Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
be dawo ba, tunda ya dauki abu ya fice be sake dawowa ba, da yana nan baze yadda da zancen da za'a zayyano musu yanzu ba.
Koda ta fito se drivern ya samu Goggonta da baba Tala ya kwantar musu da hankali ya musu magana me ratsa zuciya kana suka haqura
Mamakin hankalin sa Fatima tayi dan ce musu yayi mota ne ya ɗan bige wata mata shine suka tafi asibiti, shiyasa akaga ta dade, matar ma ba abinda ya same ta shine yace bari ya dawo da ita gida kar aga shiru hankalin iyayen ta ya tashi.
Daga nan goggo ta dinga masa godiya tana shi masa albarka, shigewa suka yi ciki, fatiman ta roqe goggo da kar ta sanar da Isuhu ko me gari abinda ya faru, dakyar goggon ta amince da hakan, can kuma Goggo tace ga abincin ta, karba tayi ta kai dakinta ta ajiye ta wuce banɗaki bayan ta gama ganin kanta a mirror tayi alola tazo tayi azahar ta koma toilet din tana cigaba da kallon mirrorn har akayi la'asar, har a lokacin kuma bata bar mamakin yanayin gidan su Maimuna ba, wato kudi yayi a rayuwa, gaskiya itama zata so ace tayi rayuwar daula, sede ko a hakan ma ta gode Allah.
Isuhu ba shine ya dawo ba se ana mangariba, me gari kuma se bayan Isha ya shigo, Fatima ganin ba wanda yayi maganar fitan ta dazu se ta sake kwantar da hankalin ta.
Me Gari kuwa Bayan ya kimtsa yace musu su kama shirye shiryen tafiya Gabur gobe idan Allah ya yadda
Koda fatima taji wannan mummunan labarin suma ne bata yi ba, dan kuka kam Seda tayi shi dan a ganin ta me gari ya karya alkawari ne, shida yace baza su koma ba shine ze canza magana, yanke shawarar taje ta same sa yanzu yanzu a dakin sa tayi daga haka ta fice ta wuce dakin nasa ta kwaɗa sallama, share ta yayi ya cigaba da abinda yake, ganin haka Fatima ta fara knocking kofar da ɗan karfi se ji yayi tace
"Baba nikam zan shigo"
Daga haka ta bude kofar ta shige ciki, ganin ta shigo ɗin se me gari yayi danasanin rufe kofar da beyi ba da sede ta gama knocking ta koma.
Karasa shigewa tayi kusa dashi
Ganin me Garin tayi da takaddu Kamar files haka kusan biyar a gaban sa hannun sa riqe da biro
Ko kallon inda take me gari beyi ba ya cigaba da cike ciken da yake
"Baba ina wuni"
Ya tsinkayi muryar ta
"Lapiya Mamana"
Ya amsa mata kansa tsaye yana cigaba da abinda yake ɗin
"Baba kaine fa kace ka min alkawarin zama a garin nan shine kuma zaka ce wai gobe ayi shirin komawa kauye?"
Ta ƙarashe tana kumbura baki hawayen baƙin ciki na kwaranya daga idanun ta
"Nidai baba sede a barni ni daya anan amma nidai bazan koma kauye ba"
Ta ƙarashe tana me jan hancin ta
Ganin me gari be kula ta ba ta cigaba da surutun, daga nan ta fara sambatun abinda be dace ba se ji tayi an dauke ta da mari kuwa
Ko bata juya ba tasan waye, kuka tasa me uban ƙara ta fice a dakin ta wuce nata
A cikin ɗakin me gari kuwa, cewa Isuhu yayi
"Da baka taɓa ta ba Isuhu"
"Toh Baba ya za'a ayi na barta, kaji abinda take ta fada fa, Allah yarinyar nan se na canza mata kama"
Me gari ne ya girgiza kansa yace 'Allah ya kyauta'
Washegari ƙin tashi da wuri tayi a ganin ta in sun gaji da jiranta sayi tafiyar su su shafa mata lapiya, se can zuwa sha biyu ta fito daga dakin ranta a dagule kamar wasa se taga ana ta haɗa kaya she me gari cewa yayi zeje meeting sai da yamma ze dawo su wuce.
Dakin Goggonta ta wuce taga har ta gama hada kayanta, gaida ta tayi ta amsa ta zauna a gefen ta
"Kin gama haɗa kayan naki halan"?
Goggo ta jefa mata tambayar
"A'a nifa goggo bazan koma kauye ba"
Baki goggo ta sake kana taci gaba da abinda take, isuhu ne yayi sallama ya shigo
Fatima kuwa tayi miqewarta ta fice a dakin ko kallon inda yake bata yi ba
Can Bayan la'asar me gari ya iso yace su fito a shiga Mota a wuce, a lokacin Fatima tace bata san zance ba, akayi akayi taqi, me gari takaici kamar ya kashe shi, isuhun da yake hanawa ya taba ta shi yasa ya kinkimota aka dura ta a mota se ihu take, goggo ranta ne ya ɓaci ta mata wani shegen dundu, shi kuma Isuhu cewa yayi in bata yi shiru ba a booth din motar zesa ta ya rufe, taji matuqar haushin zancen isuhun amma kuma se ta share, tada mota isuhu yayi bayan ya kwaso mata tsummokaran kayan ta ya watsa mata kafin ya kulle gidan suka yi gaba, sune basu dena jin ihun ta ba seda suka iso Nangere, daga nan ta hana yaran zaman lafiya se musƙulin su Musa da Zulai take, daga karshe goggo ne tayi maganin ta ta riqe mata hannun ta gamm yanda baza ta iya motsa shi ba, da haka suka samu salama har suka iso Gabur.
Sunzo daidai kofar gidan me gari suka hango su Inna larai sunzo musu Barka da dawowa, ficewa Fatima tayi tana saƙe saƙe a ranta, tazo wucewa wani yaro yazo wucewa ya ɗan bangaje ta aikuwa seda ta masa shegen dundu tayi wucewar ta cikin gidan nasu, tana jin sanda ya saki wata razananniyar kukan azaba amma ko a jikin ta, ta wuce dakin goggo tayi kwanciyar ta, basu jima ba da dawowan kuwa aka kirawo mangariba, ko motsawa bata yi ba daman bata yi azahar da la'asar ba ballantana ayi tsammanin mangariba
Da ikon Allah ba wanda ya kula ta, tana jin isuhu ya siyo wa su Musa ƙayau ƙayau bayan ya dawo daga sallah, har tayi kamar taje ta karɓe taci taga baza ta iya ba.
Can bayan Isha Isuhu yace da goggo shikam ya fita, hakan sam se Fatima ta kasa yadda da fitan, wato ita tana cikin kunci shikam har fita zeyi ko? Ai ko baze yiwu ba, ficewa itama tayi tabi bayan sa ko kallon goggo bata yi ba dan haushinta take ji, koda ta fita ta iske su me gari ana tadi shida su Liman da su ladan, tsayawa tayi tana tunanin me zata yi ta tarwatsa musu taron, ganin isuhu ze bace mata kawai se ta bishi, filin dandali taga ya nufa, binsa tayi ta hango sa da yarinyar ranan, ya saka ta a gaba se haƙuri yake bata, ita kuma da alamu alaqar tasu ce bata buqata, tana daga kanta kuwa taga Fatima a gaban ta ta riqe kunkimin ta, ganin haka yarinya ta kwasa da gudu har Fatima ta gyara tsayuwar kayanta dan ta bita se Isuhu ya riqe ta, kokuwa ta fara yi dashi shiko ganin zata ja mishi attention se ya fara janta suka yi hanyar gida, ba yanda ta iya haka suka isa gidan, shigewa dakin Goggonta tayi ko ba komai ta hana shi yin abinda yayi niyyan yi yau, da haka taje tayi alola tayi sallolin ta daga nan ko abincin dare bata nema ba tayi kwanciyar ta.
Washegari ya kama talata, kamar kullum seda rana ta fito taje ta shige bayi da niyyan tayi wanka se tayi alola tayi asuba, se kuma taga baƙon watan ta, hamdala tayi tayi wanka kawai taje ta kimtsa cikin uniform nata dan zuwa makaranta tunda jiya bata jeba, koda ta shirya tayi ficewar ta ko sallama bata ma Goggo ba, goggo kam taɓe bakinta tayi, hanyar dakin me gari tayi tayi knocking taji shiru, tura kofar tayi ta shiga ciki.
FADREES 🖋️.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘Romantic Love Story.
Na Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
13. THE FIGHT
Free Page
'Wayam' ta gani da ta shiga ɗin
Ƙarewa dakin sa kallo tayi, daga gadon sa sai wardrobe da kuma wani teburi da tulin takaddu da files akai, sai kuma kayan sa da ta gani a rataye a jikin ƙusosin da aka bubbuga a jikin ginin ɗakin, Allah Sarki gaskiya abinda me gari yake yi sam sam beyi ba, kamata yayi ya gyara musu wannan gidan tunda anan suke da zama kuma anan suke da iko, amma yaje ya siya gida a Potiskum bayan yasan ba zuwa suke ba, wato shi ɗaya ze mora kenan idan yaje.
Sake ƙarewa ɗakin kallo tayi idon ta ya faɗa bisa kan gadon sa, gashi nan alamar an hau amma sam ba'a hargitse ba, idon ta ta mayar kan teburin nasa ta hango files ɗin da ta gani shekaran jiya da daddare a Potiskum, ƙarasawa gun tayi ta fara buɗe su da ɗaɗɗaya, gani tayi kowani file gwamnatine take so ya sanya hannu domin a gina asibiti, makaranta da kuma tituna, gani tayi yasa hannu a duka, sake bude wani file tayi taga an rubuta 'Next of Kin' buɗewa tayi da niyyan ta karanta domin taga waye next of Kin' din nasa, shin Yaya Isuhu ne ko ita ko kuma Musa? ji tayi ya buga mata tsawa a hankali
"Ungo naki yaushe kika fara shigowa kiyi bincike'
Zunguro bakinta gaba tayi tace
"Ayyah dai Baba, zuwa fa nayi in gaida ka naga ba kowa a dakin, shine fa nace barin jira ka"
"Toh yanzu kin ganni se ki bani waje"
"Ayyah dai Baba banci komai ba fa, gashi makaranta xan tafi"
"Toh kije ki jira ɗumame mana"?
Ya fada cike da gajiyawa
"Nidai Baba bana san ɗumame, jiya haka ina ji ina gani na kwana da yunwa saboda tuwon be min ba, yanzu in na tafi banci komai ba ai ze iya janyo min cuta ƙarshenta kudi za'a ce za'a kashe dan a min magani, toh Gara Aban kuɗin nasan dai baze kai na maganin da za'a kashe ba
Ta ƙarashe cike da nuna tsantsan tausayi
"Banni da kuɗi, ki fice min a daki kafin in ƙira yayanki yazo ya zane min ke"
Cike da ɓacin rai ta fice a dakin, ta koma dakin Goggonta, ƙasan kayanta ta buɗe ta ciro wata sabuwar Naira ɗari, ficewa tayi a ɗakin ta hango Baba da trayn abinci a hannunta ta doshi dakin Me Gari, bin bayanta tayi tana gani ta shige cikin ɗakin, laɓewa tayi tana me jin abinda suke tattaunawa, ji tayi babar tata tana maidawa me gari magana gatsal gatsal ba ladabi, wai se ya bata kudi zata yi wanene wanenen ta, Fatima ji tayi ranta ya ɓaci, wannan wane irin renin hankali ne, ko me gari beyi jika da ita ba ze haife ta, bare kuma yayi jika da itan, shine zata na masa magana yadda taga dama dan taga yana da saukin kai? Kutsa kai tayi cikin dakin ta hango babarta ta riqe kunkumin ta tana jijjiga ashe ladabin karya take wa me gari, ƙarasa shigewa cikin ɗakin tayi ta wafce kudin hannun babarta ta wanda already Me Gari ya riga da ya bata wai wasu take jira
Budan bakin babarta tala se cewa tayi
"Ke Fatima ki fita a hanya ta, ba dake nake ba, kar kiga kina min abubuwa ina kyale ki wallahi ki kama kanki"
Fatima koda jin haka se ta dira akan Tala tana kururuwa se ihu take tana cewa
"Dan ubanki baki isa ki zagi ubana in ƙyale ki ba, wallahi wallahi ko kallo kika sake masa sena tsiyaye idanun ki munafika mummuna kawai, banda ma baba ya tsufa me zeyi dake, kekam ai sede a aurawa Iro(me kawo musu ice), ke iron ma yafi karfin ki"
Iro kuwa akayi Sa'a ya kawo ice ya ajiye yazo ficewa se yace bari yaje ya sanar da me gari ya kawo, se akayi rashin sa'a yaji abinda Fatima take faɗa daga cikin ɗakin Me Garin, duk da kalaman ta sun nuna rashin ɗa'a tunda matar ubanta ce sannan kuma tana masa kallon ƙasƙanci duk be dame sa ba, sede haɗa sa da babarta Talan da tayi ya matuqar ɓata masa rai, ai wlh ko da yake a haka mummuna mara kuɗi yafi karfin ya auri Tala, dame ma zeji fisabilillah da wannan katon hancin nata ko wannan magujejen bakinta? Kai shidai Allah ya isan sa, har ya juya ze fice se yaji kururuwa na sake ƙaruwa gashi ba daman ya shiga dakin me gari kai tsaye, se kawai ya wuce bangaren goggo dan ya kira isuhu, ji yayi goggo tana gaya wa isuhu akan Fatima bata ci abinci ba ta fita, da hanzarin sa ya tsugunna ya gaida su ya sanar dasu abinda ake ciki a dakin me gari, da gudunsu kuwa suka yi dakin me gari
A cikin ɗakin Me Gari kuwa Fatima ne zaune akan ruwan cikin Tala, me gari ya kasa tabuka komai, shi tsoron taɓa ta yake wataqila aljanune akan ta, ya hau ta karya sa daman ba wani jikin arziƙi ba gare sa ba, yana saƙe saƙen nan ne yaga shigowar Isuhu da goggo, wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauke.
Ɗago ta isuhu yayi ya warfar gefe, goggo ce ta kama ɗaga Tala wai ta taimaka mata ta miqe, ita kuwa ta warfar da hannun Goggon tana huci take fadin
"Dama girmamakin da nake ya isheni goggo, daga yau wallahi sena hana kowa zaman lafiya a gidan nan, zaku san dani kuke zancen"
Fatima tsalle ta daka zata koma kanta isuhu ya kama ta gam, ranta ne ya hasala
"Baba dan Allah ka sake matar nan, daman ba abinda take tsinana mana, ruwan wanka kawai take haɗa maka bayan haka bata aikin fari balle baƙi, tou wa ya san me take barbaɗawa a cikin ruwan wan....."
Kafin ta karasa isuhu ya bige bakin ta
"Baki da hankali Fatima, matar uban naki zaki kama da fada"
"Toh yaya rashin kunya ta ma baba, Ni se in kyale ta? Çap ban cika ƴar halak ba kenan, munafukar mata kawai, Ni da nazo nace Baba yaban kudi ai hanani yayi ita ta gode wa Allah ya bata ma wai har rainawa take, shegiya kawai"
Tabbas da bata furta cewar Tala rashin kunya tama me gari ba, da wallahi se ya sauya mata kama, amma kuma faɗin hakan da tayi se yaji ta burge sa dan abinda yaqi jini kamar yaji an wulakanta masa iyaye, koda ba me gari bane ya haife shi, shi ɗin Uba ne a gare sa dan ya tabbata koda ubansa yana raye iyakar abinda ze masa kenan, watakila ma baze kai nashin ba, Goggo kuwa mamakin furucin fatima take, me gari ne ya samu yace musu ba komai su kwantar da hankalin su, saɓani ne kawai se kuma aka samu akasi Fatiman taji amma ba komai bane
Daga nan suka fice a dakin, direct kofar waje Fatima tayi tana me sake damqe dubu ɗayan hannun ta, da babarta dame gari sunyi two zero, hanyar Nangere ta ɗauka, tana tafiya tana tunanin yadda zata kashi kudin ta tare da ciro nairan ta ɗari ta haɗa da dubun
Can bayan wasu ƴan mintinan ta iso makarantar su, direct ajinsu ta wuce, malami har ya fita, ba'a jima ba aka fita break, ajinsu Hanne ta tafi ta iske su suna zaune dasu saude suna hira,
"Hiran me kuke haka?"
Fatima ta faɗa tana haɗe rai
"Fatima yaushe kuka dawo, ya Potiskum yake, dan Allah ki bamu labari"
Ta tsinkayi muryar Barira na taho wa inda suke
"Baku amsa min tambaya na ba"
Fatima ta sake fada wa su Hanne tana share maganar Bariran
"Waifa wannan yarinyar Jummala ƴar makwafciyar su Hanne ne aka mata aure, shekaran jiya aka kaita Ƙauyen Chalimno shine muke so muje gidan nata da an tashi daga makaranta"
Koda jin abinda Saude tace se Fatima ta karɓe da faɗin
"Toh ba se mu tafi tare ba? In yaso se ina baku labarin Potiskum a hanya?"
Nan da nan kuwa suka ce Ehh haka za'a yi, daga nan kowa ya koma azuzuwan su aka cigaba da classes.
Bayan an tashi daga makaranta suka dunguma suka kama hanyan Chalimno, suna cikin tafiya ne Fatima ta saki baki se basu labarin Potiskum take harda ƙarin ta, wai ai gidansu hawan beni ne har uku, sannan kullum da kaji suke kari da shi suke bacci, wai har turewa take dan ya ginshe ta, su Barira kuwa se cewa suke ta cigaba da labarin nata dan suna enjoying sosai sede part ɗin beni da kajin kamar basu yadda ba, bayan azahar suka isa garin basu sha wani wahala ba suka samu gidan Jummala
A falon ta suka yada zango akan kujerun ta, Fatima a ranta se sha'awar gidan take duk da cewar gidan ba wani na azo a gani bane, ciki da falo ne se banɗaki da kitchen
Ayyah, itafa yanzu bata san wa zata aura ba koh? Toh yana ina ma? Me yake? Ɗan Gabur ne ko ɗan Potiskum ne ko ɗan Nangere ne? Duk dai bata da amsa, gidanta me kyau ne irin nasu Maimuna ko a'a?, ILIYA ne ya fado a ranta, sharewa tayi abinta, ƙila yana can Damaturun har yanzu yana ganawa abinsa.
Zama suka yi suka yi ta hira basu ne suka bar gidan ba se ana la'asar, sannan basu bar gidan haka nan ba seda suka tabbatar da sun kassara mijin Jummala dan kankat suka masa.
Wannan kenan.
Muje zuwa.
FADREES 🖋️.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA.!!👸
(The Female Village Head) 🦋 🦋😘Romantic Love Story.
Na Fatima Idriss Bello
A.k.a FADREES.
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
14. ILIYA IS BACK
Free Page
A hanyan su na komawa Gabur suka dinga santin gidan Jummala, Hanne Allah Allah take su kammala wannan Exams ɗin nasu a mata aure abinta dan ita yanayin masu aure burge ta yake sosai, Fatima ne ta baiwa Barira jakar ta wai ta riqe mata, karba tayi babu musu suka cigaba da tafiya har suka iso, a bakin shiga garin su kowa ya kama hanyan sa, karban jakanta tayi tare da yin hanyar ta dan kowa hanyar gidan su daban, memakon ta koma gida se ta wuce zuwa kasuwar garin su, dubun ta ɗaya da nairan ta dari ne ya fada mata a rai, murmushi ta saki kamin ta wuce zuwa wajen me balangu da tsire, ko wannan su ce masa tayi ya yanka mata na dari uku uku, zama tayi akan wani kujera tana jiran a gama haɗo mata ta ciro kudi ta bada, kusan a tare suka gama haɗa mata ta amsa, bude jakan ta da babu wasu takardun kirki a ciki tayi wai ta ciro kudi, sai kawai ta hango Naira ɗari sede babu dubu daya babu dalilin sa, dariya ta saka ta sake bincika jakan da kyau amma bata ga dubu ɗaya ba, zazzage jakan tayi nanma taga fa Lallai lallai babu kudi babu dalilin sa, ɗaga kanta tayi taga masu nama suna jiran ta basu kuɗi, ita ba abin ta basu naman su ba kuma suce ta raina musu ne, miqewa dai tayi tare da yin shahada ta gaya musu bata ga kudin ba amma gashi su ajje mata zata je ta nemo wani kudin, amsa suka yi ta miqe tayi tafiyar ta zuwa mashigan garin nasu dan yau ta ɗau alwashin se taci nama ko ana ha maza ha mata, toh amma kuma faduwar kuɗin nan da mamaki yake, tana saƙe saƙe ta iso gun ta dudduba still bata gani ba, tunani ta fara akan ai ta baiwa Barira jakan ta ta riqe mata, idan har hasashen ta ya tabbata haka ɗin ne zata ci uwar Barira kuwa, toh ai reni ne ma har ta faki idon ta ta daukar mata kudi.
Har ta dauki hanyar gidan su Bariran ta canza shawara tayi hanyan gidan su Hanne
Sallama tayi ta shige kai tsaye hango Hanne tayi tana ta sharbar tuwo da miyar kuka
"Ke Hanne tashi muje ki raka ni gidan su Barira inci mata Uba"
Miqewa Hanne tayi da rawar jiki ta dauki hijabi suka fice, mamarta tana so ta sata aiki amma ba dama dan ita tsoron fitinar ƴar Me Garin nan take, basu wuce direct gidan su Barira ba seda suka fara zuwa gidansu Saude suka ɗakko ta, duk sun canza uniform nasu banda Fatima da bala'i yake jan ta dan ko gida bata je ba daman.
Babu sallama suka faɗa gidan su Barira suka yafito ta suka fara kirɓan ta, se ihu Barira take ta rasa bakin magana
Kuma se aka rasa me karban ta a masu jin ihun nata, idan kaga yanda Fatima ta zage tana dukan ta anan ne zaka san lallai bata san zafin aihuwa ba, dan mazgarta suke kamar wanda Allah ne ya aiko su, seda suka mata lilis kana suka ƙyale ta
Fatima ne tazo gaban ta ta tsaya tace
"Miƙo min kan in ƙara Miki"
Da rawar jiki duk idon ta ya kumbura ta miqe tana ɗingishi ta dakko mata ɗari takwas ta bata"
"Ina sauran? Ko dai har yanzu baki daku bane?"
Fatima ta sake jefa mata tambaya
"Wallahi na kashe kiyi hakuri"
Bariran ta faɗa tana hawaye
"Wato ma kin rena Ni, har in baki ajiyar jaka kimin satan kuɗi, tohhh ki tabbatar da kinzo gun gaɗa da Naira ɗari biyu ta, sannan wannan ya zama na farko da karshe da zaki sake daukar wa wani abun sa, daga haka suka fice a ƙofar fita suka hadu da mamanta da daman bata cikin gidan se yanzu take shigowa
Wucewa gun me tsire Fatima tayi su Hanne suka koma gidajen su
Bada kudin tayi aka bata dari biyu ta zauna a gun ta cinye, har ta tashi zata tafi taji baza ta iya tafiya ba tare da ta kaiwa goggo ba, ita matsalar ta daya da Goggon ba wai ka kai mata ba tace se ta ba su Musa amma zata ce wallahi karta ba su Musa in ta basu kuma suka karba wallahi se ta kusan kashe su da duka
Daga haka ta koma gun nasu tace a bata balangu na dari uku, miƙa kuɗin tayi ta karɓa balangu ta fara tafiya
Jin alamun kamar ana bin bayanta tayi, ɗan juyawa tayi se kawai taga Iliya
Kallon sa tayi na ɗan dakika kaɗan kafin taci gaba da tafiyar ta, shan gabanta yayi yace
"Fatime ki tsaya mana"
"In tsaya in maka miye, Ni ka matsa a gaba na sauri nake"
Ta basa amsa a takaice
"Nidai ki tsaya mana kiji abinda zance"
Tsayawa tayi tana jefa masa harara da idanunta masu kama da ruwan gwal
Hakan da tayi kuwa se ta jefa Iliya a cikin wani hali ya zuba mata idanun sa ko kyaftawa baya yi.
"Kaga dan Allah kayi sauri tun ɗazu ya kamata in koma gida gashi maraice ya iske Ni sosai"
Ledar hannunsa da bata lura dashi ba ya miqa mata ita kuwa ta sa hannu ta karɓa
"Fatime dan Allah kizo dandali anjima na taho Miki da labarai akan Damaturu, wannan kuma tsarabar kine"
Ya fada yana nuna mata ledar
Amsa tayi babu ko godiya tayi wucewan ta dama ta riga da ta iso, barin Iliya tayi yana ta kallon ta cike da bege, tazo shiga gida taci karo da yayanta ransa a haɗe
"Se yanzu kika ga daman dawowa, sannan meye haɗin ki da wancan yaron ne wai?"
"Dan Allah yaya ka ƙyale Ni in huta kafin nan dan gabaki ɗaya jiki na a gajiya"
Koda gama fadin haka se ta shige gida shi kuma Isuhun na biye da ita, goggo ta tarar akan verandar su tana fige zogale, ajiye ledojin tayi ta wuce banɗaki se can ta fito, alola tayi a tsakar gidan tana ganin babarta Tala tana aiken Musa wai ya siyo mata fanta ta share ta, zuwa tayi tayi sallah sannan ta janyo ledar balangu ta baiwa goggo tace
"Goggo ga wannan nace barin siyo Miki"
Amsa goggo tayi tana sa mata albarka kana tace
"Daman ina so in Miki

Chapter 6 of 9