Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 13
tanada domin yin cinikin bayin dai wani ƙatoton ɗakin taro ne mai hawa-hawa har guda uku. A hawa na farko akwai mutane gama gari na zaune, a hawa na biyu kuma ƙananun sarakuna ne, a hawa na uku kuwa anan sarakunan Jinzidal da muƙarrabansu suke. Daga gaban filin akwai dandamali mai ɗan tudu. Akansa akwai wani ɗan akwati da akayi da gilashi. Ba sai ma ka tamabaƴa ba, kana gani kasan acikin akwatin gilashin ake saka wannan bayi domin gabatar dasu ga maiso. Taro yayi taro kuma babu wanda bai hallara ba, saboda haka ba jimawa aka fara shigo da bayi kala-kala ana gabatar dasu acikin wannan gilashi ga mai buƙata. Mai gabatarwar wani ɗan dogon mutun ne mai yawan ƙasumba. Muryarsa tuni ta dusashe, koda yake dai dama ba zaƙi ne da ita ba. Bayan an gabatarda sama da bayi ashirin saiga wani saurayi nan an fito dashi. Yana tafiya dakyar cikin ankoki na baƙin ƙarfe. Duk jikinsa jini ne, sannan kuma rigarsa ta yayyage. Aka shiga da wannan saurayi cikin wajen nan, sannan alƙalin ya saka masa kuɗi kimanin kuɗin Ayrid dubu sittin kacal. Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos. Ga dukkan alamu aljani Netti da aljani Kalkutu saida suka saka wasu ɗalasimai a jikin Armad tayadda babu wanda zai iya gane shi. Domin lallai da mamaki ace jaruminda yai suna a gasar Jinzidal ta wannan shekara amma duk taron dubunnan jama'un nan dake wajen cinikin bayin babu wanda ya gane Armad. Sai dai kuma wani abin Alajabi ana shirin siyarda Armad ga wani attajirin birni kawai sai aka ji murya daga cikin wajen hawa na uku, wato wajen da sarakunan Jinzidal ke zaune. Wannan murya ba wata bace illa muryar gimbiya Nostalgiya. To koma dai ya ake ciki idanun Nostalgiya sun gano wannan saurayi, kuma ga dukkan alamu babu yadda za'ai aƙi siyar mata dashi. Ana jin muryar daga inda take duk wani mai so yai jayayya akan cinikin Armad ya fasa. Lallai babu wanda zai iya jada sarakunan Jinzidal koshi wane ne. Armad na cikin wannan gilashi yana rantsuwa da dukkan abinda ya taɓa isa ai rantsuwa dashi cewa lallai tunda aka saka shi acikin wannan gilashi to kuwa sai yaga bayan Jinzidal. Kuma lallai ya maida shi dalilin rayuwarsa cewa sai ya kawo ƙarshen ranar da za'a ringa saka mutane acikin keji kamar wasu kaji ana siyar dasu. Armad dama can ya tsani harkar cinikin bayi, to amma bai taɓa sanin haka waɗanda ake siyarwa a matsayin bayi suke ji ba sai a wannan lokacin. Ai kuwa nan take Armad yai rantsuwa ya ƙara rantsewa cewa sai yaga bayan dukkan sarakunan Jinzidal da dukkan Ururu waɗanda suka kafa harkar cinikin bayi. Sai yaga ranar da zai kawo ƙarshen komai. Sai ya hana dukkan cinikin bayi kafin ya daina numfashi. A wannan lokaci Armad yaji jinin jikinsa ya fara balbalin wuta yana soyuwa saboda baƙin cikin rashin ƙarfin Izzarsa. Domin babu wanda Armad yafi zarga a abubuwan dake faruwa dashi irin kansa. Armad yana zargin kansa da rashin ƙarfin Izza, da rashin tsayawa ya koyi abubuwa a lokacinda yayarsa taso ta koya masa. Amma yanzu komai yazo ƙarshe. Yana da ragowar wata ɗaya daya rage masa ya nemo Tarifil-fakta sannan kuma ya fara shirye-shiryen ruguza dukkan sarakunan Jinzidal da Ururu. A taƙaice dai a wannan rana ta sha tara ga watan goma na shekarar 1853 bayan Amri Armad yai alƙawarin yin faɗa da dukkan duniya ya kawo sabon tsari wanda bai yadda da cinikin bayi ba. Ai kuwa abin alajabi, tamkar wani sirri acikin jinin Armad dama jira yake Armad ɗin yayi wannan rantsuwa, sai nan take ya fara juyawa. Armad yaji idanunsa suna zafi tamkar ana tsire su. Gashin jikinsa tamkar anan tsitstsige geshi saboda zafi. Bada ban bashi da ƙarfin yin ihu bama da tuni ya kwalla ƙara. Nan take ya fara zubarda gumi ta ko'ina. Idan ka ganshi fassarar kawai da zakai ita ce yana tsoron mai zaije ya tarar a wajen waɗanda suka siyeshi. Sai dai kuma abinda shi Armad da dukkan ƴan kallo basu sani ba shi ne a wannan lokaci ƙarfin da Armad ya gada na zuri'ar Wilbafos a jininsa yake farkawa. ____ Ƙarfin Izzar jarumin jarumai Armad Wilbafos zai bayyana a babi na gaba, ko wacce irin Izza ce? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 55: Sabon Farin wata Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos _____ *** Idan ka/kin manta abubuwan da suka faru a babi na takwas zuwa na sha biyu to ya kamata ku duba, domin kuwa abubuwan zasu fara dawowa yanzu. *** Wata ne daren sha bakwai a sararin samaniya, hasken wannan wata ya cika ko'ina a sararin samaniya da sauran ƙasashen duniyar ƙasa bakwai. Kwatsam sai aka wayi gari hasken wannan wata ya fara dusashewa yana duhu. Idanun duk wani abu mai rai ya koma sama da kallo. Ba jimawa dukkan hasken wannan wata ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke wuta. Da dama mutane sun fara tunanin zazzaɓin wata ke faruwa kuma tuni an fara shiga zulumi, malaman addinai da dama suma sun fara nasu aikin. Kwatsam sai aka ga wannan wata ya dawo ya fara yin haske, sai dai kuma hasken nasa ba irin hasken da aka saba gani bane. Wannan hasken ruwan ƙasa ne mai launin toka. Ba jimawa mutane gama-gari suka fara shiga tashin hankali ana raɗe-raɗen cewa masifa ce zata sauka. Amma tsofaffin ma'abota Izza wanda suka ga jiya suka ga yau sun san sarai maike faruwa. A daular sarkin Jinzidal sarki Bihanzin mai dauwamammen ciwo wani tsohon mutun ne ya farka daga cikin wani akwatin gawa, yana buɗe idonsa wata Izza wadda girmanta ya haura shekaru dubu goma ya cika wannan ɗakin. Wannan mutun dukkan jikinsa a bushe yake, fatar jikinsa tayi ɓawo-ɓawo, bashi da maraba da gawa. Amma duk da haka sai gashi ya buɗe bakinsa yana magana, "Jinin gidan Wilbafos ya bayyana." Yana gama magana ya koma ya rufe idonsa ya ci gaba da bacci. Wannan magana daya faɗa babu inda ta isa sai kunnen sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Haka dai irin wannan mutun mai kama da gawa ya ƙara tashi a daular Denizawa dake ƙarƙashin ƙasa ya kuma ƙara faɗar irin abinda na farkon ya faɗa. A can wani sashi kuwa na duniya dake kan wani siririn tsibiri, wani mutun ne riƙe da AL'ƘURANI mai girma a hannunsa. Idanun wannan mutun daɗe a rufe kuma babu wamda zai iya kwatanta shekarunsa a duniya. Yana buɗe idanunsa saiga irin hasken wannan wata aciki. Murmushi kawai yayi irin na mutanen Sannan ya ƙara rufe idanunsa. Haka ire-iren wannan abubuwan al'ajabi suka ci gaba da faruwa a dukkan dauloli na faɗin duniya. Wannan sabon hasken farin wata kuwa ruwan ƙasa ko ajikinsa, haka ya ci gaba da ƙaruwa yana game duniya. A tsakiyar wannan ɗakin cinikin bayi kuwa wani saurayi ne acikin gilashin da ake tallan bayin nan dashi. Saurayin ya miƙe ya tsaya a tsaye yana kallon dukkan mutanen dake wajen. Duk wanda ya ganshi zai iya tunanin tsoron siyarwa ne yake damunsa. Amma ba jimawa dukkan hasken wannan farin wata mai ruwan ƙasa da ratsin toka ya fara raguwa a dukkan sassa na duniya yana curewa a waje ɗaya. Kan kace meye wannan dukkan hasken ya gama curewa a waje ɗaya sannan ya fara sakkowa ƙasa a hankali a hankali har saida yazo dai-dai idon wannan yaro dake cikin wannan gilashi, sannan dukkaninsa ya shige cikin idon wannan saurayi. Wannan saurayi dai ba wani bane illa Armad Wilbafos. Nan da nan idanunsa suka fara haske suna bada launin hasken wannan wata wato ruwan ƙasa mai ratsin toka. Komai da yake faruwa a idon kowa ya faru, saboda haka a dai-dai wannan lokaci wannan mutumi dake bada rahoton akan bayin da aka saka acikin gilashin ya fara karkarwa yana matsawa baya. Armad ya kalli wannan ankoki dake jikinsa, nan take dukkan ankokin suka zube ƙasa, sannan dukkanin ciwukan jikinsa suka warke nan take. Sannan ya ɗaga idonsa ya kalli jikin wannan gilashi, ai kuwa hasken nan ruwan ƙasa na dukan gilas ɗin ya tarwatse. Armad ya bayyana a waje kamar wani ɗan ƙaramin bajimin aljani. Inda ya haska idonsa akan dukkan mutanen dake cikin wannan waje, nan take da dama daga cikinsu suka fara jin karkarwa suna rawar ɗari tamkar wanda akace mutuwa ce tsaye ke kallonsu. Koda yake a wannan lokaci Armad bashi banbanci da mutuwar kanta. Idanunsa kawai haske suke suna fitarda tsananin azabar yaƙi da ƙarfin Izza. Armad ya miƙa hannunsa sama, nan take wata taga ta buɗe akam iska inda ya miƙa hannu ya zaro takobinsa ta Wilbafos. Abin mamaki sai ga taurari guda biyar a saman takobin. Armad yai murmushin girma bayan da yaga adadin taurarin dake kan takobin kuma ya tuna wanda suke kai a lokacin da yayi faɗa Ikenga. Lallai Armad ya samu gagarumin canji a jikinsa wanda keda ban al'ajabi. Tun daga kan hawa na farko har zuwa na uku kowa yayi shiru ba'a cewa komai. Ana haka kawai sai aka ga Armad ya ɗaga takobinsa ya nufi kan waɗannan bayin da aka riga aka siyar. Ko ba'a tambaya ba kasan nufin Armad ya kwance su ya kuma ƴantar dasu a gaban dukkan duniya. Wanda zarar Armad ya aiwatar da wannan abu, to dai-dai yake da fito na fito da dukkan ƙabilar Ururu da kuma Sarakunan Jinzidal biyar. Kuma lallai a wannan lokaci zaka ga ma'abota baƙaƙen ido sun fara sauka daga ƙasa ta farko domin kama Armad. Lallai hatta sarakunan manyan gidajen Ururu goma sai sun sauka idan Armad ya aikata wannan abu. Domin wannan shi ake kira da fito na fito da Ururu. Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne kwatsam gimbiya Nostalgia ta bayyana a gaban Armad tana mai murmushi. Babi shiri Armad ya tsaya, kuma duk da ɓacin ran da yake ciki zuciyarsa bata fasa tunano masa wannan kyakkyawar gimbiya ba da suka haɗu a shekarun baya ba. Gimbiyar da ta ceto rayuwarsa sau adadi da dama tun bai ma fuskanci yadda yanayin duniya ke gudana ba. Armad yana tuno sanda ta hanashi faɗawa rami da kuma hawayenta guda ɗaya daya faɗa idonsa. Sannan kuma lallai Armad yana sane da wannan sirri daya jiyo musu acikin wannan allon tsafi, sirrin dazai rikita duniya baki ɗaya. Armad bai manta da fasahar Izza ta musamman, wadda ake iya duba cikin kwakwalwar mutun aga mai yake tunani ba wadda wannan gimbiya mai suna Zahra wadda akewa laƙabi da Nostaljiya take da ita ba. "N.....nostaljiya? Mai kike anan, babu ruwanki da tsakani na da wannan mutane da suke so su ringa bautar da bil adama. Idan kuma kika shiga tsakani na dasu, to lallai zan manta da duk wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninmu na yaƙe ki, sannan kuma...." Armad yana magana amma dole ya tsaya cak, badan komai ba sai dan saboda kwalla daya gani acikin idanun Nostaljiya bayan da tayi arba da kayan jikinsa a yayyage, kuma duk sunyi faca-faca da jini. Armad ya buɗe baƙi zai ci gaba da magana, amma a wannan lokaci yaji hayaniyar ƴan kallon dake wajen suna cewa, "Kai.... Wai wannan yaron ba shi ne Armad Djinn ba daya fafata a gasar Jinzidal ba? Lallai shi ne, ya akai da bamu gane shi ba? Wai ya akai ma za'a siyar dashi a matsayin bawa? Mai yake faruwa?" To ga dukkan alamu an cire dukkan hijabin dake hana wannan mutane gane Armad, kuma lallai a wannan lokaci kowa ya gane wanene Armad. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 56 & 57: Nostojiya nara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ _______ Nan take Nostalgiya ta juya ta kalli waɗannan ƴan kallo da suka zo wannan cinikin bayi, ai kuwa daga cikin girman Izzar ta sai ga SANYIN BABBAN SIHIRI nan ya fara sauka acikin wannan waje a yanayinsa na ƙanƙara ruwan toka. A wannan lokaci ya fara bin jikin dukkan mutanen dake wajen, kuma duk wanda ka kalla babu abinda zaka gani sai ƙanƙara ruwan toka nannaɗe a jikinsa. Nostalgiya tai ƙaraji na ɓacin rai, ta ɗaga takobinta sama takai sara kan iska. Ai kuwa saiga wasu aljanu nan guda biyu sun bayyana suna ƙoƙarin kare wannan sara mai ɗauke da Izzar sanyin babban sihiri. Abu ne sananne idan ka ɗauke Farar-laya babu abinda aljanu ke tsoro irin Sanyin babban sihiri. Nostalgiya tasan haka kuma ga dukkan alamu tayi niyyar halaka wannan aljanu ne baki ɗaya. Inda tayi tsalle sama ta dira akan ruwan cikin wannan aljanu da ƙafafunta ma'abota Izza. Yau waye ya isa ya jada ƴar gidan Bihanzin mai Dauwamammen Sara. A wani irin yanayi mai kama da hauka da tsananin ɓacin rai Nostaljiya ta hau saran wannan aljanu baji ba gani. Jinin aljanun yayi sama, kan kace meye wannan yayi faca- faca da ko'ina. Ko dama ɗaya bata bawa wannan aljanu ba na kare kansu ba kafin ta aikasu lahira. Ta juyo da idanunta ga wannan bayi da aka riga aka siyar, idanunta na sauka akansu nan take duk ankokin dake ɗaure dasu suka zube a ƙas. Armad na gefe yana kallon tsananan ɓacin rai wanda har yaso yaɗan ɗara nasa. Abu na gaba daya ji shi ne hannun Nostaljiya ta jashi sun tashi sama inda suka fice daga cikin wannan waje suka tashi sama. A can cikin wajen hawa na uku kuwa manyan jarumai ne masu wakiltar sarakunan Jinzidal. Daga ɓangaren dama jaruman sarki Rafiya ne guda uku. Dukkaninsu Izzarsu ta haura shekaru ɗubu biyar. Kai ɗaya daga cikinsu ma shi ne wanda muka gani a wannan Jinzidal wadda Armad ya taka rawar gani, wato Asifu wanda akewa laƙabi da Ruwan Bala'i. Asifun ne ya fara magana yana cewa, "Wannan yarinya bata da hankali. Bansan maike faruwa ba, amma ga dukkan alamu sa'a tana tare damu domin kuwa akwai alamun soyayya a idanun wannan yarinya, kuma wannan soyayyar dake idonta ta rufe mata ido ta aikata abinda zai taimake mu mu ruguza daular babanta baki ɗaya. Saboda haka baza mu bita ba, kuma baza muyi mata komai ba anan. Mu barta ta gudu dashi wannan yaron. Kaga da haka zamu samu damar cin galaba akan tsohon ɗan adawar mu wato babanta Bihanzin. Tunda kunga duk laifin daya faru anan kawai saimu ɗora shi akan babanta kuma rubuta a rubuce mu aikewa da Ururu." Asifu na zuwa nan a zancensa yai dariya mai cike da farin cikin, sannan ya ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryarsa domin kada sauran mutanen dake wajen suji, "Ban taɓa tunani babbar dama kamar wannan zata samu ba a garemu. Lallai wannan babban labari ne muyi maza mu tashi mu gabatar dashi izuwa sarki Rafiya." Sauran manyan ma'abota Izzar guda biyu dake tare dashi suka girgiza kai alamun amincewa. _______ Babu inda gimbiya Nostalgiya ta sauke Armad sai cikin wani sihirtaccen kogo. Wannan kogo dai waje ne na musamman wanda ke cikin daular babanta sarki Bihanzin, kuma babu wanda yasan dashi inba ita. A sau da dama idan tana so ta nutsu ta tuno babarta wadda ta mutu wannan kogo take zuwa tayi kwana da kwanaki tana hutawa tana kewar mahaifiyar tata. Acikin kogon dai akwai ƙorama mai bada sanyi mai ciƙe da ni'ima da annushuwa. Ga kujeru da shimfiɗu na alfarma, ga kuma kayan ci da sha duk na sarakuna wanda Armad ma bai taɓa yin tsinkaye da suba. Tana ajiye Armad ta ɗakko wata sabuwar rigarta ta wadda akaiwa ado da dinare ta fara goggoge masa datti da jinin dake jikinsa. Har a wannan lokaci ta kasa ɗago kai ta dubi Armad saboda hawaye da tausayin dake idanunta. Armad ɗin shima ya kasa cewa komai, abu ɗaya dai daya sani shi ne abinda ta aikata a wajen cinikin bayin can lallai saiya jawo wa babanta babbar matsala. Saboda haka bai san mai zai fara ce mata ba. Tunda dai saboda shi take duk wannan abun, kuma koma mai ya same ta shi ne zai zamo shila. Amma abu guda ɗaya daya kasa ganewa shi ne mai yasa take wannan abubuwa. Wai anya kuwa tana cikin hankalinta kuwa? Sai dai kuma Armad ya tuna ba wannan ne lokaci na farko ba data fara sadaukar da rayuwarta ba domin ta ceto shi. Yana tunano lokacinda zai faɗa wannan rami kuma wannan dordor ya so ya halaka ta, amma taƙi sakarsa. Can bayan wani lokaci Armad ya riƙe hannunta ya tsayar da ita, sannan ya ɗago da kanta domin yaga maike faruwa acikin idanunta. Amma bisa mamaki sai kurum Armad ya ƙara arba da irin sak abinda ya taɓa ji a shekarun baya, wato yaji tamkar ya santa a wani zamani mai tsaho daya gabata. Nan da nan ya cika ta yana haki. Yau dai koma mai ake ciki sai yaji amsar dukkan tambayar daya daɗe yana so yayi mata. Nostalgiya taja dogon numfashi sannan ta goge fuskarta da hankici. Ta miƙe daga inda take tana murmushi sannan ta fara da cewa, "Ka taɓa gani na babu hijabi?" Tambaya ce amma ga dukkan alamu ba amsa take nema a wajen Armad ba, domin kuwa tasan cewa bai taɓa ba. Shima Armad ɗin yasan haka, kuma nan take ya fara ƙinƙina a lokacinda yaga kamar tana nufin cire rigar dake jikinta. Muryarsa na rawa yana cewa, "Ehm.... Tsaya.....tsaya..... Ba saikin cire komai ba, na taɓa....." Kawai Armad yaji Nostaljiya tasa hannu ta doke shi aka. Nan da nan ya haɗe gira, "Laifin me kuma nayi miki harda duka?" Nostalgiya ta ɓata rai matuƙa tana mai cewa, "Mai ka ɗauke ni, a gaban naka zan cire kaya. Kawai kai mana shiru kaga mai ake yi mana, a'a!" Bayan data gama magana saita durƙusa a gabansa tana mai murmushi tana lallashinsa, "Kayi haƙuri na dake, ba zafi ko?" Armad yana rasa mai zaice, tambayar kansa kawai yake, towai mai take nufi ne? Waishin mai ake ciki nema? Ai kuwa ba jimawa Armad yaga dukkan wannan kogo ya cika da wani irin haske mai matuƙar ƙayatarwa. Da farko Armad yayi tunanin wata fitilar aka kunna, amma a lokacin ne Nostaljiya ta kashe fitilar dake ɗakin amma hasken kawai ƙara ƙaruwa yake. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan haske daga jikinta yake fitowa. Fatar ta gaba ki ɗaya ta juye izuwa wani abin kyalkyali da walƙiya mai tsananin kyawu. Armad ya fara tunowa da labarai daya karanta na tatsuniya akan wata wadda ake kira da Lasina Naitingele wadda aka ce tafi kowa kyau a duniya. Nan take Armad ya gano cewa wadda take gabansa lallai ta ma fita kyau. Idanun Nostaljiya na kaɗawa da tsananin ƙauna da tausayin Armad. Nan da nan Armad yaji jikinsa ya mutu murus. Dama Nostaljiya tama ɗan fishi tsaho saboda haka koda ta jashi ya tashi ya tsaya a gefenta ya kuma kalli dattin dake jikinsa sai yai matuƙar raina kansa. Lallai Armad ya tabbatar babu wata mai kyawun wannan yarinya a duniya. Fuskarta madaidaiciya ce kuma Armad bazai iya siffanta ta taba sai dai kawai yasan cewa wannan fuska ta ƙunshi duk wani abu da kyau zai iya bayarwa. Jikinta ya ingantu matuƙa sama da na duk wata budurwa da Armad ya taɓa gani, ba shiri Armad ya fara kamuwa da surar wannan mace dake gefensa. Nostaljiya ta fuskanci hakan sabida haka kawai tayi murmushi ta kuma ja hannun Armad izuwa ƙarshen wannan kogo. Suna zuwa ƙarshe suka ga wata ƴar ƙaramar ƙofa. Suna shiga ƙofar suka tsinci kansu a wani ƙaton lambu mai bada yanayin ni'ima da annushuwa. Armad ya fahimci cewa ashe wannan kogo a tsakiyar lambu yake. A wannan lokaci ne Nostaljiya Sisiyu da Armad Wilbafos sukai tafiya a matsayin saurayi da budurwa a karo na farko a tarihi. Nostaljiya ce ta fara magana, "Bari na fara, nasan kana da tambayoyi da yawa, amma idan na gama wataƙila ba sai kace komai ba. "Kaga dai mahaifina Bihanzin ya daɗe yana neman hanyar da zai ruguza wannan Rukunai na Jinzidal guda biyu. Amma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba indai baka da ƙarfin Izzar da zaka iya cin galaba akan sauran sarakunan Jinzidal biyar ba. Hakan ne ma yasa zaka ga ma'abota Izza wanda suke ƙin jinin cinikin bayin amma dole sai dai suyi biyayya saboda al'amarin na girman Izza ne da kuma girman runduna. Babu wanda ya isa ya fito shi shi kaɗai ya ce yau zaiyi fito na fito da dukkan manyan ma'abota Izzan dake kare cinikin bayi. Hatta mahaifina wanda ɗaya ne daga cikin sarakunan Jinzidal bashi da wannan ƙarfi. Kai hasalima bari kaji, na taɓa tambayar mahaifina akan irin ƙarfin Sarakunan Jinzidal yake cemin hatta daular Ururu da kanta baza ta iya yin fito na fito da dukkan sarakunan Jinzidal ba, koda kuwa zasu yi nasara to kuwa zasu rasa sama da rabin rundunarsu da mutanensu wanda kuma Ururu baza su yadda da hakan ba. Hakan nema yasa zaka ga Ururu na bawa wannan sarakuna na Jinzidal ƙima da mutunci sosai da sosai. "Mahaifina yayi bincike ya gano cewa idan ka ɗauke Tarifil-fakta wanda har yanzu ba'a san waye ba ko kuma a ina yake ba, akwai wani mutun ɗaya wanda ya taɓa yin faɗa da Ururu kuma yaci nasara. Wannan mutun kuwa shi ne Bayajidda, kuma shi ne wanda kaji muryarsa a cikin wannan gari dana ceto ka daga ciki. "To a binciken mahaifina ya gano cewa Bayajidda ya bar wani allon sihiri. Tun daga ranar da mahaifin nawa ya gano wannan allo yake ta bincike a kansa har zuwa wannan rana da muke magana. Wanda idan kai lissafi shekaru dubu ɗari da uku kenan, kaga shekaru tamanin da biyar kenan kafin a haifeni. "Mahaifna ya bani labarin yadda ya gano sirrin wannan allo amma a yanzu bamu da lokacin da zan baka wannan labari domin kuwa ba ƙaramin dogon labari bane. Amma dai kai sani cewa wannan allo shi ne dai wannan allo wanda muka baka kaji mana muryar Bayajidda aciki shekaru da suka gabata. Mahaifina ya gano cewa sirrin Izzar da yake buƙata ya rusa Jinzidal dashi yana cikin wannan allo, kuma kaida kaji wannan murya da kunnenka zaka fi kowa gane mai nake nufi da wannan Izza. Dalilin da yasa kaga mun neme ka domin kaji mana wannan murya ta dake cikin wannan allo shi ne babu wanda ya isa yaji wannan murya sai wanda yaji muryar Bayajidda a cikin wannan gari wanda kuma dani da ƴan uwana duk mun kasa, hasalima ni kaɗai nake iya shiga garin amma nima ɗin ban taɓa jin komai ba. Ranar dana fara ganinka kwance cikin jini acikin wannan gari nasan cewa ƙaddararka da tamu ta riga ta haɗu a wannan duniya kuma babu wanda zai iya rabata domin kuwa kai kaɗai zaka iya jiyo mana sirrin wannan allo wanda shi kaɗai muke buƙata mu cimma burinmu. "Da farko da na ganka acikin garin nan jikinka yana ci da wuta kawai na ceto kane sabida ina so kazo ka fassara mana wannan allo. Amma daga baya dana karanta tunaninka naga kana so ka taimaki mahaifiyarka ne sai naji tausayin ka ya kamani. Nakan so duk wanda naga yana son ya taimaki iyayensa. "Amma a lokaci na farko dana taɓa jikinka sai naji tamkar na taɓa ganinka a wani zamani mai tsaho daya gabata, harma inajin cewa dani da kai mun taɓa soyayya wadda aka rubuta a tarihi. Da nayi zaton ni kaɗai nake jin hakan idan na taɓa jikin naka, amma sai na gano cewa kaima kana jin irin abinda nake ji. Bansan yadda abubuwan suka ci gaba da faruwa ba a cikin zuciya ta ba, amma tun daga wannan rana na kasa daina tunaninka. Na tambayi mahaifina ko irin hakan zai iya faruwa a gaske, amma yace min bai taɓa samun labari ba a tarihi. Saboda haka sai naci gaba da bincike. "Haka na ci gaba da bincike amma har ila yau ban samu komai ba. "Amma daga baya nayi alƙawarin zan taimakeka ka samarwa mahifiyarka lafiya koda kuwa zan rasa raina. "Kayi sani cewa yanzu naga ka farkar da Izza mai ƙarfi acikin jininka, amma kana da buƙatar lokaci kaje ka sami horo ka gane yadda zaka sarrafa ta. Kuma idan ka ɗakko faɗa da Ururu yanzu baza ka sami wannan damar lokaci ba. Saboda haka nema na hanaka aiwatar da abinda kaso ka aiwatar a baya a wajen cinikin bayin can. Ni kuwa kaga ina da mahaifina dazai kare ni. Kuma kaima kasan saƙon da muka karɓa daga wannan allo, wanda kuma sauran ƙiris mu kammala haɗa wannan Izza. Zarar kuwa muka gama to babu wani Sarkin Jinzidal da zamu ji tsoro. "Armad.... " Nostaljiya taja hannunsa suka tsaya a gaban wata bishiyar giginya sannan ta matsa kusa da jikinsa tana murmushi, "Ina sonka Armad. Karɓi wannan," Ta kama hannun Armad ta saka masa wani zobe a jiki, "Ba lalle mu ƙara haɗuwa ba a wannan duniyar. Amma wannan zoben zaisa ka ringa tunawa akwai wata data taɓa sonka wai ita Nostaljiya. Ba jimawa mahaifina zaizo nan, kuma bazan so ku haɗu ba. Sabida haka ka shiga wannan ƙofa zata maida kai ƙasa ta uku. Nayi bincike na gano akwai wani sharri a tattare da wannan ɗan duba Babara, kaje kaga halin da mahaifiyar ka take ciki kafin ka ci gaba da neman wani Tarifil fakta wanda babu wanda yasan taƙamaimai inda yake. Idan kana so kaje kayi horo a shashin Ikwatora to akwai ruhi na a jikin wannan zoben zai nuna maka hanya. Akwai ajiyar abinci da abinci da shekarun Izza ɗari biyar aciki da mahaifiya ta barmin a lokacin da zata mutu. Idan kana so zaka iya amfani dasu." Ga dukkan alamu Noltajiya bata so taji amsar da Armad zai bata a yayin ta buɗe wata ƙofa ta tsafi ta tura Armad ciki ta rufe. Armad yana shiga ya waiwayo da niyyar yayi mata magana amma sai kawai yaji wani ƙarfin Izza na musamman yana zuƙe shi ciki kuma bashi da damar magana. Abu na ƙarshe da Armad ya gani shi ne kwalla guda ɗaya daga kowanne idon Nostalgiya na fitowa. Sannan kuma daga bayanta yaga wani mutun ya bayyana wanda ganinsa ma kaɗai yasa Armad yaji ruhinsa yana neman fashewa ya tarwatse. Ba komai ya jawo hakan ba illa Izzar wannan mutumi. Armad baya jira a gaya masa cewa wannan mutun shi ne Bihanzin mai dauwamammen sara kuma lallai ransa a ɓace yake matuƙa. Armad yaso a ransa ya fito ya tsaya a gaban wannan mutumi duk wani abu da zaiyi wa Nostaljiya yayi masa, idan ma kashe shi zaiyi yayi, amma dai kada ya sake ya taɓa Nostajiya, amma ina kafin yayi wani motsi wannan ƙofa ta ɓace dashi. ____ Sunan Nostaljiya zaku ga ya canja da ina saka mata Nostalgiya, sorry mistake ne saboda da english ina rubuta shi da Nostalgia so saina manta cewa saina juya 'G' ta koma 'J' Tirifil fakta ma zai koma Tarifil-Fakta (shima Triple Factor yake da english) Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 58: Sabuwar Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Bayanda Armad ya shiga wannan ƙofa sai yaji wata irin Izza mai

Chapter 2 of 13