🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
1.
Shin ka taba jin inda mace tayi jagorantar al'umma a wannan zamanin??
Al'ummar ma ta hanyar sarauta?
Sarautar ma ta ƙauye?
Sannan a arewacin Najeriya?
Macen kuma yarinya yar shekara 19 zuwa 20?
Sannan yarinyar ta kasance marar ji?
Shin waye zai yadda ta jagorance shi?
Shin ita yardar su take nema ma?
Idan tayi sarautar zata fuskance kalubale?
Wane kalan kalubale kenan?
Shin waye ze aure ta ma?
Ku biyo domin kuji labarin Fatima, Ć´ar me Garin Gabur da ta zama me Gari da kanta, domin labari ne me cike da soyayya, nishadi, abin dariya da kuma sadaukarwa.
Ku biyo ni ku sake bani dama domin na fayyace muku daga biri har wutsiya akan littafin nan me suna 'ME GARI FATIMA'
Na muku alkawari da yardar Allah wannan ba kalan wadancan bane, kodanma da gwaji ai akan gane na kwarai
Ni ce taku har kullum
FADREES 🖋️.
Fatima Idriss Bello.
Ban yadda wani ko wata yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba, ko ya haÉ—a min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wallahi billahi baza mu wanye lapiya ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.
Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.
Da fatan an fahimta.
Nagode.
_________________
1
Free Page
ME GARI FATIMA
(The Female Village Head).
Na
Fatima Idriss Bello
FADREES 🖋️ 🖋️.
YOBE STATE NIGERIA.
Jihar Yobe na É—aya daga cikin manyan jihohi dake nan arewacin Najeriya ta gabashin ta.
Babbar jiha ce dake dauke da ni’imomi da kuma albarkatun ƙasa kala kala wadanda suka haɗa dasu gyada, wake, albasa da dai sauransu.
Jihar Yobe Na dauke da ƙananan hukumomi guda goma sha bakwai waɗanda suka haɗa da; Bade, Bursari, Damaturu, Fika, Fune, Gaidam, Gujba, Gulani, Jakusko, Karasuwa, Machina, Nangere, Nguru, Potiskum, Tarmuwa, Yunusari da kuma Yusufari.
Garin Damaturu itace Capital É—in Yobe State.
GABUR, NANGERE.
Maraice ne lis se kuma yanayi da ake ciki kamar damina na shirin tahowa, garin yayi wani kalan daɗi duk inda ka sa ƙafar ka wani kalan ni'ima ne ke dauke da gun, tafe take tana tsalle tsalle har taɗan zo kusa da wani yaro dake dauke da wani roba akan shi, tun daga nesa da yaron ya hango ta ya juya da gudu ita kuwa ta bishi suka cigaba da rabza gudun, seda ta cimmasa ta zubar da hatsin dake cikin roban kan nasa tare da zungurin shi tayi gaba taji hankalin ta ya kwanta, tana jin sanda ya saka wani razanannen kuka amma ko ta kula shi tayi wucewar ta cikin garin nasu na Gabur
Tana cikin tafiyar ta taga wani rafkeken sanda a ƙasa ta tsugunna ta dauka, duk sanda tazo wuce ko akuya ko kaza se ta ɗaga sandan ta maka musu, in takaice muku kafin ta isa gida seda ta ma akuya uku, tinkiya ɗaya da kuma kaji biyu targaɗe, tana zuwa gidan nasu taga su baban ta Wato Me gari ana Sallah anbi jam'i, yi tayi kamar taje ta ta zaburar dasu, sai kuma ta tsaya tana tunanin shin taje ta zaburar dasu ɗinne ko ta shige gida kawai, bata damu da cewar hadda baban ta a cikin jam'in ba fa, ta tsaya tana wannan tunanin ne ta hango yayanta yana fitowa da alamu jam’in ze jona, ɓata rai tayi ta shige ciki tare da jefar da sandan hannun nata, cikin sa'a kuwa sandan ya daki zangorin Ladan ai kuwa beyi wata wata ba ya saki wata razananniyar ƙara na azaba, shigewa tayi ba tare da taga reaction din ladan ba, dan tasan in bata jeba Yayanta baze bata ƙayau ƙayau yau ba, amma duk da haka seda ta saki murmushin farin ciki, jin irin bahaguwar ƙaran da ladan ɗin ya saki.
Shigewa cikin gidan nasu tayi wanda gida ne na bulo sede gidan ba tsari sam, wai a hakan gidan nasu yafi ko wane gida kyau a garin kasancewar shine gidan Me Garin.
Turakar goggonta ta wuce tare da yin alola tayi sallan ta Ć´ar mubi ba yawa se lada abinta.(Ni kaina in aka ce in karbi sallan wallahi billahi bazan karba ba).
Tana gamawa tayi jifa da sallayan ta tafi dakin babarta, shigar ta keda wuya ƙannenta ta gani suna shan fura da nono a cikin kwano, babarta kuwa sallan mangariba take, itakam yadda take sallan har gara na yarinyar ma, ƙarasawa gun kannen nata tayi tare da wafce kwanon furan ta kafa shi a baki ta shanye duka kana tayi waje, tana jin sanda babar tata ta idar tana sheqa mata ashar, dawowa dakin goggonta tayi kamar ba abinda ta aikata, ganin goggonta tayi a zaune ita da yayanta Isuhu, yana baiwa goggon labari akan wani ya rusa wa ladan zangori har an tafi dashi cikin garin nangere asibi, zama tayi a kusa dashi ta gaishe shi, shiko ganin haka babu wani ɓata lokaci ya bata ƙayau ƙayau ɗin dan gudun fitinar ta, ita kuma goggonta mamakin gaisuwar take, kodanma meye na mamaki tunda abu take nema, amma nan duniya in ka cire Me Gari shima ɗin se tana neman abu, toh bata gaishe da kowa se in abu take nema.
Ana nan zaune a haka tana jin liman yayi ƙiran sallah, yayan ta isuhu ya miqe yayi alola yayi waje, ita ko tayi kunnen uwar shegu, seda goggo ta idar ne ta dauki muciya kafin aguje taje tayo alola tayi sallan ta kafi liman lada, ta shafa abinta, ta miqe taje taci tuwon dawa da miyar karkashin da taga goggo ta ajiye wanda tasan daman nata ne, shigewa tayi turakar Goggon nata ta kwanta, tana jin sanda babanta me gari yayi sallama ya shigo gida aka rufe kofa daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.
Iska ce ke kadawa cike da burgewa da kuma daddaɗan sauti, mafarki tayi me daɗi wai gata a garin nangere a cikin gidan Mai Nangere taje gun ƙawarta an zubo mata abinciccika masu bala'in daɗi, su naman rago ne, su kafar shanu ne, da su lemukan kwalabe, daukar fanta tayi ta dinga sha, Seda tasha kwalba uku kamin ta ƙoshi, can kuma taji fitsari sai ta ganta a cikin wani hadaddiyar banɗaki, hawa kan wani abu tayi ta fara sheqa fitsari me matukar dadi, can kuma sai taji goggo tana kwala mata ƙira, a harzuqe ta bude idon ta ta tashi tsaye, cin karo tayi ta fitsarin kwancen da tayi, zaro light brown eyes nata masu kama da ruwan gwal tayi, nan da nan ta dakko wani jug da ta gani ata gefe da ruwa a ciki ta kwara akan ƴar katifar tata dai dai da shigowar goggon kenan
“Ke Fatima baza ki tashi ki shirya ki tafi makaranta ba, kinsan daga nan zuwa Nangere da ƙafa da nisa shine baza kije ki kama hanya ba tukunna ma fitsarin kwance kika yi”?
Goggon nata ta riqe haɓa cike da dimbin mamaki
Zaro idanun ta masu kama da ruwan gwal tayi tace
“A'a Goggo yanzu ne fa na dauki ruwa ina sha shine ya zube” ta karashe tana kumbura baki tare da matukar haɗe rai.
Fita waje tayi hasken rana na haske fuskan ta, se anan ne na ƙare mata kallo, lahaula fi sha’atillah, fara ce tasss, me ɗauke da dogon hanci, fararen idanun ta kuwa kamar ruwan madara tsabar haske, lips ɗinta kuwa full kissable lips ɗinnan ne masu mugun kyau, in takaice muku a yanda naga labarin Fatima ƴar me Garin Gabur daga jiya zuwa yau ban ɗauka kyakkyawa bace, na dauka irin fitinannun yaran nan ne marasa kyan gani kwata kwata, sede bama a kyan kaɗai ta tsaya ba, diri ne da ita na Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, sune wadanda ake alaqanta su da cewar suna dauke da Coca-Cola shape, Gashi dai a shekaru baza ta wuce sha takwas ba, se an tsawwala ne za'a ce mata sha tara.
BanÉ—aki ta shige taga ruwa me É—umi ai bata yi wata wata ba tayi wanka da ruwan tayi alola kamin tayi waje, Seda ta koma dakin Goggonta ne taji babarta tana ta masifa ashe wai a Me Gari ta haÉ—a wa ruwan wankan Fatiman ta dauka tayi amfani dashi.
Tana gama shiryawa tasa uniform tayi asubanta tayi waje taje É—akin Me Gari dan ta gaishe shi ta samu na kashewa, tana zuwa taga ya shiga wanka, dawowa tayi ta dauki brush nata itama da MacLean taje tayi ta dawo, domin Fatima fa dauka take ita É—in É—iyar Sarkin duniya ce, duk wani abun da take a makaranta take gani a gun yaran Me Nangere, dan abota take bilhaqqi da Ć´ar me Nangeren ajin su, kuma azaba take ba yarinyar sannan ta hana ta fada, ita yarinyar ita ke nuna mata ire-iren su MacLean su turaruka da dai sauransu dan goggonta irin mutanen karkaran nan ne da sam basu san kalmar wayewa ba.
Can bayan kamar minti goma ta miqe ta sake komawa É—akin me gari ta kama doka sallama
Me gari yana ciki yana jinta yayi banza da ita, shi kam mamaki yake na halin yarinyar nan shikam besan halin wa ta kwaso ba, sannan so take ta ƙarasar dashi gashi tsufa ya kama sa, Allah Sarki rayuwa, mamarta saliha ce sosai dan kiwo suka zo arean garin nasa ya aure ta, gata a lokacin ma ƴar karama ce sosai dan bata wuce sha uku ba, ko a lokacin ze iya yin jika da ita, a sha biyar ta haife ta ko fuskan ta bata gani ba ta rasu, gashi ƴan uwanta sun ƙara gaba ba'a ma san inda suke ba, ƙarshen ta kanwarsa sa'ade ce da ta kasance bazawara tazo take kula da ita dan sauran matan nasa sunƙi karbar ta, to suma duk tsufa ta kama su ba haihuwa suka yi ba itace ɗiyar sa ta farko dan har ya cire rai da haihuwa ma, se daga baya ya auri wannan Matar tashi yaransu uku da ita.
Ya fada a wannan zurfin tunanin yaji ana ƙoƙarin bude masa kofar daki, dole ya miqe jiki a sake cike da mamaki ya buɗe kofar ya hango fuskar ta shar da ita se walwali take, gaishe shi tayi ya amsa yana hade fuska dan be manta da karan ta da aka kawo har mutum hudu jiya da rana ba
Tun kafin tace uffan ya zaro wata tsohuwar Naira Hamsin ya bata dan bashi da kudi gashi anjima dole ne ya shiga fadar Nangere ya bada gaisuwa shida muƙarraban sa.
Koda ta karba kudin, wuff tayi ta fice a gidan ko sallama bata ma Goggo ba.
Tafiyar minti talatin da Ć´an kai daidai ya kaita Garin Nangeren, minti biyar kuma ya mata a makarantar su dake Sabon Garin Nangere, makarantar dai gata ga kamar ta kawai za'a ce, aji ta wuce tana wani babbasarwa, malami ma har ya shiga.
Wucewa kan bencin su tayi na ita da Sadiya yar sarkin Nangeren, Sadiya na ganin ta tayi murmushin yaqe.
Zan dakata daga haka
Mu haÉ—e a shafi na gaba
___________.
Littafin nan na kudi ne akan Naira 300 kacal.
Zaki saka kuÉ—in ki cikin wannan account numbern 0038735953
Stanbic Ibtc Bank, Fatima Idriss Bello.
Zaki turo shedan biyan ki ta wannan numbern 09020588802
WhatsApp only pls.
Idan kina so tun yanzu zaki iya biya, in kuma se an gama free pages ne ma dukka daidai ne.
Sannan duk sanda aka yi completing takaddan nan, kudin sa ze tashi daga É—ari uku 300 ya koma dari biyar 500.
Nagode.
🤍^^^^^^^^^^^^^^^🤍
👸ME GARI FATIMA👸
(The Female Village Head)
Na Fatima Idriss Bello
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20
2.
Free Page
Ganin irin murmushin da sadiya ta sa yasa Itama mayar mata da kalan shi, dan yau tasha alwashin se taje gidan su dan ta lura yarinyar nan kamar bata san taje gidan su ne ma, kuma ma banda reni ai de itama yar sarkin ce tunda babanta Me Gari ne kuma ita Sadiyan ai ta san da hakan, sannan duk sa'annin ta bauta mata suke dan basu kai tayi abota dasu ba tunda ita É—in kamar É—iyar Sarki ce, se Sadiyan da tayi fice ta aminta da ta zama kawar ta, ita kuma Sadiyar ta lura da tana so ta shusshure ta aiko bata isa ba, dole ne suyi abota tunda ubansu sarakuna ne. Ehe.
Can bayan an tashi daga makaranta memakon tabi su Hanne su koma Gabur se cewa tayi yau a gidan su Sadiya zata wuni
Ko da jin haka su Hanne suka kama hanyan su daman ba tare suka zo ba yau, ita kuma Sadiya sam bata so ba, a haka suka dunguma suka shiga motan gidan Mai Nangeren aka ɗebe su se fada, yan uwan Sadiya se kora da hali suke wa Fatima a cikin motan ta kasa ganewa, ita tunanin motar ma take a ranta, gaskiya motar gidan sarki ma ta dabance, dan Allah dubi yadda sanyi yake hura ta, motar Babanta yadda kasan an saki kura haka take dan ƙara, gashi lock din motan ma basa buɗuwa ta ciki se ta waje, duk inda kuka je sede ka dinga zurmiyo hannun ka ta waje ka buɗe kofar ka fita, amma ga mota nan, Allah idan da da halin da zata zama me Gari seta sa an rushe gidan su an musu shegen gini, sannan ta canza motocin gidan nasu ta sawo masu kyau
Tana a haka taga har sun iso fada, kofar a cike da mutane kamar me, kodanma ai daman yawanci gidajen masu shuni baya rasa jama'a, idon ta masu matuqar kyau ta ware cike da mamaki tana karewa gidan kallo kamar yau ne zuwan ta na farko, kodanma yaune za'a ce zuwan ta na farko tunda dai bata taɓa shiga cikin masarautar ba, se yau ɗin kuma a dalilin aminiyar tane Sadiya, tana ta kalle kalle har akazo sashen su Sadiyar, gani tayi Sadiyan ta sakko tana mata alaman ta fito, fitowa tayi ta saki baki da hanci tana karewa gidan kallo
'Wai Wai Wai, ZankaÉ—i', inji Fatima a ranta, gaskiya sadiya sunyi sa'ar gida, subhanallazi.
Tayi mutuwar tsaye tana tunani ta hango Sadiya na kokarin shigewa cikin gidan nasu nan da nan kuwa tabi bayan ta, koda ta shiga parlourn idon ta kamar ya fado kasa saboda tsabar kallo, ashe kyawun gidan da ta gani a mafarkin ta ƙalilan ne, zahirin yafi kyau sosai ma, bin sadiya tayi suka shige sashen maman Sadiyan, tana ganin kuyangi sai gaida sadiya suke abin har ya bata sha'awa, itakam a gidan su masu aiki ne kawai dasu kuma suma basu wuce uku ba a kaf din gidan sannan ba ma kullum suke zuwa ba, amma ta lura na nan ɗin na daban ne tunda gasu nan a duk inda kabi.
Sallama sadiya tayi kuyangar dake gun ta amsa tace musu su shiga, koda suka shiga Fatima ta shiga karewa dakin kallo, seda ta gama kallon kamin ta gaida maman Sadiyan, Maman sadiya kuma sai tayi mamaki da taga yarinyar bata durqusa ba, lalle ma, kodai bata san ita matar sarki bace? Share zancen tayi ta cigaba da harkokin ta, daga nan su Fatima kuma dakin sadiya suka wuce, suna shiga tacewa sadiya ta haɗa mata ruwan wanka, ran Sadiya in yayi dubu toh ya ɓaci amma se bata nuna ba, babu yanda bata yi ba dan ta yakice Fatiman nan a jikin ta amma ta lura kamar sake cusa mata ita ake, gashi bata iya mata musu sam, bari zata dai nemi mafita, fita tayi ta kira wata kuyanga ta hada musu ruwan wankan sai kuwa Fatima tayi wuff ta shige, shigar Fatima banɗaki ba se tayi karo da banɗakin mafarkin ta na ɗazu da ya sata yin fitsarin kwance ba? Tunawa tayi ai bata ma shanya katifar ba, tana ta tabe tabe da kalle kalle a haka ta samu tayi wankan ta daura towel din Sadiyan tayi waje, koda ta fito se tace wa Sadiyan
"Zaki iya shiga yanzu"
Sadiya bata ce mata uffan ba ta shige banÉ—akin ranta na suya dan ganin towel dinta a jikin Fatima sannan har umarni take bata ma ita da dakin ta, wankan ta tayi ta fita ta shirya cikin wasu kayan ta masu matuqar taushi
"Ke nake jira sadiya baki bani kayan da zan saka ba"
Sadiya ta tsinkayi muryar Fatima, Ita har ta manta da wata Fatima se da taji muryan ta ma.
Wata atamfarta ta dakko ta bata, ta karba ta saka suka yi sallan azahar daga nan suka yi parlourn gidan kan dinning suka wuce suka zauna sadiya tayi serving nasu, Fatima dai sai gani take ana bude flask ana zubo namomi da kaji da kifaye, tuni yawun ta suka tsinke, ita daman tasan tunda tayi mafarkin ta na yau ɗinnan tasan dadi ne yake jiran ta, ashe dai mafarkin ta ze tabbata, ba wai bata cin abun dadi bane a gidan su, a'a ai baza ka haɗa kauye da birni ba, wani flask ne yaja hankalin Fatima tacewa sadiya
"Ya baki bude wancan kwanon ba sadiya"?
"Kedai karki damu ƙawata da abinda ke ciki, burin ki kici abinci toh gashi nan na zuba mana, ba se muci ba"?
Sadiya ta karashe cike da gundura da halin Fatima, can sun fara ci kamar an tsikari fatanta ta miqe ta buɗe Flask din, ƙundun kaza ne a cike a ciki an masa wani kalan peppering, yawun ta ne ya tsinke a take takai hannu zata saka taji an daka mata tsawa, dakatawa tayi jikin ta na ɗan rawa ta rufe tana me kallon wane dan kininibin ne haka
Sadiya kuwa ji tayi farin ciki ya kamata, ƙarasowa Bodyguard ɗin yayi yace
"Ke Sadiya yarinyar nan yar gidan uban waye ce"
Jin haka Fatima tayi kofar É—akin Sadiya a guje, tace
"Yar gidan uban ka ce"
Shi kanshi Bodyguard É—in seda yayi mamaki, wayansa ne yayi kara se ya maida hankalinsa kan wayan, se can yace ma sadiya ta saka kuyanga ta shirya abincin a basket ta kai masa waje zeyi waya, daga haka ya fice.
Fatima kuwa da ganin haka ta hado kayan ta cikin jakarta ta makaranta tayi hanyar fita, can kuma tuna irin ganimar da ta bari akan dinning yasa ta koma ta cigaba da cin abincin ta tana santi tana hararan Sadiya, tare da tunanin ko me Goggo taci? Oho.
"Fatima kinsan wa kika zaga kuwa?"
Fatima ta tsinkayi muryar Sadiya na tambayan ta
"Koma waye shi wa yace ya zagi ubana"?
Ta karashe tana murkuda baki,
"Duk da haka dai yakamata kina kiyayewa Kinga dai nan gidan sarauta ne, in har kina so ki dinga zuwa se kina yin taka tsantsan, yanzu wallahi se yasa a miki É—an banzan duka kuma ya kwana lapiya"
Sadiyan ta karashe cike da jan kunne
Tsaki Fatima ta saki kana tace
"Ai kuwa da wallahi se ya san ya taɓa Ni"
Ta karashe tana jan wani dogon tsaki.
Can bayan ta gama ci ta miqe tacewa sadiya ta raka ta, sadiya bata ce komai ba ta dakko musu hijaban da suka yi salla dashi ta bata É—aya kana tarako ta har kusa da asalin fada
Fatima da ɗaga kanta sama se ta hango babanta Me Gari, ai kuwa da gudu tayi gun shi taje wai zata rungume shi, Me Gari tsabar bakin ciki rasa inda zesa kansa yayi dan kunya, mutane kuwa suka tsaya ganin ikon Allah, daman taro suka yi tsakanin su da Masu garuruwan ƙauyukan gefe da gefen su, sun gama taron suna sake tattaunawa Fatiman tazo ta gun.
Ido Fatima ta wa sadiya akan ta karaso mana, ƙarasowa tayi ba dan taso ba tazo ta gaida jama'an
"Sadiya ga Babana, Baba ga ƙawata Sadiya"
Me gari jinjina kai yayi cike da É—an fara'a yana ganin asalin kamar da sadiya take da Me Martaba, ita kuma Sadiya mamaki take, wannan tsohon ne baban Fatima? Ita wallahi ta dauka kakan tane ganin yanda taje gunsa da gudu da farko, ashe baban ta ne, kuma ma sam sam basa kama saboda Me Gari baki ne bashi da wani kyau ita kuma Fatiman kyakkyawa ce sosai har mamakin hadin kyan Fatima da halin ta take, sannan in har bata manta ba ai Fatima ce Ć´arsa ta farko, ikon Allah kenan.
Sallama sadiya ta ma Fatima ta juya ta koma cikin gidan su tana me sakin ajiyar zuciya na tafiyar Fatiman har wani iska me cike da rahama take shaqa, ita kuma Fatima tunda taga Me Gari ta liqe masa taqi motsawa, ya mata hararan ya mata kallon ya mata nunin amma duk a banza, hasali ma nunawa take bata fahimci inda ya dosa ba, sannan su baba Liman ko kallo basu ishe ta ba balle gaisuwar arziki, suko sanin halin ta sarai yasa basu wani yi ja'in ja ba.
Su Me gari basu yi niyyan tafiya ba amma dole suka kama hanya tattaunawar da basu gama ba kenan a dalilin Fatima, already Me Gari ya cika saura kadan ya fashe, daman da sassafe an kawo mishi ƙaran ta akan targaɗen da ta wa dabbobin mutane.
Kama hanya suka yi Lokacin har la'asar ta gabata, karshen zance, Fatima shigewa gaban motar me gari tayi ta hana Baba Liman zama, se matsuwa suka yi suka zauna su huÉ—u a bayan kowa yana tsoron ya tanka besan me ze biyo baya ba, a haka har suka karaso garin Gabur.
Suna isowa gida tayi sallan la'asar tayi ficewan ta gidan su Hanne daman bata samu Goggonta a gida ba, sannan tana É—an shakkun kallon da Me Gari yake mata.
Koda ta isa gidan su Hanne bata samu Hanne ba, da ta tambaye maman ta sai tace ta tafi gidan wata kawarsu Lami da aka mata aure kwanaki, ai kuwa bata yi wata wata ba se gidan Lami, tana zuwa ta iske su duk a tare yan sa'annin nasu ana hira, suna ganin ta suka sha jinin jikin su, kujerar da Lami din ke kai taje ta daga ta ita ta zauna akai, ta saka su a gabanta kamar wasu Ć´aĆ´anta ta fara basu labarin gidan Me Nangere.
Yaqe suka dinga yi suna jin labarin da take basu, dan gani suke kamar karya take sharara musu, har ita ta isa ta shiga gidan sarkin nangere? Sannan har da ce musu wai taci abinci masu dadi?
Kawai dai sunyi shiru ne dan suna tsoron bata mata rai
Sai can kusan mangariba suka watse bayan sun gama kassara mijin Lami, dan É—an cefanan da yayi seda Fatima tasa aka dafe musu dukka suka zauna suka take kafin tasa suka rako ta gida sannan ko wacce tayi gaba izuwa nasu gidan.
Koda Fatima tazo shiga gida taga ana ta alola za'a yi sallah, har zata tsaya yin kininibi ta tuna irin kallon da Me Gari yayi mata dazu se kawai ta shige gida, dadin abun ma me gari baya shigowa se dare ya ɗan fara yi, in yaso kafin ya shigo zata ci ƙayau ƙayau ɗin da yayanta ze kawo mata tayi bacci ko ya neme ta ma baze same ta ba, da wannan ta shige sashen goggonta tayi alola tayi sallah, ita Goggon har mamakin ta tayi akan me ya hau kanta yau take yin ibada akan lokaci.
Can suna hira da goggonta daman taqi cin tuwon da akayi taji sallaman me gari, hantar cikinta seda ya kada se daga baya ta É—an dawo daidai tana tambayan kanta ma, "Toh meyesa cikin ta ze kada ma, Me Gari dai ba iya dukanta zeyi ba dan ya tsufa, sannan Yayanta yana santa baze iya dukanta ba saboda haka ta kwantar da hankalin ta ma''
Karasawa gefen Goggo me Gari yayi ya zauna yana tambayan ta Isuhu, tace masa be shigo ba, can se ga sallamar Isuhu, koda yazo Me Gari ya fayyace masa daga biri har wutsiya, daman tara ta yake ai be san sanda ya hau kan Fatima da duka ba
Mutumiyas se ihu take saki yanda kasan