ya ƙiramin ke, magana ce nake so muyi"
Me Gari ya bata amsa
"Toh gani Baba"
Ta faɗa a ƙage cike da son jin abinda ze fada mata, Allah yasa yace mata zasu koma Potiskum ne da zama
"Munyi magana da Goggonki mun duba da yakamata kice ma wancen yaron ya turo ayi magana, duk da kwanan nan kwata kwata bana ganin sa, ko dai kin kore shi ne?"
Me Gari ya jefa mata tambayan
"Ni baba ban kore shi ba, kawai dai na dena ganin sa ne, sannan ni baba karatu nake so inci gaba"
Mamaki me gari yayi, yaushe ta fara san boko, amma se ya kafse yace
"Duk da haka ki turo sa aji ta bakin sa, watakila shima yace a saka ki a makarantar tunda shi ɗin ɗan birni ne, kinga koda bayan auren naku tunda a Potiskum yake ze barki ki cigaba ai"
Tunani fati ta tsaya yi duk da bata gamsu ba, tana tsaka da tunanin ne yace mata taje tayi nazari dai zasu sake magana, daga haka tabar sashen'''
Shine kuma be zo ba se yau bayan duk wadannan lokutan? Yau ɗinma ba gunta ba gun auren abokinsa? Yayi kyau, tana cikin wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe bayan tayi Sallah ta gaida Goggo seta koma baccin ta ba ita bane ta tashi se zuwa ƙarfe goma, seda ta bari zuwa sha ɗaya tayi wanka ta shirya cikin kayanta masu ƙara mata kyau ta tafi gidan Hanne, koda taje se ta iske Barira ce kawai mutane duk basu zo ba, gani tayi Hannen se sussunne kai take yi duk sanda ta haɗa ido da ɗayan su sai hakan ya bata mamaki ƙwarai, dan seda ta jefa mata tambaya.
"Lapiya Hanne naga kina ta sussunne kai? Kunya ta kike ji ko me?"
Ganin Hannen bata ce komai ba seta share ta ta cigaba da harkokin gaban ta, can zuwa azahar lokacin saude itama tazo se kuma ɗaiɗaikun mutane taji Musa ya rangaɗa sallama.
Daga bakin kofa ya tsaya ya gaida ƙawayen ta kana yace
"Yaya fati wai kizo kinyi baƙuwa inji goggo",
Daga haka ya fice
Koda jin haka se Fatima tayi mamaki sosai, wace baƙuwa ce wannan ana zaune ƙalau, miqewa dai qtayi suka yi sallama tace inshallah zata zo anjima daga haka ta fice.
Tafiya take a hankali sannan da sakewar jiki kuma cikin sanyi, rana ne ya haske kyakkyawar fuskar ta wanda ya baiwa kwayar idon ta damar sake yin brownish gold, yanayin fatarta kuwa se ya zama so smooth kamar na models, duk wanda ya ganta inma mace inma namiji toh dole ne ya ƙyasa.
Tana doso kofar gidansu ta hango wata rantsattsiyar mota, kallon motan ta cigaba dayi dan tasan sabuwar motar me gari dai be kai wannan kyau ba, hango iliya tayi a kofar gidan nasu ata ɗan gefe, dalilin da yasa bata ganshi ba da farko saboda motar ta kareshi ne, yana mata magana ta share sa ta wuce ciki a ranta tana cewa 'toh kodai motan Iliya ne'? Se kuma ta ƙaryata hakan
A kan verandar su ta hango Sadiya a zaune, ta ƙara kyau da wayewa da girma, goge idanunta ta yi wai dan taga ko gizo suke mata, se taga dai Sadiyar ce, ƙarasawa tayi gunta tana me zare ido, se yanzu ma ta lura da goggo a zaune ata gefen Sadiyar kamar ma hira suke
Zaunawa tayi suka gaisa
"Nasan mamakin gani na kike koh?, Toh ai tun ɗazu da nazo aka ce kin tafi auren Hanne, har nace a raka ni nima goggo tace bari Musa ya fara ƙiran ki tukunna in yaso semu tafi tare"
Sadiyar ta ƙarashe tana kallon fatima
A gadarance Fatiman tace
"Ehh haka ne, bari kici abinci se mu tafi kawai"
Sadiya' ce tace
"Kar ki damu ai tun ɗazu goggo ta zuba min Naci"
Mamaki ne ya kama Fatima sai bata ce komai ba ta miqe kawai suka fito suka fara tafiya, a bakin kofa suka hadu da Isuhu, gaida sa Sadiya' tayi ya amsa yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasa a ransa kuma caa yake ita kuma wacece wannan
A hanya suke hira, Sadiya tace taga saqon ta daga Maimuna shiyasa ma tace zata zo idan sun gama term ɗin, daga nan Fatima kuwa ta bata kaf labarin zuwan ta Potiskum tun daga farko har ƙarshe, ita kuma Sadiya ta bata labarin makarantar su hadda ce mata wai ai Maimunan sune masu girman kai wai su ya'yan manya
Dariya suka yi inda Sadiya tace mata ana nema musu admission a Nile University na Abuja, ita kuma Fatiman tace mata Me Gari yace ta faɗa wa saurayin ta ya turo iyayen sa dan a saka musu rana ita kuma gaskiya karatu take so ta cigaba, dariya sosai Sadiya ta sa wanda hakan ya ɗan batawa Fatima rai
Hakuri ta bata tace wannan babbar magana ce amma ta roki Allah ya zaba mata abinda yafi alheri suna a haka suka ga tsayuwar iliyan a gaban su, daman sun zo daidai shiga kofar gidan Hanne ne
Har ya bude baki ze fara magana tayi shigewan ta gidan ta kyale sa a tsaye, biyo bayanta sadiya tayi suka shige se dariya take ƙyalƙyatawa, tarar da su barira suka yi a zaune a falon Hanne ana hira, suna ganin Sadiya kuwa suka miqe cikin jin dadi tare da bata gurin zama, zama tayi suna ta hiran yaushe gamo, daga karshe da zata tafi ta baiwa Hanne kyautar dubu goma su barira kuma dubu bibbiyu, godiya suka mata sosai kana fatima ta raka ta dan yamma yayi sosai, numbern wayan ta ta bata tace dan Allah ta kira ta koda numbern Isuhu ne, daga haka drivern su yaja ta ta tafi.
Koda dare tayi isuhu yace wa Fatima tazo suje dandali, da farko tace baza ta ba daga baya ta canza shawara akan zata je kar Isuhu yace dan shine ma bata je ɗin ba
Gaishe da su Me Gari suka yi kana suka wuce, suna isa ya wuce wajen samari ƴan uwansa ya barta a tsaye a gun.

Iliya da bata san da wanzuwar sa agun bane ya fara mata magana
"Dan Allah kiyi hakuri Fatime kiji abinda zan gaya Miki, wallahi Nijer na raka ƙanin babana kuma Kinga ke baki da waya shiyasa baki ji daga gare ni ba sannan auren Hanne kuma wallahi zuwa nayi na taradda yau ake auren Tanimun shiyasa kika ganni a gun ba wai da sanina bane, wallahi dan in ganki Nazo garin nan, sannan dan na baki kyautar da na tanada Miki, dan Allah kimin afuwa gimbiya Fatime ta, zan iya Miki tsallen kwaɗo in dai zaki yafe min",
Jin cewar yana lafiya sannan uzurin sa me kama hankali ne yasa ta yafe masa a take, leda ya miqa mata tayi wuff ta amshe shi jin yace kyautar ta ce a ciki,
"Waya ne a ciki na siyo Miki dan mu dinga magana, kıyı murmushi kinji Fatime?"
Yaƙe tayi tana juya ledan a hannun ta tare da tunanika kala kala
Iliya ne ya fada mata maganar da ya girgiza ta
"Nayi magana da baffanni na akan zasu zo dan ayi maganar auren mu"
Kallon sa ta tsaya yi cike da mamaki bama ita kadai ba, harda isuhun da bata san ma da wanzuwar sa agun ba.
Fadrees
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
❥♡👸ME GARI FATIMA.!!👸♡❥
(The Female Village Head) 🦋 🦋🤍

Na Fatima Idriss Bello🤍
FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
19. MARRIAGE PROPOSAL????
Isuhu ne ya dalla Wa Iliya harara kana yace;
"Wa yace maka aure zata yi?
Karma ka kuskura, ke kuma dauki wayar sa yanzu ki miqa masa"
Zancen ba aure zata yi ba gaskiya ne, dan ita ta kwallafa rai a san yin karatu, amma batun ta bada waya baza ta iya wannan ba, saboda haka se taqi motsawa, hasali ma sake ƙanƙame wayar tata tayi a hannu
"Ba magana nake miki ba? Ki bashi wayar sa yanzu mu wuce"
Isuhu ya daka mata tsawa
Idanun ta ne suka ciko da ƙwalla dan haqiqa tana san wayar, ce masa tayi
"Nidai gaskiya Yaya kayi haƙuri, ranan graduation nawa kace ka siyo min kyauta, da dare da nazo kaban ai hanani kayi, kuma har yau baka ban ba"
Fatima ta ƙarashe tana hararar ƙasa, dan idan yaga idanun nata ze iya gwabje mata su
Ganin tana ɓata masa lokaci se ya wafce wayan da ƙarfi daga hannun nata ya jefa wa Iliya, tare da cewa
"Ba seka siya mata waya ba, an gode, already tana da wayan ta a gida, bata ne ban yi ba"
Yana ƙarashewa yaja hannun ta suka yi gida, Fatima sai waiwayawa baya take amma yaqi sakin ta, koda suka iso majalisar su Me Gari sai Fatima taje gun da gudu ta zube a gaban su tana saka wani uban kuka, Me Gari ji yayi kamar ya sakko daga kujeran sa ya mangare ta, iliya kam kamar ya fasa ihu saboda baƙin ciki
Baba Liman ne yace tayi shiru ta faɗa abinda aka mata
Buɗe baki tayi ta kama magana kamar haka;
"Wai Baba Liman dan Iliya ya siya min waya yaya isuhu ya ƙwace ya mayar masa, hadda cewa wai shima ai ya siya min kuma kamar ƙarya yake"
Dafa goshi me gari yayi jin kalar ƙaran da Fatiman ta kawo Iliya kuma kamar ya kare ta, wai shine yake ƙaryan.
"Waye kuma Iliya?"
Baba Liman ya tambaya
Wutan kanta ne ya ɗauke na ƙalilan ɗin lokaci se ta kasa bada amsa Isuhu ma shiru yayi, me gari kam ba'a magana
Ganin haka sai Baba Liman ɗin yaɗan ɗago zancen se kawai yace
"Kai isuhu dagaske kake akwai wayar da ka siya mata"?
Da 'Ehh' isuhu ya amsa
Baba Lamba ne yace isuhu yaje ya dakko wayan, ba shiri ya miqe yaje ya ɗakko ya kawo
Baba Liman ne ya bata tare da mata kashedin kar ta sake a sake ganin tayi lefi a garin ko tsokana, idan kuma tayi ze kwace wayan ya baiwa isuhun
Be ma gama magana ba Fatima tace 'zata kiyaye' daga

Chapter 8 of 9