Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 13
Babara bai motsa ba. Nan take ruwa ya ɓarke tamkar da bakin kwarya. Duk bayan daƙiƙa biyar sai aradu ta sauka mai ƙarfin gaske. Ba jimawa wannan ruwa ya fara haɗuwa zafin aradun dake sauka suka fara narka wannnan dusar ƙanƙara data cika wannan kurkuku. Kwana uku cir aka ɗauka ana zabga ruwa kafin dukkan wannan ƙanƙara ta narke. Wannan kurkuku ta bayyana a fili. Ashe acikin wannan dusar ƙanƙara manya-manyan duwatsu ne na wuta wanda aka fafake cikinsu akai gidaje. Kana ganin wannan gidaje zasu tuna maka da ƙissar samudawan farko irin wanda akan bayyanasu da cewa suna ɗumamen safe da zafin rana. Waɗansu halittu ne sanye fatun namun dawa suka fara ambaliya daga cikin wannan gidaje na dutse da wani irin sauri tamkar na aljanun farko. Kafin ƙiftawar ido da bismillah sama da wannan halittu dubu uku sun bayyana sun kewaye Babara a inda yake zaune. Ga dukkan alamu ya tayar dasu daga baccinsu. Fuskokinsu a rufe suke da fatar farin zaki amma hakan bai hana tsananin ƙiyayya dake tashi daga cikin idanuwansu bayyana ba. Wata irin iska mai ɗauke da marmarin yaƙi na fita daga jikinsu. Sannan suna bada gunji mai amo kai kace samarin kuraye ne. Sahu-sahu sukai tare da tunkaro Babara a inda yake zaune, lallai babu ko tantama niyyarsu suyi watanda da naman Babara. Matsalar ɗaya na bayan ba lalle su samu ba. Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Idanunsa na cike da imani da dogaro da fasahar da Armad Wilbafos zai farkar. Ba jimawa tokar naman jikin Armad ta fara haɗewa tana curewa waje ɗaya acikin wannan rijiya wadda tuni ta cika da ruwa. Ba jimawa wata tsawa ta sauka acikin rijiyar wadda ta ƙone duk ruwan dake ciki. Babu abinda yai ragowa acikin wannan rijiya sai tokar Armad. Ana haka wannan toka ta juye izuwa siffar Armad Wilbafos. Armad yai wani gunji mai firgitarwa wanda yasa dukkan wannan halittu jada baya. Wani taku irin na jaririn aljani ya fara fitowa daga cikin wannan rijiya. Inda daga bisani sabon saurayi ɗan kimanin shekaru sha tara ya bayyana daga cikin wannan rijiya, a jikinsa babu komai sai ɗan bante. Yana bayyana Babara ya buɗe ido tare da miƙewa ya kawo gaisuwa. Koda ganin haka sai waɗannan halittu suka fusata tare da rabuwa izuwa gida uku. Kaso na farko suka ɗaga hannunsu sama, inda wasu masu, masu ci da wuta suka bayyana. Kaso na biyu kuwa bakunansu suka buɗe, inda suka fara yin aman ruwan narkakken dutse wanda zafinsa zai iya ƙona wuta ita kanta. Kaso na uku kuwa wani baƙin ruwa ne ya fara ambaliya daga hannayensu, idan da Armad yana gani zai gane ruwan irin ruwan da Dordor suke amai ne. Dukkaninsu sukai ƙaraji tare da sakar wannan hare-hare izuwa Armad. Babara yai tsalle da niyyar shiga tsakani amma Armad ya ɗaga masa hannu. Ba shiri Babara yai gefe. Lallai koda aljanun farko sai sun tsorata da wannan hari na wannan halittu, wanda ke ɗauke da tsantsar rashin imani. Domin kuwa idan ka kalli samaniya zaka ga masu, masu cida wuta sama da dubu, haɗe da guma- guman ruwan narkakken dutse sama da dubu, tare da wani baƙin ruwa mai alamun mutuwa. Kuma abu na farko da zai fara zo maka shi ne waɗannan hare-hare ana niyyar halaka gari ne dasu, babu wanda zaiyi tunanin wai mutun ɗaya ake so a halaka. Armad ko gezau baiyi ba, hasalima ko motsa ɗan-yatsa baiba. Yana tsaye waɗannan guma-guman azaba suka saukar masa. Wata ƙara mai firgitarwa ta tashi, sannan ƙura ta turnuƙe. Lallai ko wanda ke tsaye kimanin nisan tafiyar shekaru dubu zai iya jin wannan ƙara, kuma zai iya ganin wannan ƙura. Babara yai ƙaraji saboda ɓacin rai ya afka cikin wannan hargitsi domin ceto Armad. Amma ba jimawa yaji wani irin yanayin Izza mai firgitarwa irin wanda bai taɓa ji ba a duk tsahon shekarunsa. Ba shiri ya fara jada baya kaɗan da kaɗan kafin wannan yanayin izza ya ƙara dukansa, lamarinda yasa ya harɗe tare da faɗuwa a ƙasa. Haki sarkin duba Babara ya fara, badan komai ba sai dan saboda ƙarfin izzar da yake ji. Amma waɗannan halittu basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara fara shirin wani harin. Sai dai a wannan karan girman kaba'irar da suke nufin Armad da ita ya ƙaru. Domin kuwa kowa acikinsu girman harinsa ya ƙaru da sama da sau uku. Suna niyyar afkawa Armad sai ƙura ta lafa inda surar Armad ta futo fili. Sai dai ina, kwata-kwata ba irin Armad ɗin da aka sani bane. Babu komai a jikinsa face walƙiya. Amma abin mamakin bawai irin yanayin walƙiyar dake kewaye Armad bace a lokacin da yake amfanin da ɗalasimai irinsu Kaban'shisu. Wannan walƙiyar daga cikin tsoka da jinin Armad take. Hasalima zaka iya cewa naman jikin Armad ne ya juye baki ɗaya izuwa gundarin walƙiya. A wannan lokaci Armad ya zare wani mashi wanda ya nutse acikin ƙirjinsa. Amma babu komai ajikin mashin daya shafi jini ko fatar ɗan-adam. Lallai a wannan lokaci zaka iya cewa Armad wilbafos ya zama walƙiya, walƙiya kuma ta zama shi. Armad ya ɗaga hannusa sama ya dubi gundarin walƙiyar data haɗa hannunsa. Sannan daga bisani ya juyarda hannun nasa ya koma izuwa tsoka da jini. Sannan sauran jikinsa shima ƴa koma yadda yake. Koda ganin haka sai Babara ya zube a ƙas yana gaisuwa. "Ina ƙara jaddada mubayi'ata magajin wilbafos." Abin mamaki sai waɗannan halittu suka cire fatar dake rufe da fuskarsu inda suka bayyana a matsayin mutane. Sannan suka zube a ƙas suna gaisuwa tare da mubayi'a. "BARKA DA ZUWA MAGAJIN WILBAFOS, MAGAJIN SARKI EYRIYON, MAGAJIN SARKI ALDAIMA. Ka yafe mana rashin ɗa'ar mu, lallai mun cancanci kisa!!!" A dai-dai wannan lokaci duk wani wanda yasan sirrin dake ɗauke cikin jinin MAGAJIN WILBAFOS yasan an farkar dashi. *** Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe gari ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 81: Kwangila Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Haka Lamarudu Wilbafos ya kai Armad cikin wani shinge wanda aka kewaye shi da manya-manyan jajayen duwatsu. Daga saman duwatsun kuma ruwa ne ke gudana zuwa ƙasa tayadda suka samarda wata ƴar ƙasaitacciyar ƙorama a ƙasa. Lamarinda yasa wajen yake bada wani irin sanyi mai inganci. Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wai shin wajen horo aka kawoshi ko kuma wajen shaƙatawa. Amma kafin ya tambaya sai Lamarudu ya ɗora hannunsa akan wani dutse inda wasu hatimai suka bayyana suka kewaye dutsen. Nan take wata ƙofa ta buɗe a wajen. Lamarudu ya shige ciki sannan su Armad suka bishi a baya. Suna shiga wani ƙasurgumin daji mai kama da kasuwar muridan aljanu ya bayyana a gabansu. Babu komai sai manya-mayan bishiyun kuka wanda kowacce ɗaya tafi tsayin zira'i ɗari. Abin mamaki shi ne wasu manyan ƙayoyi dake kewaye da rassan wannan bishiyu a matsayin ganyayyaki. Lamarudu ya ce, "ga wajen koyar horo. Ga kuma ɗalasimin dazai fitar daku a yayinda kuka gama." Ya miƙa musu wata takarda mai ɗauke da hatimi. Har ya juya zai fita saiya waiwayo ya ce, "dajin nan an rabashi izuwa gida uku. Dajin kuma acike yake taf da jinsin Dordor dana aljanu masu cin naman biladama. Indai har mutun baya iya jin yanayin-izza to lallai bazai iya rayuwa aciki ba. "Kaso na farko na dajin yana ɗauke da abubuwanda izzarsu take tsakanin dubu ɗaya da dubu biyar. Kaso na biyu suna ɗauke da izza tsakanin dubu biyar da dubu goma. Amma kaso na uku duk abinda ka gani aciki izzarsa ta haura dubu goma. Lallai duk hatsabibancinmu bama shiga yanki na uku. A fito lafiya." Ya juya ya fice ya bar Armad da Babara a wajen. Bayan ya fita Babara ya tambayi Armad, "kaga irin kallon da wannan mutane ke yima?" Armad ya amsa da, "eh." Babara ya ɗanyi shiru naɗan taƙi kamar baya so ya faɗa amma daga ƙarshe ya ce, "Sunyi imani dakai kuma suna yi maka kallon zaka cece su. Hakan shi ne ma dalilin da yasa suka nuna maka waccan tsohuwar daula. Kada ka manta iyayensu sunyi wa kakanka sarki Eyriyon bauta, wanda hakan ne yasa aka ƙullesu. Cetonsu da zakai kamar ramawa kura aniyarta ne. Kuma idan ka yadda ka shiga cikin wannan daula zaka samu fasahohi da bayi na aljanu wanda zasu taimake ka a hanyarka ta zama cikakken sarki Wilbafos. Nidai ina ganin ya kamata ka shiga wannan tsohuwar daula." Armad dama yasan tuntuni Babara bai amince da rashin shigarsa wannan tsohuwar daula ba, saboda haka tuni ya tanadi amsa. "Duk na yadda da abinda kake faɗa amma kai sani cewa bazan iya sauka daga manufata ba. Kuma lallai indai ba ganin mahaifiyata ta samu lafiya nayi ba bazan iya tsayawa acikin wannna kurkuku ba. Saboda haka inaga mu fara horo kurum." Haka dai Babara ya haƙura dole. Sannan ya zana wasu hatimai guda uku a kewaye da Armad kafin ya bawa Armad umarnin ya zauna a tsakiya, sannan daga bisani ya fara karanta wasu ɗalasimai. Can bayan sa'a ɗaya ana cikin wannan hali sai fuskar Babara ta canja, inda nan take ya daina karanta ɗalasiman ya garzayo gaban Armad inda ya ɗebi kaɗan daga jininsa ya zuba acikin wata kwalba mai ɗauke tsumi. Armad dai ya ji wani abu amma yai shiru baice komai ba ya ƙurawa Babara ido. Can Babara ya kalli Armad cikin alhini yana cewa, "dama nayi tunanin haka, amma ina ta addu'a ya zama hakan bata faru ba." Armad yai zumbur ya ce, "ban gane ba. Mai kake nufi da dama kayi tunanin haka?" Babara ya fara bayani, "labarin daka bani na ɓacewar Miyurarka bawai Miyurarce kaɗai ta ɓace ba, harda wani ɓangare na ruhinka. A sakamakon haka bazaka iya amfani da idanuwanka ba har sai ka nemo wannan ɓari na ruhinka." Armad ya zare ido. "Eh?!" Babara ya ce, "bari mu gani idan zan iya gano inda ɓarin ruhin naka yake." Nan take ya ƙara ɗiban wani jinin daga hannun Armad ya kuma yaryaɗar dashi akan ƙasa, inda ya zana wasu hatumai masu rikitarwa akansa. Can daga bisani jinin na Armad ya fara yin haske, kafin daga bisani ya kama da wuta. Nan take sukai tsalle gefe, amma kafin suyi wani abu tuni jinin ya ƙone ƙurmus. Babara ya dubi Armad ya ce, "ruhinka yana katange acikin wata sihirtacciyar ƙasa amma saboda ƙasar na kewaye da Tsari baza a iya gane wacce bace." Armad yama rasa mai zaice, domin kaf maganar a baibai yake jinta. Wai ruhinsa ya ɓalle? Bayan kuma gashi nan da rai da lafiya. A iya saninsa ma wannan ba abu bane mai yiwuwa ba. Yana cikin tunani yaji muryar Babara, "nasan mai kake tunani, kuma kayi sani nima wannan shi ne karo na farko da naga mutun ruhinsa ya rabe kuma ya ci gaba da zama da rai. Amma dai maganar tana nan cewa bazaka iya yin amfani da idonka ba har sai ka nemo ɓangaren ruhinka." Armad ya kalli zoben dake ɗan yatsansa inda mahaifiyarsa ke ajiye. Can bayan tsahon lokaci Armad ya yanke shawara, inda ya numfasa ya ce, "idan za'a fara bada tarihi na, za'ace na fara ne daga nemo ɓangaren ruhina daya ɓalle. Saboda haka inaga zaman mu a wannan kurkuku yazo ƙarshe, lallai inada mahaifiyata a gabana bazan tsaya neman suna acikin wannan kurkuku ba." Babara ya rusunar dakai alamun girmamawa sannna ya ce, "ya shugaba na akwai wata hanya banda idanuwanka da zaka iya bawa mahaifiyarka izza da ban gaya maka ba." Armad najin haka yai zumbur cikin murna ya ce, "ko? Kamar ya fa?" "Kamar yadda ka sani kowanne ɗan adam yana samun ƙayyadaddun shekarun izza lokacin daya farkarda izzarsa, kuma wannan adadi a ƙa'ida baya taɓa canjawa. Koda kaima dalilin da yasa naka suka canja daga hamsin da ɗaya zuwa dubu ɗaya dan kawai baka farkarda izzarka ta haƙiƙa bane da farko. "Amma akwai wasu hanyoyi guda biyu kacal wanda ake iya ƙara yawan izza. Hanya ta farko na riga na gaya maka ita. Ita ce ta amfani da sirrin dake cikin idanun ƴaƴan Wilbafos. Hanya ta biyu wadda ban gaya maka ba ita ce hanyarda ake kira da KWANGILA!!" --- Mai kuke tunani ake nufi da fasahar KWANGILA? ** Note ------- Fasaha/Technique Farkarda fasaha/Awakening Sido-Urúrú/Pseudo-Ururu Hatimi/Ancient runes Dalasimai/spells etcMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 83: Bango Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Duk da gudun dokinsa Ubbaru saida Armad yai kwanaki goma sha ɗaya yana tafiya sannan ya fara hango Bangon arewa. Gangar ruwa iyakacin ganinka ta shafe kudu da yamma gabas da arewa, tana ta kwaranya izuwa ƙasa amma babu ko halitta ɗaya a samanta. Koda Armad ya hangi wannan sai yaja linzami ya tsaya, inda ya buɗe zoben sihiri da Nostaljiya ta bashi domin ya futo da mahaifiyarsa. Babara ya gaya masa duk bayan kwana biyu akwai wani tsumi da zai ringa bata har zuwa lokacinda zai samu wannan shekarun Izza ya bata. Shi dai wannan tsumi shi ne abinda Babara ya ringa bata tsahon shekarunda Armad yayi bayanan kuma har ya dawo ya same ta cikin ƙoshin lafiya. A lissafin Babara mahaifiyar Armad tana buƙatar aƙalla shekarun izza dubu goma kafin ta warke. Wannan shekaru ba wani abu bane a wajen sarakunan jinzidal masu fasahar kwangila, saboda haka Armad ya gama yanke shawara kai tsaye wajen Nostaljiya zaije. Kuma tunda a hannunsa akwai wani ɗalasimi daya karɓa daga wajen Babara wanda zai iya gano masa inda ruhinsa yake zai iya yin aiki biyu a lokaci ɗaya, yana neman ruhinsa kuma yana neman Nostaljiya. Amma koda wannnan tunani ya gilmawa Armad a rai saiya tuno cewa ai bama abu biyu ba, lallai abu uku zaiyi a lokaci ɗaya. Domin kuwa akwai alƙawari daya ɗauka na kawarda cinikin bayi a ban ƙasa, wanda kuma bai manta dashi ba. Koda tunanin haka sai Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya shiga inda ya samu waje ya rubuta sha huɗu ga wata tara shekarar 1855 Bayan Amri. Wato dai a wannan rana ce Armad ya fara shirinsa na rusa rukunin Jinzidal. Bayan ya gama kallon wannnan kwanan wata saiya juya izuwa ɗakin daya ajiye mahaifyarsa, inda ya shiga ya same ta a kwance, idanunta a rufe kamar tana bacci. Mahaifiyar Armad tana bada yanayin kwarjini matuƙa wanda saboda haka ba kowanne ma'aboci izza bane zai iya tunkararta ba a hakan da take a sume. Gashin kanta na nan baƙi, kuma kamar yadda wannnan cuta ta izza take a har kullum alamar kawai shi ne mutun zai zamanto a sume, amma banda haka babu wani abu dazai nuna rashin lafiya kamar irinsu tari ko zazzaɓi. Koda zama a gefenta sai kawai wani hawaye ya fito daga idonsa, babu abinda yake tunawa sai lokutan da yana yaro da kuma lokaci na ƙarshe daya ganta da lafiya. Tsahon lokaci a haka kafin ya buɗe bakinta ya ɗisa mata wannan tsumi dake cikin wata ƴar kwalba. Sannan ya taso ya futo idanunsa cike da kwalla. Lallai akwai abubuwa da dama da yake so ya tambayeta idan ta farka. Saboda haka babu wani abu dazai tsaya a gabansa. Har Armad yaje bakin ƙofar wannan zobe zai fita sai ya tsaya ya juyo inda ya durƙusa yayi alƙawari, ƙololuwar alƙawarinsa cewa a wannan fita kozai rasa ransa bazai dawo ba sai mahaifiyarsa ta warke. Yana fitowa ya rufe ƙofar wannan zobe sannan bayan yaci abinci ya mayarda Ubbaru cikin zobensa ya kuma nufi wannnan bango a ƙafa. Yana isa gaban wannan bango wata izza irin wadda bai taɓa jintaba ta dakeshi tayi cilli dashi gefe. Yana faɗuwa yaga jikinsa ya fara narkewa, fatarsa tana ɓanɓarewa. Nan take Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya. Wanda hakan ne ya cetoshi tunda hatta wuta bata isa ta ƙona walƙiya ba. Nan take Armad yai murmushi tare da cire zoben dake hannunsa ya cilla a baki sannan ya ɗaga hannunsa sama ya kirawo ɗaya daga cikin ɗalasimansa daya daɗe baiyi amfani dasu ba wato Kaban'shisu. Idan mai karatu bai mantaba wannan ɗalasimi ana iya amfani dashi ayi tafiya acikin lokaci daga wani waje zuwa wani. Matsalarsa kawai ita ce sai ɗaya kacal ake iya amfani dashi a shekara. Tuntuni dai Armad yayi tunanin amfani da wannan ɗalasimi ya fice daga cikin wannan kurkuku to amma bai gama abinda ya shigo dashi ba, sannnan kuma baya son yabar Babara anan. Nan take ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, inda ya ɓace daga inda yake. To amma a wannan lokaci maimakon ya tsinci kansa a bayan wannan bango sai kawai ya ganshi acikin tsakiyar bangon, kewaye dashi wani ruwa ne mai tsananin danƙo. Abu na gaba daya biyo baya wasu abubuwa ne manya-manya guda biyu suka bayyana a gaban idon Armad. Ɗaya daga cikinsu yana kama da wata daren goma sha uku, ɗaya kuma yana kama da rana saidai dukkaninsu baƙaƙe ne wuluk. Waɗannan abubuwa suka ƙura masa ido tamkar wasu idanun mayunwaciyar kurar da taga abinci. Nan take Armad yaji ya fara rawar ɗari. A lokacin ne ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya jikinsa ya narke babu abinda ya rage face ƙoƙon kansa. Kuma wai a hakan ma dan ya riga ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ne, lallai da tuni ya tsinci kansa a lahira. A wannan lokaci ya fuskanci abubuwa guda biyu. Na farko dai bawai a waje ɗaya yake tsaye ba, hasalima mugun gudu yake acikin wannnan bangon saboda ɗalasiminsa na Kaban'shisu. Wanda hakan ya nuna masa cewa saɓanin fahimtarsa da ɗalasimin bawai ɓacewa yake yiba a lokacin da yayi amfani dashi, kawai dai saboda tsananin sauri ne kawai yake ganin kamar ɓacewa yayi. Abu na biyu daya fuskanta shi ne wannnan abubuwa guda biyu dake kama da rana da wata ba wasu abubuwa bane illa idanuwa guda biyu na Ururu. Kuma hatta rawar ɗarin da yake ji daga su ne. A take Armad ya gane cewa lallai koda ya taho da Babara lallai bazai iya wucewa dashi ba. Domin ba daban jikinsa na walƙiya ba da tuni ya mutu aƙalla sau ɗari zuwa wannan lokaci. Sannan kuma ya gano cewa yayi dabara daya saka zobensa acikin bakinsa domin da tuni ya narke. Ana cikin haka wannnan idanuwa guda biyu suka fara haske suna fitarda wani yanayi mai firgitarwa. Ba shiri Armad yaji tamkar ana caccaka masa allurai acikin kansa. Abin mamaki sai kawai ya ganshi ya tsinci kansa a tsakiyar filin yaƙi, kewaye dashi sarakunan Ashura ne guda goma. Kowanne acikinsu yana riƙe da baƙar takobi. Kafin Armad yai wani motsi su goma sunyi tafiya acikin lokaci sun cake masa wannnan takubba acikin ƙirjinsa. Ko motsi baiyi ba ya faɗi matacce. Abin mamaki a gaske ma a wannna lokaci hankalin Armad ya gushe, babu wanda ya sani ya mutu ko kuwa yana raye. --------- A dai-dai wannan lokaci acan doron ƙasa ta farko sarakuna goma mafi girma a duniya, wanda aka fi sani da ASHURA, ne suke jin wata sarewa mai alamar ƙugen yaƙi tana kaɗawa. Wannan sarewar nada ban mamaki tayadda duk wanda yaji ta kawai zaiji sarewa ne amma banda sarakuna goma na ASHURA. Su saƙo suke ji akan wani mutun da yayi ƙoƙarin ficewa daga kurkukunsu. Amma acewar wannan murya, idanuwan sarki Ururu Kuyurussa'ayi, idanuwanda suka yaki sarki Eyriyon Wibafos, sun halaka wannnan mutun har lahira . 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Hausa ebooks - pdf,txt and doc www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks hereMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 83: Dan Baiwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Bayan gushewar hankalin Armad dukkan jikinsa saiya fara juyewa daga walƙiya yana komawa toka. Kafin ƙiftawar ido da bismilla Armad ya juye izuwa toka. Nan take wannan toka ta narke acikin wannan ruwa kafin daga bisani ayi watsi da ita ta dawo cikin wannan kurkuku. Idan da zaka ga yadda akai watsi da wannan toka zaka fuskanci cewa hatta ragowar tokar ba'a yadda ta fita daga wannan kurkuku ba. Lallai abinda ake faɗa na cewa indai ka shigo ka shigo kenan haka yake. Amma ba jimawa ƙarfin fasahar Armad ta ƙara warewa, wannan toka ta kama ci da walƙiya. Sannnan daga bisani ta juye izuwa surar Armad, kafin daga bisani ta juye izuwa Armad a kwance a sume yana aman jini. Haka Armad yaci gaba da kasancewa acikin wannan hali baisan inda kansa yake ba har tsahon kwana biyar. A kwana na biyar ɗinne wasu mutane sanye da kayan farar fatar raƙumi su biyu suka iso wajen. Dukkaninsu suna kan ingarmar dawakai, sannan kuma suna riƙe da takubba. Na damansu ne ya fara sakkowa inda ya zunguri Armad da ƙafa domin ya gano da rai ko ba rai. Kafin daga bisani ya ɗaɗɗaure shi a jikin dokinsa kafin su koma da Armad inda suka fito. Armad bai san yadda akai ba, kuma bai san kwana nawa yai ba, kawai dai ya farka ya tsinci kansa a cikin wata ƴar bukka shishi kaɗai. Yai shiru yana tunano abubuwan da suka faru dashi acikin bango, inda nan take wata tambaya ta faɗo masa. Shin ya fita daga kurkukun ko kuwa har yanzu yana ciki. Abu ɗaya daya sani shi ne idanda da matsala da lallai acikin ankwa zai ganshi, amma gashi nan a sake akan gado. A wannan lokaci yaji surutan mutane a waje saboda haka nan take ya gano cewa hanya ɗaya dazai samu amsar wannan tambaya shi ne ya fita waje ya tambayi ɗaya daga cikin mutanenda yaji suna magana a wajen tantin. Saboda haka ba tare da tunanin mai zai faru ba Armad ya buɗe ƙofa ya danna kai waje. Abin mamaki yana fitowa yaga babu ko mutun ɗaya dake gadinsa, suma masu wannan magana suna can gefe kuma kallo ɗaya sukai masa suka ɗauke kai suka ci gaba da hira. A kewaye da wajen duk irin wannan bukkoki ne sama da hamsin. Daga gaba garesu kuma akwai wannan ruwa da ake kira da bango, lamarinda yasa Armad ya gano cewa lallai akwai matuƙar yiwuwar haƙarsa bai cimma ruwa ba. Ajikin bangon akwai wani baƙin ƙarfe wanda yai sama sosai tayadda ba'a iya gano ƙarshensa. Akwai mutane a wajen amma basu da yawa, kuma abin mamaki ba ruwan kowa da kowa, kowa harkarsa kawai yake. Can dai Armad ya kasa daurewa ya tare wani mutun sanye da jallabiya ya tambayeshi, "Malan da ALLAH ina ne nan?" Mutumin ya kada baki ya ce, "baka ma san inda kake ba. Kaine wanda aka ce yayi ƙoƙarin shiga ta cikin bango kai tsaye ko?" Mutumin na faɗar haka ya wuce gaba ba tare da amsawa Armad tambayarsa ba. Armad ya haɗe rai yana niyyar finciko mutumin baya sai yaji murya a gefensa. "Kana shalkwatar ƴan-daban ƊAN- BAIWA." Armad ya juyo da kansa ɓangaren inda yaji muryar inda yai arba da wani saurayi kalar larabawan yamma mai yawan dogon gashi mai launin ja da fari. "Shalkwatar ƴan-daban ƊAN-BAIWA? Wane ne ɗan-baiwa kuma?" Saurayin ya ja dogon farin gashin dake kansa tare da yin murmushi yana cewa, "kamar yadda ka sani wannan kurkuku an rabata tsakanin ɓangarori guda uku. Shekara ɗaya baya, ɓangare ɗaya basa ƙoƙarin guduwa daga wannan kurkuku, amma dama can ɓangarori biyu sun daɗe suna ƙoƙarin guduwa. Amma a yanzu hatta wannnan ɓangare ƙoƙarin guduwa suke. Wanda hakan ya jawo sauye-sauye da dama acikin wannann kurkuku. Da dama ana ganin wannan canji yana faruwa ne saboda bayyanar wannan mutun da ake kira da ƊAN-BAIWA, duk da babu tabbashi akan wannan maganganu amma lallai a yanzu sama da kaso sittin na wannan kurkuku suna biyayya ga wannan mutun mai suna ɗan-baiwa. Babu wanda yasan daga inda yake ko kuma tayaya ya shigo wannan kurkuku amma bisa mamaki tuni jama'a suka naɗashi a matsayin sarkinsu. Suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Ni ne na ceto ka daga inda ka suma." Wannan mutun ya kammala bayaninsa da miƙawa Armad hannu su gaisa. Abubuwa da dama Armad bai fahimta ba saboda haka yai shiru yana tunanin mai zaice masa. Baima kula da dogon sunan wannan saurayi ba. Koda saurayin yaga haka sai yai tunanin ko Armad bai yadda dashi ba ne, saboda haka ya ce, "Kada da damu, dani da abokina muka ceto ka. Kuma a wannan waje babu wanda ya damu dakai, sai dai kawai kai sani cewa muna zaune Tsarin dake jikin bangon nan ya fara haske irin wanda ke nuna cewa wani yayi ƙoƙarin guduwa. Hakan ne yasa akai ƙungiya ta mutun bibiyu domin su kewaya su gano inda abin ya faru. Ta haka ne dani da wanda aka haɗani muka gano ka." Armad ya numfasa ya ce, "nagode. Amma ina da tambayoyi da yawa. Da farko dai wanne sunanka acikin sunayen daka gayamin?" Saurayin yai murmushi tare da cewa, "suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Kada ka damu a hankali zaka riƙe su. Da dama sukan ɗau lokaci." Armad yaja numfashi mai tsayi kafin ya girgiza kai. "To amma menene manufar wannan shugaba naku mai suna Ɗan-baiwa? Sannan kuma shin zan iya tafiya idan ina so?" Wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Eh zaka iya tafiya mana, amma idan har kana so kaga Ɗan-baiwa to ka tsaya domin kuwa yau zai biyo ta wannan waje." Armad ya tsaya yana tunani kafin daga bisani yai ajiyar zuciya. Babban abin shi ne duk wata tambaya da Armad yayi wa saurayin bao amsa masa ita ba kai tsaye. Hasalima har yanzu bai masan taƙamaimai meke faruwa ba. Daɗin daɗawa jikimsa bai gama warewa ba. Yana cikin tunani yaji muryar wannan saurayi a kunnensa yana cewa, "zo kaga zanensa kafin ya ƙaraso." Saurayin yaja Armad izuwa wata kwana. Suna isa wasu mutane ne guda shida suke ta kallon wani ƙaton zane dake kafe a jikin bango. Suna matsawa kusa sai Armad ya fara jin abinda suke cewa. "Shi ne Ɗan-baiwa. Yadda ka ganshi a jikin hoton nan haka yake a gaske. Kana ganinsa kasan jarumi wanda zai iya canja duniya." Koda Armad yaji wannan kalamai sai ya ƙara azama domin yaje ya ga wannan ɗai-baiwa da idonsa. Amma yana isa ya tararda hoton wanda ya sani kamar tafin hannunsa ajikin wannan zane. Wannan dai ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda. Koda ganin wannan zane sai Armad yaja da baya cikin tsananin mamaki da ɗimuwa. Ya dubi wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Wannan ne ɗan-baiwan?" Saurayin ya kyaɗa kai, "Eh shi ne. Kasan shi ne?" ** . 2)Yaku ma'abota karatun littattafan

Chapter 8 of 13