Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
12 / 13
ƙaton gado ne wanda zai iya ɗaukan mutun aƙalla hamsin. Armad yai duba izuwa manyan gilasan da suka kewaye ɗakin inda ya hango wani ƙasaitaccen lambu a bayan ɗakin. Wata iska mai armashi na ƙarawa yanayin ni'ima. Nan take Armad ya tabbatarwa kansa bai taɓa tsintar kansa a waje mai kyawu da armashi irin wannan ba a rayuwarsa ta duniya. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 97: Sammaci Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** ** Nostaljiya ce fara magana. "Ka jira ni anan ina zuwa." Sannan ta fice cikin sauri, tun yana hangen jar doguwar rigar data saka har ya daina. Ajiyar zuciya kawai yayi sannan ya faɗa kan wannan hamshaƙin gado wanda tunda yake bai taɓa yin arba da kamarsa ba a tsahon rayuwarsa. Abu kamar wasa jikinsa na dira akai ya nutse cikin laushi ai kuwa sai bacci ya ɗauke Armad. Yayi ta sharar bacci tsahon lokaci har saida rana ta faɗi. A lokacinda yaji muryar Nostaljiya na tashinsa. Da kyar ya buɗe ido yana gani hazo-hazo har dai ya wartsake. Bayan Nostaljiya Armad ya kula cewa akwai wasu kuyangi guda bakwai duk sanye da kaya ruwan kasa iri ɗaya sunyi sahu suna ta shigo da kayan ci da sha. Ƙanshi ne kawai yake tashi a ɗakin. "Ka tashi kayi wanka kaci abinci. Mahaifina yana so zaiyi magana dakai." Da akwai ragowar bacci a idon Armad amma koda yaji abinda Nostaljiya tace saiya miƙe zumbur gami da fara gumi. Ko sirikinka yawon bola yake akace zaku gaisa dashi sai kaji zufa ballantana ɗaya daga cikin mafi girman sarakuna a duniya. Cikin sauri Armad ya tambaye ta. "Da gaske kike koda wasa?" Nostaljiya ta fashe da ƴar ƙaramar dariya wadda ta dace da karfin ikonta. Bangon ɗakin na ɗaukan sautin kyakkyawar muryar ta. Nan take Armad yaji tamkar sarewa ake kaɗa masa. Lamarinda yasa ya faɗa cikin tunani ya manta da cewa shugaba mai dauwamammen sara yana jiransa. "Ka tashi yana jiranka?" Koda Armad yaga ga dukkan alamu da gaske take saiya miƙe cikin damuwa ya ce, "lafiya dai ko?" Nostaljiya ta haɗe rai cike da shagwaɓa. "Nima ban sani ba." Armad yai ajiyar zuciya a karo na uku sannan ya fara tunanin mai Bihanzin zai ce masa. Lallai da matsala. "A ina zanyi wankan? Kuma ni gaskiya..." Nostaljiya tayi wa Armad wani kallo mai cike da tsokana tana cewa, "Kai gaskiya me? Ga ƙoramar wanka can ta musamman nasa an haɗa maka." Tayi nuni izuwa wani ƙasaitaccen tafki mai ɗauke da filawowi a samansa. Wani tiriri ne mai alamun ni'ima ke tashi daga saman ruwan. Kana gani kasan an shirya shi ne domin wankan manya ƴaƴan sarauta. Armad ya juya ya nufi ƙofa yana ta zulumi. Har ya kusa kaiwa ƙofar sai yaji muryarta. "Idan ka fita kasan ta ina zaka zagaya?" Armad ya juyo fuska a murtuke yana cewa, "to kizo ki rakani mana." Nostaljiya na ganin yadda yake magana ta ƙara fashewa da dariya tana cewa, "kaci gaba da ɓata rai saina kirawo maka yaya Kiru da yaya Hasanu yanzu-yanzu." Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa ganin Nostaljiya ta taho tana rangwaɗa irin ta ƴaƴan sarakunan farko. Kwata-kwata ya manta dasu Kiru da Hasanu. Amma a wannan lokaci ya tuno da fafatawarsu da Kiru shekaru da dama da suka wuce a sanda ya fara fitowa nemawa mahaifiyarsa lafiya. Can bayan Nostaljiya ta fara jan hannusa izuwa waje ya samu ya tattaro kwarin gwiwarsa ya ce, "Kiru da Hasanu? Da fatan suna nan lafiya? Na daɗe bamu haɗu ba." Nostaljiya ta amsa da cewa, "ba wani nan. Da yaushe rabon da ka tambayesu? Kai dai kawai tsoron yaya Kiru kake ji. Dan kasan yanzu ya ƙara kwarewa matuƙa a fannin takobi." Armad na niyyar cewa shima ya ƙara ƙarfin takobinsa Nostaljiya ta fara jansa da gudu suna sassarfa. Duk kwanar da suka sha sai sun haɗu da kuyangi suna hidima, kuma duk wanda duka gansu sai sun zube a ƙasa suna gaisuwa. Nostaljiya ko a jikinta, Armad kuma tun yana amsawa harya gaji. Ga dukkan alamu zuwansa shi ne yasa aka kawo wannan kuyangi da yawa haka domin sanda yazo babu kowa a wajen. Suna cikin tafiya Armad yai ciki da wata tukunyar filawa garin ya kauce mata. Nan take ya fara jan hannun Nostaljiya yana cewa, "ki daina gudu. Wai wajen wankan nan tashi zaiyi ne? Kinga ban san hanya ba ina yi muku ɓarna." Amma Armad na magana Nostaljiya kawai ƙara jansa take tana dariya. "Komai ka fasa zan biya kar ka damu." Tun yana zuƙewa har ya saki jiki suka ringa zagayawa suna gudu acikin fadar nan suna shewa kamar wasu yara ƴan shekara goma. Bayan kimanin rabin sa'a suka iso wajen. Arnad ya waiwaya ya hango ɗakin da suka fito daga ciki sannan yaga hanyar da suka biyo, nan take ya gane cewa Nostaljiya na sane ta ringa zagaye dasu ba gaira ba dalili. Kamar ta gane mai yake tunani ta ce, "Eh mana. Ina sane na kewaya damu kaga yanzu kasan hanya baza ka ɓata ba. Kayi sauri ka shiga kai wanka tun kafin abba ya turo a ɗaukeka a tafi dakai." Armad najin wannan kalma ya fara azamar cire kaya zai faɗa cikin ruwan, amma a lokacin ya tuna tana wajen ya juya ya kalleta. "Anan zaki tsaya?" Nostaljiya ta haɗe rai. "Ko baka faɗa ba tafiya zanyi. Kawai dai kada ka nutse ka mutu ka barni." Armad ya fashe da dariya a karo na farko yana cewa, "kamar wata ke. Ɗan wannan ruwan ne zai kashe ni, mutuwa ta sai anyi shiri." "Nidai kayi sauri idan ba haka ba zan dawo na fito dakai." Nostaljiya ta juya ta fice. Armad ya jira yana murmushi har saida ta ɓace sannan ya ƙarasa cire kayansa ya afka cikin tafkin ya fara iyo. Ruwan ya kasance mai ɗumi dai-dai wanka. Sannan yana bada wani ƙanshi mai inganci. Filawowin kai kuwa na bada wani sinadari mai kama da sabulu wanda nan take ya wanke jikin Armad tas. Idan ta shawarar Armad ne kada ya futo daga cikin wannan daddaɗan ruwa har sai ya nutsu amma sarki na jiransa. Ba shiri ya fito ya maida rigarsa. Akan hanyarsa ta dawowa ya fara tunanin wanne kaya zaisa yaje dasu. Tambayoyi sama da ɗari suna ta yawo akansa akan menene dalilin da yasa Bihanzin ke nemansa. Kowanne dalili ya tuna sai yaji zuciyarsa ta buga. A lissafin Armad wannan ba wani abu bane illa sammaci. Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙofar ɗakin daya kwanta aciki ɗazu. Yana shiga yai arba da Nostaljiya zaune tana jiransa zagaye da abinci. "Na baka minti goma ka shirya. Idan ka dawo kaci abincin." Armad ya zare ido cikin sauri yana cewa, "Yunwa nake ji fa." Nostaljiya ta canja fuska sannan ta fara magana cikin shagawaɓa. "Yana jiranka fa." Armad bai san sanda ya sanya kaya cikin ƴan daƙiƙu ba ya bita suka nufi nufi cikin fadar. Ranar da zaiyi arba da mai dauwamammen sara tazo. _______ Yekuwa Manazartar littafin Magajin Wilbafos Sarki Kurussa'ayi Ururu Sarki Bisa Doron Kasa na daya 1 yana Gaisheku ya kuma ya gaisheku Sannan yace a sanar daku cewa kwamitin Rubutun magajin wilbafos karkashin jagorancin Shuraih 99% sun canja tsarin Posting, A yanzu za'a runga posting Kullum sabanin zamanin baya da sai sati sati, A kowane Rana za'a runga yi maku post Daya, . Sako daga shalkwatar Ururu ta doron kasa na Uku, Sa hannun sarki Kurussa'ayi Ururu, Dhul ururu,Yarima Dumakisu Ururu,Uznu Ururu, Haruta Ururu,Maruta Ururu,deniz ururu ______ dafatan za ku bamu hadin kai 99% Babi na 98: Armad da Bihanzin ** Haka Armad da Nostaljiya suka yita keta cikin wannan fada suna wuce manyan gine-gine masu fasali daban- daban. Nostaljiya na ƙoƙarin yiwa Armad hira amma hankalinsa baya wajen harta gaji tayi shiru. Bayan wani ɗan lokaci suka iso harabar wani ƙaton ɗakin taro da aka kewaye da mutun-mutumin mutane kala-kala. Nostaljiya ta nuna ƙofar ɗakin tana cewa, "shiga ka jira aciki ina zuwa." Armad ya nufi ƙofar ɗakin ita kuma ta kewaya tabi hanyar da tabi ta bayan ɗakin. Ɗakin nada madaidaicin girma amma abubuwan dake cikinsa basu da yawa. Wani ƙaton teburi ne kewaye da kujeru a tsakiyar ɗakin. Ga dukkan alamu wannan ɗaki kullum acikin kula yake domin ko ƙura ɗaya babu. Komai kyalli kawai yake, shi kansa teburin na gilashi ne. Armad ya ja kujera ɗaya ya zauna yana jiran shigowar mai dauwamammen sara. Ba jimawa saiga Hasanu Sisiyu, yayan Noltaljiya, ya shigo. Fuskarsa babu murna kuma babu ɓacin rai. Ya dubi Armad ya ce, "kwana da yawa. Da fatan kana lafiya." Muryar Hasanu na nan ɗauke da ƙarfi da girma irin na sarakuna. Fuskarsa ta ƙara cika da kamala, kana ganinsa kasan ba'a zaune yake ba. Armad ya amsa da cewa, "ina nan lafiya. Da fatan na same ku lafiya?" Hasanu ya nemi waje ya zauna sannan ya dubi Armad ya ce, "bari na baka shawara a matsayi na na abokinka. Kada kayiwa mahaifinmu ƙarya domin duk abinda zaka faɗa zai san gaskiya kake faɗa ko ƙarya." Armad yai murmushi. "Ai dama bana shirin yin ƙarya." Hasanu ya girgiza kai kafin daga bisani yai murmushi sannan su koma hirar takobi. Hasanu yayi ta yiwa Armad tambayoyi akan fasahar takobinsa shima Armad yana masa har dai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Wani babban mutun sanye da doguwar riga ƴar shara ya shigo cikin ɗakin. Nostaljiya na tafe a bayansa. Yana shigowa Hasanu ya miƙe tsaye tare da durƙusawa, shima Armad ya miƙe ya bashi girmansa. Mutumin na tafiya kamar ba tafiya yake ba, ƙafafunsa na motsawa cikin isa da iko irinta sarakunan aljanu. Idanunsa tsaye suke kan Armad yana nazarinsa. A tsaye zaka iya cewa wannan mutun ragowar samudawa ne domin aƙalla yakai zira'i ashirin. Wanda hakan ya ninka tsayin Armad sau wajen takwas. Yana shigowa ya nufi kujerar da aka tanada domin sa wacce ke gaba da dukkan sauran kujerun. Yana zama Hasanu da Nostaljiya suka fice suka barshi da Armad. Wannan mutun dai ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara, ɗaya daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal. Mutuminda akai ittifaƙi takobinsa tafi kowacce takobi ƙarfi a duniya. A wannan lokaci Armad ya nutsu tare da tsayawa yayi wa Bihanzin kallo na tsanaki. Bihanzin dai ya kasance mutun ne wanda kana kallonsa zaka san yayi matuƙar daɗewa a duniya. Idan kana kallonsa zaka ga tamkar shekarun ƙarni-ƙarni ne ke wucewa ta ruhinsa. Idanunsa a kafe suke kuma suna bada wani haske mai ɗauke da firgici da saka jimami. Fuskarsa nada tsayi da faɗi kamar dukkan jikinsa, sannan kuma cike take da farin gemu. Gashin kansa ma fari ne dogo mai tsayin gaske wanda har bayansa yake taɓawa. Hatta shi kansa gashin girar Bihanzin a lanƙwashe yake zubin takobinsa. Rigar dake jikinsa doguwar ƴar shara ce wadda ta bashi damar saƙale takobinsa a sauƙaƙe. Armad na ganin takobin nan yaji hankalinsa ya ɗugunzuma, tsigar jikinsa na tashi. Yanayin-izzar dake kewaye da takobin iri ɗaya ne sak dana Hankakan-mutuwan da Armad ya gani. Nan take Armad ya miƙa hannunsa kan takobinsa ba tare da ya sani ba. Tuni Armad ya manta da inda yake, babu abinda yake tunawa sai labarin da mahaifiyarsa ta gaya masa akan waccan ƙabila wadda aka manta da sunanta. Ƙabilar da tarihi ya nuna cewa saida ƙabilar Wilbafos da ƙabilar Ururu suka haɗa hannu da ƙarfe sannan suka ga bayanta. "Kada ka damu da takobi na. Ita wannan takobin tawa babu wanda take yadda dashi idanba ƴaƴa na ba." Muryar Bihanzin ce ta farfaɗo da Armad daga tunanin daya shiga. Amma duk da haka bai ɗauke idonsa daga kan takobin ba. Takobin dai bata da faɗi da yawa amma tafi tsayin zira'i uku. Lallai ba daban Bihanzi basamude bane da bazai iya ɗaukanta ba. Abin mamakin shi ne takobin har wani huci take tana kallon Armad tamkar tana jin mai ake cewa. Koda Bihanzin yaga Armad bai daina kallon takobin ba sai yaja rigarsa ya rufe ta yana cewa, "sunan wannan takobi tawa Bankái. Indai ka biya ta Bankái haka zatai ta tsokanarka har sai ta jaka izuwa faɗa." Mamaki ya ƙara rufe Armad yadda yaji Bihanzin yana maganar takobinsa yana bata suna kamar wata mai rai. Nan take Armad ya tuna yadda yayarsa Hidaya take yiwa takobinta magana. A sau da dama Armad yana yaro yakanyi tunanin ko Hidaya tsokanarsa kawai take amma takan ce masa takobin ta tana da ruhi nata na kanta kuma tana ji idan akai mata magana. Armad yai murmushi na girmamawa sannan ya ce, "barka da warhaka. Ina fatan ban ɓata maka ƙa'idarka ba dana shigo fadarka ba tare da izini ba." Bihanzin yai gyara murya haɗe da girgiza kai, lamarinda yasa muryar tayi kama da ana goga busasshen ƙashi a jikin bango. Dama dai muryar Bihanzin kaushi ne da ita, amma gyaran muryar da yayi shi ne yasa abin ya ƙara fitowa fili. A wannan lokaci Armad yayi ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma bisa mamaki baiji komai ba sai wani sanyi mai ratsa ƙashi wanda ya banbanta da sanyin-babban-sihiri kuma ya banbanta da sanyin hunturu ko na ƙanƙara. Wannan sanyin da Armad yake ji yafi dana tsohon kabari. Nan take Armad ya daina ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma duk da haka saida yaji ya fara rawar ɗari. Muryar Bihanzin ce ta ƙara farfaɗo dashi. "Kada ka damu, Magajin Wilbafos, tunda har ka shigo ba tare an kama ka ba ai gayyato ka akai." Armad ya zare ido cikin mamakin wannan magana, domin hakan na nuna Bihanzin na sane da shigowarsa. Nan take Armad ya buɗe baki zai tambayi Bihanzin amma sai Bihanzin ya riga shi magana. "Nakan ji yanayin-izzar abokan gaba tsahon tafiyar shekara guda tun ina ɗan shekara bakwai. A lokacin da na cika shekara takwas ina iya banbance mutane na gane ko su waye ta hanyar yanayin-izzarsu koda nisansu da inda nake yakai tafiyar shekara guda. Kaga bazai zama abin mamaki ba dan naji shigowar ka daula ta a lokacin da ka sauka daga jirgin Fataken-dare." Armad ya zare ido cikin tsananin al'ajabin ƙarfin izzar wannan halitta dake gabansa. Lallai ba'a zama sarkin Jinzidal a banza. Koda yake dama wannan shi ne karo na farko da Armad yai arba da ɗaya daga cikinsu. Idan dai har Bihanzin zaiji yanayin-izzar mutun kimanin nisan tafiyar shekara guda kuma ya gane waye, lallai babu wanda ya isa ya shigo wannan daula ba tare da saninsa ba. Kuma lallai ba abin mamaki bane dan Bihanzin yasan Armad shi ne Magajin Wilbafos. Kai tsaye Armad ya bugi ƙirji ya tambayi Bihanzin. "Mai kake buƙata daga gareni daka bari na shigo?" Chapter 99 & 100 MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 99: Armad da Bihanzin part 2 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos "Hmm... " Bihanzin yaja dogon numfashi sannan yaci gaba da bayani. "Wilbafos kai kake neman wani abu a waje na ba ni nake nema a wajenka ba. Zaka sauƙaƙa mana wannan tattaunawa idan ka gayamin hakikanin mai ya kawo ka daula ta." Armad ya sunkui dakai yana tuno asalin abinda ya kawoshi wannan daula. Koma meye a bayan samarwa mahaifiyarsa lafiya yake kuma lallai abinda kawai ya kawo shi kenan. "Nazo neman shekarun izza domin yiwa mahaifiyata wadda take fama da cutar izza magani." Bihanzin ya danyi shiru kafin daga bisani ya ce, "Naji labarin cewa abinda ya fito dakai daga gida kenan shekaru uku da suka wuce. Indai wannan ne kaɗai buƙatarka to babu matsala, a yanzu zan warkarda mahaifiyarka. Koba komai bai wuce biyan bashi ba, domin har yanzu bamu biyaka fassarar dakai mana ba a waccan shekara." Armad ya zare ido tare da miƙewa tsaye cikin murna yana cewa, "da gaske kake? Lallai idan ka samarwa mahaifyata lafiya bani da yadda zanyi na iya sakamaka. Nagode." Bihanzin ya ɗaga hannu yana dakatar da Armad alamun bai gama magana ba. "Nasan akwai soyayya tsakanin ka da ƴata Nostaljiya, kuma bazan ce maka ka haƙura ba indai kana sonta, amma akwai abu guda ɗaya da nake so ka sani." Koda Bihanzin yazo nan a zancensa sai ya dubi Armad a nutse domin ya tabbatar yana tare dashi sannan yaci gaba. "Shi CIKAKKEN MUTUN shi ne wanda yake ɗaukan alhakin abu idan yasan shi ya jawo shi. Nostaljiya ta ɗau alhakin abinda ta aikata a wajen cinikin bayi kuma taƙi yadda a ɗora maka laifi. Idan za'a wanke ta a idon duniya to sai dai ta yadda ta auri Deniz Bizaya wanda a zahiri ba shi take so ba. To amma idan bata aure shi ba, hukumar Jinzidal zata yanke mata hukunci. Hatta ni kaina a matsayi na na babanta bazan iya kare ta daga sauran sarakunan Jinzidal ba, kuma idan na hana ayi mata hukunci, yaƙi ne zai afku. Idan kace kana sonta, shin zaka iya zama cikakken mutun ka ɗauki alhakin komai a kafaɗunka ka kare ta, kuma ka shiga yaƙi saboda ita? Idan dai har zaka iya wannan to ka cancanci ƴata, amma idan baza ka iya ba to ka manta kawai. Biyo ni." Bihanzin ya miƙe ya nufi ɗaya daga cikin ƙofofin dake kewaye da wannan ɗaki, Armad na biye dashi. Bihanzin na tunkarar ƙofar ta buɗe, Armad ya tsinci kansa a wani ƙaton fili mai yawan rairayi. Abin mamaki iskar dake kaɗawa acikin wajen ta banbanta data cikin dakin daya baro, tamkar wata duniya ta daban suka shiga. Take saboda sanyi Armad ya tuna da cewa yana da kayan sanyi a ajiye acikin zobensa. Amma kafin ya fito dasu sai kwatsam yaji yanayin ya fara canjawa, rairayin ya fara ɗaukan zafi kamar ana kunna masa wuta. Kafin kace meye wannan gumi ya fara gudu a fuskar Armad. Suka ci gaba da tafiya Bihanzin bai ce masa komai shi kuma bai tambaya ba. Amma abu kamar wasa taku bakwai bayan an fara zafin kawai sai ruwa ya ɓarke kamar da bakin kwarya. Armad ya tsaya ido a zare yana mamaki. Lallai akwai abin al'ajabi a tattare da wannan waje. Kuma tashin hankalin shi ne bai san inda Bihanzin yake ƙoƙarin kaishi ba. Yana cikin tunane-tunane yaji murya Bihanzin, "A cikin wannan waje duk bayan minti ɗaya yanayi yake canjawa. Kaga maimakon zafi da sanyi da damina da rani kowanne yazo a shekara sau ɗaya, kowannensu a wannan waje yana zuwa a kowacce rana sau dubu uku da ɗari shida. Acikin wannan waje nake ajiye wani kaso daga cikin shekarun izza ta na kwangila ta. Ban san shekara nawa mahaifiyarka take buƙata ba amma nayi maka alƙawarin bata shekarun izza dubu goma zuwa ashrin. Fito da ita ka ajiye ta anan." Bihanzin ya nunawa Armad tsakiyar yashi inda ruwa ya ɗan taru. Da farko Armad ya fara mamakin yadda akai Bihanzin yasan mahaifiyarsa na cikin zoben dake hannunsa amma kuma ya tuna komai ma zai iya faruwa indai ana maganar sarki Bihanzin sabida haka babu wani abin mamaki. Nan take Armad ya futo da mahaifiyarsa sanye cikin fararen kaya kamar tana bacci. Amma yaƙi yadda ya ajiƴe ta a ƙasa har saida Bihanzin ya tafa hannunsa wani gado ya bayyana. Bayan wasu ɗalasimai da Bihanzin ya kira a zuci sai kawai wani ƙatoton shaiɗanin aljani ya bayyana. A tsakiyar kan aljanin akwai ƙahunhuna guda bakwai, sannan yana sanye da wata baƙar hula da aka sarrafa da fatar aljanu zalla. Abin mamaki ɗauke a kafaɗun wannan aljani hankakan mutuwa ne baƙaƙe har guda biyu. Yana bayyana ya faɗi yai gaisuwa ga Bihanzin yana cewa, "Ya shugaba na. Mai kake buƙata?" Bihanzin ya amsa da cewa, "mahaifiyar wannan yaro na fama da cutar izza, ina so ka bata shekarun izza daga ɗaya zuwa dubu ashirin. Iyakacin yadda zai ishe ta ta warke." Aljanin ya ware samudawan hannayensa guda biyu yana cewa, "An gama ya shugabana." Nan take wani jan haske mai ɗaukar ido ya fara taruwa a hannayen wannan aljani kafin daga bisani ya karkatar da hasken izuwa gare ta. Hasken na taɓa ta jikinta ta fara girgiza kamar mai farfaɗiya. Armad yai wuf zai riƙe ta amma Bihanzin ya riƙe shi yana cewa, "Kada ka damu, shekarun Izza ne ke shiga jikinta." Haka Armad ya haƙura yana kallon mahaifyarsa wannan jan hasken na shiga jikinta tsahon lokaci. Saida akai sa'a guda acikin wannan hali sannan hasken ya ɗauke, aljanin ya dubi Bihanzin ya ce, "An gama ya shugaba na. Na bata shekarun izza dubu goma sha huɗu da dari biyu da sha uku, kuma a lissafi na zata farka nan da wata tara." Cikin sauri Armad ya durƙusa a gefenta yana share mata gumi. Yana cikin haka kawai sai yaga a karo na farko acikin shekaru uku mahaifiyarsa tayi motsi. Cikin murna yai ihu yana niyyar yin tsalle yai shewa kawai sai yaga ta buɗe ido. Ta kalli Armad, Armad ya kalleta. Nan take hawaye ya fara zuba daga idanunsa. Ta buɗe baki zatai magana amma kafin tayi magana saita ƙara komawa ta suma. Amma duk da haka murnar Armad bata ragu ba. Yana cikin haka yaji muryar Bihanzin a kunnensa. "idan ka daɗe da yawa acikin wannan waje komawa duniyar daka fito zaiyi maka wahala." Armad najin haka ya maida mahaifyarsa cikin zoben sannan cikin murna da annushuwa irin wadda ba'a taɓa ganinsa aciki ba ya biyo bayan Bihanzin suka nufo waje. Koda suka dawo cikin wannan ɗaki sai suka tarar da Nostaljiya na tsaye tana jiransu. Tana ganin murnar dake fuskar Armad ta fashe da murmushi, lallai tasan an samu abinda ake nema. Koda Bihanzin yaga haka saiya dubi Armad ya ce, "Ni zan barku anan. Ka tuna da abinda na gaya maka. Ka zama CIKAKKEN MUTUN." Babi na 100: Shawarar Armad ** Armad da Nostaljiya suka nufi hanya izuwa ɗakin da aka saukeshi. Akan hanyarsu kowa yayi shiru bai ce komai ba. Nostaljiya tana jira Armad ya gaya mata abinda suka tattauna da mahaifinta amma Armad yayi shiru. Ita kuma bata tambaya ba. Koda isarsu ƙofar ɗakin sai Armad ya shige ɗakin ba tare da yace uffan ba sannan ya turo ƙofa. Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma ta fasa. Cikin ɓacin rai ta juya ta tafi. Har ta kusa ƙulewa ta juyo ta dubi kuyangar dake ƙofar ɗakin ta ce, "Ku bashi duk abinda yake buƙata, idan ya nemi ku nuna masa hanyar fita daga fada ku nuna masa." Tana rufe baki ta juya ta tafi. Armad ya faɗa kan gado yana jinta harta ƙule. Yai shiru yana tunanin maganarda Bihanzin ya gaya masa. Abu ne mai sauƙi tunda mahaifiƴarsa ta sami sauƙi ya fice daga wannan daula kada ya ƙara waiwayarta. Yaje can wani waje ya tsara sabuwar rayuwarsa cikin kwanciyar hankali. To amma Armad yasan cewa tun daga ranar da yayi rantsuwa zai tarwatsa cinikin bayi rayuwarsa baza ta ƙara kasancewa cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan rayuwa wadda za'ai aure a haihu a sami ƴaƴa biyar ko goma, sannan a zauna cikin kwanciyar rai har a tsufa a mutu ba tasa bace. Dama dai tuntuni abinda yasa Armad bai maida hankali ba akan shirinsa na tarwatsa cinikin bayi shi ne halinda mahaifiyarsa ke ciki. Amma ga dukkan alamu wannan ya kau. A yanzu ne lokaci mafi dacewa daya kamata ya fara aiwatar da shirinsa. Auren Nostaljiya lallai zai ɗaukaka martabarsa a idon duniya kuma zai saka rundunar sarki Bihanzin ta zama kamar tasa. Daɗin daɗawa daga abinda Nostaljiya ta gaya masa a wancan lokaci da suka haɗu, akwai rigima tsakanin sarakunan Jinzidal tayadda kowannensu zaiso yaga bayan ɗan'uwansa. Duk da cewa manufar Bihanzin ta yaƙi da sauran sarakunan Jinzidal ba lalle bane ta zama ɗaya data Armad ba, amma dukkaninsu suna da abokan gaba iri ɗaya. Matsala ɗaya ita ce; shin Bihanzin akan kansa yana so ya tarwatsa cinikin bayi ko kuma kawai yana so ya tarwatsa sarakunan Jinzidal ne? Domin zata iya yiwuwa Bihanzin yana goyon bayan cinikin bayi amma yana rigima da sarakunan Jinzidal. Armad na zuwa nan a tunaninsa ya yanke shawara, Idan har Bihanzin ya amince ce zai taimake shi ya rusa gasar Jinzidal to shima zai taimaka masa ya karya sarakunan Jinzidal. Bayan Armad ya cimma wannan matsaya saiya fito da Maikiro Inara daga cikin zobensa. Har izuwa wannan lokaci Inara bai farfaɗo ba, amma ga dukkan alamu ruwa kawai yake buƙata. Ai kuwa Armad yana yayyafa masa ruwa ya farka, inda Armad ya kwashe dukkanin labarin daya afku bayan ya suma ya gaya masa. Inara ya taya Armad murnar samun lafiyar mahaifƴarsa sannan yayi masa fatan alkhairi. --------- Armad da Inara suka kwana acikin wannan ɗaki, washe gari da safe Armad ya kaisu wannan tafki sukai wanka sannan suka ci suka sha. Bayan sun dawo ɗaki Armad ya fara jira ko zaiga Nostaljiya amma shiru har yamma ta kawo kai rana ta faɗi ba labari. Da magariba Armad ya tura ɗaya daga kuyangin dake kawo musu abinci ta kira masa Nostaljiya amma bisa mamaki hakan bata samu, Nostaljiya ta amsa amma bata zo ba. Haka ya gaji da jira har dare yayi gari ya waye. Washe gari Armad ya ƙara tura wata kuyangar, Noltaljiya tace taji amma har dare yayi bata zo. Nan take Armad ya fara shiga damuwa saboda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa Nostaljiya bata amsa kiransa ba. Washe gari Armad ya yanke shawara ya taka yaje wajenta da kansa. Koda ya fito bakin ƙofa saiya tarar da ɗalibinsa Inara na tsaye yana gadin ƙofar. Murmushi kawai Armad yayi ya bashi umarnin yazo ya rakashi. Armad ya dubi ɗaya daga cikin kuyangin dake wajen ya ce, "Muje ki rakamu wajen gimbiya." Amma wannan kuyanga ta kada baki ta ce, "Ai ba'a shiga wannan ɓangare daga mu kuyanginta sai ita kanta, gimbiya." Maganar bata yiwa Armad daɗi ba, ya tsaya yana ta tunani kafin daga bisani ya juya ya koma ɗaki. Har ya isa bakin ƙofa sai wata dabara ta faɗo masa, yaci birki ya tsaya tare da juyowa izuwa wannan kuyanga ya ce, "muje naga wajen saboda tsaro." Kuyangar fara ce mai tsaho sanye da farar doguwar riga. Tana jin abinda Armad ya ce ta zare ido tana mamaki. Abinda bata gane ba shi ne mai Armad yake nufi da 'saboda tsaro'. To amma ba muhallinta bane a matsayinta na kuyanga ta tsaya tana yiwa Armad tambaya, saboda haka ta shige gaba ta fara tafiya, su Armad suka bi bayanta. Abin mamaki sai Armad yaga sun ɓulle ta wata ƙofa wadda ta shigar dasu wani ƙaton fili. Duk kewayen da Armad yayi na kwana biyu bai san da wannan filin ba. Haka suka ci gaba da bin kuyangar har suka ƙarar da wannan fili suka nufi ɓangaren arewa, sannan daga bisani suka iso wata farfajiya mai yawan bishiyun dabino. Wannan bishiyun dabino sun kekkewaye wannan sashi ta yadda ba'a iya gano cikinsa sosai. Suna ƙara matsowa sai Armad ya fuskanci cewa wannan ɓangare an raba shi ne izuwa gida uku manya-manya. Abin mamaki shi ne hatta katangar da aka kewaye wannan waje da zinare aka yaɓe ta. Komai kawai walwali yake. Nan take Armad ya fara tunani yana mamakin irin dukiyar dake cikin wannan fada. Suna isowa gindin wannan bishiyu sai wannan kuyanga ta tsaya tana nuni da ginin dake tsakiyar gine-ginen guda uku. "Wancan ne na tsakiyar. Na ɓangaren dama kuma na ƴarima Kiru ne, na ɓangaren hagu kuma na yarima Hasanu me. Amma daga nan babu wanda yake da damar haurawa

Chapter 12 of 13