Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 13
ne a duniya."MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 93: Samari Biyu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Ragowar kwanakin da Armad yayi acikin wannan jirgi baiji daɗinsu ba sosai, domin kuwa kowa idan ya ganshi kaucewa yake tamkar yana tsoron kada ya ɓata masa. Tun yana damuwa harya daina, shi kuwa Maikiro Inára kullum a ƙofar ɗakin Armad ya dawo kwana, a cewarsa ɗalibi kullum yana tare da malaminsa. Babu yadda Armad baiyi ba amma Inára bai daina kwana anan ba. Hatta ma'aikatan jirgin duk abinda zasu yi sai sun nemi izini wajen Armad. A sati na huɗu suka iso daular Sisiya, ɗaya daga cikin manyan dauloli shida dake faɗin duniya a wannan zamani. Armad yayi farin ciki sosai da faruwar hakan domin koba komai ya ƙara kusantar matakin samawa mahaifiyarsa lafiya. Yana ji a ransa cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da zai fita nemar mata lafiya domin kuwa a wannan lokaci zai samu abinda yake nema kuma bazai ƙara bari ta faɗa cikin rashin lafiya ba koda sama da ƙasa zata haɗe. Sannu a hankali jirgin Fataken-dare ya sauka a gaɓar doron-ƙasa na huɗu sashin arewa inda anan daular sisiya take. Gaɓar jirgin acike take da ƴan kasuwa da kuma iyalan fasinjojin da duka zo taryar su. Cikin ƙanƙanin lokaci fasinjoji kowa yai sallama da juna sannan suka godewa Armad kafin kowa ya kama gabansa. Tuni daman Inára ya sallami dukkan ma'aikatan jirgin ya biya su haƙƙinsu, saboda baya sa ran ƙara tafiya a kowanne lokaci kusa. Koda kowa ya ɓace aka bar Armad da Inára sai Inara ya nemi iznin zuwa ya bada ajiyar jirgin Fataken-dare har zuwa lokacinda zai dawo kan ciniki. Armad ya amince kuma ya bayyana masa wajenda zasu haɗu bayan ya gama. A lokacinda suka iso gaɓar rana na tsakiyar sama amma kafin Inara ya hattama komai sai da rana ta faɗi. A lokacin ya iske Armad a ɗaya daga cikin gidajen-kwana na wannan gaɓa. Armad na zaune yana tattara bayanai akan wannan daula ta sisiya. Dama abinda yazo yi kenan. Inara na bayyana Armad ya tashi suka kama hanya. Armad ya dubi Inara ya ce, "Da fatan ka gama komai?" Inara ya gyaɗa kai. "Eh, na gama ya shugaba na. Na samu wanda zai ajiye min jirgin Fataken-dare har zuwa sanda zan dawo." "To yayi kyau." Armad ya ce, "daga binciken da nayi na gano cewa wannan daula nada adadin mutane miliyan ɗari biyar zuwa ɗar shida. Wannan mutane sun rarrabu a tsakanin garuruwa ashirin da tara da babban birni guda ɗaya wanda ake kira da Jékis. "Kowanne ɗaya daga cikin wannan garuruwa ashirin da tara nada sarki amma dukkan wannan sarakai suna ƙarƙashin babban sarkin dake mulki a babban birnin tarayya na Jékis. Wanda ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara. Daga nan zuwa can tafiyar wata da watanni ce, amma ina da sihirtaccen doki mai suna Ubbaru wanda zai taƙaice mana wannan tafiya." Armad na zuwa nan a zancensa ya hanhanga ya tabbatar babu wanda ke kallo sannan ya sha kwanar wani layi mai duhu ya buɗe ƙofar zobensa ya ɗakko Ubbaru. Inara na cikin mamakin wannan zobe na Armad yaji muryar Armad na masa bayani. "Saboda tsananin gudun wannan doki jama'a basa ganinsa a yayinda yake tafiya. Ina ganin ba matsala muyi amfani dashi mu isa babban birnin." Armad da Inára suka hau dokin sannan suka ɗau hanya. Da tsakar dare suka isa babban birnin Jekis, wanda hakan ke nuna Ubbaru ya taƙaice tafiyar wata da watanni acikin awanni. Babban abinda ya bawa Inara mamaki shi ne yadda shi yake iya ganin mutane da garuruwan da suke wucewa amma mutane basa ganinsu. Kuma duk wannan azabar gudu iska bata damunsu. Lallai Ubbaru doki ne mai yawan sihiri. Inara ya dubi Armad ya ce, "A yanzu sun rufe ƙofa sai dai mu jira zuwa asuba." Armad ya amince suka sami gindin wata bishiya suka fake har zuwa safiya. Abin mamaki har yanzu ƴaƴan itacen da Nostaljiya ta bar masa suna nan basu lalace ba, saboda haka Armad ya fito dasu suka ci sukai hani'an. Da safe suka nufi ƙofar wannan babban-birni mai suna Jekis. Duk da sammakonsu saida suka tararda layin mutane a bakin ƙofar wanda a tafe suka kwana. Wani tafkeken bango ne iya ganinka ya kewaye garin. Duk wanda zai wuce saiya nuna shedar ɗan-ƙasa ta sisiya da kuma harajin ayrid hamsin ko ɗari idan baka da sheda. A wannan lokaci Armad ya tuno bashi da ko sisi duk da akwai naira miliyan ɗaya da rabi a kansa. Koda Inara ya fuskanci halinda Armad ke ciki saiya fito da ayrid ɗari da hamsin ya riƙe a hannunsa. Kallonsa kawai Armad yayi tare da yin murmushin godiya. Sannu a hankali layi ya fara raguwa, saura mutun sha uku a gabansu. A wannan lokaci ne Armad ya hango wasu samari guda biyu a gabansa. Tsakaninsa dasu mutun goma ne kawai. Ɗaya daga ciki yana da ƙiba, ɗaya kuma siriri ne kuma yana ɗauke da takobi. Dukkansu sun saka hirami sun nannaɗe fuskarsu amma Armad yana ji lallai ya sansu amma babu dama ya sauka daga layi ya isa gare su. Saboda haka saiya rufe ido ya gane yanayin-izzarsu. Bayan wannan samari sun wuce layi ya iso kan su Armad. Masu gadi ashirin ne a bakin ƙofar. Rabi riƙe da makamai rabi kuma suna ƙirga kuɗi. Dukkansu sanye da kaya yalaye masu ratsin baƙi a hannunsu. Inara ya miƙa kuɗin dake hannunsa tare da katinsa na ɗan ƙasa yana cewa, "ga nawa ayrid hamsin, gana malami na ayrid ɗari domin bashi da shedar ɗan ƙasa." Mai gadin yayi wa Armad wani kallo mai tsayi kamar wanda ke kallon mai laifin kisa. Sannan daga bisani ya ce, "daga wacce daula kake?" Armad ya amsa da cewa, "daular Hán ta doron ƙasa na uku." Mai gadin ya ƙara matsawa kusa kamar wanda ke kokwanton kamannin Armad. A jikinsa yana ji cewa lallai Armad mai laifi ne. Nan take ya buɗe wani ƙaton littafi a gefensa mai ɗauke da hotunan mutane masu laifi wanda aka sa kuɗi akansu. Duk da Armad yasan kamanninsa a canje suke sai da zuciyarsa ta buga da yaga mutumin ya buɗo shafin da hotonsa ke ciki. Mai gadin ya tsaya tare da ƙara tambayar Armad, "Yama kace sunanka?" Armad ya amsa da cewa, "Han Djinn." Mai gadin yaja dogon numfashi tare da buɗe baki zai ƙara wata maganar amma sai Inara ya zira hannu a aljihu ya miƙa masa ƙarin Ayrid ɗari. Lamarinda yasa yai murmushi tare da buɗe musu ƙofa. Cikin sauri Armad yabi bayan wannan samari biyu daya hanga a gabansa. Suna shiga kuwa manyan gine-ginen birnin sukai musa sallama. Amma duk da haka ya iya jiyo yanayin-izzar wannan samari guda biyu a ɗan gaba da inda suke. Nan take ya umarci Inára daya jirashi anan, sannan yayi amfani sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan wannan samari biyu. Yana bayyana ya kalli samarin sama da ƙasa. Nan take sai farin ciki ya cika zuciyar sa. Cikin dariya da annushuwa ya kira sunansu. "Iliyasis... Cokali... Ina Nusi?" Iliƴasis ya juyo cikin zafin nama ya ɗora takobinsa a wuyan Armad yana cewa, "Waye kai? Kuma a ina ka sanmu? Idan baka bani amsa ba yanzu zan tsinke maka kai." ** Yi comment da cikakken sunan jarumi/jaruma acikin wannan littafiMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 94: Tsumin Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Wata biyu kafin fitar Armad daga kurkuku. ** A can daular Infiriya, babban birnin Rafiya inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki, Cokali da Iliyasis ne suka shigo domin neman bayanin ƴar'uwarsu Nusi a wajen yarima Niyashi. Tafiya suke cikin yadda dakai da rashin tsoro suna tunkarar babbar fadar ƙasar inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki. Idan mai karatu bai manta ba yarima Niyashi shi ne wanda baya tsufa. Kuma shi ne wanda ya taimaki Nusi dasu Cokali tun suna ƴan shekara shida. Saboda haka ba abin mamaki bane da Iliyasis da Cokali suka yanke shawarar su fara neman Nusi daga wajensa. Koda bai san inda take ba zai iya taimaka musu da kwatance. Iliyasis ya tsayar da wani saurayi mai jan gashi dogo ya tambaye shi, "da ALLAH mu baƙin yarima Niyashi ne. Ko kasan inda zamu iya samunsa?" Koda jin tambayar sai saurayin ya haɗe rai cikin fushi ya ce, "yarima Niyashi? Amma banda ku baƙi ne saina sare muku kai. Faɗar sunan yarima mai jiran gado gatsal babban laifi ne idan baku sani ba." Iliyasis najin haka yai murmushi tare da sanyaya murya yana cewa, "afuwa. kamar yadda ka faɗa mu baƙi ne. Amma maiya kamata mu ce masa?" Saurayin yai shiru yana hucewa kafin daga bisani ya amsa da cewa, "shi dai wanda kuke nema shi ne alfaharin mutanen wannan daula. Kuma muna girmama shi da sunan 'Nazára' wanda hakan ke nufin mai ceto. Sannan kuma kamar yadda ake yiwa ƴaƴan babbar masarautar wannan daular shima ana saka masa kalmar 'Rafiyan' a farkon sunansa. Saboda haka daga yau ku riƙe sunansa 'Rafiyan Nazára' ɗan sarki Rafiyan Kaltume." Koda saurayin yazo nan a zancensa sai yai shiru yana kallon su Iliyasis domin ya tabbarar sun fahimce shi kafin daga bisani ya ci gaba da cewa, "Idan kuka miƙe wannan hanya tsahon tafiyar wuni ɗaya zaku tarar da ɗakin bauta na sarki Rafiya wanda ke daura da fada. Anan zaku tadda shi yana karɓar Tsumin-Izza." Saurayin na gama magana yayi nasa waje ba tare da sanin ko sun fahimce shi ba. Cokali yana niyyar finciko shi Iliƴasis ya ɗaga hannu. Haka suka ji gaba da tafiya suna tambayar sunan Rafiyan Nazára har saida rana ta faɗi. A lokacin da suka iso wani ƙaton shinge kewaye da sadaukai ma'aibota izza aƙalla dubu. Dukkaninsu sun durƙusa ƙasa sanye da fararen kaya tamkar suna bauta. A can tsakiyarsu wani saurayi ne zaune yake kallon sama. Abin mamaki ƙanƙarar Sanyin- babban-sihiri ce ke zuba a dai-dai kewayen wannan saurayi. Ba jimawa Iliƴasis ya gane saurayin ba wani bane illa Yarima Niyashi. Duk yadda akai wani babban sihirn ake haɗawa. Cikin zafin nama suka je suka samo fararen kaya tare da matsawa kusa da ɗaya daga cikin sadaukan dake wajen domin samo bayanai. Sunan abinda ke faruwa dai Tsumin-izza, kuma yawanci ana yiwa duk wani yarima mai jiran gado na kowacce daula domin su sami izza maɗaukakiya. Mutun zai zauna ya karɓi shekarun izza daga asusun izza na daularsu. Wato shekarun izza da kowacce daula ke tarawa ta hanyar fasahar kwangila. Ƙa'idar shi ne duk kwana ɗaya mutun zai karɓi shekarun izza dubu ɗaya, kuma mutun zai ci gaba da karɓa har zuwa sanda ƙarfinsa zai ƙare. Sai dai a ƙa'idar ba ci ba sha har a gama. A wannan rana kwanan Yarima Niyashi bakwai yana zaune yana karɓar wannan tsumi daga asusun izza na daularsa. A kwana a tashi saida yarima Niyashi ya kwashe kwanaki tara acikin wannan yanayi. Lamarinda ya bashi izza shekara ɗai-ɗai har dubu tara. Hatta manƴan sadaukai uku da ake ji dasu a dukkan faɗin daular izzarsu bata wuce shekaru dubu shida ba. Amma ga yarima Niyashi wanda dama yana da sirrin rashin tsufa a jininsa ya samu shekaru dubu tara. Lallai a wannan rana an ƙara haifar wani babban ma'aboci izzar wanda ya kamata a saka sunansa acikin manyan gobe. Saida akai ƙasaitaccen biki tare da gayyato kowanne sarki daga cikin sarakuna talatin da ɗaya dake daular Infiriya domin a taya yarima Niyashi da sarki Rafiyan Kaltume murna. Bayan komai ya lafa Iliyasis da Cokali suka samu damar ganin Niyashi. Labarin ɓatan Nusi bai masa daɗi ba kwata-kwata amma daga ƙarshe shawarar daya basu kawai shi ne su nemi Armad. Duk inda take zai sani. Sunyi mamakin yadda Niyashi ya riƙe sunan Armad to amma bawai sakawa Armad kuɗi da akai bane kaɗai yasa kowa ya sanshi ba. Babban abin shi ne yadda gimbiya Nostaljiya wadda ake ganin tafi duk wata yarinya kyau a duniya take kareshi a gaban kotu. Zuwa wannan lokaci kowa ya san cewa Nostaljiya ita ce ta ceci Armad a wajen cinikin bayi daya gabata, amma saboda matsayin baban ta a idon duniya ake so a rufe a ɗorawa Armad laifi. Abin mamakin shi ne har yanzu Nostaljiya taƙi bada shedar Armad shi ne mai laifi. Niyashi ya dubi su Iliyasis ya ce, "sarki Bihanzin baya son yaƙi ya ɓarke tsakaninsa da sauran sarakunan Jinzidal saboda haka yau kwana uku kenan ya bada auren Nostaljiya ga yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. Nan bada jimawa ba za'a saka ranar bikin. Ina tunanin duk inda Armad yake zai bayyana a daular Sisiya kafin wannan biki. Indai kuna so ku gamu dashi can zaku tafi." Koda jin haka sai Iliyasis ya kalli Cokali cikin jimami. Indai har da gaske ne maganar auren Nostaljiya da Deniz Bizaya lallai akwai yiwuwar Armad yaje daular Sisiya. To amma akwai matsaloli da dama da zasu iya afkuwa. Bayan sun ƙara ƴan kwanaki a daular Infiriya ƙarƙashin kulawar yarima Niyashi sai sukai azama suka nufi daular Sisiya. A lokocin da suka fito labarin auren bai baza duniya ba domin kuwa suma a bakin Niyashi suka ji, amma kafin su isa babban birnin Sisiya wato Jekis labari ya baza ko'ina. Kowa yasan gimbiya Zahra wadda akafi sani da Nostaljiya Nára zata auri yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. A wani mataki na hana afkuwar yaƙin da zaiyi asarar miliyoyin rayuka. To ta haka Iliyasis da Cokali suka iso daular Sisiya, kuma gashi ƙaddara tasa suna shigowa sun haɗu da Armad kafin su isa cikin gari. **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 95: Hankakan Mutuwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** ** Tun kafin Iliyasis ya janye takobinsa Cokali yai tsalle ya rungume Armad cikin murna. Saida Armad yai da gaske sannan ya kwaci kansa. Cokali ne ya fara magana. "Armad! Ashe da gaske nan zaka taho. Amma mai yasa kake tambayarmu ina Nusi bayan tare muka barku? Kar dai kace kaima bakwa tare." Nan take wannan tambayoyi suka jefa Armad cikin tunani. Ga dukkan alamu bama saiya tambaya ba, suma su Cokali basu san inda Nusi take ba. To amma abin mamakin shi ne yadda su Cokali suka san zaizo daular Sisiya. Armad ya dube su ya ce, "kuma nemanta kuke yi kenan? Rabo na da ita tun shekarar data wuce a gasar cinikin bayi ta Jinzidal. Amma yaya akai kuka san zanzo nan?" Nan take jikinsu Iliyasis yai sanyi. Suna tunanin samun Nusi a wajen Armad amma shima bai san inda take ba. Kuma yanzu dole sai sun bayyanawa Armad tsakaninsu da yarima Niyashi da kuma yadda akai suka gano zaizo wannan gari. Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Mu ƙarasa mu samu mafaka kafin muyi magana." Armad ya kyaɗa kai sannan dashi da Maikiro Inara suka bi bayan su Cokali izuwa cikin gari. Suna tafe suna kalle-kallen wannan ƙasaitaccen birni na Jekis wanda ke ɗauke da manya-manyan gine-gine masu samfuri kala-kala. Amma Cokali baiyi shiru ba, saida ya taɓo labarin faɗan Armad da yarima Niyashi da kuma yadda Armad yai nasara, domin labarin tuni ya baza ko'ina. Armad dai baice komai ba murmushi kawai yake. Ba jimawa suka iso harabar wani ƙaton gidan-kwana a farfajiyar wata kasuwa. Har yanzu dai Armad bashi da ko sisi saboda haka Inara ne ya biya masa kuɗin ɗaki kafin daga bisani duk su huɗun su hallara a ɗaki ɗaya domin tattauna matsalolinsu. Iliyasis yayiwa Armad inkiya daya tura Inara waje dan su tattauna cikin sirri amma nan take Inara ya buɗe baki ya dubi Iliyasis ya ce, "indai daga daular Maikironomada kuke kunsan ɗalibi baya barin gefen malaminsa a kowanne lokaci har sai sanda malamin ya yaye shi. Saboda haka ina cikin wannan ɗaki, amma nayi muku alƙawarin duk abinda zaku faɗa baza ajishi a bakina ba koda bayan raina." Cokali ya kalli Iliyasis tsahon ƴan daƙiƙu kafin su kyaɗa kai alamun amincewa. Iliyasis ne ya kwashe dukkan tarihin dake tsakaninsu da yarima Niyashi ya gayawa Armad sannan kuma ya gaya masa yadda suka san zaizo wannan gari da kuma labarin auren Nostaljiya. Armad yai shiru yana tunani tsahon lokaci. Dukkan abubuwan dake afkuwa harda yaƙin dake neman ɓarkewa tsakanin sarakunan Jinzidal ta dalilinsa ne. Amma babban abinda yafi damunsa shi ne zancen wannan aure da kuma ɓatan ƴar uwarsa Nusi. Wani irin ɓacin rai mai zafi wanda Armad bai taɓa jin irinsa ba ya taso masa a ƙirji a lokacin daya hango Nostaljiya a ɗakin yarima Deniz Bizaya. Tun bayan sanda Nostaljiya ta bayyana masa tana sonsa Armad bai taɓa tsayawa yayi wani dogon tunani akan maganar ba, kuma ko a jikinsa. Amma a halin yanzu da yaji zatai aure hankalinsa yayi mummunan tashi. Da farko yayi tunanin saboda baya so ayi mata auren dole ne amma ba jimawa ya gano cewa lallai shima akwai ƙaunar Nostaljiya acikin ransa. Cokali ya dubi Armad cikin al'ajabi ya ce, "idanun ka sunyi ja ja wur. Da gaske kana son ta." Armad yai shiru baice komai ba. Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Idan zaka bi shawara ta ka haƙura. Wannan auren shi kaɗai ne zai kare afkuwar yaƙi da asarar miliyoyin rayuka. Idan ka hana wannan aure lallai yaƙi saiya afku. Ina ganin kawai kazo mu juya ba tare da kun haɗu da ita ba." Armad ya ja dogon numfashi sannan ya ce, "idan da ɗaurin auren ne ya kawo ni da nabi shawararka, amma nemawa mahaifiyata lafiya ne ya kawo ni wannan daula. Kuma lallai sai naga Nostaljiya na nemi taimakon ta. Zarar mahaifiyata ta samu lafiya sai mu tafi." A wannan lokaci Armad ya kwashe duk abinda ya faru dashi bayan rabuwarsa dasu Iliƴasis ya gaya musu. Sannan ya nemi iznin su jirashi ya je yaga Nostaljiya kafin ya fito su bazama neman Nusi tare. Daga ƙarshe Armad ya dubi Inara ya ce, "kaima ka jirani anan naje na dawo." Nan take Inara ya sunkui da kai cikin alhini yana cewa, "ya shugabana kayi haƙuri amma lallai bazan iya barin gefenka ba har izuwa lokacin da zaka sallame ni a matsayin ɗalibi." Dama Armad yayi tunanin Inara zaice haka saboda haka kawai murmushi ya kyaɗa kai. Da safe bayan sun karya Armad da Inara suka nufi hanyar fadar birnin Jekis da niyyar ganin gimbiya Nostaljiya Nára. Ba jimawa suka tsinci kansu a wata siririyar hanya da zata kaisu izuwa fadar. Armad ya dubi Inara ya ce, "ka farkar da fasaharka?" Inara ya girgiza kai. "A'a." Armad yai murmushi tare da cewa, "nayi tunanin haka tunda daman baka da yawan shekarun izza. Amma ba matsala ba ce. Kamar yadda ka sani zaka iya kwarewa akan harkar fasahar aljanu, ko kuma akan takobi ko kuma akan ɗalasimai. Naga kana iya amfani da takobi da kuma fasahar aljanin wuta. Kai sani cewa wannan bazai isa ba. Indai kana so ka kware akan harkar izza saika haɗa da ɗalasimai sannan kuma daga baya bayan ka farkar da fasaharka sai ka zaɓi hanya guda ɗaya. Ina da malami mai suna Babara wanda ya kware akan harkar ɗalasimai. Zarar muka gamu dashi zansa ya farkar da fasaharka, amma kafin lokacin zan fara da koya maka dabarun amfani da takobi da kuma fasahar aljanu. "Kaga dai amfani da aljanu yana buƙatar shekarun izza. Kuma iyakacin yawan shekarun izzarka iyakacin ƙarfin fasahar da zaka iya amfani da ita. Da shekarun izza hamsin da ɗaya da kake dasu baza ka iya wuce mataki na farko ba daga cikin matakai shida na amfani da aljanu. Kuma indai...." Armad na cikin bayani yaji wani yanayin-izza mai tsananin ƙarfi da buwaya ya tunkaro shi ta baya. Tunda Armad yake bai taɓa jin irin wannan yanayin izza ba. Idan a misali zai iya kwatanta girman yanayin-izzar duk daya taɓa ji a matsayin kofin ruwa ɗaya to wannan izzar takai girman tekun maliya. Bawai kuma girman izzar ne yasa Armad ya fara gumi ba, tsananin zafi da muni da azabar dake cikin izzar ne yasa Armad yaji tamkar ruhinsa zai fashe. Kafin Armad yai wani motsi Inara ya faɗi ƙasa sumamme. Yana juyawa bayansa wani ƙatoton hankaka baƙi-ƙirin mai ido kwaya ɗaya tak ya kawo masa wafta. Armad ya manta da cewa zai iya juyewa izuwa walƙiya ya baje a ƙasa wannan hankaka ya wuce. Kafin ya miƙe hankakan yayiwo kwana. Cikin sauri Armad ya kirawo Hannun-Aradu ya fuskanci wannan hankaka. To amma bisa mamaki sai hankakan ya tsaya cak yana kallon Armad sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga bisani ya juya ya ɓace. Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wani labari da mahaifiyarsa ta taɓa bashi akan wata ƙabila wadda aka manta da sunansu. Wannan ƙabila sune asalin tsafin Sanyin-Babban-Sihiri. Dukkan tsafinsu suna yinsa da baƙin aljanin-hankaka wanda ake kira da HANKAKAN- MUTUWA. Acewar wannan labari hatta sarki Eyriyon Wilbafos da sarki Kuyurussa'ayi Ururu baza su iya sawa wannan hankaka ya durƙusa musu ba. Shi yasa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suka halaka wannan ƙabila. Kuma tun daga wannan rana babu wanda ya ƙara ganin Hankakan- mutuwa a doron ƙasa. Amma indai Armad ba mafarki yake ba lallai yau yaga hankakan-mutuwa da idonsa. **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 96: Shiga Fada Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Koda Armad yaga wannan baƙin hankaka na neman ɓace masa saiya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya cilla Inara aciki. Sannan yayi amfani da fasahar Kaban'shísu ya ɓace daga inda yake tare da bayyana acan nesa dai-dai ƙasan inda hankakan ke tafiya a sama. Hankakan na ganin haka ya sha kwana tare da ƙara azama wajen iyo akan iska yana ƙoƙarin gujewa Armad. Amma murmushi kawai Armad yayi tare da barin hankakan yayi nisa kafin ya ƙara yin amfani da ɗalasimin Kaban'shísu ya bayyana a ƙasansa. Sannu a hankali Armad yana bin wannan baƙin hankaka sai kawai ganinsa yayi a kusa da fadar sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Abin mamaki sai wannan hankaka ya ƙara shan kwana yabi jikin katangar wannan fada ya nufi yamma. Armad nada ragowar ɗalasimai biyu kacal saboda haka ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kama wannan hankaka idan bai tsaya ba. Yana cikin tunani ya hangi hankakan ya tsaya a ƙarshen katangar ta ɓangaren yamma. Har wani waiwayo wa yake yana kallon Armad tamkar yana jiransa. A fusace Armad ya yanke shawarar yadda zaiyi ya kama wannan hankaka. Ya buɗe baki ya kira ɗalasimin Kaban'shìsu amma a wannan lokaci saiya canja maimakon ya bayyana a ƙasa saiya bayyana akan katangar wannan fadar dai-dai gefen wannan hankaka. Yana bayyana ya miƙa hannu ya damƙe jelar hankakan tare da finciko shi da niyyar jefashi cikin zobensa na sihiri. To amma bisa mamaki sai Armad yaji tamkar ya finciki dutsen uhudu. Ko motsi wannan baƙin hankaka baiyi ba. Hasalima kaɗa jelarsa kawai yake ba tare da ya waiwayo ya kalli Armad ba. A fusace Armad ya sanya ƙarfin shekarun izza dubu a hannunsa ya finciko hankakan dashi. Amma bisa mamaki ko motsi baƙin hankakan baiyiba. Armad ya haɗe gira yana tunanin maiya kamata yayi domin dai bazai iya amfani da hannun-aradu ba a wannan hali. Koba komai duk wanda yaji ƙarar saukar aradu wajen zai taho yaga ganshi, wanda hakan zai tona masa asiri. Armad na cikin tunani yaji jelar hankakan dake hannunsa ta motsa ta fincike shi. Kafin yayi wani abu hankakan ya jashi ƙasa daga saman wannan katanga sun faɗa cikin babban gidan sarautar daular Sisiya. Saida suka kwashe daƙiƙu suna faɗawa sannan suka isa ƙas, badan Armad yayi sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ba da tuni ya karairaye. Kafin ya miƙe hankakan ya tashi ya gudu. Armad ya tsaya yana nazarin wannan katanga. Kaurinta yakai ƙafa goma, kuma dukkaninta da duwatsu aka sarrafa ta. A tsaye kuwa takai zira'i casa'in. Lallai koda kuɗi ɓarawo bazaiyi ƙoƙarin haura wannan katanga ba. Yana cikin haka yaji motsin tafiya daga nesa haɗe da maganganu wanda sukai kama dana masu tsaron fadar. Nan take ya rufe ido domin jin yanayin izzarsu da kuma adadinsu da kuma ta inda suke tahowa. Amma bisa mamaki abu na farko da Armad ya fara ji wata sanyayyar izza ce mai ni'ima da faranta rai daga can gefensa ɓangaren arewa. Ya waiwaya ɓangaren tare da buɗe ido. To amma wajen cike da yake da bishiyun goba dana inubi wanda sukai masa duhuwa tayadda baza'a iya ganin wanda ke ciki ba daga nesa. Amma bisa mamaki Armad ya gane waye aciki. Murmushi kawai yayi tare da nufar wannan waje kai tsaye. Ƙanshi ne ya fara yi masa sallama, ƙanshin da yasha banban dana turare. Wannan ƙanshi mutun ɗaya ne kacal yake da irinsa a duk faɗin duniya. Armad ya tsaya kimanin taku uku kafin ya ƙarasa. Nan fa zuciyarsa ta fara bugawa kamar zata fasa ƙirjinsa. Bashi da cikakkiyar masaniyar maike faruwa amma yaji gumi na ƙoƙarin kwace masa. Sanyayyar murya wadda Armad ƴasanta sarai ita ce tayi masa sallama. "Mai yasa ka tsaya?" Armad ya fashe da murmushi ba tare da yasan dalili ba, ya amsa da cewa, "Mai yasa kike tsaye a duhu?" Muryar ta amsa masa da cewa, "ka bani kunya daka kasa kama hankaka guda ɗaya tak." Armad ya fashe da dariya yana cewa, "dama ke kika turoshi. Nasan zaki aikata. Amma meye alaƙar ƙabilarku da Hankakan-mutuwa?" Muryar taja dogon numfashi tare da yin ƴar ƙaramar dariya sannan ta fito daga cikin duhun. Kyakkyawar sura wadda babu kamarta ce ta bayyana. Wato gimbiya Zahra wadda aka fi sani da Nostaljiya Nára. "Baka yarda zoben dana baka ba kenan." Armad ya kalli zoben dake hannunsa sannan ya ɗago kai ya dube ta ya ce, "kona mutu dashi za'a binne ni." Nostaljiya na sanye da doguwar riga mai kwalliya da bezar gashin farin aku. Jikinta kamar lokaci na ƙarshe da Armad ya ganta acikin wancan kogo haske kawai yake yana bada ƙawa da armashi. Gashinta na kwance har gadon bayanta babu abinda yake sai sheƙi da ƙanshi. Babu kalmar da tafi dacewa da wannan gashi illa mudubi domin tsaf zakai kwalliya kana kallon kanka acikinsa. Armad ya buɗe baki zaiyi magana sai yaji masu gadin fadar sun matso kusa saboda haka ya fara lisaafin neman wajen ɓuya. Koda Nostaljiya ta fuskanci haka saita jashi izuwa cikin duhuwar wannan bishiyu. Da farko Armad yayi tunanin ɓuya zasu yi har sai ma'aikatan sun wuce amma sai kawai yaga sun wuce izuwa wata siriyar hanya wadda ta ɓulle izuwa wani shinge mai kama da lambu. Baki a buɗe Armad yaci gaba da kallon ikon ALLAH a yayinda Nostaljiya take jansa izuwa tsakiyar wannan fada. Abin mamaki ko mutun ɗaya basu gani ba a hanyarsu. Amma idan akai duba da cewa wannan fada gidan Nostaljiya ce kuma anan ta taso to ba abin mamaki bane. Ba daɗewa Armad ya tsinci kansa a wani kewayayyan sashi mai dogayen ɗakuna wanda aka gina bangwayensu da gilasai da yaƙutu. Dukkan wajajenda suka wuce babu wanda yakai wannan waje kyau da armashi. Hatta ƙasar wajen da lu'u-lu'u aka shimfiɗe ta. Nostaljiƴa taja Armad ɗaya daga cikin manyan ɗakunan dake kewaye da wajen. Suna shiga Armad ya tsinci kansa akan wani farin gilas da ruwa garai-garai yana gudana a ƙasansa. Kifaye masu haske kyawawa suna ta wasa acikin ruwa. Daga can gefe kuma wani ƙasaitaccen

Chapter 11 of 13