Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 13
haka ne, idan ɗalasimi guda ɗaya ya wutar dashi rabin hanya an watsoshi waje, to idan yayi amfani da ɗalasimi goma a lokaci ɗaya zai iya wucewa. Daɗin daɗawa wannan sabuwar fasaha ta Armad zata bashi damar cin galaba akan abokan fafatawarsa cikin sauƙi. Domin kuwa komin sharrin daya tunkaro shi zai iya ɓacewa ya dauje masa. Sannan zai iya bayyana a bayan abokin fafatawarsa ya aiwatar da harinsa ba tare da an ankara ba. Armad yayi niyyar sakawa wannan fasaha sabon suna amma daga ƙarshe ya yanke shawarar yaci gaba da kiranta da Kaban'shìsu. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 89: Hannun Aradu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Armad na tafe yana goge takobinsa, rabonsa da amfani da takobi an kwana biyu. Kai hatta harin ƙawanyar-walƙiy a an daɗe rabonda yayi amfani dashi. A iya tunaninsa tun bayan fafatawarsa a gasar Jinzidal. A halin yanzu hannunsa ƙaiƙayi yake, saboda haka maimakon ya kewaya ya zagaye wannan daji sai ya yanka ta tsakiyarsa. Ai kuwa ko taku goma bai yiba Dordor uku masu kai ɗai- ɗai da wasu aljanun-shirwa guda biyar suka tunkaro shi. Dordor suna kawo masa hari ta ƙasa, shirwa na kawo masa hari ta sama. Armad yai murmushi tare da dunƙule hannunsa na dama. Sannan ya juyarda dashi izuwa walƙiya ya daki iska dashi yana cewa, "HANNUN-ARADU." Haka na faruwa wata farar walƙiya mai layin kore-kore ta fara ɓulɓula daga hannunsa tare da afkawa wannan shirwowi da Dordor. Wannan shi ne karo na farko da Armad yayi amfani da wannan fasaha mai suna Hannun- aradu, wadda ta banbanta matuƙa da ƴar walƙiƴar daya saba amfani da ita ada. Idan ka kalli dunƙulen hannunsa na dama zaka ga ya juye izuwa walƙiya sannan kuma walƙiya tana ɓulɓula daga cikinsa tamkar ana ambaliyar ruwa. Duk abinda wannan walƙiya ta taɓa saita narkar. Babu wani abu dake tsaye a gabanta face Armad Wilbafos. Bayan daƙiƙa bakwai Armad ya saki hannunsa ya ɗauke walƙiyar sannan yai duba izuwa abinda ya aikata. Dukkan abubuwan dake gabansa sun ƙone ƙurmus, babu shirwa babu Dordor babu koda bishiyu da suka rage. Babu komai sai ƙarfin izzar Armad wilbafos. Wannan daji ya ƙone ƙurmus tamkar ba'a yishi ba. Daga inda Armad ke tsaye yana hango Bango. Armad yai murmushi tare da tunkararsa. Tuni dai ya gano wata hanya da zaiyi amfani da ita domin ƙirƙiro sabuwar fasahar takobi amma ba sauri yake ba zata iya jira. Saboda haka ya tunkari wannan Bango gadan-gadan. Yana isa ya juye izuwa walƙiya sannan ya kira ɗalasimin Kaban'shísu. Armad ya tsinci kansa a tsakiyar wannan ruwa mai kauri wanda ke narka jikin ɗan adam. Yana bayyana ya ƙara ido biyu da wannan baƙaƙen idanuwa na Ururu. Amma tuni Armad ya shirya musu, kafin wani abu ya faru tuni ya ƙara kiran wani ɗalasimin, ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaba da inda yake. Wannan idanu suka ƙara bayyana suna neman haɗiye amna Armad ya ƙara ɓacewa da taimakon sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu. A haka saida Armad yayi amfani wannan ɗalasimi sau goma, a kowanne lokaci yana ƙara kusantar ƙofa amma wannan idanu suna ƙara cimmasa. Armad yasan iyakacinsa ɗalasimi goma, kuma indai ya wuce haka to a take zai fara aman jini ya sume. Amma babu yadda zaiyi, baiyi tunanin ɗalasimi goma baza su isa ba. Saboda haka ya rufe ido ya ƙara kiran wannan ɗalasimi a karo na goma sha ɗaya. Abun mamakin shi ne duk da yana walƙiya amma hakan bai hanashi aman jini ba da jin zafi da radaɗin wannan ɗalasimi ba. Gabda Armad zai sume ya ga wani haske ya rufe masa ido, bashi da tabbas mene ne amma yana fatan hasken fita daga kurkukun ne. ** A can doron ƙasa na farko kuwa wannan sarewa dake gadin wannan kurkuku ce ke ƙara bada labarin wani mai ƙoƙarin ficewa daga cikin kurkuku. Amma a wannan karan ya samu damar fita, sannan kuma abin mamaki irin ruhi ɗaya ne sak da wancan mutun da yayi ƙoƙarin fita a watan baya. Nan take wannan sarewa ta bada umarnin ayi maza-maza a kamo wannan mutun sannan a gane mene ne alaƙarsa da wancan mutun da yayi ƙoƙarin guduwa a watan baya. Shin duk mutun ɗaya ne bai mutu ba ko kuma wani ne mai irin ruhinsa. Gidan Uznu Ururu shi ne gidan da aka ɗorawa alhakin kamo wannan fursuna. ** Al'ada ce sananniya kwararrun matuƙa jirgin ruwa sukan sakawa jiragensu sunaye. Wani suna kawai na sha'awa ne wani kuma yakan dace da tsarin jirgin. A dai-dai wannan lokaci wani madaidaicin jirgin ruwa ne ke tafiya akan Bangon arewa ya nufi doron ƙasa ta huɗu, daular Sisiya. Sunan wannan jirgi Fataken-dare. Yakan ɗauki jama'a aƙalla ɗari biyu da hamsin zuwa ɗari uku, kuma shaidar safararsa tana tsakanin doron ƙasa ta uku data huɗu. Duk da kasancewar yawan ƙofofin Eycigan da ake tafiya ta cikinsu amma duk da haka masu sana'ar jirage basu rasa abinci ba, indai ka yiwa jirgin ka shaidar kariya ta hukumar tafiye-tafiye ta sarakunan jinzidal to zaka samu fasinja. Rashin yin shedar na nuna kana daga ɓata gari ku kuma ɓarayin ruwa. Jirgin Fataken-dare na tafiya sannu a hankali iska na kaɗashi izuwa hanyarsa. Fasinjojin wannan jirgi na harkokin gabansu cikin kwanciyar hankali, sun san nan da wata ɗaya mai zuwa zasu isa garuruwansu a daular Sisiya. Shi kuwa kyaftin ɗin wannan jirgi sunansa Bisaiya Sisiyu. Asalinsa ɗan daular Sisiya ne kuma tunda ya taso yake yin sana'ar kwandasta a irin wannan jirage, yanzu gashi a ɗan shakara talatin ya mallaki nasa jirgin. Duk da bashi da izza amma yana da ma'abota izza guda shida dake aikin tsaro a jirginsa. Kuma ko a wannan lokaci mutun biyu daga cikinsu na tare dashi. Bisaiya ya dubi ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ce, "idan iska ta bamu dama nanda kwanaki ashirin zamu isa. Shi yasa dole saina ɗauki ma'abocin aljanin iska aiki." Mutumin sanye da fararen kaya ya gyaɗa kai yana cewa, "gaskiya ne, kyaftin Bisaiya. Amma duk da haka ina tunanin zamu isa a yadda muka tsara." Bisaiya baice komai ba, kawai yaci gaba da kallon gangar ruwan dake gabansu. Yana sane da cewa ƙaro wani ma'aikacin dole zai jawo ya kori ɗaya daga cikin ma'aikatansa shida dan bazai iya biyansu ba, amma dole yana buƙatar wanda zai ringa ɗaure masa 'iska' a yayin tafiyarsu. Yana cikin wannan tunani ne sai ya hango wani abu kwance a gaban jirginsu. Abun yana ta iyo yana sama da ƙasa kamar ƙirgin itace. Da farko Bisaiya bai ɗauki wani abu ba saida yaga abin yana motsi kamar ɗan adam. Nan take ya haska fitilar jirgin saitin abun domin ya tabbatarwa da idonsa. Ai kuwa wani saurayi ne kwance a sume ba kaya a jikinsa. Abu na farko daya fara zuwa ran Bisaiya shi ne wannan ɗaya ce daga cikin dabarun ƴan fashin ruwa. Domin ka tsaya ceto suyi maka fashi. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 90: Sa'a ko Kaddara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** "Ɗakko shi." kyaftin Bisaiya ya umarci ma'aikacin dake gefensa daya ɗakko gangar jikin wannan saurayi dake yawo akan ruwa. Ba jimawa aka shiga da wannan saurayi cikin ɗakin duba marasa lafiya na jirgin tare da kirawo wani siririn mutun sanye da fararen kaya ya dubashi. Idan kayi duba izuwa wannan saurayi zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos. Shi kansa kyaftin Bisaiya bai san mai yasa ya ceto shi ba, duk da kuwa yana tunanin ƴan fashi. Amma koda yaga Armad sai ya zare ido cikin mamaki tare da fara tunanin mai ya kamata yayi. Abin mamaki duk da Armad na numfashi amma sun kasa farkar dashi. "Ransa yana hannun ALLAH. Amma tashinsa zaiyi wahala." Likitan ya bayyana wa kyaftin Bisaiya bayan yayi iya yinsa ya kasa. A kwana a tashi saida Armad yai sati ɗaya cir a sume kafin ya farka. Bayan ya buɗe ido ya fara ganin dishi-dishi kafin daga bisani ya warware ya fara jin surutan fasinjojin jirgin suna tattauna rayuwa. Armad ya daddagira ya sakko daga kan gadon inda ya nufi bakin ƙofa. Jikinsa na nan yadda yake babu gajiya ko tsami. Yana isa ya buɗe ƙofar, hasken rana ya haske masa ido lamarinda yasa ya kare da hannunsa. Iska mai ɗumi ta daki fuskarsa lamarinda ya gano lallai ya rabida wancan sanyi da ƙanƙara na cikin kurkuku. "Kunga ya farka... " "Ashe zai rayu.." "Yana da ƙarfin ruhi..." "Kai yaushe rabon da naga wanda yai sati a sume kuma ya rayu.." "Ko maiya sameshi?" Haka dai Armad ya fara tsintar maganganu fasinjojin daga nesa. Ga dukkan alamu kowa ya san da zuwansa. Armad ya gano cewa ɗakin cin abinci ya buɗe bayanda ya fuskanci cewa jama'ar na zaune a zagaye da tebura na abinci. "Koma ka kwanta karka faɗi.." Likitan jirgin ya tallafi Armad ta gefe. Abinda bai sani ba shi ne Armad tar yake jinsa kamar ya rungumi zaki. Juyewar jikinsa izuwa walƙiya yana bashi damar shanye gajiya da ciwo cikin ƙanƙanin lokaci. Armad ya dubi likitan ya ce, "Ehmm... Nagode amma naji sauƙi. A ina nake?" Likitan ya amsa da cewa, "kana cikin jirgin Fataken-dare, muna hanyar zuwa doron ƙasa ta huɗu daular Sisiya." Armad najin wannan jawabi yai murmushi tare da cewa, "Sa'a ko ƙaddara?" Likitan bai gane mai Armad ya ce ba saboda haka ya tambaya, "Sa'a ko ƙaddara? Mai kake nufi?" Armad ya amsa da cewa, "Ba komai. Kawai dai nima hanyar Sisiya nayi, ban sani ba ko zaku taimaka ku isar dani domin bani da ko sisi tare dani amma idan muka isa akwai wacca zata ranta min na biya ku." Koda jin wannan batu sai Bisaiya ya taso a fusace, "Da kuɗinka nake buƙata da ban ceto ka ba. Kai dai kawai ka samu sauƙi kurum." Armad na ganin Bisaiya ya gane shi ne kyaftin din wannan jirgi. Saboda haka yai shiru yana kai-komo da karamcin da Bisaiya yake nuna masa a zuciyarsa kafin ya kyaɗa kai cikin murmushi yana godiya. "Nagode." "Zo ga abinci." Bisaiya ya kira Armad izuwa teburinsa. Tuwo da nama haɗe da kifi soyayye sune cike a kwanon da aka turowa Armad. Cikin annushuwa ya fara danna tuwon nan yana korawa da sanyayyar fura samfurin daular Sisiya. Kowa idonsa na kansa amma ko a jikinsa. Kan kace meye wannan tuni ya gama da kwanukan dake gabansa. "Bari a ƙaro ma, lallai yunwa kake ji." Bisaiya yai odar wasu kwanukan. Armad baice a'a ba, koba komai baya so mutanen wannan jirgi su fara yi masa kallon aljani wanda baya buƙatar abinci. Bayan ya ci ya sha sai Bisaiya ya kaishi wani ɗaki domin ya huta. "Ga ɗakinka kafin mu ƙarasa. A lissafi na nanda sati biyu zuwa uku zamu isa." Armad yai godiya, har ya doshi ɗakin saiya waiwayo ya dubi Bisaiya yana cewa, "baza ka tambaye ni daga ina na fito ba. Baka tsoron ɓarayin ruwa ko kuma na jawo muku wata matsalar?" Bisaiya yai murmushi, "Tuni nasan ko kai waye, Armad Wilbafos. Amma ka kwantar da hankalin ka babu wanda ya gane ka acikin fasinjoji na." Nan take Armad yaja da baya ido a zare yana cewa, "mai kake nufi? Ya akai kasan suna na?" Bisaiya ya kada baki ya ce, "Kada ka manta hotunan ka sun baza ko'ina. Kuma duk wanda ke karanta jarida yasan fuskarka. Saboda haka nasa likita na yaɗan kyara maka hanci da baki da ido." Yana magana ya nunawa Armad mudubi. Abu na farko da Armad ya gani shi ne hancinsa ya loma ciki sannan ya gajarce kamar na biri. Idanunsa sun futo waje sun zama manya-manyan kamar na masu maƙoƙo. Sannan bakinsa ya ƙara faɗi kamar an yaga. Kalmar farko data zo bakimsa zagi ne amma ya fasa, "Kut... wa yasa ku mai dani haka?" Bisaiya ya dubi Armad babu alamun wasa a fuskarsa, "Idan ban maida kai haka ba ya zanyi da fasinjoji na idan suka gano akwai Ayrid miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar acikin jirgin?" Armad yai zumbur ya buɗe baki kamar wanda wani abu ya faɗo masa, "Idan haka ne to mai yasa kai baka miƙa ni ba? Ko kana jira ka isa gaɓa ne ka miƙa ni?" Bisaiya ya amsa da cewa, "ba zance maka ka yarda dani ba, amma nayi maka alƙawarin baza ka samu matsala daga jirgi na ba. Shekarar mahaifina bakwai a kurkuku yanzu, saboda an saka kuɗi akansa akan abinda bai kai ya kawo ba. Kaima ina da yaƙinin ba wani abu ka aikata ba aka dora wannan kudi akanka. Kawai dai ana so a wanke gimbiya Nostaljiya ne a ɗora maka laifi saboda kai baka da galihu. Idan baka yadda dani ba zaka iya sauka a kowanne lokaci." Yana rufe baki ya juya ya bar Armad a tsaye a wajen. ________ Shuraih 99% . Ai tunda aka ce za'abani Gimbiya Zahra (Nostolgiya Nara) na kidime kuma zan jajirce matuka wajen sambado maku da littafin nan har karshe, Sai ku jirani zuwa MAKO mai zuwa ta yiwu ma ku jini Gobe, amma fa sai na ga Respond naku akan wayannan MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 91: Gashin Belbela Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Kwanan Armad shida acikin wannan jirgi yana ta kai- komo da abubuwan dake ransa. Abu na farko gaskiyar mutanen cikin wannan jirgi, zai iya amince musu ko kuwa. Abu na gaba mai zaije ya tarar a daular Sisiya. Tunda Armad yake bai taɓa saka ƙafa a babban birnin ɗaya daga cikin garuruwan sarakunan Jinzidal ba, saboda haka bai masan mai zai tarar ba. Yaya yanayin garin yake? Shin wacce irin karɓa Nostaljiya zata yi masa? Abu ɗaya da yake da tabbas dashi shi ne mahaifin Nostaljiya Bihanzin mai dauwamammen sara bazaiyi murna da ganinsa ba. Ko a gamuwarsa ta farko kuma ta ƙarshe guduwa yayi dan kada su haɗu. Duk da Armad bai ga laifin Bihanzin wajen ƙoƙarin kare ƴarsa ba amma yana jimamin haɗuwa dashi. Musamman duba da cewa wannan shi ne karo na farko da zai gamu da Sarkin Jinzidal. Sannu a hankali Armad yaci gaba da gudanar da ragowar kwanakinsa acikin wannan ɗaki da Bisaiya ya bashi. Lokuta kaɗan yake fita yaga hasken rana saboda baya so wani acikin jirgin ya gane shi. A rana ta bakwai yana kwance akan gado yana tunanin yadda rayuwarsa take kasancewa sai kurum ya fara jin hayaniya daga waje. Da farko Armad yayi tunanin fasinjojin ne ke caca kamar yadda suka saba, amma ba jimawa ya gane cewa hayaniyar tafi ta haka. Bayan ya ɗauki daƙiƙa ashirin yana nazarin hayaniyar saiya fuskanci ƙaraji ne kawai da ƙuwwa. Nan take Armad ya yasan faɗa ake. Kodai ƴan fashi sun kawo musu hari ko kuma faɗa ya kaure tsakanin fasinjojin jirgin. Koma dai wanne ne bai shafi Armad ba. Koda ƴan fashi ne, kowanne jirgi yana da dabarun kare kansa daga irin haka. Rufe idonsa kawai yayi, yaci gaba da nazarin yadda zaiyi ya gamu da Nostaljiya zarar ya isa daular Sisiya. Abu kamar wasa sai Armad yaji ihun ya fara raguwa, lamarinda yasa yayi tunanin cewa anci galaba akan ƴan fashin. Amma kuma wata zuciyar ta gaya masa cewa lokacin yayi ƙaranci ace har an gama da ƴan fashin. "Hmmm..." Armad yaja dogon numfashi tare da girgiza kai. Bai san mai yasa ba amma hankalinsa yaƙi kwanciya, saboda haka ya rufe idonsa ya fara laluben yanayin-izzar ma'aikatan jirgin. Nan take ya miƙe zumbur ya nufi ƙofar ɗakinsa. Yana buɗewa wani koren hayaƙi mai ratsin yalo yai masa sallama. A ƙasan hayaƙin mutane ne fululu a kwance sun sume. Armad na ganin haka ya gane maike faruwa. Wannan hayaƙi guba ne kuma shi ne dalilin suman mutanen cikin jirgin. Koma waye ya feso wannan hayaƙi ba abokin Armad bane. Armad ya riƙe numfashinsa tare da tsayawa, tsaiwa irin ta ma'abota izza, sannan kai tsaye ya afka cikin hayaƙin. Bayan kimanin taku uku sai ya tsaya ya buɗe bakinsa ya huro iska waje. Amma maimakon iska sai feshin walƙiya ya fara ambaliya daga bakinsa. Kan kace meye wannan tuni feshin mai ɗauke da walƙiya ya kawar da wannan hayaƙi. A wannan lokaci Armad ya gane ashe wani ƙaton jirgin ruwa ne ɓoye cikin duhu a gaban jirginsu. Girman jirgin yasa jirgin su Armad ya zama kama wani ɗan kwale- kwale. Daga inda Armad ke tsaye yana hangen sunan jirgin ansa GASHIN-BALBELA da manyan baƙi. Armad ya dawo da hankalinsa kan mutanen da ke cikin jirginsa. Da yawansu wannan hayaƙi yasa sun sume, amma wasu na tsattsaye. Ga dukkan alamu hayaƙin bacci kawai yake sawa kuma rayuwarsu bata cikin hatsari. Har Armad zaiyi ajiyar zuciya ya godewa ALLAH saiya hango Bisaiya kwance cikin jini riƙe da ƙirjinsa. Ƙarshen kibiya ya leƙo ta gaban ƙirjinsa. Dukkan ma'aikatan tsaron su shida na kewaye dashi suna ƙoƙarin taimakonsa. Armad na shirin ƙarasawa ya bada nasa agajin yaji murya daga cikin Gashin-balbela. "Ku bamu dukkan kayayyakin ku da makaman ku idan kuna so ku tsira da ranku." Kyaftin ɗin jirgin shi ne yai wannan kashedin, amma a bayansa akwai ma'abota izza guda goma sha bakwai. Babu ko tantama jirgin ɓarayi ne domin ko fasinja ɗaya babu acikinsa. Armad ya dubi ma'aikatan jirginsa guda shida yaga dukkaninsu sun cika da tsoro, babu ko alamun kwarin gwiwa a tattare dasu. Ya juya izuwa ragowar fasinjojin da bacci bai ɗaukesu ba yaga tuni wasu daga cikinsu sun fara tattaro ragowar kayayyakinsu da niyyar miƙawa wannan ƴan fashi. Ana haka Armad ya lura da wani jarumin saurayi tsaye akan Bisaiya riƙe da takobi, idonsa babu ko alamar tsoro. Cikin ƙiftawar ido Armad zai iya ƙarar da wannan ƴan fashi amma mutanen jirginsa zasu gane waye shi, wanda kuma hakan zai jawo masa matsaloli da dama a yayin tafiyarsa. Daɗin daɗawa wannan ƴan fashi basu cancanci ya kashe su ba indai ba wani suka taɓa ba, sannan kuma fasinjojin jirginsa sun yadda da sharaɗin ƴan fashin. Wasunsu tuni sun fara haɗo kayansu. Armad ya yanke shawara maimakon yaƙar wannan ƴan fashi kamata yayi ya fara ƙoƙarin ceto rayuwar kyaftin Bisaiya. Saboda haka ya nufi inda yake. Yana isa ya fuskanci cewa wannan kibiya a kusa da zuciyar Bisaiya ta cake, lallai ana taɓa ta zai rasa ransa. Duk ƴadda akai hayaniyar farko daya ji ƴan fashin ne suka fara yi musu sallama da kibbau kafin su aiko wannan hayaƙi maisa bacci. Kala-kalar tunane-tunane suka fara yawo a zuciyar Armad. Akwai tausayi na mutumin daya taimakeshi, akwai kuma haushi na wannan ƴan fashi. Ana haka Armad yaji wannan saurayi dake riƙe da takobi yayi ƙaraji ya afkawa Gashin-balbela. Wuta ce mai ruruwa tayi tsiri ta tsinin takobinsa ta daki akalar Gashin- balbela. Nan take wajen da wutar ta daka ya tsage, jirgin ya fara ƙara zai fashe. Ana cikin haka ɗaya daga cikin jaruman dake cikin Gashin-balbela ya tafa hannunsa, ya samarda wata ƙanƙara wadda ta ɗinke wajen daya tsage. Sadaukin ya ƙara tafa hannunsa ya samarda ƙatoton mutun-mutumin ƙanƙara wanda ya aikawa saurayin da saurin gaske. Kafin saurayin yai wani abu ƙanƙanra tayi masa akwati. Armad ya lalubi izzar wannan saurayi yaji hamsin da ɗaya ce kamar tasa a lokacin daya fita daga gida. Shi kuwa ma'aboci ƙanƙarar izzarsa shekaru ɗari da sha bakwai ce. "Yaro kayi ganganci. Babu wanda ya isa ya kwana da rai bayan ya taɓa min Gashin-balbela." Kyaftin ɗin jirgin Gashin-balbela ya gayawa saurayin. Kafin ya juyo ga mutumin dake gefensa. "Kawo min kansa." Mutumin yai tsalle ya diro cikin Fataken-dare. Sannan ya zare takobi ya nufi saurayin da niyyar sare masa kai. A wannan lokaci ne Armad yai tsawa mai tsananin firgitarwa daga yake zaune. Abin mamaki Armad bai ɗaga muryarsa ba, amma babu wanda baiji tsawar ba har cikin ransa, musamman mutanen cikin Gashin-balbela. Nan take wannan sadauki daya tunkaro saurayin ya tsaya cak a inda yake, kafin gumi ya fara keto masa. A hankali ya ɗaga kansa cikin tsoro yai tsinkaye da ma'aboci wannan tsawa, lamarinda yasa ya fara karkarwa kamar wanda aka jefa tubalin ƙanƙanra acikinsa. Armad yakai ƙololuwar ɓacin rai, kuma tuni ya yanke shawarar nitsar da Gashin-balbela. Ya dubi wannan sadaukin dake ƙoƙarin kashe saurayin ya kirawo ɗaya daga cikin kalaman izzarsa, "Sanyin-babban-sihiri!" Nan take ƙanƙara ruwan toka ta haɗiye sadaukin. Armad ya nunashi da ɗanyatsansa, lamarinda yasa ƙanƙarar ta tamke shi tamau kamar zata fasa ƙasusuwansa. Kan kace meye wannan ya faɗi ƙasa sumamme. Armad ya dubi kyaftin ɗin Gashin-balbela ya ce, "idan kana so ka tsira da ranka, toka koma inda ka fito. Amma kayi sani cewa anan zaka bar wannan jirgin naka." **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 92: Maikiro Inara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Armad bai jira amsar ƴan-fashin dake cikin jirgin Gashin- balbela ba ya wuce izuwa wannan saurayi ya rusa akwatin ƙanƙarar daya rufe shi. Sannan ya juya izuwa jirgin dake gabansa. Kyaftin ɗin cikin jirgin, wanda ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce shi ne ya bada umarnin a kashe wannan saurayi saboda ya taɓa masa jirgi, shi ne ya fara yin tsalle ya afka cikin ruwa. Kafin daga bisani sauran ƴan fashin su bishi. Lallai duk wanda ya rayu a wannan zamanin yasan menene sanyin-babban-sihiri, babu ko tantama akwai ratar izza mai yawan gaske tsakanin mutumin da yake iya sarrafa sanyin-babban-sihiri da wanda bai iya ba. Armad yai ajiyar zuciya sannan ya juya izuwa kyaftin Bisaiya, a lokacin ne ya gane cewa dukkan mutanen dake cikin jirgin kallonsa suke kamar wanda suka ga wani mala'ika. Kowa ƙoƙari yake yasan wane ne shi. Kasancewar Armad yana iya sarrafa sanyin-babban-sihiri hakan na nuna yakai aƙalla izza shekaru dubu ɗaya, wanda hakan ke nuna Armad ya futo daga ɗaya daga cikin manyan dauloli biyar na ƙasa bakwai. Domin kuwa bawai abu ne mai sauƙi ba ka samu wanda shekarun izzarsa suka kai dubu, saboda duk hanyoyin da ake iya samun izzar da takai dubu hanyoyi ne wanda zaiyi matuƙar wuya wanda baya cikin wannan dauloli ya samu. Koda isar Armad saiya tarar Bisaiya na kakarin mutuwa, inda yana ganinsa yayi masa manana jini na fita daga bakinsa. "K....kayimin abu ɗaya badan na... isa.. ba." Armad ya riƙe hannunsa cikin tausayi. Bai san mai Bisaiya zaice ba amma kawai ya kyaɗa kai. Bisaiya ya ɗaga ɗan-yatsansa da kyar yai nuni izuwa wannan jarumin saurayi ya ce, "Ka kularmin da ɗana." Armad najin haka ya zare ido cikin mamaki da al'ajabi. Tun farko dai bashi da masaniyar Bisaiya nada ɗa, sannan kuma shi kansa wahalhalun kansa sun masa yawa ballanta ace ya kula da wani. To amma a halinda Bisaiya ke ciki na gabda mutuwa babu yadda za'ai yace masa a'a. Daɗin daɗawa kafin Armad ya gama tunani yaji kakarin da Bisaiya ke yi ya ƙaru, kafin daga bisani ya faɗi matacce. Armad na ganin Bisaiya ya mutu ya canja shawara yai tsalle ya faɗa cikin ruwa yabi wannan ƴan fashi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya dawo dasu a ɗaure cikin igiya. Wannan saurayi na zaune a gefen Bisaiya yana hawaye. Sauran ma'aikatan cikin jirgin duk kuka suke, kana gani kasan sunji daɗin aiki da Bisaiya. Duniya budurwa wawa, yanzu kake da rai in anjima babu. Waye zai taɓa tsammanin Bisaiya wanda ke da cikakkiyar lafiya ƴan daƙiƙu da suka wuce zai faɗi matacce yanzu. Su kuwa sauran fasinjoji wanda ke kwance a sume sun fara farkawa, abu na farko da suke iskewa shi ne gawar Bisaiya. Nan take Armad yasa aka rataya igiya a wuyan dukkan ƴan-fashin goma sha bakwai. Sannan ya dubi wannan saurayi ya fara bayani. "Wanda ya kashe wani shima kasheshi za'ayi. Idan kana so ga igiya." Armad ya miƙawa saurayin igiyar dake hannunsa wadda ana janta zata ƙarasa rataye ƴan-fashin. Babu wani kokwanto wannan saurayi ya miƙe ya nufi inda Armad yake ya karɓi igiyar dake hannunsa. Idanuwan wannan ƴan-fashi suka zazzaro cikin tsoro, sun san cewa rayuwarsu na gab da ƙarewa. Wasu daga cikinsu suka fara roƙon yafiya wasu kuma suna jiƙa wandonsu. Wannan saurayi ya ja igiyar ya rataye su. Da dama daga cikin fadinjojin kasa kallo sukai suka koma ciki. Amma Armad da saurayin da ma'aikatan cikin jirgin na tsaye suna kallon har ƴan-fashin suka gama harɗe- harɗensu suka mutu. Armad ya jefa gawarwakinsu cikin ruwa sannan ya bada umarnin ayiwa Bisaiya wanka. Bayan Armad ya tambayi ɗaya daga ma'aikatan jirgin akan al'adun ƙabilar da Bisaiya ya fito daga ciki ta fannin binne mamaci saiya fuskaci cewa ƙonawa suke sannan su jefa acikin ruwa. Armad ya tambayi saurayin idan akwai abinda yake buƙata ko kuma wani canji da yake so ayi wajen binne mahaifinsa, saurayin ya amsa da a'a. Sun samu dukiya mai yawa acikin jirgin Gashin-balbe wanda hakan ke nuna ba ƙananan ƴan fashi bane aciki. Daga ƙarshe suka zaɓi suci gaba da tafiya acikin jirginsu domin girmamawa ga Bisaiya. Kwanaki uku akai ana jimami acikin jirgin Fataken-dare kafin Armad ya samu damar tara kowa ya fara yi musu bayani cikin tattausar murya mai cike da kwarjini. "Marigayi kyaftin Bisaiya shi ne wanda ya ceto ni daga cikin ruwa yayimin maganin ciwuka na a lokacinda bai sanni ba. A lokacin rayuwarsa ya kasance jarumi ne mara tsoro, domin kuwa baiji tsoron komai ba a lokacinda yake ceto ni. Lallai bazan taɓa mantawa da abinda yayimin ba. Kowa da lokacinsa, lokacin ɗan-uwanmu Bisaiya yayi babu wanda zai iya hanawa. Amma nayi muku alƙawari zan kare wannan jirgi daga nan har zuwa sanda zamu isa daular Sisiya." Armad ya ɗanyi shiru na ɗan lokaci kafin ya wuce izuwa ɗakinsa yana tunani akan wasiyyar da Bisaiya ya bar masa taya kular masa da ɗansa. Tsahon kwanakin nan uku bai cewa ɗan komai ba, domin bai san mai zaice ba. Bai san mai ake buƙata daga gareshi ba. A rana ta shida saurayin ya gabato izuwa ɗakin Armad. "Suna na Maikiro Inàra." Saurayin ya ce, "Asalin mu ƴan daular Maikironomada ne amma dani da mahaifina mun zaɓi zama a daular Sisiya. Idan ka yadda zan bika na koyi al'amuran izza daga gareka na ɗan lokaci kafin mu rabu." Armad yaja dogon numfashi, sannan bayan ɗan tunani ya amince. Koyarda al'amuran abu ne mai tsada wanda sai anje manyan makarantu na manyan dauloli kafin a koya, amma idan kana da babban ma'aboci izza wanda zai koya maka ba saika je ba. Shi ma Armad kakansa shi ne ya koyar dashi. Koyawa wannan saurayi ba wani abu bane, kuma zaisa Armad ya biya bashin ceto shi da Bisaiya yayi. "Na amince zan koya maka al'amuran izza amma a halin yanzu ina kan hanyata ta zuwa daular Sisiya domin samawa mahaifiyata lafiya. Ban san yadda zata kaya ba, kuma abubuwa zasu iya rincaɓewa. Bazan iya gaya maka koni waye ba, amma ni mutun ne wanda keda kuɗi akansa. Bina zai zamo abu mai hatsari a gareka. Abu na ƙarshe idan zaka bini saidai ka haƙura da sana'arka ta tuƙa jirgi, domin kaga nidai ba'a ruwa nake yawo ba." Saurayin yai murmushin takaici tare da zubewa akan gwiwowinsa yana cewa, "Nasan haƙiƙanin kokai waye, Armad Wilbafos. Kuma a kowanne lokaci zan iya dawowa sana'ar tuƙa jirgi baƴan na gama koyon al'amuran izza. Koyon al'amuran izza shi ne abinda rayuwata ke buƙata a yanzu, babu wanda na zarga da mutuwar babana sai rashin ƙarfin izza ta. Indai zaka koyamin al'amuran izza zan bika ko'ina

Chapter 10 of 13