ranta ake cirewa, Gashi dai a fuska wallahi kaman ba zata yi ba dan innocent face ne da ita, wlh yanda take saka ihu, da ba gidan su bane cewa za'a yi yanka ta ake da ranta.
Mu haɗe a na gaba.
FADREES 🖋️ 🖋️ 📝.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
3.
Free Page
Mutanen dasu ke makwabtaka dasu suna jin ihun ta suka yi banza da ita, kowa inda zaka duba ransa daɗi ne fal a cike dan Fatima ta addabi kowa da komai dake cikin Garin Gabur, Kai hatta tsinke Fatima ba barinsa take ba, a rana za'a iya kawo ƙaran ta sau ashirin, babu yadda Me Gari beyi ba amma ba yadda ya iya, ƴa ce Ubangiji ya albarkace sa da ita sede kamar ɗan aljani haka take, a fuska baza kayi tsammanin zata iya wani abu wai shi rashin ji ba, amma hmmm
Sannan Goggo daman ita ba me masifa bace, sanyi ne da ita sosai gashi itama ya ɗan hadu mata da ɗan tsufa, shiyasa Fatiman take abinda taga dama.
Fatima takai awa goma tana kuka, muryar ta kuwa yadda take ɗaga sa yadda kasan naman jikin ta ake cirewa, kowa shigewa ciki yayi yayi banza da ita, daman dakin Isuhu a gefen dakin su ita da goggo yake, yana gama dukanta ya miqe ya kira ƙannenta ya basu ƙayau ƙayau ɗin, kana ya shige dakin sa, suna ci kuwa tana jefa musu kallo.
Me Gari kuwa miƙewa yayi dakyar ya nufi sashen sa cike da zullumi na halin Fatima, zama yayi yana tunanin rayuwar duniyar ma gabaki ɗayan ta, be taɓa tsammanin ze sami ɗa a rayuwarsa ba, matan sa su biyu duk basa haihuwa har an dauka matsalan sane tunda har su biyu ne, se daga baya da ya hadu da mamarta ya aure ta su kuma suka ce baza su zauna da jikar su a matsayin kishiya ba suka watse, lokacin har ta haifi Fatima ta rasu, da badan kanwarsa sa'ade ba, da besan ya zeyi ba, duk da yaso ace Fatima namiji ce, da a yanzu ma zeyi murabus in yaso tana gama secondary ya daura ta akan kujerar sa, amma kuma ma yanzu ai yana da ɗa namijin sede kuma yaro ne sosai, in ya mutu yanzu yasan sarautar fita zata yi daga gidan sa, Allah dai ya sa koda sarautar ta fita in ɗansa ya girma a maida masa da sarautar, da wannan tunanin bacci ya sure shi daman shi abincin sa waje ake kai masa yaci da mutanen sa, damuwar sa ɗaya ce daman, ta Fatima.
Sanyin asuba ne ya tada goggo ta miqe ta fice dan tayi alola, kwatsam tayi tuntube da wani abu a ƙasa a bakin ƙyauren dakin nata, wai ta duba da kyau ba se taga Fatima ba? Share ta tayi taje tayi alolan ta, hakika jiya Fatima ta bata tausayi sede in ba'a mata hakan ba baza ta canza ba, bayan ta gama alolan ta miqe hannun ta dauke da butan da tayi alolan, tana zuwa setin kofan ta kwara wa Fatima ruwan, a matuqar firgice tare da tsala ihu ta miqe, dan Fatima kan dakyar in tasan salati ma, abinda yasa goggo ta mata haka, Fatima gigin bacci ne da ita na bala'i, idan ba haka aka mata baza ta taba tashi ba.
"Ki wuce kije kıyı alola kiyi sallah"
Fatima ta tsinkayi muryar goggo na mata magana
Bata ce komai ba ta miqe tayi waje, da tunanika kala kala a ranta, ita kadai tasan irin abinda zata musu ta huce, tukunna ma ba wanda ya bata haushi sama da goggo, tana jin wannan azzalimin dan nata Isuhu na dukan ta ko ta karɓe ta ko? Toh wallahi yau ko makaranta baza taje ba, a gida zata wuni, seta tabbata ta hana kowa zaman lapiya wallahi.
Da haka ta miqe bayan ta gama alolan ta shige dakin Goggon dan tayi salla, sallaya ta gani a shimfide, ko uffan bata ce ba ta fara yi, tana Sallah tana kumbura fuska da ƴan harare hararen gefe da gefe, tana idarwa ta fice tsakar gidan nasu, hakan da tayi ya ba Goggo mamaki dan Fatima bata taɓa tashi wai tayi sallah bata koma ba, amma se ta share ta cigaba da lazimin ta, Fatima kuwa ficewa tayi a gidan ta shige gonan Me Gari da yake ta ɗan bayan gidan nasu ta kwaso ƙaiƙayi ta dawo ta wuce dakin goggo ta samu ƙasan akwatin ta ta saka, kamin ta koma bacci.
Can gari yayi haske goggo ta matso daidai kanta ta kama ɗan ƙiran sunan ta akan ta tashi tayi shirin makaranta, jin tayi shiru yasa ta mata shegen dundu, tashi Fatima tayi tana haɗe rai, ko gaishe da Goggon taqi yi
"Ki tashi ki shirya ki tafi kamin kıyı latti"
Ta tsinkayi muryar Goggon akan ta.
Yi tayi kamar ba da ita ake ba, itafa tunda tace baza taje ba bata ga wanda ya isa ya sata taje ba.
Tun goggo nayi da karamar murya tazo ta fara yi da babba, ana haka isuhu ya shigo, shima ko ta gaida shi, beyi mamaki ba duba da abinda ya auku jiya, tambayan ba'asi yayi a gun goggo ta fayyace masa komai, lallaba ta suka fara yi ana cikin haka suka ji muryar Me Gari na tambayan ko lafiya, matar shi kuma na biye a bayan shi
Gaya masa komai goggo tayi, daga nan fa aka fara batu, ita Goggo ba wai damuwa tayi da bokon ba, sanin mahimmancin sa da tayi agun me gari ne yasa take so Fatiman tayi tunda gashi yayanta isuhu shima yana karatun bokon dan yana matakin NCE ne acan garin Potiskum, shi kuma Me Gari dalilin da yasa yake so tayi makaranta shine yana so yaga ana karatun boko, yasha bin ƴan kauyen akan su saka yaran su sunƙi, da aka ga ya saka isuhu ne ma aka fara kaiwa, daman akwai firamare a Gabur din Sakandire ne babu se a Nangere, sannan yana da alwashin ya kaita itama tayi ilimi ta samu wayewar zaman duniya dan haka se ya fara saka baki akan ta shirya ta tafi makarantar, amma yarinyar nan tayi kunnen uwar shegu da su, me gari harda laluba aljihu ya ciro Naira ɗari da hamsin sabi dau ƙal ya bata, wuff tayi ta wafce kudin amma taqi motsi, ganin haka me gari ransa ya fara ɓaci se kawai ya fice a dakin, ita kuma babarta se dariya take ƙasa ƙasa, ganin haka sai ran Fatima ya ɓaci sosai, tace zata yi maganin ta
Goggo ganin iskancin Fatima yayi yawa yasa ta fice itama ta barta ita da Isuhu, lallashin ta ya fara yi dakyar da sidin goshi da alkawarin ze kaita Potiskum ta haqura akan ta sakko amma dai baza ta makarantar ba, ganin haka ya fice shima ransa na ɗan suya.
Nairan ta dari da hamsin ta dakko ta fito daga dakin, hango qanin ta Musa tayi ta kira sa akan yazo ya siyo mata ƙayau ƙayau, babarta ce ta fito a kewaye daga gani haɗa wa Me Gari ruwan wanka tayi, tana ƙarasowa gun ta tambaye Musa ya akayi ya gaya mata, tana jin haka tace mata baze je ba, ita kuma se Fatiman bata ce uffan ba ta fice kawai, tana tafiya tana rangwada abinta ta hango su Hanne suna hanyar tafiya makaranta, ko kafin ta musu magana taga sun karaso inda take, Saude ce take ce mata
"Wai Ni kam Fatima yaushe zaki fara fitowa gaɗa ne, jiya baki ga abinda ya faru ba, se fada ake akan Hanne gashi baki zo ba ya wuce ki, daga karshe Seda abu ya kusa zuwa kofar gidan ku ma fa"
Koda jin haka Fatima ta tuna da jiya dukan tsiya aka mata amma baze yiwu ai ta gaya musu ba, amma kuma koma me ze faru yau itama se taje gadan nan, itama so take ayi fada akan ta, can tayi zurfi a tunani barira tace su wuce kar suyi latti, har sun juya zasu tafi tace musu su dakata
"Idan kun tashi daga makaranta kuyi wanka ku canza kaya se kuzo gidan mu akwai abinda nake so ku min"
Da 'Toh' suka amsa kana suka juya suka yi tafiyar su.
Daga nan wucewa tayi gun me kosai, a hanya ta karyi itacen maina tana tafe tana ɗan yiwa yara ko akuyoyi bulala, musamman wanda taga be kwanta mata a rai ba, koda taje layin kosan se ta samu har an gama saura ƙayau ƙayau da be wuce na Naira Hamsin ba, miqa kudi tayi tace a bata wani yaro yace ai nashi ne ya riga ta, Fatima ko kallon sa bata yi ba ta wafce ledan a hannun shi ta jefa ma matar hamsin tayi gaba abinta, yaro ganin haka yabi bayan ta wai se tabashi tunda ya riga ta
"Da alamu baka san wacece niba ko"?
Ya tsinkayi muryar Fatima
"Koma waye ke ki bani abu na"
Yaron ya fada mata haka
Ganin haka Fatima ta daga bulalan hannunta ta masa dukan tsiya tayi shigewan ta gida, tana shiga ta wuce dakin goggo ta bude kasan kayan ta ta ciro kaikaiyin da ta tsinko dazu ta wuce gun drum din ruwan su ta juye a ciki, ta juya da niyan komawa daki ta hango goggo ta fito a wanka, taji haushi da taga goggo tayi wanka amma ai babarta da ƙannenta basu yi ba, ganin irin kallon da Goggon ta mata kamar na me tuhuma yasa ta wuce daki tayi kwanciyar ta.
Can zuwa sha biyu na rana taji an fara ihu ana soshe soshe, ta leqa ba se taga babarta tana sosa jiki ba? Dariya kamar ya kashe ta, goggo kuma tsayawa kallon ta tayi, daga bisani ta fice dan ganin yanayin babar Fatiman hankalin ta a tashe ta karasa ta kama ta, su Musa kuwa suna tsaye a gun ba kaya suna jiran a musu wanka sannan Kuma suna kallon ikon Allah, karshen ta se asibitin nangere aka yi da ita, kamar hadin baki suna fita se ga Musa da wani jibgegen mutum wai shi yayanshi sunzo dukan Fatima
Koda ma'aikacin gidan nasu yazo ya samu Fatima da batun wani yazo da yayansa suna kofa, se tasha damara ta fita, tana zuwa tayi kicibus da wani wargajejen halitta, ai da ganin haka da gudu ta ranta a na kare zata koma Cikin gida, cikin rashin sa'a ya damqo hannun ta.
Zan dan dakata daga haka
Mu haɗe a shafi na gaba
FADREES 🖋️.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
4.
Free Page
Fisge fisge ta fara yi amma ina, karfi ba daya ba, da dai taga ze illata ta se ta gantsara masa wani mahaukacin cizo, besan sanda ya sakar mata hannu ba aikuwa tayi ciki a guje taje dakin goggonta tana maida numfashi, mutumin kuwa me suna Isiya da yaga haka se ya tafi, amma yasha alwashin duk sanda ya hadu da Fatima se ya sauya mata kamanni, daman yaji irin jita jitar da ake yi akan ta, akan ta dami kowa a garin hatta kadangare babu a gidan su saboda tsabar muguntan ta.
Fatima kuma da taga zaman ya ishe ta, se tayi gun dakin babar ta, ta tadda iya larai me musu aiki ta ma su Musa da Zulai wanka, sannan ta sa an zubar da ruwan drum din, dan lokacin da babar take soshe soshe tace daga ta diba ruwa a drum tayi wanka hakan ya faru.
Kama Musa tayi ta masa ɗan banzan duka akan wai ya mata rashin kunya dazu haka ya gama kukan sa ya share hawaye dan babu me rama masa.
Su Goggo kuwa koda suka je asibiti emergency akayi da baba Tala, dan ta riga da ta galabaita, gashi duk ta guggurje jikin ta da farce, dakyar aka samu aka shawo kan abun, se kusan la'asar suka kama hanyar Gabur, suna zuwa suka ji shewar Fatima da ƙawayen ta, koda baba Tala ta saka kafa a cikin gidan se suka kwashe mata da dariya, hakan se ya ɓata wa baba Tala rai bata san sanda ta fara kukan bakin ciki ba, gashi me gari baya nan balle ta aika a gaya masa, ana haka Isuhu yayi sallama ya shigo, duk da gajiyar makarantar da ya kwaso, yana ganin ƙawayen Fatima ya fatattake su ya kora su, kafin su tafi seda suka sake jaddada mata kan zuwa gun Dandali, sannan dariyan da suka ma baba Tala ita ta saka su, shiyasa sukayi dan mugun tsoron ta suke.
Goggo kuwa kama haɓa tayi cike da zullumi, Isuhu yana gaida ta ma bata ji sa ba, can kuma se ta tsinci bakin ta da furta, "Isuhu yau Fatima ta kusan aika Tala lahira, dukkannin mu ma"
Maida hankalinsa kan goggo yayi yana sauraren ta,
"Ƙaiƙayi fa ta zuba a ruwa Tala tayi wanka da ruwan muma Allah ne ya rufa mana asiri da har damu za'a yi ta susan"
Yadda ta karashe maganar da yin tagumi ya matukar basa dariya amma ya kafse, lalle Fatiman nan inaga ba ita kadai bace duk yanda akayi tana da almatsutsai.
Juyawa yayi ya kalla fuskan Fatima tayi wani kalan abun tausayi, fuskan ta kamar yar malam saboda salihanci, shidai gaskiya yakan tambayi kansa akan halayyar yarinyar nan, amma ba komai ze san nayi
Yana nan yana zurfin tunanin sa yaji mutum a gefen sa
Muryar ta ya tsinkaya tana ce masa
"Yayana ina wuni"?
Kasa amsa wa yayi yana mamakin ta
Zuwa gefen sa tayi ta zauna tana basa labarai, wai dan duk ya siyo mata ƙayau ƙayau yau, bece komai ba ya miqe ya fice dan yaji har an shiga sallah, Fatima kam ko motsawa bata yi ba, toh ita bata ma yi niyyar yin sallan ba ƙarshen ta ma bacci ta kwanta tayi, goggo tayi ta tashinta taqi hatta ruwa Seda ta watsa mata amma taqi tashi, qarshen ta kyale ta tayi, gashi abun haushin ma ko wanka bata yi ba.
Ba ita ta tashi ba se can zuwa isha, kuma kamar an tsikare ta tashi a firgice, da hanzarin ta ta shige banɗaki ta chanchaɗa wanka, ta dakko kayan sallan ta ta saka, tayi wuff zata fice Isuhun da bata san da zuwan sa ba ya riqe mata hannu, fisgewa ta fara yi yaqi sakin ta, tsabar baqin ciki har cizo se da ta apka masa amma ɗan tahalikin nan yaqi sakin ta, daga karshe kururuwa ta kama yi, Seda goggo ta saka baki ya cika ta, da sharadin se tayi sallah kapın ta fita, kapın ma Goggo ta rufe bakin ta taje tayo alola, sallan da tayi sunan ta 'ƴar mubi ba yawa se lada', da wurwuri ta idar tayi hanyar kofa Isuhu ya tare mata hanya (dan Allah jama'a a dinga kiyaye lokacin sallah, kar a samu novel a dinga jinkiri da lokaci), da taga ze kawo mata cikas a fita tace ya fada mata meye yake so ne wai
Goggo tana ganin su ta riqe baki ta kasa cewa komi, daga karshe dariya ma suka bata
Las las, a tare suka tafi gun gaɗan bayan jan kunnen da isuhu ya mata, tare da ja mata babban warning, ita kuwa ta dinga gyaɗa kanta kamar kadangaruwa, sede, abinda be sani ba shine, duk gargadin da yake mata, shiga suke ta kunnen dama su fice a na hagu dan da zaka sa mata wuqa a wuya ma baza ta iya maimaita maka abinda yace ba.
A bakin kofa suka hadu da majalisar me Gari, ɓata rai Fatima tayi dan tasan majalisar ze iya kawo mata cikas, isuhu ne ya zungura qeyan ta har gaban me gari, koda suka isa Fatima har qasa ta tsugunna ta gaida babanta da kuma muƙarraban sa bayan taga isuhu ya sake gaida su, daga nan wucewa suka yi filin gaɗan, dama tayi tsammanin Me Gari ze kawo mata cikas wurin zuwanta amma se taga akasin hakan.
Dandalin a cike yake da mutane, ga gun akwai hasken lantarki sannan hasken ya haɗe da na wata, hakan yasa yanayin yayi wani kalan burgewa, sannan ga yanayin da ake yi na damuna na shirin tahowa, wanda hakan ya baiwa Fatima mamaki sosai, wato munafurtan ta ake ba'a taba ce mata taje ba se yau, wucewa tayi gun su Barira, take da niyan fada ta manta daga karshe suka dinga wasanni kala kala, wanda akasarin su Fatiman ce kan gaba, duk da yawancin su bata iya ba amma seda akayi da ita, tana ganin ƴammata se hira suke da samarin su, ita kam bata da wanda ya taba cewa yana santa ma, Allah Sarki😥, alabasshi wani ya taba cewa yana sonta a Nangere ta wurge shi da dutse daga nan be kara cewa yana sonta ta ba, ko ganin ta yayi daga nesa guduwa yake, da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya sa'annin nata suka fara zamewa dan zuwa hira, hango Hanne tayi ita da wani suna hira, duk se yammatan suka watse ganin Hanne ta tafi gun saurayin ta aka barta ita daya, ba abinda yafi ɓata mata rai kamar ganin yayanta Isuhu ya tare wata suna hira, yarinyar se rufe fuskan ta take wai ita kunyar shi take, wato da farko har hana ta zuwa yake yanzu jibi har ya samu budurwa suna hira, ai wallahi baze yiwu ba, bari taje ta koya musu hankali dukkan su kawai, baze yiwu ace an barta ita kadai ba, ta juya da niyyan ta fara zuwa gun nasa se taga an tare gaban ta, daga kafar shi ta fara kalla, so take taga wani mahaukacin ne ya tare mata hanya, daga kanta tayi cike da bacın rai sai ta sauke idan nata akan sa, sunan sa Isiya, shine yayan yaron da ta daka ɗazu, dogo ne me jiki ba wani sosai ba, fuskar sa ta kalla taga babu annuri a ciki, nan take hantar cikinta ta kaɗa
"Kafin kije ki kwaso magana NI zan kakkarya ki anan"
Ido ta zaro kana ta fara ƙyaƙƙyafta su, ita gashi bata iya bada hakuri ba
Can kuma se tace
"Me na maka da zaka karya Ni, wallahi ka shiga hankalin ka, kaga can"
ta faɗa tana nuna gun Isuhu,
"Toh yaya nane, wallahi kace zaka min abu se insa ya maka dukan tsiya"
Ta karashe tare da murkuda masa baki
Sharewa yayi yaɗan murmusa, dan yasan a dake dai isuhu be isa ya duke shi ba
"Ga guri acan kizo muje mu zauna"
Ya fada mata yana nuna mata wani wuri
Kamar baza taje ba se kuma ta bishi suka je suka zauna, shi kansa mamaki yayi, shi niyyan koya mata hankali yayi amma dai bari ya gani
"Meye sunan ki ma"?
Isiya ya tambaye ta
"Sunana Fatima, yar Me Garin nan, ƙanwar Isuhu"
Ta karashe cike da alfahari da jan kunne, wato in besan ita ƴar me gari bace to yanzu ai ya sani
Dariya yayi yace mata
"Kina zuwa makaranta kuwa"
Caraf ta karɓe zancen tace
"Makaranta kai, kaf garin nan babu me ilimi na wlh"
Ta karashe tana masa kallon banza
Ji yayi kamar ya mangare ta se ya share yace
"Kina wane aji toh"?
"Wannan ai tambayar renin hankali kake min, da farko hadda tambaya na ko ina zuwa makaranta, na maka kama da jahila ne? Sannan da kake cewa ina aji nawa, toh ina SS3, mun kusa fara WAEC idan ma bakin ciki kake min Wallahi sede ka mutu"
Ta karashe zancen tare da jefa masa muguwar harara
Murmushi iliya ya saki kamin ya mata tambayan da ya sata yin shirun dole
"Wani ya taɓa ce Miki kina da kyau kuwa?"
Shiru Fatima tayi na wucin gadi kamin ta samu bakin ta, ita kanta tasan ita kyakkyawa ce sosai ma kuwa, dan arean su ba kasafai ake samun kyawawa ba, zata iya cewa kaf garin su ma bata ga me kyanta ba, sede, ita bata taɓa saka hakan aka ba, hasali ma, kyawun nata be wani dame ta ba, toh me kyan ze mata ma? Ai dai ba'a cin kyau, sannan duk kyan mutum ai dai be isa ya haɗiye kyan ba, ƙannenta ta tuna, su Musa da Zulai, sam sam basa kama, sannan sam basu da annurin kyau a jikin su, kodanma hakan yana da nasaba da rashin kyan da babarta Tala take dashi
Hannun sa yasa a setin idon ta jin ta fada duniyar tunani
"Baki bani amsa ba?" Isiya Ya sake tambayar ta, kamin ma tace wani abu isuhu ya karaso inda suke yace ta tashi su wuce gida
Ce masa tayi baza ta tafi ba se ya siya mata ƙayau ƙayau, wucewa gun me suyan kosai suka yi suka kyale Isiya a zaune a gun, Seda suka jima kafin suka siya, daman Fatima tasha alwashin baza ta ci tuwon da aka yi a gidan su ba sannan daman ya mata alkawarin ƙayau ƙayau ɗin.
Sune basu bar gun ba se kusan sha ɗaya, suna zuwa daman su ake kira, nan take aka rufe kofar gidan daga nan wucewa Fatima tayi dakin goggonta ta haye kan katifarta saboda gajiya, tana jin goggo tana sakin minshari, ai kuwa se bacci yace besan zance ba, tinani ta fara yi, tunanin abinda ya auku tsakanin ta da ısıya da kuma tambayar da ya mata, shi da yakamata ya mata dukan tsiya shine ze tsaya yana mata wadannan tambayoyin? To me yake nufi ne.
Ku biyo domin kuji me iliya yake nufi game da Fatima.
Fadrees.
_________________
Littafin nan na kudi ne akan Naira 300 kacal.
Zaki saka kuɗin ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan kina so tun yanzu zaki iya biya, in kuma se an gama free pages ne ma dukka daidai ne.
Idan anyi completing kuma it'll be 500.
FADREES 🖋️🖋️📝.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
5.
Free Page
Yau Juma'a an tashi da damuna, gari yayi wani kalan duhu cike da sanyi, zan iya cewa wani kalan ni'ima ne ke cike da garin wanda idan kaine a ciki zaka ji dama ka dawwama a cikin yanayin.
Kwance take akan katifar ta wanda ɓari daya an cire, daya ɓarin an yanke, ɗaya ɓarin kuma gashi nan ga kamar shi, tun asuba goggo take tashin ta tayi sallah taqi, har safiya tayi sosai dan bazan ce rana ta fito ba duba da yadda ake iska da hadiri, ƙarshen zance har Inna larai tazo ta aiki amma Fatima taqi tashi daga bacci, ganin haka yasa Goggo ɗibo ruwan randa ta kwara mata, amma yarinyar nan taqi tashi, da Goggon taga taqi tashi se ta aiki Musa da yayi sauri ya tafi gonan me Gari ya tsinko ƙaiƙayi a watsa mata, dan ta lura kamar iskanci ne ke damun ta
Abinda goggo bata sani ba shine Fatima idan ta biyu, tun lokacin da take tashin ta na uku, sallan ne take gandan tashi tayi, sannan dadi take ji in taga ran goggo ya ɓaci, sbd itama so take ta rama abinda aka mata shekaran jiya, sede kuma jin za'a yi amfani da ƙaiƙayi, ai nan take ta tashi, yau ɗinnan dama bata yi niyyan zuwa makaranta ba koda ba'ayi hadiri ba ma, tunda wai inji su Hanne ba wanda ya tambaye ta jiya da bata je ba duk da ba ajinsu ɗaya ba, hatta Sadiya bata tambaye ta ba, wani sashen jikin ta na san zuwa wani sashen kuma baya so, sashen da baya so ɗin sbd tsanar makarantar ne, sashen da yake so kuwa so take taje ta samu Sadiya taji ba'asin dalilin da yasa bata tambaye ta ba, da haka ta shige banɗaki tayi wanka, tana fitowa ta hango Musa da ƙaiƙayi a hannun sa, mamaki ta tsaya yi, wato munafurtan ta zeyi, toh zata yi maganin sa, shiko yana hango ta ya ruga a guje
Bata