Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 13
mai ɗauke da Izzar gidan Ururu ya bayyana a idanun nata tsahon daƙiƙa biyar kafin daga bisani ya ɗauke idon ya koma fari. Suwainah ta nufi gindin bishiyar dake kusa da ita inda ta ajiye kayanta, ta ɗauki robar ruwa tasha. Sannan daga bisani ta juyo ta fara wasa da takobin dake hannunta. Kai kace wannan takobi bata da nauyin komai, domin kuwa yadda take sarrafa ta tana juyata tamkar kawai takobin wani ƙari ne na hannunta. Haka dai taci gaba da rawa da wannan takobi har saida rana ta ɗaga, sannan ta fara shirin komawa cikin ƴan- uwanta domin karɓar horon safe. A dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya bayyana a gabanta, cikin tsananin zafin nama, Suwainah ta kawo sara da takobin dake hannunta. Amma ruhin Armad ko motsi baiyi ba. Ya bari takobin ta ƙaraso, sannan ta sari wuyansa, amma bisa mamaki sai takobin ta shige ta cikin wuyan tamkar babu kamai a wajen. Ruhin yayi murmushi tare da girgiza kai yana mai cewa, "takobinki baza ta iyayin aiki akaina ba." Suwainah ta ja da baya tare da fara kiran ɗalasimai. Amma a dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya ɓace daga inda yake sannan ya shige jikinta. Yana shiga taji tamkar zatai atishawa amma bata zo ba. Ta tsaya tana tunanin mai zatai amma a lokacin ne taji muryar ruhin yana mata magana. "Dani dake zamu iya taimakon juna. Ki taimake ni na taimake ki." Suwainah ta haɗe rai tana cewa, "Mai zaka iya taimako na dashi? Na gane ka, ba kaine wanda kuka zo tare da waɗannan mutane ba ƴan watannin baya. Dama sarki yana nemanka." Ruhin Armad yai kyaran murya sannan yaci gaba da magana tamkar baiji mai take cewa ba. "Zan iya baki ƙarfin Izzar da kike buƙata ki farkar da Ururu mafi girma a tarihi. Idan baki yadda ba tsaya na gwada miki." Ruhin Armad dai daya ɓalle yazo wannan tsibiri shi ne ruhin dake cikin Miyurar dake goshinsa. Hasali idan mai karatu bai mantaba wannan Miyura tana iya ƙarawa Armad Izza, kuma tunda Armad ya rasa ta ya daina samun wannan ƙarin Izza. A dai-dai wannan lokaci, tun kafin Suwainah ta amince, taji ruhinta ya girgiza, sannan izzarta ta fara juyawa. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 76: Alƙawarin Urúrú da Wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ---------- A dai-dai wannan lokaci, idanun Suwainah suka kaɗa sukai baƙi-ƙirin, ta fara ƙoƙarin fitarda da ruhin Armad daga jikinta. Amma ana cikin haka taji izzarta ta fara girgiza tana juyawa. Jikinta ya fara ɗaukan zafi, kafin daga bisani taji wani tsananin ƙarfi irin wanda bata taɓa jinsa ba. Nan take taji a ranta cewa indai za'a zo yin jarabawar rantsar da Ururu a wannan hali sai tayi nasara. Tana cikin haka taji muryar ruhin Armad na cewa, "zan iya baki izza sama da haka. Amma kiyi min alƙawarin zaki yimin abu ɗaya." Suwainah ta ɗanyi shiru na ɗan taƙi kafin ta yanke shawara. "Mai kake so?" Ruhi ya kada baki ya ce, "Fasahar sarrafa lokaci ta ƙabilar Ururu." Suwainah tai murmushi tare da cewa, "Babu wanda ya isa ya mallaki wannan fasaha idan ba manya goma na Ururu ba wato Ashura. Kuma mai kake so kayi da ita?" "Abinda zanyi da ita ni ya shafa. Kamar ƴadda abinda zaki yi Ururun ki ke ya shafa. Kuma nasan kowanne ɗaya daga cikin gidaje goma na Ururu suna da wannan fasaha guda ɗaya a rubuce a ajiye. Idan kina son Izza to ki samo min wannan fasaha." Bayan tsahon lokaci tana tunani ta kada baki tace, "Ba zanyi alƙawari ba har sai naga girman izzar da zaka bani. Zuwa ƙarshen shekarar nan za'ayi jarabawar rantsar da Ururu a doron-ƙasa ta farko. In har ka taimake ni na samu matakin Ururu na biyar zuwa sama to nayi alƙawarin samo maka wannan fasaha." Ruhi ya kada baki ya ce, "Na amince." Idan mai karatu bai manta ba, Uznu Ururu yayi amfani da irin wannan fasaha ya canja sakamakon Jinzidal wanda hakan ya bawa Armad damar wuce matakin Alkadar. Da irin wannan fasaha abu ne mai matuƙar sauƙi ruhin Armad ya koma jikin Armad ya kuma haɗe da gangar jikinsa. Amma a duk faɗin duniya ƙabilar Ururu su kaɗai keda wannan fasaha. Hasalima hatta acikin Ururu, manyan nan guda goma wanda ake kira da ASHURA su kaɗai keda iko su mallaki wannan fasaha. Ruhin Armad yana da tunani nasa daban dana Armad, sannan kuma abin mamaki kowanne yana zaman kansa ne a matsayi ruhi guda bawai rabin ruhi ba. A taƙaice madai abin ya saɓawa al'ada baki ɗaya. Domin kuwa tunda ake rayuwa a duniyar ƙasa bakwai ba'a taɓa samun wanda ruhinsa ya rabe gida biyu ba sannan kuma ya rayu, to amma wani sirri wanda har ƴanzu ba'a san menene ya saka Armad ya zamo mutun na farko da ya iya rayuwa duk da kuwa ruhinsa ya rabe gida biyu. Wani abun mamakin shi ne yadda kowanne acikin ruhin guda biyu keda tunani nasa na musamman. Misali, ruhi mai ɗauke da Miyura yana da wasu ilmummuka wanda ke ƙunshe acikin Miyura wanda shi Armad baima san dasu ba. Musamman tunda dama Armad bai gama kwarewa wajen sarrafa Miyurar ba. Ta haka nema ruhin yake da masaniyar wannan fasaha ta Ururu da kuma yadda zaiyi amfani da ita wajen komawa jikin ɗan'uwansa. To a wannan rana ruhin Armad da Suwainah Ururu suka ɗaura alƙawari zasu taimaki juna domin cimma burinsu. Duk da kuwa ruhin Armad baisan cewa burin Suwainah guda ɗaya ne kacal a duniya, wanda shi ne ta ƙarar da dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos da Bayajidda da suka rage. Sannan kuma ita ma Suwainah Ururu bata da masaniyar cewa wanda zai taimake ta burinsa ya ruguza gidan Ururu da Rukunan su ba guda biyu na Amri da Jinzidal. Suwainah da ruhin Armad haka suka ci gaba da kasancewa a wannan hali tsahon wannan shekara. Ruhin yana ƙara mata ƙarfin Izza, ita kuma tana ƙara dagewa wajen samun horo domin cimma burinta. ---------- A can duniyar ƙasashen-ƙasa kuwa, Armad ne tare da sarkin duba Babara ke ketawa ta cikin Bangon arewa domin zuwa wajenda za'a fara horar da Armad. Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya riƙe kefensa ƙam, ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma bayansa. Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar ba. Iska mai ƙarfin gaske ta cikawa Armad ido da hanci. Amma ana cikin haka ya fuskanci cewa Babara ko a jikinsa. Hasalima nishaɗi yake yana murmushi ganin halinda Armad ke ciki. Babara ya tafa hannayensa ya fito da wata ƴar tasa mai launin ja. Acikin ta akwai wani ruwa mai ɗauke da ɗalasimai na musamman. Kafin Armad ya farga, Babara ya watsa masa wannan ruwa. Ai kuwa ruwan na taɓa jikinsa yaji tamkar an zare masa rai, nan take Armad ya sume. Armad bai tashi farfaɗowa ba sai bayan kwanaki uku. Yana farkawa ƴa tsinci kansa acikin wani ɗan tanti mai duhu-duhu. Abu na farko da Armad ya fara fuskanta shi ne wani tsananin sanyi mai ratsa ƙashi, tamkar an sashi a tsakiyar tekun ƙanƙara. Ana haka ya miƙa kansa ya kalli wajen tantin ta wata ƴar taga, inda ya fuskanci cewa ƙanƙarar ce kuwa ke zuba da gaske. A sashin arewa doron-ƙasa ta uku, akanyi sanyi amma bai taɓa kaiwa inda ƙanƙara zata zuba ba. Saboda haka nan take Armad ya fara karkarwa, domin kuwa wannan shi ne karo na farko daya taɓa fuskantar irin wannan sanyi. Ba shiri ya fara tunanin a ina yake. Bayanda ya duba ya tabbatar jikinsa ba ciwo saiya miƙe ya futo waje. Wata iska mai ɗauke bushin farar ƙanƙara ta daki fuskarsa. Yai duba izuwa ƙafarsa ta hagu yaga inda ya taka ya nutse acikin ƙanƙara. Dukkan wajen yayi duhu tamkar lokacin isha saboda tsananin ruri da rugugin iska da ƙanƙara dake kaɗawa. Yayi haka zai juya ya koma tantin sai yaji an dafa kafaɗarsa. Inda ya jiyo amma baiga kowa ba. Nan take Armad ya zare takobinsa ta Wilbafos sannan kuma ya ɗaga hannunsa na hagu inda wata ƙatuwar ƙawanyar aradu ta bayyana. Wannan aradu ta haske wajen amma duk da haka Armad baiga kowa ba. Can yaji an ƙara taɓa shi, amma ta ɓangaren dama. Nan take yakai wawan sara wajen, amma kamar yadda yai tsammani bai samu komai ba. Armad na shirin ƙara kai wani saran yaji muryar Babara a kunnensa. "Baza ka iya gani na ba, saboda da idon ka kaɗai kake gani. Cikakkun ma'abota Izza suna gani kuma suna ji koda sun makance kuma sun kurumce. Lallai idan kana so ka rayu a wannan kurkuku na tsahon kwana ɗaya to lallai saika fara gani izzarka bada idonka ba. Kuma wannan shi ne mataki na farko na horonka." Armad yaji duk bayanin da Babara yayi, kuma dama Armad baiyi tsammanin zai samu horo ta sauƙi ba. Amma abu ɗaya ne bai gane. "Sarkin duba kurkukun gaske ko kuma salon-magana kake?" Babara yai murmushi tare da girgiza kai yana cewa, "lallai ba salon-magana nake gaya maka ba. Wannan ita ce kurkuku mafi girma da tsaro a duk faɗin duniyar ƙasa bakwai. Yau sama da shekaru dubu da ɗari biyar kenan da gina ta, amma tunda aka halicce ta ba'a taɓa samun wani ya fita daga cikinta taba ko sau ɗaya. Duk wanda ya shigo, ya shigo kenan har abada. Koda gawarsa baza ta fita ba." 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 77: Mubayi'a ta farko Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ------------ "Kurkuku?!" Armad ya faɗa cikin ɓacin rai. Yana niyyar ƙarewa Babara tanadi sai wani abu ya faɗo masa. Nan take ya ce, "idan a kurkuku nake to ai kaima a kurkuku kake kenan?" Babara yai murmushi inda dattijon takarsa ta ƙara bayyana. "Lallai kayi gaskiya. Idan kana kurkuku to nima ina kurkuku. Ko a baya dana gaya maka cewa na taɓa keta rabin wannan Bango a zahiri bawai Bangon na keta ba. Mu kanyi amfani da manya-manyan hatimai wanda ƙungiyar duba ta duniya ta samar domin kawo yara wannan duniya ta bango domin muyi musu horo. Amma a zahiri hatimin yana canja taswirar waje tare da mutanen dake kai, a saboda haka bawai cikin nan muke kawo suba. A taƙaice dai ni kaina wannan shi ne zuwa na wannan waje na farko." Koda Armad yaji haka saiya haɗe gira yana mamaki. Nan take zare ido gami da tambayar Babara. "Idan baka taɓa zuwa ba to tayaya kake niyyar fita daga wannan waje?" Babara najin tambayar ya sunkui da kansa ta yadda Armad bazai iya karanta halinda fuskarsa ke ciki ba. Lokaci ya fara tafiya, gari na ƙara duhi, sanyin dusar ƙanƙara na keta ruhin Armad yana sashi rawar ɗari. Can daga bisani Babara ya zube akan gwiwowinsa, kansa na kallon ƙasa cikin miƙa wuya. Abu na farko da Armad yayi tunani shi ne sanyi ne ya yiwa Babara yawa, ko kuma wataƙila ciwon ciki yake. Amma kafin Armad ya kaiwa Babara ɗauki yaga Babara ya zare doguwar wuƙa daga aljihunsa, ya yanki tafin hannunsa, inda jini ya fara kwaranya. Sannan yayi amfani da hannunsa mai jini ya cake sandar tsafinsa a ƙas. Armad ya rasa mai zaiyi tunani sai kawai yaji muryar Babara a kunnensa. "Ni Babara Bayajidda nayi mubayi'a ga sarkin mutane da aljanu Armad Wilbafos na uku." Idan ba daban tsananin imani da kafiya da Armad yaji a muryar Babara da lallai zai ɗauka wasa yake. Amma duk da hakan Armad bai gane abinda ke faruwa ba, nan take ya buɗe baki ya ce, "wai maike faruwa ne? Lallai kana sani ina jin kunya, kuma idan wannan ɗaya ce daga cikin dabarunka na horo bai bada ma'ana ba." Babara ya ja ɗan ƙaramin numfashi tare da ƙara sunkui da kansa yana cewa, "lallai wannan ba wata dabara bace. Ni Babara na bar muƙami na sarkin duba na dawo gefenka domin ganin cewa ka zama sarki wilbafos na uku. Ina fatan zaka karɓi mubayi'a ta." Armad yai farat ya ce, "to saboda me? Ni bance ina son na zama sarki wilbafos na uku ba. Sannan kuma ni ban masan abinda hakan ke nufi ba." Babara ya amsa a nutse, tamkar dama yayi tunanin Armad zaice hakan. "Zama sarki Wilbafos na uku ba abu ne da zaka iya zaɓa ba koda kana so. Abu ne da mutane su zasu gani su naɗa ka, kamar yadda yanzu nai amanna acikin raina cewa ka cancanci wannan muƙami. Kamar yadda na labarta maka a baya sarki Wilbafos na farko wato Aldaima Wilbafos da Wilbafos na biyu wato Eyriyon Wilbafos sune mutane na farko da suka taɓa yin yaƙi domin rusa rukunan Jinzidal da Amri. Kaima yaƙin da kake da rukunin Jinzidal yasa kabi sahunsu. Sannan kuma daɗin daɗawa kaima ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Na daɗe ina ƙin jinin siyarda marasa ƙarfi da ake a ban ƙasa a matsayin bayi dasa hannun manyan sarakunan duniya, amma ƙungiyar duba suka nuna min basa son shiga rigima da sarakunan Jinzidal dana Ururu domin a cewarsu babu wata nasara da zata futo daga ciki. A saboda haka na zaɓi na bi sahunka domin ganin an daina wannan kaba'ira ta siyarda mutane a matsayin bayi." "Hmmmm...." Armad yaja dogon numfashi Babara na durƙushe a gabansa yama rasa mai zaice. Can bayan tsahon lokaci ya ce, "to amma idan na fuskance ka kana da wani dalili na musamman da yasa kake ganin zan iya aiwatar da wannan abu. Domin dai baza ka ajiye babban muƙamin ka na sarkin duba ba kawai ka dawo ɓangare na ba tare da wannan ba. Zanso naji mene ne." Babara ya fara da murmushi wanda daga bisani ya juye izuwa dariya sannan bayan ɗan lokaci ya tsagaita tare da cewa, "lallai kamar yadda ake haifar duk wani ɗan ƙabilar Wilbafos ko Bayajidda ko Ururu ko kuma ƴaƴan sarkunan Jinzidal da Izza ta musamman kaima kana da taka ta musamman. Amma bazan ɓoye maka ba, lallai abu ɗaya tak da yasa nayi mubayi'a shi ne manufarka ta cimma Jinzidal. "Kada ka manta akwai wani yaro wanda aka haifa da baiwa irin taka kuma ɗan ƙabila ta. Nasan ka gamu dashi. Ana ce masa Ikenga O. Bayajidda. Lallai Ikenga yana da ƙarfin da zan iya yi masa mubayi'a to amma manufarsa ba irin tawa bace. Hasalima Ikenga tuni ya farkar da fasahar gidan mu ta Byajidda wato Takun-sarki, wadda Izza ce wadda ke matakin Ururu. Amma a halin yanzu kai baka farkar da fasahar gidanku ta Wilbafos ba ballantana asan wacce irin fasaha zaka samu. "Sanin irin fasahar da zaka samu shi ne zai nuna ko zaka iya karawa da Ururu da sarakunan Jinzidal. A taƙaice dai ina gaya maka ni Babara na ajiye muƙamina na sarkin duba a duniya nayi maka mubayi'a ba tare da sanin wacce irin fasaha zaka samu ba. Kuma na biyo ka cikin wannan kurkuku ba tare da sanin irin fasahar da zaka samu ba. Kai sani cewa irin fasahar daka samu ita ce zata nuna ko zamu iya fita daga wannan waje ko kuma anan rayuwarmu zata zo ƙarshe." Armad yai shiru yana sauraren Babara. Babara ya gayawa Armad cewa fasahar sa ta Ɗorawa da Wilbafosiyan-si wod-dans da Al-yaya duk ba nasa bane na aro ne. Da farko Armad bai yadda ba, amma daga bisani Babara ya labarta masa cewa kowanne kabila suma da tarin fasahohinsu. Amma kadan daga cikin yan kabilar suna iya farkarda fasaha ta musamman wadda zata zama tasu. Hakan bawai yana nufin wasu baza suyi amfani da ita ba. Sai dai kawai duk wanda zaiyi amfani da ita to kamar da aro zaiyi, kuma bazai taba kaiwa asalin karfin masu ita ba. Ya gaya masa fasahar Dorawa ta Hidaya ce ta ara masa, sannan kuma fasahar Wilbafosiyan-siwod-dans ta kakanka ce Zaikid. Hatta fasahar Al-yaya wadda bai taba amfani da ita ba ta aro ce, asalin ta daga gidan Maikironomada ta fito. A saboda haka Armad yana da bukata ya farkarda fasaharsa ta musamman tasa shi kadai. *** ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 78: Yanayin Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos --------- Armad ya numfasa tare da duban Babara cikin mamaki ya ce, "To amma duk da haka baka bayyana min dalilin da yasa ka zaɓi wannan kurkuku a matsayin wajen da zamu yi horo ba." Babara yai murmushi yana cewa, "sannu a hankali zaka ga dalili, ya shugaba na." Armad najin kalmar 'ya shugaba na' ya haɗe rai. A ganinsa irin kalmomin nan ne da yakan ji aljanu na faɗawa iyayen gidansu acikin littattafan yaƙi. Amma haka dole Armad Wilbafos ya karɓi mubayi'ar sarkin duba Babara, duk da cewa bai san haƙiƙanin mai hakan ke nufi ba. Washe gari suka cire tanti tare da nausawa cikin dusar ƙanƙara suka nufi gabas. Suna ƙara nausawa waje na ƙara duhu, ba daɗewa Armad ya gano cewa tsananin duhu ne yasa baya iya hango abinda ke gabansu. Babara ya dubi Armad ya ce, "A ganinka taya ya mutun ɗan adam yake iya yaƙar aljanu? Kasan dai ba'a ganin aljanu indai basu suka bayyana maka kansu ba." Armad najin tambayar ya tuno abinda Babara ya gaya masa akan yayarsa Hidaya wadda ke can tana yaƙar aljanu a wata duniya ta daban. Lallai kuma haka ne, tunda sai kana ganin abu zaka iya yaƙarsa. Armad ya girgiza kai alamun bashi da amsa, inda Babara yaci gaba da cewa, "To wannan shi ne dalilin da yasa na gaya maka cewa cikakken ma'aboci Izza bada idonsa yake gani ba. Kuma horonka na farko zai fara daga wannan." Babara na faɗar haka ya tsaya a tsakiyar dusar ƙanƙarar nan tare da kirawo waɗandu ɗalasimai a zuci, lamarinda ya bayyanarda aljaninsa. "Zaka fara horo da aljanina mai suna Ji-Inara." Aljanin ya kasance jinsin muridi, yana da farar haɓa doguwa da koren gashi wanda ya futo akan ƙahonsa guda ɗaya. Hannayensa kuwa ƙananu ne ƴan gajeru kamar na jariri sabuwar haihuwa. Amma ƙafunsa sunkai tsayin zira'i sittin. Yana sanye da farar alkyabba ta ƙasaita, kana ganin yadda yake ɗaukar kansa kasan wannan aljani yana ji da kyau. Koda rufe bakin Babara sai aljanin ya rusuna tare da miƙa gaisuwa. Sannan kafin ya ɓace wani ƙaton al'amudi ya bayyana a hannunsa. Babara ya numfasa ya ce, "Kada ka damu, bazai kashe kaba amma zaka sha wahala. Kayi duba izuwa Tsarin- ruhinka, yanayin me kake ji idan ka kalli Izzarka? Armad ya girgiza kai yana cewa, "ba wani yanayi da nake ji." Babara ya ce, "a'a dai ƙara dubawa da idon basira." Armad na niyyar cewa a'a amma wata zuciyar tace ya duba. Saboda haka ya rufe idonsa yayi duba izuwa Tsarin- ruhinsa inda yai tsinkaye da abubuwan nan guda uku: Izza da takobi da kuma wannan mutun-mutumi mai idanu ruwan ƙasa wanda shi ne a matsayin aljanin Armad da Uznu ya kashe. Armad ya maida hankalinsa akan Izzarsa domin jin wannan irin yanayi Babara yake faɗa amma baiji komai ba. Yana niyyar buɗe ido ya bayyanawa Babara sai yaji wata iska mai zafin gaske na tashi a hankali daga inda izzarsa take. Nan take ya fara mamakin shin dama wannan iska tana nan ne ko kuma yanzu ta bayyana, domin kuwa dai bai taɓa ganinta ba. "Naji iska mai zafi na tashi." Babara yai murmushi tare da cewa, "wannan iska ita ce yanayin Izzarka. Kayi sani cewa akwai yanayin izza da dama. Amma wanda aka fi sani sune yanayin zafi, yananyin hunturu, yanayin kaka, yanayin rani, da kuma yanayin damuna. Kamar kai kana da yanayin zafi ni kuma yanayin rani ne dani. "Irin wannan yanayi da kake ji ajikin shekarunka na Izza shi zaka yi ƙoƙari kaji ajikin wannan aljani nawa tunda baza ka iya ganinsa ba. Zan tafi nayi bincike akan sharrikan dake cikin wannan kurkuku da kuma hanyoyin da zamu iya ficewa, kai kuma zaka tsaya anan ka koyi jin yanayin Izza da aljani na Ji-Inara." Armad ya kyaɗa kai tare da amincewa. Lallai yasan cewa ba ƙaramin ƙarfi zai samu ba idan ya koyi wannan al'amari na Izza, domin hakan na nuna cewa zai iya faɗa da mutun ko aljan koda kuwa idanunsa a rufe suke. Indai zai iya jin Izzar dake jikinsu yadda yake jin Izzar dake jikinsa to lallai koda baya ganinsu zai iya sanin inda suke da kuma motsin da suke da kuma yadda zasu yi motsin. Ta haka babu wani abu da zai ɓoye masa. Armad na cikin tunani Babara ya ɓace ya barshi da aljani Ji-Inaru. Koda ganin haka sai aljanin yai dariyar mugunta tare da ɓacewa. Abu na gaba da Armad ya sani shi ne saukar wannan al'amudi a bisa doron kansa, ba tare da yasan daga ina ba. Ƙarfin dukan ya tayarda iska wadda tayi cilli da Armad cikin dusar ƙanƙara. Yana tashi yaga jini na tsiyaya daga cikin kansa. Babu aljani Ji-Inaru babu alamunsa. Kafin Armad ya gane maike faruwa yaji wata gudumar ta sauka a bayansa. Nan take yaji wata ƙara mai nuni da cewa bayansa ya ɓalle. Ba shiri ya zare takobi ya fara kai sara ko'ina da ina amma a banza, ko sau ɗaya bai samu aljani Ji-Inara ba. Baya ganinsa ballantana yasan inda yake. Nan take Armad ya gane haƙiƙanin abinda Babara yake so ya koya. Inda ya rufe idonsa ya kuma yi ƙoƙarin jin yanayin Izzar dake tashi daga jikin aljani Ji-Inaru. Armad baiji komai ba a karo na farko, lamarinda yasa ya ƙara karɓar wata gudumar. Koda Armad ya tabbatar aljanin nan baida imani kuma zai iya karairaya shi indai baiyi da gaske ba, saiya ƙara zage damtse. A kwana na goma bayan kimanin kowanne ƙashi na jikinsa ya ɓalle sau kamar biyu sai kwatsam Armad yaji wani abu mai kama da ruwa sanyi yana tunkaro shi ta ɓangaren dama. Nan taje yakai sara ɓangaren. Ai kuwa nan take yaji ya daki ƙarfe, saiga al'amudin aljani Ji-Inaru ya bayyana. Armad yai ihun murna tare da ƙara rufe idonsa, yana neman wannan yana yi. Amma kawai sai ji yayi al'amudin ya ƙara sauka a kansa. Amma duk da haka Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, ya tashi tare da ci gaba da neman wannan yanayi na Izzar aljanin. A haka dai Armad yai ta fama, wani lokacin yaji wani lokacin yasha tafka har saida ya gane haƙiƙanin mai ake nufi da jin yanayin Izza. A haka saida Armad yai wata uku yana faɗa da wannan aljani kafin Babara ya dawo. Lokaci lokaci aljanin zai bayyana ya tausayawa Armad tare da koya masa abu ɗaya ko biyu akan Izza kafin ya ƙara ɓacewa yaci gaba da tafkarsa. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan aljani Izzarsa ce mai wannan yanayi na hunturu. Ana haka sai Babara ya dawo, ai kuwa abu na farko da Armad yayi shi ne fara jin yanayin Izzarsa inda yaji ta da yanayin kaka, gab da saukar damuna. "Lallai kayi ƙoƙari." Babara ya ce cikin farin ciki. "Na gano mana hanyar fita, amma lallai saika farkarda fasaharka zamu iya wannan aiki. Saboda haka yanzu abu na gaba shi ne farkarda fasaha." Armad yai murmushi tare da cewa, "muje zuwa." *** Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe gari ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 79: Magajin Wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos *** Tuni Babara ya zaunar da Armad a tsakiyar wani hatimi, a ƙoƙarin farkarda haƙiƙanin fasahar Armad. Armad na zaune ido a rufe, wasu ɗalasimai na haske suna kewayashi. Lokaci yaci gaba da tafiya a haka. Tuni hankalin Armad ya gushe babu abinda yake gani acikin kansa sai haske. Ana haka wannan ɗalasimai suka fara cinye ƙasar dake kewaye da Armad. Ba jimawa sukai wani ƙaton rami mai kama da rijiya, inda Armad ya rufta ciki. Amma duk da haka Armad bai buɗe idonsa ba. Daga nan sai kawai wannan ɗalasimai suka kama da tsawa da walƙiya wanda suka juye izuwa aradu. Ba jimawa wannan aradu ta fara cinye jikin Armad. Armad na zaune ko motsi baiyi ba. Hasalaima tamkar ba jikinsa ke ƙonewa ba. Ƙafafunsa ne su suka fara cinyewa izuwa toka, sannan sai gangar jikinsa, kafin daga bisani hannayensa da wuyansa da kansa. Armad ya ƙone ƙurmus acikin wannan rijiya amma ko tari baiyi ba. Shima Babara na zaune a wajen rijiyar bai motsa ba. Anma duk da haka wannan ɗalasimai masu bada walƙiya da aradu basu tsagaita ba. Hasalima juyewa sukai izuwa launin ja, sannan nan take walƙiyar ta fara tsiri tana sama har saida ta taɓo sararin samaniya. Ba shiri wani baƙin hadari ya taso mai ɗauke da aradu launin ja. Samaniya ta fara rugugi tana kaɗawa tamkar za'a saukar da ruwan azaba. Amma duk da haka

Chapter 7 of 13