Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 13
acikin saƙon amma na ƙara baka lokaci naga ko zaka iya farkar da jininka na wilbafos. Kai sani cewa nayi farin ciki kwanakin baya da naga hasken farin-wata ya canja kala. Domin nasan cewa lokaci yayi dazan biya Hidaya bashin da take bin ƙungiyar ƴan-duba ta duniya. "Amma fa kai sani wani hanzari ba gudu ba...." Armad ya katse Babara ta hanyar yin ƙaraji ya zare takobinsa yana huci, "Wai kana nufin duk wahalar dana sha ta nemo Tarifil-fakta a banza!!" Armad bai san lokacin daya kaiwa Babara wani sara ba cikin ɓacin rai. Babara yai tsalle gefe guda yana murmushi, "To yanzu da ban tura kaba zaka farkar da jininka? Kasha wahala, amma yanzu zaka ga amfaninta. Sannan kuma indai hanyar Izza zaka bi wannan baka ga komai ba a fannin wahala. Yanzu duniya tasan dakai, idanun kowa zai dawo kanka. Idan bakai da wuri ba ka farka lallai yanzu ne zaka san wahala." Babara yana magana amma Armad kawai huci yake yana kallonsa a fusace. Bayan ɗan lokaci Babara yaci gaba da jawabi, "Sai ansha wuya ake samu Izza. Kuma lallai indai kana so ka zama ma'aboci Izza yanzu ka fara. Saboda yayarka Hidaya nayi alƙawari zan koya maka yadda zakai amfani da idanuwanka wanda ita kaɗai ce hanyar da zaka zama ma'aboci Izza na gaskiya ka iya tsayawa a gaban Ururu sannan kuma ka ceto mahaifiyarka ta hanyar bata shekarun Izza. Amma kai sani cewa hatta yayarka Hidaya wadda hatta a duniyar aljanu ana labarin ƙarfin kwakwalwarta da gane abubuwanta saida tayi shekaru uku tana koyar yadda zatai amfani da idanuwanta. Lallai zaka iya yin shekaru goma kana koya wanda kuma mahaifiyarka baza takai wannan lokaci ba. "Naji daɗin ganinka da wannan zoben domin zai taimaka mana wajen ajiye mahaiyarka aciki." Babara yai nuni da zoben da Nostaljiya ta bawa Armad. Babara ya tafa hannunsa tantin dake bayansa ya ɓace, babu abinda ya rage sai wata ƴar jaka a hannunsa. Ya zira hannu a jakar ya ɗakko wata leda mai cike da Ayrid ya jefawa matan nan guda biyu ladan aikinsu. Sannan ya juyo wajen Armad yana mai cewa, "Zan koya maka yadda zakai amfani da idanunka dama kuma duk wani abu dana sani a shekaru na dubu ɗaya da ɗari uku a duniya. Saboda Hidaya." Armad yama rasa mai zaice. Kansa yana nema yai tsawa saboda tsabar caji. Ya za'ai ace abinda yai shekaru yana nema wai dama duk gwada shi kawai ake. Sannan kuma babban abin haushin ma shi Babara yana nunawa ba wani abu bane. Hasalima har ya gama yanke shawara zai koya wa Armad al'amuran Izza kamar ma babu abinda ya faru. Armad ya kasa daurewa, "Zan bika sabida mahaifiyata, amma idan wannan ma ya zama wani kwajin to lallai sai na sare kanka." Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya killata mahaifiyarsa aciki sannan yabi Babara. Babara yai dariya, "Kai sani cewa idan na bari mahaifiyarka ta rasu kona mutu sai Hidaya ta ƙara kashe ni." A wannan lokaci hankalin Armad ya dawo kan Hidaya, inda ya buɗe baki ya tambayi Babara, "Wai kana da tabbas yayata tana raye? Kakana ya kawo min takobin ta shekarun baya da suka gabata." Babara ya kyalkyala dariya yana mai kallon sama tare da cewa, "Kasan mai suke cewa yayarka a doron ƙasa ta farko? Hmmm.... Koda yake wasu suna cewa sunan ya samo asali ne daga jinsin Dordor wasu kuma suna cewa daga aljanun farko. Amma dai yayarka hatsabibiya ce ta rubutawa a jarida! Lallai baza ta mutu ta sauƙi ba, kuma idan ta mutu sai labari ya cika duniya." Armad ya haɗe gira, "Wanne suna suke gaya mata?" Babara yai murmushi gami girgiza kai, "Bari ta gaya maka da kanta idan kun haɗu." ________ Alhamdullh rabbil alamin. Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAH madaukakin sarki daya bani ikon kammala littafin farko na jerin littattafan Magajin wilbafos. Ina rokon ALLAH ya ci gaba da bani lafiya da ikon rubuta wannan littafi har zuwa karshensa. Godiya ta musamman ga dukkan makaranta Wanda suka kasance tare dani tun daga farko har zuwa karshe. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 63: Eyriyon Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos _____ *** Shekarar 1841 Bayan Amri, acikin garin Kanyu, Armad ne ke zaune shida kakansa Zaikid Wilbafos da Mahaifiyarsa da kuma yayarsa Hidaya a kewaye da teburin cin abinci suna cin abincin dare. Zaikid dai mutun mai yawan farin gashi da manyan gaɓɓai, kana ganinsa zaka san duk da shekaru sunja amma yana nan da jarumtarsa. Hidaya kuwa tana kama da Armad sosai sai dai cewa ita fara kamar mahaifiyarsu. Hidaya ta leƙa ta tagar dake dai-dai saitin ta sannan ta juyo ta dubi Armad tana cewa, "Kaga kai sauri ka cinye abincinka ka kwanta dare ya fara yi. Kalli kwanon kowa ya gama amma banda kai." Tundai fara cin wannan abincin Armad yake ta cakwala kuma yaƙi tsayawa yaci abincin. Hasalima da Hidaya tayi masa magana baima nuna yaji ba, kawai yaci gaba da abinda yake. Zaikid ya kalli Hidaya, Hidaya ta zare ido da sauri tana cewa, "Dattijo, bafa ninai girkin nan ba kake kallo na, abincin Mama ne baiyi daɗi ba shi yasa ƙani na yaƙi ci." "Hahaha..." Zaikid ya kyalkyala dariya yana ƙifta ido tare da satar kallon gefe. "Ƴata Fatima kinji dai me ƴaƴanki suke cewa! Wai abincinki baiyi daɗi ba!" Fatima dai irin matan nan ne fara re kyakyawa masu girman jiki. Sau da dama Zaikid yakan ce shi ta gado a girman jiki da kuma fari domin kuwa yana bada labari cewa matarsa, wato babarta, bata da girman jiki kuma baka ce wankan tarwaɗa kamar Armad. Fatima nada idanu dara-dara masu cike da ƙaunar ƴaƴanta guda biyu. Zaikid na kyalkyala dariya irin ta manyan mutane, Fatima na ɓata rai tana cewa, "Sa'a ta biyu cir ina wannan kirkin sannan ace baiyi daɗi ba. Ɗana Armad gayamin maiya hana ka ci." Armad yai shiru baice komai ba. Wasa kawai yake da cokalinsa yana kallon kasa. Hidaya taja kujerarta kusa dashi ta caka cokalinta akan naman dake kan kwanonsa sannan ta haɗa da wainar dake kan kwanon ta buɗe bakin Armad ta danna masa. "Cinye kaji ƙanina." Hidaya ta shafa tambarin Miyurar dake ɗamfare a goshin Armad tana mai cewa, "Indai kacinye gobe kafin na fita zan tashi dakai sama." "Nhi....fa bha tasshi nakeh so ba....." Armad ya furta bakinsa cike da abinci. "To mai kake so?" Armad ya ɗau lokaci ya haɗiye abincin a hankalin sannan yace, "Ina Abba?" Tambaya ce mai sauƙi amma duk ɗakin saida yayi tsit. Armad bai san mai yasa ba amma mahaifiyarsa da kakansa basa san zancen baban nasa. Nan take sukai kyaran murya suka fice daga cikin ɗakin suka bar Armad da Hidaya. "Indai ka cinye abincin nayi maka alƙawari yau zan gaya maka abu biyu ko uku a game da babanmu. Amma sai kayimin alƙawari baza ka ƙara yin maganarsa a gaban mama ba." Tana rufe baki Armad yai tsalle, fuskarsa cike da murmushi ya amsa wannan alƙawari. Cikin daƙiƙa kaɗan ya gama cin abincin. Hidaya taja shi suka fita ta bayan gidan suka zauna a gaban wasu tagwayen bishiyu suna suna kallon farin wata. Hidaya taja numfashi ta dubi Armad, wanda ke kallonta, ta fara da cewa, "Da tuni sunanka Eyriyon, Eyriyon Wilbafos. Ina tuno sanda Abba yace shi ne sunan da yake so a sa maka. Amma mama tace sunan baiyi ba, Armad Wilbafos take so." "Eyriyon??" Armad ya karkata kai, domin kuwa bai taɓa jin sunan ba. Hasalima sunan yafi kama dana mutanan da. Hidaya tace, "Eh... Amma dai abinda nake so ka riƙe shi ne Abbanmu yana sonmu sama da komai a duniya. Yama fi sonka akaina. Sannan kuma yana da rai kuma zaka ganshi indai muna raye. Armad...." Hidaya ta ɗan ja numfashi kamar tana kokwanton ta faɗi abinda ke ranta ko kuwa. Amma dai daga ƙarshe ta yanke shawarar ta faɗa, "Armad kasan mai ake cewa Zaɓi?" Armad ya kyaɗa kai, "Eh.. Shi ne kowa a bashi dama yayi abinda yake so?" Daga jin sautin Armad bashi da tabbas domin kuwa sautin yafi kama da tambaya a maimakon amsa. Amma yaci sa'a Hidaya ta kyada kai. "To mahaifinmu zaiso ace idan ka girma ka zama jarumi ko kuma wani jagora ko kuma mai yin doka, kada ka takurawa mutane akan abinda yake ba dole ba, ko kuma abinda yake ra'ayinka ne kawai. Zaiso ace kowa ka bashi zaɓi. Ka gane mai nake nufi?" Armad yai shiru idanunsa cike kokwanto. Lallai kallo ɗaya zakai masa kasan bai gane mai take nufi ba. "Hmmmm..." Hidaya taja dogon numfashi, "Ba sai ka gane yanzu ba, kawai ka riƙe kalmomin kuma ka tuno su anan gaba koda na mutu. Kaji ƙanina." Armad ya kyaɗa kai, sannan a lokaci guda fuskarsa ta canja domin kuwa baya so ko kaɗan yaji yayar tasa tana zancen mutuwarta, wanda kuma abu ne data saba. *** Shekarar 1854BA ____ Babara ya ja dogon numfashi gami da tafa hannunsa akan iska, lamarinda yasa iskar dake wajen ta kaɗa tare da yin ƙuwwa. Sannan ya juyo ya dubi Armad wanda ke tafe a gefensa, "Daga yau zaka iya kirana da Bóka, Boka Babara." Armad ya haɗe fuska cikin mamaki, "Bóka kuma?" Babara ya kyaɗa kai, "Boka shi ne sunan da ake kiran duk wanda yakai muƙamin sarkin duba." "Ohoo.." "Kakanka Zaikid yazo watanni kadan bayan ka tafi. Nayi mamaki da baka tambayeshi ba." Armad ya cake ƙafa a ƙas tare da tsayawa. "Ina sane dashi." Lallai bawai mantawa yayi da Zaikid ba sai dai kawai daman bai taɓa tsammanin zai dawo ya tarar da kakan nasa a gida ba. Abu ɗaya daya sani bayan sunyi magana dashi ta hanyar Ayrid a shekarun baya shi ne lallai Babara bai isa ya cutar da mahaifiyarsa ba, tunda kakan nasa zaije ya same shi. Armad ya ɗanyi shiru an ci gaba da tafiya sai kwatsam yai zumbur kamar ya tuno da wani abu, "To mai yasa shi ɗan tsohon baiyi mata maganin da kansa ba. Ai shima Wilbafos ne, kuma indai ni ko Hidaya zamu iya shima ya kamata ace ya iya." Babara yaja dogon numfashi, "To kai a tunaninka waye ya koyamin yadda zaka iya sarrafa idanunka. Nima ban san mai yasa yaƙi yi mata maganin ba, amma dai ya bar saƙo na baka sannan kuma ya ce na tambaye ka mai kake so ka cimma a rayuwarka bayan samarwa mahaifiyarka lafiya?" Armad yai shiru yana tunani naɗan lokaci kafin daga bisani ya kyaɗai yayi magana ƙasa-ƙasa, "Daman nasan ɗan tsohon nan zaiyi abinda yafi haka ma." "Me kace?" Babara baiji mai Armad yace ba. Armad ya kyaɗa kai, "Ba komai!Babban abinda nasa a gaba bayan samarwa mahaifiyata lafiya shi ne hana cinikin bayi. Kuma ina mai rantsuwa da mahaliccin ƙasa bakwai, saina hana cinikin bayi a doron ƙasa kafin na daina numfashi." "Hmmmm....." Boka Babara yaja dogon numfashi gami da kyaɗa kai. "Ruwa baya tsami banza. Jini kuma baya ƙarya. Da bakai haka ba da ba'ace kai jikan Wilbafos bane. Bari na tambaye ka, shin ka taɓa tunanin mai yasa mahaifiyarka ta hanaka gayawa mutane sunanka na wilbafos?" Armad ya girgiza, "Na sha yin tunani akai amma har yanzu bansan mai yasa ba." Babara yayi murmushi, "Ga dukkan alamu ƴan uwanka basa son gaya maka tarihinka. Amma kada ka damu yau zan gaya maka mai yasa akan hanyar mu kafin mu ƙarasa wajen da zaka fara karɓar horo." ______ Ku saurari chapter gobe. Sannan kuma ina buƙatar wasu daga cikinku su rinƙa yin comment a ɗaya group da nake sharing littafin domin sauran mutane sufi gani. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 64: Magajin wilbafos na farko Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Babara yai kyaran murya ya fara bawa Armad kaɗan daga cikin tsohon tarihin ƙasa bakwai, "Yau muna shekarar 1854 Bayan Amri(BA), kamar yadda ka sani Amri kalmar yaren Aldurish ce wadda take nufin saukar da mutane zuwa ƙasashen ƙasa. Al'ummar ƙasa bakwai suna da ilmi akan abubuwan da suka afku acikin wannan shekaru dubu ɗaya da tamanin na bayan Amri, amma kaɗan ne daga cikinsu suke da masaniya akan al'amuran da suka afku kafin Amri. Ni Boka Babara ina daga cikin waɗanda suka san kaɗan daga abubuwan da suka faru a wancan zamani domin kuwa an haifeni a shekarar 27 kafin Amri (KA). Wanda idan ka haɗa zaka ga shekaru na a yanzu sun kama 1881 da haihuwa. "Lokacin da aka haifeni lokaci ne mafi tsanani a tarihin ɗan adam. Lokaci ne na yaƙi, lokaci ne wanda ba'a taɓa samun irinsa ba a tarihi. Mahaifiya ta tana haifata aka biyo ta za'a kashe ta, kuma saboda ta ceci ni ta salwantar da rayuwarta ta hanyar bani dukkan ragowar shekarunta na Izza. Babana dama ya daɗe da mutuwa a filin daga. Babu kowa babu wanda na sani haka na rayu saboda shekarun Izza da mahaifiya ta barmin. Shin kasan menene ya jawo wannan yaƙi?" Armad ya girgiza kai, "A'a." Boka Babara yaci gaba da bayani, "Doron ƙasa ta farko ya kasanse bashi da sashin Ikwatora, amma a maimakonsa wani katafaren ruwa ne wanda ya raba ƙasar gida biyu. Wannan ruwa shi ake kira da Ruwan maliya. A shekarar 9541KA anyi wani sarki mai suna Aldaima Wilbafos wanda akafi sani da Wilbafos na farko. Aldaima shi ne mutun na farko daya taɓa mulkar dukkan doron ƙasa ta farko ɓangaren gabas da ruwan maliya, kuma ya haɗa kan dukkan ƙabilu a tafarki ɗaya. Aldaima ya rayu tsahon shekaru dubu shida zuwa shekarar 4033KA, inda bayan ya mutu ƙaninsa mai suna Eyriyon Wilbafos ya haye karaga kasancewar Aldaima bashi da ɗa. Eyriyon Wilbafos ya zama Wilbafos na biyu. Nima ba'a haifeni ba a lokacin kuma lallai bansan haƙiƙanin taƙamaimai mai ya faru ba, amma nasan cewa Ururu ƙabila ce wadda tafi kowacce girma a ɓangaren yamma da ruwan maliya. Kuma sarkinsu, Kuyurussa'ayi Ururu da ɗansa Dumaƙisu Dul'ururu Kuyurussa'ayi sune halitta ta farko da suka taɓa haye ruwan maliya suka shigo sashin gabas da ruwan maliya a shekarar 945KA. Wanda idan ka lissafa zaka ga bayan Eyriyon Wilbafos yayi shekaru sama da dubu uku kenan yana mulki. Kuma abin mamaki shima Eyriyon bai sami haihuwa ba har zuwa wannan lokaci. "Naji labari mutanen gabas da ruwan maliya basu karɓi Ururu ba, musamman saboda baƙaƙen idanuwansu, amma daga baya sarki Eyriyon yai magana aka daina kyamarsu. Shekaru ɗari biyar bayan Sarki Ururu ya bayyana a ƙasar gabas saiya fara kira izuwa tafarkin rukunai biyu. Wanda sune dai rukunan daka sani wanda ɗaya shi ne na Jinzidal, ɗaya kuma na Amri. A wancan lokaci ana kiransu da 'Amri da Jinzidal'. Bansan maiya biyo baya ba, amma dai nasan sarki Eyriyon ya nemi Ururu da su daina wannan tafarki ko kuma su koma inda suka fito. "Ururu sukai kunnen uwar shegu da wannan kashedi na sarki Eyriyon Wilbafos. Shekaru kaɗan bayan sunƙi sai Eyriyon ya kira kwamandojinsa guda ɗari dake ban ƙasa izuwa yaƙi da Ururu. Yaƙin da aka shafe shekaru ɗari uku ana yinsa. Yaƙin da yai sanadiyyar asarar sama da rayuka miliyan dubu a ban ƙasa. Bazan taɓa mantawa ba ina ɗan shekara ashirin da biyar saida takai duk wata ƙasa ta juye izuwa launin ja launin jini saboda tsabagen jini dake kwaranya. "Sarki Eyriyon kafin fara wannan yaƙi ya bar wasiyya a cikin wani sihirtacce littafi wanda akace ya juye izuwa takobi. Sannan ya aiki ɗaya daga cikin kwamandunsa da wannan littafi/takobi. "Wannan yaƙi dai kamar yadda ka sani Ururu ne sukai nasara kuma a sakamakon haka rukunai biyu wato Amri da Jinzidal suka kasance. Ina tunano lokacinda sarki Ururu ya kira wani ɗalasimi wanda yasa dukkan wani biladama wanda bashi da baƙin ido bacci. Wanda bayan mun tashi daga wannan bacci muka tsinci kanmu acikin duniyoyi shida na ƙasa. Shekaru kaɗan bayan munzo sarki Ururu ya aike da ruduna wanda suka zo suna binciken wannan kwamanda da sarki Eyriyon ya aiko. Naji daga baya cewa suna neman wani abu ne da Eyriyon ya bari mai suna Littafin-takobi. Amma dai ga dukkan alamu har yanzu basu samu wannan abu ba, domin kuwa har yanzu akwai tsofaffin ƙungiyoyi dake neman wannan abu mai suna Littafin-takobi. Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin duniyar ƙasa bakwai." Boka Babara ya daki ƙasa da sandarsa inda ƙoƙon ruwan ya bayyana. Ya kwankwaɗi ruwan sannan ya juyo ya dubi Armad wanda ke tsaye yana mamakin wannan tsohon tarihi da yaji. Ko a mafarki bai taɓa tunanin ƙabilarsa ta Wilbafos takai haka tsufa ba. Sannan kuma ga zancen Littafin-takobi, sai a yanzu ya gane dalilin da yasa Uznu Ururu yake matuƙar neman wannan littafi. Kuma Armad ya gano cewa indai har da gaske littafin ya narke a cikin jininsa to kuwa lalle bazai taɓa bawa kowa shi ba har sai yasan meye aciki. Armad ya tuna da zancen ɓacewar Miyurarsa wanda abu ne wanda har a wannan lokaci bai daina damunsa ba. Lallai ko a iya haka Littafin-takobi ya janyo masa masifu da dama kuma babu yadda za'ai ya rabu dashi ba tare da yaga abinda ke ciki ba. Muryar Boka Babara ita ce ta katse masa tunaninsa inda ya juyo ya kwashe duk labarin daya faru dashi akan Littafin-takobi ya gayawa Babara. Lalabarin da yasa Babara ya daɗe yana tunani wanda har suka iso inda zasu fara horon baice komai. Daga bisani Babara ya juyo izuwa Armad da murmushi yana mai cewa, "Ga dukkan alamu jininka na Wilbafos ba ƙarami bane. Amma lokaci ne kawai zai nuna, domin kuwa ba kai kaɗai ne jinin Wilbafos ba. Idan baka da wata tambaya zamu fara bayanin horo." Armad ya dubi Babara fuskarsa ɗauke da murmushin fahimta yana cewa, "wato idan na fuskanta a shekarun baya daka tambaye ni suna na tuni dama ka riga ka sani saboda kasan yayata Hidaya. To amma mai yasa ka turani nemo Tarifil-fakta indai burinka kawai na koyi horo ne? Ai akwai hanyoyi da dama wanda zan samu horo wanda basu kai wannan hatsari ba. Mai yasa?" Babara ya ƙara yin murmushi, "lallai kana da zurfin tunani. Wannan haka yake, akwai hanyoyi da dama wanda da naso da ban tura ka nemo Tarifil-fakta ba, to amma kada ka manta nasan cewa da Hidaya da Mahaifiyarka Fatima da kakanka Zaikid suna daga cikin wanda suka yadda Tarifil-fakta shi ne kaɗai mutumin da yasan yadda za'a sarrafa Littafin-takobi. Na tabbata wani daga cikinsu ya taɓa yi maka zancen neman Tarifil-fakta." Nan take Armad ya tuno da abinda mahaifiyarsa ta gaya masa akan neman Tarifil-fakta. Komai yanzu ya fara yi wa Armad ma'ana. Babara yasan iyalan gidan Armad sosai: yasan Fatima Wilbafos tana neman Tarifil-fakta kuma yasan neman da take masa yana alaƙa da Littafin-takobi, sannan kuma yasan Hidaya. Hakan nema yasa ya tura Armad nemo Tarifil-fakta. Babara ya daga ɗan-yatsa, "Amma dai duk da haka kada ka gayawa Hidaya halin daka shiga a yayin neman Tarifil-fakta, koba komai kaga ai yayi maka amfani ka samo Littafin-takobi. Ina roƙonka da koda na mutu kada ka gaya mata." Armad ya gwale ido cikin mamaki, "Koda ka mutu?" Babara ya girgiza kai, "Eh koda na mutu! Baka da labarin akwai wasu Rauhanan aljanu goma da suka yaudari Hidaya a shekarar 1801BA kuma suka sha guba suka mutu kafin ta kama su. Amma Hidaya ta kira taron aljanu tasa aka tashe su sannan ta ƙare kashesu ta mummunar hanya. Kasan sunan da suke gayawa Hidaya a tsakanin aljanu?" Idan Armad yana jin irin waɗannan maganganun a game da Hidaya sai yaji kamar ba yayarsa ba daya sani. Yai murmushi ganin yadda fuskar Babara ta fara canjawa, "Indai kana tare dani kada kaji komai, bazan gaya mata ba. Amma wanne suna suke gaya mata?" Wata dariyar mugunta tazo gefen fuskar Armad, lallai ya samo lagon Babara tunda dai ya gano abinda yake jin tsoro. "Ka ƙyale wannan sunan, idan kun haɗu ta gaya maka da kanta." Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 65: kasa bakwai Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Haka dai Armad da Babara suka ci gaba da tafiya sannu a hankali har zuwa faɗuwar rana. Mafi yawancin hirar tasu Babara ne yake yiwa Armad tambayoyi akan abubuwan da suka faru dashi a yayin neman Tarifil fakta. A dai-dai wannan lokaci ne suka fara hangen ƙatoton bangon ruwan nan wanda akewa laƙabi da bangon arewa. Babara ya tsaya tare da neman waje ya zauna a ƙasan wata bishiya. "Nayi wa kakanka Zaikid alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka ka taimaki mahaifiyarka, amma daga nan dani dakai zamu yi hannun riga. Saboda haka har zuwa wannan lokaci, Zaikid ya barmin amanarka a matsayin ɗalibi da malaminsa. Zanyi zaton ka bani irin girmamawar da kake bawa Zaikid a yayin da nake koyar dakai." Armad yayi murmushi. Dama dai shi Armad ba mutun ne mai raina manya ba, kuma koda Babara bai faɗa ba bashi da niyyar raina shi. Babara ya ƙara duban Armad, "Mai ka sani game da tsarin ƙasa bakwai? Ina so kayimin bayani dalla-dalla." Armad ya ɗanyi shiru yana kokwanton wacce alaƙa wannan tambaya take dashi akan abinda Babara zai koya masa, amma daga bisani ya yanke shawara yayi wa Babara biyayya kawai kada yace ya rainashi. "Ƙasashe bakwai sune kaɗai wajen da bil adama zai iya rayuwa aciki. Nasan waɗannan ƙasashe a jere suke ɗaya a saman ɗaya; daga doron ƙasa ta farko zuwa na bakwai. Nisan dake tsakanin wannan ƙasashe bazai misaltu ba, kuma haka ne yasa ƙasa ɗaya bata taɓa iya hangen wata ƙasar. Hasalima wata ƙasar baza ta taɓa sanin samuwar wata ƙasar ba idan banda kasancewar bangon ruwa wanda ya haɗe dukkanin wannan ƙasashe. Shi dai wannan bangon ruwa ya sakko ne tun daga doron ƙasa na farko har zuwa na bakwai, kuma tun a farkon lokaci yake tsaye a yadda yake bai daina zuba ba. Da dama daga cikin masana sunyi rubutu akan wannan ruwa da dalilin da yasa yake ta zuba amma yaƙi ƙarewa, sannan kuma wajen da yake zubar yaƙi cika da ruwa yayi ambaliya, amma har zuwa wannan lokaci amsar kawai da suka samo ita ce 'TSAFI'. Wato dai kowa ya yadda tsafi ne ke riƙe da wannan katafaren gangar ruwa wanda ake kira da BANGO." Armad yaja numfashi sannan shima ya nemi waje ya zauna a gefen Babara kafin daga bisani yaci gaba da bayani, "Ada bansan mai yasa ake cewa wannan ruwa bango ba, amma lokaci na farko dana fara ganinsa shi ne shekarar dana zo wajenka. Bayanda na tafi na haɗu dasu Nostajiya naga yadda ake ganin wannan gangar ruwa ya shafe ko'ina sannan yana ambaliya a tsaye cikin ƙasaita tamkar tamkar wani bangon duniya wanda bazai taɓa faɗuwa ba. Nan take na gane dalilin da yasa ake ce masa Bango. A sannanne na gano cewa ashe akwai Bango ɗaya a ɓangaren gudu ɗaya kuma a arewa: wadanda ake kira da bangon kudu da bangon arewa. Waɗannan bangwaye guda biyu sune suka datsa kowacce doron-ƙasa acikin ƙasashen nan guda bakwai izuwa gida uku: ɓarin arewa, ɓarin kudu, da kuma ɓarin tsakiya wanda shi ake kira Ikwatora. "Kowanne ɓari duniya ce mai zaman kanta wanda take ƙunshe da mutane miliyoyi. A kowanne lokaci na shekara ɓarin kudu suna da sanyi sosai kuna a sau da dama har ƙanƙara ke zuba, amma ɓarin arewa zafi ne dasu kaf shekara. Kakana Zaikid ya gayamin ɓarin Ikwatora sune suke da sanyi da zafi: rabin shekara ai zafi rabi kuna ayi ƙanƙara. "Akwai hanyoyi biyu kacal da bil adama suke iya yin safara daga wata doron ƙasa zuwa wata. Hanya ta farko ita ake kira da Eycigan, hanya ta biyu kuma hanyar jiragen ruwa. Eycigan kalma ce ta yaren Aldurish wadda take nufin gida. Kuma haka abin yake, Eycigan tsarin gidaje ne guda goma sha huɗu wanda aka gina su a kowacce tasha na ɗaya daga cikin doron ƙasashen nan bakwai. Babu wanda yasan yadda aka gina su ko kuma yadda suke aiki, amma indai ka biya kuɗinka ka shiga ciki to zaka bayyana a inda kake so. Bayanda ka buɗe min wannan ƙofa na shiga a shekarun baya na gano cewa Eycigan tana kama da irin wannan ƙofofi na tsafi da ake yawo ta ciki. Nostaljiya ma ta buɗe min wata a ƴan kwanakin baya. "Hanya ta biyu ita ce amfani da jiragen ruwa ayi tafiya daga ƙasa zuwa akan Bango. Amma duk da cewa hanyar Eycigan nada matuƙar tsada mutane sunfi amfani da ita saboda sharrin ƴan fashin ruwa da Dordor masu cin naman mutane da kuma lokaci da ake ɗauka a jiragen." Armad yai shiru yana jira Babara ya jinjina masa, domin a ganinsa babu wani abu daya shafi fasalin ƙasa bakwai da bai faɗa ba, amma Babara yai masa irin kallon nan mai nuna ana so kaci gaba. Armad haɗe gira, yaya za'a ce da saura. Babara ya kyaɗa kai, "Eh... bayaninka yayi to amma baka faɗa min yadda ake safara daga wani ɓarin zuwa wani ba akan doron ƙasa ɗaya. Wato dai ina so naji yadda zaka iya ketawa daga ɓarin arewa zuwa ikwatora zuwa kuma ɓarin kudu duk akan doron ƙasa ɗaya? Kai sani cewa hatta gidajen Eycigan da ƙofofin daka ga muna buɗewa basa iya kai mutun daga wani shashi zuwa wani." Nan take Armad gwale ido cikin mamaki. Bai ma taɓa tsayawa yayi wa kansa wannan tamabaya ba. Duk a tunanin Armad tafiya daga doron wata ƙasa zuwa wata shi ne mai wahala, amma tafiya daga wani sashi zuwa wani ba zaiyi wahala ba. Armad ya gurgiza kai, "Ban sani ba gaskiya." Babara yayi murmushi, "To wannan shi ne dalilin da ya na tambaye ka bayani akan doron ƙasa bakwai, domin najin ko kasan irin haɗarin da zaka shiga nan bada dadewa ba." "Hatsarin dazan shiga kuma?" Armad ya kasa yin shiru. Babara yayi kamar baiji tambayar Armad ba yaci gaba da maganarsa, "Ketawa ta cikin Bango wani babban abu ne wanda hatta manyan ma'abota Izza suke jin tsoro. Kai sani cewa Bangon arewa dana kudu suna da girma sama da yadda kake zato ko tsammani, kuma acikin su akwai sharrika wanda kaɗan ne daga cikin biladama suka taɓa gani ko ji. Ina daga cikin wanda suka yadda cewa duniyar dake cikin Bango ita ce waje mafi hatsari a duniya. Dani dakai zamuyi tafiya acikin wannan waje, kuma aciki zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka. Kai sani cewa sau ɗaya kacal na taɓa iya keta rabin wannan waje. Lallai dani dakai duk zamu iya halaka, amma na riga nayi wa kakanka alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwa ka, kuma lallai mu ƴan ƙabilar Bayajidda bama saɓa alƙawarinmu." _______ 1) Na ɗan samu free time, so zaku ga post ya ƙaru amma fa ba cewa nayi zai ɗore ba. Saboda kada kuga daga baya mun koma yadda muke yi da. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna

Chapter 4 of 13